Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gudu, harma a kama shi a cikin tarkonsa.........., Babu abinda na sani, ba kuma na son sani, a ganina bai cencenci ki ci gaba da rayuwa kamar wata yar tatata ba, ki yi aiki da iliminki dan tsira da mutincinki!"

Daga hala NADIRAH ta muke ta shiga tatare kwanonin nan tana nufar hanyar da ta tabata ko yayane a nan zata samu kicin
Ai kuwa a nan din ta samu kicin din da ta zama kamar mahaukaciya wajen kallo, domin kafin ta fito sai da ta sha kallo har kamar zata kwana a wajen

Kayan ta ringa kwashewa tana kaiwa, sauran madarar da ba'a sha ba kuwa ta tsiyaye a kofi ta sake kafa kai ta aikata sannan ta kai kofin ciki ta fito ta nufi falo hankali kwonce dan tafia


A zabure Auta ta mike daga zaunen da take, kamar an tasheta a barci ta biyo bayanta da sauri tana fadin" Aunty, Aunty, Aunty BAHIJA "

Har ga Allah bata tsaya ba dan ba sunnanta bane BAHIJA sam bata gane da ita take ba sai da ta karasa ta ciro alkyabarta ta ankara itace BAHIJA fa, hakan ya sa ta juyo tana murmushi ta ce" Ni ba zakina ce min Mama ba?"


Rubutun da yake yi a computer ya dan dakatar , tunda Auta ke kwala kiran nan ya bisu da kallo har furucinta da ya saka shi jin kamar ta gaura masa mari, Mamah?, Sai ya samu kansa da dagowa ya dan zuba masu ido, zai iya rantsewa Auta ta girmi wannan abar, ama ta dubi idannuwanta tace ta ce mata Mama? To a kan mema?

Itama Autar abinda ke ranta ta dan kawar tana dubanta ta ce" Mamah?, To ke ba auntyna bace?"

NADIRAH ta rage murya tana dage girarta daya tak, dayar kuwa ta yi kasa da ita ta ce" yo mana, matar Abah ba mama bace?"

Auta ta saka hannunta ta rufe bakinta tana yar dariyar da ta saka yayanta kureta da ido,
Sai kuma ya saukar da dubansa kan hannayensu, a lokacin da NADIRAH ta saka Alkyabar ta ja hannunta ta ce" Mu je "

Maimakun ya ga Auta ta kiya, kamar yadda take yi a lokuta da dama idan yace ta je Umma ta rakata, ko yace ta je HUZNAH ta rakata, sai ya ga ta yarda a bakuwar fuska, ko dan ta ji ance har uwarsu ce zata saki jiki da ita?, Subahanalah idan haka ne kuwa ya zama wajibi ya dauki mataki da wuri wuri, domin ba zai yarda ta saki jiki da matar da ba ita bs, ajema zuwa ta yi ta cutar da ita a banza a wofi, gashi Auta ba lafiyar kirki ba ta yarda da ita a banza da wofi

Yana ji yana gani suka fita, hannayensu rike da junna, bai hanna ba, bai yi ihun da yake ji yana son masu ba, ya kame girmansa ne dan kar ya cika hayaniya a gaban yarinyar ta raina shi, rainin da ta yi masa a yanzuma ya isa, ama in sha Allah a gobe zai yi kiranta daga shi sai ita ya ja mata kashedin da zata fahimta, ko da me ta zo ya fita iyawa, ya sarara mata ne dan ance ya saurara, da ba dan shi ba ta yiwu da yanzu tana kurkukun azalumai!

___________________________________

"Ta yaya zan iya ganar da yayana ni ba mahaukaciya bace?, Dan Allah ki fada min?" Auta ta fada a lokacin da suka karasa bangarenta

NADIRAH dake bin falon da kallo, bai cika hayaniya ba, haka kuma da dan kwaliya irin na yara ƙanana, kayan dakin dai gasunnan dai, tarkace sai hamdallah

Kallonta ta yi da mamaki ta ce" Haka kike son dakinki ya kasance ne?"

Auta ta bi dakin da kallo, kai ta girgiza ta ce" Umma ce ke sonshi haka, wai tace tunda baki da hankali a zuba min abubuwam yara zan fi sakewa, kuma du ta cire hotunan iyayenmu tace a boye kar su ringa rikitani"

NADIRAH ta gyada kai, zuciyarta cike da mamakin matar da makircinta

Kasa kasa ta ce" Ki duba ki gani, kina iya sakawa a cenza maki kayan, a hankali kuma sai ki san ta yadda zaki biyowa yayanki, dan ni ba sanninsa na yi ba ai kin gani, ama abinda zaki fara yi shine daina hadiye maganin nan, idan an baki, ko waye ya baki, ki makale shi a kasan harshenki ki sha ruwan ki faki ido ki cire, ai kin fahimta ko? Kuma gaskiya ki daina irin kallon na kamar mai farfadiya inaga harda shi da kike yiwa yayanki ya yarda kin tabu"

Murmushi ya subucewa Auta, domin a yadda Nadirah ta fada din abin murmushin ne

A hankali ta zauna ta ce" Dan Allah ki kwana a nan kin ji?"

Ido NADIRAH ta zarro, sai kuma ta girgiza kai ta ce" Innata na jirana, kun ga, sai da safe"

Daga haka ta fice, tana fitowa sarai ta hangi mace ta yi saurin bada baya, irin daga tsaye da take tana hangen bangaren AUTA ta juyar da bayanta

Baki ta tabe ta yi gaba, itama ta yi kamar bata gane komai ba ta nufi bangarenta, a zuciyarta tana cike da tunanin wata jarabar na cen tana jiranta

Ajiyar zuciya ta sauke har ga Allah wani lokacin tana jin kamar tsoro na son kamata , sai dai kuma in ta ga zalunci karrara sai ta ji bata tsoron uban kowa!

A hankali ta bude bangaren nata bayan ta yi salama tana sake kallon dogaran dake gadin bangaren nata,

A yanzuma, ko idasa rataye Alkyabarta bata yi ba, ihun maganar matar da ta tabata dama tana jiranta, da tasowarta a hargitse da nufin maimaita haukan da dakikin kanta ke bata cewar zata ci gabaa da cin bilis ya sakata juyowa a zabure, a lokacin ne kuma Innarta ta fara saka hannunta bayan ta sha gabanta ta tare marin da ta yi niyar sake kwada mata

Da sauri NADIRAH ta zagayo ta tare hannun Umma da ta so sauke wani marin a fuskar Innarta

Rai bace ta ce" Menene haka? Me kike son aikatawa ne?, Ki nutsu walahi kar ki aikata abinda zai zamto maki dana sani ba, domin da wahala hannunki ya kai kasa ban rama wannan ba gaskiya!"

Da karfi ta warce hannunta, a harzuke ta ce"Kina nufin ki mareni?, Ki fada da bakinki kina nufin ki mareni? Da kaf danginki sai na karar da su da hannayena walahi!"

Abin mamaki, tar ido cikin ido NADIRAH ta ce" Da gawarwaki sun amsa kiran ubangijinsu kennan?, Ina mamakin yadda kika kawo warhaka a gidan nan a zuciyar mutane da yawa, ko dai a kanmu ne bakya iya boye halinki? Karara nake karantarki, sam baki iya takunki ba, ko sunne idannuwansu ya rufe suke ci gaba da maki kallon da suke yi maki? Abinda na sani shine, rashin hakurinki, da zafin zuciyarki zai kai ki ya baro ki!, Na fada maki ba lale bane na ringa zuwa ina fada maki shirina!, Yayama kike so na iya aikata aikin da ake so na yi ba tare da na saba da shi ba? Ke bakya so a zargi uwar gidansa ne? Dan Allah ki saka ido ki sarara min na gabatar da abinda nake son gabatarwa, in da hali in kin san zaki ringa manta cewa tafiyarmu daya in ina aikata wani abin ki daina zuwa inda nake idan muna zaune da su!, Magana ta karshe itace, ki kula da hannunki, in ya sauka a jikina yana iya wanyewa lafiya, ama ba a jikin wannan ba, bana tunanin an yi halitar da zata daketa ina waje na kyale!, Shegema fa ya san iyayensa!"

Daga haka ta yarfar da hannun ta nufi ciki rai bace, walahi sai da ta ji kamar zata hankade banzar nan, ita komai na hauka da karambani? Bata yin komai a ilimance? A yadda ta sako burin nan ai sai ta dan ringa nuna tanada kwakwaluwar cin zalin din, gaskiya tama rainawa ASADEEK wayo da wannan matar ta iya rufemasa ido har zuwa yanzu du iliminsa da ganno mai laifinsa? Mtssss!

Tana shigewa Hindu ta yi iya yinta dan zaunar da Ummah

A nutse ta fuskanceta ta ce" Hajia, ya dace zuwa yanzu mu yi abin fahimta, magana ta fahimta wace zamu fitowa junna a mutun, zan so ki gane, wannan hargagin da rikicin babu inda zai kaimu sai mu falasa kanmu, mu tonawa kanku da kanmu asiri, UMUGHLUK ITIBEL fa ba mahaukaci bane, ba makaho bane, ba kuma yaro karami bane, kuma ke kika raini abinki, kin fimu sannin idan ya fara fuskantar lamari irin na rashin yarda zai iya dora ayar tambaya a kai, yarinyar nan kuwa da kika gani abu daya zuwa biyu zai iya sakata ta tona lo meye kowa ya shiga uku, Hajia ita ba baiwa bace, iyayenta suke bauta, kin ga a dole yannayi na sada kansu a taka su ya sha bamban, sannan tanada ra'ayi nata na kanta, wanda ya saka take iya dubanka tace ba zata yi abu ba, ko bata son abu, to irin wannan abin yanna sakawa a sha wahalar zama da mutun, mutun mai ra'ayin kansa inaga ko a bariki yanada wuyar sha'ani, ba'a juya shi yadda aka ga dama, HAJIA tunda ta yarda aka yi wannan abu da ita inaga mu bata damar da zata aikata aikinta ta hanyar da ta ga zai fi gyarata, ba mu hannata sakat ba ta hanyar saka mata ido a dukkanin motsinta da neman hannata rawar gaban hantsi, ki sani, bata shigo gidan nan dan ta gaje ba ko dan ta kwace maki wajenki, idan kika yi hakuri gyaranku ne ku duka , watau in kika bata dama kika dauke kanki shiga jikinsu ba dan ta lalata mana aiki bane, Hajia na san baki taba ce mana da bakinki kina cikin tsarin gannin an kawar da shi ba, ama mu ba makafi bane, ba kuma mahaukata bane, bokon ce kawai bamu je ba, ama mun rayu da sannin me yake faruwa a tare da mu, ba gardawan yan kauye kara zube muke ba Hajia, haka kuma muna kishin kanmu, wannan gigi naki na daga hannu ki kawo kusa da mu matsala ne baba, idan ya zamto mun fara cin kanmu da kanmu ba zamu ji dadin tafiyar ba, shawarmu kanta na iya zuwa ba daidai ba, kin ga a haka ba dadi ko?"

Umma ta ja numfashi, idannuwanta da suka cenza kala da jikinta dake rawa na bacin rai da fargaba ta dubi HINDU ta ce" Ta yaya zan yarda fakat daya cewa ba ni take son zurmawa ba?, Kin ha abinda ta yi kai tsaye, abin mamaki komai bai ce mata ba?, ASADEEK yanada zafi sosai fa, ama take shige masa hanci da dukunkunne?, Ina fata ba kokari take yi idan ta aikata aikin ta sakayani a ciki ba, domin a yau ta saka na yi abinda ban taba yi ba a gabansa, watau hasala da daga murya!"

HINDU ta yi boyayen murmushi, a bayane kuwa ta sake kausasa yannayinta ta karra tabatarwa Umma cewa ta fa yi da aniya, in ba haka ba zata iya saka su a halaka baki dayansu!

Da wannan ta karra rufe Umma har ta mike ta tafi

Bayan ta tafi ta je dakin NADIRAH

Saman salaya ta sameta tana jan carbi dan haka ta zauna tana jiranta har ta gama ta shafa fatiha sannan ta mike ta karasa tana shagwabe fuska ta ce" Innata na kwari cikina da yawa, dubi tumbina ya cika makil walahi"

Murmushi innarta ta yi tana cewa" To ai na ga kin yi sallah zai ragu, tunda itama motsa jiki ce"

Jikin imnarta ta lafe tana sauke ajiyar zuciya

Innarta ta dubeta a sanyaye ta ce" Indina, me ya faru yau?"

NADIRAH ta dago a hankali ta zuba mata ido, sai kuma ta sakar mata murmushi ta mayar da kanta ta dora a hankali saman cinyarta
Muryarta a tausashe ta ce" Abinda na fahimta shine, muguwar yarda, kauna irin ta haihuwa, kusanci mai girma, yarda gaba da baya da ya dauka ya dora mata, bashi da darr ko dari dari a kanta, ransa nan take yake bacewa idan aka tabata, a kanta yana iya yi maka komai, domin yana kiranta da Mamah, mamansa, innata a uwa yake daukanta"

HINDU ta lumshe idannuwanta cike da tunani
Muryarta a raunane ta ce" In kuwa haka ne, juye mata aniyarta zai zamo aiki mafi wahala a gabanmu"

NADIRAH ta ja numfashi itama ta dago ta ce" Innata, jan aiki ne mai wahala, sai dai na fara hango matakin takawa dan karasawa cen, kanwarsa, watau Auta itace matakina, dan kuwa a soyayar tasa da Umma na hangi ta Auta ta maketa, da Auta zan jingina dan ya fara gane yarena, da ita zan jingina dan ya fahimci kumurcin dake tare da shi, domin Innata , Auta da kike ganni, hankalinta rasss, tana dauke da miki ne a tare da ita, da sharin matar cen, ta san yadda ta ci karfinsa har ya yarda cewa kanwarsa mahaukaciya ce, take rayuwa a haka, a zaman da muka yi, na fuskanci shi kadai ke makance da lamarin Umma, domin matarsama bata wani yarda da ita ba, ama kuma bata san girman sharinta ba, a tunaninta kiyaya ce irin ta wasu iyayen mijin, sai dai kashhh, wanda yakeda mahinmancin ne ya yarda da ita, sosai akoy aiki Innata, akoy gagarumin aiki"


Ajiyar zuciya Inna ta sauke, a hankali ta ce" in sha Allah, sannu sannu bata hanna zuwa, ita kuma wancen da izinin Allah sai mun kaita kass, sai halinta ya fito karara a gabansa, wanda take dannewa idan tana gabansa na tsayin shekaru, ba an fara yau ba?, Yanzu muka fara!"


Da wannan suka yi ta tataunawa da wasu shirye shiryensu hankali kwonce dan su cinma manufarsu!




___________________________________


Dawakai ne kwara biyar, tafka tafka irin ginanun nan masu ji da karfi da isa, sunna tafe sunna sakin huci da abubuwan adon dake jikinsu yana bada sautin cas cas cas


Su biyar din dake saman dawakan dukkaninsu manyan mutane ne masu daraja da fada a ji, a cikinsu UMUGHLUK ITIBEL ne a tsakiya, SHEIK a gefensa, sai rikakun yan siyasa, yan kasuwa, sannan jinnin sarautar a gefe da gefe sunna tafe a nutse tafia irin ta ziyara a asibitoci da sanyin safiyar yau, haka kuma sunna tataunawa kan babar Sallar BIANU da bugaje ke yi du shekara shekara

SHEIK ya dubi ASADEEK yana murmushi ya ce" ina fata wannan shekarar , iyayen talakawa zasu yi nasu taron da zaman gaisuwa?"

Linzamin dokinsa ya rike ya dan ja, hakan ya saka dokin tsayawa, sannan ya juyo barin Sheikh ya dan zuba masa ido

Kai ya kada sannan ya kalli gefensa ya ga sauran sunna dan zantawa ne, sannan dogaransu sun barbazu ne sunna tare mutanen dake son yi masu cincirodo

Kasa kasa ya ce" Madarata fa , madarar da kake yi min tofi kulun a jiya ban shata ba"

Da mamaki Sheikh ya dube shi ya ce"
8/15/22, 09:19 - Buhainat: *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍?*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*


🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻
*OUMOUGHLOUK ITIBEL*
_(ZAKIN SARAKAI)_
🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻

_FREE BOOK_

*Na*


*SAJIDA NIGER*





3️⃣6️⃣


Ya daga ya sake kusantata da kunnensa ya yi shiru yana sauraro

"Dan Allah ka saurareni, bana so ka yanken hukunci kai tsaye, ka sani ni ban taba soyaya ba, ban taba sannin yaya take ba sai a kanka, iyayenaa kuwa ba bijire masu na yi ba, kuma mijin da suka so bani ba sonshi nake yi, na tabata shima haka, ka ga hakan bashida wani anfani ko?" Ta fada muryarta na nuna tashin hankalin da take ciki

A hankali ya iya bude bakinsa, ya ce" Baiwa?, Baiwarki?"

Tambayar ta zo mata a wata iri, dan haka ta nemi karrin haske

A tausashe ya ce" Kina nufin ke din jinnin sarauta ce?"

Amsar da Bahija ke tunanin a gaban kowa tana iya badata da takama da isa domin abu ne na isar da takamar kasancewarta yar sarki, a yau sai ta samu kanta da mugun tsoro da zulumi, bata san me zata ce a matsayin amsa ba, tana tsoron ta fadi abinda ya saba muradin Balarabenta ya bace mata kamar yadda ya saba, hakan ya saka ta cewa" Baka son famillyn sarauta ne?"

"Kusan haka, kin san ni lamarin sarauta ne bana so, bale auren yar sarakuna? Anya zata iya yin biyaya? Gashi inada aiyukan da basa son ciwon kan mace!" Ya fada yana sake danne zafin da kirjinsa ke yi masa

Muryarta ta tausasa sosai, a sanyaye ta ce" Sarautar ba wata mai karfi bace, idanma da hali mu bar maganarta , ka dauka ni ba jinnin sarauta bace in dai hakan ne zai faranta maka, dan Allah ka zo gidanmu, ko ni ka fada min a wace kasa kake da gidanka, zan zo, zam zo walahi"

Da kyar ya sake iya bambarar bakinsa ya ce" In sha Allah, zan saka rana na zo, zan yi kiranki domin bani da isashen lokaci"

Haka yauma, tans ji tana gani, bata koshi da sauraronsa ba, bata san matsayarsu ba, bata gane zai zo din ba da gaske ko aa?, Ya katse kiran da nufin yana busy, haka kuma ta damu kanta da sanyaya zuciyarta, da fadawa kanta cewa ai da sauki, wanda zai tashi ya taka leda, ko ba komai sannu sannu bata hanna zuwa, ta tabata a yanzu da ya ji saboda shi har ta ki auren wani zai dubeta, ta tabata kuma zai aureta idan suka zauna, in har maganar sarauta ce baya so ba sai ta fada gaskiyar asalim sarautar tasu ta yayane suka sameta ba?, Tunda abin na neman hadawa da farin cikinta komai na iya faruwa, ciki harda iyayenta walahi!
(To dai, baki ke yanka wuya)

....................................................

*BAIWA?*
Baiwarta?
Wace irin baiwa?
Baiwa dai?
To ama, shi kansa ya shiga cikin duhu
Bawa fa du yancin da zai samu kansa kasa yake gaisar da uban gidansa
Babu mutumen da ya san darajar sarki da tsoron sarki irin bawa
Bawa komai fitsararsa fa son duniyarsa a tsorace yake da sarki
Du arzikin da bawa zai yi a duniya kuwa idan ya tashi gaishe da sarki sai ya duka
Wacece ita a duniyar bayi?
Wace irin wayewa ce da ita a lamarin bayi?
Ta yaya zata kasance Baiwa bayan idannuwansa take kallo ta ki bashi amsa?
Ta yaya zata zamto baiwa, bayan ta yi sa in sa da Huznah?
Wacece ita a duniyar bayi? Su waye iyayenta a tarihin bayi?


A hankali ya sake gyara zamansa
Afkawa ya yi a tunanin me yasa za'a aura masa baiwa to? Yaya sunnanta na gaske? Me ta zo yi? Shin Umma ta sani ko bata sani ba?
Tabas wani abu ya dan tsaye masa a rai na hargagin da Umma ta yiwa yarinyar nan a jiya,
Koda karama ce, koda Umma uwa ce a wajensa, Yarinyar sarauniyarta take, a laluma ya dace ta dakatar da ita .......ama, ama sai.........
Da sauri ya kore wannan tunanin yana astagfari, domin ya gane shedan ya fara kawowa tunaninsa hari

Wayarsa baba ya dauka ya yi kiran number Umma

A tausashe ya sanar mata a sanarwa HUZNAH da Auta yau ba zai yi zama da su ba a falo

Ta tambsyeshi tana fata lafiya yake? Harda nuna masa cewa zaman da yake yi da auta tana jin dadinsa domin Auta na kwontar da hankalinta idan tana tare da shi

Ya tabatar mata lafiya kalau, yana da bukatar hutu ne

A dole ta hakura ta yanke kiran

Wayar tafi da gidanka ya janyo da kansa ya sake zaunawa yana dan tunani
A nutse ya bude litafi ya saka code din bangarenta

A irin wannan lokacin zaune suke sunna hira da kyakyata dariya ita da Innarta,
Kukan shigowar kiran sai da ya saka suka tsorata sannan suka zubawa abinda ke ihun ido

Da kyar a kira na biyu Innarta ta yi shahada ta karasa tana fadin" Ki tsaya ke dai daga nesa, idan kiran mai sama ne ya sameni kya fadi ga abinda ya kasheni, ama ni kamar ma gani a wayar Habu wani lokaci muna kallon masu jan kunne kamar salula ce, bara dai na gani"

NADIRAH ta yi tsuru tsuru, ita dai ta ga abin nan har a dakinta, har a kicin dinta, ko'ina fa, tace kwaliya sai yan birni, sai ga abu na kuka kirrrr kamar tsohon keke mai rubabiyar kaca?, Allaaj jishe su alkhairi

Takarkarewa Inna ta yi tana dagawa ta ce" Hallo, Hindu ce a kan layi waye ke magana?"

Shirun da ya biyo baya ya saka Hindu cirewa ta kalli NADIRAH ta ce" Indi anya waya ce? Kin ji shiru kamar mutuwa ta gitta"

Karasowa ta yi, da sanyayar muryarta wace idna ta yi magana da ita kamar ba zata tofa komai ba sai zikiri ta amsa gana fadim" Innata bara na ji, Mutun ko aljan daga ciki muna sauraro"

Gaban goshinsa ya sake dafewa a hankali yana shafawa yana tunani a zuciyarsa

A hankali ya furta" Da dare, ina son ganninki a Bangarena"

Wata zabura da ta yi ta fancakalar da abin wayar a zabure, kasa kasa sosai ta ce" Inna Abanku ne Fa" saurarawa ya yi sosai yana jin abinda suke fada, Abansu? Aban su wace inna toh?

Innarta kuwa sai da ta wuntsila tana dora hannayenta a kai ta ce" Kin ga NADIRAH zan ci ubanki Habu bilahilazi, yaya zaki ce Zaki ne ya kira?, Ta yayama zaki zai kira?, Bayan wannan ina yan aike da takarda? Ke kam inaga dole na fara neman na aljanu kuma, abin na rikecewa a hankali bamu gane ba"


NADIRAH ta dauki abin ta mayar ta makala ta zauna kusa da Innarta ta ce" Innata walahi muryarsa ce, abinda na san muryarsa yadda kika san rusheshen kato idan yana magana, bobobobobo abu a hade dai kin gane ba kamar maganar Aminu aminu ruwan sanyi ba, jiyan nan ma fa ya ja min kashedi, cewa ya yi da dare na je, na je na yi me kuma? Ni mai kaurin sunnan nan,ban yi bama ance na yi?"

Da kyar innarta ta yarda, sai kuma ta shiga yi mata nasiha tana cewa ta yiwu wani abin ne , sannan ta shiga tsoratar da ita da kiyayewa da yi masa haye, sannan ta kyaleta ta mike ta shiga tunanin me ya dace yau yar ta saka? Lamarin ne kowa na kula nasa a boye, itama tana tura NADIRAH da su kwaliya su gyara jiki su matsewa a zuwan ta saka abinta ta more, kayanta ne, kuma ba haramun bane kafin su tafiyarsu ta san ta mora, ita kuwa gaba gadi ta yarda.


A bangarensa kuwa sunnayen nan uku uku ya kawo ya hade da maganar da ya yi da BAHIJA

Kai ya girgiza yana dan tunani, sai kuma ya mike a nutse ya haura sama domin ya hanna kowa shigowa dan hidimta masa wani abin idan ba shi ya bukaci hakan ba


____________________________________


Zuma ce farar saka, irin sabuwar nan mai kyan gaske Hindu ta juye a cikin hadin da ta yi na gumbar mata ta dameta sosai sannan ta rufe a kwano mai kyau ta sake nufar dakin INDI

Kwonce take a kasa, watau saman kafet barci na wartarta, jikinta wando ne irin mai laushin nan mai lafewa a fatar jiki , sai riga mai siririn hannu wace ta dauke mula mulan mamanta , domin mamanta ba yan biri biri bane gaskiya, ta baje tana barcinta hankali kwonce

HINDU ta zauna tana tashinta a hankali

Dagowa ta yi tana shanye lumsasun idannuwanta ta ce" Inna barci fa nake zaki tasheni?"

HINDU ta ce" Na sani, ki tashi ki je ki ji kiran da yake maki mana"

Baki ta turo ta ce" Inna, na fara barcin? Ki bari sai gobe mana"

Kai ta girgiza tana talabota ta ce" Kin ga damu na yi ungo shanye ba yawa, kuma ki je ki dawo ki yi kwonciyarki, kin dai ji abinda Aunty tace ko?"

Sosai ta sake bata fuska ta amshi abin sai turo baki tale yi ta dan kafa a bakinta
Dandanon zakin ya sakata bude bakin da kyau ta shanye sannan ta nemi neman komawa ta kwonta, bata san abinda ta shawa kanta ba, Gumba ce VIP, gumba ce ta gagararum matan da suka san kansu suka kuma yarda da kansu, a hadin gumbar ana saka sinadarai na mugun motsa sha'awa, ko budurwa kike idan kika sha sai lamari ya motsa maki bale wace ta san hanya, gumba ce mai saka ka tamkar ka yi maye, karfi ne da ita dan idan

Please Login or Register in order to submit comment