Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

magana idan Indi matar Aminu ce kina raye ko kina cikin ƙasa za'a yi a gama kina kallon yan dugwui dugwui a gabanki, idan kuwa ba matarsa bace du tsiya sai dai kowa ya yi hakuri, dan Allah kina abu kamar jahila, ki fice a gidan nan in ba haka ba, in ban cuje maki dan kwali na danna kanki a cikin ta murhun cen ba ni bace HINDU bace!"

Gannin yadda Hindu ta farra hawa sama tana zarro mata ido tana neman dungure mata kai ya saka ta sake tatara kudaden da take jinsu da yawan gaske kamar sun fi natanma yawa ta karasa inda suke tsugune ta damki hannunsa ta ce" Tashi mu je, yau yau yau zan ga ubanka mu tsayar da magana daya fa yarinyar gidan rabe, yarinya na sonka kana janta a kas, tashi mu je"

Kamar jansa take, a kan kaffafuwansa yake tafiya ama kuma kamar jansa take ya bita suka fice a gidan

Hindu dake tsaye kallon NADIRAH take yi tana jira ta ga ta zabura ta bi su, sai ta ga ta share hawayenta ta mike ta dawo kusanta ta tsaya tana kallonta, sai kuma ta fada jikinta ta saki kuka mai tsuma zuciya tana cusa kanta cikin kirjinta


Idannuwanta ta lumshe itama hawayen nata suka samu digowa daga gurbin idannuwanta, ta dagota tana kallonta ta ce" Kulan ya tafi ne ko? Kukan abinda mamansa tace kike yi ko? Yi hakuri yar albarkana kin ji? Yi hakuri ki daina kukan nan, na sha fada maki ki barsu du abinsu abinda Allah ya hukunta fa zamu gani a rayuwarmu kin ji?"


NADIRAH ta ja hanci tana fadin" Ni yanzu na fara tsoron matar nan, ginnin da yake yi dakina da nata a hade suke, idan har ya gama ya tabata a gidanta zamu zauna makotaka, anya zata barni na rayu a gidan mijina? Imnata ko kaini zaki yi a bibila min fuskata na zama mai munin da take so? Ita in ba abinta ba ai nima ba wani kyan ne da ni ba tunda banida tsayi ko Innata , kuma na ji ana cewa mace idan ba tsayi batada wani kyau ko Inna?, Dan Allah ki kaini a bilen fuskata"

Janta ta yi suka karasa wajen zamansu domin rana bata fito ba bale su je kasan shuka suka zauna

A sanyaye ta ce" Kin san na tabata wata rana Innar Aminu sai ta kaunace ki, Allah zai saka mata kaunarki tunda batada dalilin tsanarki, kuma ba za'a maki bile bile a fuska ba, babu kyau fa a lahira da wutar jahannama za'a gogewa masu shi, ke nu kam banma ga abin daga hankali ba Indirahna, ki kwontar da hankalinki, idan kuwa zaki bini birni satin nan mai kamawa sai mu leka mamanki mu gaisar da ita sannan mu wuce gidan kallo mu yi kallo sai mu karkato kasuwa mu dayi kayan yan gayu harda takalmi kin ji?"

Kai ta gyada tanna murmushi ta ce" Inna hala asusun da zaki siya min gadon mai runfa ne kika fasa? Ko na Abana ne da yace zai min gara buhu takwas?"

Yar dariya ta yi ta ce" ina ai asusun gadonki ba za'a fasa shi ba ko ana ha maza ha mata, na abankine, barama na kimtsa tarbansa dan na san yana iya kirtan ba dadi dan na taba asusun nan na gararki, zo tsefen kaina na yi sheme sheme a tsakar gidan nan ya tardomu a haka sai ace innar Aminu ta shinfideni, na tanata ba zai ji haushin kudinsa da yawa ba"

Dariya ta yi ta kwontar da kanta a saman kafar Innarta, a hankali ta ce" Innata, ina yin adu'ar nan fa, ko yau da kika tadani sallar asuba da na yi raka'atanul fajr kafin a yi kiran sallar asubah na fara salatin nan, da aka yi sallar aka gama na dora na yi ta yi , na yi ta yi sai da na kai dubun nan, sannan na dora fa adu'o'in tsarin da Innar birni ke koya min, na yi azhkar sannan na roki Allah ta bani miji na gari Aminuna......."


Murmushi Innar ta yi tana shafa kanta a hankali ta ce" Ki ci gaba da yi, ki yi ta yi, kin ga ni yanzu idan ban yi dubun nan kafin na kwonta ba bana iya barci, komai gajiya sai ki ga ina zabura, kuma adu'o'in neman tsari sunne makamin mumuni, babu boka ko malamin da ya fi bakinka da na iyayenka, ka fadawa Allah da kanka, to fa in du duniya zata tsaneka Allah na tare da kai, wani lokacin zaka ga kana ta Adu'ar kana ta yi biyan bukatar bai zo ba, to ka sani alkhairin ne a wani bangaren wanda Allah zai tabatar maka, kai da kanka sai ka yi mamaki, yanzu dai ai ba'a kai rikici irin na makada ba, ama ki duba ki ga Abanki kulun yana sama, makadi ne ama a haka yake neman kariya a wajen ubangijinsa, ki ci gaba da neman zabin Allah, ama ki daina cewa alkhairi Aminu dan baki san wannan mai wuyan uwa marikin lema bane alkhairin ko mai garin nan bane"

Kai ta dago da sauri tana cuno baki ta mike tana fadin" Kai inna, ke dai ba za'a yi hira ta zaman lafiya ba sai kin kawo masu mulkin nan da basuda tunanin komai a rayuwa sai mulki, ni fa ko sarkin yan tasha bana so walahi in dai sarki ne!"


Da ido ta rakata domin ta warci dayan tulun fa ya rage da garaje ta yi gaba

Ajiyar zuciya ta dauke ta ce" Tuluna, Allah ya sa ka dawo da ranka kar wani ya tabata ta mula masa, ni kam ban san a ina Indirah ta gaji fada ba sam" ( to fah😁😁😁)

_________________________________


Shayin da ta kurba a bakinta mai dumi da dandanon zuma kamar zata yi tagia ta furzo a zabure tana sakin kofin kwalbar mai dauke da ruwan shayin ya bare a saman cinyarta

A haukace ta saka ihu tana fadin" FADIME FADIME, shigo shigo bani ruwa da gishiri ciki na kone kafata"

A hanzarce ta shigo ta yi kicin kanta a kasa domin Mai martaba na zaune ba zaka yi kallo irin na kure waje ba dan gudun yin laifi wajen matarsa mai haukatacen kishi

Da sauri ta dawo kanta a kasa domin kunyar lamarin take ji a zuciyarta ta fan zuba mata ruwan a saman cinyarta da ta kwaye gaba daya kamar wata wace ta soye wannan tona sirrin jiki haka

"Duba min da kyau na kone ko?" Gimbiya ta fada tana rinrintse ido

A hankali ta duduba wajen, ya dan yi ja dai ama ba zai tashi ba tunda an zuba ruwa mai dauke da gishiri ai

Kai ta girgiza da nutsatsiyar muryarta ta ce" In sha Allah ba zai tashi ba "

Kai ta gyada tana cire dubanta a kanta ta mayar gefe tana saka yar yatsarta a bakinta ta dantse ranta a bace da maganar da mijinta ya zo mata da ita, ba dan komai ba sai dan tunaninta ai kashe mata ya kawai za'a yi, duda baban mutunci da daukaka ne zasu karkarowa kansu,ama kuma yarta fa?


Da ido ya raka FADIME har ta bacewa ganninsa a hankali ya sake shafa gaban kirjinsa yana cire tunanin dake ransa ya sake fuskantarta ya ce"
8/13/22, 22:55 - Buhainat: *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍?*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*


🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻
*OUMOUGHLOUK ITIBEL*
_(ZAKIN SARAKAI)_
🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻

_FREE BOOK_

*Na*


*SAJIDA NIGER*



0️⃣9️⃣




Ya sake fuskantarta ya ce" Kina nufin maganar nan ce ta saka ki sakarwa jikinki shayi?"


Juyowa ta yi, dan a lausashe ya yi maganar yanzu ta zuba masa ido

Kai ya gyafa ya sake kausasa muryarsa yana kallonta ya ce" To ki kama kanki, ki tuna babu wanda ya sakani a wannan matsalar sai ke......, Bakida hurumi a wannan maganar, bakida abinda kika isa ki ce a wannan maganar sai fatan na shawo kan yata ta aminta da maganar nan, idan har kika kuskura kika yi wani abu na rantse maki sai kin kasa gane kanki bale har wani ya ganeki!"

Da ido ta rakashi har ya ficewarsa
Bayan fitarsama ta dauki minti biyu kafin take mikewa tsaye ta yi dakinta
Wayarta ta lalubo ta zauna ta ci gaba da doka wayar sarauniyar dogon dutsi, sai dai amsar daya ce wayar bata shiga

Wurgar da wayar ta yi ta doka hannunta a jikin abin gadon nan ranta bace ta ce" Ni zaka dauka , ka kaini gaban dan cikina ka gurfanar da ni, n bashi hakuri sannan na bashi yata kyauta? Yar da nake da burin a aurenta na tara dukiyar da ban taba tarawa ba a duniya? Yar daya mace kwalin kwal ka zo min da maganar wai idan ta shiga ba zata dauki lokaci ba zata zamto itace magajiyar garin Agadaz? Ta yaya? Ta ina? Lalle yau da na same ki a wayar nan sai na fara maki alkawarin idan har aka aurawa yata UMUGHLUK ITIFAL Walahi walahi sai na halaka ki da kaina kafin zakin sarakai ya kama ki,!" Ta idasa tana cure daurin dan kwalinta ta zauna ta shiga tunanin abinda ya dace da hanyar da ta dace ta bi dan magance wannan matsala, ta san waye mijinta, tanada iko a garinsa ama fa a wajen talakawa, bata isa da shi ba, abinda ta fi karfi kishiyoyinta ne, summa dan ta tara yaya da shi fiye da su, dan a cikinsu daya tak ce ta haihun itama shamatarta ta yi, ama idan abu ya hado su magana daya yake yi baya sake bi ta kai kuma ta zauna dar ba maganar dagawa


____________________________________


*Madina garin manzo, BAYAN WASU KWANAKI*


"Ya salam ki daidaita numfashinki, dage nikaf din ki shaki numfashi haba BAHIJA!" Kawarta ta fada a dan rikice a lokacin da ta shiga wani irin numfarfashi sama sama tamkar zata sume

Yadda tace din ta yi, watau ta dage nikaf dinta domin ba zata iya shakar iska da kyau a rufen nan ba, sannan ta mike ta dan yi gaba kadan ta lumshe idannuwanta har numfashinta ya daidaita sannan ta sake dawowa ta zauna ta sake zuba masa ido tamkar zata ciro idannuwan nata ta lika a fatar jikinsa


A nutse yake tsaye ya basu baya, shigar dake jikinsa yau sak irin ta larabawa ce, wato ya daka alkyabar nan tasu mai ruwan yelow, ya dora hirami a saman shigarsa ya dan nade hiramin baya, haka kuma a tsayen da yake hannunsa daya a bayansa haka a jimke, dayan kuwa daga gaba sunna magana da wani mutumen da kana ganninsa ka san shima baba ne

Kai ta dora saman table din cin abincin a hankali idannuwanta suka ciko da kwallah tana sake yi masa kallo wanda ya wuce misali

A tausashe balaraben da suka yi aikin umurar tare ya sake dubanta duba daya tak ya dauke dubansa yana dan sake kallon restaurant din a ransa yana ayana shi yasa hotel din nan wani lokacin takeda matsala, domin akoy dan wajajen da ake hadewa mata da maza ba wajen ibada ba, hakan kuwa ba dadi, dan yanzu matan da mazan duka sai a hankali,

Dogarinsa ne ya karaso ya yi masa bayani kasa kasa sosai, a kan maganar juyawarsu gida ne

A tausashe ya ce" Aa, ka daukar mana na gobe idan da hali, garina na zuciyata, ga kuma Auta"

Kai ya gyada ya juya cikin takun karfinsa, shima shigar larabawan ce a jikinsa abinsa


Kujerun alfarmar dake ajiye suka karasa suka zauna, a nutse ya lankaya carbinsa a hannunsa ya sake duban Abu huzaifa ya ce" Sosai sunna saka abaya, zan iya ce maka a yanzu a garina Abaya da lafaya ta zama kayan ado a wajen yan mata da kuma matan aure, ai sunna son shiga irin ta larabawa"

Kai ya gyada yana murmushi ya sake duban ASADEEK ya ce" Ka san me ya fi bani sha'awa da kai?, Irin yadda kake nema, kanada dama sosai, ama kuma kana nema sosai, babu ruwanla da kwonciya a nemo a kawo maka ka ci ka tada kai, idan dai zaka mayar da taro kadago baka tsoron hakan"

Murmushin da ya yi a yanzu shi ya saka BAHIJA furta" Wayo Allahna, zan je, walahi yau zan je, zan tunkare shi"

Kai kawarta ta girgiza tana dafe goshinta ta ce" Dama ki daina ba kanki wahala, irin larabawan cen ba zasu taba auren bak'ar fata ba, bayan wannan irin yafda kike tsoronshi ina tsoron ki zamto baiwarsa, ki duba ki gani sati biyu kennan ke ko masalaci baki je ba, tun baki san lokacin da yakan dan wulgawa ba har kika sani, sau nawa kina yinkurin hakan bakya iyawa, uwa uba kwaliyar yi kike yi ama kamar bai san da ke ba, ki yi hakuri kawai ki........."

Ido ta zarro sanadiyar gannin Bahija ta mike ta nufi inda suke din

Sai dai kafin ta karasa ta ga rusheshen bodyguard dinsa ya tsaya a gabanta fuskarsa ba alamun dariya a kausashe ya ce" Ina zaki je?"

Gabanta banda dokawa babu abinda yake yi, hakan ya haifar mata da fitar hawaye tana shirin bashi amsa suka ji muryar Balaraben nan ya umarta kan a barta ta karaso

Wata irin ajiyar zuciya ta sauke jikinta har rawa yake ta karasa wajen da suke zaune ta yi salama muryarta har tana rawa rawa

Sannin mahinmancin salama ya saka shi amsawa a saman lebensa sannan ya dan juyo kadan ya sake kallonta ya kuma dauke kansa

Tsaye take tana murzar hannunta har sai da balaraben ya ce " Bismillah mana yan mata?"

Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta zauna a kujerar dake face da su gabanta na ci gaba da faduwa

Rasawa ta yi, shin kuka zata fashe da shi ko kuma ta ci gaba da kokari har ta gama abinda ya kawota?
Nikaf din ta sake dagewa dan ta tabata bai ga kyanta da kyau bane wannan mutumi

A sanyaye ta ce" Dama , dama zuwa na yi, ina so na ganshi......"

Inda ta nuna din ya kalla, sai kuma ya sake kallonta

Dan murmushi ya yi ya furta" Bismillah"

Sake kallon balaraben ta yi da kyai, gannin ba zai basu waje ba ya sakata sauke ajiyar zuciya, kirjinta na ci gaba da dokawa ta sake kallon bawan Allahn nan

A hankali ta ce" Sunnana BAHIJA, ni yar sarkin garin Tanut ce, mun yi tafia tare har gashi za'a fara komawa, ban san shi ba, kuma ina son na sanshi..... Ina matukar son na san shi"

Da mamaki balaraben nan ya kalli ASADEEK, wanda idannuwansa kawai ya lumshe yana mamakin lalle lamarinta ya girmama, al'amarinta ya giga,
Dan sake kallonta ya yi, a sanninsa masarautar TANUT da ta AGADAZ masarauta ce ta familly daya? Bata sanshi bane ko menene?

Da mamaki ya ce" Aa, baki gane shi bane? To ai.................."


"Hhhhhhhhhhhummmmmmm, " ya yi gyaran muryar da ta saka su kallonsa gaba dayansu

A hankali ya kalli wajen pepper da byro ya janyo su cikin nutsuwa ya rubuta mata numbarsa ta sirri ya mika mata ta hanyar ajiyewa a saman table din hankali ya sake kallonta da firgitatun idannuwansa sannan ya ce" Cl me."

Wata irin ajiyar zuciya ta sauke hadi da sakin lalausan murmushi ta dauki takardar har kamar ta duka wajen godiya ta juya ta nufi wajen kawarta kamar zata kwaso shoki dan farin ciki


Da mamaki ya kalli ASADEEK ya ce " Me kennan MAN?"

ASADEEK ya dube shi, yana basarwa ya ce" A ina fa?"

Murmushi ya yi shima yana girgiza kansa kawai ASADEEK kuwa ya dantse lebensa a kasan zuciyarsa ya ayana' Yaro man kaza.... Koda yake ba laifinki bane laifin zuciya ne'
Daria ta fashe da ita tana sake rike takardar nan da hannayenta biyu biyu, ta kai daidai hanci ra ta sinsina tana lumshe idannuwanta sannan ta dauki jakarta a hannun baiwarta ta saka tana kallonta ta ce" ki rike takardar nan Mudin ranki kin ji?"

Kai ta gyada da sauri tana rikewa da kyau din

Da mamaki kawarta ta tafa mata ta ce" Lalle na yarda, kin kamu sai gyaran Allah, Amma kawata bakya tsoron wulakanci irin na Da namiji?, Kika yarda ya san kina sonsa bakya tsoron abinda ke iya haifarwa? Kin san fa maza bale masu kudin nan"

Murmushi ta yi ta ce" Ai koda ya yi girmansa ne, kawata kin ji hannuna har yanzu kanshin turarensa yake?, Zan bi ku gida jibi dan burina na je na samu mama da wannan albishir, na tabata sai ta fi kowa farin ciki domin irin burin namijin da take min kennan"

Haka suka ci gaba da hirarsu cikin sakewa, wani tsare tsaren da basu yi a kwanakin da suka shude bama sai yau suka yi shi a sake hankalinta kwonce, domin gani take yi tunda har ta damu number wayar mutumen cen, komai ya gama sai shafa fatiha, ta yi miji na kece raini, dan kwalisa mai kanshi.


__________________________________


Yan umarah masu babar tafia watau VIP tuni jiragensu sun fara dawo da su gida

Tun da safe suka karaso garin Niamey, daga nan luma suka nufi AGADAZ a wani jirgin, hakan ya sa tunda ya samu ya shige, sallah kawai le fitar da shi ta boyayiyar hanya har dare ya shigo ya kwonta dan samun hutu ko yayane, domin ya sani a gobe zai yi fitar wuri Fada dan gannin abinda ya faru bayan baya nan


____________________________________


Tarba ce akai mata wace ko mahaifin nata ya sameta ya more

Yayunta biyu suka daukota daga filin jirgi, sai sangarta take zuba masu irin ta sangartatun yaya, ga baban farin cikinta fa murnarta shine ta karasa gida dan ta sanar da abinda ke zuciyarta wa mahaifanta

Gaisar da ita ake yi, ama sam hankalinta ba a kan kowa yake ba, ga alkyabar da ta dora sai walwali take hakoran makarta na wal wal wal

A nutse Mahaifinta ya mike ya tarbota a jikinsa yana murmushi ya dago fuskarta ya furta" Farin cikin Aba?"

Murmushi ta saki ta karra dubansa ta ce" Abana"

Mhaifiyarta ta karaso itama fuskarta dauke da fara'a tana kamota jikinta ta ce" Mu karasa ciki, wannan farin cikin fa?"

Ajiyar zuciya ta sauke tana daga idannuwanta tana hangensa a idannuwanta a lokacin da zasu tafi jiya, kamar ta biyo su su dawo tare

Har sun shige mahaifinta ya dan biyo bayansu yiwa mahaifiyarta maganar ya ce" ki tabatar kin shirya tafiyar nan, da sasafe zamu fita, sannan ki tabatar a yau ba sai goben ba kin fara yi mata maganar dan ta san da abinda ke jiranta"

Jiki ba karfi ta gyada kanta ta shige cikin tana kallon yar tata da ta cire Alkyabarta ta kuma cire abayar dake kasa daga ita sai Pant da bra ta dauki tawul ta nada a kirjinta tana murmushi ta ce" Mama, tsaya na fito mamana, mamana akoy hira"

Mahaifiyarta ta dan zarro ido ta ce" Ke baki gaji bane hala? Aikin umura ga kuma zaman jirgi gaki da son jiki?"

Murmushi ta yi tana girgiza kanta ta ce" Mama, ba zaki gane ba, abinda nake tare da shi ya bige maganar gajiyata, mama bani minti daya"

Da murmushi ta rakata sannan ta mike ta janyo abubuwan da aka zuba mata abinci ta shiga zubawa a cikin plate tana dan duba wayarta

..........MAMA........

Ta fada a hankali bayan ta zauna daf da ita

A hankali ta dora kanta a gefen kafadunta ta ce" Bam taba tunanin a Africa, a karamin gari irin namu zan hadu da shi ba.......,ama na tabata zuwa ya yi, da ganninsa ba haifafen kasar nan bane........, Mama ban taba gannin tsarin halita, nutsuwa, kyau, aji da nutsatsen arziki irin nasa ba, shi din ba tara bane, goma ne..... Mama tunda na je ko zama ban samu ba kulun tunaninsa, har kuka na yi............ Mama na samo maki sirikinki, wanda kike min fatan samowa, mama zan faranta maki ranki, zaki yi yadda kuke so, farin cikinki zai zaga duniya, zaki kece raini......idan kika ganshi sai kin yi farin cikin da baki taba yi ba....., Baban burina shine ya amsaniya kuma yarda da ni"...... Ta karashe maganar tana dora kanta a kafadar mahaifiyarta, wace ta yi mutuwar zaune

Hankalinta tashe ta dago fuskarta tana kallonta, a sanyaye ta ce" BAHIJA, maganarki ke kaini wani tunani daban, kamar wace ta fara soyaya?"

BAHIJA ta yi murmushi har idannuwanta suka cika da kwallah ta gyada kanta a hankali ta ce" Mamah, soyaya kam na shigeta mai karfin gaske Mamah"

Da sauri uwar ta mike tsaye tana sake fuskantarta

Ajiyar zuciya ta sauke mai zafi da kunna tana kallonta

Sai kuma ta dawo ta zauna bakin bed tana dauko yannayi na serius ta ce" Ki saurareni da kyau BAHIJA, kina jinna, ko me kika dauko daga tafiyarki li ajiye shi ki zubar ki fuskanceni da kyau, wannan magana da kika dauko sam ba zata yiwu ba, domin mahaifinki ya bada ke wa UMUGHLUK ITIFAL!, A gobe gobe zamu je maganar nan in sha Allah, idanma me kika dauko ki barshi domin lin san ba maganar wasa ko ta kawo wasa a ciki!"


Wata irin zubowa kasa ta yi har tawul dinta na kwoncewa daga kirjinta yana neman faduwa

Bata damu da riko shi ba, sai idannuwanta da ta fitar waje gaba daya ,

Da wata irin muryar kuka tana kallon mahaifiyarta ta ce" Mama? Ni? Wa zakin sarakai?, Mama ni? Mama yaya ina maki maganar namiji, namijin da na gano da idannuwana, wanda na kasa zuwa masalaci dan kar ya bace min, ke kuma kina min maganar wani wai shi zakin sarakai? Mutumen da babu wanda zai ce ga kamaninsa? Aba kulun yana kwatanta kamaninsa dan shi kadai ke ganninsa ba rawani, ko ke kin taba ganninsa ba rawani? Ta yiwu wani nakasashe yake, ko wani mai cutar hauka ne irin na kanwarsa? Wai mema ya kawo maganata ni da wani ZAKIN SARAKAI? Mama, ki cireni a ciki, bana gaba bana baya Mama, dan girman Allah ki ga abana ki sanar masa walahi walahi idan ya saki ya aurani wa ZAKIN SARAKAI komai na iya faruwa, ciki harda mutuwata, uwa uba harda tonuwar asirin mutuwar GWAG.................."




HADIYE maganarta ta yi, sakamakon gigitacen bakon abin da ya ziyarci fuskarta, wanda bata taba ganni ko hasashensa ba, HANNU ne mai zafi fa kunna ya sauka a fuskar da hannu bai taba hawanta ba dai dan ya shafata ko ya yi mata kissssssss,

A haukace uwar ta mike tsaye, jikinta na rawa tana kallon mai aikin nan

A haukace Yar ta budi baki zata sake kurma wani ihun ya dake saka bayan hannu ya kai mata ............













Asalamu alaikum wa rahamatullah 🥰🥰🥰🥰
8/13/22, 22:56 - Buhainat: *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍?*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*


🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻
*OUMOUGHLOUK ITIBEL*
_(ZAKIN SARAKAI)_
🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻

_FREE BOOK_

*Na*


*SAJIDA NIGER*





🔟




Wani bahagumen duka da bayan hannu ya sauke mata a gefen bakinta wanda ya sakata kusan summa a zaunen da take ta kwala wani ihun ta nemi jirkicewa kasa tana sakin tawul din gana dayansa, domin ji ta yi kamar ranta za'a raba da gangar jikinta

Sake binta ya yi ya maka mata kafarsa ya sake dagawa zai kuma dima mata wani dukkan mahaifiyarta ta rukunkumeshi tana ihu da kuka tana sake rikeshi idannuwanta waje tana fadin" INNALILAHI WA INNA ILAIHI RAJUNE, KASHETA ZAKA YI? KASHETA ZAKA YI?"

Jajayyen idannuwansa ya sauke a kanta, da karfi ya hankadeta itama gefe sannan ya nuno masu yatsarsa gaba dayansu muryarsa a kausashe ya ce" A kan mulkina, ina iya kashetan , ke koda ita daya na malaka idan har sakaken wawan bakikin mai jaza min masifa ya sake furta mata sirrina da hannuna zan shaketa sai na kasheta sannan na saketa!, Ke ba sakarya bace? Ke ba mahaukaciya bace? To ki sani wahalar sai dai ta kare a kanki, ba dai ni kadai ba, wato ke baki iyawa bakinki ko? Jira kike na zo na fada maki sirri ki bazani ko? Sai dai mu lalace baki dayanmu dan na rantse maki da Allah tare zamu rufta!, Kin sakata a gaba dama har

Please Login or Register in order to submit comment