Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tale sirrina ce har ta fito daga cikin gidansa ta yadu a wajen da ban shirya jinta ba dama me zai sakani ni bawa da Allah ya halita dauka cewa zan zartar da mulki a doran kasarsa dawamame? Wai su basa tuna mutuwa ne? Ko sunna manta wanene mai Mulki? Mu jagoranci ne muka samu na talakawa, mai mulki shine ALLAH, Yah SHEIK, dan kawai ina kamanta adalci sai na zama abin farauta?"

"Ka yi hakuri ALLAH ya taimakeka" Sheikh ya fada a sanyaye, domin shima abin nan ya dake shi, jakafiyar matar sarkin garin Dogon dutsi ce ta miko sakon da akace ta bada, tana kuka tamkar ranta zai fita cike da tsoron kashedin da aka yanka mata a kan ahalinta, sako mai dauke da takarda fara mai dauke da magana kamar haka *ka yi zamaninka, iya damarka kennan, ba zamu bayana ba sai lokacin da ka gushe, domin kai la san sarautarka takaitaciya ce, kai da baka iya saka kukan jariri a gidanka ba bale a yi tsoron dan tsako ya giga?, Ka yi ta kanka kawai domin ka sani yanzu kakeda abokan gaba!*


Numfashi ya sauke mai zafi ya ce" Ka daina ce min Allah ja da zamanina idan muna daga ni sai kai SHEIKH, ka dubeni kawai ka fada min gaskiya!"


Sheik zai yi magana aka nemi izinin shigowa bayan an yi salama

Kasancewar sun gane mai son shigowar ya saka Sheik ya bashi dama

Kasa ya duka sosai kansa a kasa ya ce" Allah ya taimakeka, sako ne daga Bafanka, a kan maganar zuwansa dan son ganninka, yace da da hali kafin ka yi tafia"

Shiru ne ya biyo baya, shiru mai tsayin gaske, sai da ya gama tunaninsa sannan ya sake dantse lebensa a kausashe ya ce" An bashi dama"

Sheikh ya kalleshi da sauri, ya raka Dogari da kallo ya sake dubansa
A tausashe ya ce" ASADEEK, ka san rigima ce ta cikin gida ko?, Kar ka daukaka abin nan , ka yi hakuri ka ji?"

Rawanin da ya sasabto kada ya ja a hankali ya mayar ya rufe har wajen hancinsa da shi sannan ya duba agogon hannunsa domin ba zai shiga gida yanzu ba sai ya gama karatunsa an gama salolin da suka rage , to mema zai shiga ya yi ne? Ya tabata Auta tana nan bata yi barci ba , rigimarta na nan tare da ita, matarsa kuwa bai san me zai je ya nema a wajenta ba tunda bashida abinda zai bata, yana so sai ya je ya dawo daga tafiyar nan zai zauna da ita, zasu yi zaman da ya dace, zai yi kokarin kwatanta mata abinda ya dace ta fahimta, sannan zai yasare mata wahalar da yake gannin tana tare da ita, domin shi dai wada yake ciki shi kadai ya san ukubar da yake ciki, baya rabo da ciwon mara, tamkar zai kashe shi wani lokacin.....ama ba komai Allah ne gatansa


Dare ya cika sosai a ranar nan, domin sai kudan karfe dayan dare suka doso babar farfajiyar ta masarauta shi da makarabansa, mutun takwas sunna tafe cikin nutsuwa, haka kuma sun sakashi a tsakiyarsu


Dakatawa ya yi yana duban dogaransa mutun hudu,da dima diman bodyguard dinsa mutun hudu, watau masu rike da bindiga

Dan murmushi ya yi wanda bai yi tunanin a yau zai iya samunsa ba sakamakon irin bacin ran da ya hadu da shi, sai dai zama a cikin datijai da zikirin da suka yi ya sanyyayar masa da zuciyarsa harma yana jin a yanzu ko wani hukunci ya yanke bafa da bacin rai ya yanke shi ba, ba zai yi nadama ba



"Duba ku ga Namiji har namiji, sai dai ba husssss.................." Ya fada daga saman dakin da ya sauka, watau bangaren bakin ahalin gidan, baban dakin da yake nasa a matsayinsa na bafan Sarki


Abinda ta saka ta kare fuskarta ta sake ja ta rufe fuskar tata sosai itama ta karaso wajen labulen ta tsaya tana kare masa kallo, alkyabarsa sam bata boye cikar halitarsa ba, bama zakak gigice ba dai ka ganshi ba alkyabar, domin du wani bayanannan abu da Gymnastics ta haifar masa a jikinsa kan bayana ne, bai yi irin wannan bulewar ba har ta baci, ama wace ya yinma a nan kusa dai babu ginanen namiji irinsa sai dai a nesa

Ajiyar zuciya ta sauke ta fita daga wajen labulen ta koma saman kujera ta yaye lulubinta gaba daya tana kallonsa ta ce" Munaa cikin gagarumar matsala, shirunsa da rashin hargaginsa ba yana nufin bashida kulaliya a zuciyarsa ba! Ni na raine shi, ko mahaifiyarsa ba zata fada min wanene shi ba!"


Labulen Bafansa ya saki cike da jin kishin yaron da tarin kasar da Allah ya tara masa a cikin zuciyarsa ya koma ya tsaya kikam a saman kanta
A amon muryarsa zaka gane ransa a bace yake ya ce" Yanzu ace, daga jin wannan magana ta bila na kasa zaune bale tsaye sai da na kawo kaina? Ni da nake bafansa kennan? Da wani ne fa?"

Baki ta tabe tana duban agogo ta ce" Ba zaka gane ba, kasancewarka bafansa a idannuwan talakawansa kadai ka tsira, summa dan basu san wanene kai a rayuwarsa bane, ka ga ASADEEK? Yanada mugun daukaka a idannuwan Agadasawa!, Da ace maganar nan gari ta zaga da yan cikin garinka zasu fara kai maka farmaki !, Yanzu du ba wannan ba, da me zaka tunkareshi a goben?"

Zaunawa ya yi yana fuskantarta ya ce" Da me zan tunkareshi kuwa? Tunda na taso na zo da kaina zan bashi hakuri ne kawai na koma komai ya wuce, abinda gimbiya ta aikata kuwa na mata kashedi ta min alkawarin ba za'a kuma ba"

Ido ta zarro tana kallonsa cike da mamaki

Da dumbin mamaki ta ce" Anya zaka iya mulkar garin Agadaz nan gaba?"

Da bacin rai ya ce" Ki gyara furucinki a kaina , kar ki manta wacece ke?"

Bakinta ta tabe tana cire kanta, muryarta da haushi haushi ta ce"Kaima kar ka manta me yake tsakanina da kai? Kafin ka ffara tunanin watsar da ni ka tuna da me da me zaka yi wasa!, Maimakun ka tambayeni dalilin furucina sai ka hau kan isa da iza bayan magana muke a kan SARKINKA?"

wannan karron kasa ce mata komai ya yi,dan babu abinda ya fi kona masa rai irin ya ji an kirayi yaron bayansa a matsayin sarkin da ya fi shi fada a ji!


Ajiyar zuciya ta sauke ta saisaita muryarta ta ce" Ka yi hakuri, ina so ka fahimci girmann laifinka, sannan mu samu mafita, ka sani idan bamu yi da gaske ba neman gira ne zai saka mu rasa ido, kar ka manta namiji kake, yaya zaka ji idan talakanka ya zagi mazakuntarka? Uwa uba a gaban wani dake kasa da kai? Zarafinsa aka ci, mutuncinsa aka ci, dole a samu hanyar da za'a wanke kai, kuma a wanke shi a idannuwan wanda aka zageshi a gabansa!, Dole zaka duka a gabansa ka nemi kanka, dukawa wada baya hannawa a mike da tsayi, ka fuskanci furucina ka samawa kanka sauki, idan har ba haka ba zaka sakawa kanka damuwa ne!"

Ikon Allah shi yake kallo, ransa a matukar bace ya mike daga zaunen da yake ya nuna mata hanyar fita a kausashe ya ce" Kin ga, tashi ki tafi"

Da mamaki take kallonsa

A tsawace ya ce" Na ce ki bace min da gani, tunda a yau ni zaki zagarwa mutunci ki dubeni ki ce na je na dukawa yaron da na haife shi da cikina? Tashi ki tafi!"

Murmushi ta yi mai ciwo da ma'ana da dama a zuciyarta, tabas idan ta daki kirji ta ce ta fi kowa sannin wanene UMUGHLUK ITIFAL bai dace a yi mata gardama ba


A nutse ta mike, cike da ita ta gyara hijabinta da yannayin shiga irin ta bayi dan yin bada sau ta sake rufewa da kyau kasa kasa ta ce" WANDA BAI JI BARI BA, ZAI GA UWAR BARI!"

A labe ta fice a boye ta samu ta koma bangarenta ta ringa kai kawo dan bacin rai, tamkarma abin ya fi damunta fiye da sarkin, sam baya gannin abinda take gani, ama ba komai idan da rabon su sake zama sa zauna!




Washe gari
8/13/22, 22:55 - Buhainat: *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍?*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*


🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻
*OUMOUGHLOUK ITIBEL*
_(ZAKIN SARAKAI)_
🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻

_FREE BOOK_

*Na*


*SAJIDA NIGER*


0️⃣6️⃣



*Washe gari*


Da misalin karfe tara da dori kadan

A hankali ya sake debo abincin a cikin spoon ya sake nufo bakinta da shi yana murmushi , cikin tausashiyar muryarsa kasa kasa sosai ya ce" To naji, zaki bi ni ko? Ha sai kin koshi tukunnan kin ji?"

Idannuwanta ta lumshe, idan yayanta na irin abubuwan nan takan ji hankalinta na sake tashi, idan ta tuna dukkan abinda yake yi a kallon mahaukaciya yake yi mata irin a lalabakan nan, sai ta ji duniyar baki daya ta fice mata a ranta

Yawun bakinta ta hadiye ta sake bude bakin nata ta amshi abincin a hankali ta ringa taunawa still tana kallonsa


Murmushi ya yi yana sauke ajiyar zuciya ya dauki tissu ya goge mata bakinta sannan ya dauki ruwa mai dan sanyi sanyi kadan ya nufi bakinta da shi

A hankali ta amshi ruwan, ta fara sha kennan aka shigo da salama

Kwarewa ta yi da ruwan dake bakinta da sauri ta shiga tari, sai dai abin mamakin, ba ta tarin da take take ba, watau tana tarin yayanta yana riketa da yi mata sannu da kokarin kafa mata ruwan a bakinta dan ya sasauta ama ita ta rike hannunsa kakam tamkar zata shige cikinsa , lokaci daya kuma jikinta ya dan dauki rawa rawa tana dake kankameshi


Da sauri Umma ta karaso tana fadin" Subahanalah, my baby ruwa ne ya kwarar da ke, yarona ka bata mai sanyi da yawa ne? Ka dan bana bata mai sanyi dan yana dakata tari, yannayin jikinta sai ana kula Yarona, fan sako min ita na gani? Zo nan na gani autana?"

Da karfi ta dake dantse hannunsa tana rintse idannuwanta hawayen cikinsu suka samu zirarowa daga gurbin idannuwan nata ta kifa kanta a gaban shadar dake jikinsa ta ja numfashin dake nuni daf tale da fashewa da kuka

A hankali ya sake zuba mata ido yana nazartarta, sai kuma ya dago ya kalli UMMA dake kusansu sosai

Hannun UMMA dake dan taba Auta, Auta na warcewa ya bi da kallo, a hankali ya sake kallon UMMAN wace ke aikin da ta saba, watau nuna mata kauna da tsantsar soyaya


Idannuwansa ya cire a kanta yana sake duban Dogari da ya sanar da son shigowar Bafansu, haka kuma ya sake duban Umma

Dan murmushi ya yi a hankali ya ce" Yauma fada kika yi da mamanki ko?"

Da sauro UMMA ta dago tana kallon fuskarsa, furucinsa ya tsoratar da ita, hakan na nufin ya fara gannin wani abin dake tsakaninsu ne? Watau turetan da Auta ke yi?

Dan murmushin yake ta saki ta dan ja da son taba Autar ta zauna tana fadin" Ai ka san halin Auta, ita fa damuwarta a kan shan magani ne, jiya har ta kwonta na tayar da ita , shine aka yi ta kuka da kyar na lalabata ta yi barci"

Murmushi ya sake yi bai ce komai ba, domin Bafansa ya shigo tuni yana tsaye yana kallon Auta da irin abinda ke faruwa


Dan tsaki bafansa ya yi yana dafe kai ya kai zaune ya ce" ASADEEK , na rasa me yasa ka ki a kai yarinyar nan asibitin masu irin ciwonta, gata abu sai karra yin gaba yale, wannan rukunkuma haka kamar wata yar yarinya bayan mace take magidanciya? Ai gwara ka yi hakuri a kaita a ringa bata magani ko abin ya yi sauki ko?"

Jimke hannunsa da Auta ta yi ya saka shi sake dubanta a hankali, domin hakan da ta yi ya sheda masa dayan biyu ne, Au ta ji abinda bafanta ya fada har ya mata ciwo, ko kuma bata son jin muryarsa ne.


A hankali ya sake riketa yana sake gyara mata hijabinta dan kar ya shaketa, murya a tausashen da ita kadai yake yiwa magana a haka ya sake talabo fuskarta kasa kasa ya ce" Menene? Bakya so a kaiki asibiti ko?"

A hankali Auta ta gyada kanta, sannan ta dago idannuwanta ta dube shi muryarta a raunane ta ce" Ni ba mahaukaciya bace ABAHNA kar a kaini ka ji?"


"Ahaf, idan ba haukan ba me zai saka aikata wani aikin yar nan? Yayanki ne fa kike ce masa ABA, ai ke ba magajiyarsa bace, kuma wannan zama haka ai idan ba ana cikin hali na rashin hayaci ba ba za'a aikatashi ba sam" bafansu ya fada yana dan kada kafa

Kasa kasa ta dan mike ta dauki jus din dake ajiye ta kai gabansa ta ajiye masa, cikin dabara ta saka kafarta ta take tasa da karfi, harda murzawa sannan ta koma baya ta zauna tana murmushin yake ta ce" Aa fa bafansu, ba za'a kai min yarinya asibiti ba, a nan din ai zata fi saukewa idan tana ganninmu a gefenta, a hankali sai ka ga kamar ba'a yi ba, tunda likita yace ciwonta na dan lokaci ne, damuwa ce ta haifar mata da shi, idan har ta samu kwonciyar hankali ko yayane zata samu sauki"

UMUGHLUK dake rike da ita idannuwansa a lumshe, zuciyarsa na tafarfasa ya dan ja hannunsa a hankali wanda ta nitsa masa farce ya sake dago fuskarta ya ce" Auta, kina ji? Tashi ki je ki kimtsa kayanki kin ji? Sai mu tafi ko? Ki shiryasu sosai fa, ki saka harda bruch da maganinki duka kin ji?"

Wata irin ajiyar zuciya ta sauke mai sanyi ta mike tana sauri harda hade tafiyarta ta yi waje , wanda ke nuni da kamar wani irin farin ciki ta ji na furucin nan


A hankali ya juyo inda Bafansa yake ya dan wara kafafuwansa ya dora hannayensa biyu a saman gwuiwoyinsa ya kai hannunsa wajen gashin kansa dake daure ya fan shafa kadan sannan ya saka idannuwansa cikin na Bafansa ,
A kausashe ya ce" Bismillah "

Bafansa na zarar ido ya dago shima yana sake kallonsa, dan sai ya ji kamar amon muryarsa yanzu ba daya ba da ta dazu

A dan rikice kadan ya ce" Dangane da abinda ya faru ne dama jiya na kasa zama nace zan zo"

Shiru ya yi ko zai ji ya yi magana? Sai ya ji bai ce komai ba

Bafansa ya ci gaba da fadin" Ka san lamarin mata ne da rashin jin magana, ka yafe masu ba zasu kuma ba in sha Allah "

Ikon Allah kawai yake kallo, kwata kwata bafansa bashida wayo bale tunani

Kai ya fan girgiza yana cire dubansa kadan ya ce" Ok ba damuwa"

Da mamaki ya kalle shi, kasa rike mamakinsa ya yi ya ce" Kana nufin komai ya wuce kennan?"


ASADEEK ya muke tsaye , gaba daya tsayinsa ya mike a gabansu

Dan murmushi ya yi ya dubi Ummansu dake zaune kanta sade kwata kwata bata damu da maganar da suke yi ba, ya tabata ta shigo ne dan a kimtsa masa kayan tafiyarsa, yana son fada mata umura fa ya nufa yana kuma cewa ba zai fada mata ba zai mata surprise ne idan ta je su hade a cen

Dubansa ya maida kan BAFANSA a hankali ya ce" Babu wata damuwa ai, Mata ne, bakinsu bashida linzami sai sun samu dorinar da ta daki bangonsu..............., Allah ya takaita ama ina tsoron fushin da dogarai suka dauka, harfa cewa BABAYE ya yi in ba dan bafana kake ba, me ya hauda kai saman karaga bayan dan kaka hajia kake ba dan kaka elhaji ba?"

Gabansa sai da ya kwonci kwonci ya fadi har ya mike tsaye cirr daga zaunen da yake hannayensa na rawa

Da sauri ya ambaci sunnansa gannin ya juya ya nufi uwar dakansa, sai dai bai tsaya ba

Da sauri ya daga kafarsa da nufin binsa, sai dai ya dakata da karfi yana kallonta gabansa naa faduwa

Da idannuwanta ta masa nuni da waje sannan ta sake shi da sauri ta fara ficewa ta nufi bangarensa

Tana tsaye a dakin tana kai kawo ya bude ya shigo hankalinsa a mugun tashe ya nufota yana fadin " Me wancen marar mutuncin yake nufi? Me yake nufi da furucinsa a kaina?"

Da sauri ta karaso ta dora hannunta saman lebensa tana fadin" Shuiiiiit, safiya ce, WA'INDA ke jira yace a yi sun fara bazuwa ka rufawa harshenka asiri kar tun daga nan ya kirayi Sarkin damagaram su tujeka daga kujerar mu shiga uku baki dayanmu!"

Yanzun kam tsakaninsa da Allah jikinsa rawa yake

Zaune ya kai dan ba zai iya jure tsayuwar ba, muryarsa na rawa ya ce" Me yake nufi da ni? Yaya zan yi kennan?"

Idannuwanta ta wanna tamkar wata yarinyar mace ta zauna itama a daf da shi sosai tana kallonsa ta ce" Abunda yake nufi da kai ramuwar gaya ce, abinda zaka yi kuma a yanzu idan ka saurareni ina iya saka ka a hanya!"

Fuskantarta ya yi sosai dan haka ta yi murmushi ta ce" INA BAHIJA?"

Zufar dake gaban goshinsa ya share yana sake jan ajiyar zuciya yana jin meye na tambayar Bahija bayan ba wannan ya kawo shi ba, ba shine matsalar ba!

A takaice ya ce" Tana Hotel zata je Umarah wai bana!, Ki min maganar da kika ce mana"

Murmushi ta yi ta sake gyara zamanta ta ce" Dama shawarata a gareka itace, ka sake samunsa wannan karron tare da Gimbiya, ku zauna a saman cafet ku zanta, ka dube shi ka bashi hakuri mai sunnan hakuri, sannan ka nuna masa ka zo da maganar bashi yarinyarka mace kwalin kwal ya aura!"

Ido ya zarro yana kallonta

Da mamaki ya ce" Lalle yau na fara tunanin ke ya dace ki hadiyi maganin saka barcin nan na wancen mahaukaciyar kanwar tasa ba ita ba!, Kina nufin ni na dauki yarinyata na bashi? Kyan zata zauna kallo har duniya ta nade ne ko me? "

Kai ta girgiza tana safe dafe kanta, lalle wannan mutumen babu mahaukaci irinsa, ba kuma zai taba zama mai hankali ba

Sai dai tunda so take yi su fuskanci junna sai ta sake tausasa muryarta ta ce" Ka gane inda na dosa mana Aban BAHIJA, kasancewar babu abinda zai iya yi matan na kwadaita mana haka, sannan zamu jefi tsuntsu biyu da jifa guda ne!"

Kallon me kuke nufi yake yi mata, dan haka ta sake gyara zamanta ta ce" Ka san menene burinmu, wanda muke fata yaron nan kar ya jima a saman kujerar mulki, idan yau BAHIJA ta zamto iyalinsa hakan na nufin itace mafi kusanci da shi fiye da kowani dan Adam a duniya, ta haka a kwanaki kalilan tana iya kawo karshen rayuwarsa, kai ka gaje abinda ya gada cikin ruwan sanyi ba tare da mun wahala baki dayanmu ba, sannan ta fita ta auri wanda take so ko?"

Ido ya zuba mata sosai yana kallonta

Bai san lokacin da wani murmushi ya kubuce masa ba,

Da sauri ya mike yana fadin" Bara na koma na ganshi yanzuma"

Hannunta ta saka ta janyo shi har sai da ya zauna daf da cinyarta, a hankali ta dora hannunta saman cinyarsa ta dan matsa ta ce" Ka manta tafiar yamacin nan zai yi? Ai ba zaka samu kebewa da shi ba kuma , inaga zai nufi kasashen turai ya huta ne, ka zauna kawai zan je na hanna wancen mahaukaciyar binsa, domin idan har ta bi shi komai na iya faruwa, ka bari idan ya dawo sai ku zo da Gimbiya ku same shi, nima zan kasance a wajen kafin lokacin dan na tayamu yaki"

Cike da bege ya rakata da kallo har ta gama bada sawunta ta tsaya ta gamsu da hanyar ba mai ganninta ta fita da sauri ta nufi bangaren AUTA



Karar bude kofar ya sakata dagowa da sauri daga cusa hijabanta da take yi a cikik akwatinta ta juyo

Gabanta ya sake yankewa ya fadi da sauri ta zauna ta hade gwuiwoyinta ta dora kanta a sama tana yin gaba da baya kamar tana zizigar jariri a bayanta , tsoro da faduwar gaba sun cikata

Dakin ta rufe da ky ta karasa inda take zaunen nan ta duka cike da takaici ta ce" Ina kike tunanin zuwa? Ama bakida hankali yarinyar nan kwata kwata!, To bari ki ji, idan har kika yarda kika bi yayanki tafiyar da zai yi na rantse maki da wanda raina yake hannunsa kina dawowa zan makala maki mugun sharin da yayanki da kansa zai haka rami ya saka ki kanki a fili sannan ya jefe ki da duwatsu har sai kin rasa ranki......, Ke kin san ciwon wannan zai halaka shi shima dan makahon son da yake maki!, Ta rage naki , ki duba ki ga abinda zai gyara ki!"

A hankali ta dafe zuciyarta ta silale a kasa ta dora kanta a saman akwatinta ta rintse idannuwanta
A bayane ta furta" ALLAHU AJURNI FI MASIBATI, WA KHALIFUNI KHAIRAN MINE HA....." sai kuma ta karashe tana mai sakin kuka tana jin kanta tamkar zai tarwatse gida biyu

A hankali ta sake dafe gaban kirjinta, ita ba waya ba, ita ba komai ba, an amshe , yanzun a barta ta je ta yi ibadar ko zata sake neman gafarar ubangijinta da fatan ta gama da duniya lafiyama ba zata samu ba? Lalle ta fara kulatar mijinta, shin ina yake ya bari ake neman kasheta? Ba zai lekota ya ga amanar da aka bashi ba? Ba zai nemi ganninta ba ko zai karanci damuwarta? Ko dan ta rasa cikin dake jikinta ne ya tsaneta?....... A wannan rana sallah kawai take tashi ta gabatar ta koma ta nade, har lokacin tafia ta yi, tana ji tana gani ta gilawa yayanta karyar juwa take ji ba zata iya tafiyar ba, zata je haji idan Allah ya nufa, tana ji tana gani ya mata salama ya fice tamkar zata mutu dan tashin hankali, sai dai ta sake mayar da kanta ta sha madarar ruwa ta kuma fuskantar alkibla, ta san Allah yana gani, ta kuma san idan bata ga warwarewar matsalarta a duniya ba tabas a kiyama Allah zai saka mata, dan haka sai ta ringa kai masa kukanta tana fada masa yayanta dai, yayanta dai, domin babu babar fargabar da ta kai shi a zuciyarta, idan ta tuna shi takan dimaucewa, takan rasa komai nata, sai idan ta fuskanci gabas ta yi kuka ta fadawa ubangijinta sai ta ji sanyi a zuciyarta, sia ta ji kamar komai normal ne tunda akoy Allah.



A cikin JIRGIN VIP, watau wanda ya fara daukan manyan mutane dan sada su da babar kasa, kasa mai tsarki dan gabatar da aikin Umurarsu


Cike da kasaita take tafe tunda ta shigo
Daidaikun mutanen dake dan yi mata murmushi ko su gaisar da ita sakamakon shirin da ta yi wanda ke nuna ko ita wacece take dan kallo ta amsa su da dan yatsina baki ko ta dan dauke kanta
Baiwar dake biye da ita ke dan sake gyara alkhyabarta har suka karasa daga ciki wajen VIP plc ta zauna a wajen da yake nata ne domin shine numberta ta karra gyara zamanta tana maganar karshe da kawarta wace suka yi zasu hade a cen su yi wani program dinsu na harkar auren kawar tata

A hankali ta girgiza kanta a lokacin da baiwar ta karra tambayarta ko akoy bukatar wani abin?

Juyawa baiwar ta yi ta koma nata wajen cen cikin jirgin cikin jama'a tana sauke ajiyar zuciya da tunanin ta shiga ukunta da akace ta yiwa BAHIJA rakiya, ta tabbata tana ji tana ganni zata shiga garin manzo ta fito ba tare da ta yi sallah ba, watau ba tare da ta je masalaci ba, dan kuwa Bahija kashinta ne kawai ba'a wanke mata, yadda take zuba mulki a rayuwa ko ubanta bai kaita ba!


A hankali ta dan karra gyara zamanta tana daura belt, sai kuma ta shiga dan duban gefe da gefenta dan gannin su wanenen Elhazan da duka hau VIP a wannan tafiyar?

Na farko da ta fara kallo sai da ta kureshi da ido, domin sam bai mata kama da

Please Login or Register in order to submit comment