Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fuzge sannan ta daga kafarta ta shige cikin motar Umma ta rufo ta ja baya tana kallonsu har motocinsu biyu suka tafi

Juyowa ta yi ta zubawa masarautar ido, nan idannuwanta suka sauka a kan wata baiwa yarinya wace tale bakuwar baiwa ce a masarautar

Murmushi ta yi domin yarinyar ba dai sannin hannunta ba

Da ido ta mata alamu sannan ta kama hanya ta wuce bangarenta cikin gadara tamkar itace uwa a wajen sarki!


Tana shiga baiwar nan na karasowa , dan haka da ido ta kori sauran masu kula da ita sannan ta sabule rigarta tana yi mata wani kallo mai kama da dan iskan kallo kafin ta miko mata hannu suka shige ciki a daidai lokacin da ake kiran sallar magariba (subahanalah, Allah ka rabamu da lalacewa)

A hanyarsu ta dawowama basu yi tsaye tsaye ba, mazan nema ke sauka sallah , daf da magariba suka karaso garin su


A lokacin da mota ta tsaya Gimbiya ta sake fitar da wani huci na mamakin gannin ta kasa yiwa Fadime maganar nan a hanya bayan haka suka yanke da mijinta

A lokacin da Fadime ta fito ta mata rakiya har dakinta tana shirye shiryen yi mata salama ta dakatar da ita tace ta tsaya ta fito

Tana shigewa Fadime ta daura Alwallah ta gabatar da sallolin dake kanta domin ji take kamar ta fado daga motar ta yi su a hanyar nan

Taba tsaka da adu'arta da yan yatsunta Gimbiya ta fito ta sanar mata tana iya tafia

Dukawa ta yi ta yi godiya sannan ta juya ta tafi tana tunanin me ya sa da farko aka tsayar da ita?
Watsar da tunanin ta yi domin bashida wani anfani

Zama Gimbiya ta yi ta ringa kiran malamanta tana sheda masu kamar yadda mijinta ya kirayeta ya fada mata cewa bai yiwa Sarkin dogarai maganar ba, duda ya san abu ne wanda zai yi murnarsa, sai dai abinda ke boye a lamarin yake so idan lokaci ya yi ya fito masa a mutun kar ya nasa gardama, dan haka du su sanarwa malamansu na tsubu kan su rufe masu baki , watau Dogari da matarsa, duda ta ga kamar hakan wani basu darajar da basu kai bane, a tunaninta sun isa su tankwasa su kai tsaye su amince da komai, ama mijinta sai yake nuna alfarma zasu nuna sunna so, ba zasu nuna cewa za'a yi haka a matsayin bahija ce aka aura masa ba, no, zasu nuna mace ya nema kari shi kuwa ya ga babu wace ta dace irinta, abubuwa dai tsare tsare irin nasu wanda su suka amince da kayansu

A yau da darema hira suka sha, bama kamar Hindu da ta tsatsare yayarta da tambayoyi a kan BABAR MASARAUTA, karra karkata kai take tana sakin murmushi yayarta na fada mata irin tsarin masarautar

Tana murmushi ta ce" Aunty, kuma kin samu gannin sarki?"

Fadime ta zarro ido tana kamma haba ta ce" Gannin sarki kuma?, Da ace na samu zuwa wajen bayar da kyautar masu saukar na tabata da zan hango shi, kin san nima ina so na ga UMUGHLUK ITIFAL ganni na biyu, kawai na duka har kasa na gaishe shi na sake yi masa jinjina irin ta ban girma"

Hindu ta karkace kai tana sake dora kankara a saman kitson da NADIRAH ta matse mata kai ta yi mata ta ce" Baki san wani abu ba aunty, ai du ranar da na je babar masarauta, ko ana ha maza ha mata sai na ratsa na ga UMUGHLUK ITIFAL!"

Aban NADIRAH dake zaune yana sake nuna mata yadda ake daura damarar hawa doki da kyau dan idan ka yi rashin Sa'a ka hau doki mahaukaci kar ya ilatar da kai ya juyo yana kallon su ya yi murmushi ya ce" An fada maki kamar masarautar nan ce da mule yawo son ranmu?, Ko sarakai sukan nemi damar zuwa ne basa mata shigar kai tsaye, ko a yau na tabata dan a bude take du wanni na annabi na shiga kai tsaye, da ba dan wannan ba na tabata da sai mun jira koda zamu samu shiga, HINDU masarautar dake zagaye da masu kakin sojoji? Dogaransu fa horo ake basu irin na sojoji, dogari dake rike da bindiga? Salarry garesu du karshen wata mai tsoka , dogarensuma sarakin wani kauyen ne nake fada maki, wai inama mijinki?"

HINDU ta yi murmushi tana gyara zama ta ce" Yaya ai a nan muka wuni shima ya tatso nonon Indi, yaya dan Allah wata rana ka kaimu mu ga masarautar koda bamu je mun ga sarki ba, ka san me nake son gani? Wannan kofar da aka ce a cikinta gangar dake kuka idan jinnin masarautar ya rabo, wanda aka ce a kulin sai gangar ta yi idan UMUGHLUK ITIFAL ya zo wucewa, ina mamaki, shin tsafi ne ko menene?"

Ajiyar zuciya ya sauke zai yi magana ya ga yadda NADIRAH ta cika tana neman fashewa sai kumbura take yi, ya tabata dan sun barta sun shige hirar sarauta ne, murmushi ya yi ya ce" Kin ga Hindu ku zanta da yayarki, ai itama na kula idan abu ya shafi sarautar Babar masarauta ce har sai na nuna na gaji idan ta fara labarinta, bara na iya da yarki"

Haka suka sha hira sai da dare ya tsala sosai sannan ya tafiyarsa su kuwa suka kwonta barci

Washe gari da sasafe suka fice wajen aikinsu, da nufin sai dare yauma, ita dai NADIRAH da ido ta raka mahaifiyarta tana cike da tausayinta a zuciyarta har ta bacewa ganninta, a irgenta dai gobe zasu tafiyarsu gidan bikin nan na kawar innarta, daga cen kuwa su yi tafiyarsu LABA, ta kagu ta je ta tarda masoyi, barowarta kauyen yana ciwon yatsa da suka je yana ihun kuka innarsa ta koro su tana cewa mai nacin namiji wannan ai sai ta tsotse mata Da!
Murmushi ta yi kasa kasa ta ce' Aminu aminuna, iyeah, aminu ina sonka, iyeah........'

_____________________________________

Jus din dake ajiye ta sake kallo, gaba daya jinnin jikinta kamar zai tsinke take ji, a hankali ta sake duban Gimbiya dake zaune kafarta na dan girgizawa itama tana kallonta


Gimbiya ta sake kallon jus din, ta kalleta ta ce" Baki taba lemun ba fa Fadime?"

Gaban Fadime ya sake faduwa, a sanyaye ta sake duban Gimbiya jikinta na karra mutuwa, sosai take son tambayarta ko lafiya? Domin abinda take ganni yana nan girmamar tunaninta, sai dai ta kasa, domin ba yar haka a tsalaninsu ai, sai sada kai da ta yi kawai tana sauke ajiyar zuciya a ranta tana Adu'ar ko menene Allah ya kawo mata shi da sauki


A hankali Gimbiya ta dan sake matsota tana dubanta ta ce" To shikenan tunda ba zaki sha lemun ba, dama abinda ya saka nace yau zamu zauna da ke dan ina tafe da gagarumin albishir, albishir din da na tabata shine burinki, shi kike jira, idan kika same shi hankalinki ya gama kwonciya, zaki kerewa Sa'a, zaki samu abinda kike so hankali kwonce"

Fadime ta sake dago idannuwanta masu kaifi ta tsare Gimbiya da ido ba ko kyaftawa

Gimbiya ta sake gyara zamanta a nutse ta ce" Gagarumin albishir din shine, Mai martaba ya yanke shawarar aurar da yarki wa UMUGHLUK ITIFAL a cikin sirri, wanda kafin a yi haka sai kun kaura daga gidan nan naku kun koma daya daga cikin maka makan vila dinsa, an zuba maku masu aiki, an yantaku yantawa mai girma, an baku makudan kudade ga mota, dukkan abunda kuke tunani na ci gaban rayuwa zaku same shi a kwana kusa, idan har komai ya daidaita nan da sati biyuma an yi an gama!"

Gaban Fadime sai da ya rugurguje ya fadi, a zabure ta sake kafeta da ido tana son fahimtar shin wasan kwaikwayo Gimbiya ta koma yi kuma ko menene?, Wannan tsarariyar maganar da ta zubo mata kai tsaye ba kwane kwane ba dan sakayawa da alamu irin na wasan poisson d'avril, ko tace magana irin ta yan maye? Gashi kuma su ba wasa suke yi da junna ba sai kawai ta zamto tamkar mutun mutuni tana kallon Gimbiya, wace ke dan neman damuwa da yannayin Fadime din, dan haka ta sake gyara zamanta ta ce" Fadime?"

A hankali Fadime ta sake saka kaifafun idannuwanta a cikin nata tana kallonta, muryarta a cen ciki ta furta" Bahija din, ta ki amincewa da abinda kuka tsarawa rayuwar nata kennan?"

Gaban gimbiya itama sai da ya yanke ya fadi, ta sake fuskantar Fadime ido cikin ido ta ce" Ban fahimci maganarki ba, ko kina so ki nunan labe kike min ni da mijina a cikin gidana da y'ayana?"

A hankali Fadime ta girgiza kanta tana dan gyara zamanta kadan ta ce" Ba labe bane, maganar ce kuka yi tun karfi, a yanzuma dan ta kama ya saka na fadeta"

"Yaya kike min magana a wani tsaye kamar kin samu wata sa'arki ko talaka irinku?" Gimbiya ta fada a kausashe tana duban Fadime, dan ta fara kular da ita, aa, dazu fa na gangare yace mata ta tarbi matar kai tsaye domin a kanta ya kwana, watau ya kwana yana surkulensa da sunnan Fadime din ya tabata ana fada zata hau tsalen hakan, bale an yi magana ta yanta bawa daga bauta? Ai a guje zata amshi wannan tayin har ta duka ta yi godiya, sai dai ga wani raini na nan.shiga tsakaninta da baiwarta bayan ta isa da ita?

Fadime ta sauka daga saman kujerar da aka sakata zama ta duka kanta a kasa sosai a sanyaye ta ce" Allah ya huci zuciyarki, ba nufina haka ba, idan na bata maki ki yi hakuri, ama NADIRAH tanada wanda take so, Allah ya karra maki lafiya!"


Fadime bata taba zato, ko tunanin zata dauki mari a saman fuskarta a kan wannan magana ba, ku gane ta san ta shiga matsala kennan, ama bata yi tunanin matsalar mai zafi irin wannan bace, mari? Ai mutun mai daraja baya marin fuskar mutun, ko yaro ne ka dali keyarsa, domin fuska daraja gareta, ba'a son marin fusla, bale tata da girmanta da komai wace ta tabata ta girmi gimbiyar?

Rai bace kunnayenta suka shiga jiyo mata kalaman da suka sake dagula lisafinta , domin Gimbiya bata tsaya iya nan ba ta nunata da yatsa ta ce" Saurara ki ji, na zauna da ke a nan har na nemi sulhu da ke dan an nunan haka ya dace, ke kin san baki isa na nemi alfarmar nan a wajenki ba domin baiwata kike, tunda kin san maganar bara na sake bude maki ita dala dala, a kan wannan maganar ana iya wayar gari babu ke, babu ubanta, na daukota na daura mata auren na kaita ta cika min burina!, Zata je ne a matsayin yarmu ba taku ba, zata tafi a matsayin Bahijata ba yarku ba!, Idan kika yi hakuri aiki ne zata min na dan lokaci ta dawo gareki, idan kika min gardama walahi baki dayanku a yau ina iya batar da ku na saka ku a halin ha'u'la'in rayuwa ta yadda da kanku zaku nemi a kasheku!, A kan bukatata babu abinda ba zan iya yi ba, na saka auren yarki nan da sati biyu, idan kina so a yi ba ke ki yi gigin bijire min, idan kuwa kina son zaman lafiya ki min biyaya!"


Jikin Fadime ne ya kama rawa kar kar kar kar karkamar zara kifa

Da sauri ta mike tsaye tana yin baya baya tana kallon Gimbiya har ta samu ta fice ta nufi bangarenta da mahaukacin sauri sauri mai kama da gudu gudu

Tun daga nesa ta ringa hango Hindu na tsaye ta daura dan kwali a tsatsonta tana kakaba dariya tana tare tare har dai ta hango Nadirah a saman Dokin mahaifinta mai sanyin hali tana ta wahalar da shi sai aukin fadin CAI CAI take


A haukace ta karaso ta damki hannun Hindu tana kallonta ido cikin ido ta ce" Maza ki dauki yarki da kayanku mu gudu!"

Daga haka ta saki hannun Hindu ta nufi dakinta da gudu tana wartar dukkan abinfa hannunta ya kai kansa tana cusawa a jakunkunna idannuwanta a rufe

Dagowa ta yi zata warci zannuwan Hindu da Nadirah ta ji a riko hannunta da riko mai karfin gaske an juyota

A haukace ta saka ihu ta juyo hannunta a dunkule ta kai bugo a kirjin wanda ya yi mata rikon, tana dago kanta ta ga........















😞😞😞😞 Oh rubutun sarauta ba fai rikici ba
8/13/22, 22:56 - Buhainat: *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍?*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*


🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻
*OUMOUGHLOUK ITIBEL*
_(ZAKIN SARAKAI)_
🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻

_FREE BOOK_

*Na*


*SAJIDA NIGER*



1️⃣4️⃣

*NOVEL DINMU MAI TAKEN CARBIN KWAI YANA NAN YANA TAFE CIKIN TSARI DA NISHADI, LITAFIN AKOY DUKKAN ABINDA KAKE NEMA A CIKI, SHAGALIN SAI KA LEKA, KA GARZAYO KAWAI KA SAMU NAKA HANKALI KWONCE😍😍😍, labarin Kwatena ne watau mai BADAKALA DA BAIWATA*





A haukace ta saka ihu ta juyo hannunta a dunkule tadakawa wanda ya riketan bugo a kirjinsa tana dago kanta dan gannin ko wanene

Wani ihun ta saka mai hade da barkewa da kuka ta jimke hannunsa tana sake kallonsa ta bude baki jikinta na rawa ta ce" Mu tafi, mu tafi, idan muka tsaya zasu fito mana da rikicin da ya fi karfinmu, kana ji barazanar da ta yi min cewa zata iya batar da mu, ko ta saka mu a ukun da mu da kanmu zamu nemi a kashemu?, Ita tana son y'arta har haka ni zata saka min ya a uku? Da UMUGHLUK ITIFAL take magana, yata zata mika dakinsa a matsayin y'arta? Duk ranar da hakan ta bayana da kansa zai zo ya tsire mu a jikin kanta, mu da kanmu sai ya mayar da maganarmu rikicinsa, bana ciki, babu maganar alkhairi, da ace magana ce ta alkhairi abin farin cikina ne, abanta, mu gudu ka ji?"

Sake riketa ya yi a hannayensa a hankali ya janyota jikinsa ya rukunkumeta shima jikinsa na wani irin rawa tamkar zai kifa

Gab gab gab haka jikinsa yake yi, muryarsa a matukar raunane ya ce" Marinki ta yi ko?"

Tana cikin gunjin kukanta ta gyada kanta, numfashinta tamkar zai dauke dan tsoratar da ta yi, tunda take , tunda ta taso ba'a taba daga hannu aka sauke mata biyar ba sai yau, ikon Allah

A hankali ya ce" Muna zaune mijinta na min maganar da ta maki ta fado tana sanar masa cewa ba zamu sauraresu ta laluma ba sai ta tsiya domin ita yanzu har marinki sai da ta yi da ranta ya baci, ban san dalili ba, ni dai na ga irin bacin ran da ya nuna har ya bani mamaki, domin a nan ya dauke fuskarta da mari har jikinsa na rawa......, Zahrau ban san dalilinsa ba, ama irin yadda ya nuna bacin ransa ko ni sai haka, a cikin fadansa ne ya manta wayon da ya so yi min ya fada min cewa idan muka yarda aka yi auren nan na dan lokaci ne zaki kawar da UMUGHLUK ITIFAL ki dawowarki wajenmu......., Wannan abu shi ya rikitani ya sakani kuka......." A hankali ya karashe yana kifa kansa a kafadarta ya ja wani irin numfashi hawayensa suka sauka a saman hijabinta, sannan ya karra matseta a jikinsa sosai ya ce" UMUGHLUK ITIFAL, sarki ne mai koyi da manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam , shi din bawa ne mai jin kan wanda yake wajen masarautarsama bale na ciki tsundum, UMUGHLUK ITIFAL idan ke bai kara ki ba ni ya karra ni, idan bai karra mu ba to fa in muka fita waje muka yi shela ya karra dubanmu, Fadimata na rantse da wanda raina ke hannunsa idan akace a yi fito na fito a yakin da ba za'a dawo ba dan a taya UMUGHLUK zan je ba tare da na yi tambayar menene ba'asin yakin ba, domin na sani ne shi din mai yi ne domin Allah ba dan ya karre kansa ba!, Zahrah ko ke bakya jin haka a ranki ne?"


Itama tana kukan ta ce" Haba Abanta, idan akoy masu takama da sunnansa idan sunna maganarsa ai bayana suke!, Ko a yanzu da ace wata magana ce ta zuciya daya, ciki harda NADIRAH ta kasance baiwa a masaraitarsa, bani da darrrr zan saketa ta je da Adu'ar tsari, domin na san koda an sakata cikin halin kaka naka yi kafin ya yi zagayen karshen mako ne zai kwatar mata hakinta!"


"Nima abinda na sani kennan, sai kuma furucinsu ya gigitani!, Ki sani maganar batar da mu bata gigitani ba, domin ni bawa ne, mai sallah, wanda ya yarda da kadara, na tabata idan duka duniya zata taru dan ta cutar da mu sai idan Allah ya aminta, idan Allah bai yarda ba, babu wanda ya isa ya yi mana koda kwarzane ne!, In kuwa kadararmu mu gama da duniya a haka ne muna dakinmu A'lah zai kawo dalilin fitarmu!, Wannan magana kamar tsarin film? Basu tashi hawanmu ba sai da suka nuna mana dukiya, lalle basu sanmu ba, a shekarun da muka yi a karkashinsu da wannan ne a gabanmu da mun taka wani mataki mai girm, domin da mun kasance bafadai masu hada husuma dan su samu na kashewa!, Sai Dai Zahrau Uban marayu ne zasu taba!, Zahrau hakan na nufin idan bamu amince din ba, zasu samo wani wanda zai amince din, hakan na nufin idan har muka kiya din, zamu zo mu tardo abu goma da gomi ya tara na halin ha'ula'i a gabanmu!, Zahra hakan na nufin munna da hannu a dukkan abinda zai faru"


Idannuwanta ta dago da tuni suka yi hulu hulu tana kallonsa ta ce" Idan muka amince din, hakan na nufin mun kasance cikin masu mugun nufi dan mu cutar da shi? Idan ta je nesa da mu, hakan na nufin mun saketa a dokar dajin da ta yiwu wata rana su yi galaba a kanta har ta aikata abinda suke so? Abanta kar ka manta yarinya ce ita karama, wace ake iya yiwa barazana da rayuwarmu ta amince da ko menene kai tsaye dan kar a cin mana!, Sannan ita din tunda ta zo duniya ta ki jinnin gidan sarauta da abinda ya shafe shi, ko a jiya ina ce sai da ta yi maka hirar Aminu?"


A sanyaye ya sake riketa a jikinsa yana rintse idannuwansa ya ce" kin fi kowa sannin na fi ki shakuwa da kulafurcin NADIRAHNA, kece ke min nasiha a kan soyayar da nake nuna mata, a yanzu haka wannan shine abinda ya dakatar da ni Innarta, a yanzu haka wannan din shine abinda ya zamto min katanga da daukan matakin amsawa kai tsaye, yaya zata dauki maganar? Yaya zata iya amsar maganar? Domin idan har hakan ce zata kasance sai na fuskanceta na sanar mata gaskiya, koda kuwa hakan zai zamto ajalina!, Innarta, shekararta kwata kwata ashirin babu yan watanni a duniya, yaya yarinyata zata iya daukan wani nauyin? Na tabata akoy abinda ya tunzura su daukan wannan matakin!"


A sanyaye ta sake dubansa, ta rage muryarta sosai domin tana hangen Hindu dake kai kawo ta dan leko su ta koma kamar zata saki zani dan rikita
A hankali sosai ta ce" Bari ka ji abinda yake faruwa......................" Gaba daya ta dauke duka kaf abinda ta sani wanda ya saka gimbiya da mijinta daukan matakin bada yarsu daj su wanke kansu, abin ya zo da rikicin nan n yar ta kiya shine gimbiya ta zame y'arta take neman tura NADIRAH

Sosai hankalinsa ya sake tashi, ya rasa me zai ce , da kyar ya iya zama yanzun ya zamto itane a tsaye jikinta na rawa

A hankali ya nuna mata daf da shi sosai, ta zauna tana sake dora kanta a gefen damtsansa

A sanyaye ya ce" Ina cike da tsoro Fatina, kin ga ina jin tsoron halin da yata zata iya kasancewa a ciki, ina tsoron fuskar da UMUGHLUK ITIFAL zai duba idan ya gane cewa NADIRAH ba itace aka bashi a matsayin mata ba, duda na tabata ya aminta da wannan hafi ne dan shima da wani abin a kasa, domin na sani sarai dan kar a zage shi ko sirrinsa ya fito fili ba zai taba yarda ya kashe rayuwar wata ba!, Haka kuma ban san yaya yata zata rayu a cen ba, shin zata iya kaucewa cutar bawan Allah ko zata kasa?, Abinda na sani shine yarinyar cen ita daya na malaka, kuma ina son abita fiye da kaina, a kanta ina iya yin komai, sannan a yanzu da na ji maganar dake boye a cikin son su mayar da ita matar SARKI, sai na ji dama ace zan iya na yarda ta je, da zuciya daya ba dan sarautarsa ko arzikinsa ba, ta kasance wata jigo a rayuwarsa? Ko ita din wata mahadin rayuwarsa ce?"


Hindu dake kofa a tsaye kamar ta afko ta sake daga labule ta musu kuriiiiiiiiiii, a dole summa suka kallota

Gaban goshinta ta murza sosai ta ce" Yaya mu fece din ne ko kuwa?"

Ajiyar zuciya ya sauke a hankali ya ce "Hindu zo mana"

Ai kuwa kamar jira take ta shigo da sauri, sai dai gannin sunna kallon kofar ya sakata juyawa da sauri
Haba ta kama ta juya tana fadin ina zuwa

Karasawa ta yi ta kama hannun NADIRAH ta mayar da ita wajen zaman ta sake bata doguwar wukar babanta ta ce" Ki zauna a nan mana yar Hindu ba kyau labe ina zuwa, wannan riketa du wanda ya maki eh yane ki auna masa yar albarka ina zuwa"

Kai ta gyada hankalinta gaba daya a tashe , har yar yatsarta ta gurde wajen dirowa daga kan dokin babanta gannin mamanta na rusa kuka, kuma sai ga babanta ya wuce fuuuuuuu shima, shine Hindu tace ta zauna ta jiyo masu, kuma gashi ita ta ji ama ta hannata labewa ta jin itama


Komawa hindu ta yi tana sake zuba masu ido

Gannin da gaske kukan mijin yayarta ya yi shima sai ta nemi rikice masu, ta yi zaman yan bori tana dabar kai ta fashe da kuka ta ce" Wayo mun shiga uku,wani abu ba ka yi za'a yanke maka kai? Ko aunty ke kika yi wani abin? Ku tashi mu gudu idan laifi kuka yi ba zan rasa wajen boyeku ba babu wanda zai same ku,wayo ni Hindu kunne uwata, kunne ubana me ya aikeku aikatawa sarki bafan UMUGHLUK ITIFAL laifi? Kun sakani a uku ni da yar marainiyata? Innalilahi wa inna ilaihi rajune mun shiga uku!"


A hankali Fadime ta kalli mijinta a sanyaye ta ce " ka tabata wannan hirar ta ayi ce da Hindu?"

Shima idon ya kura mata yana kallo, bama irin yadda take turbuna kaffafuwanta a cikin kasa ba ta yarda dan jonanen dan kwalin kan nata a kasa kamar kace fit ta fice a dubu kota yi ciki da kai

Ajiyar zuciya ya sauke ya sake rike hannun matarsa a hankali ya ce" Hindu ki nutsu mana, babu fa abinda muka yi"

Hindu ta dakatar da kukan tana sake kallonsa ta ce" Kuma kake kuka? Yaya me zai zo maka da karfi ya shirgaka a kas fisabililahi? Aunty hala kukan amare ya yi? Wayo ni wayo kaina ni Hindatun Habu makadi!"

FADIME ta gyara zamanta tana jan hancinta ta ce" Ka daina batawa kanka lokaci, babu abinda bata ji ba, ka je kanka tsaye kawai Abanta"

Da mamaki ya zubawa Hindu ido ya ga sai micui micui take da ido da baki ta kalle shi, ta kalli FADIME

Kai ya gyada yana sauke ajiyar zuciya ya ce" Yaya kike gani , me ya dace mu tsayar? Mun rasa ina muka dosa"

Sai da ta yi murmushi ta gyara zamanta kamar ba ita ke share sharen hawaye ba ta dube shi ta ce" Matsalar da ta dan sage min gwuiwa har na koka din nan daya ce kwalin kwal, yaya shi zakin sarakan da bashida anfani?"

Sai da suka zabura sunna kallonta su dukansu

Harshen zaninta ta saka ta sake share hawaye ta ce" Na tabata sihiri ne bawan Allah na san ba uwa ba uba ba dangi masu jin kai, ama ba komai idan muka je in sha Allahu zan ringa dan bada taimako na karya tambaya da tashin tsakiyar dare ina kama sunnansa ina li'ilafikuraishi, in sha Allahu zai dawo mai anfani, in kuwa

Please Login or Register in order to submit comment