Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kallon yannayin Saraki

Ya dora da fadin" Dukan Hanyar da za'a bi dan a nuna masu wanene Ubangijinsu ba zata kai ta laluma da nasiha da wa'azi da ja a jiki ba....., Idan an kone masu a yanzu za'a kona zukatansu, idan har an kone masu a yanzu za'a tunzurasu ne, kuma ba'a isa a hanna su zuwa wani wajen su aikata wanda ya gimami wannan ba, ta yiwu masu halayar garin su bazu wani garin su ja ra'ayin masu jiran su ji amsa irin haka, Ba wai ina nuni cewa nasiha da kawo ayoyin Allah ne zai tseratar da dukannunsu ba, aa, wanin ko me ka nuna masa ya rigaya ya yi nisa...., Mu dai dama kwatantawa ne namu da yaki da abinda Allah ya halata mana mudin ranmu, idan a cikin dari ashirin suka gane mun ci riba ITIFAL..............................., Da so Samu na yi Ya ITIFAL mu bude masu magangannun da suka zo a cikin Alkur'ani, domin kuwa a cikin kaso d'aya na ukun Alƙur'ani ana magana ne akan tauhidi ma'ana kaɗaita Allah, sannan ayoyi bila'adadi Allah ya yi magana akan shirka, idan muka duba Suratul Lukman aya ta 12 inda mahaifi yake wa dansa wasiyya cewa "
و إذ قال لقمان لابنه و هو يعظه يبني لا تشرك بالله، إن الشرك لظلم عظيم."

"Mahallin sha'ir anan ranka shi daɗe shine shirka, munin shirkar yasa uban ya fara nusar da danshi da lamarinta har ya kirata da zalinci ne mai girma."


Suratul Muhammad aya ta 32 tana tunasar damu cewa "Ya ku wad'anda sukayi imani ku yi da'a ga kuyi da'a ga manzonsa, sannan kada ku b'ata ayyukanku. A rayuwar dan adam babu abinda yake saurin ruguza aikinshi kamar shirka, zaka shekara dubu kana aikin lada, amma sakan d'aya ya wadatar ya bata duka wannan ayyukan indai shirka ce ka yi."

Kara sadda kanshi yayi ya d'ora da" Akwai bukatar mu fara sanar dasu me ye shirka da illarta, dan daga cikinsu akwai wadda basu san muninta ba, kuma magana ce daga bakin fiyayyen halitta a hadisin Abu Huraira ruwayar Bukhari da Muslim cewa " *Lallai Allah yana kishi, sai dai kishin Allah shine ya ga bawansa na aikata abinda ya haramta masa*, a wani hadisin kuma yana magana ce cewa *Allah na matukar kishin ganin bawansa ya had'a shi da waninsa.*, ranka shi dade, shirkar nan tsabar muninta mai aikata ta ma Allah alkawarin wuta ya masa, kamar a Suratul Fathi aya ta 5 da ya ce *Zai azabtar da munafiki da munafika, na biyu sai ya ce da mushriki da mushrika, bayan shirka ne sannan aka kawo zina sannan Allah ya ce yana hushi kuma ya tsine musu albarka tare da alkwarin wutar masira.* , a suratul bayinat aya ta 5 ma Allah yace *Lallai wadannan kafiran daga ahlil kitabi da kuma mushrikai suna cikin wutar jahanna zasu dawwama a cikinta...*, sarkina, a ganina in dai girman matsalar ya kai haka, to dole sai da laluma za mu bisu da dabara har mu samu cimma nasara, dan bai kamata mu bari lamarin ya kai kamar yadda muka shina *a suratul Suratu Baqara aya ta 101 wanda suka tabbatar mana da lallai mai hada bautar Allah da wani to tabbas kafiri ne*."

Sosai ya sake zuba masu ido, a hankali ya sauke ajiyar zuciya bai ce komai ba ya shige bayan motar ya zauna yana gyara zamansa irin zaman daram din nan ya sake waigowa ya zubawa jama'ar ido har suka tatara da jama'arsa suka fice gaba dayansu dafifin yara da manya na daga masu hannu ana masu byby da rakiyar motocinsu da dawakansu

A hankali a hankali masarautar ta ringa hautsinewa, labarin barinsa garin ya idasa rikita garin Dogon dutsi, bama kamar dangin matar sarki da ita din kanta

A rikice ta karasa dakinta ta dauki wayarta ta shiga kiran number auntynta, watau mata a wajen sarkin garin TANUT

Hajia na dagawa ta shiga labarta mata abinda yake faruwa tana sheka kuka

Itama hankalinta ya yi kololuwar tashi, domin a yaune ta ji ainahin maganar ta gaskiya, a da an sanar mata cewa matar ce ta tardo shi da lalata garin ya guje mata tsautsayi ya sauka a kanta har ta rasa numfashinta

Rai bace, hankali tashe ta ce" Dama kin san abinda ya faru kennan kika yi sanyar da har UMUGHLUK ya san labarin? Yaya kika yarda uwar yarinyar ta fito ta zaga gari har ta fito magana ta fito duniya ya ji? Ke kin san baya tare da zalunci kuma ja tsoron uban wani yake yi ba, kina tunanin shi kawun nasa ya isa ya tankwasashi ne a kan gaskiyarsa? Bari ki ji, muma a nan a cikin tamu muke, domin magana ce boyayiya ke son fitowa saman ruwa amkar an zuba mai saman ruwa, maganar dake sirrin dakansa ce ke son fitowa fili, wace in tsoron da abinda Sarkin garina zai fanshi zaman lafiyarsa!, Ba zan ce maki babu maganar gannin Uban yara ba, ama ban maki alkawarin komai a kai ba, kar ki manta har yanzu Mahfuz bai gama kason da aka dibar masa ba, da ya isa da wani abin da ya hanna hakan!, Ki san hanyar da zaki fitar da danki idan ba zaki iya jure a kashe maki shi ba, ko ki san hanyar da zaki maye gawarsa da ta wani! Wannan shine shawarata a gareki , nima ta kaina nake!"

Murya a raunane ta ce" Yanzu kina tunanin idan na masa hanya ya gudu ba zai gano nice na aikata haka ba? Idan ya gano kin san halinsa fa komai yana iya yanke min ba kunyar wani zai ji ba"

Lebenta ta dantse da karfi tana jin ciwon lamarin yaron

Tunani ta yi mai dan tsayi kadan , sannan ta ce" Zamu fara karkatawa wajen neman sulhu kan kar a kashe shi a barshi a suluru har wa'adinsa ya cika......, Ki sani mulkin UMUGHLUK ITIFAL takaitace ne! Idan lokacin hakan ya kai sai mu ci karanmu babu babaka!"

Dakatar da shashekar kukanta ta yi a hankali ta ce" Kamar yaya takaitace ne?"

Idannuwa Gimbiyar Tanut ta dago da dan sauri, sai kuma ta batar da maganar ta hanyar mikewa tana fadin" Ki share hawayenki zan kirayeki, ki fara neman mafita, nima zan buga ta nan, ga Bahija cen bata da lafiya ne zan tabo ki"

Tsai ta yi da wayar a hannunta ta zubawa waje daya ido, ta tabata abinda ya kai bakin Gimbiya da yin wannan furuci abu ne ginane mai tushe, ta tabata Gimbiya ba zata yarda bakinta ya furta furucin da yake na karya ba, abinda ta fi ja ta tsaya a lamarin daya ne tak..... Shin menene boyeyen digadigin abinda aka boye a lamarin Zakin sarakai?, Basaraken da ya gaji sarauta ne aka yiwa furucin takaitaciyar sarauta ke gabansa yaro mai jinni a jika?, Shin tanada labarin wani abu zai sameshi ta sanadin mijinta ko kuma wata boyayiya take kasa a kan usulinsa? .....wannan furuci ya sakata manta abinda ya dace ace ta mike ta kamanta a matsayinta na uwa, watau taya yaronta rokon gafarar ubangijinsa da fatan hakan shine alkhairi a gareshi
Sai ta bige da dogaro da maganar cewa yaronta zai fito ya rayu cikin isa da iza ya ci gaba da wulakantar da ƴaƴan mutane dan yanada DAMA!, Karshema zaman jiran kiran Hajiarta ta yi dan ta bata dama ta gama da sangartaciyar y'arta mai raini da raina na gaba da ita!


__________________________________

A TANUT

Da dan sauri Gimbiya ta karasa Tankamemen falon y'arta tana fadin" Fadime? Fadime? Shin bata yarda ta sha maganin bane?"


FADIME mace ta hannun damarta, wace ke tare da ita tun shekarun tuwo, take bauta mata da ƴaƴanta ta juyo tana sauke ajiyar zuciya da sake rage tsayinta ta ce" Allah ya karra maki lafiya, tace ba zata sha maganin ba, shine nake jira idan ta farka ko zata yarda ta amsa?"

Takalmin dake kafarta mai laushi ta cire ta haye saman gadon tana dora kafarta daya ta tankwashe ta saka hannayenta biyu ta yaye abin rufar ta miko hannunta da tsawa tsawa ta ce" Dan Allah bani ni, tun dazu na baki wannan dan aikin ki wani zo ki sakata a gaba bayan kin san dan kankin kanta ba sha zata yi ba? Tafi dan Allah ke kam kwata kwata bakida wani anfani a rayuwa sai shirme!"

Jikinta na dan rawa ta rage tsayinta sosai ta mika mata kofin dake dauke da maganin sannan ta nemi afuwarta ta juya har tamkar zata kifa dan sauri

Ina jira na ga an dago wata yar yarinya a bata abin nan, sai gani na yi an talafo wata gindimemiyar budurwa ana ta faman shafa gefe da gefen fuskarta ana tambayarta idan har jikinta ne ya yi kamari a kirayi docter? Ita kuwa tana langwabewa da ture maganin wanda kana ganni zaka fahimci tsabar tabara ce irin ta wanda ya samu dama ke damun wannan baiwar Allah mai sunna BAHIJA ya a wajen sarkin garin TANUT, wato ya mace daya kwal a wajen uwar gidansa sarautar mata

...........................................................

Saurin da Fadime take bata zame a ko'ina ba sai a wajen ciyayin dake cen bangaren dawakai

A hankali ta ringa amsa gaisuwar da bayin dake kasanta ke yi mata cikin girmamawa a matsayinta na baiwa mafi kusanci da uwar gidan sarki kuma mata a wajen sarkin dogarai wanda yake sshine sarkin dogarai kuma shine wanda ke kula da lamarin dawakan wajen


Tunda ta karaso yake kallonta da ciyawar dake jibge a hannunsa wadda ya kwaso dan ya ciyar da bakin doki, domin dokin ne yakeda fada babu mai rabarsa da garaje

Dakatawa ya yi sosai yana kallonta har ta karaso

A hankali ta dan dago idannuwanta da suka shanye tamkar wace ta shanye su da gangan , bayan haka suke, da farko an zatama ciwon ido me da ita, domin idannuwanta a shanye suke koda yaushe irin tana kallon kasan idon nan, kuma girmansu da tudun samansu ya daka idan ta lumshe din kamar mai barci, ba kasafai take maka kallon cikin ido ba dan akan ce da ita wai kallonta na kayar da gaba, ta dan dago ta yi masa kallo a fuzge sannan ta maida dubanta wajen dokin dake kakawar da kai irin jibgegen dokin nan


Murmushi ta yi har kananun hakoranta duka bayana jere reras ta daga hannunta fari kallll tana kallonsa ta ce" Zan so na shafa Dokin nan"

Dokin ya kalla, sai kuma ya dake kallonta

Shekarun matarsa sun ja, shi din kansa ya fi a irga yana neman hutu ko dan yarsa kwalin kwal da Allah ya bashi a duniya dan su koma inda take so su rayu su kula da ita, ama abin ya gagara, yarinyar ta ki yarda ta zauna a masarautar zai je ya daukota ya kawota ama tana gannin mijin kanwar maman nata zai koma kauyen *LABA* zata silale ta gudu, tamkar wace ake cizo a masarautar, a rayuwarta ita dama lamarin rayuwar sarauta ce sam ba tata ba, bata so bata kauna, ita tana kaunar rayuwa ce irin ta yanci, yadda zata bararaje ta walwala abinta, shi yasa take guduwa tana barinsu su kadai hankalinta kwonce

Dokin ya sake kallo, sai ya yi murmushi ya kade hannayensa yana girgiza kansa ya shiga nufar bangarensu yana fadin"
8/13/22, 22:54 - Buhainat: *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍?*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*


🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻
*OUMOUGHLOUK ITIBEL*
_(ZAKIN SARAKAI)_
🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻

_FREE BOOK_

*Na*


*SAJIDA NIGER*



0️⃣3️⃣



Dokin ya sake kallo ya yi murmushi, sai ya kade hannayensa ya shiga nufar bangarensu yana fadin" So kike yi a garin Tanut a gile min kaina? Domin wannan dokin mahaukacin doki ne, idan ya bale nima a tsorace nake, kina so ya bige ki na soke shi? Bayan zuciyar sarkin garin nan ne?......... Fadime ni kam ina mamakin me saraki ya gani a dokin nan da ya kamu da kaunarsa, doki bakin kirin ba annuri ko daya? Gashin idannuwansama bakake ne sidik"

Dan murmushi ta yi tana tafe jikinta tamkar bata da lakka, hakan ya dakashi fakatawa yans dubanta sosai ya ce" INNARTA?, kamar hankalinki a tashe yake?"

Dakatawar ta yi itama da tafiar da take yi ta juyo tana kallonsa

A hankali ta sauke ajiyar zuciya ta karasa wajen zama ta zauna fuskarta na nuna alhinun da zuciyarta ke ciki

Jiki ba karfi ya karasa yana sakin labulen kofarsu ya zauna a gefenta kadan yana kallonta da yaren buzanci ya ce" Yauma wani abin ya faru da ke da uwar gijiyarki ne?"

Idannuwan nata ta dake dagowa tana kallonsa

Numfashi ta ja mai zafi, kai itafa a yanzu bama wannan ne damuwarta ba, danma rai da riko ne ta kasa sabawa da wulakancin dake bilowa lokaci zuwa lokaci a tsakaninta da Gimbiya, lalle a karkashinta take, ama an jima da goge bauta irin ta zamanin bayi, albashi garesu, aiki suke yi, dandai aiki ne na mudin rai, ama an jima da goge irin rayuwar nan ta rashin yanci, shi yasa take shan wahala, shi yasa ta kasa yin rayuwaa irin ta daba, shi yasa take yawan jin wani abu a cen kasan zuciyarta idan aka wulakantata

Dan murmushi ta yi tana kallonsa ta ce" ABANTA, ka san da ta kai shekara goma sha tara har ta dora a duniya? Nakan damu da tarin zulumin tarbiyarta, ka san wacece kanwata ka san halayanta, duda na san ba zata taba bari ta zamto mai irin halayar nan ba, ama ina cike da tsoron ta zamto wata iri daban, ina matukar son na ajiye aikina na koma kusa da yarinyata, da ace a zaman kalau ne ka dan da yanzu tana dakinta, irin halayarta na rashin zama waje daya kan dagan hankali, kar aje tana cen tana cafta tarai a dajin Allah, kar aje abubuwan da take gwadawa na jarumtar da ya dace ace namiji ke nuna su ta damka ta mayar ruwan darenta, kana tune dawowa ka yi ka tarar ta yanka sanuwar Ladan dan ta tungujeni, ........ni kam damuwar yarinyata ta fara taba min nutsuwata, idan har zan iya ci gaba da wannan aiki to fa sai idan na mikata dakin mijinta"

Ajiyar zuciy ya sauke ya gyara zamansa yana sake fuskantarta

Murmushi ya yi yana kada kai, ba dan komai ba sai dan tino damarar yarinyar tasa,
Rawani take yi tamkar dan saurayi tana shagalinta hankali kwonce
Dira take ta haye saman doki ta warci linzaminsa ta kada akalarsa tun bata wuce sha uku ba
Hm........... Lalle ya san ya dace ya nemi zama wa matarsa koda shi bai zauna ba, domin gidan Hindu ba gidan rainin budurwa bane, to wane ba wanema a cikinsu daga ita har mijinta? Ai tamkar makaho ne a saman makahon doki...........

Da son kwontar mata da hankali ya sake fuskantarta, hannayenta masu laushi da hasken fari dan tsaftarta da kuma zama a cikin ACn da take koda taushe a bangaren Gimbiya ya dan karra murzawa a hankali ya ce" In sha Allah, zan kamanta sake shigar da takardar ajiyewar aikinki, idan amsa ta fito mana sai mu je mu daukota, ama nima ba zan so ku fita nesa da ni ba, domin ina da bukatarku a gefena kin ji INNARTA?"

kai ta gyada tana sauke dan murmushi, duda tana cike da tunanin kamar aikin banza ne, domin an taba shugar da takardar a gabanta uwar gijiyarta ta yaga takardar tana fadin shirmen banza ba zata ajiye aiki yanzu ba, ama a yanzun tana tunanin ko a dace, domin ta kula ta ishi Gimbiya, bata san itama har ga Allah ta fara gajiyawa ba, zata so ta samu yanci irin na kowa ta kula da y'arta da kuma mijinta, ba bauta a banza ba!

___________________________________


Shigar yamaci suka yiwa baban garin na AGADAZ bayan tafia ta kwana biyu a hanya sanadiyar nisan dake tsakanin ziyarar da ya kai garin Dogon dutsi da kuma dan tsayawar da suka yi a hanya dan yada zango a wata masarautar da ziyara irin ta zumunci

Tunda suka shigo baban garin ya haye saman bijimin dokinsa fari kal mai dauke da kwaliya irin ta ALBE da azurfa harda salkar zinari

Kamar yadda yake da haske a fatar jikinsa, haka suturar jikinsa take, da kuma kamanin DOKINSA, takalmin kafarsa kafa ciki ne shima sai nasa walwalin yake


Jama'ar gari du an fito tarbansa, tamkar wanda ya yi doguwar tafia
Yawanci masoya ne, wasun kuwa yan su ga ya dawo da ransa da lafiyarsa ne? Taro dai taro na alkhairi ne, domin babu yaro babu baba, babu talaka ko mai kudi, sunna girmamashi sunna kaunarsa

A hankali ya ringa tafiyar da dokinsa ga dogarai a gefe da gefe rike da lema tafkekiya itama sai walwali take ta haske ko'ina

Kafafuwan dokin kan bada sauti cas cas idan ya ajiye kofaton kafarsa dalilin kwaliyar dake jikin kafar

A haka har suka karasa baban masalacin masarautar suka yada zango dan gabatar da sallar Magariba da kuma ta isha'i


Sai da suka gama sallar sannan ya shige Fada a nutse ya nufi bangarensa direct domin a mugun gajiye yake, danma an saba da hawa da saukar da kuma doguwar tafiyar? Ga umarah da zai tafi wace zai yi tafiyar sirri domin baya so a san inda ya nufa


A nutse ya kama hannun falonsa bayan sun gama gaisawa da UMMA, wace take jalabiyarsa uwar goyonsa shi da kanwarsa sama sama domin ba zai zauna ba ya gaji over ya shige falon nasa da yar salamar dake saman leben bakinsa

Idannuwansu ne suka sarke da junna a lokacin da ya shigo gaba dayansa
Tsadaden murmushi mai sanyayar da zuciya ta dakar masa daga tsayen da take sannan ta nufo shi da yannayin taku irin nata cike da girmamawa ta dan gyara doguwar rigarta ta baza alkyabarta a kasa ta sada kanta sosai a sanyaye ta furta" Barka da karasowa ITIFAL"

A hankali ya saki kofar dakin nasa ta dawo ta rufe, wanda hakan ya rufe kallonsu da UMMA ke yi daga nesa

Murmushi ta yi ta girgiza kanta ta juya ta koma nasu bangaren, watau bangaren matan masarautar

Idannuwansa ya lumshe mata yana sake binta da kallo a lokacin da ta duka har kasa ta saka hannayenta wajen kafarsa ta shiga sulube masa takalmansa dan ta san baya shiga ciki da takalmansa, yakan cire su a saka a wajen ajiyar takalmansa

A hankali ta kara dukawa sosai wajen fara kal din safar kafarsa ta kai bakinta da niyar yiwa wajen kisss sai dai baai bata damar hakan ba ya janye kafarsa da dan sauri yana sake wara dubansa a kanta dan ba zai barta ta aikata hakan ba

Murmushi ta yi ta mike ta saka hannayenta ta dalube alkyabarsa mai nauyi da masifar kyau ta karasa wajen ratayawa ta ratayata sannan ta juya

Da ido kawai yake binta domin bayan ta samu amsa irin ta fatar idannuwansa dan son gane me take yi haka?
Ita kuwa cike da takun kasaitar nan tata ta nufi wajen cin abinci tana fadin" Menene bukatar Uban gidana? A nan zaka ci abinci ko a dakinka? Domin burina na ciyar da kai da hannuna ko zan samu albarkar mai Albarka"

Jin shirun ya yi yawa dosai fiye da da, domin a da din takan samu dan gyaran murya ko kula irin ta dan sasaukan murmushi ya sakata juyowa itama ta zuba masa idon

Sake gyara tsayuwarsa ya yi a tsayen da yake yana harde hannayensa a dake ya furta" ME KIKE YI HAKA?"

Ido ta zuba masa na dan sekwani, sai kuma ta sada kanta a sanyaye ta ce" Allah ya huci zuciyarka, shin na aikata laifi ne?"

Lebensa na kasa ya dan dantse a hankali , sai kuma ya saki a hankali ya ce" Allah ya saka da alkhairi, ki je bangarenki"

Ido ta dake zuba masa, kallo irin mai tafe da ma'anonin da bakinta ba zai iya furta masa kai tsaye ba

A harhade ta iya budar bakin nata ta ce" Me yasa kake sake saka nisa a tsakanina da kai? Shekara tara fa ba kwana tara bace"

Kafarsa ya daga da kyar ya karasa cikin falonsa ya zauna saman lalausar kujerar falon mai laushin gaske da shinfidar dake samanta ta alfarma dannan ta daga kansa sama yana mai lumshe idannuwansa

Karasowa ta yi ta sake dukawa a kusa da shi sosai ta kamo kaffafuwansa ta dhiga cire safar nan sannan ta kama dogwayen yatsutsansa ta shiga matsawa a hankali a hankali tana dan shafa gashin dake kwonce a saman yatsutsan nasa lufluf masu tsantsi da baki
A hankali ta ringa yin dan sama da hannayenta tana dan matsa masa kafafuwan nasa tana jin yadda gashin jikin ƙafafuwan ke yi mata susa a tafukkan hannayenta

Idannuwanta ta lumshe da ciwo a ranta sosai na yannayinsu ta ce" Bayan na san cewa matsalar mijina a kaina kadai take da tasiri? Me zai hanna yauma mu kwatanta ko maganin da ake nema ya yi anfani? Ina tunanin irin yadda ake rokon Allah a lamarin ta yiwu a yau mu samu magaji?"

Kafarsa ya janye a hankali ya dago idannuwansa da sukai masa ja

Da kyar ya iya budar bakinsa a hankali ya furta" Ki tafi bangarenki"

Kai ta sake sadawa tana hadiye hawayenta sannan ta mike a sanyaye ta nufi hanyar fita tana rufa alkyabarta a saman kanta tana rike kukan da ya zo mata dan kar ta yi a gaban tarin bayin bangarensa da ba kasafai suke kwonciya ba

A hankali ya saka hannunsa ya ringa warware rawanin dake nade a fuskarsa har sai da ya dauke shi baki daya sannan ya sauko hular da aka dora masa aka nada masa rawanin a saman kanta

Gashin kansa baki sidik irin na bugaje ne ya warware daga nanadewarsa ya sauka a saman kafadunsa haka kuma sajen dake gefe da gefen fuskarsa mai baki da lufluftu ya wanzu a saman fuskar tasa da tsararen halitar fuskar

A hankali ya dago fuskar tasa, nan halitar ubangiji mai cike da kamala da tsari ta bayana, watau kyan halitar fuskarsa har zuwa kan jajayen lebensa dake walwali da dogon karan hancinsa wanda ya tafi har kusan girarsa mai cika fa baki a tare da ita sai razananun idannuwansa da suka dauki ja da kallo irin na hatsarin gaske wa'inda suka kawatu da gazar gazar din gashin ido masu duhu da kyali

Lebensa ya dake dantsewa, alamun maganar dake cikin zuciyarsa mai cin zuciyar ne, watau mai zafi ce a cen kasan zuciyar tasa ya mike tsaye yana saka hannayensa ya cire babar rigarsa sannan ya cire karamar ya rage masa dogon wandon shadar dake jikinsa fari kal sai dan shatin wando irin na maza na ciki baki wanda kana iya ganninsa ne ta cen saman tsatsonsa a lokacind a ya mike tsayinsa yana lumshe idannuwansa ya nufi baban dakinsa da tafiyar nan tasa tamkar wanda bashida laka a jikinsa


Bayi ya zarce direct yana idasa sabule dukkan wani abu dake sutura a jikinsa sannan ya shige cikin ruwan jakuzi mai hasken blu da aka hada da turaran ruwa na wanka mai sansanyan kanshi da dumi daidai misali ya zauna a ciki har gashinsa ya shige ya lumshe idannuwansa yana sake jin halitar jikinsa dake murde masa tamkar wace zata iya aikata masa wata tsiyar, bayan idan har ya fito da ita a haka ya tarbi wace take da damar karbarsa yanzu zata lange ta koma tamkar lagwami......? Wannan abin na ci masa tuwo a kwarya, haka kuma shine gagarumin matsalar da ya kasa daukan mataki a kanta, domin ya fi a irga ya nuna zai sawakewa iyalinsa dan kar a shiga hakinta ama firrr an tare gaba an tare baya, ita dinma ta kafa kai da kasa ta nuna ita ba dan wannan take tare da shi ba, bayan yau da gobe kayan Allah ko a yanzu shi yana hangen cewa matarsa ta kawo gabar nuna bukatuwarta a lamarin nan, kawaicinta na iya karewa wata rana, idan har sanadiyar haka ta fada halaka shin WANENE SILA?, tun bai yarda ba cewa aikin sihiri ke tare da shi har ya yarda bayan dogon bincike na kwararun likitoci da tabatar masa lafiyarsa kalau, a dole ya dawo yake sauraron SHEIK, domin lamarin abin duba ne, har yanzu kuma shiru, shi bai san dadin abin ba, ita bata sani ba, wannan

Please Login or Register in order to submit comment