Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nan kuma Auta ? C'est très simple hein?, Ki cewa mamanki kina sin zama tare da auntynki ba sai ki je ki zauna ba? Duka dai ai cikin gidan guda ne ko? Maganin kuma a ko'ina ana iya baki shi ki sha, wai inama magungunnanki na tabata baki sha na kwana biyun ba, oya tashi ki je ki dauko min maza share hawayen dauko min su dukansu"

Kai ta gyada tana dan share hawayen nata sannan ta mike jiki ba karfi ta bi ta hanyar nan ta cikin falonsa

Umma ce ta daga kafa da nufin bin bayanta ta ci kaniyarta kamar yadda ta saba, hakan ya saka NADIRAH mikewa tsaye , sai dai idon da ta ga ya zuba mata da alamun da ya yi mata kan ta koma ta zauna ya sakata zaunawa tana jin hankalinta na neman tashi da lamarin, ta sani sarai Auta ta riga ta tsorata da matar nan sai gyaran Allah kawai

A hankali ta dago ta dube shi, muryarta ba karfi ta ce" Abahnta, ta yaya yarinya ta nuna maka bata so zaka nemi tirsasata ne?"

Idannuwansa dake kanta ya sake zuba mata har yana wani dan kashe girmansu irin ita din dai yake kallo

HUZNAH ta kalleta da mamakin karfin halinta da iya shegenta, kai ta girgiza ta ci gaba da jiran nata maganar, dan ta san ba gamawa ya yi da ita ba, ita kam zata je ta ringa fadawa Allah a kan lamarin yarinyar nan, idan tana wani abin har tsoro take bata

NADIRAH ta karra dagowa ta dube shi,yanzu fuskarta ta fara hadewa sosai daga yannayin sakewar nan

Ido cikin ido ta ce " ina son tarda ita"

"Me ya sa?" Ya fada a tausashe yana sake kallon réaction dinta

Matarsa ta kalla, sai kuma ta kalle shi, a taysashen itama ta ce" kawai ina son zuwa kusa da ita!"

Hanyar ya kalla shima, sai kuma ya yi dan murmushi bai bata damar tashi ba, hasalima a hankali ya ce" zan so na dan ringa samun lokacin da zaku ringa kasancewa tare, gashi kun nuna bakwa son lokacin cin abinci, shin wani lokaci ne zamu ware?"

HUZNAH ta sake jingine bayanta a jikin kujerar nan tana jin du abin wani ba wai, kai kishiya? Kishiya ko ta kara ce gaskiya tana da daukan hankali, shekararsu nawa a cikin tsarin nan ba'a taba magana a kansa ba sai ita isashiya ta nuna bai mata ba, da acema mijin nasu na ratsa tantanin halitarsu ne da sai tace dole ai an riga an san dadin abin, to ama babu wannan ita me take yiwa neman fitinar?

Shi kuma a zaunen da yake wani irin abu kai kama da kishadi yake ji idan ya kalli fuskar HUZNAH yadda ta cikota, sannan ya kalli ta NADIRAH yadda ita kadai ke harare harare abinta tana kada kafarta ta dama, hankalinta gaba daya ya yi wajen da su UMMA suka shiga

Dan murmushi ya yi, watau abinda take yi du da dalili ko?

Zai sake yin magana Auta ta fara shigowa, Expression din fuskarta kadai ya kalla ya ji yannayin nishafi nishadin da yake ciki na neman gagararsa, hakan ya saka shi dauke dubansa a kanta yana mai ambaton Allah har ta dawo ta zauna a nesa da NADIRAR da kuma Shi Aban nata, hakan ya saka NADIRAH lumshe nata idannuwan tana dannar zuciyarta da tambayar kanta anya zata iya ci gaba da jure wannan cin zali irin na UMMA?

Ummar ce ta shigo itama, fuskarta a washe yanzu, watau ta nanagawa Auta abinda ta ga dama ta huce ko? Ta dawo ta zauna tana sake kallon NADIRAH, irin abinda suka yi da Nadirar jiya zuwa yau tana son ganewa wai a cikin tsare tsaren ne ko menene? Ta ga ai a lokacin baya nan, kuma ta sanar mata baya nan komai tana iya yi a bayan idannuwansa ama sai ta ga sam bata saurareta ba

A kausashe ya ce" Ku tashi ku tafi, zan neme ku, banda UMMA"

Su ukkun suka mike, sai ya ga kowace na neman daukan hanyarta daban

Watau harda AUTA da NADIRAH

A cikin sasaukan Furuci ya ce" AUTA, ki bi Maman naki kin ji?"

Da Auta da NADIRAH suka juyo sunna kallon fuskarsa, duda sun so fahimtar me yake nufi ama basu yi gagawar yarda da haka din bane, sai da ya masu alamu da idannuwansa sannan ya ga ikon Allah murmushin da ya fadada fuskar NADIRAH, murmushi irin na jin dadi sannan ta kama hannun Auta suka wuce da dan saurinsu

Dubansa ya maido Kan UMMA wace harda zarro ido ta yi dan mamaki tana kallonsa

Murmushi ya yi a tausashe ya ce" UMANA, ki yi hakuri da su dan Allah, kin san jiya tafiya muka yi cen garin gabas wajen gonakina, ana yin barna a ciki ne kuma ana neman a tayar da fada tsakanin manomana da makiyayan yankin, kin san makiyayi da abin kiwonsa, to fa shine muka je abu karami ya zamo baba domin a dole muka zauna aka yi ta rabiyar rikicin, da na dawo tuni dare ya yi sai muka zauna a masalaci muka gabagar da sallah sannan na shigo, Inaga lamarin AUTA dole zan fitar da ita, abin nata yanzu ya fara kawo yar gardama , duba ki ga ke fa take yiwa musu?, Allah dai ya bata lafiya" ya ajiye a tausashe da siga irin ta lalami, baban burinsa ya kawar mata da dukkan wani shaku a kan fitarsa, da du wani sake sake, ya kuwa kai ga ci ya kamata a cikin game dinta, domin ta yarda da hakan harma ta dora da kalar nata munafurcin na yin galaba a kansa a da ta shiga shashekar kuka da share hawaye ta ce" Idan na ga haka sai na ji hankalina na neman tashi yarona, shin Auta tanada wani wanda ya fi ni ne?, Tana ja baya da ni ne dan ina bata magani ina kuma tursasata cin abinci"

Murmushi ya yi yana fan sake dafe gaban goshinsa yana kuma ankare da kiran dake ta shigowa wayar Umman ama ta ki dagawa

Umma ta sake dubansa ta ce" Yarona kuma ka ga, dole sai ka yiwa Bahija magana fa, kar ta ringa anfani da damar da Allah ya bata ta kasancewarta yar uwarka ta ringa muzgunawa abokiyar zamanta sannan ni ta ringa rainani "

Kai Allah mai mutane, a cikin mutanensa ya halici rikakun munafukan da duka iya tafiyar da rayuwar munafurcinsu cikin kwarewar da ba zaka iya gani kai tsaye ba sai idan Allah ya so ka gannin, da wannan dama da Allah ya bashi ya dake budar bakinsa ba tare da gajiyawa ba ya ce" Hakane, inaga ko harda yarinta dake damun BAHIJA?, Ba laifi in sha Allah zan kwatanta mata, kema sai kin tayani UMMA ni bani da time din abubuwan nan ne ma, ta rikicin cikin gari na ji ko tasu?, Ama maganar cin abincin nan nine nake da wannan ra'ayin, ba dan komai ba dai dan a baki lafiya ki ringa hutawa kema, shekaru karra ja suke yi wannan zama na karfe takwas a dauki wasu lokutan masu wani tsayin yanzu ba naki bane UMMA, sauran magangannun kuwa dole zan zauna da su na sanar masu ke uwa ce a gareni du mai son zaman lafiya ya girmamaki"

Magana ne yake yi mata du a dadaure, sai ya fadi wace ya dace ta rikita mata lisafi sai kuma ya fadi wace zata Kwonce tunanin cen nata na cewar ko wani abu na faruwa ne?
Fahimtar da ta yi ta fa ishe shi fa yawan maganar ya sakata mikewa ta yi masa salama ta tafi

Bayan ta tafi maganin Auta dake hannunsa ya cusa a cikin aljihun jalabiyarsa, sannan ya cire alkyabar gaba daya a hankali ya ci gaba da jan carbinsa yana neman sauki a wajen ubangijinsa har sansanyan barci ya dauke shi a nan saman kujerar, domin kafafuwansa kawai ya hauda sama ya shiga hutawa

__________________________________


A ranar UMMA bata kula kiran da aka yi ta yi mata ba, a tunaninta so syke su ji ko an saka masa maganin a abincin, har sai da wata safiyar ta waye, da sanyin safiya ta daga kiran da abin barci a idannuwanta domin ko salllar asubah bata yi ba, yawancin lokutama idan ta tashi ta ga rana ta yi bata yi kwata kwata gaskiya

Muryarta a ciki ciki ta ce" Wai dan Allah ku idan kuka so abu kamar Da ya so fita daga cikin uwarsa ne? Haba dan Allah ban saka maganin ba a gaba fa, ama sai wani kirana kuke yi ba dare ba rana ?"

"Ke dan Allah ki min shiru da banzan maganarki, ke har kin san yadda da yake yi idan ya so fita daga cikin uwarsa ke da baki taba haihuwa ba sai na kashi?, Ba maganar magani ake son yi maki ba, so muke mu sanar maki abinda ya faru da iyayen yarinyar nan, an neme su an rasa yau safia ta biyu kennan wai sun yi fada da wani mutun, mu muna nan cikin tashin hankalin abin ke kina cen kuna hauka!" Muryar mahaifiyar Bahija a zafafe ta fada har tana huci da takaicin Umma

Gaba daya Umma ta rigijo daga saman gadonta lokaci daya kuma jikinta ya dauki mahaulacin bari gab gab gab , haka kuma kafafuwanta suka dauki mijirya

A rikice ta ce" wani irin an neme su an rasa, gidan uban wa suka shiga yo? Ina masu tsaron nasu?"

"Gidan ubanda kika aikesu!, Fada ya yi da wani mutun mai kama da yan ta'ada, a yadda yan anguwa suka ce mutumen ya masa alkawarin batar da shi da danginsa, maganar da nake maki harta BAHIJA sai da ta wuni a summe bale masu gadinsu, sai da likitoci suka wuni a kansu baki dayansu sannan suka dawo hayacinsu!, Ki gagauta bincikar yarinyar nan dan ni abin nan na kasa amincewa da shi, gashi kina nan kinaa shirme kin ki maida hankali a kan dan aikin da aka baki ba wani ba, ni kam babu abinda zai mayar min da aiki baya na fada maki, wayar uwar ke hannuna sai kira yar uwar tata take yi, ki je ki sanar masu gaskiyar lamari cewa an sace yan uwansu mu babu hannayenmu a ciki, kuma su mayar da hankali su mana aikinmu ko suma da suka rage mu kuma mu salwantar da rayukansu!" Ta sake fada a kausashe

Wata ashariya UMMA ta lailayo ta lailaya mata a haulace ta ce" Ke ama mahaukaciya ce !"

"Kece mahaukaciyar daba da baki san abinda kike yi ba!" Ta rama itama rai bace, hakan ya saka Umma mikewa tana rarumar tufafi domin zannin kansa watsewa ya yi tsabar firgicewa da kidimewa

Zata yi magana Muryar sarkin tanus ta dauke tata muryar, cikin hali naa bacin rai da daguwar hankali ya ce"






























Salam
10/3/22, 10:10 - Buhainat: *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍?*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*


🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻
*OUMOUGHLOUK ITIBEL*
_(ZAKIN SARAKAI)_
🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻

_FREE BOOK_

*Na*


*SAJIDA NIGER*





5️⃣6️⃣




Sai da ta watsa Hannayenta sannan da bakinta ta ce" Inna Indi?"

Gaba daya sai Umma Ta nemi neman wacece Indi a cikin kwakwaluwarta, dan harga Allah a irin lokacin ba lallene in ta tuna sunnanta na kantama bale wai wani Indi

Wajen da take Innar ta kai dubanta, sai kuma ta kai zaune ta saka hannayenta biyu kaf ta rangada tagumi kasa kasa tana fadin" Yau kam ana falatsin uwar kowa a gidan nan, ta yiwu bamu san inda su Auntyn suke ba za'a yi tsirenmu da ranmu, kun saka mu a masifa muna zamanmu a lungunmu, na tabata ba zai saurari maganar kowa ba zai hada jiji da jan kanwa ne ya mana cakuden luguden surfen uwar kishiya, innalilahi wa inna ilaihi rajune Indi zuwa kika yi wajensa ki ce masa me?"

"Wace Indi? Ta je ina?" Umma ke fada bakinta har yana hadewa

Inna Hindu ta ki bata Amsa, da kanta ta gane wace ake nufi, hakan ya sakata kaiwa kasa tana dora hannayenta bibiyu a saman kanta idannuwanta tamkar zasu fado kasa ta ce"Ban gane ba, me zata je ta yi? Tana ina? Dama mahaukaciya ce ita? Bata san ba'a wasa da wuta ba?"

Guguwa ce? Kusar kan INNA TA HABU MAKADI ce ta kunce? Menene ya sauka a kanta mai karfin da bai ji komai ba, ya kwasheta daga inda take ta rarafa ta dauke fuskar UMMA da wani mahaukacin marin da ya saka Auta faduwa ta yi zaman yan bori sannan ta dora hannayenta saman kanta tana neman haukacewa
Bata gama tantance hannun surfe ba inna ta rike hijabinta da kyau ta ce" Kwarankwatsa ki ce tak na tataka ki a wajen nan, ke baki san na jima ina dakon fuskarki ba zaki dubi idona ki ce yar Hindu mahaukaciya? Kin kusa gama aikata laifi a duniya in dai kina hadawa da irin wannan dan ni ba zan kyaleki ba kafin ki je mai sama ya tambayeki, banza shashasha abinda kike tunani ta je ta yi in dai Indi ce, sai mu zauna gaba dayanmu mu jirayi sakamako dan na tabata a yau yau din nan ba juma'a ba ba litinin ba zamu je inda ba kofa bale taga a ci ubanmu!, Dilla sai tsamin kwartaye kike yi!"

"Wayo Allahna, Mamah wai me yake faruwa wayo na shiga uku me yake faruwa ne?" Hindu ta saki wuyan Umma dake kici kici din kwace kanta

Umma ta mike tsaye fuskarta har ta nuna alamu ranta a bace ta ce" Ni kika mara? Ni kika daukewa hannu a fuskata? Zaki gane maganata da taki ba daya take ba a wajen yarona , zaki gane ke din ba kowa bace ba idan na je na same shi na fada masa su waye ku, zaki san shari iyawa ne idan kika samu kanki dumu dumu a cikin laifin da baki san hawansa baki san saukarsa ba, harta laifin kisa a yau sai ya hau wuyanki zaki gani"

Inna ta daga murya tana rakata da fadin" Sai me, da kisa da ba kisa ba mun san yau sai an ci ubanmu, ki fitar da kan naki, dama ai mun san hakan na iya faruwa !"

Tana bacewa ganninta sai kuma ta dora hannayenta biyu tana fadin" Wayo Allahna, ta yiwu habunma ba zan kuma gani ba, Yar Hindu an yi y'a gatanan dai ba tsari, maimakun ki tsaya a san ta inda za'a hau kya tarda zaki ki kai masa nama? Yanzun ko a wace take ciki? Ta yiwu ya yi gunduwa gunduwa da ita, bale ni yar tsurut da ni kamar sauran maye"

Hawaye na balewa a saman kumatunta ta kuma cewa" Mamah ina ta magana kin kyaleni, gaba daya kin min shiru, bayan ina ta jin maganganun da ba dadi daga bakinki da bakin Umma?, Mama me yake faruwa ne? Sai na ji wai kamar wai wai wai......" Wasu hawayen suka kuma balewa a saman kumatunta shap shap shap tana kallon Hindu, wace itama jikinta a mace yake ainun ita din take kallo

Hannayenta ta miko mata , hakan ya sa ta rarafa ta karasa inda take zaune ta zauna hadi da dora kanta a saman cinyarta

Ajiyar zuciya take saukewa, a sanyaye ta ce" Auta, Dole fa sai kin yi yaki da kuka, da rikicewa, da saurin nuna tsoro, sannan sai kin dage da addu'a, na dan kina yi, na kuma san kina da hakuri, ina so ki ninka ne, in ba haka ba kema shafeki zata yi daga doron kasa kin ji?"

Auta ta dago tana kallon Inma, muryarta a raunane ta ce" Mamah, tsoronta nake ji sosai, ama yanzu da kuke nan na rage jin tsoronta walahi, kin ga Mamah na tabata ba zaku bari ta cuta min ba ko?"

Hindu ta lumshe idannuwanta zuciyarta na yin rauni

A sanyaye ta ce" Mu fa bamu isa mu saka ko mu hanna ba, muma da kika ganmu a nan ta ranmu muke , kin ga an wayi gari babu danginmu, babu mahaifiyar NADIRAH, kuma babu mahaifinta, gashi ta je ta tona mu da kanta, bayan shi din baya ragawa masu laifi irinmu"

Irin yadda ta kureta da ido ne ya saka Hindu sauke nata idannuwan, a raunane ta ce" Bari ki ji su waye mu, ta yiwu ke zaki yarda da mu, sannan ki yi mana kyakyawar fahimta ko?"

Auta dai gaba daya magangannun bakinta sun shafe sai kallon Inna take yi


Inna ta shiga warware mata dukkan abinda ya faru a sanyaye, tun tana fada idannuwanta na kallon kas har ta dago tana kallonta ido cikin ido tana yi mata bayani...........tun daga kuruciyar NADIRAH, har zuwa yanzu...............





A bangaren NADIRAH kuwa
Gangar jikinta ce ke tafia, hankalinta kuwa ya yi nisan da bata gane komai, watau bata jin kira in ji hausawa

Da manya manyan idannuwanta take dube dube a falon, bata ga kowa ba, hakan ya sakata fara taka matatakalar ta nufi baban dakinsa wanda take tunanin samunsa a cen

Fitowarsa kennan daga bayi, ya yi wanka ne domin bai jima da gama Gymn ba, gashin kansa a jike yake, kirjinsa a bude ya dakata yana amsa waya a karamar wayarsa na maganar kasuwancin masarautar , watau maganar tanada mahinmanci shi yasa ya dakata yake amsawa

Tunda aka murda aka shigo ya saka a ransa HUZNAH ce, domin a sanninsa kai tsayen nan ita bata zuwa, a jiya ba irin kiran da bai mata bama a karshe tace da shi ita kam zata fada masa gaskiya bata son wasan tabe taben jiki, kowa ya kama kansa kawai gaskiya ita fa ba wata mai jimawa a waje bane idan ta zo, haka ta kashe kiran hankali kwonce ta barshi zaune kamar sumame yana al'ajabin duniya da abinda ke cikinta, sai gata yau ta shigo, shigowar kuma kai tsaye shi ta nufo, ko bata lura da bashi da sutura a jikinsa bane ko me?

Sai da ta zo daf da shi, kamar zata shige jikinsa, ta kurawa fuskarsa ido da duba irin wanda ake yiwa abinda ake son gane fari ne ko baki, sannan ta ringa dauke duban nata har zuwa wajen kirjinsa, a hankali ta tsayar da dubanta a nan kirjinta na dokawa kamar zai bale ya bar gangar jikinta

"Hey?" Ya fada da wata murya dake fita daga cen lungun makogwaronsa, sannan dan dabinon dake makogwaron nasa ya yi dama kadan ya dawo tsakiya tsakiya yana dan motsi a hankali

Wayar dake kange a kunnensa ya janye a hankali yana furta" Ina zuwa" ya datse kiran ya yi tsaye yana sake kallonta, gannin kamar bata san ta zo wajen ba ko menene?

A hankali ya saka hannunsa ya janyota dan gannin ko zata tirje? Sai gani ya yi gaba dayanta ta fado saman jikinsa har dan kwalinta ya fadi kasa

Hankalinsa ya ji yana neman tashi, hakan ya saka shi dagota da sauri yana kallon fuskarta ya dan girgizata ya ce" Lafiya? Menene?"

Sai a lokacin ta gama yanke shawarar ba zata iya yin shiru ba, ko wace wace, a kan iyayenta ya kasheta idan yanna so

Silalewa kasa ta yi tana watsa zannin dake jikinta, lokaci daya ta kai kwonce ta mike hannaye da kafafuwanta ta saka ihun da ya saka shi sake zuba mata ido yana kallon sarautar Allah

Neman yin birgima take yi bakinta na fadin" Wayo Allahna sun sace min innar birni da Aban birni, na shiga uku, na mutu na lalace mahaifiyata da mahaifina ban san inda zan samo su ba, innalilahi wa inna ilaihi rajune iyayena ne ala nema aka rasa"

Lebensa na kasa ya danne da dan karfi, ba dan komai ba sai dan ya hanna kansa fashewa da dariyar da ta tuko shi yana kallon cinyoyin da ake masa kwalele, uhum su tuzuruwar kauye manya
Da kyar ya iya cijewa ya nuna alamun tashin hankalinsa ya duka yana biye da ita har ya riketa ya dagota yana kallonta ya ce" BAHIJA, meye kike fadi haka? Su bafa je aka sace ko me? Wani irin sacewa kamar kwondala?"

Fuskarsa ta tsurawa ido, shi kuma a dole ya kawar da nasa duban dan kar ya fashe da daria, sai dai idannuwansa na sauka suka sauka a kan fari kal fin pant dinta da ya bayana sakamakon birgimar da take yi a kasan
Daukewar kukanta ya yi daidai da daukewar son ya kwashe mays fa dariar da yake yi, a hankali ya dora hannunsa saman cinyar tata cen kusa da pant din nata a hankali ya hadiye wani irin wahalalan numfashi ya ringa matsa hannun nasa da dabara yana ta lumshe jarababen idonsa

"Zan sanar maka komai dala dala , ka yiwa Allah kafin ka kasheni ka nemo min iyayena ka ji? Kuma ka sani basu da laifin komai, gaba daya laifina ne ni dayan nan da ka gani, komai nice na yi, komai laifina ne, ka rufa min asiri kamar yadda Allah ya rufa maka kar ka sako min iyayena a cikin fadan nan, kai baka san me yake faruwa bane, a zaunen nan da kake baka san komai ba, kana ji ko, ni din nan ba kowa bace face gagarumar yar cin amana, nice nan na zo gidanka a matsayin wace zata kashe ka.................................................... Kai, tsaya mana, cire hannunka a nan yanzu yanzun nan, ana maka maganar Allah kana kawo irin abubuwan nan wayo Innat................................."
Ta rike hannunsa da duka nata hannayen, tana girgiza kai

Idannuwansa ya dago a raunane yana kallon fuskarta, a haka din da ta rike shin babu abinda ta hanna shi domin ya idasa kai hannunsa nasa ita kuma sai zarro ido take yi

A ransa ya ayyana ' dama kashenin kika yi ke kam'

A bayane kuwa kasa kasa sosai ya ce" Wannan dinma ai sunnah ce, mai ladan gaske, bari mu dan bata hakinta sai mu ji option din gaba me yake faruwa......... NADIRAH.......yanzu banaa gane komai, ke fa kika bude.....mmmmmmmmmmmmmmmmmmmmm"

A yanzu kam sai ta rasa BAHIJA yace ko NADIRAH, kokowa ta shiga yi da tunaninta dan ta tinano me ya ambata yanzu yanzun nan, jama'a kamar yace da ita NADIRAH fa? Kamar NADIRAH yace fa?


























🤔🤔🤔🤔
10/3/22, 10:10 - Buhainat: *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍?*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*


🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻
*OUMOUGHLOUK ITIBEL*
_(ZAKIN SARAKAI)_
🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻

_FREE BOOK_

*Na*


*SAJIDA NIGER*





5️⃣5️⃣



Cikin hali na bacin rai da daguwar Hankali ya ce" Saurara hakanan mana Laure, kina jina ki san yadda zaki yi da maganar, ni dai ban san ina suke ba, abinda na sani aikina da kike nan kina jan jiki har yanzu ba'a yi ba bayan na tura maki maganin, ke kin san ribarki ce, kamar yada take tawa, shawararki ce ki maida hankali a yi ko kar ki maida na fada maki!"
Daga haka ya kashe kiran ya shiga balbale matarsa da masifar da ba laifinta ba, har hutawa yake yi yana dorawa daga inda ya tsaya, fadi yake du itace mai laifi da bata iyawa kanta a komai sai masifafen la'ananen kishi marar anfani, maimakun ta je ta tsaya a inda y'arta take ta karra gargadinta kan haukan nuna kanta kafin a kashe sarki tana nan tana hauka, wai itace harda gayatar wani kato gida bayan an boyeta ne? To ta yi da kyau , ta maida hankali sosai, idan har ta yarda ta yi shirme ta falasa kanta shi ya san inda zai kai kansa ya tsira, tsakaninta da UMUGHLUK ITIBEL kuwa sai ta san ta yadda zata guje masa! Babu abinda ya dada kansa a kas walahi

Abubuwa suka taru suka yiwa mahaifiyar Bahija yawa , ra rasa ina zata kama, ta ina zata fara, itama kwana uku kennan yau tana kiran number yar uwarta bata samu, ko a whatsup din ko a kira direct, tun ranar da ta sanar mata dan banzan danta ya saka layinsa na Nijar rabonta da su, Allah dai

Please Login or Register in order to submit comment