Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya sa ba wata jarabar bace ba kuma, domin idan har ta yi wasan da UMUGHLUK ya damke su sun bani walahi
Hijabinta ta saka mai nikaf dan ficewa a boye a taxi dan ta je inda ta boye BAHIJA dake cen kamar mai sabon kamu sai ihu take yi wayoyinta, number balarabenta meye meye, abu dai gayanan ya same su ba shawara ba sasauci ga sarki sai dora mata laifuka yake yi ita daya

____________________________________


Komai take yi jikinta rawa yake har ta gama saka rigar atampar da ta yayumo a cikin suturunta

Bata taba tunanin zata ji dan labarin da zai rikitata a kusa kusa ba har ya sakata fita ba alkyaba irin na yau, to dama hakane a duniya mutun marar gaskiya ya fi kowa saurin kidimewa da neman shiga a rikicewa komai kankantar abu

Hijabin sallarta daya tak wanda yake warin ruwa da ajiya dan ba wani wankeshi ake yi ba, shi da ba alkyaba ba? Ai bashi da wani anfani tunda ba na sakawa a yagawa mutanen masarautar AGADAZ

Idan fa makantar ta nufo zuwa take yi da dukan karfinta

Hankalinta tashe direct bangaren NADIRAH

Tana zuwa ta samu NADIRAR ita kadai a falo tana zaune, kasancewar karfe tara na safiya ta wuce tana kallon film din hausa a TV tana ta doka murmushi, ta sha shiga irin ta hausawa watau riga da zani na atampa dinki mai kyau mai sauki, dauri ne ta rangada ture ka ga tsiya wanda ya yi wani irin kyau a saman kanta, kanshin da jikinta ke fitarwa kuwa kadai abin takamar kowace mace ne ace tana fitar da shi, sansanyan kanshi mai saka nutsuwa, babu inda baya fitar da kanshin a sasan jikinta har zuwa gashin kanta, akaifunta kuwa har wani daukan ido suke na gyara

Ido cikin ido suke kallon junna ita da UMMA
Da mamaki take bin UMMAN da kallo har ta zauna saman kujera tana ta wani dan tabe tabe haka a jikinta, ta kalli nan, ta kalli cen

Sai da ta gama waige waige irin na munafukai sannan ta dan matso kusa da NADIRAH wace ta kama kanta ta shiga neman hijabinta dan gaba daya bata son wata mu'amula da matar walahi

Umma kasa kasa sosai ta ce" Kin ga jiya bamu zauna ba ko NADIRAH?, Du irin yadda na so na salami baki da wuri mu zauna mu sha dariyar diramarki abin ya gagara, gaskiya kin kware ina matukar sara maki, idan kika gama aikin nan ina mai tabatar maki nima sai na maki kyauta taki ta bajinta"

Irin kallon da NADIRAH ke yi mata da tana cikin hayacinta da ba zata taba amincewa da shi ba, ta yiwu sanadiyarsa har sai ta kawo kararta wajen ASADEEK, ama da yake yanzu hankalin nata gaba daya ba a jikinta yake ba sai bata gani ba

Kullin dake boye a jikinta ta fitar, kasa kasa sosai ta miko mata tana fadin" Shin yaushe ne zaki yi anfani da wannan? Lokaci fa sai ja yake yi NADIRAH"

Gaban NADIRAH sai da ya kwonci kwonci ya fadi, ta tsurawa abin ido ta ki tabawa ko da hannunta ne

Umma zata sake mika mata AUTA ta fito daga daki dan Inna ta gama mata abinda take yi mata tuni, Innar cema ke ta bige bigen waya bata samu yanzu dai ta ji ta samu mijinta shi yasa ta fito ta bata waje

Da sauri UMMA ta mayar da hannunta tana soke Maganin gabanta na faduwa, lokaci daya kuma ta hade girar sama da ta kasa tana jira Auta ta gaisheta ta koreta daga wajen su gama magana da NADIRAH, dan so take yi yanzu yanzu ta bata abin nan idan da hali a yau yau ta zuba masa a abincin kowama ya huta

Ba tare da sakewa ba ta gaisar da Umma, daga nesa nesa , sannan zuciyarta cike da mamakin shigar ta UMMA, ashe Umma zata iya zuwa wani waje ba Alkyaba? Ai ita tana iya rantsewa tunda aka yanta Umma da saka alkyaba bata taba ganninta babu ita ba

Gefen NADIRAH ta zauna a hankali ta sadda kanta, dan ba zata taba iya sakewa a gaban UMMA ba

Kasa kasa sosai NADIRAH ta ce " Dago min kanki!"

A hankali ta dan juyo zata kalleta, sai ta sake sinne kan nata gabanta na faduwa

NADIRAH ta ja tsakin da ya saka UMMA kallonta, zata yi magana a zafafe salatin INNA Hindu ya katseta

"Lah Ha ila Ha illalahu, Muhamadu Rasulullahi Sallallahu alaihi Wa salam, HABU ka yiwa darajar sy gwagwo ka daina ce min ba'a san inda su aunty suke ba, wani irin ba'a san inda suke ba, Habu wannan wani irin magana ne? Shine bake kiranka jiya wuni guda cirrrr ka ki dagan waya?, Habu ina yar uwata da mijinta suke? Wa bilahilazi ana neman a mutu, ana nan a shiga uku! In na yarda Ubana goma!, Kan uba wayo na shiga ukuna!" Ta karashe a haukace, tana idasa fitowa falon gaba dayanta, lokaci daya tana cuje dan kwalin kanta ta yar

"Innata lafiya?, Menene?" NADIRAH ta fada muryarta na amayara da alamun tashin hankali

Hannaye kawai take ta watsawa, ta yi nan ta yi nan tamkar wace ke hali na maye, gaba daya Nadirah da auta suka kasa tsayar da ita daga yawon , tana yi kumatana rusa kuka tamkar wace aka yiwa mutuwa

Da kyar hankalinta ya kawo kan UMMA , wace ta yi tsaye itama hankalinta a matukar tashe tana kallonsu fargaba shinfide a saman fuskarta

Hannunta da NADIRAH ke rike da shi ta janye a birkice ba tsoro ko dar ta karasa kusa da Inna idannuwanta tarr cikin nata ta ce" Ina yayata?, Ke ina yar uwata?"

Umma ta ringa son nuna mata ba fa su kadai bane ta hanyar fadin" Ban gane hausarki ba fa ni, wace yayarki kike tambayata a nan ni kadai ce mutun?"

Inna ta kunce zaninta ta mayar da shi saman cikinta ta daure shi tam, ta fuskanci Umma muryarta a matukar tashe ta ce" baki gane cewar a yanzu na kai matakin da bana tsoron kowa da komai sai mahalicina ba? Ya dace ace kin jima da karantar haka a cikin idannuwana, Habu yace yau dare na biyu kennan da ba'a ga yayata da mijinta ba, wai wata magana kamar ta yan giya ya yi musu da wani mutun ya masa alkawarin karar da danginsa, bari ki ji , gabs daya a tsarin nan da kuka yi babu abinda na yarda da shi, ku kuka sacen yar uwata da mijinta, ku fito min da su ko tarayar tamu ta yi gagawar watsewar da bakwa tunani na rantse maki da Allah a kan haka ko kaina aka sare bani da damuwa dan ban zabi duniyar fiye da kiyamar ba, na san cewa zamani muke ciki mai shudewa tunda uwata da ubana sun mutu nima tawa na kusa mutuwar, ke ina AUNTY FATIME DA MIJINTA!"

Wata irin sakaryar juwa ke son dibar NADIRAH a lokacin da ta fahimci inda innarta ta nufa, a hankali ta saka hannunta ta dan matsa kafadar Auta dake tsaye tamkar mutun mutuni tana son fahimtar inda magangannun nan suka nufa

Tana zuwa gaban Umma ta kalli Umman, ra kalli INNARTA

Inna hindu da bata daina kukan nan ba tana rike ne da hijabin Umma kan sai ta sanar mata ina yayarta da mijinta suke, ita kuma bakinta a dinke, zuciyarta na wata irin rawa da suya tana tunanin ya zama wajibi kennan a kashe auta kafin yayanta tunda mahaukatan nan suka tona asirin nan a gabanta walahi!

Muryarta a birkice ta ce" Innata, wai innar birni ce ba'a gani ba? To ama innar birni ai bata da yawoma ko?"

" Ba maganar yawo bane, gidan da aka kilaceki aka shiga aka sace su ita da Aban birni bayan an bugar da masu gadi da dayar algungumar!" Inna Hindu ta fada tana fitar da idannuwanta , masifa na ciciyarta dan ta riga ta rike matar nan yau sai ta nuna mata menene hannun surfe wa bilahilazi!

"Kilacewa?" Auta ta fitar da furucin a rarabe tana kallonsu

Gaba dayansu suka juyo sunna kallonta, sai kuma NADIRAH ta fara dauke dubanta ta sake mayarwa kanm UMMA, muryyarta a matukar sanyaye ta ce" Ama, ina ce mun yi magana mun ajiye, mun samu matsaya daya mun kuma yi biyaya ko?, Inace a kan abinda aka doramu muke bamu sauka ba har zuwa wannan lokacin ko?, Inace tsayin lokacin nan tsakaninmu da ku kune iyayen gidanmu, mune bayinku ko? Inace aikin kwatar rayukanmu muke yi tukuru, ba ji ba gani, innata na tare da ni a nan, ta zubar da gidanta, ta baro mijinta dan burinmu , mu yi mu gama muma mu samu sa'ida, ko kuma akoy lauje cikin nadi ne? Ina nufin ko kuma idan muka gama aikin ba za'a barmu bane muke ciki haikan?"

Umma ta kama gefen hijabinta ta ringa ja Inna na ja, a birkice ta ce" Ki cika min hijabi mana na samu damar yin magana!"

Inna Hindu da kyar ta sakar mata Hijabin Ama ta yi wata tsayuwa ta kaka gida a gabanta

Umma ta yi tsaki ta ce" Kawai daga jin magana sai ki nemi zuba min komai saman kaina bayan nima abinda aka kirayeni aka sanar min kennan har na fito ko alkyaba babu a jikina?, Kun zo kunna ta sakin magangannu a gaban yarinyar nan duda ni ba tsoronta nake ji ba kuma inada damar da zan sakata yin shiru koda a gabanta na aikata aikin nan, ama ku fa?, Zaku zo ku yi tsaye kunna wasu irin abubuwa bayan muma abinda ya daga mana hankali kennan ana cen ana nemansu?"

"Ana neman wa? Waye yake neman wa? Da wace siga? Da wani dalili? Ta yaya?, Dan girman Allah ki sanar mana abinda kuke nufi , wani nema zaku yi ne bayan mun san me yake nade a harshenku bayan kyakyawan furuci da shinfidadiyar fuska mai fara'a?" NADIRAH ta sake fada, a wani irin sanyaye, wara irin juwa na dibanta, tana ta son rike abu ama babu abinda zata iya rikewa karshe sai da ta samu kanta a kasa warwas domin Juwar nan sai da tamakata a kasssss

A rikice su biyu suka yi kanta, watau Auta da Inna Hindu
Taimaka mata suka yi suka jinginar da ita da kujera Auta hankalinta na sake tashi

Umma ce ta ci gaba da magana, babu abinda ya dameta da faduwar ta NADIRAH , itama damuwarta ta isheta ana neman dora masu laifin sace mutanen da basu sace ba, a sanninta dau basu sace din ba, in dai ba sarauniyar Tanus ta saka aka sace din ba to fa bata da takamaimiyar amsa , da son convincng dinsu ta ce" Cewa ta yi an fito daga masalaci suka yi fada shi da wani mutun a gaban kowa mutumen ya ce sai ya kashe shi da danginsa baki daya, kuma ga sheda nan an kwashe su, an ce mutumen kamar wani kasurgumin dan ta'ada, wai yannayin halitarsa mai saka a ji tsoronsa ne , shikenan sai ku ce mu ne? Mu bamu dauke su ba"

Zuciyarta dake beating da karfi ta dafe tana lumshe idannuwanta zazafan hawayenta suka shiga gangarowa a saman kumatunta
Innalilahi wa inna ilaihi raj'une
Dishi dishi take kallon yadda rigima ta kaure tsakanin innarta da UMMA babu mai ba yar uwarsa hakuri, ita kuma auta magangannun dake fitowa daga bakinsu ke neman tsayar da numfashinta, bata san haukan nata ne ya motsa ba ko menene har take tunanin matar da take ji a ranta a yanzu fiye da kowace mace a matsayin yar uwa rabin jiki, da matar da take kira Mamah bayan mahaifiyarta ba ainahin wace take zato bace na neman sakata jin kamar zata shiga a hali na hauka ya saka babu wanda ya ji motsin NADIRAH, basu ankara da ficewarta ba, sai karar rufe kofar da suka ji wace ita dinma dan ta murda Ky din wajenta da ta cire ta mayar da shi ta baya ta rufe suka gane cewar wani zai shigo, ko wani ya fita

Cikin Umma daga sama sai da ya dawo kasa, lokaci daya ya shiga bada wani kuka kuuuuuuuuuuuu alamu na gudawa na tatara kanta sannan wata makirar zufa irin ta saman goshin nan tace Bismillah, lokaci daya ta karra jin bata yaba fuskantar fargaba da tashin hankali irin na yau, lokaci daya kuma wajen ya dauki shiru ya zanto kamar babu wata halita a wajen , kowa ya yi tsittt hanyar yake kallo da jiran wanda zai shigo, dan babu wanda ya gane cewar fita aka yi, ba shigowa ake son yi ba

Wanzuwar shirun da ya yi yawa ya saka INNA HINDU karasawa ta leka

Idannuwanta ta kankance tana hango abinda take gani, watau babu KY din wajen, Hakan ya sakata zarro ido ta juyo tana kallon UMMA da a lokacin take ji a cikin jikinta kamar lokacinta ne ya yi, irin yadda zuciyarta ke dokawa da karfin masifa kamar zata bar gangar jikinta

Sai da ta watsa Hannayenta, sannan da bakinta ta ce"
10/5/22, 08:44 - Buhainat: *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍?*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*


🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻
*OUMOUGHLOUK ITIBEL*
_(ZAKIN SARAKAI)_
🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻

_FREE BOOK_

*Na*


*SAJIDA NIGER*





5️⃣7️⃣



Tabas baya gane komai, domin gaba dayanta ya dauketa ya karasa saman bed da ita
Sai da ya rikita mata jiki iya rikitawa, sabon salon da ya dauka ne watau sai da ta nemi fasa ihu dan rikicewa da irin salon nan nasa sannan ya auna mata lamarin nan nasa mai wuyar fasara
Ya jima yana abu daya sannan ya samu saukin nasa lamarin, inda mararta ta dauki dumin da take dauka a kwanakin nan ta yi wani iri kamar ya ajiye mata wani dutse a wajen

Hannunta dake kai idannuwanta a lumshe ya dauke ya dora nasa a wajen a hankali yana dan shafa wajen, ya kula yanzu in dai zai tabata ko yayane in dai har ya shigeta sai ya ringa damkar mararta

A hankali ya ce" Ko dai baki samu nutsuwa bane ?"

Jajayen idannuwanta ta dago a raunane ta tsare fuskarsa da ido

Nasa idannuwan ya lumshe mata, kasa kasa ya sake cewa" Na saka harshena?"

Ds karfi ta rintse idannuwanta tana son juyar da bayanta, ama ya kiya, a dole ra tsaya masa yadda yake so din, sai sake nanikar wuyanta yake yi ciki ciki ya ce" Kin ga, idan na yi kiranki dan Allah ki ringa zowa kin ji? Baki san ba kyau ba? Jiya fa da yau ranarki ne, ke ko irin a sayi zuciyar mijin nan bakya siya? Ki dan tausaya min mana maraya ne ni fa"................


Bakinta dake ta neman fasa ihu ta kwashashabe a hankali ta daka kuka irin na sangarta da shagwaba da kuma ambaton maraicin da ya yi tana kallonsa ta ce" Nima ai ina daf da zama marainiyar, kilama na zama, wayo Allahna innar birni"

Fuskarta ya zubawa ido, dan kuwa da ihu ta fadi haka din kuma ta wani dafe kyakyawar fuskarta , watau dai kukan na daf da balewa

Dan murmushi ya sauke ya gyara zamansa da kyau kasa kasa ya ce" NADIRAH"

Dif ta yi da kukan ta dago ta saka idannuwanta a cikin nasa tana kallonsa da Expression din son karra jin furucinsa

Dan murmushi ya yi dan sarai ya gane so take ta ji BAHIJA yace ko NADIRAH, ya rab ya so ya jima yana tsokanarta da haka, sai dai gaba daya ji yake yi bashi da karfin yin haka kwata kwata, yayama zai iya yin haka dogon zango bayan kuka take yi da hawayenta? Bai ce ba zata iya yin kuka ba a rayuwa, ama ba zai so ace shine sanadiyar hakan ba, a tausashe, dan ya tabbatar mata eh ya san me ya fada ya sake maimaita sunnanta idannuwansa a cikin nata

Ido ta zarro, gudun zuciyarta ya dadu, da sauri ta nuna kanta da yaren bebanci ta ce" A san ice Indi?" (Ka san nice Indi?)
Ita da kanta bata san ta iya yaren bebaye ba sam

Murmushi ya yi ya gyada kai, a hankali ya ce" Na san ke ce Indi, na kuma san kece yar gidan INNA HINDU, da BABA HABU, da inar birni fa kuma Aban Birni"

Kirjinta ta dafe, sai kuma ta yi saurin zarro ido, da sauri ta silalo kaffafuwanta ta mike haihuwar Innar birni ta nufi bayi da gudu halitun bayanta na auka sittin saba'in, hakan ya saka shi zarro idannuwa ya sake zubawa kofar da ta bude ta bari a bude ido yana sauraron zubar fitsarinta a cikin WC har ta gama yana jiyo zubar ruwa da wankewarta ta gama ta fito yanzunma a kidime jama'a ta kasa tuna a yaya take tsaye a gabansa ta yi tsaye ta rike gugu, ko iskar sanyin AC bai ankarar da ita cewa mikowar ingozoma take ba, hankali kwonce ta masa tsaye da bindigun kirjinta ta shiga bayani tana kai kawo irin na oga a office , ko hamshakin da yake yin bayanin da yake so a fahimta, kuma a haka take so ya fahimta , ta yi ya kai sau uku tana masa zannen da ya jima da sani watau wacece imnar birni, waye aban birni da na kauye sannan ta juyo ta ce" Wata rana ne, muna zaman zamanmu, mun gama yin fada da Aminu fa innarsa , innarsa ta leta rantsuwar ba zata yarda da aurenmu ba, na cewa tawa innar ta yi hakuri zan hakura idan ta sheka lahira ko mun tsufa ne ba komai sai mu yi aurenmu, sai kawai innata ta ce zata zo birni da ni wajen bikin kawarta da ta haihu, nufinta kafin mu koma na huce sai mu yi zamanmu, ashe ashe harda nufinta ta ji kishi kishin din za'a yiwa Aminu suren dole da wata yar gidan ladan dake sonsa, kai dai wannan shine farkon shigarmu tashin hankali mai zaman kansa, domin a zuwanmu birni ashe marabinmu da kauyen LABBA kennan, muna zuwa muka tarar da ........"


"Ke, dakata min, idan kika kuma ambaton sunnan wani kato a gabana NADIRAH, zan karra nuna maki nima kato ne, kuma dukkan abinda yake iya baki ina iya baki shi , koma fiye da hakan malama!" Ya fada a kausashen da bata taba ganninsa ya yi ba, bayan ya mike daga saman gadon fuska a hade harda su nuno mata hannu, domin yana cikin binta da kallo ido na masa radadin tashin hankali ta wani katse masa farin ciki da sunnan wani kato, wollah kamar ta wanka masa mari ya ji

Ido ta zarro ta juya ta ce" Baka da sutura fa "

Goshinsa ya dafe dan takaici , jama'a ita tanada ita ne? Gaba daya so take yo ta caza masa kwakwaluwa bayan ana abun arziki
Muryarsa da amon bacin rai ya ce" Juyo min nan ki ji, a hirarki idan kika saki kika ringa sako min maganar wannan shedanin mai bin zuciyar mace gidan miji sai na babala maki du abinda na warto, kuma sai na wuni a kanki a dakin nan yau koda mayar da ke zan yi kamar tsohon zani sai dai a dinke ki kamar kwarya!, Aminun da kike hauka kansa yana cen mata biyu innar tasa ta aura masa har sun dauki ciki ni kina nan kina juyani kamar waina a cikin tanda, ki kuma min maganar Aminu ki gani!" Yana gama fadi ya juya a haka dinsa ya shige bayi, hakan ya sakata sake zarro ido tana kallonsa har ya bacewa ganninta

Bakin gadon ta zauna tana mamakin dama ya iya masifa da ihu wa mutane haka?, Dama ya iya fada murya a dage haka? Me ta masa? Ba ko tausayi? Ba zai tsaya ta gama masa maganar dan ya fahimci basu san komai ba? Innalilahi wai harda su cewa Aminu da mata biyu kuma da ciki, yo Aminu ko farcen mace ya kalla bayan nata ne? Hum za'a hadata da Aminu kiri kiri

Fitowarsa da tawul da karasowarsa bakin gadon ya zauna saman kujera ta bakin hado murya a hade ya ce" Ci gaba" ya sakata sada kai a ranta tana mamakin manyan gaban jikinsa da ginanen jiki irin nasa

Murya a tausashe ta ci gaba da sanar masa abinda ya faru dala dala, har zuwan su UMMA garin, wanda daga zuwansu ne aka saka aka kirawota, da kilaceta da aka yi, da irin gyaran da ake bata, a nan ne ya ringa yi mata tambayoyi a hankali, yannayin amon muryarsa kuwa na amayar da déception, yakan kawar da kansa gefe ya dauki dan lokaci yana fitar da huci sannan ya juyo inda take, ya sale bata damar idasa maganarta

Idannuwanta na kallon kirjinsa, wajen da ya fi bata sha'awa a jikinsa bama idan baya da riga, a sanyaye ta ce" Shi kadai ya zo ya daukeni, a gaban INNAR BIRNI, tana kuka tamkar ranta zai fita, a lokacin da zata sakani a motarma ta sake jadada min magana kamar haka NADIRAH, DUK RINTSI, KAR KI ZUBA MAGANIN DA ZA'A BAKI, KO KI FESA ABIN FESAWA, KO DUK WANI LAUNI NA HANYAR KASHE ABAN DATAWA, KAR KI CE BARI KAWAI KI AIWATAR KI DAWO KI SAMU YARON DA AKA RABAKI DA SHI, KI SANI SUNNAN HAKA KISA, A JAHILCIN DA AKE MAKI IKIRARI KUWA BOKO CE BAKI TSAYA KIN YI BA , INDIN HINDU KI RIKE AMANAR BAWAN ALLAH MARAYAN ALLAH KIN JI?"

Idannuwansa ya lumshe a sanyaye , yanzunma a sanyaye ya sake zuba idannuwansa a cikin nata yana kallonta
Haka kawai ta ji ba zata juri kallon ba, dan bata daba gannin idannuwansa da rauni ba, bata saba kallon idannuwansa na neman agaji ba, bata san haka a tatare da shi ba

Da kyar ya iya cijewa, ya sake bude bakinsa a sanyaye ya ce" Dan Allah, kar ki ce min a zuwanki gidan nan, a fahimtarki harda HUZNAH a cikin wannan rikici kin ji? Kin ga HUZNAH matata ce, matata ce wace ta nuna min sarki ko ba sarki ba tana so na, kuma na yarda da hakan Nadirah, nima ina son matatah, dan Allah kar ki ce min harda ita a cikin wa'inda zasu hadani da bugun zuciya?"

Haka kawai ta ji wani irin suka a daidai lokacin da ya yi furucinsa, haka kawai ta ji wani irin zafi a cikin kahon zuciyarta, har ta ji kamar wasu hawaye na cika cikin idannuwanta

A hankali ta ringa jin sanyin da bata ji a dazu, harma ta samu a sanyaye ta janyo abin rufar dake saman gadon ta dan raba a jikinta

Idannuwanta da suke ta yawo a tsakiyar tsadaden dakin ta maido sakan tsadadiyar kafarsa mai dauke da ni'imtatun kashin jiki luflufluf sun yi baki sidik sunna ta sheki, sannan ta ajiye a kan yan yatsun kafarsa masu tsayi summa samansu akoy gashikan nan
Kanta ne ya sara mata, lokaci daya ta ji wani irin zufa da zazabi na son keto mata

*HUZNAH* sunnan da mamalakin sunnan , halitar da bata taba kayar mata da gaba ko sakata a hali na jin kishi a da ba, me yasa ambatonta a cikin wasu kalamai na bakon rayuwarta a yanzu suka sakata jin sunnan gaba daya bashi da wani tsari ko dadi a baki? To ita me yasa iyayyenta suka saka mata wani wai HUZNAH? Filon cen filon kawai, sam bata da tsari kwata kwata fa sai kyan jaraba!

"NADIRAH" ya fada a sanyaye yana so ta yi masa bayani, duda irin faduwar masa da gaba da bayanin nata ke yi na yanzu, dan sam baya so wani abu mai zafi ya fito daga bakinta a kan HUZNAH, anya zai jure na HUZNHA kuwa? Huznah matar rufin asirinsa ce, ya kirta nata ba dadi ta dawo ta likun masa, a ransa yake ji Huznah matar da zata tarbi mashin da aka harbo masa ce ba ta labe a bayansa ba, idan kuwa ya ga akasin haka an shige shi sosai Walahi

Ita kuma da ta dago ta zubawa jajayen lebensa ido sai ta ji a nan fa gaskiya kamar sarki bai yi adalci ba, yo ta yaya zai ringa saka H a karshen sunnan HUZNAH yana wani karasa fada a sanyaye ita kuma ya wani ce NADIRA gatsau ba sakayawa? Oh wato shine namiji mai nuna ya fi

Please Login or Register in order to submit comment