Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dan tsayi kadan ta ja gashin gefe sannan ta saka macaji karami a hankali ta ringa caje wanda bashi da yawan har ya kwonta luflufluf, sai kuma ta saka yan yatsunta a na gefen ta dan kara sakashi ya karra tudu kadan ta barshi zube a gaban kijinta da gefen fuskarta kadan

Jan baki take ta kallo, da kyar ta iya janyo mai ruwan kasa kasa ta bude shi ta shafa dan kadan a bakinta , sannan ta dauki kwali tana ta kallo da tunanin anya ba sai ta yi kiran innarta ta saka mata ba? Domin bata taba sakawa da kanta ba ai

Karshe dai dagewa ta yi ta ringa karkata kai da kyar ta saka kwalin tana tsale da ihun ta saka sannan ta koma wajen kayanta bayan ta ga takwas ai ta gota tuni t dauka ta saka pant din da rigar ta koma wajen madubin tana kallon kanta harda dan juyawa a gabansa kadan ta dora hannunta a saman cikinta dake shafe uwa babu hanji a ciki ta yi murmushi , sai dai tudun duwawunta ne suka bata mamamaki, ba kasafai ta cika kallonsu ba, aminiyarta, kawarta Yar dubu ke yawan cewa ta ringa saka sutura mai rufe jiki saboda maza lalatatu masu bata ya'yan mutane dan Allah ya bata kira, ita kuwa sai tace Aminu zai iya tarda mutun ya kashe shege a kanta Alkur'an!

Murmushi ta yi tana gyada kai, idan ta koma ta labartawa yar dubu abinda ya faru da ita bata san ko zata yarda ba, ta yiwu sai ta sakata ta sha Kur'ani ko zata yarda, ama in sha Allahu ko kwana zasu yi sunna dambatuwa sai ta sakata ta yarda tunda ita ba makaryaciya bace bale a mata iya shege

Turaruka ta dauka a fili ta ce" Ku zo nan yayan albarka mu bare banza, tunda an zubaku uwa ba siya aka yi ba"

Karshe dai ta kai mintu talatin bayan karfe takwas din sannan ta fito da takalmi plat mai laushi ta yiwa Innarta salama bayan ta ja rantsuwar ba zata aikata aiki makamancin na jiya ba sannan ta fice ita daya babu ko yar rakiya ta bi ta babar hanya hankali kwonce tana tafe tana kallon yannayi da tsare tsaren ginnin sarautar ta garin AGADAZ, komai a al'adance sannan da tsarin zamani, kana gannin abin zaka gane an narkar da kudi fa ba abin wasa bane

Bata san cewa shiga ita kadai sai ta sha wahala ba sai da ta karasa bangarensa

Hanyar ta samu kanta da zubawa ido da tafka tafkan dakarun masu tsaitsaye sunna gadin wajen

A lokacin da ta sanar masu itace Bahija amarya aka yi mata tambayar zata halarci cin abinci ne? Ta bada amsa aka nemi da ta bada takardar gayata sai da mamaki ya kamata

A nutse ta aro halaya irin nasu, a dake ta bada umarnin a shiga a sanar da zuwanta idan an bada umarnin ta koma sai ta koma

A kan dole suka aikata hakan, bayan kamar minti biyar aka bata danar shiga

Baki ta tabe a ranta tana ayana' dama na zo da redion innata na saka kidan kai ku kama sana'a mata na maku habaici kitika kitikan banza kunna gafin kato...., Koda yake na san yana dan baku na sakawa na salati'


Haba dai ta samu ta karasa ta wuce bayin dake zaune bayan sun zube sun gaisheta sunna mamakin ganninta ita daya kuma amsa masu harda su ya gajiya sannan ta bude madubin dake fitar da danshin AC ta shiga da salama kasa kasa a bakinta

Ta tabata koda shi namijin bai kalleta ba, yan matan sun zuba mata ido, domin tana ji a jikinta kallonta ake yi,

Wajen da ake sarkafe kaya idan a shigo ta karasa, hankali kwonce ta cire Alkyabarta ta rataya a jikin abin ratayawar, wanda haka sai da ya saka HUZNAH kwarewa da abinda ta saka a bakinta ta dan shiga tari kadan tana sin cire idonta a kanta ama dan jaraba tana karra kallonta

Kasa kasa ya dan dago da dubansa daga abincinsa ya dan kalli HUZNAH
Sai kuma ya kai dubansa inda take kallo tana fan tari hadi da kai kofin ruwa bakinta

Samun kansa da zubawa yarinyar ido ya yi na yan dakiku sai kuma ya dauke kansa a ransa ya ayana' Ta tabata, yar daba ce yarinyar nan, ko irin yan duniyan nan rikaku'

Tana murmushi itama a nata ran tana ayana' Haka nake so, so nake na haukataki, ki yi zaman aure da mijinki mai sunna zaman aure kafin na tatara tsumakaraina na karra gaba Alkur'an, ama kina abu kamar wata bagidajiyar da bata da ilimin adini? Ilimi ai haske ne, kuma ko ni da nake kauye a wannan fannin na san me nake yi sarai!'

Bata tashi idasa neman rikita masu lisafi ba har Auta da ta karra zarro ido, Uwa uba Umma, matar dake bata mamaki, zaman cin abincin dare da ya dace ace ya yi daga shi sai matarsa a dakinsu abinsu aa, ga wata mai zarro ido kamar mai farfadiya, sai wannan rusheshiyar mata mai ruwa da munafukai a saka su tsakiya, ita kuma matar kai a kasa uwa tsohuwar algunguma a gaban mijinta? Uhum, sam basu da tsari gaskiya


sai da ta karaso facing din da yake ta dan kama gefe da gefen rigarta, ta dan baje tsayuwarta kadan sannan ta saki dayan hannunta tana murmushi ta yi wani yannayi da hannun da muryar murmushi tace" Barka da warhaka Aban su Datawa......"


Yanzun kam Umma ce ta ji miya miyar zata sarketa, a dan rikice ta cire dubanta daga kan Nadirar ta maida kan abincinta tana yin iya yinta dan hanna kanta sumewa da tashin hankalin da take kallo

Auta da du take a hali na rashin jin dadi dan an sakata cin tuwo mai nauyi bayan ita bata cika son tuwo irin haka ba , asalima nonon sanuwar dake cikin katon flask na yayanta take so a zuba mata, ama Umma tace wannan zata ci dan maganinta sai ta samu kanta da sakin boyayan murmushi tana sake satar kallon yayanta da abin al'ajabi irin na mahaukatan zamani ya saka shi dafe haba a bayane, duda rawaninsa iya bakinsa da habarsa kadan ya bayanar yana kallon rikakiyar yar gajaliyar nan

Dagowa ta yi tana fadin" Kai kuguna"

Sai kuma ta karasa ta kalli HUZNAH ta sakar mata murmushi a takaice ta ce" Sannu fa"

Sai kuma ta kalli Auta itama ta zarro mata ido yadda take ta zarro mata ta ce" Ke kuwa gyara dubanku mana haba"

Sannan ta sake kallon Umma, ta sakarwa Umma murmushi wace idannuwanta tamkar zasu fado dan kallo itama a takaice ta ce" Sannu dai Ummanmu"

Kujera ta ja ta zauna tana sauke numfashi irin ta sha aikin nan sannan ta ce" Walahu nake fada maki aunty dan kwali na nema na rasa karshe dai haka na taho kar aje na yi lati

'Latti? Dan kwali? Ya Allah ka sakani gane wannan mata tun kafin ta kasheni, wannan wace irin mace ce? Wani lati bayan sai da sarki ya zauna ta zo?, Wani dan kwali a tarin suturunta?, Ta rasa me zata saka sai wannan rigar?, Ta zo ta mana gaisuwa kamar sa'o'inta? Koda yake shima sarkin ga yadda ta gaishe shi uwa uba Umma?, Ya Allah menene wannan ne? Wacece wannan matar ne? Allah ka shiga lamarina da ita ya Allah ka dorani saman kanta kar ta rikita min zamana, ni dai banida matsala da ita, ama sai wani haroni take yi!' HUZNAH ta ayana a ranta sannan ta dauke kanta bata ce mata komai ba, dan baya so ana saman table a ringa yawan magana haka

Baki NADIRAH ta tabe, ita fa ba fa za'a yanka mata baki ba har ya zo yanai mata tsami dan bakin hali da rainawa kai wayo ba walahi, tsaf bakinta na magana ne Allah walahi

Abincin take kallo
Kaf abincin nak babu abinda ya yi mata, ba cika son abinci ta yi bama a rayuwa, hakan ya sa ta fara yin tsuru tana kallonsu daya bayan daya ta ga dai abinci kowa ke ci banda Auta dake dan fama da nata ta kasa ci da kyau

A hankali ta ce" Bakya son tuwon ne?"

Auta ta dago da sauri ta kalleta, a hankali ta saci kallon sauran, gannin babu wanda ya kalleta sai ta amsa NADIRAH da ido

NADIRAH ta dan karra kallonta ta ce" To ki bari mana ko dole ne?, Kina wani abu kamar an wanka maki mari"

Umma ta dago ta zuba mata kakausan kallo kafin ta budi baki a sanyaye ta ce" Allah ya karra maki lafiya, i ya zama dole ta ci abinci dan ta sha maganinta"

NADIRAH sarai ta karanci sakon idannuwan Umma, ama sai ta watsar

Hasalima mikewa ta yi ba kwaramniya ta shiga dan bubude abincin tana rufewa, yannayin da take yiwa fuskarta kamar ta ga wani abinda bata son ci mai warin nan ke karra kunna HUZNAH

Karshe ta maida dubanta kan abubuwan dake gabansa
A soyayarta da nono ko a me aka saka shi kallo daya zata yi masa ta gane menene

Murmushi ta yi ta dauki manyan kofuna na kwalba biyu ta ajiye ta mika hannu ta dauko nonon da ake tofe masa da addu'a daga wajen SHEIK sannan a kawo, nonon da ko Umma bata tabawa bale HUZNAH, ta bude ta cika a kofi daya ta mikawa Auta sannan ta cika a daya tana murmushi ta rufe ta koma ta zauna ta sake kallon Auta ta ce" Ki ajiye abincin sai ki sha wannan, yanada anfani sosai ga lafiyar dan Adam"

"A kan wani dalili zaki taba abin madarar mai martaba?" Muryar HUZNAH, da yannayi na ta fara hasala ta yi maganar

Kafin HUZNAH ta sauke harufanta Umma ta dauki nata itama a dan hasale ta ce" A kan wani dalili zaki saka yarinya ta sha madara bayan tuwo nace ta ci ta sha maganinta ne?"

Idannuwansa ya rintse, hayaniyar ta farra hawa kansa, jira yake ya ji ta yi magana a haukacen da ta saba, sai ya ji shiru
Hakan ya saka shi dago dubansa ya shiga binsu da kallo su dukansu
Su amsa suke jira daga gareta
Ita kuma ta dauki madarar da aka mata magana a kanta dan bakin rashin ji ta kai baki ta lumshe ido tana shanye masa madararsa, madararsa fa, shi fa, shi ASADEEK jama'a Rasulullah (S.A.W) 🚶🏻‍♀️🚶🏻‍♀️🚶🏻‍♀️🚶🏻‍♀️🚶🏻‍♀?


NADIRAH kuwa a ranta ayanawa take yi' ku bari na sha na dawo hayacina, sai mu baje idan hali ya kama, ai ba'a gwa da gwa da yinwa kawuna uwa dutsin jifan shedan!'












Tashin hankali, ita bata san me ake nufi ba hala? Mun shigesu🥺🥺🥺🥺
8/13/22, 23:01 - Buhainat: *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍?*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*


🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻
*OUMOUGHLOUK ITIBEL*
_(ZAKIN SARAKAI)_
🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻

_FREE BOOK_

*Na*


*SAJIDA NIGER*





3️⃣3️⃣



Sai da ta gama shanye madarar nan, ta lumshe ido tana jin yadda take ratsa mata kirjinta, watau sanyi ne da ita madarar, tana matukar son madara mai sanyi ama innarta sai tace aa in dai zata sha ga mai dumi kawai ta sha

Idannuwanta ta bude hankali kwonce ta sake mika hannu ta dauko dan tsinken sakace hakori kamar wace ta ci naman kazi ta dan bude bakinta kadan ta tsatsaka sai kuma ta yi wani tsut tsut da bakin nata sannan ta barshi a ciki tana dan wasa da shi a bakinta

A wajen nan Auta ta fi kowa jin kamar zata kurma ihu, domin tun kallon na mutun biyu ne har ya dawo na mutun uku sunna kallonta, amsa suke jira ama NADIRAH ta gama ta yi shiru abinta da bakinta

Umma, ji take yi, wani irin ashariya, irin na maguzawa, irin na mutanen kafurci na mata yawo a harshenta, so take ta yiwa yarinyar nan abinda bata taba tunanin ana iya yiwa mutun a duniya ba, sai dai wanzuwar UMUGHLUK a wajen ya sakata kasa barkata hakan

Ajiyar zuciya NADIRAH ta sauke ta kalli HUZNAH dake kallonta ta daina cin komai
Murmushi ta yi mata ta ce" Aunty, ba'a taba madararsa ne? Ko nice ban zama ta gida ba?"...........

Sai kuma ta kalli Umma ta ce" Umma, magani ai idan an sha madarama ana iya sha ko? Bata ra'ayin cin tuwon idan aka takurata sai ta samu matsala ai inaga ko?"

"Ba maganar kasancewarki yar gida ko yar wajen gida bane, babu mai taba madararsa, yaya zaki taba baki tambaya ba kanki tsaye"...... HUZNAH ta fada tana dake fuskantar Nadirah

Ko ajiye maganar bata idasa ba Umma ta ce" Bama wannan ba, maganar cin abincin Auta, shanta, komai nata nice a gidan nan, babu macen da zata shigo ta shiga ciki domin nice mamanta, kin gane? Kuma rashin lafiyarta dole ta ringa cin abinci a kai a kai "

HUZNAH ta sake cafewa, dan bata ga a kan me Umma zata hannata fadin nata damuwar itama ba, a birkice ta ce" Aa Umma, ai dolene nima na fada mata ta gane cewa madararsa, abu ne mai matukar mahinmancin da shi kadai ke shan abinsa, ko ke bakya tabawa, haka nima, ta zo ta dauka ba izini ba komai ta sha ta ba Auta?, Ai ba haka ake yi ba, ba wai maganar tana matarsa ko yar uwarsa bane, a gidana ta sameni dole zata bi takun tafiyata!"

NADIRAH ta sake waro ido wata shegiyar dariya na tukota, a hankali ta kai hannunta wajen bakinta ta furta" Toh fah" domin abin ya bata mamaki ainun, bale da kamar hayaniya da yar cacar baki ke neman kaurewa a tsakaninsu, hakan ya sa da sauri auta ta shanye madararta tana sake kallonsu itama
NADIRAH ta kalli wannan, ta kalli wannan mamakinta ya ki barinta, gaba daya sai ta samu kanta da raina masu ajawali walahi

Kamar daga sama, muryarta a tausashe ba a kausashe ba ta ce" Ku dan dakata ku huta mana, abin nan dai tunda ba sabon Allah bane ya dace ku saurara hakanan gaskiya, na gama fadin amsar kawai a wuce wajen mana, karawama zan yi!"

Sai da Umma ta ji zata kifu a sama, da karfi ta ce" Lah ha ila ha ilalahu......."

Kara talabe haba ya yi a bayane, kasa kasa sosai ya tare da fadin" Muhamadu Rasulullah salalahu alaihi Wa salam"

Umma ta nunata da yatsa ta ce" Babu abinda zaki karra a nan, yaushema kuka shigo da zaki nemi fin yan gida?, Dokata babu mai taka min domun ba zaki taba fina sonta ba, yarinyar dake fama da ciwon hauka ne zaki saka ta kwonta da dan ruwan madara a cikinta da magani?".........

Tunda ta furta kalmar nan, sai ASADEEK da HUZNAH suka zuba mata ido, kalmar haukan da ta ambata kai tsaye ba wani dan sakaya ya saka su zuba mata ido su biyun, Auta kuwa sai ta samu kanta da sada kai bata ce komai ba

NADIRAH ta zuba mata ido itama, kallon da take yi mata ya dan ankarar da ita cewa a yau ta so barin bacin ranta fitowa, uwa uba itace har da yin hayaniya a saman kansa bayan basa yi masa haka, hasalima abinda ya sa ta ci galabar sace zuciyarsa dan ta kasance mai tausasawa a gabansa, sam bata wasa da yarda da yin hayaniya a gabansa, shi yasa baya taba daukan maganar Auta dan ita da koke koke, da hauka haula take son ganar da shi, har kwanan gobe, shi yasa a kulun yake yi mata kallon da Umma ke nusar da shi cikin hikima

Wata wawuyar ajiyar zuciya ta sauke ta dauki tissu mai girma ta shiga goge fuskarta, sannan ta koma ta zauna
Kanta ta sada, ta rage muryarya sosai, kasa kasa ta ce" Allah ya huci zuciyarka, na nemi zurmawa dan bana son na ga wata fitina ta billo a cikin gidanka, mu barka da rigingimun cikin gari da na wajen gari mana? Ama sai abu ya nemi bilowa, ina son dakushewa ne dan kar Bahija ta yi aiki da isa da takamar ita yar uwarka ce ta kawo mana cenji a zamantakewarmu, ba zan lamunci haka ba, idan har na bata maka ka yafe min, na tuba ba zan kuma yin hayaniya a gabanka ba"

Ta idasa tana karra sada kanta sosai, wanda hakan ya saka Auta kafeshi da ido tana ta yin magana da idannuwanta ama baya gane komai, sai kwalar da ta cika mata ido da ya iya gani kawai

A hankali ya gyadawa Umma kai, hakan ya sakata sake sadawa ta furta" A tashi lafiya"
Daga haka ta fice ta bar falon tamkar zata tashi sama ta kuma nufi bangaren NADIRAH

Shiru ne ya karra biyowa baya, na yan dakiku

Cike da darajawa, da girmamawa HUZNAH da bata taba kamanta irin haka a rayuwarta a gabansa ba ta sada kanta itama tana share yar kwalar da ta tarun mata a gurbin idannuwanta
Ta rasa me yasa, ko kallon yarinyar ta yi sai ta ji wani katoton kaho ya tsaye mata a kirji, uwa uba irin abinda yarinyar ke nunawa , yayama za'a yi ta zo jiya jiyan nan ta nuna zata koya mata zama da mijinta? Yaya za'a yi ta zo jiya jiya ta zauna a kujerar da ta fi kusa da mijinta sannan ta dauki madarar UMUGHLUK ITIBEL ta sha har ta yi kyauta?

Da kyar ta iya hanna kanta yin kuka, muryarta a raunane ainun ta karra sada kanta ta ce" Allah ya huci zuciyarka, Allah ya karra maka lafiya, na bari abinda nake gannin duhu a gareni neman rufe min ido, lamari ne na halitacen abinda ban isa da shi ba a zuciyata, in sha Allah zan kiyaye gaba,.....zan je bangarena na yi shafa'i da wuturi, Allah ya tashemu lafiya"

Kallon abar sonsa yake yi, kallon matarsa mai laushi da nutsuwa yake yi, sosai ya yi mamakin gannin ashe ta iya fada?, Sosai ya yi mamakin gannin an hasalata da wuri haka, yana kallonta ta mike da idannuwanta da take tare hawaye ta sake rufa alkyabarta sosai ta juya ta bi ta dayar hanyar nan domin ba zata bi ta kofar shigowa ba bayi su fahimci halin da take ciki

Tana tafia wajen ya rage su uku kacal

NADIRAH ta yi wuki wuki ta kalli wannan kujerar ta kalli wancen, watau kujerun Umma da HUZNAH, sai ta ji kamar wajen yanzu yana neman yi mata yawa, dazu kuwa da abokan hamaya wajen har kadan ya so yi mata, dan so ta yi a yi ta yin rikicin har safe

"Kin san daraja da girman uwa kuwa?" Ta tsinci wata murya, mai cike da kamala, da nutsuwa, uwa uba da kaifi a zuciya ta daki kunnenta

A hankali ta juyo ta kafe fuskarsa mai dauke da rawani ido, a yanzu ta karra yarda da taken gadonta da ake yiwa maza, watau buzu babu rawani gwara babu wando (😁🙄), in ba wannan ba, menene ta kangama rawanin a cikin dakinsa, falonsa, tare da iyalinsa? To shi yana cire rawanin nan kuwa?

Sai kuma ta samu kanta da sake dora dubanta a wajen da shara sharan rawanin ya fi yawa, sam fuskarsa ba yaba yaba irin ta tsufa, to ama me yasa ake ce masa Aba?

"Ita uwa, itace halita mafi daraja a duniya, ita wannan da kika yiwa rashin kunya tamkar uwa take a wajenmu, kin san darajar uwa kuwa?" Ya sake ambata a tausashen da ya sakata lumshe idannuwanta ta mayar da jikinta ta jinginar jikin kujerar sannan ta sake bude zaburarun idannuwanta ta zuba a fuskarsa

A rants take ayana magana kamar haka' Sannin darajar uwa, ya sakani fadawa a bakin kura, sannin darajarta ya sakani tarban aradu da kai, sannin darajarta ya sakani juya baya na baro wanda nake so dan zuwa na rayu da bakin rayuwata, sannin darajarta ya sakani zama tamkar gimbiya bayan ni ba kowa bace face mutun dan Adam, ka sani da ban san darajar uwa ba, da yanzu wata maganar ake yi ba taka ba!'

Auta dake kallonta, ji ta yi kamar ta bude bakinta ta koya mata dukawa da bayar da hakuri, ji take yi kamar ta girgizata tace mata hakuri ake bayarwa gaba daya cikinta har wani kuuuuu yake neman yi gannin Bahija ta ki cewa uffan bayan yayanta na magana yana kuma son amsa ne

Kakausun idannuwansa ya lumshe, yana danne zuciyarsa dake tunzura da sake gannin tsantsar rashin kunya a tare da ita

Dubansa ya maida kan Auta, ya fitar da hannunsa mai dauke da birda birdan jijiyoyi masu girma da nuna halitar girma ya ce" Bana son abinda zai taba min ita, haka kuma bana son abinda zai taba min matata, ki kula kin ji......, Yayama sunnanki?"

Auta dake wuwulga idannuwa ne ta budi baki a hankali ta ce" Abah, dan Allah ka yi hakuri ka ji? Sunnanta BAHIJA"

Kakausan kallon da ya wurga mata ya sakata sada kanta sosai tana sauke ajiyar zuciya

Bai ce komai ba ya mike ya nufi falonsa ya zauna cike da wani irin tukuki shima na haushin Yar, wannan yarinya ai yanaga da ya samu haihuwa da ya nasota duniya, ama dan iya wulakanci da girmansa, da darajarsa ya ringa magana kamar zai ari baki tana kallonsa ba amsa? Zai yi maganinta ne, abu daya ya hannashi babalata maganar CHEIK walahi!


Bayan tafiyarsa, NADIRAH dake kallon Auta a hankali ta ce" Ya tafi fa, ki dago kanki"

Da sauri ta dago tana kallon NADIRAH, sai kuma ta rafka tagumi ta ce" Yaya na magana bakya bashi amsa?, Innalilahi aunty Bahija bakya tsoronsa?"

Maimakun NADIRAH ta bata amsar nan sai ta kafeta da ido, a hankali ta ce" Tun yaushe yake maki kallon mahaulaciya, me yasa kila yarda ake maki kallon wace bata da hankali?"


A zabure Auta ta sake kafeta da ido, wannan karron har hannunta na rawa sanadiyar bugawar da zuciyarta ta yi, tana kallon NADIRAH, NADIRAH na kallonta
Muryarta na rawa ta ce"
8/13/22, 23:01 - Buhainat: *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍?*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*


🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻
*OUMOUGHLOUK ITIBEL*
_(ZAKIN SARAKAI)_
🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻

_FREE BOOK_

*Na*


*SAJIDA NIGER*





3️⃣4️⃣

Muryarta na rawa ta ce" Yaya aka yi kika gane lafiyata kalau?"

NADIRAH ta yi shiru tana kallonta, bata san me zata ce mata ba, bata san ta inda zata fara ce mata komai din ba

Ajiyar zuciya ta sauke tana dan kawar da dubanta daga inda suke ta hango falo, a zaune yake yana operat din computer , hankalinsa baya kansu kwata kwata

A nutse ta karra fuskantar Auta , wannan karronma ta ki bata amsar tambayarta ta dubeta ido cikin ido ta ce" Idan shekaru suka fara ja, ko ba'a yi maka aure ba, ko iyayenka da rai, zaka zamto nama a gaban mahauta, idan na ce maka mahauta ina nufin du wani wanda numfashin da kake shaka a duniya ne ya zamto masa abin jin haushi da tsana a rayuwa, shekarun da suka hau kanka, ko nisa da iyayenka zai zamto ne ana wawurarka ba ji ba gani, idan har ka zama komai ka labe ko ka saki kuka yagalgalalen nama kake wanda kowani wawa zai wawura ya ce zai iya siya ya ci, ban ce maki wane ne makiyinki ba, ban kuma san kowa a cikin masu sonki da bataciyar rayuwa ba, ban san me kika rayu a cikinsa ba, ban san me kike rayuwa a cikinsa, ban san girman tsoron da kike yiwa koma menene ba, ban kuma san me yasa kike tsoron abin har haka ba, abinda na sani shine, babu bawan da ya isa ya tsalakewa kadararsa, kuma babu bawan da ya isa ya ja da hukuncin ubangiji, ka rayu kawai ba dan ka birge wani ba, ka kuma tuna da mutuwa da tsayuwa a gaban ubangijinka, wasa kike yi da sallah? Ke din mutun ce mai shagwabar da kika kasa jajircewa rayuwarki, ko me ya mayar da ke abinda ake dubanku kina da damar kaucewa, rashin sannin mafaraucinka shine matsala, idan har ka sani wayance masa zai fi komai zama abu mai sauki, kin ga ba fa fito na fito ake yiwa kowani mafarauci ba, dan wanin mashinsa ta fi karfin ya harba bai samu nama ba, ama ana iya yin wayo a

Please Login or Register in order to submit comment