Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ne? Birni birni basa jin tsoron Allah sam!


_________________________________


Bayan sallar Magariba da isha'i

Zaune suke su ukun , kowane ba yalwataciyar fara'a a saman fuskarsa, dama dama Innar Birni tana dan shan shayi ne a kofi irin na bugaje tana dan kallon su a ranta kuwa tana adu'ar Allah ya kawo masu koma menene da sauki

Tun kafin ta shigo, samsanyan, rikitacen kanshi ne ya fara shigowa, sai da ta tsaya bayan ta yi salama har aka amsata sannan ta shigo da tafiar da ita bata san ta shiga jikinta ba , a tunaninta yadda ta saba ne take yi, sai dai daga Mahaifiyarta, da mahaifinta, da kanwar mahaifiyarta ido suka zuba mata dan abinda ya shiga jikinta abin girmamawa ne su a wajensu

Zama ta yi daf da Innarta tana sake kallonsu da son gane abinda yake faruwa,

Da sauri HINDU ta mike tana fadin" Bara na je falo na dan dakata, zagayawa zan yi ina ga cikin nawa ke son hautsina min"

Innar birni ta dubeta da kaifafun idannuwanta , fuskarta na daukan yannayi na ba wasa take yi ba, kuma ba zata bi abin da taushi ba ta ce" Ki zauna malama, bana son shashanci kin ji?"

Mijinta ya sauke ajiyar zuciya kamar shi aka yiwa tsawar ya dan kura mata ido sannan ya maida dubansa kan Y'arsa da gaba daya ta zamto abin kallo a wajensa, kamar ba NADIRAH ba, dama yarinyar akoy ruwa irin na manyan mutane a tatare da ita, ama abin bai kai haka ba, a yanzu kwana uku kacal du kamar ba ita ba, akoy halayanta na da, ama kuma ta wani irin salo take sakinsu a yanzu


HINDU zata ta yi ta sada kanta tana sauke ajiyar zuciya, hakan ya sa NADIRAH zubawa mahaifiyarta ido hankalinta na neman tashi


Mamanta ta fuskanceta da kyau ta ce " NADIRAH, wannan zama da kika ga mun yi a nan, zamanki ne, mun zauna ne dan mu baki amsoshin tambayoyinki, sannan mun zauna ne dan mu yi magana ta fahimta wace zamu ganewa junna mu kuma dauki abinda zai tunkaromu da kyakyawar fahimta ko ma gudu tare mu tsira tare"
8/13/22, 22:57 - Buhainat: *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍?*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*


🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻
*OUMOUGHLOUK ITIBEL*
_(ZAKIN SARAKAI)_
🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻

_FREE BOOK_

*Na*


*SAJIDA NIGER*





1️⃣8️⃣


Hpy juma'at




A sanyaye NADIRAH ta ce" Inna lafiya? Kamar wani abu ke faruwa?"

Innar Birni ta sauke ajiyar zuciya, ta kalli mijinta a tsanake sannan ta sake duban NADIRAH ta ce" Eh wani abu yake shirin faruwa, wanda bamu da tabacin zai kasance din ko aa, idan ya kasance bamu san yaya zai bile ba, abinda muka sani shine abin mai hatsari ne, da kuma muguwar rikicewa, wace bamu isa mu saka ko mu hanna ba, ......Abanta, ko zaka taimaka ka bata tarihin iyayen gidanmu a kanmu? Ka kuma shaida mata alkhairan ZAKIN SARAKAI?"

Zamansa ya gyara yana hadiyar yawu mai daci a wuyansa ya fuskanci NADIRAH a sanyaye ya ce" Tarihi ne ginane, tsohon iko ne da yake da tasiri tun a lokacin da ake yin mulkin kama karya, An yi zamani kala daban daban na sarakai masu iko daban daban a NIGAR, an yi zamanin sarkin dake yiwa budurwa cabe a jikin garu har sai ranta ya bar gangar jikinta, magana ne ce ta zamanin da da yanzu, magana ce ta mulki mai matukar daraja da wanda yake na kama karya, ko a shekarar da democradiya ta shigo mana a shekara ta 1960, ta zagaya ta yadu mun rike har bayi sun tashi daga dabobi sun zama masu darajar da har ake basu albashi na bauta, ama bawa sunnansa bawa kuma uban gidansa ya isa da shi a kan komai, saukin abin da muka samu a cikin sarakanmu akoy jajurtatu da duka giga har suka fi iyayensu karfi da tsayawa a kan gaskiyarsu, basa tsoron kowa ciki harda mutuwa, domin sun riga sun san cewa mutuwa da rayuwa hukunci ne na ubangiji, kuma lahira ce dawamamiya....Nadirah shin kina fahimtar abinda nake fada kuwa?"

NADIRAH ta sake fuskantarsu, har wata zufa zufa ke neman tarun mata a goshi, dan tsakaninta da wanda ranta ke hannunsa bata san dalilin da ya sa iyayenta sakata a gaba ita NADIRAH suke dauko mata wata magana kamar ta aljannu ba, yo ita me ya shafeta? Ita ba baiwar kowa bace gaskiya, kuma ita kam harkar sarkakiya irin ta sarauta sam bata sonta, magangannunsu kulun a cakule basu da abu a bayane, ita kam ina ta ga hankalin gane maganar Abanta?

A hankali ta girgiza kanta ta ce" Abana, gaba daya ni ban san me yasa ake maganar nan bama"

"Abinda ake son nuna maki, karfi, da ikon da Sarki yake da shi a kan bawansa, koda an shigo zamani na yancin kai akoy abubuwan da suke da karfi da tasirin da yancin kai ba zai goge ba, bale idan ba haramun bane, Abinda ake son sake nuna maki shine sarauta da kike dauka makiyiyarki itace gatanki, domin Allah ya yi umarni da mu yiwa shuwagabaninmu biyaya, sannan a zamaninmu na yanzu munna cikin zamani da ya kasu kalla biyu ne , a cikin tafiyarmu munna tare da rikitaciyar tafia wace ta hada adalin da yake adali a garemu da kuma adalin da yake adali a gare shi!, NADIRAH kin fahimci maganata?" Innar birni ta fada a kausashe, hakan ya saka Nadirah jin numfashinta na mata kadan a hancinta, a hankali ta dan ja gindinta da niyar matsawa kusa da innarta, sai dai bata idasa aikata hakan ba ta ga innar birni ta matso daf da ita ya kasance sun sakata a tsakiya

A hankali ta kamo hannunta ta rike da kyau a cikin nata tana kallonta ta ce" A lokacin da mahaifiyata take raye,an yi rikicin da ya hadu fa shari irin na bayi, aka dora a kanta cewa lamari na zina ya shafeta, shi UMUGHLUK yana zartar da hukunci ne bisa hukuncin musulunci, an kaita an garkame har an saka ranar jefeta, ashe shi din ba wanda ke aiki da gadara bane, yana bincike ta kasa, mun gama fawalawa Allah komai mun kauracewa kowa aka wayi gari da sanyin safiya aka fitar da rakardar wanketa tas faga sharin nan, tun daga lokacin nake kallonsa da kallo mai girma a idannuwana, cikinmu irinmu mun fi a irga dake dauke da daraja mai girma tasa a kirjinsa, wadda bamu taba haduwa gamu gashi ba, ama kuma a kulun muna binsa da addu'a"

"Inna me yake faruwa?" NADIRAH ta fada muryarta na mugun gargada tana kallon mahaifiyarta

Innar birni ta ja numfashi ta ce" Abinda yake faruwa shine, kadara ce zata biyo ta kanki, ta yiwu fara ce ko baka, koma wacece ita kike iya dauka muguwa ko mai sauki ta yannayin fahimtarki, abinda yake faruwa shine hukuncin rayuwa dake zuwarwa bawa ne ya riskeki, watau babu bawan dake rayuwa d asalin yadda yake so, kowa da irin takun salon kadararsa, ko wanene!, Ba komai bawa ke nema ya samu ba, mun yarda da wannan, hakane ya kasance a kanki NADIRAH............"

Yanzu kam har jikinta ya fara rawa, haka kuma sun fara bata tsoro, haba, gaske take jin wannan shorye shiryen da ake yi mata baya birgeta, kennan da lauje cikin nadi?

A hankali HINDU ta ce" Aunty, dan Allah kar ki rikitata, ba a haka zata fahimci maganarki ba, Kim ga Indi dubeni nan kin ji?" Hindu ta fada tana juyo da NADIRAH, domin gani take yi wannan salo da auntynta ta dauka sam ba zai kaisu da ci ba, ba Nadairah kadai ba itam dake sauraronta jikinta rawa yake yi bale NADIRAH

A tausashe ta kama hannunta tana kallonta ta ce" Kin sani cewa, wani lokacin abinda bawa ya nacewa a so ba shine alkhairinsa ba, da yawama soyayar ake kamar za'a cinye junna har a yiwa iyaye tabara, da zarar an shige gidan kuma a dawo kiyayar junna, tunda ba'a nemi zabin Allah ba ko?"

NADIRAH ta ce" Innata, Aminu ya rasu ne?"

Kai ta girgiza ta ce" Da ransa Indi"

NADIRAH ta kalli abanta da innar birni ta ce" To menene? Ku fada min menene kun ji? Me yake faruwa ne? Kalli Innar birni kamar wace ke kuka ko?"

HINDU ta karra hadiye nata kukan itama a hankali ta ce" Abinda yake faruwa shine, sun so bada yarsu aure wa UMUGHLUK ITIFAL dan ta je ta isar da bukatarsu na kawar da shi a doron duniya, sai ta kiya , kasancewar tanada damar hakan a wajensu, sai abin ya juye zuwa................"

"Hindu" Aban NADIRAH ya fada a hankali yana katseta

HINDU ta saki hannayen Nadirah ta sad kanta hawayenta suka bale

A hankali ta juya wajen Abanta tana kallonsa

Mahaifinta ya yi dan murmushi ya ce" kina ji?, Na amince da haka, innar birni ta amince da haka, dan baban abinda ya fi janmu amincewa da hakan shine tunaninmu zamu iya kare wani abun ta damar da Allah ya bamu, Gaskiyarsa da kare yancin talakawa ya siya masa makiya, barima ki ji NADIRAH, ina iya guduwa da ku, domin masu tsaron kofar cen su biyu babu abinda suka isa su yi, na tabata idan na shiga masarautar da ku na sanar masa abinda yake faruwa zai iya daukan mataki, sai dai tsorona shine , shin sunne kadai mafarautansa ko maciji zan kashe ban sare kansa ba?, Na karashe maki magana , a amincewar tamu mu din ba masoya zamu kasance a gaban idannuwansa ba, ta yiwu idan mun yi nauyin baki har muna iya samun mugun hukuncin da kawunnanmu ba zasu iya dauka ba....., Haka kuma cikin hatsarin da zaki je ana iya cin galaba a kanki, a haka duka muka amince NADIRAH muka salwantar da farin cikinmu, ba dan komai ba sai dan mu kamanta kyautatawa wanda yake kyautatawa bayin Allah "


Irin kallon da NADIRAH ke binsa da shi, kamar tana son gane a fuskarsa me da me aka hada aka haliceta ne!, Muryarta na rawa ta ce" Aba , da me kuka amince?"

"NADIRAH ke fa ba karamar yarinya bace, shekaru ashirin ba kwana ashirin bane, a birni ko a kauye kin isa ajiye ya'ya uku rass naki, abinda ake nufi shine an saka aurenki ke da UMUGHLUK ITIFAL nan da kwana goma sha biyu bi'izinillah, zaki je a matsayin yar sarkin garin nan, zaki je ki rayu a cen a matsayin matarsa, bisa umarninsu, sannan zasu biki da wani aiki wanda idan kika aikata ke da ubangijinki, watau kawar da shi a doron kasa!, Abinda mu muke maki nuni a nan kuwa shine, biyaya ta zame mana dole, itace abu ta farko da zamu yi a matsayinmu na wa'inda ke karkashinsu, muna iya bijirewa duda irin tarin alkawarin salwantar da rayuwarmu da suka yi, haka kuma muna iya guduwa wajen da za'a iya hukunta su, ama muka zabi amincewar dan mu kamanta kyautatawa wanda ke kyautatawa talaka, ta hanyar amincewa ba dan mulkinsa ko arzikinsa ba, zamu mika ki bayan mun gama fada maki cewa duk rintsi gwara a tsire ki da ki aikata abinda suke bukata, watau kashe UMUGHLUK ITIFAL!"


Innalilahi wa inna ilaihi rajune, mahaifiyarta na magana ne, barin jikinta na ninkuwa ninkin ba ninkin, wanda ya tsoratar da su baki daya ama kuma ta ki dasa aya sai da ta kai karshen maganarta sannan ta dasa aya tana mai saka idannuwanta cikin na yarta wace girman idannuwanta suka karru , fuskarta har ta dauki ja dan rikicewa, haka kuma numfashinta ya wuce misali a irin gudun da yake yi, watau sama sama kamar zata bar duniya

Da kyar ta iya juyo kanta da ya mata nauyi ta kalli mahaifinta, sai kuma ta kalli Innarta wace kukanta ke shiga kunnenta

Tabas maganar nan ba wasa bace, tunda a yadda suka sakata a gaba suka yi mata da kukan Innarta kadai zai tabatar mata da ba maganar wasa a lamarin

A hankali ta sake duban mahaifinta da ya jimke hannunta da karfi dan ya hannata barin jikin da take yi

Idannuwanta na shigewa sunna budewa ta kalle shi , muryarta na rawa ta ce" Abannnnnn, abbannnnnnnah, kunna nufin nice za'a za'a yiwa aure da UMUGHLUK ITIFAL Na baban Garin Agadaz a matsayin wace zata je ta kashe shi?"

Mahaifinta ya girgiza kai da sauri ya ce" Ba zaki kashe shi ba Nadirahna, idan kin je ba zaki kashe shi ba domin ke ba azaluma bace, ke ba makashiya bace....."

"Abana , to ni ai ya mutun zan fi so Abana....., Abana ku ce min muna iya guduwa a yanzuma, domin ba zan taba iya kasancewa yadda ake so ba, Abana kun san da wanda nake so ko? Kuma kun son bana son rayuwar sarauta ko ta dakika guda ce ko?, Abana ku taimaka min ku ce min zabi gareni, dan zan iya ce maku ya mutun ba zai dameni ba da a kaini gidna sarauta!" Ta fada muryarta a mahaukacin raunane, hawaye na bale mata, haka kuma tana haki tan sakw kure fuskar mahaifinta d ido

Hankali tashe mahaifiyarta ta ce" Kina nufin, gwara ki kashe shi da ki je aure gidansa?"

A zabure ta zarro ido tana girgiza kanta, muryarta a raunane ta ce" Ba zan kashe shi ba, Innar birni da na kashe gwara a samu gawata, ina fata da na kashe gwara a wayi gari a samu gawata, ama idn ya mutun ni kam babu ruwana, innar birni ku ce min shikenan mu tatara mu koma LABA kun ji? In sha Allah ba zamu kuma dawowa birni bama kun ji inna?"

Mahaifiyarta ta ja numfashin samun dan kwonciyar hankali, dan har ga Allah ta tsorata da farko

Komawa ta yi ta jingina da jikin gado ta ce" Ki yi hakuri, ki mana biyaya, bana son jan magana ki je dakinki ki yi sallah ki fadawa Allah, idan har alkhairi ne Allah ya tabbatar, in ba alkhairi bane Allah ya kade ta hanyar da kowa zai ji dadin abin , ki tashi kawai ki tafi zamu sake zama gobe in sha Allah "

Da mamaki Mahaifinta da Hindu ke kallon Innar birni, amaa ta hade fuska tama daina kallonsu

Magana abanta ya so yi ama innar Birni ta bashi barin fuska ta kara hade fuska alamun bata son maganar

Hindu ta sake kallon NADIRAH dake cicibawa jikinta gaba daya sai bari yake har kanta ba a daidaice yake ba, sai zabura take yi, kana kallonta zaka gane magana take son yi ama tana tsoron innar Birni

Tana idasa mikewa ta juya zata fita sai ji suke dimmmmmmm ta dimu a kasa ba numfashi a tatare da ita


A haukace suke rige rigen karasawa inda take

Da tsawa mahaifinta ya tare hannun Innar Birni ya ce" Ki barta, kar ki tabata Fadima!, Ki barta haka kar ki idasa kashe min ita!, Dan ni ina sonta, ina son abina!, Ko menene bako yake a rayuwarta, idan kika yi duba da irin kulafurcinta da abin, kuma mun zo mata kai tsaye da abubuwan da a maganar gaskiya sun girmami tunaninta dole mu sasauta, na san idan bamu yi mata da gaske ba, ba zamu iya tankwasata ba, ama kuma komai yanada lokaci, a kan me tashi tsaye zaki fitar mata da komai kuma ki koreta? Ki tuna ke kika sab da rayuwar bauta ba ita ba, Fadimata ki tuna ke kika san irin haka ba ita ba, ita din bata rayu da haka ba, shi yaa bata zama inda muke , dan bata son ganninmu a yadda muke, shi yasa take tafiyarta a wajen da babu hasken lantarki, dan ta fi ganewa ta yi dire direnta a birni hankali kwonce da rikicin cikin gida!, A hankali zata shiga irin rayuwar nan ba tashi daya ba, so kike ta gujeki? So kike ta kulaceki? So kike abinfa muke so ta kiyaye dan kauna ta aikata dan kiyaya? Haba dan Allah, dan muna talakawa ba mahaukata muke ba Fadimata, sai da muka yarda cewa mun amince, idan baki amince ba a yanzuma ina iya fitar da mu, da mu saketa a birkice gwara mu gudu tare!, A kan me zaki ringa irin haka? Kin hanna innarta ta bita ta yadda ta saba binta, kin ce ba zata saurara ba, bayan na tabata da ita din ce ta mata hirar sai dai su sha koke kokensu zata dawo ta rarasheta!, Haba Zahrah da wane kike so na ji? Ke Hindu daukarta mu je dakinta, ke kuma kar na ga kafarki a nan!"

Rai bace suka tafi suka barta a nan tana tsugune, a hankali ta silale ta hade kanta da gwuiwarta ta fashe da kuka tana kai hannunta daidai kirjinta ta jimke da karfi , muryarta cen ciki ta ce"
8/13/22, 22:58 - Buhainat: *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍?*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*


🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻
*OUMOUGHLOUK ITIBEL*
_(ZAKIN SARAKAI)_
🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻

_FREE BOOK_

*Na*


*SAJIDA NIGER*



1️⃣9️⃣


Ba edditing 😊😂



Muryarta cen ciki ta ce" Allah, kaine gatan bawa, mai kudi da talaka, sarki da bawa, Allah ga yarinyata nan, ka tankwasa min ita cikin ruwan sanyi, Allah kai ka fi kowa sannin irin halin da nake ciki, wannan daula da tunanin zamantowarta matar mutun mai daraja baya dadani da kasa, na fi tsoro da zulumi a cen kasan zuciyata, bana iya ci, bana iya sha , bana iya rintsawa, dan na san wacece yata, na kuma san zata kasance ne a filin da babu wargi, ya Ubangi ka mayar da bakin abu fari a tafiyar NADIRAH"............... (Amen innar birni)


A saman gadon dakinta Hindu ta shinfideta, jikinta na rawa a amshi ruwan da Abanta ya miko ta gumtsa a bakinta ta fesawa NADIRAH fesawar farko a fuskarta
Sai dai bata farka ba, hakan ya saka mahaifinta a rikice ya ce" Hindu ko ki dauketa mu tafi asibiti?, Hindu ta ki farkawa?"

Kai ta girgiza da sauri ta sake gumtsa da karfi ta fesa mata, wannan karron kam ta farka a rikice, sannan tana nan rarume rarume

Da sauri HINDU ta rukunkumeta a jikinta tana bubuga mata bayanta tana ambaton sunnanta da sanar mata cewa itace a tare da ita kar ta tayar da hankalinta

Murya a raunane, cikin yaren kuka mai tsuma zuciya ta ce" Innata, innata mu yi tafiyarmu, innata mu tafi, innata bana sonsa, bana kaunarsa, kuma bana son maganar a sakani kashe mutun, innata mu yi tafiyarmu wajen Aminuna, mu tafi innata"

Hankalin Abanta tashe ya ce" HINDU, tunda tace bata so ni kam na hakura, ki kimtsata zan fita na sama mana hanya, na hakura ba maganar yi mata tunda bata so, tayar da ita ki shiryata mu tafi!"

NADIRAH ta dago da sauri tana riko hannun mahaifinta tana gyada kai harda alamun fara murmushi ta ce" Abana, toh, toh Abana, mu tafi, ba sai an wani shiryani ba, mu je Abana, mu je!"


"Mu je ina?" HINDU ta fada da dan karfi sannan a kausashe tana kallonsu

Aban NADIRAH ya dubeta ya ce" Mu tafi ko'inama, ko ina mu je mana HINDU?"

HINDU ta girgiza kai da mamaki ta sake saka hannayenta ta zaunar da NADIRAH da take kokarin mikewa ama jikinta ba karfi

A kausashe ta fuskanci Aban NADIRAH ta ce" Ai kuwa yaya idan ta haka ne zaka iya yin wani abu gwara ka je kawai dakinka ka sasanta da matar cen da ka baro, domin zan iya rantse maka da Allah soyayar da kake yiwa yarinyar nan bata kama farcen wace take yi mata ba!, Itafa ta haifeta, du kusancinka da ita ba kai ka yi dawainiya da cikinta ba, ba kai ke gagara barcin dare idan tana wutsil wutsil ba, ba kai ke yawo, rana, zafi, ruwa, sanyi da ita a bayanka ba, yaya du wahalar soyaya da zaka nuna nake fada maka ragagiya ce a kan wace take yiwa y'ar nan!, Kuma ta fi kowa sannin wacece yarinyar nan!, Wai bama wannan ba, kana nufin zaka je ka rike makogwaron masu tsaron kofar cen, idan Allah ya baka Sa'a a kansu ta yiwu ka kashe su ka kwashe mu ka nufi wajen UMUGHLUK ITIFAL da mu ko ka je wani kauyen da a kankanin lokaci za'a kwasomu a dawo da mu nan?, Yaya kana tunanin du yar tsamar da suke tsakanin su idan ya tsaya a gaban dansa maganarka zata yi tasiri ne bayan bakada huja bayananiya wace zata saka a dubeka? Sunna aiki da ilimi ne, ka san wani laifi za'a lankaya maka kai da mu baki daya? An kar da dubu a kan laifin da ba nasu ba, ko kana musu?, Kai da zaka tayamu yaki a kan haka? Kai da zaka sheda mata Aminu fa karya ce a cikin gaskiyarta, zuma ce mai dacin balaki? Yaron da mahaifiyarda ta saka mata karan tsana ina take tunanin zasu je? Aminu ba zai taba biyota ba dan za'a masa aure da wata dan iyayensa na gaba da ita, itama ta sani, idan sun a shirmen soyayarsu uwarsa na tsaye a tsakiya, itama ta sani, sau nawa tana cewa zasu gudu idan aka hanna masu junna? Dan ubansa ba kudin aurensa aka kai ba? Me yace mata? Ciwon yatsa yake yi yana gindin babarsa!, Kuma ya dace ne ka ce da ita mamanta ta yarda, kai ka yarda haihuwarta aka yi dole ta yi biyaya, idan har NADIRAH ta kai wajen da zata bijire luma ba sai mu janye mu zuba mata ido ba, Yaya bana cikin wannan tafiyar, lalle abin ya zo wani iri, an mata wani kwana kwana bayan ya dace ne mu fuskanceta, ni da take wajena nakan fada mata abu kai tsaye ne, sannan na nuna mata a adini ba haramun bane ko haramun ne, koda ta yi kuka zata dawo ta yi hakuri! Bata fa kai wajen da ba zamu iya tankwasata ba yaya, haba dan Allah!" Ta karashe babu ko digon hawaye a cikin idannuwanta sannan ta juya wajen NADIRAH da ta yi dif kamar ba ita ke rizgar Kuka ba ta fuslanceta ido cikin ido ta ce".NADIRAH tsaya ki ji, maganar da aka fada maki gaskiya ce, bamu yi labe labe da kame kame ba dan muna jin tsoronki, mun yi ne dan muna gudun tashin hankalinki da rikicewarki, ba bacin ranki ba!, Idan mu namu tashin hankalin ba komau bane a wajenki ki bijire ki fice ki tafi ga kofa nan, NADIRAH kar ki amince dan an ce za'a batar da mu, kar ki ce zaki amince dan farin cikinmu, domin hakan na iya sakawa a cin maki da wuri, ke hakan na iya sakawa a wayi gari ki amshi gubar da zaki kashe Sarkinmu!, Ki shiga uku a duniya sannan ki je kiyama ki hadu da ubangiji, NADIRAH ke baiwa ce ba kowa ba, le yarmu ce, mu kuma bayi!, Ba maganar kina sonshi ake ba, ba maganar kin tsane shi ake yi ba, magana ce ta damar da Allah ya baki ake yi, wace kina iya cenzata da izinin ubangiji!, Nadirah gaskiyar mahaifiyarki ke ba jaririya bace, ba kuma dai na maki dogon tarihi ba, ke ba kurma bace a wajen dandali, a cikin kauye, a wajen sarakan kauyenmu, a bakin samari da yan mata masu shiga birni kina jin wanene UMUGHLUK ITIFAL!, shi din Uba ne, kuma kimarsa ta fi kargi laban bakina!, Yanada daraja, dan mutunci ne, mai kishinki ne ke talaka, kina iya zaunawa ki yi nazari idan zaki zauna mu tatauna ta yadda zamu ci karfin makiyan UBAN GIDANMU mu tatauna, ba dan maganar soyaya ba, bamu kawota kusa ba!, Ki yi dan ceto ne, ki yi domin Allah, idan komai ya lafa ta yiwu yana iya sawake maki cikin ruwan sanyi , idan har Allah ya bamu nasara yana iya yi maki abinda kike buri, a yanzu kam bara muke, kuma Umarni muke baki, dan ki kasance mai biyaya a garemu ba a garesu ba!, Ta yadda zamu buga wasan biri da ayaba!, Babu makiyinki a nan, kar ki kuma manta abinda nake fada maki *BA KOMAI DA KAKE SO KAKE SAMU BA, BA'A TSANANTA KIYAYA

Please Login or Register in order to submit comment