Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ce ta tashi tana murmushi ta shige ciki dan su yi sirri


FADIME a sanyaye ta ce" Hindu kin kaura ba?"

HINDU ta yi shiru

FADIME ta ce" Ki tataro ki dawo dakinki kin ji abinda na fada maki, kina nan ko bakya nan abinda Allah ya nufa zai samu yarki sai ya sameta, kar ki yi wasa da aurenki mana"

HINDU ta gyara zama ta ce" Aunty ba wasa nake yi da auren ba, dama dan Habu baya nan ne, kuma kin ga jiya dai Indi cewa ta yi a cewa UMUGHLUK sai wani jikon zata je gaishe shi"

Ai kuwa rikicewar da Fadime din ta yi har ta zarce ta HINDU, haka take salalami itama ta saka aka ba NADIRAH wayar, kamar zata fito ta wayar haka take yi, fadi take tana maimaitawa cewa Babansu ne fa, a kan me zata yi aiki kamar na yar kwaya? Tsaf suka karra sileta, ita kuma ta yi shiru, dan a ranta ayanawa take yi' Ba ku gane komai bama yaya da kanwarta gaskiya, ni ba zan fara kai kaina ba fa, yo ai ba haka ake yi ba'!


Haka suka wuni sunna yan abubuwansu dan debe kewa, sai dai kowace zaman dakan ya fara isarta, domin ba sabawa suka yi ba gaba dayansu

A haka har kwanaki biyun suka shige, a ranar na ukun ne sabuwar maganar zuwa bangarensa ta karra tashi, wannan karron kam ta ga da gasken gaske suke,

Tun karfe goma aka shiryata akace cin abincin rana a bangarensa
Kwata kwata sai ta ga abin nan ba wani tsari sai shirme

Bata dai ce komai ba , haka ta zuba ido tana bin motsin kowa har lokacin ya yi aka rufa mata wata mahaukaciyar alkyabar da ita da kanta sai da ta ringa shafata, domin har ga Allah ba dai laushi daa kyau ba

A nutse aka bude hanyar baya domin rana ne gatse gatse da nufin bi ta bayan da ita,

Sun dauko tafia su hudu Umma sai karra gyarata take yi tana sake gyara mata rufarta ta ja ta tsaya

A hankali ta nemi dukewa, hakan ya saka jakadiya tareta da sauri ana faman ambaton Allah da yi mata sannu

Ido rintse ta kwashi barin jikin karya kab kab kab kamar da gaske

Hankalin Umma tashe take talabota tana tambayar menene? Lafiya? Ama NADIRAH ta kasa fadin komai

Hankali tashe Umma ta sake dagota tana girgizata ta ambaci sunnanta tana tambayarta menene?

Muryarta na rawa ta furta" Umma, bayi nake son shiga, innalilahi zai bale"

Har ga Allah Umma ta yarda, haka kuma da mahaukacin gudu ta saka aka juya da NADIRAH aka nufi ciki da ita hankali tashe aka nufi dakinta da ita Inna naa tambayar lafiya?

Bayin ta shige bayan ta watso alkyabar ta ja ta rufe ta haye saman abin aikin ta ringa jan ruwan tana kakari kamar wace ke aikata aikin da ba jira😌

A waje Umma da inna ke kai kawo ana tambayarta yaya da sauki? Tana buga gyaran murya

Umma ta dubi Inna hankali tashe ta ce" Sai fa mun yi da gaske, kar aje kishiyar ke son cin mata, kina ga haduwa ta gagara bayan an daura aure ba yau ba?, Kar fa aje mun raina wayonta ita tana mana kallon shashashu, kar aje wankin hula ya kaimu dare, kar aje ta san me muke shiryawa tana neman yi mana sakiyar da ba ruwa, ina zuwa zan je na sanar masu abinda yake faruwa sannan na fita da kaina na kawo jikakun karya tambaya da kaikayi koma kan mashekiya, ko me ta aikata mata sai dai ya koma kanta walahi, wannan wace irin masifa ce, ki duba ki ga kwaliyar da yarinyar nan ta sha fa? Ai karya take idan takamarta bokaye ni a hanya na kwana dan ubanta!"


Inna na tsaye bayan fitar Umma ta samu kanta da zaunawa tana kallon kofar bayi, haka kawai sai take jin damuwar rashin lafiyar da kuma rashin yarda idan har Indi bata da lafiyar ne, koda yake shi gudawa ai kawai zuwa yake yi kai tsaye, bara ta samo kuka ta bata ta sha sai ya tsaya, wannan abu dai kam itama bara idan ta bata kukar ta tofeta, idan har aka yiwa UMUGHLUK ITIBEL da NADIRAH faraku ai ita ta shiga uku, ko haduwa ba zasu yi ba kennan? Firgit ta mike ta fice itama ta rufo dakin ta tafi neman kuka a wajen kicin din bayi, ta tabata ba za'a rasa ba

__________________________________


Kasancewar har sha biyun ta gota ya zamto shima ya sauko dan cin abincin

Shigarsa ta sababin kaya ne kamar yadda ya saba, rawaninsa wanda aka rufe fuskarsa gaba daya ne

Tun daga Auta har Huznah sun sha kwaliyar da sai da suka birge shi

Sai dai mamakinsa gannin bai tardo harda yar mulkin a wajen ba

Sakon da Umma ke sanar masa ya saka shi dora dubansa a kan Auta, wace yana kallonta ya hangi boyayiyar dariya a fuskarta

Samun kansa ya yi da mamaki mai tsanani da kuma jin haushi hadi da son gaskatawa

A kausashe ya ce" Karfe takwas na dare ya mata a falon nan, koda tana tafe ana tare abinda ke damunta ne!"

Daga nan ya mike ya fice, domin bama zai ci abincin ba, ikon Allah shi za'a rainawa wayo? To ita me take takama da shi da har zata aikata haka?, Idan tunani take yi akoy maganar soyaya ko makamanciyarta da zara saka ya fuskanci me take nufi ta makaro!, Ba zai dauki rainin wayo ba sam!, Zara zo zai kuma fada mata gaba da gaba!

Jikin Umma ya yi sanyi ainun, ba dan komai ba sai dan sanin da ta yi dole ne Nadirah ta zo koda ana tare mata gudawar kuwa, ita da ta so ta shigo kanta a sama? Ita da ta so idan ta zo sai hankalin kowa ya tashi? Akoy matsala


Daga nan bangaren Nadirar ta koma dole, a lokacin Innar Nadirah ta dawo tuni ta tarar da Nadirah kwonce a dakinta tana rera wakar dandali tan kada kai, bayin ta shiga da sauri, ai kuwa bata ji alamu ko gannin alamu na abu mai doyi ya sauka ba, a lokacin ne ta yanke hukuncin lalle sai sun fuskanci junna ita da y'arta, sun yi magana ta fahimta

Abinda Nadirar ta fada cewa ai ba aji ne ya sakata rushewa da kuka sai da Nadirar ta ringa rarafe tana bata hakuri da rike kafarta sannan ta saurareta, ta gama yanka mata kashedi ta fito Umma ta dawo

Fuska da alhini Umma ta sanarwa Inna umarnin UMUGHLUK ITIBEL

HINDU ta ce" In sha Allah zata kasance a wajen a lokacin, kar ki damu Umma"

Da wannan Umma ta fice dan zuwa ta amso su karya tambayar nan dan ba zata yarda a cinma yarinyar ba! ( Uhum, hakane, wani lokacin makashin naka ke baka kariya kuma cikin kudurar ubangiji)

_____________________________________

"Sannu, kar ki fadi mana" Muryar Umma ke fada kasa kasa tana karra shakar kanshin tutaran yarinyar domin ita ke rike da ita a jikinta, sai HINDU dake gefe tana rike da alkyabarta, domin sharadin NADIRAH sai dai idan da Innarta za'a je

HINDU ta karra waigawa gabas da yamma, kudu da arewa, sai ta samu kanta da share hawaye tana karra wara idannuwanta tana kallo

Tafkeken hotonsa dake makale, wanda rawaninsa mai shara shara ne ana gannin yannayin fuskarsa sosai ta zunawa ido, hakan ya saka ta ci tuntune da rigar Nadirar ta je ta gwarunma Nadirar

Taga taga NADIRAH ta yi a dole ta kama Alkyabarta ta rike gam hankali tashe ta ce" annabi ka san da zuwanmu zamu rufto kasa!"

Inna ta tareta raf tana fadin " Sannu Indi bamu kai kasam ba"

Nadirah ta ja numfashi dan har ta rufe ido, sannan ta kama Alkyabar ta cire gaba daya tana jan numfashi ta kai dubanta wajen Umma zata yi magana Umma ta tareta da gagawa ta ce" Ya salam, Bahija sannu, baki ji ciwo ba?"

Tsuru NADIRAH ta mata, sai kuma ta samu kanta da juyawa wajen da a shigowarsu take hangen kamar mutane

Ido ta zuba masu itama, kamar yadda suka zuba mata,
A hankali taa lumshe idannuwanta tana jin kanta na sara mata sanadiyar tino abinda ke boye

Daga Auta kuwa, har HUZNAH idannuwansu tamkar zasu mana mata shi a jikinta hakane
Fuskarta babu kwaliya ko diz a jiki,
Dinkin dake jikinta doguwar riga ce ta leshi fari fal bashida ko digon wata kalar daya a jikinsa, haka kuma dinkin ya bi jikinta ya lafe a jikinta ya amshi jikinta har kirar jikinta
Gashin kanta dama ba'a daura mata dan kwalin ba, alkyabar kawai ta rufa dan ita aka bari ta shirya ita kuma ta yi yadda ta ga ya dace da ita
Kunnenta dan siririn dan kunne ne, hannayenta ba komai a jikinsu, sai sarkar dake kafarta a daure wace ana ganninta a bayane


Mikewa suka yi dan karamata, da kuma yi mata sannu
HUZNAH, jikinta har rawa rawa yake tana karra kallon NADIRAH, sai dai gannin kamar bata masu kallon wulalanci ba sai ta samu kanta da dan sauke ajiyar zuciya


Auta kuwa ta rasa me take ji a ranta game da matar, ita dai ta zuba mata ido tana son karantarta

Ba tafiyarsa ta sheda saukowarsa ba, domin takalman dake kafarsa na fata ne, basa kara idan ana tafiya da su

Fankamemen madubin dake kafe ya sheda mutun zai sauko, hakan ya sa a tare suka juya kowa ya daga kansa dan gannin ko wanene


Abin mamaki, kasancewar rabonsu da shi tunda safe dole zasu masa gaisuwa irin ta dukawa, ciki harda Umma domin wannan din hakan yake, Uwa uba HINDU da har neman kwonci take yi bama dukawar kasa gaba dayanta ba, ya zamto NADIRAH ce a tsaye, kanta a sama tana kallon saukowarsa cikin nutsuwa, da sandar dake hannunsa mai ruwan zeba tana walwalwal, da alkyabar dake jikinsa, uwa uba da rawaninsa mai masifar kyau wanda ya hau da shigarsa mai tsari da kyan gaske, a gangaro zuwa farin hannunsa kar mai jimke da sandar, dayan kuwa a cikin Alkyabar, haka kuma girman jikinsa wanda koda a cikin alkyabar ne ana iya ganewa da bashida karamin jiki, da irin nagartar shigarsa mai dukkan kirji


A hankali ta yi luuuuuuuuuu da idannuwanta a lokacin da idannuwan nata suka shiga cikin nasa, sai kuma ta gane jikinta babu abinda ke nufi da itace BAHIJA watau Alkyaba

Juyawa ta yi ta karasa kusa da Umma ta rage tsayinta kadan ta ce" Bani abin na rufa"

Umma ta dago daga sada kanta ta mika mata alkyabar ita kuma ta gyarata kawai ta wani yafata a kafadunta sannan ta sake duban Umma da ta fara mikewa tana sake yi masa sannu da saukowa ta karasa kusa da NADIRAH cikin dabara ta shiga fitar da hular alkyabar ta dora mata a saman kanta a tausashe tana murmushi ta ce" BAHIJA, ki karasa ki gaisar da Mijinki mana"


A hankali ya karra zubawa wace aka kira da BAHIJA ido, wannan karron ba duba daya da dauke ido ba, duba irin na tsanake dan ya gane me kennan?, Tun daga kanta har kaffafuwanta yake kallo sannan ya sake kallon Umma wace sam bata gane abinda ke wakana ba, burinta su daidaita dan ya yarda Bahijar ce a gabansa

Umma ta rike hannun Nadirah suka karasa wajen zaman , gefen daya, ba inda su Auta suka zauna ba ta nuna mata tana fadin" Zauna a nan kema sai ki kawo gaisuwa"


Zaunawar ta yi tana sake leka Innarta, ko dai inna ta summa? Take ayannawa a zuciyarta,
Haka kuma a koye koyen abubuwan nasu sun manta basu koya mata baban abin ba, watau gaishe da UMUGHLUK ITIBEL, ai su basuma kawowa ransu cewa sai an koyar da ita wannan ba, gannin ita fa yar bayi ce ko?

Bata sake kallon idannuwansa irin na dazu ba, bale har ta lura cewa kallon da yake mata ya gane ba ita bace Bahija
a fuzge ta ce" Sannu da saukowa"



Ba Umma da su Auta ba, harta Innarta sai da ta ji kamar an gaura mata mari , irin da busashen hannun nan, marin nan mai zafi da bada sautin DAU a kunci!


A rikice Umma ta dubeta , sannan ta dubi ASADEEK da ya sake komawa da kyau saman babar kujerar da take tasa ya hade kansa da kujerar ya afka tunanin me hakan ke nufi? Ta ce"
8/13/22, 23:00 - Buhainat: *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍?*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*


🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻
*OUMOUGHLOUK ITIBEL*
_(ZAKIN SARAKAI)_
🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻

_FREE BOOK_

*Na*


*SAJIDA NIGER*





2️⃣9️⃣



A rikice Ummaa ta ce" Har yanzu bataa dawo normal ba, Bahija ko mu mayar da ke bangarenki ne?"


Shiru ne ya dauki wajen, domun Itama NADIRAH sai ta samu kanta da yin shiru tana ta auna me ya dace ace ta ce? Baba ne ai ya daace ta duka ne ai tana gannin ta gaishe shi a duke haka

Ajiyar zuciya ta sauke ta dauke kanta daga kan Innarta wace dama sai da aka ce mata idan sun zo a matsayin baiwa zata kasance har su koma

Idannuwanta ta sake ɗorawa a kansa

A facing dinta yake, domun kujerarsa na kallon su ne gaba daya

Yawu ta hadiye aa hankali ta sauko kasa gaba dayanta kantga a kasa ta furta" Barka da warhaka, Fatan aan sauko lafiya?"

Dama dama, watau gaisuwarta mafi dama da sauki kennan, mafi daraja kennan, sai dai kashhhh tun a nan ta tona kanta cewa ita din ba jinnin sarauta bace, domin ko Umma a yanzu ta wuce gaisuwar nan bale UMUGHLUK ITIBEL

Ga mamakinta sai ta ji muryar mutanen da suka fi kusanci da shi sunna nema mata afuwa, bayan bata ga laifin da ta aikata na hakan ba

Daya bayan daya ta shiga binsu da kallo, tun daga kan Ummar har wace keda fuska kamar ta yara sai shegen kallon tsiya

Baki ta dan tabe ta nemi mikewa,

Da sauri Umma ta mata alamun kar ta mike daga tsugunin nan, a dole ta sake gyara tsugunin nata tana girgiza kai irin abin nan fa ba zata iya ba walahi!


A hankali ya dago kaansa dake jingine idannuwansa a lumshe y bude su y fara sauke dubansa a kan Umma, wace ke gurfane kanta a kasa

Tambaya ce ke saman lebensa, wace take daf da fitowa daga bakinsa, itace wannan din kuma wacece?
Sai kuma ya ji wani sashi na zuciyarsa na yi masa wata tambayar, shin UMMA bata san Bahijar bace aka miko mata wannan a matsayin Bahija? Wannan din wacece? Me yasa aka ce za'a bashi auren Bahija aka bashi na wata? A sanninsa bafansa y'arsa mace daya tak ce, itace wace suka yi tafiyar nan tare, bayanta a ina ya samo wannan?, Alamun wannan sun nuna ita din ba yar gidan sarauta bace, domin dan gidan sarauta ko yaro karami in dai ya fara iya hada magana ya iya gaisuwar sarki

"Allah ya huci zuciyarka, yarinta ke dawainiya fa ita, a yafe mata, tana tuba in sha Allah ba zata kuma aikata makamancin wannan gangancin ba" Umma ta sake fadi a tausashe tana sake sada kanta

"Yarinta?, Ganganci? Wannan din ai ya fi karfin ganganci ga mace ɗaya tilo da aka bashi a matsayin BAHIJA, lalle sunne suka yi ganganci wajen manta abu mafi mahimmanci, to shi a yanzu tamabayar da ta maye gurbin wacece wannan din itace....menene dalilin yin hakan? Ko yace menene mission din da aka ba wannan din?, Shi sai yake gannin kamar fitsarariya ce yarinyar, jama'a wannan kallonsa da take yi ido cikin ido fa?, Ga kuma gaisuwa irin sako da sako

A hankali NADIRAH ta sake satar kallon Umma, to wai ita a ina du ta fadi magangannun nan da ake cewa ta ce?, Uhum, wai yarinta ganganci, zaki ga aikin ganganci kuwa


A hankali ya gyada kansa yana sake dauke dubansa ya sake mayarwa kan Auta

Ido hudu suka yi da Auta, sai yake karantar kamar ta afka a tunanin son gane yarinyar nan a cikin mahaukatan ita baba ce ko?


A hankali ya sauke dubansa a fuskar HUZNAH
Idannuwanta cike da lamari irin na rarashi da girmamawa, shigarta ta birge shi sosai, itama HUZNAH leshen ne yanaga a jikinta, kuma dinkinta sakake sosai , Huznah kam akoy hankali
Kan matar dake duke, wace yake kyautata zaton baiwarta ce ya sauke dubansa, tun dazu take duke haka, sai ya samu kansa da yin gyaran murya yana duban matar

Shirun da ya gani bata tashi daga gurfanawarta ba ya saka shi sake dora dubansa a kan Umma
Lalle matar nanma ba ta gidan sarauta bace, ba kuma baiwa bace

Da sauri Umma ta mike, kafafuwanta har sunna neman yi mata nauyi, rabonta da shiga dimuwa irin haka tun wani lokaci da mahaifiyarsu ta tardota tana zane Auta,

A hankali ta dafa Inna kasa kasa ta ce" yana nufin kina iya tashi"

Inna ta dago tana jan hanci ta saci kallon y'arta, oh duniya yau ga abin jibga Indi ta yi ba halin ta zauneta ta jibgeta? Innalilahi ita HINDU ashe zata ga wannan rana irin haka? Dole yau ta Jibgi Indi walahi!

Kanta a kasa ta shiga kokarin kamanta gaisuwa da neman afuwa kamar yadda ta ji matarsa da kanwarsa da Umma na yi, sai dai itama bata san a yi masa maganama masu wannan yancin kai tsaye makusantansa ne

A hankali ya jimke hannunsa jin kamar bacin rai na neman hadasa masa mijirya a gaban jikinsa

Umma ta salami HINDU fuskarta har tana gyatsine dan rikicewa

A hankali ya budi bakinsa maganar farko ya ce" Umma, kina iya tafia"

Umma ta kalle shi, hankalinta a tashe ainun, sai dai ba damar jan maganar dan an masa laifuka a jejere sosai

A hankali ta karra neman afuwarsa sannan ta nemi da NADIRAH ta mike su tafi

Da mamaki Auta ta kalleta, hakama HUZNAH

HUZNAH ce ta yi karfin halin fadin" Aa umma ki je zata zo, bamu gaisa ba fa"

Umma ji ta yi kamar ta karasa ta shaki wuyan HUZNAH ta gaura mata tagwayen mari, sai dai ba hali, a hankali ta saki.lalausan murmushi sannan ta kafe NADIRAH da ido, wace ke duke ba'a bata damar tashi ba, ita gaba daya bama fahimtar wannan magama kamar masu ciwon baki take yi ba, kamar ta yi kisa ? Wai shi sarkin adalci? Walahu harda zalunci a jerin sunnayen nasa , in ba wannan ba me ta masa daga haduwa? Koda yake mutumen da ya tsofi su Inna ai sai hakuri da hali, itafa kowama ya kama kansa fa, itafa bata zo wajen nan dan komai ba sai dan ceto, ceton kuwa zata yi shi ne ta hanya daya tak, idan sun tashi karshi ta fada masa, dan ba zata iya kayan takaici ba,wani zuwa gaishe gaishe da sauransu gaskiya bata so, ita da ta so ta fita bayan magaribar yau ta zazaga masarautar babu alkyaba? Ta gaji da zaman dakin ya fara hadasa mata ciwo


Jiki ba karfi Umma ta juya ta fice, ji take dama tana iya zama kuda ta lane a jikin NADIRAH ta ringa daidaitata?, Ya Allah!



Tana fita Auta ta sake kallon Yayanta

A sanyaye ta ce" Abah, ta mike daga tsugunnin? Ta tuba a gafarceta"

Baki NADIRAH ta turo kai kace zaa saka mata ribom ne a daure ta kalli Auta da kallo irin na harare harare wanda hakan ya saka Auta zarro ido tana kallonta

Bai ce komai ba ya mike a hankali ya juya ya shiga haurawa sama, wanda hakan ya saka Matarsa mikewa da dan sauri ta bi bayanshi


NADIRAH dai da ta dafe kugu sannan ta kai zaune a fili ta furta" A gayasssss" wanda sam bata san ya fito fili ba


Auta ta sake wangale baki da zarro idannuwa kamar zata fado dan mamaki tana kai hannunta daidai bakinta ta furta " Lah "

NADIRAH ta dago tana kallonta, samun kanta ta yi da karra kallonta itama , sai kuma ta ce" Yo tsakaninki da Allah me na masa ni, tun dazu kuke cewa na tuba kuma bakwa fadin laifina, shikenan dan nice bakuwa sai a cuceni? Haba dai"

Da mahaukacin mamaki hadi da wani zarro idon Auta ta ce" Aban ne zai cucekin ko wa?"

NADIRAH ta yi shiru tana kallonta, sai kuma ta mike tana kabe Alkybarta kamar ta yi kasa din nan ta ce" Babanki ne kennan?"

Auta ta girgiza kai tana murmushi itama ta mike tsayen tana kallonta ta ce" Yayana ne"

NADIRAH ta kama haba da mamaki ta ce" To fah, shi kowa Aba yake ce masa ne?"

Auta ta dage kafadu tana jin mamakin yadda Bahija ke magana a sake, irin ba abinda ya shafetan nan

NADIRAH ta ce" To sai an jimanku, bara na koma na san ana cen ana jirana"

Auta ta yi saurin fadin" Da wuri haka zaki koma? Ga fa abincin da aka tara mana saman table"

NADIRAH ta waiga wajen abincin, tsarin kwanonin kadai abin birgewa ne, sai dai a ranta ta ayana' kai ina, aje an zuba gubar a ciki' a bayane kuwa sai ta ce" Aa a koshe nake fam da kika gani a nan, a ringa bismillah dai in za'a ci abinci......
.."
Daga haka ta yi ficewarta hankali kwonce, ta bar Auta cikin tatauna maganarta
Haka kawai sai Auta ta ji kamar da wata manufa tace a ringa yin bismillah

Sai kuma ta koma ta zauna tana murmushi, rabonta da ta ga rikicewar Umma haka an jima walahi,
Ama wannan matar ko wacece ta birgeta, sai ta ji kamar kar ta tafi , kamar ta yi ta zama da su a nan din, tunda ta shigo wajen ake haba haba gwanin dadi



A tsaye take a gefensa, bayan dogon hakurin da ta bashi har ta rufe bakinta bai bata amsa ba

Sai da ya gama yanke shawarar abinda zai yi ya dubeta yana murmushi ya ce" Ba komai fs, ki je ku ci abinci"

Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta juya ta tafi


Wayarsa ya dauko yar karamar ya zauna a bakin bed yana warware nadin Rawanin dake kansa


A hankali ya shiga wajen tarin uban miscall din da yake samu na number da aka duba masa aka tabatar ko ta wacece

Number ya dauka ya turawa yaronsa sannan ya rubuta masa mesage cewar a yi gagawar yi masa tracen number nan zai yi kira a sanar masa ina mai number take?


A nutse ya gyara zamansa sannan ya danna kiran ya ajiye wayar a kusa da shi yana dan shafa gemunsa idannuwansa sun kada sun cenza launi



Wayar na fara kuka aka daga, ringin ko na biyu bata yi ba aka daga hafi da sauke wata nanauyar ajiyar zuciya murya a birkice da kukan dadin gannin kiransa ta ce" Asalamu alaikum yah habibih"


ASADEEK ya sake murza sajen habarsa cike da takaici a takaice ya amsa salamar da lalausar muryarsa da karyewar harshensa tamkar balarabe


BAHIJA ta kai zaune tana kashe TVn dake kida ta dora hannunta daidai zuciyarta ta ce" Ina ka shige? Dan Allah ina ka shige? Har na cire rai, na yi kukan har na hakura, kulun cikin tunaninka nake, ka bani number na kira na kira ba amsa, tun bata shiga ta zo tana shiga, mamana tace ta yiwu aiyuka sun maka yawa, dan Allah ka fada min a wani gari kake a NIGAR zan zo, idanma baka da lokaci ni zan zo"

'innalilahi wa inna ilaihi rajune, ya Allah ya Allah me yake faruwa da ni ne? Wace aka daura min?...........'
A kala ta dauki minti daya tana ratabo zance na rashin kamun kai, har ya tabata ko menene sun gama masa a sanyaye ya furta" Zan yi kiran ki, zan je na dawo"

Muryarta a sanyaye ainun ta ringa magiyar dan Allah kar ya manta ya yi kiranta dan Allah tanada wata mmagana mai mahimmanci da zata sanar masa

Uhum kawai yace ya katse kiran,

A nutse ya mike ya shiga cire kayansa dan ya fara jin sun masa nauyi

Ya rage daga shi sai karamar rigar ciki da wandon shadar da ya cire

Kiran yaron nasa ya shigo, nan yale sheda masa daga garin Tanut ne, harta da anguwar sai da ya sanar masa

Wayar ya tsurawa ido, still kirjinsa na dukan tara tara


A hankali ya lalubi number SHEIK


Wayar na fara ringin shima ya daga a kamilance ya yi masa salama da gaisar da shi


ASADEEK ya bude idannuwansa yana fadin" Da wa ka daura min aure ne Sheikh?"

Sheikh ya yi shiru dan bai fahimci hausar ba, sai kuma ya dan gyara zamansa ya ce" Da yar gidan Sarkin Tanut ko?

Please Login or Register in order to submit comment