Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

abin a jikinta ne kuma ta yiwu a kansa ne kadai abin, ta yi sake abu ya riketa tunda yarintarta har shekaru sun fara taruwa a kanta, a yanzu idan abin nan ya bayana yaya zata ji a zuciyarta ne? Ga HUZNAH da baban kishi mai tsananin gaske, HUZNAH bata hada mijinta da kowa ba kuma ta so a rabar mata abinta, danma ta san bata da yadda zata yi ne ta hakura da wannan lamari, to ina ga ta ji baban abin nan? Subahanalah lalle akoy kura a baban daki!

A cen kasan zuciyarta kuwa dodonta take kamaltawa, tana tinano irin abinda ke iya faruwa, idan ta tuna magangannun Umma a kan yayanta cewa shi da mace sai dau a lahira in ana badawa, shi da samun Da sai dai in ana haihuwa a lahira? Sai ta ji du duniya babu wanda ya yi asara irin mai hada UBANGIN SAMAI DA KASAI DA WANI ABIN HALITA KO GUNKI!, ya Allah ka karra durmiyar da mu a duniyar musulunci😊




____________________________________



Tabas, dukkan abinda ya dace a tarbi bako dan karama shi, an gabatar a tsaftace a kuma tsare, sai dai bakon nata tunda ya zauna zama irin na hamshakai bai kalli abubuwan ci da sha din ba kwata kwata, hasalima shi ba danna waya yake yi ba bale tace dannar waya ne, shi kuma ba wani abin yake yi daban ba gayanan dai a zaunen ya dake har wani tsoron sake gaishe shi take yi bayan irin ihun da ta sha da ta karanta sakonsa cewar gayanan zuwa gareta?


Wayar dakin ta je ta daga, a dake ta ce" FATIME, KI KAWO WANI ABIN WANNAN BAI MASA BA"

tana gamawa ta koma ta zauna ta sake zuba masa ido,
Shi kuma ci kanki bai ce mata ba yana ta nazartar girman wautarta kafin ya dirar mata

An dauki minti kusan goma a haka sai TV dake hasko yan indiya sunna soyaya,

Fatime ce ta yi salama yana dauke da wasu plate plate na kwalba masu nauyi da kyan gaskw, kyansu zai sheda maka kudinsu ta kawo ta ajiye ta juya bakin kofar da baiwa ke tsaye tana amsowa tana ajiyewa a gabansa sannan ta duka muryarta a sanyaye kanta a kasa ta ce" Barka da yamaci uwar gijiyata, wadinne zan kwashe a ciki?"


Da zafi zafin gannin jimawar Fatime din BAHIJA ta ce" Dillah tashi daga gabansa karki saka ya shaki karnin dati malama kin matse masa waje kina magana daf da shi kamar kin samu talaka dan uwan............................

Dif ta yi shiru sakamakon kakausan kallo, mai hade da tarin mamakin gannin wannan abin rashin da'a a gaban idannuwansa na wannan yarinyar karama tana wulakantar da matar nan da muryarta kadai ya ji ya fahimci ta girmeta ba tare da ya kalli fuskarta ba

A hankali ya dawo da dubansa kan FATIME da kanta ke kasa ta rintse ido tana jin kunnar magangannun BAHIJA yar da ta haifi sama da itama ama dan tana aiki a karkashinsu take neman wulakantata har haka?

Sake kallon BAHIJA ya yi, sai kuma ya maido dubansa kanta a hankali ya ce" TASHI KI TAFI"

Tunda ya zauna sai yanzu bakinsa ya yi magana, hakan ya sa Bahija sake dubansa kirjinta na dokawa, gashi da ta so zama daf da shi kiyawa ya yi ya nuna mata kujerar dake facing dinsa wai a kiyaye shedan

Fatimema a hankali ta dago kanta da idannuwanta jin magana a tausashe an yi mata ta sauke kan fuskar mutumen

Fuskar ta yiwa tsai na yan sakwani sai kuma ta dauke da sauri sanadiyar gannin ya wani dan warra dubansa a kanta

Kai ta sake sadawa a sanyaye ta ce" Allah ya huci zuciyarka, a huta lafiya"

Daga haka ta mike ta juya da niyar tafia,

Muryarsa ya sake budewa a hankali ya furta" Dakata "

Fatime ta dakata, gabanta na tsintsinkewa ta juyo daga inda take ta duka ta ki yarda ta hada ido da shi sakamakon fuskar dake son yi mata yawo a ido wace ta tabata hade hade ne kawai

Sake zuba mata ido ya yi kirjinsa na bugawa da dan karfi, sai kuma ya kawar da kansa da hannunsa ya yi alamun tana iya tafia

Har ta bar dakin yana kallon hanyar da ta bi ta fita

A hankali ya maido dubansa kan BAHIJA dake kallon abunda yake faruwa zuciyarsa na ta ambaton kamanin da ta ganni a fuskar matar nan

Murmushin yake ya yi yana sako kalar serius a hade hade ya ce" Haka dama suke jinnin sarautar?, Basu da tausasawa wa mutun?"

BAHIJA ta sauke ajiyar zuciya jin ya fara bata hankalinsa ta ce" Kar ka damu da wannnan, baiwata ce ai"

"Dama a masarautarku ba'a daina bautar da bayi kamar a zamanin jahiliya ba? Ko bakwa girmama daraja irin ta dan Adam?" Ya fada a sanyaye, fuskarsa na fitar da murmushi, ama kuma bayanansa na suka

Kwarai da tana da hankali da tun a nan ta fara gane wani lamari a tatare da zaki, yana magana a wajen da yake nata ne tamkar nasa hankali kwonce yana neman birkita mata lisafi

Sai dai murmushin dake saman fuskarsa ya fi komai dauke mata hankali, dan haka ta ringa mayar masa da sakon murmushin itama tana ji a zuciyarta da ace zai amince ta dawo daf da shi da ya taimaka mata fiye da tunaninsa
Cikin rashin ba maganar mahinmanci ta ce" Ita wannan din hasalima bata yi min ba, mun cika fada da ita, duda ta min wani dan kokari ta bada yarta auren da nake fada maka ni aka so yiwa shi, ama kwata kwata ba zata taba birgeni ba, bata da aiki sai son yiwa mutun fada kamar itace Gimbiya, a haka da ka ganta ba tsorona take ji ba, tana wani sasada kai tsaf take iya hada ido da ni ta gagaya min magana, abinda ka ga gimbiyama bata tsira ba bale ni?, Ka manta da batunta dan Allah ka sanar min, wai da gaske tafiyar nan tawa ce ni kadai?"








'YA SALAM......., YA SALAM, YA SALAM..............MMMMMMMM.......' yake ta ayannawa a cikin zuciyarsa, da kyar ya iya hadiyewa duda ya dan san lamarin, ama a yanzu da ya ga mahaifiyarta da kamaninta fa irin relation din dake tsakaninsu sai ya fara tunanin anya da son ranta aka yi kuwa?

Dan kurmushi ya yi a saman lebensa ya ce" To ita yarinyar itace ke son auren sarkin ko?, Ke bakya so sam?"

Cike da jin maganar wata ba ita ba zata dameta ta dage kafadunta ta watsa hannayenta ta ce" Anya kuwa?, Inaga biyaya ta yiwa iyayenta, inma menene cen ta matse mata ta je ta runguma ni kam bana so bana bukata me zan yi da wani bayan gaka?"

Kallonta yake yi, ita kuma zuba take yi hankali kwonce har ta dasa aya tana kallonsa ta ji shiru bai ce komai ba kallonta kawai yake yana mamakin asarar mace har mace da aka yi a wajen nan, tap lalle ya tausayawa wanda zai iya kwasar wannan yar idan ta tsira da duniyar!, Ikon Allah yaya zaki ringa magana kina nuna wata biyaya ta yiwa iyayenta bayan ke kin bijire a gaban namijin da kike ikirarin gashi shi kike so ki aura? Uhum

Basarwa ya yi yana kallon gefe a lokacin da ta taso tana fadin" Bara na zuba maka jus din plz, ko shine ka dan sha mana?"

Jus din ya dan kalla a lokacin da ta zuba harda su rage tsayi tana sakin murmushi hakoran makarta a waje abinta

Hannunsa ya saka ya amsa ya gyara zamansa kadan ya dan surba sannan ya ajiye ya sake dubanta a lokacin da take shirin zaunawa tana murmushin gannin ya sha ya ce" To babu tauye haki? Idanfa tana son wannin itama kuma aka yi mata dole?"

Yanzu kam ido ta zuba masa tana son karantar asalin menene damuwarsa da maganar nan ne Fisabililahi? Yaya zai zo bayan ta yi doguwar tsumayin ganninsa bayan lokaci mai tsayin nan har ta cire rai ya zo ya ringa fitinar tumaninta da zancen wace bata da wani daraja? Menene a cikima dan an mata auren dole? Da ya san abinda zata aikatama da ya yi mata wa'azin hakan ga dukkan alamu

Girairakinsa ya dage yana dan kausasa kallonsa kadan a kanta, hakan ya bata damar jan numfashi tana sauke nata duban domin wani irin kyau da ya karra yi mata tamkar aljani, ita kam ta shiga uku da ranta da soyayar wannan mutumen

A sanyyaye ta shiga fadin" Tamkar ba maganana bane a gabanka , tamkar ba nu bace a gabanka, ka duba ka gani ko yaba kwaliyana baka yi ba bayan sai da na kirawo kwarariyar mai kwaliya ta yi min, gaba daya yanzu hankalina ya fara tashi, ina tsoron jin bayani a kan abinda ya shafe mu"


Gannin idan ba sake sasautawa ya yi ba ba lalene ya samu dukkan abinda yake son samu ba ya saka shi dan sakin fuskarsa ya ajiye maganar NADIRAH gefe ya dan ringa biyewa shirmenta har ya kara minti biyar ya mike ya yi mata salama

Nan hankalinta ya yi mugun tashi, gaba daya ta nemi rikicewa,
Gani take yi idan ya tafi ta yiwu sai wata shekarar kuma?, Dan haka a birkicenta ta ringa tambayar sai yaushe kuma?

A nutse ya ce" Na zo fa, kuma tafiyarki ce "

Wannan kalamau su suka sakata kwonciyar hankali har ta so yi masa rakiya, ama ya nuna sam baya son hakan ta koma gida, a dole ta komawarta shi kuma cike da kamala yake takawa a cikin kebaben gidan da aka kebe NADIRAH har ya kawo baban get din da mai gadi da kuma mahaifin NADIRAH ke zaune sunna dafa shayi sunna dan hirarsu, a dazu baya nak su ASADEEK suka karaso, shi yasa bai ganshi ba sai yanzu

Tunda ya yi masu salama bakin mahaifin NADIRAH ya katse da amsa salamar da ya dauko da nufin yi

Kallonsa yake kamar ba gobe, har ya zo ya shigewa ganninsa

Daga kafar da ya yi ya yi takun sauki har ya karada wajen motarsa nan da nan ya saka mahaifinta farga da binsa da kallo da ya yi

Cikin takun sauki ya karasa wajen motar ta barin da SHEIK yake ya kama ya bude kansa tsaye

Ido hudun da suka yi da Sheik, da zaburowar da SARKIN yanka ya yi daga maboyarsa haniniyar dokinsa ya fargar da ASADEEK abinda yake shirin yi watau sare hannun wanda ya bude motar da suke ciki ya saka shi saka hannunsa ya bude motar da karfi ya fito gaba dayansa da rawanin da yske shirin daurawa ya taka kafarsa taku biyu ya tarbi gaban SARKIN yanka da yaren buzance ya ce" Basssss! BASSSSSSSS ITBAL!" (JUYA , JUYA SARKI)

"UMUGHLUK ITIBEL" MURYAR mahaifin NADIRAH ta furta a lokacin da ya kai gwuiwoyinsa gaba daya ya dire ya sada kansa dan girmama mutumen da koda ba zakin sarakai bane tabas ya ciri tutar amsar gaisuwarsa koda baya so

Dif ASADEEK ya yi daga tsayen nan ya kasa juyowa har sai da ya ji kokowa da kuma shirun da ya wakana a wajen sannan ya juyo a hanzarce ya shiga bayan motar ya rufe da kansa ya mayar da kan nasa jikin motar ya jinginar yana lumshe idannuwansa lokaci daya ya damki rawanin ya dafka shi da abin motar muryarsa a bace da amon bacin rai ya shiga fadin"















😩😩😩😩😩😩😩😩🚶🏻‍♀️🚶🏻‍♀? Ni fa bana yi weekend fa😩
9/30/22, 07:47 - Buhainat: *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍?*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*


🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻
*OUMOUGHLOUK ITIBEL*
_(ZAKIN SARAKAI)_
🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻

_FREE BOOK_

*Na*


*SAJIDA NIGER*





5️⃣3️⃣



Direct gidan SHEIK suka nufa , a nan SHEIK ya jagoranci wajen da zasu zauna, waje mai tsari da tsaro

Ba su su bar gidan SHEIK ba sai da karfe hudu da rabi ta yi, ASADEEK na tsaye da rawaninsa yana gannin yadda aka basu masauki mai kyau, matar SHEIK wace ke turaka a daren tana tsaye a kan kaffafuwanta dudaa bata san ainahin da wa ake tafe ba tunda ta ga Mijinta ya fitar da ita a irin daren nan ta bada dukkan kulawar da ta dace ta hanyar saukar bakin da mahinmanci

Sunna komawa fada masalaci suka yada zango , sai da duka yi sallar asubahi sannan suka yiwa junna salama kowane ya koma gidansa dan hutawa, domin tafiyar ta ja masu dogon zangon da basu zata ba, ba laifi kowa ya gaji danma jiki ya saba da wasu wahalhalun ai da ba za'a iya jurewa ba

Cikin nutsuwa ya haye saman gadonsa yana mai Adu'ar neman tsari sannan ya shiga neman barci ido rufe, ama abin ya gagara
Yinwa yake ji a cikinsa, ama ya san ba zai iya ci a yanzu ba, uwa uba damuwar da yake kaucewa tana ta so ta yi tasiri sosai a zuciyarsa har ta hanna masa yin barci

Du irin yadda yake yin karfin halin kautar da tunanin UMMA ta san tsare tsaren bafansa shin tana tare da su dan kaunar lamarin ko fin karfinta aka yi ta amince ya kasa fita daga zuciyarsa
Kwarai ya san baban burinsa ya tarbeta ya tambayeta, sai dai banzan tunani irin nasa ya hannashi hakan, ya fi ganewa bin sawayenta dan ya gani da idannuwansa domun baya tunanin a irin wasi wasin da zuciyarsa ke ciki in har zai iya yarda da kalaman bakinta, ba dan ya taba kamata da wani hali irin karya ba, sam, dan kawai zargi ya rigaya ya darsu a zuciyarsa dangane da ita lokaci daya, zargi mai girman gaske

Haka ya ringa cenza wajen kwonciyar ko zai ji dadin yannayin kwonciyar, ama abu ya gagara tamkar yaron dake laluben mahaifiyarsa haka ya dawo yi a saman bed din , ya kula wannan ya kunce wannan har kuraye kirayen wayar tafi da gidanka dake garkame ta fara damunsa ainun

Da mamakin gannin kiran masu gadinsa ya daga yana karama a kunnensa, dan ya san dai ya sheda masu barci zai yi in ba dalili mai karfi ba kar a tashe shi, sai ga kiransu ba kakautawa

Jin bayaninsu ya saka shi bada umarnin a barsu su shigo, lokaci daya kuma ya zauna yana dan dafe gabak goshinsa, sai kuma ya mike ya shige bayi dan yin wanka, ko ba komai zai so ace da dan karfi a jikinsa ta yadda zai iya fuskantar matan dake cikin rayuwarsa a irin wannan lokacin

Ya dan dauki lokaci a ciki sannan ya fito da alkyaba a jikinsa mai ruwan maroon da golding, kansa caje ba hirami a jiki, daga kasan alkyanar kuwa jalabiya ce fara sol da wandonta dogo , sai lulumshe luhu luhu din idannuwansa da suke da bukatar yin barci yake yi ama abin ya gagara

Tunda ya sauko sau daya tak suka yi ido hudu, a hankali ta sinne kanta ta lalubo hannun Auta ta jimke dan har ga Allah sai ta ji tsoron kallon idannuwansa jama'a kamar idan yana ganiyar cin zalin dinta wannan lumshe lumshe kamar kwarto?☹️


Gaishe da shi suke yi, kusan a tare, gaisuwa irin wace kowace ke yi masa, kowace da kalar tata , shi kuma yana amsawa hadi da dan sakin dan murmushi har ya dawo kan UMMA dake ta huci itama ta gaishe shi a yannayin da idan tana cikin bacin rai sannan wajen ya dan dauki shiru

Umma ce ta ja numfashi tana kallonsa ta ce" Yarona, abinda ake neman yi min a gidan nan yana neman kaini bango ta yadda ba zan dauka ba, sosai hakurina na son zuwa karshe a gidan nan gaskiya, haba dan Allah, da girmana da darajata? Ina kawar da kai ama sai an nunan iyakata?"

Nanauyun idannuwansa ya dago ya sauke dubansa a kanta, gaba daya sai ya ji irin tashin hankalin da a da yake ji idan wani ya dan bata mata yau ko diz baya ji, hasalima sai yake sin ƙaryata abinda ke saman fuskarta

A nutse ya cire dubansa yana dorawa kan HUZNAH wace itama tata fuskar har wani irin kumkum take yi, ga dukkan alamu itama kalar a kumbure take
A dan sanyaye ya ce" Huznah, zan sha tea"

HUZNAH ta kalle shi, sai kuma ta kalli NADIRAH wace ta yi tsuru tsuru a dan yannayi na jin haushi ta ce" To uwar iyayin gaure gyare sai ki bani ky na kawowa mijina Tea, hajia mai kwana!"

Gaban goshinsa ya dafe da dan mamaki ya kalli HUZNAH, sai kuma ya kalli Umma wace tamkar ruwa ya cinyeta gannin ga maganar da ta yi ama ASADEEK yake maganar yana son tea?, Hala cikinsa ana gaba da ita yai kuma?

A nutse ya gyara zamansa ya dubi Umma , a hankali ya ce" Umma, me yale faruwa ne?, Wani abu aka yi ne?"

Yar ajiyar zuciya ta sauke, duda yannayin da ya yi maganar kansa bako ne a gareta , ama da sauki tunda ya tambaya, dan haka ta fuskanceshi ta ce"Dangane da matanka ne da kuma Auta, jiya mun zo a tunaninmu kana nan ashe ka yi tafia baka dawo ba, ita wannan ta nuna mana ai ka yi tafia ne, ita kuma wannan ta dubi idona tace itafa ta fadi sako ko ban samu ba? Da na tambayi wani sako fa? Sai ce min ta yi ita gaskiya ta soke cin abincin taren nan idan kwananta ne, wai ta dubi tsabar idannuwana tace min ana iya hannata sirri da mijinta?, Ita kuma wannan din ita dake baba ta biye mata harda cewa ai kwanakin nata zasu kare itama bata son gannin kafar kowa a nata?, Me kennan? Nice na zama tsohuwar banza nake gannin irin haka? Karshe sai na tambayi ita kuma Auta ina take daga shekaran jiya zuwa jiya, budar bakinta tace wai tana bangaren BAHIJA, wai ko tana som zama a cen? Bahijar dake yarinya zata iya kula da ita ne? Ka fa san Auta bata da lafia dole sai ni ke iya mata, ama haka ina ji ina gani suka tafi taren, kennan na yi abinda zan yi ko? Barci ban samu ba dan tunani , ina dakon shigowarka !"

Har Umma ta kai aya yana kallonta ne, kallo irin wanda yake son sake karantar harshenta da kuma abinda ke zuciyarta

A hankali ya kalli HUZNAH wace itace baba da Auta da kuma NADIRAH, a nutse ya ce" Ke din da girmanki ne kika aikata haka maimakun ki tsawatar? UMMA ce fa?"

HUZNAH ta sauke kanta, muryarta na dan rawa ta dago dubanta tana kallonsa ta ce" Allah ya huci zuciyarka shin yaya zan yi ne ni? Ka ga ina zamana sai ta ringa nemana da masifa, na fada mata ni bana so ama a banza, wai tace idan kwananta ne kar ta ga kafar yarinya ko ta tsohuwa a wajen, kennan ni da Umma ko???????"

Ido NADIRAH ta zarro, hakama auta, NADIRAH ta gyada kai tana sake kallonsu

HUZNAH ta ci gaba da fadin" Sai ta ringa nuna kamar ta fini sannin mijina bayan bata jima da shigiwa gidana ba, ni ban yiwa Umma rashin kunya ba, gani na yi tunda hakane nima a barni da mijina ranakun girkina ko?"

NADIRAH ta tabe baki a ranta tana ayana' mijina mijina, da acema ana son mijin naki ne malama sai a yi fadan?'

Bakinta dake musmusmus yake kallo har ta zabga harara ta tabe bakin sannan ya gyada kansa a ransa ya ayana' Hum abama yace tuzuruwar kauye'

A bayane kuwa ya ce" To ke BAHIJA me yasa kike haka ne?"

A dan zabure ta kalle shi jin sunnan da ya kireta da shi kuma yanzu, sai kuma ta sauke ajiyar zuciya a kasan zuciyarta tana ayana' Kai Alhamdulilah ashe gwara da ban sanarwa innata cewar wani ya fada masa wacece ni, ta yiwu an kawo masa maganar ne ya karyata, uhum ka ji dai da shi!'

A bayane kuma Sai da ta tabe baki, wanda ya kula idan ya kireta da Bahija take aikata hakan sannan ta dube shi ta ce " Yo ni me na yi kuma a nan, ni fa ban ce kafar yarinya da ta tsohuwa ba, cewa na yi kafar baba da ta y'a, ina nufin Auta ai itace y'ata ko?"

Daga su har Autar kallonta suke yi bayan ta dire maganar ta kuma cuno baki tana gyara zamanta a dole ita ta gama magana kennan, wai Autar ce y'arta yau kuma mai gaba daya, watau ba zata daina cusawa HUZNAH haushi ba ko? Kennan Auta na kiran ASADEEK aba, ita Mama ☹️

Habarsa da ya talabe ya saki yana girgiza kansa ya ce" Uhum, Allah shi kyauta, kin ga Bahija ki kula, bana so ana raina baban mutun, Umma dai da HUZNAH sun girmeki kin ji ko? Ki daina rainasu kin ji?"

Irin yadda yake maganar tamkar yana rarasshinta ya saka daga UMMAN har HUZNAR zuba masa ido da mamaki, Auta kuwa dariyarta take ci a zuciyarta, dan dama tunda suka farka NADIRAH ke fadin kar dai ta yi barci ta san Umma tace yau zata kai kararsu ya dace a yi komai sunna nan kar a zaluncesu

Auta yake kallo, yannayin shigarta ta yau, irin yadda idannuwanta basa neman rufewar nan kamar yar maye kulun, labewar nan da tsoron nan, uwa uba irin zaman da suka yi ita da Nadirah na kugu da kugu hannunsu rike ya saka shi dubanta da kyau, a hankali ya ce" AUTA?"

Fuskarsa ta sauke fararen idannuwanta , a nutse ta amsa shi tana dan sakin murmushi

Hannunsa ya miko yana kallonta ya ce" Zo nan "

A hankali ta karasa ta zauna a kusa da shi kamar yadda ta saba, a sanyaye tana mai fitar da murmushi ta ce" ABA "

Murmushin nata ya saka shi sakin murmushin shima a hankali ya shafa habarta sannan ya kama hannunta na dama yana kallon fuskarta ya ce" Me yasa ga yadda Ummanki ke so, ke kuma kike son daga mata hankali? Ummanki ce fa?, Kin san kaunar dake tsakaninki da ita ya dace ace kina bin umarninta ko?, Kin ga saboda rashin lafiyarki take tsaye take faman ki daina fita ko?"

Idannuwanta ta sada, hannayenta na son su dauki rawa kamar yadda suka saba a da, sai dai da karfi yana jin irin yadda take son controling din tsoronta, wanda karara ya gani a cikin kwayar idannuwanta, hakan ya saka shi a tausashen ya kuma cewa" Idan kuma kina da bukatar mutane a gefenki ne ko da dare ki sanar min mana Auta?"

Dago idannuwanta da suka cika da kwallah ta yi ta saka a cikin nasa
A sanyaye ta ce" ABAHNA, NI BA MAHAUKACIYA BACE"

Dum gabansa ya buga yana kallonta, kanta ta sake sadawa sannan ta ce" ABAH ni ba mahaukaciya bace dan Allah Aba, ka barni na ci gaba da zama tare da aunty BAHIJA ko ka mayar da ni gidan SALEEF "

"Ba zaki koma gidan SALEEF kina yin abu ana bazaki a duniya ba, Gidan saleef din ba a cen kike koke koken abanki kike son gani ba?, Yaya muna magani ido rufe kina son mayar mana da shi baya? Babu inda zaki je, dakinki zaki ci gaba da zama!" Umma ta fada a kausashe da kuma dan karfi, hakan ya saka Auta jimke hannunsa kanta a kasa , lokaci daya kuma jikinta ya shiga rawa, ya salam, ta zata zata iya din kamar yadda NADIRAH ta sanar mata cewa idan ta jajirce zata iya, sai gashi tana rawa kamar farar takarda a cikin iskar sararin samaniya a gaban UMMAN, to ita ta yaya zata iya cire tsoron matar nan gaba daya a zuciyarta ne? Ta ina zata fara wannan aiki mai girman gaske ne? Aikin nan fa ya girmameta sosai, ta yaya zata fara shi ne?
9/30/22, 07:47 - Buhainat: *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍?*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*


🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻
*OUMOUGHLOUK ITIBEL*
_(ZAKIN SARAKAI)_
🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻

_FREE BOOK_

*Na*


*SAJIDA NIGER*





5️⃣4️⃣



A hankali ya dan sake rike hannunta yana danne zuciyarsa da kokarin ci gana da buga game din UMMA ba tare da ya sdakar da wuri ba ya ce" To menene na kukan a cikin

Please Login or Register in order to submit comment