Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shiga darza, wanda Hakan ya saka Innar birni zuba mata ido tana kallonta da tunanin ita rabonta da ta darji kafarta ba har ta manta ba? Sai dai ta darji ta wasu, watau ta gimbiya ko ta bahija

Da dan sauri ta dauki lafayarta mai ruwan dalbejiya ta nada a saman yar doguwar rigarta sannan ta suri kwanon da innar birni ta nuna mata ta nufi fita a ranta tana ayanna' Ban san yaya aka yi hankalinsu ke kwonce a cikin gidan sarauta ba, rayuwa irin ta prison ? Baka isa ka yi kwakwaran motsi idan wani dan Adam din na kusa?, Ai wannan din sam ba rayuwa bace, ukuba ce walahi!, Ina dalili rayuwa ba yanci ba sauki ko kadan?, Ba zan taba irin rayuwar nan ba, ya zamto abinci sai ka zo baban dakin madafa ka amso naku ka juya? Iyayen gidan gidan na hangenku sunna maka maku harara tamkar dabobin da suka siya a kan dole?, Shi yasa ta fi ganewa rayuwar kauye, ta fita ta sakata ta bararake ta wala da ranta ta saki karinta ta hau sama ta fado hankali kwonce, idan ta yi ra'ayi ta yi wanka a teku, ko ta je rafi ta yi, kauyen da ake sako budurwa a gaba dan bata yi aure da wuri ba, kauyen yanzu da sauki, bale Innarta a gefe?ai sai dai ku kashe junna kai da ita!,

A hankali ta kai dubanta wajen baban falo, watau falon uwar gidan Sarki

Kai ta cire ta karasa tana gaishe da masu kula da madafar sannan ta musamman ka nasu kwanon

Mai zubawar ta kama haba tana fadin" Iyeah, wannan dai kamar Nadirar sarkin dogarai?"

Nadirah ta yi murmushi tana dan kawar da kanta tuni ta shiga jan wala haula, domin ya zame mata jiki ko dan azalzalar da innarta ke mata a kan haka cewa ko ido hudu suka yi da mutun ta ja masa wala haula dan ba'a san irin mutun ba sam

Amsa ta yi tana ji sunna ta maganarta harda mai tambayarta kuma an saka ranar aurenta ko kuwa? Ita fai murmushin dai ta karra basu sannan ta wuce abinta cikin takunta a hankali tana kuma sake kallon bayin dake ta kai kawo ta tabe baki a ranta tana ayana' ku kunna aiki, su kuwa sunna sama?'


"Wacece wannan?" Gimbiya ta tambaya daga tsayen da take a jikin babar tagar dakinta tana dan shan Lipton mai dumi dan tuni ta shirya fitowar mijinta wanda baki suka dakatar kawai take jira domin har alkyabarta ta rufa

Da sauri wace ke kula da ita da sasafe kafin Innar birni ta karaso ta duba wace ake tambaya

Da dan murmushi tana sada kai ta fadi ko wacece, domin a jiya ai sun jima sunna hirar yarinyar, dan kuwa du ta leleka su, yarinya mai dadin hali da kyau kamar ba yar bafade ba

Kara zuba mata ido Gimbiya ta yi har ta bacewa ganninta

A hankali ta koma cikin dakinta ta zauna saman kujera ta dora kafa daya a kan daya tana kallon waje daya

Wani irin murmushi ne ya kubuce mata ta kai dubanta wajen wayarta dake haskawa alamar kira na shigowa

Dagawa ta yi ta amsa , sai kuma ta mike da sauri ta idasa hada abubuwan da ya dace ta zuba a jakarta sannan ta ba baiwar nan dama ta dauko suka fito


NADIRAH na komawa ta tarar da mahaifanta sunna ta kimtsawa, watau shiri na fita

Da mamaki take kallonsu ta ce " Innar birni ga abin karrin fa? Aban birni ina kwana?"

Hannunta abanta ya kamo yana murmushi ya ce" Lafia kalau indin innarta, kin ga zamu je Agadaz ni da mamanki, in sha Allah da yama zamu dawo, ki zauna dam kin ji ko? Banda tabin magana"

Da dan sauri ta daga kafa tana binsu ta ce" Ama ai baku karya ba fa?"

Mahaifiyarta ta dakata daga tafiyar da ta fara domin sun yi bankwana da kanwarta tuni ta juyo ta kamo hannun Nadirah, Gefen fuskarta ta shafa a hankali, ta sakar mata murmushi kadan a sanyaye ta ce" Ai zamu karya, abanki ba zai barni da yinwa ba tunda tare muke, ki kula kin ji yar albarka?"

Murmushi ta yi tana gyada kanta tana hangensu har suka fice kwata kwata a balbalin

Kwanon abincin ta kalla innarta ta zuba mata

Zama ta yi ta turo baki ta ce" Innata, ni bana son cik abincin nan nasu, wainar fulawa nake so da yaji mai dadi, sai kuma , yauwa sai kuma in hau doki"


Ido innarta ta zarro tana kallonta ta ce" zo nan yar albarkana mu ci mu gama, sai mu ga yaya za'ayi da maganar dokin, ama wainar fulawa ina muka ganta mu a nan? Bari da rana zan fita na damo maki nono da kaina , na tabata rigimar ba ta wainar fulawa bace ta nono ce"

Ai kam, innarta ta gama sanninta ciki da bai, ta saba idan ba karyawa ta yi da sabuwar tatsa ba har wata kasala ke lulubeta, da murmushinta ta karasa suka shiga lamarin gabansu ita da innarta, sunna yi sunna tadi da kyakyata dariya.
( Alhamdulilah, idan har da salatin annabi da wadatar zuci, zaka fi mai kudin farin ciki da kwonciyar hankali, Allah mun gode maka ka karra haskaka mana zukatanmu bijahi Rasulullah salalahu alaihi Wasallam)




______________________________


Tafia ce ta dan kankanin lokaci, duda rashin kyan hanya, da wuri suka karaso GARIN AGADAZ

Ba tsaye tsaye suka nufi gidan sarki, sai dai tun daga nesa da hanyar karasawa babar fadar suka fahimci ana wani abin mai mahinmanci, domin taron motoci sun cika wajen sosai

Dogarin da ya bada damar a barsu su shige ne yake sanar masu cewa baban taron saukar alku'ani ta ɗaliban babar makarantar islamiyar garin, wace ta yi sunna ta kuma zaga garuruwa dan kwazonsu da kokarinsu a harkar adini

Baki ya tabe yana duban gimbiya yana fadin" Ki sauka ku karasa , ni zan je a yi da ni"


Itama bakin ta tabe ta kai dubanta daga gaba, inda Fadime ke zaune ta yi gyaran murya
8/13/22, 22:56 - Buhainat: *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍?*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*


🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻
*OUMOUGHLOUK ITIBEL*
_(ZAKIN SARAKAI)_
🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻

_FREE BOOK_

*Na*


*SAJIDA NIGER*



.
1️⃣2️⃣


Fadime ta fito tana sake kallon jama'ar zuciyarta na wani irin farin ciki ta bude mata motar sannan ta gyara mata alkyabarta ta amshi jakarta ta rike ta tsaya jiran ta fito

Murmushi ta yi ta kalli mijinta, cikin kissa ta ce" FADIME, da ace tana cikin matan da kake iya karrawa, da ka huta Uban gidana....., Matar nan akoy biyaya!"

Da sauri ya kalleta, sai kuma ya sake zubawa Fadime ido na dan takaitacen lokaci sannan ya dauke dubansa yana sake hade fuskarsa

Murmushi ta yi ta bude ta fita daga cikin motar sannan ta yi gaba Fadime na biye da ita a baya

Direct bangaren da ake sauke su ta nufa , domin karya ne walahi ba zata je ta gaisar da matar sarki ba!, Ita din banza ita din wofi, ba zata je ba!

Sunna shiga ta karasa tana cire alkyabarta ta yar a nan

Da sauri Fadime ta dauke ta karasa wajen makala kaya ta makala alkyabar, sannan ta dawo ta zauna daf da ita ta shiga cire mata safar kafarta sannan ta shiga dan mamatsa mata kafafuwan a hankali a hankali, har aka gabatar da kayan saukar baki


Kwanonin take kallo, kwanoni ne da ita bata san ina zata shiga ta samo irinsu ba dan itama a ringa mata anfani da su a bangarenta, yanzu haka tana kallon kishiyoyinta kowace rai bace tana son sannin ina mijinsu zai fita da ita, ama ya masu banza, ta yi murmushi tana girgiza kai, su a tunaninsu fitar gadara ce? Koda yake haka take so su yi ta tunani, watau fitar gadara ce ta soyaya ce

Kai ta maida wajen labulen dakin baki, to yaya na masu gidan zai kasance kennan? Ita bata taba shiga bangaren Sarki ba, a kulun tana hasashen yaya nasa bangaren yake kennan?

Sake mayar da dubanta ta yi kan FADIME, tana aikinta hankali kwonta, babu rawar jikin nan da son a birge irin na wasu ma'aikatan gidan nasu

Sake gyara zamanta ta yi da kyau tana ringesawa kadan a saman kujerar ta alfarma kasa kasa ta ce" Kin kasance mai biyaya a gareni Fadime, kin kuwa san na san da haka kuma ina gani?"

Da mamaki Fadime ta dan dago ta kalleta kadan, sai kuma ta sake sada kanta bata ce komai ba

Gimbiya ta cire daurin dan kwalinta tana sake lumshe ido dan barci zata yi a hakan tunda ta yiwu su kwana ko kuma idan sun taki Sa'a su ganshi a yau?, A hankali ta ce" Ban san yarinyarki ko tanada BIYAYA wa manyanta ba?"

Dan tsam Fadime ta yi gabanta na dukan uku uku, ba dai Gimbiya hasashen saka NADIRAH a layin bayin masarautar garin Tanut take ba? Ai kuwa da ta fadi ba nauyi, domin a wannan karron babu maganar biyaya wa manya, bata cikin wannan, ita ta saba da bautar, zata yi har lokacin da Allah ya cire mata, ama bata tunanin NADIRAH zata iya wannan aikin, sai dai ta yi abinda za'a iya gile kanta walahi!

Sunna nan a yannayinsu, sallah ke tashin Fadime, da zarar ta gama kuma zata dawo ta zauna tana jiran tashin Gimbiya daga barci, har aka yi sallar la'asar sannan aka bugo waya cewat ta shirya zasu samu gannin sarki nan da minti talatin

Ita dai Fadime na biye da ita har ta gama shiryawar , bata yi sallolin dake kanta ba tace idan ta fito zata yi sannan ta fito cikin shiga ta sabuwar alkyaba tana baza kamshi ana mata jagora har zuwa bangaren baban falo , falon amsar bakin cikin gida

Takalmanta ta cire a nan kofa, sannan ta shiga tana jin yadda ake sanar da ko wacece ita, sannan ta kai dubanta wajen mijinta dake zaune barin hagu din Sarki a saman kujera, barin damarsa kuwa UMMA ce zaune ta hakimce tana murmushin da ta tsana a rayuwa tana kallonta


Sake gyara alkyabarta ta yi ta idasa shigowa da kyau sannan ta tsaya, ta rage tsayinta sosai ta sada kanta ta shiga miko da gaisuwarta zuwa wajensa

Umma ta sake yin murmushi ta kalli ASADEEK, gannin ya gyada kansa a hankali sannan ya sake cire idannuwwansa a kanta ya sakata sasauta zamanta a hankali ta ce" Yin hakan ba laifi bane adalina, yin hakan ba ramuwa bane, idan har ka amshi hakan ka sani an daki tsuntsu biyu ne da jifa daya"

Dubansa ya sake kaiwa wajen Bafansa, hakan ya saka bafan nasa fuskantar matarsa ya ce" Ki karaso ki zauna, ki karra bada hakurin abinda ya zamto shirme wanda kika aikata, ki zo ki tabatar masa da bukatarki dan sake wanke kanki!"


Wani irin nauyi ya dake dane mata gaban kirjinta, lalle ya zama wajibi ta dauki mataki a kan du wani wanda ke wulakantatata, lalle shawarar da ta yankewa zuciyarta itace daidai da shi!, A hankali kuma wannan mata mai sunna UMMA sai ta kwakule mata idannuwa da hannayenta, bata san wanda ya rigayeka kwonci sai ya rigayeka tashi bane!

A kasa ta zauna, ta sake sada kanta, cikin tausasashiyar murya ta ce" Halaya ne irin na mata, shaci fade ne, domin banida tabas, ka yafema bakina da bashida tsaiko wajen yadda muguwar magana Allah ya taimakeka"

Kaffafuwansa ya dan murza daya a jikin daya masu dauke da farin safa karkar yana sake sauraronsu baki daya

A nutse, cikin fitar harufa a hankali ya dan dubeta ya ce" Ai ba muguwar magana bace, zan iya kiranta da gaskiya"

Kai ta karra sadawa tana mai neman afuwa, haka kuma mijinta da Umma na dake tayata neman afuwa

Murmushi ya yi, ya ringa kallon Mijinta da ita din kanta, a cen kasan zuciyarsa kuwa tunanin da yake yi shine, shin ko yarinyarsu ta san waye shi tun kafin ya fara sakata fadin abinda bata yi niyar ba? Idan haka ne me kennan?, Tabas shima yana so yarinyar ta kasance wata wace zai iya jin wani abu daga gareta a cikin tunanin dake damunsa a kan bafansa, sai dai yana cikin zulumin idan ya yi haka me ya yi kennan? Ya cutawa yarinyar fa? Me zai iya yi mata? Shi baya anfanar kowa, yana fama da lalura, wai menene a karkashin hadin nan nema? Ya kasa gasgata dan su wanke kansu suka dauke yarsu mace daya kwalin kwal zasu bashi, bayan sun san namiji yake a waje, daga cikin sai a hankali? Mutanen da son kansu yake a bayane ba a boye ba? Kai ya kasa gaskata wannan lamari kwata kwata

A nutsensa ya ce" Aunty?"

Watau gimbiya, dan haka ta dago tana dan kallonsa

Murmushi ya yi ya ce" Yaya zaki iya yin hadin nan bayan babu riba a cikinsa?"

Dan daburcewa ta so yi, kafin take daidaita kanta tana kallonsa ta ce" Naw aka zauna da namiji har aka mutu a wannan halin Allah ya karra maka lafiya?"

"A wannan zamanin da ido ke tsakiyar kai?" Ya fada shima tamkar ba shi ya yi furucin ba

Kai ta sake sadawa ta ce" Ka isa da mu ma, bale ita?"

Baki ya dan tabe yana dage kafadunsa ya ce" Hakane kuma"

Kallonsa Bafansa ya yi da sauri, kennan ya yarda y isa da su din?

ASADEEK ya sake kallon bafansa ya ce" Yaya magana ta hakinta kuma?"

Da iya layance abu Bafansa ya fuskanceshi ya ce" Na jima da nema ka bani dama na nemo maka magani, na tabata da tuni yan jikokina na yawo a gidan nan, ama a yanzu ina neman wannan alfarmar, ka bani dama na je na nemo maka magani, ba maganar shiga hakinta tunda muna neman magani, kuma na tabata Allah zai sakamu a hanyar da zamu samu Yarona"

Murmushi ya kuma yi mai dauke da ma'anoni da yawa, ya sake dubansa da kyau, ya kalli Umma, sai kuma ya kalli Gimbiya

Murmushi ya sake yi sannan ya mike tsaye a kan kaffafuwansa ya sake dubansu daya bayan daya

A hankali ya ce" Hakane kuma, Allah bai saukar da cuta ba, sai da ya saukar da maganinta......Bafa ka daura auren kawai..............., Allah ya tabatar da alkhairi"

Gaba dayansu ido suka zuba masa na mamaki, Bafansa ya yi gagawar tashi shima yana fadim" Kamar yaya na daura kawai ASADEEK? Aure ai abin a zauna a tatauna ne ko?, Kuma na ga aure mai daraja irin na yar uwarka ai ko sadaki sai mun girgiza mun girgiza sosai ko? Ga saka rana da sauransu?"

UMUGHLUK ya dakata ya juyo
Lalausan murmushi ya sauke masa ya ce" Ai yarda da na yi cewa, da kai da kaya duka malakar wuya ne ya sakani baka dama, sadaki kuwa ai dama kai kake biya min Bafana,"

"Ama......?" ......

A hankali ya dakatar da shi ta hanyar fadin" Auta nake son yiwa lesson kafin magariba ta shigo, tana falona zaune, Bafa du abinda ka yanke ka sanar min ta waya in sha Allah, a sauka lafiys"

Daga wannan ya shige ciki ya barsu da kallon kallo kowa da abinda ke masa kai komo a ransa

Babu wanda ya ce uffan sai bangarensu da suka nufa , shi a gaba Gimbiya a bayansa da Umma


Sunna shiga Gimbiya ta fara cire Alkyabarta ta kuma yarwa a nan, a mugun kufule ta ce" Me yake takama da shi a duniya?

Mijinta ya kai zaune yana dane nasa bacin ran sosai ya ce" Kudi, da karfin mulki!"

UMMA ta zubawa Fadime dake tsugune nesa da su kadan ido, kasa kasa ta ce" Ku iya bakinku, ku fitar da Baiwarku"

Gimbiya ta kai dubanta kan Fadime, sannan ta maido kan Umma , a sharar fagen abinda ta yi niya ta ce" Baiwa? Ai baiwama mutun ce, balle wannan tawar amintaciyata kennan, bana darr da magana a gabanta!"

Da mamaki Umma ta zarro ido tana kallonta, sai kuma ta juya wajen Fadime wace ita dinma mamakin ya nemi kasheta ta ce" Tashi ki bamu waje zamu yi magana"

Mikewa ta yi, sannan ta rage tsayi a nutse ta furta" Ku huta lafiya"

Daga nan ta fice
Tana ficewa Umma ta juyo wajen Gimbiya ta ce" Lalle gimbiya, baki san a bayi akoy masu baban burin dake iya rikidewa su zamto matsala a tafiyar gaba ba?"

Gimbiya ta dubeta da duba irin na ki kuyayeni fa ta ce" Nice kat, domin kema rikidafiyar baiwa ce ta dawo mafi kusanci da UMUGHLUK ITIFAL!, Bama wannan ba, kema da baki zauna a kan kujera kin dauki darasi a makaranta kika iya zagaye bale ni? Idan na yi kwai da zakarana!, Allah ya karra maka lafiya aban Bahija magana nake da ita!"

Dubansa ya maida sosai a kanta, Umma kuwa ta karasa ta zauna sokoki a kasan zuciyarta cike da tunanin wannan mata , tan kyautata zaton sai ta yi da gaske a kan lamarinta!

Sosai Umma ta lakanci mijinta da sannin wanene shi, shi yasa cikin ruwan sanyi take gasa kishiyoyinta ba tare da ta bari sun san cewa itama yakan zuba mata hauka irin nasa idan ta raya masa,

A tausashe ta ce" Lalle ban taba ji hankalina ya tashi, raina ya bace irin na yau ba, ace mu tashi mu zo har masarautar nan, da mu da sauran baki du daya!, Wai yana ba WA'INDA suka yi sauka kyauta shi ga musulmi ko?, Ya bamu damar ganninsa ama a raine a wulakance? Ace kai da kanka Sarkina kana zaune yaron nan na maka magana da gadara da wulalanci da raini?, Lalle abinda ya dace da shi shine wulakanci, ina mai tabatar maka wannan yaro baban wulakancin da ya dace da shi shine mu dauki baiwa mu aura masa a matsayin yarmu!, Walahi sarkina wannan ne kawai zamu yi mu rama wulakancin da ya yi mana, duda baya iya tsinanawa mace komai ama ya zamto mun saka a tarihin rayuwarsa cewa ya taba zama mijin kaskantaciyar baiwa an gama, kafin mu gama da shi kuma sai mun bada dama ya sani sannan ta gama mana da shi?"


Wani irin zuba mata ido suka yi su dukansu

Da sauri Umma ta ce" Ama Gimbiya kin cika neman fitinar da kanki ba zai iya dauka ba!, Kina nufin zamu yarda a aura auren UMUGHLUK ITIFAL da wata daban da ba yarki ba kuma ya kasa sani??"

Gimbiya ta dubeta a kausashe ta ce" kamar da kasa in ji mai ciwon ido, ni inada yarinyar da ta isa ta amsa sunnan matar sarki!, Kuma a yadda na hangi yannayinta tana iya yin kisa a kan yan kudade kalilan, in dai ba so kike a bar maganar kisansa ba sai ki sanar da sarkina na ji!"

" Ba haka nake nufi ba, yau babu wanda ya kaini son gannin ya kauce nima na samu cikaken yancin baza abinda bake yi a boye a rayuwata!, Sai dai ina yi ne ina yi mana hannunka mai sanda, domin muna iya kai duka dubu bamu same shi ba a kawowa guda ya tarwatsamu!, Magana muke yi da ASADEEK BRAHAM!, Kuma da kika ce baya iya tsinanawa mace komai kar ki manta, shi abinda yake tare da shi da sunnan wace yake aure a yanzu kadai aka aikata masa da nufin ya fadawa wata ko shima zai samu hukuncin da ubansa yake yankewa yayan mutane dan sun kwonta da wata dan ra'ayi!, Idan har za'a aura masa wata ai dole zamu je mu nemo matar da ta bamu na farko ta sake bamu da sunnan wace za'a hada , dan kar ki aikatawa kanki aikin mugunta da kanki, watau kina gannin kashi da rana, da dare ki zo ki taka!" Umma ta fadawa Gimbiya tana cire kanta a bangarenta, dan ta kula yadda take shayin gimbiya haka itama ke shayinta


Kafarsa dake kan cinyarsa yana karkadawa da sauri da sauri ya sauke kasa, wani irin Farin ciki da hasaso nasara da jin dadi a maganar nan cewa a hada UMUGHLUK ITIFAL da baiwa na sheke duniyarsa a farin ciki ya fuskanci matarsa ya ce" Wace baiwa ce wannan kike magana a kanta?"



Gimbiya ta saki murmushi tana fuskantarsa ta ce"












🤔🤔🤔🤔🤔🫢🫢🫢🫢🫢🫢🫢🫢🫢🫢🫢🫢🫢🫢🫢🫢🫢🫢🫢🫢🫢🫢🫢🫢🫢🫢🫢🫢🫢🫢🫢
8/13/22, 22:56 - Buhainat: *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍?*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*


🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻
*OUMOUGHLOUK ITIBEL*
_(ZAKIN SARAKAI)_
🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻

_FREE BOOK_

*Na*


*SAJIDA NIGER*





1️⃣3️⃣



Gimbiya ta saki murmushi tana kallonsa, hum maza kennan, watau yadda ta lakanci bawan Allahn nan gaskiya zata iya cewa babu wanda ya sanshi irinta, ko haulan fada yake yi ta san me yake isarwa a sakonsa......, Kofa yake a da soyaya suka yi har ta kazance din nan, sun yiwa junna so irin makahon nan
Tana murmushin ta sake aro wata kalma dan sake buga zuciyarsa, a matsayinta na mace, tana cike da kishin kalmar, ama a haka ta riketa a matsayin makami dan ta kashe fitinar dake neman kunno mara kai na samun mugun sabani tsakanin mijinta da cilon y'arta mace, itafa mazan basa wani gabanta, ta sani ne sarauta tata ce zuwa gaba domin kuwa mazan manya kaf nata ne, shi yasa take tatala auta dan itama ta samu wajen da ya dace da ita, ta tabata abinda ya ruda zuciyar autarta ba karamin abu bane, ya cencenci jarida!

A tausashe ta ce" JINNIN FADIME CE!"

Idannuwansa a kan lebenta , tunda ta ambaci sunnan dake girgiza tunaninsa da rayuwarsa baki daya tsayin shekara da shekaru

Har wata zufa zufa ta nemi karyo masa a cikin kirjinsa, ya dan kawar da dubansa sannan ya sake kallonta a lokacin da ta yi kalar serius tana fadin" mun jima da rikon Fadime a hannunmu, mun san wacece ita!, A maganar halayanta mun dameta mun shanye mun san mecece ita, a maganar kyau kuwa da kira ko a yanzu da Fadime ta haura shekaru suka fara zuwar mata ai inaga ba boyayan sirri bane cewa kyakyawa ce akoy diri......., Ina mai tabatar maka yarinyarta ta girgije ta fi uwar komai, tsayi ne bai kai cencen ba, ama tsayinta daidai misali ne, ita ta dace da shi ba yarka mai daraja ba!"

Naman gaban goshinsa shi kadai ke harhadewa yana kallon matarsa yana sake jimke hannunsa dan daidaita yannayinsa da tunanin abinda ya zamto abin hangensa daga nesa
Me? Tana nufin y'ar matar Bafadensa ta fi uwarta haduwa? Lalle idan hakane kamaninta sun isa , sai dai nasabarta! Idan kuwa ya iya boye maganar wanda ya ba UMUGHLUK ITIFAL har ya auri baiwa ya rama kaskantar da shi da yaron ke yi ,
Wani murmushi ne ya kwace masa, murmushin da ya saka ginbiya sake sakin ajiyar zuciya boyayiya dan samun nutsuwar da ta gaza samu tun jiya, a hankali ta mike ta shige ciki dan shiga bayi kafin su kama hanya, domin wani abu ya rike mata kirji sai ta kakaro shi ko zata ji sanyi sanyi kar ta kumbura a hanya

Tana shiga Umma ta dubeshi da duba irin waanda idan bakinta da kumsashiyar magana sai ta yita take jin sauki ta ce" Wani irin yarda ka yiwa uwar wace kake son hada wannan abin da ita?"

Sarki ya gyara zamansa yana dage kafadunsa ya ce" Ba maganar yarfa bace, su din bayina ne"

"Ka kiyayi lamarin bayi, karamar allura na iya zamewa galma" ta fada tana sake fuskantarsa

Murmushi ya yi yana kada kai ya ce" Ki gane, ba zamu tarbi aradu da kai ba tare da mun yi tunanin abinda ya dace ba, basu da zabi a maganar, haka kuma yarinyar bata da zabi a hukuncin da zamu yanke!"


Kai ya gyada tana jira, har Gimbiya ta fito suka mimike zasu tafi

Rakiya ta masu har bakin mota, a nan ta ga wannan karron Sarki ya ba matarsa umarnin su shiga baya tare da Fadime dan ta yi mata maganar tun a kan hanya, shi fa a yanzu yake da bukatar a yi a gama da wannan yaron ko fili zai zamto nasa!

A lokacin da Gimbiya zata shige Umma ta yi saurin rike hannunta tana kallonta ta ce" Ki tabata da zabinki, ki daki maganarki da karfi, domin idan baki nuna a kan haka kowa na iya rasa ransa ba zaki ga shirme, ki kula, domin bana cikin lalatacen wasa!"

Hannunta ta

Please Login or Register in order to submit comment