Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*


🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻
*OUMOUGHLOUK ITIBEL*
_(ZAKIN SARAKAI)_
🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻

_FREE BOOK_

*Na*


*SAJIDA NIGER*





6️⃣4️⃣



Muryarta a raunane, kanta na kallon kasa sosai ta ce" Abah, sai bayan an mayar da ni gida, an sake dawo da ni na fahimci maganin ba na taimakona bane, na kwaya ne, daga baya ita da kanta ta sheda min hakan"

Idannuwansa ya rintse, lokaci daya kuma ya bude a dan zafafe ya ce" Ta shaida maki haka? Kuma kika yi shiru baki ce min komai ba?, Bayanshi me da me take yi maki? Idan tana nuna maki soyayya a gabana du ba haka bane a bayan idannuwana ko?, A kan me zaki boye min? Me yasa?"

Dan matsawa ta yi, dan irin yadda yake maganar a zafafe har ya fara dan daga murya, alamu na ransa a kololuwar bace yake ya bayana a tatare da shi

Hankali tashe ta duka kasa kanta a kasa, hannayenta a jimke tana girgiza kai kuka na fitowa daga bakinta ta ce" Abah, ta yaya zan sanar maka cewa , Matar da Mahaifiyarmu ta yi mana nuni da mu kirayeta UMMA dan ta isa ba dan mun hada dangi da ita ba sai dan tsabar yarda da kaunar da take tsakaninta da mu baki daya cewa ta rikide ta koma aljana a gabana, tana zalintata , ta tsoratar da ni da kalamai masu muni a ranar da ta nuna min zata so aikata sabo mafi muni da ni, sabon da take aikatawa da wasu matan, na bijire na nuna ta rufa min asiri ko me take so na zama zan zama in dai zata rabani da wannan maganar, ta ju haushina a kan haka, ta kara kaimin yaki da ni da farin cikina, ta hanyar nunawa duniya mahaukaciya na zama sakamakon mutuwar mahaifana dan ina jahila wace bata da tawakali?, Take muzanta min ba dare ba rana , ta sakani zamtowa mahaukaciyar domin tsananin tsoronta da nake ji ya da ko maganarta aka dauko nake rikicewa, bayan ba za'a iya yin hira ba maganarta ba a cikin gidanmu, a cikin fada ana mutuntata dan ana mata kallon Uwa a garemu, a gabanka kana mutuntata dan kana yi mata kallon Uwa a wajenmu, Abah a yadda take da tasiri a rayuwarka ta yaya zan maka da maganar nan ka gane me nake nufi, bayan a cikin tsoratarwarta ta min nuni cewa idan har na yarda na sanar maka maganar nan ta yi alkawarin zata dora min shari mafi muni a rayuwa, sharin da kai da kanka zaka jefeni a matsayina na matar aure idan na aikata domin kana zartar da hukunci ne bisa koyarwar adinin musulunci, sannan ka dawo bakin ciki ya kasheka?, Wannan matar ce zan iya kokowa da ita Abahnah........."

Da zafin rai, har hannayensa na bari ya katseta ta hanyar tafka mata tsawar da ta saka su dake ciki kamewa waje daya sunna kallon junna

Muryarsa da fada fada ya ce" Kina nufin a cikin kazantaciyar rayuwar da take yi har ke ta so yi da ke? Kina nufin tsoratarwar da ta yi maki harda ta zata iya yi maki sharin Madigo?"

Auta da ta hade kanta da gwuiwoyinta tana sheka kuka hankalinta tashe ta gaza furta koda A ne, domin zata iya rantsewa rabonta da ta ga bacin ransa haka tunda aka ce masa ta haukace, zai kwaso bacin ransa sosai ama fa zai yi kokarin boyewa a gabanta dan bata iya jurewa yanzu ne zata rikice masa da koke koke, sai gashi yau ya rikide mata tamkar ba shi ba , tamkar wanda zai iya zaneta idan ta yi wasa, sai hankalinta ya yi kololuwar tashi ta rasa yaya zata yi masa

Zuciyarsa da ciwo, hankalinsa tashe, kirjinsa na tafarfasa yake kallonta, har Inna Hindu ta gaza jurewa dan ta gama fahimtar Auta kuma ta tsorata fa ba zata iya kare kanta ba, bayan yau din rana ce da ya dace ta kare kan nata, a dole ta fito da zumbulelen hijabinta har yana jan kasa domin Hijabin NADIRAH ne ta dauka dan a dakin Nadirar suke

Tana zuwa jiki a sabule ta duka daf da Auta, hannayenta ta saka ta dago Auta ta rungumota jikinta , sannan ta sada kanta sosai, muryarta ba nauyi, a sanyaye sosai , kanta a kasa ta ce" Allah ya huci zuciyarka, ka yi hakuri ka yafe mata, ka gafarta mata ka yi mata uzuri, dole sai a hankali koda zata dawo yadfa kake so, ka tuna fa babu abinda ke saurin zama gaske irin yin abu da gangan, ko ciwo ka dorawa kanka da gangan yana iya rikide maka ya zama gaske, , Matar nan ta fi kowa kusanci da ita, rana tsaka ta wayi gari take haduwa da ainahin fuskarta, ta kuma fi kowa sannin ta inda zata biyo ta daureta gaba da baya, Auta kuma yarinya ce, a duniyarta kuwa ku hudu kawai ta sani, sai mijinta da yake bako a gareta, da wahala ta iya gane rayuwa ko ta gane cewar idan ta sanar maka kana da girma da hankalin da ba zaka tashi ka warware maganar kai tsaye ta yadda matar nan zata fahimta har ta yi mata sharin ba, ba zata iya gane cewar Allah ya azurtaka da ilimi irin na sarakuna, wanda yake banban da wasu kwakwaluwar, a dole idan abu ne aka fada maka zaka saurara ne na farko, zaka kuma yi duba irin naka ba wai na mai fadin ba, ka yafewa kanwarka domin a dole ta tsorata da makircin matar cen, idan kuwa ta kula ka jefe AUTA lalle kai kuma zuciyarka zata buga, kennan an bar talakawa a hannun su wa?, A irin wulakantar da Auta da ta yi sai da ta rabata da kowa, babu kawaye bale miji ko danginsa, uwa uba ta fitar da fuskarta a matsayin mahaukaciya, dan Allah ka fuskanci baiwar Allahn nan da ta zubar da komai ta hakura take yaki dan gannin ka take makiya, take kaiwa Allah kukanta ba dare ba rana har yanzu adu'arta ta karbu ta ga wannan ranar itama da ranta da lafiyarta, Ka yi hakuri dan Allah na shigo hurumin da ba nawa ba, ba dan na isa ba, ba kuma dab matsayina ya kai ba, ......ama Auta a nan muke zaune da ita, ta bude bakinta ta sanar min abubuwa da yawa wa'inda suka sakani kuka du irin kwamacala tamu ta kauye sai da lamarin rayuwarta ya gigitani...........idan a yau ka kasa fahimtarta ka karra rufeta ne a cikin hali na kaka naka yi, bayan kaine ABAHNTA......" Inna aka kare hawaye na bin kumata, sannan ta mike jiki ba karfi ta karra neman afuwarsa ta fice gaba daya a falon dan ji take yi idan ta zauna tana iya rushewa da kukan da za'a dawo bata hakurin itama, gwara ta he cen wajen bayi ta karra cakudewa da su ta yadda zata idasa nununa munafukan cikinsu wa y'arta saboda rayuwa ta yau da gobe da ta kama y'ar tata a gidan, dan kuwa babu gidan ubanda INDI zata je da cikin dan masu gida, ai it yanzu kuma tashin hankali ya kau, Auntynta da rai tana hannu mai kyau, sai shagali yanzu zata sake fuskantar karamar arniyar cen


Sosai jikinsa ya karra yin sanyi, hankalinsa kuma ya karra tashi
A birkice ya dawo kasa inda Auta ke dukunkunne bata daina kukanta ba, haka da Inna zata fita yana gannin yadda ta yi kamar zata bita, kennan tsoronsa ta ji da ya yi mata ihu? Shi kuwa ya yi ne a rashin control din kansa, a ganninsa ta yi wasa da shi ta yadda take tunanin zata kawo magana mai girma irin wannan ya wani banzatar da ita ta zauna shekara da shekaru tana shan wahalar arniya banza da wofi!

A hankali ya dagota ya matsota gefensa kamar yadda yake yi mata a dama idan tana hali na rikicewa,
A sanyaye yake taping din bayanta yana dan riko hannunta dake jimke a cikin nasa

Muryarsa a raunane, hankalinsa du a tashe ya ce" Ki yi shiru haka Uman Abahnmu, haba Mariya mai baban daki, haba matar Lamido , dubi nan, dubi ban fa yi fushi ba dan wanu abu sai dan jin ciwo a zuciyata, Auta ina gefenki, ina tare da ke ba dare ba rana ina fita da isa da takama na je garin wanda na ga dama na kwato yancin wanda aka cutar na dawo kasata na kuma ja layi na tsaya na zartar da hukunci a zauna lafiya ama na gaza gannin hali na ukuba da aka saka min kanwata?...........kin san me haka ke nufi a wajena?, Auta na yi karatun rayuwa tunda na hau karagar mulki, abinda yake karkashin tunanina ni da kaina na san wani lamari ne na ubangiji, mutun kuwa na yi masa karatun da yake da nisan gaske, na riga na san cewa babu abinda ke gagawar juyar da kwakwaluwar dan Adam irin abu ukun nan *ARZIKI, MULKI, MACE*, a kansu dan Adam na iya mance kansa da asalinsa, a kan neman duniya da abinda yake cikinta dan Adam na iya mantawa ba matabaciya bace ya saki jiki ya yi ta tafka lamuransa sai a cikin bulala ukun nan daya ta riske shi sai kuma a dawo ana dana sani ko a rikice a bar dabi'u na alkhairi a koma kwashe kwashe watau *RASHIN LAFIYA, TSUFA, MUTUWA*, wa'inda basa yiwa kowa uzuri ko su baka dana ka sake gwada wani tashin daban da wanda ka yi..................................."
Ya ajiye maganar yana jan numfashi, dan ya zame masa jiki idan dai ya yi doguwar magana irin haka yakan ji ya gaji ne tikis kamar wanda ya yi wani aiki , sai yana yi yana ajiyewa ko zai iya karasa yawan maganar

A hankali ya sake budar bakinsa ya ce" Tabas mun bata yarda, ta ci amana, a lamarinta yanzu abu daya ne ke cikin duhu a zuciyata shine rasuwar mahaifiyata, me ya hadasa kumburin cikin ANNA kai tsaye? Harta a likafaninta cikinta a tashe yake sosai wanda na jima a cikin tunanin nan, da kuma bakin jinnin da ya fita ta hancinta..............Shin matar nan ta kai wajen da ta kashe min uwata Auta?"


Dummmm gaban Auta ya yanke ya fadi, zuciyarta ta shiga yi mata zafi domin tunano kamawar da ta yiwa Umma da irin rikicewar da ta yi kafin kuma ta ga ta sauke ajiyar zuciya a lokacin da ta ji jan numfashin Mai dakin Mai martaba na karshe, jan numfashi da ya yi wani irin tsayi ya fita bai kuma dawowa ba, kukansa a kunnenta da irin ajiyar zuciyar da ta ga UMMA ta sauke alamu na kwonciyar hankali ya wadata fuskarta, ama kuma sai ta kamata ta kaita dakinta ta rufo ta fada mata mamanta ta mutu , bayan tana cikin kukan wai mahaifinta ya rasu.............ta barota a ciki, ita daya kwal da ranta , ta yi kuka har nunfashi ya yiwa kofar hancinta kadan ta summe, wanda sai a washe gari aka ringa nemanta hankalin ASADEEK din a tashe kamar zai summa dan tashin hankali da kyar aka ganota a dakin nata summe.......

A harhade ta sanar masa komai , dukkan abinda ta sani, irin abinda ta gani a fuskar UMMAN har rufewar da akai mata Umma ce ta rufeta a daki

Ya jima idannuwansa lumshe, gaba daya ji yake yi me kuma ya rage masa na jin dadi a duniyar nan? Gaba daya ji yake yi sarauta bata yi masa rana ba , ji yake yi da ace su ba kowa bane da ba'a rabe su dan a cutar da su ba, saima yake ta kokonton anya zai iya sake yarda wani ya masa shigar da Umma ta yi masa a zuciya ta cutar? Wani tarin takaici gefe daya kuma yake mintsininsa, wannan maganar idan har haka ce dole zai ji ciwo a zuciyarsa mai tsanani, domin ya so ne ta rayu a cikin gidan kaso ta yadda zata yi doguwar rayuwa tana kallon abinda zai yi ta nukurkusarta, idan kuwa harda maganar kisa a ciki ai dole za'a kasheta itama, sai dai kashetan nan walahi walahi ba zai
aikata da wuri ba, bi'izinillah sai ta yi rayuwar gidan kaso koda ta shekara biyu ne tare da fargabar yau ko gobe, da rikicin tunanin kwonciyar kabari da irin abinda ta aikata, sai ya sakata daki mafi muni da duhu ta yadda zata ringa auna a duniyar kennan ina ga lahira da nauyi irin nata? Sai ya wakilta malamai irin masu zafin wa'azin nan sun ringa zuwa du safiya ta Allah sun yi wa'azi a kan mutuwa da girman laifin wanda ya cutar da bawan Allah da irin azabar dake cikin wuta, uwa uba hanyoyin da za'a tarar kafin a kai tsayuwar hisabin, bi izinillah sai ya bata damar dandanar ukubarta daidai misali, ta yadda zata zamo mahaukaciya ta gasken gaske ba wai ta karya da hade haden magani ba, sannan zai zartar mata da hukuncinta ta hanyar bawa du mai iya ganni damar zuwa dan hakan ya zamo babar bulala wa mai rabon dacewa da shiriya tun kafin lokaci ya kure masa

Daga hakanan kuma ya kasa furta komai sai idannuwansa da yake kawarwa baya so Auta ta kalla du irin yadda take son kallon dan kamalta abin a zuciyarta ta san yana cikin wani hali mai wutar fasara,

"ABAH" Auta ta fada a sanyaye tana kallonsa

Da kyar ya iya daga idannuwan nasa yana kallonta

Auta ta lumshe idannuwanta cike da jin tausayinsa a zuciyarta, ita ta fi tausaya masa fiye da nata, dan shi ya zame masa dole ya dauka ya kuma shanye, ya dauki damuwarsa ya kuma dauki ta talakawansa
Murmushi ta dora a saman lebenta, a hankali ta ce" Abahna, Aunty NADIRAH....... Au, Momy NADIRAH fa tana da ciki, Abahna zamu samu baby muma ABAHNA....." Ta karashe tana kallon yannayinsa a lokacin da ya zarro manyan idannuwansa yana kallonta, kamarma bai yarda ba, kamar kuma abu ya shigo maka kai tsaye, dama burinta kennan abin ya shigo masa kai tsaye , cikin tarin duhun da yake gani haske ya ratso alfarmar annabi da Alkur'ani.............

Muryarsa a cen ciki ya iya sake budar bakinsa da kyar yana kallonta idannuwansa a wajen nan ya ce" Me kika ce?"


Auta ta sake maimaitawa, yanzun har yar dariya take yi tana share hawayenta hadi da jan hanci

Jikinsa ba karfi , ama kuma yannayinsa na cenza salo ya dan rangwabar da kansa aa sanyaye ya ce" kuma tsokanar da zaki yi min kennan Auta?............"

Daria Auta ta saka mai dan sauti kadan, ta ce"












Hello people, morning all
10/14/22, 21:24 - Buhainat: *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍?*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*


🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻
*OUMOUGHLOUK ITIBEL*
_(ZAKIN SARAKAI)_
🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻

_FREE BOOK_

*Na*


*SAJIDA NIGER*





6️⃣5️⃣





Ina kuke MATA, MATA masu ji da kansu,MATA masu aji, WA'INDA suka san girma da darajar gyara, WA'INDA suke iya cire kudade masu yawa dan gyaran kansu? Ku garzayo ku tuntubemu, ama ku tabatar jakarku ta cika taf, domin bamu da lalan kaya bamu da na kudi kadan, kayanmu gyara ne hajia magani ne na mata mai mayar da busashe tamkar teku..........ku tumtubemu ta wannan numbar *80229915* MAIMUNA MATAR ABDULAHI..... Sai kun zo




Daria Auta ta saka mai dan sauti tana kallon irin yadda yayanta ya yi kamar wani bakin marayan dake jin yinwa ta ce" Abah, ana wasa da irin maganar nan mai daraja da girma?, Ama fa ba likita ne ya fada mana ba, Mamah ce ta sanar mana, Aba ka san datijai sunna ganewa ko yau ka tashi da ciki sunna iya fahimta , a shekaran jiya n....................................................."

Sauran maganar ne ta hadiye tana zarro ido hadi da binsa da kallo, domin kafin kace meye wannan ya mike daga zaunen da yake ya durfafi dakin da Nadirah ke ciki

Bai tsaya tsaye tsaye ko jin kunya ba ya kama ya bude ya shige cikin dakin, hakan ya saka Auta sakin murmushi ta mike ta fice da wayar wajen Inna HINDU ta janyo kofar ta rufe da ky ta shiga tafiya a nutse da wayar tana neman layin wanda take mararin jin muryar mai shi


_________________________________

Karar bude kofar ta ji, tana tsaye gaban madubi daure da tawul, wanka take shirye shiryen shiga dan kuwa tun na asuba da ta yi kafin ta daura alwallah dan jikinta ya saku sai yanzu da zata yi wani, tana kallon mamanta da ya kumburo, bama irin kansa da ya yi mata wani iri ta yi saurin daura tawul din tana hade goshi a zuciyarta tana ta tunanin shin zata sanarwa Innarta abinda nononta yake yi ko zata yi shiru da bakinta ne? Idannuwanta suka sauka a saman fuskarsa

Irin kallon da yake binta da shi ko makauniya ce ita dole zai samu effet a jikinta
Da sauri ta dauke idannuwanta ta juya ta shiga rarumar abinda zata rufe jikinta gaba daya , kaffafuwanta da hannayenya sai bari suke tamkar mazari

A hankali ya sake lumshe idannuwansa ya ciro bayansa daga jikin garun da ya jingina ya ringa takowa zuciyarsa na bugawa har ya karaso inda take tsaye jikinta na mugun rawa ya rungumeta ta baya a hankali ya dora kansa a saman wuyanta lokaci daya kuma ya kama hannayenta da nasa, yana sake lumshe idannuwansa yana fitar da huci daga zuciyarsa ta bakinsa mai dumi a dokin wuyanta, muryarsa a sanyaye ainun, sannan a cen ciki ciki ya ce" Dan Allah, ki sasauta min haka mana Tarhanine?......"

A hankali ta ringa daidaita kokowar da take ta son yi da shi, zuciyarta na dokawa da masifar karfi, kanshin jikinsa na ratsa dukkan wata kofa ta hancinta, bakinta, kofofin jikinta sunna wanzar mata da muguwar kasala da mutuwar jiki ta karra lumshe idannuwanta tana cije jinjirin lebenta tana jin zafafar zufa mmai dumi na sauka daga gaban goshinta tana zuwa jikinta

A sanyaye, muryarsa na matukar son halakata ya sake riketa a jikinsa a hankali ya ci gaba da fadin" ki tausaya min haka dan ALLAH, kin ga ni marayaa ne gaba da baya, wace ta rikeni ta wulakantani......, Kin san a yau ji nake kamar zan mutu?, Zuciyata ciwo take min Indinah...., Zafi nake ji sosai momyn Autah.........." Ya karashe yana sake riketa a kirjinsa

A hankali ta ringa son juyowa har ya fahimta daga riketan da ya yi ya dan sasauta mata ta yadda ta juyo idannuwanta lumshe sunna zubar da ruwan da baya san ko na meye ba
Kanta ta dora a saman kirjinsa ta danna da dab karfi tana jin irin yadda kirjinta ke bugawa, ta rasa a wani mataki zata ajiye abinda ke son girmamar tunaninta

Muryarta a raunane ainun, cen cikin da bata yi tunanin zai iya jiyota ba, bayan ta dora kaffafuwanta a saman nasa hankali kwonce, muryar cen ciki ta ce" Aban Datawa, kai kuwa mai zai raunana maka zuciya har ya saka ka bugun zuciya haka?"

Subahanalah, watau ko a ina tuzuruwar kauye ta koyo salon nan ta koyo shi daidai da zamani, idan da gangan ta yi zai iya cewa Allah ya karro rashin ji, idan kuwa a rashin sani ta yi haka take tabara a jinnin jikinta ne zai iya cewa Allah ya karawa mata daraja duniya da kiyama
, Sai ya ringa jin kamar ya fashe mata da kuka wollah, kamar itace babar shine karamin, bale da ta zagaya hannunta daya ta rungume bayansa da shi, sai ya ji shi a yau baya jin wani dar a kan tuzuruwar kauye

A sanyaye ya furta" Waye ni, da ba zan ji tsoro da abinda zai iya mugun tsoratar da ni bs?"

"Kaine fa , UMUGHLUK ITIBEL, kaine jiran Maza, kaine Aban su Innata........" Ta fada a sanyaye bayan ta dago rinanun idannuwanta tana kallonsa

Hawayen dake saman kumatunta yake ta kallo, a hankali ya ce" Nine kuma bakon INDIH, nine wanda indi ta ki duba, nine mai bara da kokona a gabaan Indi, NADIRAH zuciyana na dokawa ne idan na kalle ki na shiga halin tsaka mai wuya a tunanin kar aje har yanzu kina kwana da wanina a zuciyarki............" Ya karashe yana fadin wani da wani yannayi na jin daci, wanda kiri kiri ta fahimci hakan

Idannuwanta ta mayar ta lumshe, a ranta ta shiga ayanno kalmar wani, da kuma wannan dake gabanta,
A dama fa, tunda ta ga ASADEEK ba rawani, sai da ta ce dole zata kiyaye yawan matse masa waje da kallo dan kar Aminu ya dawo yi nata muni a idannuwanta, sai kawai Aban datawa ya tube a gabanta malan...., Ba fa zata manta ranar da aka yi tsere a kauye ba, samarin kauye suka cire rigunnansu dan a yi gudu a sake jama'a, kowace budurwa ta je gaba tana doka yar gangarta dan ta karrawa gwarzonta kwarin gwuiwa, ana sako samarin nan suka bazo a waje jama'a yar dubu ta karewa Aminu kallo tace Ke indi duba ku ga Aminu kamar dan yayen kaka, tana kallon Aminu ta hango wuyan da kan sunna rangaji na gudu, dan cikin nan nasa ya yi dan tumbin kunnu gefe daya, Aminu gudu yake kansa da kafarsa yana jan wandonsa, a dole ta kawar da kai domin har ga Allah yar dubu ta cuceta, ta jims tana nazarin zululu wuya uwa marikin lemar da ta ringa hangowa, a dole da Kato ya cire riga ta baza ido tana kallon ikon Allah, Aban datawa kam ba dai kirji ba, harda wasu gida gida a cikinsa, ko baua shan koko ne shi?

Hannunsa dake ta yawo a saman cikinta, irin shafawar da yake yi da son cusawa samn cikinta ya sakata tuna abinda aka ce, wai tana da ciki, sai ta karra jin wata kunya na son lulubeta wollah, idan labari ya fita cewar ta samu abin nan da sai an yi abin nan ake samu yaya zata kalli jama'a, jama'a su kalleta?

A hankali take dan ture hannun nasa, hakan ya saka shi sakw tsureta da kallo zuciyarsa na dan bugawa a hankali

Muryarsa a sanyaye ya ce" Ba dai zaki daina tureni ba ko?, Wai meye tuzurun kauyen ya fi ni da shi?"

Kai jama'a, sai da ta zabura, Aminun ne tuzuru? Wannan ai kalmar aban birni ce, ba shiri murmushi ya subuce a saman fuskarta, ta sada kanta kasa kasa ta ce" Ka takurawa tuzurun kauye , bayan kaima mijin HUZNAH ne"
Murmushin ne shima ya sake kwonciya a saman fuskarsa, ya salam, da gaske kennan itama tana jin haushin matarsa dan tana kishinta, wannan dadi da yaya zai kamanta shi? Jinsa yake a cikin zuciyarsa har cen kasa kasa

Gabansa na dari dari ya fitar da abinda ya fi saka shi bugawar zuciya, a sanyaye ya ce" Wai kina da ciki?"

Dum ta ji gabanta ya fadi, da sauri ta rufe idannuwanta tana son janye jikinta daga nasa da kuma harhade fuskarta hankalinta na dan nuna alamun tashi

Sakinta ya yi ya zuba mata ido yana kallonta har ta karasa wajen gadon ta zauna ya saka Hannayenta ta dafe kanta da su tana kallon kasa

Sosai hankalinsa ya nemi tashi,
Juyawa ya yi yana dafe gaban goshinsa dan kansa ne ya sara masa
Lokaci daya ya yankewa réaction dinta hukuncin hakan na nufin bata son cikinsa ne?, Cikin da ya tabata kowa yake jira? Cikin da za'a fitar da maganarsa yau garin AGADAZ da kewaye sai an wuni ana bikin samunsa? Cikin da kowace mace marar aure wace take cikin hurumin malakarsa zata so ace a cikinta ya samu?
Hankalinsa a matukar tashe ya karaso gabanta, yana tsayen nan , muryarsa a tausashe ainun ya ce" Zaki mike, mu tafi wajen likita ya aunaa ki, idan kina fauke da cikina daga bakin wannan lokacin zaki dawo rayuwa daf da ni, ba zan iya raba daki da ke ba sai idan ranar yar uwarki ne, a bangarena inada dakunna sun ishemu daga ke da ita da ni kowa ya kama dakinsa,......."
Gaban goshinsa ya karra rikewa dan gaba daya abin ke son saka

Please Login or Register in order to submit comment