Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na koma na dawo na san sakaran son da kike mata komai na iya faruwa, ki saurareni da kyau, walahi, walahi bilahilazi ki iya da ita, ki san yadda zaki yi da ita, a gobe gobe zamu sauka a garin AGADAZ mu kai maganar nan, kuma ta zaunu idan har kika yarda wani abin ya bilo daga ke har ita kunna jan numfashi ta bakinku kunna kallona sai na kashe ku!, Har kiyama zan aika ku!, Kin ji na rantse maki, sha sha sha, bakinta ya saki ya fadi wani abin....zaku kwashi kashinku a hannunku walahil azim!"

Ga mamakinsu, ga baban mamakinsu, idannuwanta ta dago tarr ta saka dubanta a cikin na mahaifinta, duda idannuwanta sun rine sun yi wani irin ja sanadiyar marin da ta sha ta budi bakinta tana kallonsa ido cikin ido ta ce" ABA, kan nufin idan ban yarda aka aura min mutumen da ka fi tsana a duniya ba sai ka kasheni?"


Babanta ya gyada kansa yana sake tabatar mata

Wani irin murmushi ta yi mai tsauri ta taka tna daura tawul dinta ta nufi wajen bayi, sai da ta kama bayin ta rike kofar tana kallonsu ta ce" Lalle kuwa da ka jima baka kasheni ba, domin na rantse maka da Allah ba zan auri Sarki ba, bana cikin tsarin wahalarku ku duka, ba zaku sakani a ciki ba, idn kuwa ka nace ka aura min din ka gani, dukkan abinda kake tunanin ban sani ba na sani kuma ba uwata ta sanar min ba!, Kar ka manta da ni kake yawo?"

Bam ta shige ta mako kofar tana dingishi

Wani irin kukan kura ya yi ta karasa ya ringa jijiga kofar yana fadin ta bude masa,ama firrr ta ki budewar

Juyowa wajen mamanta da ta yi mutuwr tsaye tana kallon taurin kan da yarsu ta yi irin na ubanta ya ce" Lalle yarki bata sanni ba, ama ina mai tabatar maki zata sanni kwana kusa in sha Allah, ki tabatar kin sameni a falona!"
Fuuuuu ya juya ya bar dakin, ya fice yana sake kallon FADIME dake rabe cen kanta sade, da sauri ta daga kafarta dan ta bishi sai dai ganin kamar ya juyo yana kallon Fadime sai ta tsaya tana sake kallonsa

Har ya wuce Fadime din ya dawo ya tsaya , a kausashe ya ce" Ina fata halinki na rashin saka kanki a inda bai shafeki ba yana nan?"

A tsorace ta dago ta dan dube shi, sai kuma ta sake sada kanta tana gyada kanta

Huci ya sauke ya juya ya wuce a falon gaba daya


Ita kuwa Gimbiya dake tsaye tana kallon Fadime juyawa ta yi ta koma dakin wajen Bahija

Bayi ta nemi zarcewa, sai dai abin mamaki sai ta ga Bahujar a saman gadonta a dukunkunne tana rawar sanyu


Da sauri ta karasa saman gadon da Bahija take dukunkunne tana rawar dari ta hau ta kuma talabota tana kallonta a tsorace da halin da ta nuna ta ce" Bahija? Abanki yau kika kalla kika yiwa wannan furuci? Bahija Abanki?"

Bahija ta dake fashewa da kula tana mayar da kanta saman cinyar uwar
Mamanta ta ce" Bahija, ki yi shiru haka kin ji? Ki yi shiru Bahija kin fa san idan ran mahaifinki ya bace babu abinda baya fada, ransa ne kawai a bace kin ji? Ama kuma wannan abu da kika yi ya tsoratar da ni, Bahija abanki ne fa, kin fi kowa sannin irin soyayar da yake yi maki, dan yau ya nuna yana so ki masa wannan yar alfarma ta takaitacen lokaci dan kema ki karra samun kwonciyar hankali a rayuwa sai ki kiya? Ina cewa abin alfaharinki ne ko cikin kawayenki a ga waye mijinki, ina cewa sai kin fi kowa farin cikin wannan hadi fa Bahija?"

Bahija ta dago rinanun idannuwanta tana kallon mamanta, a hankali ta budi bakinta muryarta a shake sosai ta ce " Mama, ransa a bace? Na masa alfarma? Kennan ni na kashe kaina ko? Ai alfarmar da zan masa shine na bijirewa auren nan, Mama ni fa ban damu ba, da gaske ko da wasa yake duka ba sunne a gabana ba, abinda na sani shine ba zan taba yarda da auren wani da ba wanda na gani a cikin jirgi muka yi hotel daya da shi ba, mama kina maganar kece raini, akoy wace zata fito da mijinta na fito da nawa a cikinsu ta isa daga kai? Mama kyan, ajin, kudin , hutun, tsarin, ilimin ya fi su walahi, Mama bara na karasa maki magana domin Allah, ni fa ba zan auri Sarki ba, ga wanda nake so zan nemo shi ko a ina yake, zan kuma kawo shi gidan nan a aura min, idan ba haka ba kafin ya kashenin sai na tona waye shi kuma na kashe kaina da kaina, ni fa a kan wannan mutumen ba mutuwar nake tsoro ba, tsoron rasa shi ya fi mutuwar karfi! Ba zaku fahimci me nake ji a zuciyata ba? Taba kirjina ki ji? Ko menene na hadu da shi mai zafi ne, kuma ina shirye da samama kaina shi ko ta aure ko ta wanin aure, ni dai sai na raba wannan mutun da kowa ya zama nawa ni kadai!"

Tabas mahaifiyarta bata taba haduwa da tashin hankali irin na wannan rana ba, kanta ya coshe, ta rasa me zata tuna , ta rasa wani irin tunani ya dace ta yi, gaba daya hankalinta a tashe yake

Da kyar ta ringa rarashin yar tana fada mata ta fauna maganar zata kashe kanta, mahaifintama ransa ne a bace, ita kuwa ta tsaya a kan bakanta bata da niyar ja baya, a kan mutumen da ta hadu da shi tana iya yin fito na fito da mahaifinta! UMUGHLUK ITIFAL kuwa su da shi, ba zata taba aurensa ba, ita inama zata iya zaman aure da mutumen da kowa ke tsoro, mahaifinta kansa tsoronsa yake yi kamar ya mutu, ama ita zai mikata ko? Aa walahi ta san ciwon kanta idan kowa bai san mata ba


Da kyar ta rarasheta ta sha maganinta sannan ta rufo mata dakin t tafi da ky din da kanta dan ba zata bari ba aje ya dawo su halaka junna, tana so mijinta ya gane idan me y'arsa ta zama halinsa ne kuma shi ya kaita ya nuna mata, a yanzu bashida kaico walahi!


Wajen fa FADIME ke zaune ta karasa ta tsaya rana karra kalle mata kallo
Ta sani sarai, a duniya idna akoy matar da mijinta ke rakawa da ido wannan matar ce, ko me yake yi idan ta zo waje sai ya dakatar ya bita da ido, koda bai fada ba ita ta dade da sannin begen Fadime ya cika zuciyar mijinta, shi yasa take kafa kafa sam bata wasa da sakacin da zai saka UMUGHLUK ITIFAL jin labari ya kashe mata miji a kan baiwa!

A kausashe ta ce" Kina iya tafiya "

Ajiyar zuciya Fadime ta sauke ta mike tana sake dan dukawa ta ce" Allah ya tashe mu lafiya Ranki ya dade"

Gimbiya ta tabe bakinta ta rakata da muguwar harara har ta fice tana tafiyarta cikin sanyin hali


A nutse take tafia, duda dare ya yi ama da fitilu haka kuma da mutane dake yan shagulgulansu jifa jifa

Tana karasowa bangarensu ta kunna tocila domin a nan din akoy duhu , haka kuma a zuciyarta sai Adu'ar tsari take yi

Da sauri ta dakata da tafiyar a haskawar farko sakamakon kan fuskar mutun da ta haska

Sai da ta sake haskawa ta zuba mata ido da mamaki muryarta kasa kasa ta ce" Kamar INDI?"

NADIRAH ta turo baƙi tana sake shagwabe fuskarta sai soshe soshe rake yi

Hindu ce ta fito tana fadin" Dan karbi wannan shafa mu gani? Haba tar autana ki bari mu musu kwana daya jal sai mu tafiyarmu kin ji?"

Da takaici Fadime ta ja dan tsaki ta karasa tana janyo tabarmar kaba ta yada masu a nan tana amsa gaisuwar Hindu dake mata marhaba da gaisar da ita a mutunce tana murmushi

Fadime ta ce" kun ci abinci kuwa?"

Hindu ta ce" Aa so nake na lalabata, kin san ita daga mun sako kafarmu masarautar nan sai tace ita ranta baci yake, kaikayi masarauta ke sakata, ita ji take kamar ta je ta mari Gimbiya, shine nake mata yan turarw turare kar aje iskarsu ce bata hadu ba"

Kwaryar da Inna ta dauko da ludayi dan dama masu furar da ta tarar mijinta ya kawo mai yawa ta dan dakata ta kalle su daga ita har innar tata

Bata ce da su uffan ba ta cira kai ta karasa wajen tabarmar kaba ta budeta sosai, domin ita ta saka abinta da kanta fadadoya ce tabarmar ta cire hijabinta sai dan kwalin dake ciki ta yafa shi da kyau a kanta ta tankwashe kafafuwanta ta saka ludayin nan sannan ta shiga damawa

HINDU ta turo baki tana sake kamo hannun yarta kasa kasa ta ce" Kin ga, ki rufa mana asiri mu yi kwana biyun nan lafiya mu gama lafiya ba tare da ta zane min ke ta sakamu kuka ba kin ji? Kina gani kamar haushinmu take ji din nan?"

Itama kasa kasa ta ce" Innata me zai hanna mu kaura gidan amaryar mu yi bikin a cen har a gama? Na tabata hararan da take na sarkar kafana ne da kuma kitson da aka yarfa min, Innata ban san me yasa Innar birni ke haka ba"

Kasa kasa ta amsata da fadin" Wuce mu zauna mu nutsu mu gama lafiya , abinda safiya na yi take zuwa bangaren wancen tabi tabin ta sarki sai kuma wani daren, ke dai kafin nan zuwa safiyar ne zamu kama kanmu"


Saman tabarmar suka karasa ita kuwa ta gama damawa sannan ta kalli NADIRAH ta ce" Tashi ki shiga ciki kusan gado ki dauko min mazubi, harda na babanki ki wanke su a cen ki bani"

Tashi ta yi, sai kuma innarta ta tashi zata bi bayanta

Kallonta Fadime ta yi ta ce" Ina zaki je?"

HINDU ta ce" Tayata zan yi , na ji aikin da kamar yawa"

Da takaici Fadime ta ce" Zauna malama"

Hindu ta kalleta da irin kallon nan na ban fahimta ba

Fadime ta sake dagowa ta ce" Ki zauna na ce ko Hindu?, Ke kam Allah ya shirya ki, meye na yawa a wanke yan kwarayan da basu wuce hudu ba? Ki dai ringa tunawa yar taki daki zaki mikata , idan ta je tana aikata wani mugun aikin na kazanta ko lalaci babu abinda zai hanna a zage ku, duba ki ga wani shiga a jikinku daga ke har ita, na rasa me Habu yake yana kallonku kunna tsiyar nan, zauna min!"

Hindu ta gyada kai ta je ta zauna tana kallon yayarta

Kasa kasa ta ce" Aunty, nawama take yar? Ashirin ne fa zata cika, Allah na tuba dama ai da ni zaki mikamu na ringa mata yan share sharen da dan wanke wanken da dan girkin har ta gane , kuma in sha Allahu in bata gane bama sai na ringa safiya ina yi ina dawowa, Allah na tuba abinda da kokarinta, a wuni fa sai ta je rafi sau biyu kuma ta je dandali rai abinta, dama ita bata cika son wahalar sosai ba, to ganu aikin me nake yi?"


"Muhammadu Rasulullah salalahu alaihi Wasallam, ke Hindu ki san annabi ya faku ki gyara halinki, yau ina anfanin mace ba shara, ba guga, ba wanke wanke, bale girki? Ai walahi ba kyau ba ko yar uban wanene sai ta wahala, kika san gidan wa zata je? A cen din zata samu sasauci ko wahala? Ke wani namijin kin san ya fi kishiya masifa, daga ke sai shi a gidan zai zamar maki balaki, bale idan da dangin miji masu jira a yi ? Kunna nan ku a tunaninku kyan da iya shegantakar kadai ke ja ko, kar ki manta talaka kike, yarki talaka take, idan kuka daukarwa kanku wannan hali yaushe garinku zai waye? Kanwata ki ringa tsawatawa Indi, ki ringa nuna mata an ki, ba komai ake nema a samu na, ba kulun take tare da ke ba kin ji?"


"Aunty yi kasa kasa kar ta ji ki mana, aunty tsaya ki ji, bari ki ji labari, kun ga yar cen ko? Ni ina ji a jikina in sha Allah sai mun yi alfahari da ita, kuma auntu da kike fadin mu talakawa ne sai me kennan? Mu talakawa ne ama kuma masu rufin asiri a cikin talakawan ma, talaucinmu bai hannamu fara'a ba, bai hannanu bautawa Allah ba, bai hannamu farin ciki ba, bai hannamu hulda da jama'a ba, aunty shegantakar nan kuwa da kike ganni maza da yawa na dauko ta biyu ko ta uku fan ta farkon bata iya shegantaka ba sam...... Allah ma kuwa, ki dai dan bari kawai ki karra Adu'a, ama ko Aminu ne ko? Ni walahi dai dai ya san yadda zai yi da mu duka domin ba zan bari a wulakanta min ya ba!" Ta karashe harda dan buga cinyarta tana kara alamu irin na iya gaskiyarta take fada kennan


Salamar Aban NADIRAH ya sakata sake dagowa tana murmushi daga wanke wanken ta ce" Abana ka dawo, dan rike min daya mu kaima inna ta zuba furar nan mu rangada"

Yana murmushi harda yi mata sannu ya amshi biyu ya nufo innarta, wace ta saki baki da hanci tana kallonsu Nadirah na bashi labari ya fara kyakyata daria y ajiye kwarayen ya kuma amshi sauran ya ajiye ya juyo ya ce" Shi Aminun?"

Nadirah zata yi magana Innarta ta fashe da kuka tana ture furar dake gabanta tana kallonsu gaba dayansu da suka rikice sunna tambayar ba'asin kukan nata

Da yatsarta take nuna su ta ce" Yanzu, tsakani da Allah idan muka mace gaba dayanmu fa?, Ko idan wata kadara na tare da ita fa? , Jama'a bakwa gannin sangartar ta yi yawa? Ke Indi dan ubanki je kwaso kayana da na abanki kaf ki wanke su yanzu yanzu ba sai gobe ba, kuma Innarta walahi sai dai ki kauro nan mu zauna tare ama yar cen ko? Yar cen? Sai na bata kyakyawan horon da ba zaki ganeta ba, ! Balen abin nan na kafarki kar na tashi na karya ki, kin shigo birni wata fasara za'a maki dalilinsa?, Abanta abanta yanzu ka riko mata mazubin nan da kanka? Ka riko mata??????"







☹️☹️☹️☹️☹️☹️Tap wollah yau gaba daya in fada maku rubutun ya ringa min gwalo☹️ dan kar na barku shiru ne na samo wannan😍😍😍😍😍
8/13/22, 22:56 - Buhainat: *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍?*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*


🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻
*OUMOUGHLOUK ITIBEL*
_(ZAKIN SARAKAI)_
🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻

_FREE BOOK_

*Na*


*SAJIDA NIGER*




1️⃣1️⃣



Sorry ba edditing 😁


Gaba dayansu rasa ina zasu sakka kansu suka yi, ya zamto sai neman gwaruwa suke ciki harda NADIRAH

A rikice NADIRAH ta yi ciki ta haska fitilar Abanta ta shiga ciro kayan , duda a hade suke a kule sai da ta fitar da su kaf ta kawo ta ajiye ta je wajen manyan robobin wankin ta dauko ta ajiyesu sannan ta shiga hada ruwan wankin

Innarta idannuwanta ne suka cika da kwallah, a hankali ta muke ta shigewarta ciki dan ta dan yau mijin yayar tata ba zai kwana a nan ba, dama idan sun zo yakan yi tafiyarsa wajen mazan gidan ya yi kwonciyarsa,

Da ido FADIME ta rakata sannan ta sake maido dubbanta wajen mijinta tana jan hanci ta ce" Yanzu haka kuka zata shiga ta yi dan an saka Yarta wanki ko?"

Murmushi ya yi yana sake gyara zamansa yana kallonta ya ce" Wai menene?, Na tabata kukan nan ba haka kawai zaki kwashe shi ba, meye aka maki yau? Me yake damunki?, Duba ki gani yarinyarki ta tsorata ji yadda take wankin jikinta na rawa?, Kin sani sarai wa kuka haifa Dimana, kuma kin san wankin dare ba kyau, me zai hanna ki mata uzuri ta kule kayan cen ta kwonta kusa da mamanta da sasafe in sha Allah ta tashi ta yi wankin?, Kin ji Fadimana?"

Ajiyar zuciya ta sauke, domin kukan da ta yi sai ta ji sanyi sanyi a ranta, a hankali ta saci kallon y'ar tata, sai kuma ta dauke kanta kasa kasa ta ce" To ka ce mata ta bari, ni dai ba zan mata magana ba , dan kar ta raina ni"

Sai da ya sauke ajiyar zuciya, domin a gaskiya da bata yarda ba bai san ba ko zia iya hakura NADIRAH ta yi wankin nan da daren nan, basuda wuta a bangaren nasu da sai ta yi idan da hasken fitila, kuma fa rikicin Fadime ne, ya tabata akoy abinda ya daga mata hankali , domin har ga Allah yarinyar fa ba laifi tana da kokarin aiki walahi,

A sanyaye ya umarci NADIRAH kan ta ajiye ta je wajen mamanta ta kwonta dare ya yi

Kai ta gyada ta daure kayan ta ajiye su da ci masu alwashin sai dai a tashi a ga ta gamasu, ita abinma ya rikitata me ya saka mamanta kuka?

Sumui sumui ta zo wucewa Innarta ta saka ta dauki furarsu ta kaima innarta su sha

Dauka ta yi harda su godiya ta shige ciki

Mahaifinta ya yi murmushi ya dake kallon iyalinsa
Kamar yadda ya kware wajen yi mata nasiha ya ce" Me yake damunki?"

Ido ta zuba masa na dan kankannin lokaci, sai kuma ta girgiza kanta a hankali tana jinginar fa bayanta a jikin garu a sanyaye ta ce" Ba komai Abanta"

Sake kafeta ya yi da ido, sai kuma ya sauke ajiyar zuciya a hankali ya ce" Kin san ta yiwu gobe ace da ke za'a je baban birni ko?"

Kai ta gyada a hankali tana kallonsa

Ya ce" Kina son zuwa ne?"

Kallonsa ta yi da yannayi irin na son gane da gadke yake da tambayar nan?, Sai kuma ta yi murmushi a hankali ta ce" Inada zabi ne Abanta?"

Kai ya sada yana dan murza yan yatsunsa, sai kuma ya sauke ajiyar zuciya a hankali ya ce " Ina iya samun hanyar da zan hanna a je da ke"

Murmushi ta yi ta girgiza kai, a sanyaye ta ce" Zan iya, idan har hakan ya tabbata in sha Allah"

Idannuwansa ya lumshe sosai yana jin abu mai girma a ransa a kan iyalinsa, sai kuma ya sauke ajiyar zuciya ya mike ya dauki kasonsa na furar yan murmushi ya ce" Ko dan rakiya ba za'a yi min ba Madame?"

Itama murmushin ta yi ta mike ta dauki hijabinta ta ce" Mu je na taka maka mijin Fadime........"


Raka shi ta yi sosai sunna hira sannan ya tsaya yana hangenta har ta shige bangarensu kafin ya ja ya rufe masu ya tafi

Tana dawowa ta tarar da HINDU zaune saman tabarmar kabar kanta ko dan kwali babu ta nade kafafuwanta tana kallon waje daya

Dan murmushi ta yi ta karaso ta zauna a daf da ita tana fadin" Kamar wace kika kulaceni daga fadin gaskiya?"

HINDU ta dawo da dubanta kan yayarta, kallonta take yi har sai da ta mata alamu na kallon fa? Sannan ta girgiza kanta tana dankwashi a kanta ya bata kas kas kas ta ce" Gaba daya rayuwar gidan nan so take ta dauke dukkan wani abu mai daraja da kike da shi a rayuwa, kama daga fahimta, fara'a, nutsuwarki baki sani ba"

"Ikon Allah daga yiwa yarki fada shine za'a dora min wani abin daban?" Fadime ta fada tana zama daf da ita, domin ta ga ta yi kalar serius, ko menene ba da wasa ta zo mata da shi ba

Matsowa ta yi ta kama hannunta ta rike tana kallonta , a sanyaye ta ce" kin san na san ba lamarin Indirah bane ya saka ki kuka, shin me yake damunki da kika kasa fadawa Yaya bayan kunnada kyakyawar alaka tsakaninku, bakya boye masa komai?"

Ido ta fara zuba mata, kafin ta waiga wajen dakin da NADIRAH take, ta karra tabatarwa ta yi barci, sannan ta sake dubanta

A hankali ta sada kanta, sai ga hawaye ya shiga bin gurbin idannuwanta

Muryarta na rawa rawa ta ce" Ina tsoron wata rana na gaza kanwata, abubuwan da nake gani nake ji sun fara neman fin karfin kunnuwana da kuma hankalina da tunanina.........., Bayan neman shiga mutuncina da ake yi wanda na jima da fuskantar haka, shi yasa nake sake lulube jikina da tufafi dan na kare mutuncin kaina da na aurena, a yanzu maganar da nake maki abinda kunnayena suka jiyo dangane da UMUGHLUK ITIFAL nake tsoron kasa rikewa!, Shin me y masu da zafi haka?, Me ya kashe masu ne? UMUGHLUK ai uban kowa ne, yanada kannanun shekaru ama kuma ya dauki girman, ni ba zan taba manta shi ba domin shi ya wanke zargin da ake yiwa Ummu kafin ta rasu, a dazu na ji abinda ke neman tarwatsa min tunanina, na san banida wata hanya da zan iya kare shi sai dai Adu'a, ama ina jin tsoron kar karambani ya sakani tarban aradu da kai, bayan na san banida nasara a kokowar....., Hindu ina ji a cen kasan zuciyata wata rana zan iya shiga uku idan na ci gaba da aikin nan"

Hankali tashe Hindu ta ce" Aunty dole ne? Ki bar aikin mana, dan Allah ki samawa kanki sauki , innalilahi wa inna ilaihi rajune wa yake son shiga mutuncinki? Me suke so su yiwa UMUGHLUK ITIFAL? Na zata dan uwansu ne?, "

Ajiyar zuciya ta sauke mai zafi ta ce" Idan na bar aiki ba zan iya zama a gidan nan ba, kennan na tafi na bar mijina? Sia yaushe zamu ringa gannin junna? Karshen wata ko shekara?, Idan na bar aikin nan aurena na cikin hatsari!, Kuma da kike fadin dan uwansu, ai na rabaki da giyar mulki, du wanda ya kurbeta ba zai taba sakuwa daga maye ba!"


Hindu kam ta rasa me kuma ya dace ta ce, gaba daya auntynta ta sakata a hali na tunani da cikin duhu, ta rasa me ya dace ta yi tunani a kai a yanzu

A sanyaye ta ce" Ko me suke takama, zakin sarakai ubansu ne!"

Itama a sanyaye ta ce" Haka ne, idan yana gannin fada gaba da gaba ba, idan kuwa ta karkashin kasa ake binsa da sharin fa? Sai dai A'lah ya kare shi kamar yadda yake kare shi a kulun!"

"Allah ya tsare shi, aunty, wa yake bibiyarki?" Hindu ta fada

Gabanta ya sake faduwa, a hankali ta janye hannunta tana mikewa ta ce" Ki tashi mu kwonta kar mu rasa sallar asubahi a kan lokaci"

A dole Hindu ta yi hakuri da abubuwan dake zuciyarta ta je itama ta samu waje gefen y'arta ta kwonta barcin

Tunda suka rashi sukai sallar asubahi su biyun suka dinke a daki sunna zantawa tsakaninsu, ita kuwa wannan lokacin ta riika ta matsa kusa da pampo ta darji wankin nan gabaa dayansa

A lokacin da mahaifiyarta ta fito dan yin wanka ta shirya ta ganta tana shanyar karshe

Da mamaki ta bita da kallo, sai kuma ta nufi pampo dan dibar ruwa a bokici

Da sauri NADIRAH ta ajiye ta zo ta tararwa mahaifiyarta ruwan ta mika mata bayin sannan ta koma ta ci gaba da wankinta

Wata biyayiyar ajiyar zuciya mamanta ta sauke ta karasa ciki ta yi wankan ta fito

Tana kimtsawa tana jin muryar Hindu na fadin ta bar sharar nan ta je ta yi wanka bara ita ta karasa sharar, watau dai sunna ja in ja sunna kus kus ga dukkan alamu gardamar kar ta ji ake yi

Murmushi ta yi ta kintsa da kyau sannan ta dauki lafcecen hijabinta ta fito ta ajiye kujerar tayani tsegumi ta zauna tanaa fadin" Kin ga je ki yi wankan ki zo ki je ki amso abin karinmu yi maza"..
Murmushi ta yi ta nufi bayin, domin ta mika ruwan tuni , ita kuma HINDU ta gama kamaala sharar ta kwashe taba murmushi ta kalli abin shanyar ta ce" Ka ga yar arziki irin albarka, yarinya mai albarka gaba da baya, ina fata a sallarku ta yauma kin mata Adu'a mai kyau Aunty?"


Murmushi Fadime ta yi, kasa kasa sosai ta ce" A kullun inai maku Adu'a ku dukanku, ina fata Allah ya sshiryar min ku, gashi kuwa ashe dai da dan sauki a halayar naku"

Murmushi kawai hindu ta yi ta zuba ruwa a roba mai dumi ta zauna ta saka kafarta ta

Please Login or Register in order to submit comment