Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

makanta da me ta yi kama?...........

Mikewa ya yi ya fito daga cikin ruwan ya karasa kasan shower ya tsaya lokaci daya yana danna ruwan sanyi dan baya so ruwan dumi ya dakeshi sannan ya sake lumshe idannuwansa

Sai da ya dauki lokaci a cikin bayin nan ya fito ya cenza kayansa

Shi dake dauke da muguwar gajiya, maimakun ya nemi waje ya kwonta sai kawai ya fice ya shige dakin Gymnastics dinsa ya rufe a hankali ya karasa wajen yar karamar redion dake ajiye ya danna karatun Alkur'ani ya karasa wajen injin gudu ya hau ya danna ya shiga gudun da dukkan jarumtar da Allah ya bashi, wace idan har ka dubeshi a haka ba zaka taba yarda cewa wai UMUGHLUK ITIFAL ne a haka , watau *ASADEEK BRAHAM*

______________________________________


Karfe goma na safe ya fito daga bangarensa, da yannayi irin na dan gagawa

Ja ya yi ya tsaya sakamakon kanwarsa da ta karaso da sauri jikinta na rawa ta zube kasa muryarta cikin alamun Kuka kuka ta ce"
8/13/22, 22:54 - Buhainat: *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍?*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*


🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻
*OUMOUGHLOUK ITIBEL*
_(ZAKIN SARAKAI)_
🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻

_FREE BOOK_

*Na*


*SAJIDA NIGER*



0️⃣4️⃣




Ja ya yi ya tsaya sakamakon kanwarsa da ta Karaso da sauri ta zube a gabansa, yannayin nan nata na kulun mai tafe da alamun tashin hankali wanda magabatansu suka tabatar masa ciwo take fama da shi, wanda ya kaita asibitin, haka kuma ana yi mata rukiya ama abin sai a hankali, harta zama da mijinta na neman gagararta domin abin rikicewa ya fi yi ba sauki ba

Muryarta na rawa, alamun kukan zata fashe da shi kanta a kasa da jajen da ya zamto mata jiki ta dago rinanun idannuwanta da sam bata samun isashen barci da su ta zuba a saman fuskarsa

Mruyarta a raunane ainun ta ce" Aba?"

Idannuwansa ya lumshe, yana jin zuciyarsa na dokawa da karfi

A hankali ta fashe da kuka tana sada kanta, kuka ne take yi wanda idan har ka dubeta zaka gane akoy abinda ke damunta, gaba daya baiwar Allah a birkice take, tarin dukiyar gidansu da sarautar gidansu bai hadata da komai ba fface tashin hankali da rigingimmun rayuwa, gaba daya ana kallonta da haka ne ana danganta hakan a matsayin dan ta wayi gari ta ga gawar umansu gangar jikinta rabe da kanta ta samu tabuwar hankali, babu wanda ya san menene CIWON wannan baiwar Allah

Kukan ta idasa fashewa da shi, wanda ke hadasa masa hauhawan jinni da tashin hankali

A hankali ya sake rintse idannuwansa a hankali ya duka, lokaci daya dogarin da ya shigo dan tabatar da fitowarsa dan su gyara abinda zai kaishi filin jirgi ya tafi garin dogon dutsi da suka wayi gari a safiyar yau ba gimbiya ba danta hankali tashe ana nemansu baki dayansu wanda a yanzu mijinta da kansa ya bada umarnin idan aka gansu a kawo su baki daya masarautar garin agadez dukkan hukuncin fa ya hau kansu a zartar, dan kuwa ba zai yarda ta jaza masa masifa ba yana zaman zamansa

Da sauri Dogarin ya tare hanyar shigowar yana hakimcewa a dokin kofar

Hannayensa ya saka a hankali ya dagota

Bai ce da ita komai ba har sai da ya dangantata da doguwar kujerar falon a hankali ya zaunar da ita sannan ya zauna ya kuma riko hannayenta duka biyu yana murzawa a sanyaye ya ce" Autana? Menene? Kin ji jikinki kuwa? Zafi sosai, me kike so ne?"

Shigowar UMMA ya saka Auta saurin sake damke hannunsa sannan ta nemi shigewa jikinsa tamkar wace ta ga wani dodo

UMMA ta karaso tana rage tsayinta sosai, cike da iya tafiyar da wanda ta saba ta shiga kawo masa gaisuwa sannan ta tambayi lafiyarsa tana hankalce da Auta da abinda take yi

Auta muryarta na mugun rawa tana sake shigewa jikinsa ta ce" ABA, dan Allah ka maida ni gidana ka ji?"

"Wani irin gidanki za'a maida ke a haka Auta? UMUGHLUK yayanki ne ba abanki ba kulun nusar da ke nake yi, ki dauki dangana kin ji babyna?, Zo nan zo mana jikina na rarasheki yar autana kin ji?" Ta fada tana mika hannunta da nufin janyo autar

Da sauri Auta ta doke hannun UMMA tana sake shigewa jikinsa, sai dai wannan act da ta yi ya saka shi dakatar da ita yana nuna bacin ran da yake ta dannewa , da dan kausashiyar murya ya ce" Hey, UMMAN kike dokewa hannu?"

A dan zabure ta dago tana kallon idannuwansa domin a cikin rawani yake , fuskarsa a boye take

Da sauro UMMA ta ce" Aa ka barta dan albarkana, ka san yannayin jikinta, ai takan min hakan sai a hankali zata daina in sha Allah, ka tashi ka tafi uzurin gabanka ka ji? Allah ya tsare , zan kula da komai nata kar ka damu ka ji? Ka san yannayin jikin da ya zamto haka sai a hankali"

Idannuwansa ya dake lumshewa cike da gamsuwa da maganarta

A hankali ya ringa bambare hannayen Auta dake kallonsa tamkar zata summa, wani irin kallo mai tafe da tashin hankali da firgici har ya gama zarewar shima yana kallonta da tarin tausayinta a zuciyarsa ya juya ya karasa ya yi gyaran murya aka bude ya fice a falon gaba daya


Jikinta ta hade, ta sada kanta tana wani irin makyarkyata da jikinta mai nuni da a birkice take

Murmushi Umma ta yi tana dora kafarta daya kan daya tana kadawa

Kai ta cira tana jan zaren alkyabar dake jikinta a kausashe ta ce" Dama zaki ba kanki lafiya, ki aminta da maganin samun lafiyarki? Ke kin san menene zaki yi ki samu lafiya, idan har kika ci gaba da naci, da nuna mini taurin kai, kina ji kina ganni yayanki da ya fi kowa sonki zai ci gaba da yi maki kallon mahaukaciya!, Ba kuma zan taba bari a fitar da ke daga masarautar nan bama bsle har wani ya kalleki da mutunci, haka zaki wulakance ki lalace har ki kashe kanki!, Ki sani mulkin wanda kike kira ubanki kayadade ne, takaitace ne!, Muna nan kamar yadda kika ganni da alkyaba bayan ban gada ba gaba da baya, zaki ji ana kirana gimbiya........ Ki ci gaba da yi min taurin kai, zaki kwashi kashinki a hannunki yarinya!"


Kanta ta dago tana kamo abin hijabinta tana dake rukunkumeshi a jikinta tana kallon Umma, abu daya take ji a zuciyarta a kan matar nan shine tsana, tsana mai tsananin gaske, sai dai abin tashin hankalin ko a cikin zuciyarta bata isa ta furta cewa Allah ya rabata da Umma ba, sai dai ta ringa Adu'ar A'lah ya rabata da wannan masifa dake damunta......., Idan ta budi baki a yau ta fadi wacece Umma ta tabbata yayanta ne zai fara soketa da ranta, bale jama'ar fada da kowa ke son UMMA saboda munafurcin da ta kware a shi ta iya siyan kowa? Bata tunanin akoy wanda zai yarda da maganar dake cikin bakinta, sai dai ta janyowa kanta balakin da ya fi karfinta, ita bama mutuwar take tsoro ba a yanzu, ta mutu ta bar matar nan a tsakanin yayanta da jama'ar garinsa!,

Idannuwanta ta sake rintsewa hawaye na zubo mata tana ji Umma ta mike ta fice

A hankali ta sake bude idannuwanta ta kankame jikinta ta budi bakinta dake bari ta ce" YA ALLAH, KAINE GATAN BAWANKA, KAI KA SAN ABINDA YAKE BOYE, KUMA KA SAN WANNAN MATA NA NEMAN FIN KARFINA YA ALLAH, SAI DAI NA SAN KANA NAN KUMA KANA AMSAR ADU'AR WANDA AKA CUTAWA, YA UBANGIJINA KA RABANI DA WANNAN MASIFAR DAKE DAMUNA, ALLAH KAR KA DAUKI RAINA A WANNAN HALI YA ALLAH....." Ta karashe tana sake fashewa da kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro.................


____________________________________


*Kauyen LABA, nesa da gari kadan daf da kogin garaje*

A hankali take kara yin dage a saman yatsutsanta masu dauke da dogwayen yatsu da faratunna masu dan tsayi da haske tass, haka kuma kafarta ta hagu daure da wata sarka fara kal ta azurfa

A zabure kawarta ta mike tana sake dafe kanta da hannayenta biyu, kirjinta na fokawa fat fat fat tamkar itace ta goce zata afka a kogon nan

Karkacewa ta yi tana bin yadda kawar tata ke yi ta rike igiya da sauri tana dake zarro ido
Bata daina sake dosar kwaduwar dake cen tanakula irin na kwadi ba, haka kuma numfashinta a sama yake sosai dan idan har tga afka a wannan kogon itama ta san sai ta ci ubanta a wajen nan


Ido kawar ta rintse tana sharce zufa ta ce" ki yowa Allah ki juyo hakanan, ki bar kwadin nan haka, le wai kwado halal ne kuwa?"

Dara daran idannuwanta ta sake zarrowa ta juyo tana dora yatsarta a saman lebenta ta sake furta" SHIIIIIIIII, idan kika yi na afka a ramin nan kin san Hindu sai ta karar da danginku kaf, domin ba zata iya rayuwa babu ni ba!"

Shirun kuwa ta yi, domin koda da wasa a tsakaninsu akoy kanshin gaskiya, dan kuwa a jiya har magariba ta sanyo kai ana masifa tsakanin Hindu da kanwar Babar mijinta, matar ta zo ta fadawa Hindu ta daina tura mata aljanar yarnan tata, domin mijinta idan ta shigo masu gida har ta fita bashida abin yi sai kallonta, yarinya ana neman koya mata karuwanci, Hindu ta dauki tafin hannunta mai dauke da yan yatsu biyar ta kifawa matar mari wanda nan da nan garin LABA ya dauka aka yi ta masifa da kyar wutar ta mutu, domin tace ba zata iya hakura a mari daya ba, ita kuwa tace sai dan yayarta ya saki matarsa, shi kuwa yace atafau bai ga abin saki ba a kan dan mari bayan da gaskiyar Hindunsa!


Ledar dake kugunta ta dauko ta bude tana murmushi ta dan duka da nufin kwashe kwadin dake tatare a waje guda kamar an hade su anai masu nasiha

Ta kawo hannu zata famka wani bakin maciji ya damki guda a bakinda

Ihu ta saka ta watsar da ledar, a haukace ta juyo tana takawa da wani irin sauri ba kamar na dazu ba nan da nan sai gata ta tsalako bakinta na fadin" Baki ne a cen, baki ne wawa zai hadiye kwado bai dan ajalinsa ya hadiya ba!"

Takalmansu kawar tata ta kwasa ta kwasa a guje , itama ta mara mata baya suka fala da gudu kai kace wasu yan kannanun yan mata ne

Basu zame ko'ina ba sai karkashin bishiyar da suke hutawa suka zube sunna ihu da kyakyacewa da daria

Kawar tata ta ce" Yau da jarabarmu ta haifar mana da Da da ido!, A yau sanadiyar neman soyawa Aminunki kwado da mun tafi lahira !"

Daria take yi har tans dafe shafafen cikinta , hakan ya bayanar da wushiryar dake tsakanin hakoranta na sama yar siririya da kuma dumple din dake gefe da gefen kumatunta tana numfarfashi tamkar zata summe itama ta ce" Yanzu yaya zamu yi kennan? Aminu fa a jiya a dandalin lami da idannuwana na ga yana siyan naman Habu!"

"Wai ke naman kwado halal ne?" Kawar tata ta fada tana dafe haba

Hannayenta ta watsa ta ce" an dai ce dukkan halitar dake kasan ruwa halal ne, bama a yankawa ai"


Kawarta ta kama haba ta ce" Dankari, toh shi kwadon a cen kasan ruwa yake ko yayane?"

NADIRAH ta yi tsai, sai kuma ta ce" Kin ga dan Allah kar ki hafen tunani kin ji?, Ai kawai nama nama ne, ni dai takaicina abin kauna ya siyo nama a titi, yo aikin me nake?"


Murmushi ta yi ta ce" Kin san menene? Na tabata idan kika dafa masa kwado fushi zai yi da ke, kwado fa"

Itama murmushin ta yi tana mikewa ta zauna da kyau sannan ta janyo fararen kafafuwanta da suka yi budu budu da datin farar kasa ta ce" Na tabata zai sauka da wuri, ya kuma san a kan SO NE"

Kai kawar tata ta girgiza tna dafe habarta ta ce" INDIRAH, lokuta da yawa idan na ga kunna soyewa ke da Aminu sai na ji tsoro ya kamani, ina tsoron furucin mahaifiyarsa da tace sai dai idan bayan ranta, wai me yasa suke aiki da halitarki suce idan kyau ya yi yawa masifa ne? Gaskiya ana cenfe cenfe a ruga!"

Itama murmushin ta kuma yi, murmushi mai matukar karbar fuskarta, ko an fada mata yana yi mata kyau ne ya sa take karra bashi mahinmanci du idan zata yi?, A hankali ta janye dan tsinken da ta nade nanadaden gashinta da shi ta sokashi a cikin kasa ta dubeta ta ce" To idan ta mutun ba sai a yi ba?, Ban san me yasa nakeda bakin jinnin wasu mutanen ba, kema da ba dan kin raina kaka ba da ba zamu yi kawance bafa, an ce mata ina iya dusashe tarmamuwarki in muna tare, ba za'a ringa ganninki ba sai ni kadai?, Ni dai abinda na dani a kan AMINU daya ne, iya rai muna tare, ko na kashe shi ko ya kasheni ba zan iya rabuwa da shi ba, domin tun ban iya so ba har ya koya min.......... Na tabata yana kofar godan Hindu tashi mu karasa na ga ABINCIN RUHINA kin ji? Mamansa kuwa ta sake daure kugu da kyau, idan muka buga mata muhamada a zo a kada kalangum daurin auren danta da ni!"

Ta karashe tana janyo takalmanta ta saka na hannun hagu din, da na damar ta dake wani katon kadangare da ya nufosu gadan gadan ta jefar da shi ta saka takalmin sannan ta janye abinda ta soka a cikin kasa ta sake hade gashin nata a tsakiyar kanta ta nanade ta soke sannan ta nufi wajen kawarta watau RAMA suka dauki hanyar gidan KANWAR MAMANTA watau HINDU shagali.


A tsaye suka tarar da ita, ta sha wani irin daurin zani wanda ya haura cen saman kaurinta , kanta ba dan kwali ta Barbaza gashin kan nata tana tsaye tana rike da kofar dake jikin hanyar shigowa tana leke

Idannuwanta na dauka a saman fuskar y'ar yayar tata ta daki murmushi ta mika hannu ta janyota tana fadin" Lalle da yar so yar cikin kirjina, yarinyar da zan wanke na mikawa sarki, dan walahi uban talaka ya yi kadan na bashi yata, na fada na kara, nu har an min iya shege ne a kan yarinyata? Idan da ubanda ya ga a wajen da aka ce dan ta cika kyau maya ce ita ko aljana ya kawo min wajen na karanta, iskancin banza iskancin wofi, yau sai na ci uwar maman Aminunki a garin nan!''


Ido ta zarro a haukace ta idasa shigowar tana kai hannunta ta rufe bakin Hindu tana sake zarro idannuwanta ta ce" Innalilahi Inna me dangin abin kauna suka maki kuma kike zagi so kike ta karra cewa ba zata bani shi ba?"

Ido suka zuba mata, daga innar tata har kawar tata, ba za'a bata shi ba? Innalilahi wa inna ilaihi rajune, yau sun ga salwatacen bakon iskanci a wajen NADIRAH!


"Ke indirah Hindunta , kar ki ce mun a kan namiji kina iya kuncen zani a kasuwa?, Dan ubanki yanzu uwarsa ta fita ta zo ja min kunne wai kar ki kuma shiga sabgar danta, itafa ba zata taba bari da ranta ki aurar mata da ba , salon ki saka ya manta wacece uwarsa a duniya? Wai sam bama zata iya bari ki shiga ahalinta ba , domin yayansama sonki yake, ke bari ki ji ni kuwa nace ai ubansama yana iya sonki dan kin keru, kuma nima na ja mata kashedin danta kar na kuma ganninsa a kofar gidana ya zo zance, ya kiyayeni ya kiyayi yata, dan walahi a kanki sai na nada mata duka, muma bama so!" Hindu ta fada tana zarro ido da sake gyara tsayuwarta

Silalewa Nadirah ta yi a kasa tana cire abin dake soke a kanta ta fadi" Shikenan, na shiga uku na lalace, ku ina ruwanku da soyayarmu ne wai? To guduwa zamu yi idan kuka shiga ciki, mamansa kuwa ai kyaleta na yi idan da rabo ba dai ta je kiyamar ba a yi? Haba Innar Indi ke da kanki? Gaskiya wucewa zamu yi a je a basu hakuri"


Kamar an gaurawa Hindu mari a kuncinta haka ta dafe kunci a zabure, sai kuma ta kai hannayenta saman kanta ta fashe da kuka tana fadin"









Asalamu alaikum.......fatan kunna kalau? Yaya ake ciki? Yaya kuke gannin ake ciki? Yaya kuka ga salon?........ Shin me yake boye mai zai bayana a rikicin tafiyar labarin UMUGHLUK ITIFAL?

WANENE UMUGHLUK ITIFAL ASADEEK BRAHAM?

ME YAKE FARUWA DA KANWARSA

YAYA LAIFIN DAKE CIKIN GARIN TANUT? YAYA ZAI WARWARE?


ME KE TAFE DA ZUCIYARKU DANGANE DA NADIRAH, WACE AKE KURA DA INDIRAH, YAR GIDAN FADIME DA INARTA HINDU? .............. BAN FARA DAN NA DAINA BA IN SHA ALLAH KUMA FREE NE.......LADAN BIYANKA KAWAI COMMENT NE 🥰🥰🥰🥰🥰🥰











*Yar uwa, shin kin sayi labarin kwatena mai taken CARBIN KWAI?, idan bali siya ba lalle zan iya kiranki mai wasa da dama, carbin kwai shine ke tafe da abubuwan da zaki iya fadowa daga saman gadonki dan dariya da farin ciki, akoy abin tausayin, uwa uba cakwakiya............CARBIN KWAI akoy ilimantarwa, tunatarwa, nishadantarwa, ke harta motsin gado😁, ki dai garzayo kawai hajiyata tuni mun fara posting a naira 300 kacal ki samu naki ki more*
8/13/22, 22:54 - Buhainat: *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍?*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*


🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻
*OUMOUGHLOUK ITIBEL*
_(ZAKIN SARAKAI)_
🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻

_FREE BOOK_

*Na*


*SAJIDA NIGER*




0️⃣5️⃣



*Wai kun siya kuwa? Ku fa zo ku samu naku, takensa shine CARBIN KWAI na KWATENA, kawata , maman jariri, wannan marubuciyar BADAKALA na AMMAR dan aljannah, da kuma BAIWATA mai lulube da baiwar alkhairi......., Ba zigi a ciki ba kuma kodawa irin ta mai siyarwa, idan ka siya sai ka ji tamkar ka karra ninka mata kudin dan farin ciki da jin dadi.....MALAMAR hazika ce mai baiwa a lulube a tare da ita....... MAZA GARZAYO KA SAMU NAKA A FARASHI MAI SAUKI 300 NAIRA*




Hindu ta fashe da kuka tana kallonta ta ce" La ila ha ilalahu muhamadu Rasulullah salalahu alaihi Wasallam, yanzu Indin Hindu ni zaki tisa mu koma na baiwa matar da na gama yiwa alkawarin yata sai saraki? Ke wannan yarinya ki raba kanki da lamarin maza, ke yanzu wace irin soyaya ce zata saka ki gudu da kato ki barmu da abin kunya a NIJAR? Kar ki manta wanene ubanki a gidan sarkin garin TANUT, kar kuma ki manta wacece mahaifiyarki a fadar matar mai Garin TANUT!, Ni din nan kin san wacece ni, kuma ki wulakantamu haka? Ko dai magani ya yiwa y'ar nan ne wannan shegen langayayen yaron?"

NADIRAH ta kwabe fuska, sosai ta nuna daf take da yi mata kuka ta ce" Ba zaki je ba dai ko? Imnata ba zaki je ba? Ai shikenan Innata ki yi zamanki, ki zauna idan Aminu ya tsaneni duniya zan bi Innata, ki zauna, kuma kin sani sarai a duniyata ba ni ba maganar ratse ta hanyar da sarki ya bima bale wai ni na kasance a innuwa daya da sarki, Innata ko sarkin yan iskan garin nan aka aura min in dai sunnansa sarki in sha Allahu ko gawata aka mika sai ta yi fatalwa ta dawo da kafafuwanta, me ake da rayuwar sarauta rayuwar matsi rayuwar rashin barkatawa kai abin kirki? Kana zaune tamkar duwawu komai sai an yi maka? Innata ki daina yi min mugun fata kin san fa uwata ce ke ko?" Sai kawai ta karashe tana mai fashewa da kuka harda kwonciya a nan wajen ta dora kanta gashinta du ya shige cikin kasa

Tsuru tsuru suka yi, daga innar tata har kawarta sunna kallonta

Innarta ta sake dantse lebe, ita kam jarabawarta a rayuwa kaunar yarta ne, a duniya bata iya cewa NADIRAH aa, walahi tana iya yin ba dadi da mijinta ta kwonta kalau abinta , ama idan hankalin NADIRAH a tashe ko ruwa bata iya sha, tunda yayarta ta haifi yar take jin tamkar ita ta nakudo abinta ta haifo, shi yasa harta sunnanta yan gari suka hade suke kiranta INDIRA wasu suce HINDIRAH, domin a bayane soyayarsu take ba a boye ba, soyaya irin ta uwa da d'a, a kan Nadirah fa ita sai ta zagi mai rabo walahi ko uban wanene!

A hankali ta dubi Kawar NADIRAH ta ce" Ki kamata mana kema kina kallonta?"

Ajiyar zuciya ta sauke ta ce" Inna kin san halinta sarai fa, bafa zata saurareni ba"

Inna ta sake sauke ajiyar zuciya ta kunce mayafinta ta yafa a saman kanta ta duka tana rike hannun NADIRAH ta ce" Shikenan, tunda so kike a raina maki uwa salon gobe idan an zo taron auren naki ace uwar taki wacece ita yo a wajenki tashi mu je, ama kar ki manta bafanki bai san zan fita ba, kuma kin san ba kyau matar aure ta fita mijinta bai sani ba ko?, Sannan kuma idan muka je na bada hakuri an kama maki gori kennan, Haba ta Aminu, haba aminar Aminu?, Idan kika yi hakuri da kaina zan raka ki dandali na ba Aminu hakuri ku ci gaba da hirar tsakiyar ranarku kin ji yar arziki irin albarka?, In kuwa kin fi so mu je din mu je kawai sai na dukama na bata hakurin ai ba komai rayuwa ce dan an min gori an zagi innarki ai ba komai"

Kukan nata ne yaa rage tana kallon Innarta

Innarta ta ce" Yi shiru tashi ki daina kukan, in dai dan tisa keyar uwa ne a kaita ta bada hakuri ai ba yau ba kika fara, yau kika fara kaini na bada hakuri idan mun yi fada da mutane ne? Tashi mu je Allah na tuba mai bada hakuri ai shine dan aljannah!"

Manyan idannuwanta ta kikifta, sai kuma ta sada kanta bayan ta dago shi tana kakabe kasar dake kanta, haka kuma ta yi shiru da kukan da take yi

A sanyaye sosai ta ce" Innata, baki yi tatsa ba?"

Hindu ta yi murmushi ta ce" Haba dai ai ba zan zauna har ki dawo ban yi tatsa ba, bayan na san shine abincinki, gayacen cikin kwaryar cen a lulube da saki dan ya kara sanyi"

Murmushi ta yi itama ta mike ta karasa wajen kwaryar ta zauna ta bude tana sake sakin murmushi, domin an shake mata kwaryar sosai
Gaskiya ba zata kai innarta ba innar Aminu hakuri ba, matar bata son zaman lafiya, me yasa ba zata yi hakuri bane wai? Kulun sai ta zazageta , da a iya ita ta tsaya lafiyar Allah ba zata fadawa Innarta ba, ama ta taso ta tardo inna? Bayan in dai a kanta ne inna batada hakuri? Sam bata kyauta ba walahi, ama ba komai zasu hadu da Aminun ne, bara ta sha ta koshi ta yi shirin dandali, ta tabata bawan Allah shi yau bama zai iya cin komai ba, ai idan suka yi fada tamkar zai muti yake dawowa, aminu kennan aminin arziki abin kaunarta!................


___________________________________


Tafiyar jirgi suka yi, zuwansu da dawowarsu, hakan ya sa dudu basu wuce awani biyar ba a tafiyar tasu da zamansu da sarkin garin da kuma dawowarsu garin AGADAZ, domin tafia ce ta takaitacen lokaci a jirgi


Kana gannin fuskar Mai garin Agadaz zaka fahimci yana cikin wani hali, domin fuskarsa ba alamun ya taba yin daria, duda a cikin rawani take, ama haka zaka iya fahimtar hankalinsa ba a tashe ba

Sallar la'asar suka gama a baban masalacin fadar, ya zamto kusan kowa ya watse sai shi sai Sheik

Kansa a sade yake yana jan carbin dake hannunsa a hankali ya sake duban Sheik dake magana a sanyaye

Ajiyar zuciya ya sauke a nutse ya ja rawanin dake saman fuskarsa ya dake mayar da dubansa saman makarar dake ajiye a cikin masalacin sannan ya sake duban SHEIK a nutse ya ce" Wanene ni, da za'a ringa maimaita min cewa Mulkina takaitace ne? Da ni din wanene da zan shagala cewa mulkina dawamame ne? In ba shirme irin na Bafana ba da ya fitar da maganar nan wace

Please Login or Register in order to submit comment