Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya amsa gaisuwarsu da murmushi kawatace sannan ya zauna a kujerar da take tasa ce, dama babu wanda ya hauta yana duban Umma cikin fitar haruma kamilalu ya ce" kin jima a nan ba Umma?"

Umma ta yi murmushi tana kallon Matarsa da ta dawo dauke da abin sha mai sanyaya zuciya ta tabe bakinta a boye sannan ta budi bakin tana kallonsa ta ce" Ban jima sosai ba Yarona, ai ko wuni na yi ba zan gajiya ba tunda magana ce da ta shake ka, ka ga kuwa dole na bada hankalina dan gannin na tsaya tsayin daka a kan komai"

Kopin ya amsa dauke da jus na Tataciyar Kankana uwar ruwa ba siga sai madarar peak da aka kwalala ta zamo mahadin markaden kankannar ya sakar mata murmushi a saman lebensa ya furta" Allah ya maki albarka"

Murmushin ta mayar masa itama tana jin wannan Adu'a har kasan zuciyarta sannan ta mayar ta sake dawowa ya zauna a daf da kafafuwansa ba ruwanta da wata Umma bale Auta da sam hakan ba damuwarta bane ta kamo kafarsa ta dama ya dora a saman cinyarta dake dauke da tufafi fati irin shigar mata, watau lesh mai tsarin kwaliya fa kyau a hankali ta shiga dan mamatsa masa yatsunsa wanda hakan ya saka shi dan sake kureta da ido sannan ya dauke dubansa a hankali ya maida kan Umma da mamaki ya kusan kasheta da tunanin lalle tana sake fa da yarinyar nan, itace har ta samu damar taba kafar ASADEEK? lalle wannan din wani shinfida ne dake nuna mata cewa gaba ana iya zarce haka

Lebe ta dantse a ranta ta ayana' Sakarya, babu anfanin haihuwa ama sarauta da kudi sun zaunar da ke shekara tara, haka zaki kare in dai ba zaki tafi ba, barama na cusa maki bakin ciki'

A bayane kuwa ta ce" Dangane da maganar sadakin da ka ce Bafanka zai biya ne na zo mu sake yin maganar sannan mu tatauna a kan maganar yan zuwa daurin aure da komai da komai, ka san aurenka ake magana, ya zama wajibi a sheda"

Daga shi din, har Matarsa da Auta dagowa suka yi suka zuba mata ido
Bama matarsa da ta dan dakatar da murza kafarsa da take yi ta zubawa Umma ido gabanta na dukkan uku uku

A hankali ya janye dubansa, a ransa yana ayana' me kennan wannan Umma ta yi? Kai tsayen nan zata fitar da maganar nan a gaban HUZNAH? Koda ya mata hirar ya dace a fan ringa kiyaye idannuwanta, ba dan komai ba sai dan a daraja hakurinta da kawaicinta'

A fili kuwa sai ya dauke duban nasa a tausashe ya dora saman fuskar HUZNAH

Umma ta ci gaba da fadin " Ita din y'arsa ce, idan har ka ce ya biya sadaki ai ba'a mutunta ba yarona, ya dace mu kai sadakinmu, sannan mu ware yan zuwa daurin aure da yan dauko amaryar ko?"

Idannuwansa ya lumshe wannan karron, a sanyaye ya sake duban Auta da gaba daya ta daina dukkan abinda take yi tana kallonsu su dukansu

Dan murmushi ya sakar mata kasa kasa ya ce" UMMA, idan lokacin ya yi zaku tafi da sadakin......., Ama bana son gangami domin bana bukatar hakan"

Umma ta sake dubansa ta ce" Ba zaka je daurin auren ba kai yarona?"

ASADEEK ya dubeta da dan mamaki, Shi? Kai yau fa Umma gaba daya sai wani abu take yi bako a wajensa, to me ya hada shi da zuwa daurin aure shi kuwa bayan tarin abinda yake gabansa? A yanzu haka shari'ar da zai zauna a gobe ta manyan sojoji uku ne, an kashe daya a cikinsu kotu ta turo masa dan ya yi tsakani sannan su koma kotu a dora da shari'ar domin so ake yi idan har aka gane waye makashin a zartar da hukuncin bisa shari'ar musulunci, dan abin na neman ya zamto ruwan dare, sai kuma kawai ya tashi ya je wani shirmen auren da suka hada? Shi fa wasu abubuwa ne yake tunanin zai samu daga yarinyar ya sa zai amince, ko meye ai mataki ne na gane sirrin dake birne mai mahinmanci!

Kai ya dan girgiza bai ce komai ba

Cike da kissa, Umma ta ce" To shikenan, in sha Allah hakan za'a yi yarona, bara na je na ga me ake yi a bangaren madafa, yau kana gida bana so a maka abinda ba zaka iya ci ba"

Da ido kawai ya iya raka Ummar, wani lokacin mata kam na abubuwa a duniya na kai sake, sai dai hakuri kawai


A hankali HUZNAH ta sauke kafarsa daga saman cinyarta ta mike a nutse ba da kwaramniya ba ta nufi hanyar fita ba tare da tace komai ba

Muryar Auta a ba zata ta saka HUZNAH dakatawa da juyowa ta kalleta, haka shima da sauri ya kalli Autar yana son fahimtarta, domin sunnan HUZNAR kawai ta kama sannan ta mike ta ajiye kayan rubutunta a nan ta fice ba tare da ta ce komai ba

Ido ya dan kifta yana cike da tunanin kennan Auta kan gane wasu abubuwan wasu lokutan? To in ba ta gane ba'a kyautawa HUZNAH ba bai fahimci reaction dinta ba, bayan ba wani shiga harkar junna suke yi da Huznar ba, ama kuma basa fada ko gaba, kawai ba ruwan kowa da kowa ne, kowa ta kansa yake yi

Kai ya cira ya mayar kan Huznah

Hawayen dake saman kuncinta ya saka shi zuba mata ido yana kallonta

A hankali ta dawo ta zauna a saman kujera tana fuskantarsa muryarta a dan rikice ta ce" Aure zaka yi ?"

Gefensa, watau daf da shi ya mata nuni da idannuwansa, dan haka ta karaso ta zauna tana sake zubawa kasa ido

Shima nazartarta kawai yake yi har sai da ta tsargu ta dake dubansa

Murmushi ya sakar mata kasa kasa ya ce" Wai ba, aure zan yi, suka ce saura kwana 12 yau"

Idannuwanta ta rintse sosai, domin bata taba tunanin a irin yadda rayuwa take ita da shi dan ta ji irin haka zai iya daga mata hankali ba, sai dai ku gane, koda auren hadi ne, koda babu wani abu da ya mashe su guda, shi din mijinta ne, abin alfaharinta, kuma ya isa a yi kishin nasa, dan haka ba zata ji haushin kanta ba dan ta ji kishin abinta, kawai dai ta ga ta yi garaje ne, bayan ta san menene gidan sarauta tunda itama daga ciki ta fito, ko a gidansu daki hudun nan na matan mahaifinta mata ne nasa yare daban daban

Sunnayen Allah ta yi ta ambata a cen kasan zuciyarta, hakan ya sa ta samu kwarin gwuiwar kamanta halaya irin na matan zamanin da ya shude

A sanyaye ta furta" Allah ya sa hakan shine alkhairi a garemu baki daya, Allah ya sa idan ta shigo ta kasance mabudar warwarewar abinda yake cikin duhu ko menene a cikin Fadarka UMUGHLUK ITIFAL"


Ya ilahi Manzan tsira, bai taba tunanin haka ne zai fito daga bakinta ba, duda ya shiryawa tarota tsaf, sai gaba daya ta saka shi zuba mata ido yana kallo kamar bakuwar Halita, ga dai yannayinta hankalinta ya tashi ainun, ga yannayin zamanta abinda ya fi karfi a auren bats samu, domin rashin samun sex shine babar matsalar lalacewar aure da kuma rashin samun care daga wajensa, banda hirar baki yana kiyayewa dukkan abinda zai hada jikinsa da nata, dan jikinsa na amsawa, ya murde tamkar karfe, idan ya zo a haukace sai ta koma ta langwabe, ya yi kwana da kwanaki yana jinyar kansa, da bacin rai da komai, shi yasa kawai ya dangana sannan ya bata damar salamarta ko zata rayu irin rayuwar farin ciki? Ama firrr ta kiya ta nuna zata zauna da shi a haka, bayan ya san koda yaushe tana iya gazawa, dan Adam take ai ba cikin jinsin da Allah bai halitawa bukata ba, wannan yannayi kuwa ya fi kowa sanninsa da zafinsa


A hankali ya kamo hannayenta ya janyota jikinsa a ba zata ya rungumeta a cikin kirjinsa ya dora hancinsa a saman gashin kanta da ya ture dan kwalin da kansa ya lumshe idannuwansa yana shinshina
Ya Allah ga mace fa, har mace, bafilatana mai kawaici da nutsuwa, halalinsa mai kanshi, wace da ace yanada lara bulaleta zai wanzar da rayuwa irin ta mafarki da ita, burinsa da iyalinsa idan suka rufe a bangarensa ko nata har tsere su yi, burinsa mace ta ringa masa yawo a ita dinta yana kallo, shi so ya yi zumuntarsa da matarsa ya kasance ko anguwa ta je idan ta tuna ta zabura sannan ta saki murmushi, a tsarinsa zasu kadance aminan junna, mashawartan junna , kawaye, kuma yaya da kanwa, zasu rayu cike da adinni da koyi da manzon Allah Sallallahu alaihi Wa salam, sai dai kashhhh duka kaf katangar nan na masa tsayuwar giginya tsakaninsa da ita,domin ko yaya ya so sakewa yanzu gwaurancinsa zai zake ya haifar masa da ciwo, ama kuma ko menene ya kaima Allah kukansa, ya san zai samu sauki yau ko gobe, ama ba wai ta karrin aure ba, aurenma BAHIJA yarinyar da ya ji kallonta kadai na neman saka shi amai dan ta yi abubuwa kusan uku da suka saka ya sarewa ƴaƴan yanzu har yake dubanta da wawuya wace ta bari shedan ya yi tasiri a kanta!


A hankali ya furta " Kar hakan ya dameki MATAR ASADEEK, ke kin san sunna ne babu wani tasiri a tafiyar"

Idannuwanta ta dago a hankali tana kallon pink lebonsa, sannan tana shakar sansanyan turarensa ta ce" Ni kuwa zan damu,domin ina kishin mijina.........., Kuma tasirin nan da muke nema muna barar mu wayi gari mu ga cewa ya tabata"

Tabas hikimar iya hira da mijima abu ne mai kyau, murmushi ya sakar mata yana dubanta ya rike habarta a hankali ya ce" Menene abinda ya dace a yi wanda zai sanyaya zuciyar mai ASADEEK?"

Ya Allah kamar ta daka tsale dan murna haka take ji, dan wana idannuwanta ta yi tana kafe lebensa da kallo, kasa kasa ta ce" Ana iya yin sharar fage da rarashi irin na uwar gida, sannan a goya ni, harfa da su kishin laifi ake yiwa mata, irin na dira na yi ta ihu kana rikonin nan ur excellency"


Murmushin da bai shirya ba harda dafe haba ya yi yana wara manyan idannuwansa madu launin ja kadan ya ce" To fah, ke da ba mai shigar jinnu ba HUZNAH? Rada min a kunnena zaki rakani zuwa shan ice cream da dare a fitar sirri?"


Da dariya a fiskarta ta ringa gyada masa kai sannan ta dora kanta a saman kirjinsa ta kwontar tana jin yau tamkar wata gagarumar sallah ce a wajenta, rana mai daraja ce ainun a wajenta, sai take jin kama zata summe dan dadi..........................................................................
( Lalle zaku shiga uku, watau rayuwa sak irin ta an gayu abinku , laushi ruwan sanyi😁 bayan ga mata tafe🚶🏻‍♀️🚶🏻‍♀️🚶🏻‍♀️🚶🏻‍♀? oh)


___________________________________



A TANUT



A cen cikin dakin da aka ware dan gyaran amarya a yau rana ta uku da tsayuwar zancen da ita mai tafiyar bata san da shi ba, sai a yau mahaifiyarta ta shirya tunkararta tunda a kulun idan za'a je wannan bangare na koyon abubuwan da ake koya mata sai an zarre mata ido take tafiya, domin bata ga anfanin tafiyar ba, bata san ma'anar yin hakan ba!



Daga ita sai tawul fari a daure a kirjinta, wanda ya rikide ya koma kalar yelow dan abinda ke mulke da jikinta, ta rike shi tsaf tana harare harare , a cen kasan zuciyarta kuwa cike da tunani kamar kanta zai fashe dan rashin amsa

HINDU ce ta yi salama tana kallon Buzayen dake zaune wa'inda hausar kirki basuda ita ta yi dan murmushi tana sake rike abinda yake hannunta da kyau tana boye shi ta ce"
8/13/22, 22:57 - Buhainat: *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍?*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*


🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻
*OUMOUGHLOUK ITIBEL*
_(ZAKIN SARAKAI)_
🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻

_FREE BOOK_

*Na*


*SAJIDA NIGER*





1️⃣7️⃣


Tana boye abin hannunta da kyau da yaren hausa ta dube su tana daga masu hannunta tana murmushi ta ce" Yan kundun uba ana aikin ko?"

Dariya ce ta kwacewa NADIRAH wace ta hada gabas da yama tana aika masu harara, domin aiki ne suke yi mata mai masifar zafi, gashi ko magana sai wani iri suke yi mata sai su ce muryarta tana tashi sama a dole sai ta tausasa muryarta kuma sai tana yi tana ajiye dubanta tana hutawa ba dan ta gaji ba, ta rasa wannan masifa da me ta yi kama, jama'a burinta su fece da innarta su tafi kauye, itafa lamarin birni nema take gannin an cika fariya, wai ace yau a gidan nan innarta abinci kala biyu take yi safe daban dare daban? Kala biyu fa jama'a kuma da kunduma kunduman nama a ciki, an tatso nono an saka a wai shi friza an shake, yar iska ce ita zata sha kankara sanyi ya kamata? Ai innarta na zuwa ta tatso mata mai dumi walahi, ya fi tsaki ai, gaba daya sai a mikota gaban matan nan da magana ke masu wahala ace su shafa mata kayan shafe shafe irin na yan gayun da suka gagari iyayensu, yo suka gagari iyayensu mana, abinda a kauye ana fada cewa mai shafa abin nan dan ya yi ja dan iska ne? Abu dai sai karra yawa yake yi sai Adu'a kawai kuma Abanta na kallo? Gida an saka karti biyu na gadi babu mai fita sai innarta sai Abanta, umantama bata zuwa ko'ina bale ita rabonta fa rana ta kwali fatar jikinta kwana biyu kennan, sai dai ta hangi rana , rana ta hangeta, idan ta tuna wannan abun hankalinta kan tashi, bama idan ta tuna wani shegen laushi da fatarta ta fara yi da wani kanshi da take fitarwa sai ta ji ta sarewa duniyar, yau idan ta koma LABA aminu yace ta zama yar iska ba shi ba ita fa ina ake so ta saka ranta? Dama innarsa ta san sai gyaran Allah, dan tana iya cewa ta zama yar iska ta haramta aurensu da Aminu bayan ita da Aminu sai balbalin balaki ne kawai zai iya rabasu da junna


HINDU itama tana yar dariyar kasa kasa ta sake duban NADIRAH da hausa dai ta ce" Ki daina dariya da karfi kar su koreni su ce sunna aiki ina mayar da su baya mana yar gudaliyata"

Sai kuma ta koma yaren buzanci ta dube su ta ce" Barkarku da aiki, gaskiya kun iya aiki , Allah dai ya karra girma"

Amsa a wani yangance ta samu, ita dai ba shine a gabanta ba, abinda ta dawo da shi ta karasa ta yi zaman kaka gida ta basu baya ta saka y'arta a gaba ta ciro leda biyu ne , dayan a cikin galan dan karami, dayan kuwa a kule a leda guda ta girgiza ta bude ta ce" Maza maude ki bani galan din da shi zan koma gobe in sha Allahu"

Abin take kallo, sai ta kalli Innarta ta ce" Inna, shima maganin zahin ne?"

Innarta ta harareta ta ce " Ni wai Indi a me kika daukeni ne ni? Ya du idan na miko maki abu sai kin tsatsareni da tambayoyi kamar wace zan saka maki susau a ciki? Kin maude ko sai na moda maki mari?"

Da sauri ta kafa ta rintse ido a tunaninta wani dabri dabri zata ji, ko kaifin wani abin, sai ta ji rubutu ne babu dabri babu kaifi sai kanshin tawada da irin kanshin rubutun nan, dan haka ta shanye shi tassss, ta miko hannu ta amshi na ledar shima ta tila ta kafa a bakinta ta shanye shi tassss tana murmushi ta ce " Innata wannan ai rubutu ne dama kin saba bani walahaula a gida ai, na zata wancen abin ne maganin zafi ko me? Ki ga fa wanda kike sakani tsakiyar dare, innata sai na yi barci ba gaba ba baya barci ya yi masifar dadin nan kike sungumata ki tsomani wai dan kanoma da bakin duniya, Innata ki duba ki gani kika wuni kina rubuta yusufa kika wanken na sha wai meye ake yi dan Allah?"

Hindu ta yi tsuru tsuru zata bata amsa mai murzartar nan ta taso da hadi na kwai , da sauro Hindu ta boye abubuwan da ta shigo da su tana watsa mata hakora

Matar ta sakata mikewa ta dubi Hindu ta ce" Ki koma ciki, zan mata wankan madara"

Hindu ta yi wata yar dukawa ta ce" Yanzu kuwa hajia, Yar gidan Inna sai na kawo maki maganin zafin zan fada maki, ai zafi ke rarakarki yar albarka sai na dawo"

Kamar ta bi innarta haka take ji, wai wankan madara, wannan abuma na kona mata rai, ruwan madara da ake sha a yi kat ita dumamashi ake yi a masa hadin su zuma da duminsa a sakata ciki a dora mata kokomba a gurmin idannuwanta a lafta mata hadin kwai da nescafe da madara a fuska a mata gargadin banda magana ko dariya kar ta bata fasalin fuskarta? Ai ita take kan gannin rayuwa , tsakninta da su bata san ba sai ta hada su da Allah ko ba sai ta yi ba? Ta dai zubawa sarautar Allah ido

HINDU na komawa ciki ta tarar da Fadime ta gama girki tuni tana gyara komai , falon kansa yana fitar da dadadan kanshi ta zauna saman kujera tana fadin " Ya arahamani ya rahimi Allah mai gabas da yama, kudu da arewa, mai tudu d gangare na gode maka da ka dawo da ni lafiya ka saukoni daga saman jaki a cikin kasar sahara"

Fadime ta sake juyowa da mamaki tana kallonta, ruwan da ta yi niyar daukowa ta dauko ta zo kusa da ita ta zauna tana kallonta ta ce" Yanzu tsakaninki da Allaj daga Timiya kike HINDU? Me yasa bakya jin magana ne ? Yanzu da ake tarewar nan da aka tareku fa? Kariya ba tana Adu'a ba muma kuma muna yi? Haba HINDU"

HINDU ta dauki ruwan sanyin nan ta sha ya isheta ta ajiye tana yin mika ta gajiya ta ce" Aunty tunda na dawo ai shikenan, ama aunty na ga ikon Allah,malamai irin namu masu tsoron Allah, ba malaman tsubu ba, Aunty tsaf aka rubuce wakadimna kafa dubu arba'in da daya aka bani na wanke da dan ruwa kadan , sannan aka rubucen wasu na tsarin aka wanken na kamo hanya, kin ga harda tsuminsu na kauye na matan sarakansu aka bani, ai ni tafiya ta yi kyau sai hamdallah kawai, nema kuwa du abinda akace in ba Indi zan bata ne, Allah ya kama mana ya tsareta"

Haba ta rike tana kallonta ta ce" To ina rubutun yake?"

Hindu ta dubeta tana murmushi ta ce" Haba ke kuwa, a saman jaki fa ana tafe rike nake da galan din ba da igiyarsa ba, yaya zan yi wasa ai fatana na shigo gidan nan, ina shigowa na bata ta shanye tasss, Aunty yaya maganar ruwan zigalan kin saka min a frij din?"

Fadime ta sauke ajiyar zuciya tana jinjina kai ta ce" Na saka, na zuba peak dinma a ciki, sannan na markada maki kankanar itama, kuma na markada cocumbar da peak din, tunda kin riga kin saka kanki a tunanin da bashida wani tsari ai sai ki yi, ni dai ido ne nawa, kuma in sha Allah yau zan mata bayanin nan, tambaye tambayenta sun isheni gaskiya"

A firgice Hindu ta mike zaune daga ringesawar da ta yi ta yi wiki wiki da ido ta ce" Yau yau Aunty?"

Fadime ta gyada kanta

Hindu ta ce" Ama me yasa yau?"

FADIME ta dubeta da kyau ta ce" Kamar yaya me yasa yau? A irgenki yau saura kwana nawa igiyar aure ta hau kanta?"

HINDU ta sake yin wani iri ta ce" To ama, me zai hanna ki bari in je gida sai ki sanar mata?"

Fadime ta girgiza kanta ta ce" kin ga ki daina irin wannan sarewar, kar ki saki ko nuna gazawarki a gabanta walahi, kuma da kike cewa ki je gida ya dawo daga tafiyar ne?"

HINDU ta ce " Aunty dan Allah kar ki yi maganar nan yau, walahi rikitamu zaki yi, karma ki mata maganar nan"

Fadime ta mike tana tabe baki ta ce" Ai sai ki yi,ke da kin san da mi za'a shiryata ama kike haka? Ya dace tunda wuri ta san abinda ke jiranta ba sai lokaci ya kure mana ba, domin bamu san lokacin da zasu dauketa ba, su kuma kwaliyar kawai zasu koya mata sai mugun nufin"

A haka HINDU ta idasa wuni a ranar, sukuku da ita tamkar bata da lakkah, sai idan lokacin cin abincin ya yi ta je ta kai mata madarar da dan abinci kadan sai kuma wani hadin cikin dubunnan hade haden da take bata na gyara, tun daga na sanhi har na gyaran mata, ita babu ruwanta da wani wai ga yadda mijinta yake, wannan su ta shafa, ko wace wace kawai

Aban NADIRAH na dawowa shima da Innar birni ta sheda masa a yau fa zata fuslanci NADIRAH da amsar tambayarta domin kwata kwata ta hannata sakat, in me take sai ta tsareta da tambayoyi, tana tambayarta gidan nan fa? Wa ke basu abincin nan? Yaushe zadu tafi? Me yasa ake mata wannan abin? Na menene? Ita bata so dai da sauransu

Shima jikinsa sukukun ya yi har yama ya yi sosai aka dawo da ita aka kuma shige da ita aka yi mata wanka da turaren ruwa a cikin ruwan wankan sannan aka bata sutura mai dumama jiki da su safa aka umarceta sakawa bayan an shafa mata mayukan gyaram kafa da su tafin hannu


Zaunawa ta yi saman babar kujera a falonsu tana girgiza kai, gajiya na tare da ita tilis ama magariba ta shigo ba danar yin barci yanzu, Innar birni na kusa ba zata bari ba, innarta kuwa tana daki wai nafila zata yi, ko sallar magariba ba'a yi ba a gaba ama innarta ta shige nafila, ko ta mecece?

Yannayin zamanta matar nan ta yi tsaye a kanta tana mata fadansa, ta fuskanceta da kyau ta ce" N hannaki zama irin wannan, wannan din ba zamanki bane, ya dace ki ringa zama irin na masu matsayinki, daga yannayin zamanki ne jikinki zai dauki yannayin tafiyarki, kin ga fa kanki, da idannuwanki komai zaki yi da su ne, idn ba ke da makusantanki ba babu wanda zai samu yawan maganarki, ki gyara zamanki ko mu yi gyaran dare yau!"


Da sauri NADIRAH dake hararen gefe ta zarro ido ta juyo tana gyara doguwar rigar dake jikinta ta gyara dan kwalinta da kyau sannan ta gyaran zamanta, ba zama irin na kafa daya kan daya ba, no, zama irin na hade kafafuwa wahe daya sannan a basu karfi gefen hagu ko na dama, haka kuma bayanka kan bada yannayin halitarsa da kyau, kuma dukkan wani fasali naka kan fitowa da kyau da irin girman isar da sakon yannayi a irin zaman

Ido ta zubawa NADIRAH, har yanzu takan ji a rants yarinyar kamar ba Yar bayi ba, koda yake ko menene ta tabata mai girma le tunkarar rayuwarta

Idannuwanta na matukar bata mamaki, kamar ba yar africa ba?, Yannayinta na bata mamaki, mutun ce mai son sakewa,

Dan murmushi ta yi a boye, kasa kasa ta ce" Ki dan saki fuskar taki, ki kasance mai aika murmushi koda ranki ya bace ba fushi ba kin ji?"

NADIRAH ta gyada kai, tana kallon matar ta juya ta fice cike da takama hakan ya sa ta rakata da harara har kamar idannuwanta zasu fado kasa dan rigima

Innar birni ta sauke ajiyar zuciya, a hankali ta ce" Hararanta kike yi?"

A zabure ta juyo tana daidaita yannayinta, kasa kasa ta yadda ita da kanta bata san cewa abinda take gujewa ya fara tasiri a kanta ba ta ce" Aa innar birni, bara na je na yi sallah"

Kai Fadime ta gyada a hankali ta ce" Idan kin gama, ki same mu a dakin Abanki"

Dan juyowa ta yi, sai kuma ta amsa ta shige nata dakin da har yanzu take mamakinsa, waje aljanar duniya ace nata

Please Login or Register in order to submit comment