Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

son daya fite da daya ko? Irin wa'inda basa tsoron tashi da shanyayen jiki ko yayane?

Gannin ta kure shin nan ya daka shi lumshe idannuwansa yana ayana' shikenan, kasheni zasu yi, zuciyata ba zata jure ba'

Baki ta murguda tana sake rufe jikinta ta ce" Wannan kayanka ce, da ita ko ba ita duka lamarinka ne, ni ban sani ba gaskiya, na UMMARma ni ba komai na sani ba, kamar dai inaga harda kwartanci tana yi!"

Tana gama fada ta mike tana jan bargon hadi da neme nemen atamparta a ranta sai mitar abinda bata san dalilinsa take yi ba...........................................
10/5/22, 08:44 - Buhainat: *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍?*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*


🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻
*OUMOUGHLOUK ITIBEL*
_(ZAKIN SARAKAI)_
🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻

_FREE BOOK_

*Na*


*SAJIDA NIGER*





5️⃣8️⃣



"Wani irin kwartanci kuma?" Ya fada yana juyo da ita bayan ya mike

Lululu din da take ji ya sakata dan jinginuwa da jikinsa, muryarta cen ciki ta ce" Juwa nake ji ASADEEK, ina so na je kusa da Innata kafin hukuncinka ya same mu "

Shiru ne ya wanzu a wajen na dan lokaci, a hankali ya dora hancinsa a saman kanta yana sinsina , muryarsa cen ciki ya ce" Me yake hadasa maki juwa ne? Ko baki da lafiya ne?"

A hankali ta dora kanta a saman kirjin nasa tana sake lunshe idannuwanta, kanshin jikinsa daban ne, kanshin jikinsa mai dadin gaske ne, bata taba jin kanshi mai sakata jin nutsuwa irin haka ba, a hankali ta ringa dan matse kaffafuwanta, domin irin abinda zuciyarta ta raya mata daga jin kanshinsa sai da ta ji a ranta kamar ta zama yar iska fa?

Muryarta a raunane ta ce" Walahi ban sani ba, ni dai dazu da na tsorata ne na jita sosai, dama ina jinta yan kwanakin nan ama ba wani sosai ba , inaga idan raina ya bace ne nake jinta"

Hannunsa dayan ya saka ya rungumeta sosai a kirjinsa, ya karasa saman kujera da ita ya zauna tana saman kirjinsa
Idannuwansa ya lumshe tana kwonce a kirjin nasa, bai san dalilin da ya sa yake ji a ransa a kanta yana iya jure komai, har ji yake yi koda da amincewarta ta amshi magani dan t kashe shi zai iya yafe mata, kome yasa? muryrsa a sanyaye sosai ya ce" Kin san UMMA, tamkar mamanmu muka dauketa, bama kamar Auta, idan ani abu ya fito Auta zata fi kowa shiga a halin tashin hankali ko?"

Kanta ta dago tana kallon lebensa, tun dazu ranta raya mata yake yi ta kama ta yi ta tsotsa , bata san dalili ba, ita dai ba yar iska ba ama kuma abu irin wannan na mata yawo a tunaninta na kimtsatsiya?
Kan nata ta maida da sauri dan kar ta aikatan, a hankali ta ce" Aa, Auta ta fi kowa shiga halin matsi sanadiyar matar da kake kira UMMA, mai sunnan maman Aba ta fi kowa shiga tsanani a tare da ita, sai ko matarka, kaima ka shiga ama ba a jikinka bane ai..............................."

"Kina nufin, kin san da abinda ke jikin HUZNAH?, Kina nufin shima aikin Umma ne? Kina nufin itace ta saka bana iya shigar matata?"
Matsar da ya yiwa hannayenta, da furucinsa suka karra zaffafa zuciyarta

Tana kallon idannuwansa ta ce" Cikani "

Sai a lokacin ya kula ya mata matsa mai dan karfin da take iya yi mata rauni

A hankali ya sasauta mata , ita kuma ta mike ta karasa ta dauki kayanta ta kabe ta saka abinta ama ta dunkule pant dinta ta dauki dan kwalinta ta kabe ta daura sannan ta juyo ta ce" Babu iyayena a ciki, ko me zai tardoni ya sameni ni kadai , idan da hali dan Allah ka barni na je Tanus dan neman iyayena!"

Dagowa ya yi yana mai gardama da tunaninsa cewa yar gidan Hindu ta yiwu tanada aljannu , a saukake ya ce" Babu inda zaki tafi!"

Ja ta yi ta tsaya tana rike kugunta ta ce" Kana ji fa aka ce ba'a san inda inna take da aban birni ba?"

Baki ya tabe yana sake kallonta ya ce" Eh , kuma nace ki je ki yi zamanki a dakinki, saura idan an jima kar ki dawo turaka ni sai in zo tunda na matsu"

Wani haushi ya karra rike mata wuya, haka fa, tunda ita shine aikinta ai dole ya ce haka, ba zata zo din ba a yi gunduwa gunduwa da ita!

Sai da ta karasa kusan katon hotonsu shi da HUZNAH ta zubawa hoton ido, haka kawai ta ji hoton ya mata mugun muni a idannuwanta, dan haka sai ta janyo kujera ta taka tsaf ta sauko shi kasa ta kifa shi sannan ta zagaye shi tana zabgawa hoton harara ta fice

Idannuwansa a ware yana kallonta har ta fice ta bar wajen ranta a bayane da bacin rai, a fili ya samu kansa da sakin murmushi ya mike ya karasa yana lekenta harta sauka ta nufi corridor din , hakan ya saka shi sakin wani murmushin ya girgiza kansa ya juya ya nufi wajen wayar tafida gidanka ya shiga neman bangaren UMMA

A kalla ya yi kira ya kai sau biyar sannan aka daga , aka kuma yi shiru

Shima shirun ya yi har sai da ya ji muryar Umma kasa kasa tana tambayar waye? Hakan ya saka shi a kausashe ya ce" Bata wayar"

Jiki na bari wace ta daga wayar ta mikawa UMMA wace ta ji kamar zata summa daga tsayen da take

Muryarsa ya sakawa alamun tashin hankali ya ce" UMMA, taushe rabonki da Bafana? Ina nufin kun yi waya da su a kwanakin nan?"

Cikin UMMA ya yi wani irin murdawa, zufa ta shiga karyo mata, muryarta na rawa ta ce" Wa, wa, wani abu yace na yi ne?"

Lebensa ya dan dantse, sai kuma ya saki ya ce" Kamar yaya wani abu Ummana, wani abu ya faru ne ban sani ba? Yanzu Bahija ta zo tana kukan wai ba'a ga Bafa da sarauniya ba, wai an sace su, ni na rasama me zancen nan yake nufi, ama ganinan zan sauko na ji meye hakan kuma? Kafin na zo zan saka sarkin yanka ya fara yin gaba , inaga zan je tanut din yanzu yanzu in sha Allah, dan bana son karamin rikici irin na rebelle din garin nan!"

Salama zata ce? Ko karin rikicewa da kidimewa? Ita dai ta ji wani abu mai sunna sasauci a kan dazu na zulumin an kaita gaba shikenan tata ta kare, a yanzu kuwa sai take tunanin tabas sunna iya gujewa hukuncinsa, hakan ya sa ta nuna rikicewarta a bayane harda su fadin bara ta shirya da ita za'a tafi, ba zata iya zama a nan ya tafi shi kadai ba, wani irin sacewa? Sarki guda? Lalle da an tsokalo tsuliyar dodo walahi!

Katse kiran ya yi da wayar a hannunsa, sai kuma ya yi murmushi yana girgiza kai kasa ka sa ya ce" Ta yayama zan tashi kai tsaye na sawaka maki hukuncinki? Dole ne ki fuskanci fargaba, tashin hankali na yau daban na gibe daban, dole ki gane ba sai an kasheka kadai bane aka sakaka a uku, babu abinda ya fi tayar da hankali irin fargaba, da rashin sannin abinda ake ciki, in sha Allah zan sace sun summa a yau da taimakonki zan kawo ku na saka ku a halin rayuwa ko mutuwa!, Sai kun fadi su waye ku da bakunnanku! Da ASADEEK kuke magana!"




Umma kuwa a rikice ta ringa doka wayoyin sarauniya da shi sarkin da kansa

Da kyar ta samu aka daga, hankalinta a cakule take sanar masu abinda ya faru, har kiran da ASADEEK ya yi mata

Bafan Tanus da ya ji hankalinsa na neman tashi da lamarin ya ce" Kina nufin, a tunaninsa mune aka sace?"

Umma ta tabatar masa da eh

Ya sake cewa" Yanzu nufinki zamu fita mu buya har a kashe shin ko me kike nufi?"

Umma dake share zufarta ta ce" Haka nake nufi, yanzu haka da shi da ni zamu taho bincikar abinda yake faruwa, zan san yadda na yi aka bani madararsa na zuba maganin nan a ciki, gwara idan ya zama gawa mu san yadda zamu batar da dan balaki!, Bari ka ji ba zan taba yarda ya ritsa da Ni ba, muryarsa kadai abin tashin hankalina ce, bale ya kamani da mugun laifi!, Bana ciki, ina so a yau yau na kashe shi idan ya so ko me zai biyo baya ya biyo! Na rantse sai na zuba masa gubar nan a yau yau, ka shirya hawa kujerar garin AGADAZ, ka shirya yaki da du wani dan buro'uban da zai nuna bai san zancen ba, ka shirya birne gawa biyu a yau domin ina kashe shi zan kashe MARIYATU kanwarsa idan ya so sauran sai na wulakanta rayuwarsu, sai na yi fatafata da rayuwarsu kafin na halaka su, yadda ta sauke tafin hannunta a fuskata sai ta ci kashina da bakinta!, Maza ka shirya ka fita da banzar nan, saura ku yi yadda za'a gane, kubar abin a matsayin saceku aka yi, kowa da kowa ya gane haka kafin mu iso!"





...........Baki dadara fa buga wasan ba kennan?..........uhum wanda baya jin bari sai ya ga uwar bari😂😂😂😂😂😂........ READERS MUN KUSA GAMA SHI FA🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣☹️☹️☹️☹️☹️☹️☹️
10/6/22, 23:39 - Buhainat: *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍?*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*


🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻
*OUMOUGHLOUK ITIBEL*
_(ZAKIN SARAKAI)_
🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻

_FREE BOOK_

*Na*


*SAJIDA NIGER*





5️⃣9️⃣



Idan baka iya kama barawo ba, shine zai kama ka
Umma ta yi shiri cike da tabacin za'a yi tafiyar nan da ita bayan kamar awa biyu ta yi fita ta kai sau uku, ama shiru bata samu ganninsa ba, hasalima kofarsa bakin dakaru ne ta gani wa'inda ba zata ce ta taba sanninsu ba, sun nuna mata barci yake yi, a irin lokacin da tuni ya kusa karasawa garin TANUT ba tare da sanninta ba
Yan magana sun ce ice da zafinsa ake dukansa
a lokacin da yake tunanin yana tare da mutanensa na hannun dama a irin lokacin aka ainahin sace shin daga shi har iyalinsa , watau shi da matarsa da kuma yarsu mace cilo inda aka sheka su a duniyar barci aka yi doguwar tafia da su wace basu gane komai ba aka kai su boyayen ma'adani mai dauke da dakunna masu duhu da tsayi tamkar gidan yari, an wadatasu da dukkan abunda zasu iya bukata kama daga wajen kwonciya katifu biyu, abin rufa, buta , darduma, ruwa, abinci, sai dai ba'a zuba masu kayan shayi ba, shayi irin na bugaje, shayin da buzu na iya shiga halin kaka naka yi idan ya yi wuni daya tal bai sha shi ba, abinda ya fi kayan maye saurin rike zuciyar buzu, domin abu ne da ya rayu da shi tun yana karaminsa, ya zamto masa jinnin jikinsa zai fi gane ya wuni bai ci abinci ba da ya wuni bai sha shayi ba!


A cikin dokar dajin suka tsaya , motoci ne irin Mitsubishi manyan nan masu baya bude na shiga sahara, a kalla sun kai su goma sha daya domin a wajen sun hadu ne da manyan ikon kasa wa'inda ya yi kiransu a hanya ya kuma sanar masu ga inda yake so su hadu, domin ko ba komai bafansa SARKI ne, koda garin da yake mulka dan karamin gari ne bstansa bat lokaci daya ba abu ne mai sauki ba bale garinsa ba karamin gari bane fit, dole sai an yi zaman nan dan su ganewa junna

Kowane shi yake kallo, inda yake tsaye cikin shiga ta farin yadi kall, ya nada rawani na farin rawani kal, kafarsa sanye da takalmi baki sidik , irin takalmin nan mai yar siririyar igiya , hakan ya sa ake gannin fara kal din kafarsa da kuma wajen tsintsiyar hannunsa, Dinkin simple dinki ne ba gari da yar ciki ba, dinki ne irin sakaken nan ba mai lafewa a jiki ba sam, sai dai duda haka damatsunnansa a rike suke tak a jiki sun kama shi tak kakar zasu tsage

Tunda ya tsaya fuskokin wa'inda ke laye yake bi da kallo, irin kallon nan na son karantar kowa abinda yake kan fuskarsa, domin ai labarin zuciya a tambayi fuska
Sarkin yanka kuwa a tsate yake a gefensa, tsayuwarsa irin ta a mutun nan, shi kadai sai ka ji ya fitar da huci kamar bijimin sa , idannuwansa kuwa ba zaka so ka yi ido hudu da su ba a irin wannan lokacin

A kan fuskar sarkin DOGON DUTSI ya sauke dubansa, sukaiwa junna kallo na kirki sannan ya dan sauke murmushi kadan kafin ya sake fuskantarsu a nutse ya ce" Ba zaku min tambayar dalilin dauko shi da na yi ba? Ko ba wannan ke damunku ba?"

Elhaji Idriss ne ya sauke numfashi a nutse ya ce" Allah ya karra maka lafiya UMUGHLUK ITIBEL, dole hankalinmu zai tashi, wannan fadan cikin gida ne ko na waje? Munada hurumi a ciki ko bamu da shi?, Me yasa harda matarsa da yarsa? Kuma a ina ka boye su?" Me suka yi da tsanani har haka?"


Da girmamawa, da kuma gannin girman Elhaji Idrisss a tausashe ya ce" Alhamdulilah, tabas wannan rikici ne da ya hade rigima biyu, ta cikin gida da kuma ta waje, kusan shekara hudu kennan da na kama takardun dukiya ta marigayi sarkin Agadaz, dukiya mai tarin yawan da aka nema aka rasa, har aka so yin rigima a kan hakan ama abin ya yi tuwo ya yi miya, aka zauna a haka nima na yi shiru na zuba ido, ba dan ban san adadin dukiyar ba, ba kuma dan ban san a ina da ina suke ba, sai dan na san ko waye yake rike da dukiyar nan zai falasa kansa wata rana, ko ya cita a hankali ko da garaje dukiya ce da bata boyuwa, dole wata rana sai ya falasa kansa da kansa, domin zinari ne na yankin rijiyar wuta ta gabas, wace take ta ainahin jinnin marigayi, ya gada take dauke da takardu har kwaya tara na nan Nijar da manya manyan kasashe masu fitar da Zinariya, wa'inda suka saka hannu cewa rijiyar nan zata zamto gado ne wa Namiji , idan sarki ya samu maza da yawa tasu ce, idan kuwa mata ne kadai da shi zata zamo ta talakawa ne!, A lokacin da aka zo rikicin rijiya da takardunta tun a lokacin da na sanarwa sarki cewa ba zan taba zaunar rijiya ba, ta talakawa ce!, Tatalin arzikin kasata ce, tun daga lokacin abubuwa suka ringa bilowa, karshe bayan rasuwarsa aka nemi takardu harda na gidan azurfa dake cikin kauyen Ingal ba'a samu ba! Daga wannan ranar na yi shiru da bakina, ama kuma na damu mutanena na daji na baza su du inda na san akoy dukiyata da ta talakawana na basu damar dora kiwo, noma da daba, ta yadda sako zai same ni a kan gaba!"

Ya dakatar yana duba agogon hannunsa, ya juya wajen da su SHEIK ke tsaye, ya sake juyowa ya dora da fadin" Ya yi kokari sosai, domin ya dauki shekaru bai je ba, bai aika ba, sai dai mun fi shi juriya da hakurin jiranshi, tunda mu a wajenmu muke, kuma Allah ya ara mana aron rai da lafiya , Bai fara turawa ana masa bincike ba sai nan da shekaru hudu da suka shige, a lokacin yake dan bincikensa, har ya yi rashin wayon zuba mahaukatan karya jefi jefi suke rayuwa da mu dan su gane me muke ciki, a ciki akoy wannan wanda shine baban yaronsa na hannun dama, kuma shine wanda ya tsorata ya sake shi da wuri ya kama mu cikin hikima yake masa aiki yana zayane mana komai, duda ya iya takunsa, ba lale ka san cikinsa ba,........na kayade maku, mutuwar sarki ciwon ciki ne wanda kowa ya sanshi da shi, ama mutuwar marigayiya guba ce mai kumbura ciki, ita ta kashe uwata!"
Ya idasa a kausashe yana kallon yadda suke zarro ido , wasunsu har sunna jan rawani baya sunna kallonsa

Da tarin mamaki Kambori ya ce" UMUGHLUK, kar ka ce da mu Asarki nada wani abu a cikin hakan?, Idan haka ne ka fitar mana da maci amana mu sare kansa da hannayenmu, domin ba zamu taba bari irin haka ya wuce banza ba!"

Daga gefensa , sarkin garin Dosso a tsanake ya ce" Bama wannan ba, yaya nake ji an ce da yarsu, a sanina yarsa mace daya ce jal, kuma ba ita bace ka aura kwananan? Ko ka kamata da wani mugun aiki ne?"

Ajiyar zuciya ya sauke a nutse ya ce" ba ita suka aura min ba, wata suka bani a matsayin ita ce"

Wannan abu shi ya karra girgiza masu zuciyoyinsu, domin dai babu wanda bai san abinda hakan yake nufi ba, tabas bayan kishirwar arziki , ta mulki ta shiga, idan kuma za'a bi tarihi dama mulkin haye ya yi masa , dan yanzu yana harin babar kujera ba mamaki, babu wanda mulki ya fi wahalarwa kamar wanda ya yi masa shige da karfi ko ya siya,

Yawanci sun ajiye maganarsu ne kan ya yi yadda zai yi da shi da du wani mabiyin bayansa, watau koda hukuncin kisa ke kansa, ya aiwatar sunna tare da shi
Kwaya biyu ne suka nema masa sasauci, sasauci a baki sai dai baban tashin hankali a zuci, domin sun sani da a kwacewa asarki sarautar nan gwara a kashe shi, sun nema masa sasaucin hukunci ne cewa idan har shi ya kashe sarauniya a kule shi a kaso cikin bayin da ya saka kaso na kulin rai da rai, yarsa kuwa idan bata da wani laifi ana iya sakinta, ita da mahaifiyarta, in kuwa suka tsaka tsandam wuka ta sha jinni kawai


Da wannan suka rarabe da tsayuwar jejin, sannan ya sake kadaicewa da SHEIK

Sosai Sheik ke karra tausarsa, ya san shirun nan nasa ba yana nufin baya jin ciwo bane, ba kuma yana nufin ya kyale bane, duda ya fara kai duka yana tsoron abinda ya boye a karkashin zuciyarsa

Dan ajiyar zuciya ya sauke, a sanyaye ya ce" ban san ta yadda zan binciki HUZNAH ba, ina matukar jin kunyar sanarwa HUZNAH cewa a wajenta kadai nake ba namiji ba, haka kawai nake ji kamar nine ban yi mata adalci ba, sai nake ji kamar ni na yi sake wani abin ya sameta, idan har ta ji dacin hakan yaya zan rarashets?, Idan ta yi kukan hakan me zan ce mata?, Ina matukar jin kunyar amsar da zan iya bata "


Da tarin tausayawa Sheik ke rarashinsa, yana karra nuna masa komai na duniya mukadari ne, in sha Allah itama ba zata dauki komai da zafi ba, kasantuwar abu a haka kuma Allah ya hukunta bata da yadda zata yi, fatana Alllah ya sa akoy maganin abin, domin idan babu maganin abin kam matar nan in har wannanma itace gaskiya tana da kin jin tsoron Allah, to ina zata kai hakin mutun ne Fisabililahi?


_________________________________


A bangaren NADIRAH kuwa tana karasawa bangarenta ta tarar da Hindu da Auta a zaune rike da carbi sunna ja, hankalinsu a kan kofa kowane kana kallon fuskarsa zaka ga tsantsar tashin hankali a kan fuskar tasa

A zabure Hindu ta mike tana kallonta, a rarabe ta ce" Yar indi yaya dai? Zo mana kar ki fadi"

A sakalce ta karasa ta rungumu a jikin innarta, wace ta silale da ita saman kujera
Muryarta a kurya ta ce" Auta taimaka min da ruwa , ama dan Allah matsa min lemun tsami da siga a ciki ko na ji dadin bakina, kuma ki taimaka min da gorin innata a saman gado ko na daina jin tashin zuciya?"

Innarta dake rike da ita ido ta zuba mata, irin yadda take ta langwui ya sakata zarro ido, ta kalli Auta, ta kalleta

A kausashe ta ce" ke dan ubanki ki sanar min abinda ya faru dala dala komai da komai da kika je cen, indi kin sanar masa su waye mu?"

Da sauri ta kalli innarta, sai kuma ta kalli Auta, wace ke tsaye tana kallonta itama

Kai ta sada tana murza yan yatsunta, hakan ya saka Hindu idasa kwashewa da salati tana rafka tagumi ta ce" Yaushe aka ce za'a kashe mun?"

Auta ta kalleta a tsorace, hakama NADIRAH,
NADIRAH ta ce" Kashemu kuma?"

Hindu ta nuno mata hannu a watse ta ce" Kashemu mana dan ubanki, haka ai yake hukunci, ke yanzu idonsa idonki kika ce masa mune yan ta'adar da muka zo kashe shi ko?"

NADIRAH ta turo baki, sai ga hawaye shap shap shap ta shiga sharewa tana kallon innarta, da hannunta ta ce" Inna, bama wannan ya fi yi mini ciwo ba, wai sai ya ce NADIRA gatsau, ita kuma yace HUZNAH, innata me na masa da zafi? Inace in kina kirana har lumshe ido kike yi, kece kika ce du duniya bakya jin dadin sunna irin nawa ko? Wai wani Matata ko kunya baya ji s matsayinsa na abanku!, To ta Allah ba ta mutun ba, da yace kar na kuma masa maganar Aminu yanzu na fara dan Allah ya kasheni ya huta!, Yo inama dalili wai Fisabililahi ashe ya san wacece ni nake zaune tun sarai yana wani ce min Bahija, bahijar nan sai na ci uwata ni din nan innata Allah kuwa, kuma mu jira shi ya zo ya fadi hukunci na san dai bai fi saki ba, ya sakeni mu karra gaba ba cuta ba cutarwa ah to!"

Auta yadda ka san zata kifa haka take kallon salamamen tuburaran bakon iya shege a gaban idannuwanta

Bata idasa tantancewa ba ta kifa din a lokacind a Inna da zafin rai ta ce" Cuta ta nawa kuma dan ubanki da cikin ina zamu je? Ai du tsiya mun liku sai dai hakuri kaska a jikin kare?..........










Wayo udona😭🥹🥹🥹🥹
10/10/22, 08:37 - Buhainat: *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍?*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*


🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻
*OUMOUGHLOUK ITIBEL*
_(ZAKIN SARAKAI)_
🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻

_FREE BOOK_

*Na*


*SAJIDA NIGER*





6️⃣0️⃣




A kusan tare muryoyinsu ke tambayar CIKI? idannuwansu a waje

Shiru inna ta yi tana kallonsu, bama kaamar y'arta da ta tino irin nata haukan, watau nufi irin na nata cewar zamanta da zaki na dan lokaci ne, hum, koda yake tama kyaleta ne, da kanta zata cenza ra'ayi tunda gashinan karara ta nuna bama kashe bane ya fi bakanta mata irin runanin yana kiran dayar da mene, dayar kuwa da me?

NADIRAH na kallonta a tsaye , muryarta a sanyaye ta ce" Innata ciki?"

Innarta ta fuske sosai, a maze ta ce" Ke kila wa kala ne"

NADIRAH ta sake zuba mata ido, sai kuma ta kalli Auta
Ta dan jima ta kalli wannan , ta kalli wancen, sai kuma ta juya ta nufi dakinta jiki ba karfi kwata kwata

Tana shiga Inna Hindu ta zauna tana cire zumbulelen hijabin kashe su ta ajiye carbin a gefe tana sauke ajiyar zuciya sannan ta kalli Auta dake kasa tun faduwar nan ta ce" Taso mana autata, yar karama , yan matan Hindu gajera, zo nan"

Daria ce ta kubucema Auta, a dan rarafe ta karasa dan kafafuwanta har kamar sun mutu ta zauna tana dora kanta a saman cinyar Inna

Inna a hankali ta ce" Tabas ciki ne da ita, sai dai dan Allah ku kama bakunnanku, kar ku saki maganar nan ta fita yanzu, domin cikin bai wani yi kwari ba, kai ko kwarin ya yi ku barshi ya rayu a boye, idan Allah ya budi ido du mai son ganni da wandama baya so zai gani, ke kin san a inda Abanki yake, kin san su waye ke zagaye da shi ko?"

Kuka ne ya kubucewa Auta, kuka mai tsuma zuciya, hakan ya saka ta rungume kafafuwan inna sosai tana zubar da hawaye
A sanyaye ta ce" Alhamdulilah, ko yanzu raina ya bar gangar jikina

Please Login or Register in order to submit comment