Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wani hamshaki ba, sai kuma ta tabe baki ta juya hannunta na dama daga wancen bangaren

Ido ta zubawa wanda ke zaune a nan, cikin shiga yake ta simple doguwar riga fara kal kal kal , kansa baya dauke da hirami ko hula hakan ya bayanar da lalausan gashin kansa, hannayen doguwar rigar kuwa har kusan tsintsiyar hannunsa daidai da agogon da sai da ta karra zuba mata ido domin ko a ido ka kalleta ka san ba ta yara kannana bace, watau ba ta mun taso nace, ta ginanu ce har zuwa dan madaidaicin Alkur'anin dake hannunsa

Wani irin yarrrrr tsigar jikinta ta bada, a hankali ta dan cire dubanta , sai dai tana juyar da kan nata ta sake juyowa ta kuma zuba masa ido, gashin kansa zuwa na girrarsa da na idannuwansa da dogon hancinsa da bakinsa sun fi komai daukan hankalinta

A hankali ta dora hannunta daidai zuciyarta tana jin yadda take wani irin buga mata

Da sauri ta rintse idannuwanta tana jin tamkar zata summa dan wani irin yannayi mai karfi dake sake ziyartarta........
'Ya salam, wannan wanene a cikin garin AGADAZ? bako ne ko dan gari? Wani yare ne? Daga ina ya fito? Hasbunnalah..........' shine abinda take ta ayannawa a cen kasan zuciyarta, har aka gama maganar a daura belt da sauransu suka daga hankalinsa a kan Alkur'aninsa, ita kuma hankalinta a kansa......ta kasa gaskata irin dokawar da zuciyarta ke yi a kan wannan bawan Allah............ Ta yarda yau ta hadu da wanda yake daidai da ita




.....A hankali ta dan sake gyara hijabinta da kuma alkyabarta ta yi dab gyaran murya dan baban burinta shine wannan bawan Allah ya dago idannuwansa su yi ido hudu da junna, sai dai kashhh har sadaden barcin dake surarta idan tana cikin tafia ya saceta bai dago din ba,


Sai da ya kai karshen karatun da yake yi a hankali ya rufe Alkuranin ya rike shu a hannunsa ya kai dubansa kan Amintacensa yana dan masa alamu da agogo dan son sannin lokaci duda ta hannunsa dake sarkafe ama bai duba ba

Lokacin ya sanar masa yana mai girmamashi sannan ya sake aunawa idan har sun yi tafia mai kyau nan da awa biyu sunna iya sauka domin sun yi tafiyar da dan yawa

Sake komawa ya yi ya gyara zamansa ya 'unshe idannuwansa yana tunna Auta, ko yaya juwar? Ko ta saketa? In sha Allah idan ya dawo zai gayato mijinta ya zo su wuni tare ko zata ji dadin hakan, shi baya so ne idan ya zo din nan ta ringa kukan sai ta bishi, bayan a yanzu shi babu inda zai iya barinta ta je nesa da shi, sai ya gamsu da yannayin lafiyarta, ga Umma a kusa tana hakuri da ita sosai tana kula da ita, bata yadda amana ba, bata yadda zumunci ba, ya tabata wata rana Auta zata dawo normal irin na kowace mace

Dan murmushi ya yi, idan har ta dawo haka, yaya zai yi da farin ciki? Ya Allah ya nuna masa
8/13/22, 22:55 - Buhainat: *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍?*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*


🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻
*OUMOUGHLOUK ITIBEL*
_(ZAKIN SARAKAI)_
🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻

_FREE BOOK_

*Na*


*SAJIDA NIGER*




0️⃣7️⃣




Dan murmushi ya yi, idan har ta samu lafia ina zai saka ransa dan murna?, Ya Allah ka nuna min.....ya yi wannan addu'a a kasan zuciyarsa



Lafiya suka sauka a baban Birnin MADINA garin Manzo

Tsakanin aéroport din da Hotel din da suka dauka da dan tafia, kasancewar ga gajiyar jiya, ga ta yau sai suka shige taxi su hudu suka nufi BABAN hotel din NOZOL ROYAL dake Abi Obaida ibn al jazrah street

A hanzarce take, karra kallon motar dake gabansu biyu take wace ke dauke da mutumen da kuma jama'arsa, Adu'a take yi a zuciyarta Allah ya sa kar Motocin su bace masu, haka kuma ji take yi tamkar ta kwace motar ta tuka da kanta ko zata samu ta sada kanta a Hotel din nan

Sunna karasowa shi fita ya yi ya yi gaba, Mutanensa suka tsaya biyan kudin, a lokacin ne itama ta fito tana mikawa Baiwar jakarta ta ce" Biya shi" da sauri ta shiga bin bayan wannan bawan Allah

Kasancewar tun daga mettre dari ake tarboka dan a sadaka da dukkan abinda ya dace a wannan Hotel idan ka sauka a cikinta ya saka bai tsaya tsaye tsaye ba ya dan zanta kadan da balaraben dake yi masa magana cikin yaren larabci yana mai tambayarsa sunnansa da kuma number dakin fa akace masa an cirar masa

Dan tsai ya yi ya dan shafa gaban goshinsa kafan dan shi kam bai san number dakin ba tunda ba shi ya cira ba gaskiya,
Dan waigawa ya yi dan gannin ko sun zo, sai ya ga ta juya da dauri daga kallonsan da take yi
Murmushin takaici ya yi yana basarwa, ya tabata bata gane shi ba, tun a cikin jirgi yake mamakin irin yadda ta lakanci kallo kamar wata bagidajiya, sannan da ya ga tana yawan kallon mutanensa ya zata ko ta ganne su ne? Shi dama gaskiya ba zata gane shi ba, dan ba wannan damar, idan ba na gi da gi dinsa ba ba wai lalle ka ringa ganninsa ba rawani ba, shima a lokacin da ta cika kallonsan nan gaba daya ya ringa ji a jikinsa an kura masa ido, da farko yaronsa ya duba ya zata ko shine ke masa kallon nan dan ya ji dalili? Sai ya gane ba su bane, asalima suma sun dan damu da yannayin kallon nata, sai ya basar ya ci gaba da karatunsa sai da ta yi barcin nan ne ya dan dubeta , kamanin mahaifinta ya fara ganni sai kuma suka karra tabatar masa itace yar gidan Bafansa ce

A tausashe ya ce"ها هو الشخص الذي أخذ هذه الغرفة من أجلنا" ( ga wanda ya kama mana dakin nan zuwa)

Ido ta zarro, a zuciyarta ta ayana 'Ya salam, balarabe ne ashe? Wayo Allahna, Ya Allah ka bani ikon tunkararsa '

Da sauri suka karaso ya fadi dakunnan, hakan ya sa akai masu jagora

Idannuwanta sun gama rufewa, neman binsu take yi a lokacin ne mace yar uwarta cikin shiga harda nikaf da safar hannun ta tareta tana mai yi mata salama da fara kwatanta mata da tambayarta bata basu dakin da ta dauka ba kuma tana neman shiga lft

Ido ta ringa zarrowa, hankalinta na neman tashi
Ta san a nan kasar da ta sauko darajarta daya da baiwarta
Babu wanda zata yiwa tinkaho ko isa, hasalima ba kowani balarabe yale mu'amalantar bak'ar fata da mu'amala mai kyau ba, duda ita din fara ce kal , ama kuma bakinta baya dauke da larabcin da matar nan ta yi mata

A hankali ta ce" S'il vous plaît pouvez vous m'expliquer en français ? Je ne comprends pas très bien l'arabe " ( Dan Allah ko zaki kwatanta min da french, domin bana fahimtar larabci da kyau)

Matar ta dan yatsina fuska ta juya ta koma ta fada a cen cewa matar cen freinch kawai take ji, dan haka aka turo mata wanda ke jin freinch

A nan ya fada mata komai cikin nutsuwa

A sanyaye ta ce" Kennan idan har mutun mai dauki daki tun daga gidansa ba, ba zai iya samu ba?"


A tausashe ya ce" Gaskiya da wahala, ama bara na tambaya idan har akoy dakin da ba'a kama ba sai ki kama"

Tana tsaye ana ta aiki da computer, kwararun ma'aikatan sunna ta aikinsu

Wata mata da ta kama wani daki ta ce kawarta ta kamama suka sake tabowa, nan ta sheda masu kawar tata tace bata san dakin a wani hotel bravia zata sauka, dan haka sai suka cenza sunnan suka bata dakin sunna yi mata bayani kamar haka" Zaki ji dadin Hotel Nozol royal, domin a wannan waje akoy tsafta, akoy restaurant, sannan tsakaninta da kofar baban masalaci Al-masjid al nabawi tafia ce ta yan mintuna 10, kana yi kana hailala, sunnada gadaje uku, baban gado na Queen royal, da gadaje biyu, sunnada bayi tankameme guda mai dauke da jakuzi, ruwa na shower, WC, da kuma Buta ta karfe, a kulun za'a cenza maka abin shinfida da na rufa koda baka kwonta a sama ba, sunnada kur'anai da abubuwan sallah, idan budurwa ce ke bakida damar kawo maza wajenki, idan matar aure ce ke wanda yake da damar shiga wajenki mijinki ne,kina iya shiga dakin motsa jiki na mata, sannan akoy parking space idan kina iya hayar motar da za'a yi yawo da ke domin bakuwa kike ba zaki yi tuki da kanki a Madina ba, bakida takardar yar kasa, kudin parking din du minti talatin sarl biyar ne ba tsada........."

Ita kam dakin ta shige tana kallonsa ta ce" Na gode"

Kai ya gyada ya yi baya dan ya kula ta gaji ya fice


Da sauri ta cire Alkyabarta da abin wuyanta ta ajiye a nan ta ringa kai kawo farcenta daya a cikin bakinta kanta tamkar zai tarwatse da tunani


A hankali baiwarta ta dan duka ta ce" Allah ya karra maki lafiya, me kike da muradi kafin ki shiga wanka? Sai kin shiga kin fito zaki ci abinci ko kafin ki shiga za......"


"Dan Allah ki barni da maganar abinci da dukkan abinda ya shafe shi, ba kin ga mutumen da muka taho tare ba, ga wannan kudin ki rike idan kin ji yinwa ki nemi abinci ki ci, ki sauka ki samo min wani daki yake, kar ki dawo sai kim samo min kin ji abinda na fada!"


Jiki a sanyaye ta amshi kudin, zuciyarta na bugawa

Wai mutumen da suka biyo wanda ke tare da baban bawan garin AGADAZ? To ita bata ji numbobin dakunnan da suka dauka bane? Ko kuwa?


Har ta juya zata fita sai kuma ta dawo ta sake zubewa a kasa ta sheda mata ai gafa numbobinsu na dakunnansu


Wani irin ajiyar zuciya ta sauke tana jin wani sanyi mai dadi na ratsata

Har ta daga kafarta zata fice, sai kuma ta ja tana kallon jikinta

Muryarta har rawa take ta ce" Ki bude akwatina ki ciro min abayata wace ta fi kyau, ki fitar da turare ki yi mata wanka sannan ki shigo bayi ki cudan bayana....." Haka kawai ta ga ya dace ta dauki wankan da ya dace dan ta leka bawan Allahn cen, ya Allah bata taba jin namiji ya shiga zuciyarta irin na yau ba, ji take kamar zata summa, gaba daya ta manta tabo kawar tata da tace ta sanar mata Hotel din da ta sauka dan tace mata ko ta kama mata daki a Hotel din da suka sauka da mahaifiyarta ko me? Ita kuma ta kiya domin ba zata so ta shiga dakin yaku bayi ba gaskiya, ta so ta je Hotel din da suke sauka sai gata a nan, duda kudin dakin ya bata mamaki tsadarsa haka ta dauki adadin kwanakin da take so ta saka masu kudin.....bata tunanin zata iya barin wancen gayen a yau


Bayan ta shige ne aka sake kira, kawar tata ce, a dole baiwarta ta daga dan idan bata daga din ba tana iya jawa kanta matsala
Da girmamawa ta sheda mata cewa ai a Hotel Nozol royal ne suka sauka

Da mamaki kawar tata ta ce" A wani daki? Nima a nan din nake ai, nan din ne na kama mata ta saka na yi annuler, gani nan zuwa!"



Wannan kennan

______________________________________


Hasken farin watan na yau ya masifar haska lungu fa sako na kauyen LABA
Ga kuma fitilun aci balbal fa suka kunna harda gagan samarin da suke da Uba sanjo ya kasa watau wannan fitila mai shegen hasken tsiya sun kunna sun dage kafa sunna kallon yan matansu na wake ana shewa da tafawa abin gwanin birgewa

Aminu ne ya yi murmushi yana kallon NADIRAH ya ce" Ta Aminu kin tabata yau zaki yi rawa a dandalin nan? Ta Aminu a kanki in ba sai na yi karin hamsin ba ubana goma!"


Fari ta yi da idannuwanta ta kara gyara tsayuwarta ta ce" Aminun Indirah, sha kuruminla ka huta, mu bakwai ne zamu shiga ai yanzu yanzu, dan haka gyara aljihunka, ka dan dai ido a kanmu gaskiya yau ka saki kudi ka ji Aminuna?"

Wani irin murmushi ya yi ya cira kai ya ce" Barama ki ga na karo a wajen Mutaha"

Da ido ta rakashi har ya bacewa ganninta, haka kawai ta samu kanta da sakin yar dariya har tana rufe bakinta a lokacin da ya bacewa ganninta

Yar dubu da ta dawo dan kamota su je su shige rawar ta tsaya kallonta ta ce" Dariyar me kike yi haka ke kuwa?"

Murmushi ta yi tana sake dora daurin zanninta a saman rigarta mai hoto ta ce" Wai ki ji fa Hindu cewa ta yi walahi ifan Aminu na tafia kamar wuyan rakumin jeji, shine yau na ga ya yi gaba wuyan ashe zolo zolo yake biyarsa......" Ta karashe tana sake fashewa fa dariya dan har ga Allah abin ya shamaceta, kai Innarta? Innarta sai ta kasheta wata rana,

Itama dariyar take yi ta girgiza kai ta ce" Ai kuwa ke kin san du kauyen nan babu ya Aminunki a gayu, zo muje dan Allah daga lamratu fa sai ni sai ke a wale, yau Adamu ya zo kallo Allah ya sa ya dubeni"

Binta ta yi suka shige layin yan matan dake wake, kowace idan ta shigo da kalar bajintarta take kada abinda ta san tanada shi ta wake samrayinta ta koma, idan da yan cenjinsa tsaf ,ai shigo ya zuba mata su, idan babu kuwa abinda yake da shi zai yiwa makadin kyauta da shi


Murmushi take yi a lokacin da Yar dubu ta yi wakenta tana kallon wajen Adamu, ama sam sai ya ki shigowa ya mata kari, karshema hala ta kusan gamawa ba'a yi mata ba


Tana rangaji ta je ta dauko Uba sanjon Aminu hankali kwonce ta kai gaban makadi ta ajiye ta rada masa magana kamar haka" Na yiwa kawata kari da Uba sanjon nan, in da budurwar da ta isa ta tarbi uba sanjon saurayinta ta dauka ta yi kari da ita bismillah, Aminu ya saka min albarka, kuma zan yi rawa da kalabina a saman kaina idan ya fadi na yi alkawarin yiwa Aminu gabar kwana biyu!"

Ihu aka dauka, makadin nan har saba babar rigarsa yake ya mike ya biyo bayanta ya sanar da danarwarta sannan ya gyara yar gagarsa ta kofi ya shiga kada mata

Sai da ta yi gamo da fan kwalinta ta dora saman kanta sannan ta gyara tsayuwarta cike da bege ta shiga rerawa Aminu waka , ga fitinaniyar rawar da HINDU ta koya mata, wai rawar daka, jama'a rawa ce tamkar babu yayan hanji a cikin mutun, rawa ce tamkar kugu zai tsinke ana wani irin abu kamar babu komai sai duwawun, watau rawa dai irin ta SHAKIRA

Har zanzana Aminu yake yi a lokacin da ya shige filin nan ya ringa mana mata yan goma goma a goshi yana bubudewa

A kadan sai da ya zuba mata sitin da biyar ya laluba ya laluba sai kudin innarsa da ta aike shi kaiwa na dashi

Wani irin zigashi da ake yi a yau ko mai gari ya ji sai gabansa ya fadi, shi ya san a kan NADIRAH ya shiga gaban maza, dan haka ya zarro kudin zubin dashin Innarsa ba tare da tunanin komai ba ya kalli makadi, makadi ya kalle shi ya shiga zarra yana zuba masa jiki har rawa yake


NADIRAH ta fara zarro ido tana kallonsa, hakama jama'ar gari, ihu fa waje ya zagaye kira ake Aminun Indirah wuta Aminu wuta aminu, Aminu na wuta ba ji ba ganni

Kanwarsa ta juya ta dankara a guje ta nufi gidansu har taka karangiya take yi, ama bata damu ba, baban burinta ta kaiwa Innarsu labarin cewa lokaci ya yi da zasu kai bayin Allan cen baban birni a masu tsakani, ga danta cen ya haukace ko kudin teburin nasa ya amsa yau yake bayarwa ko yayane? Abu dai ya giga Aminu ya bale









☹️☹️☹️☹️ Aminu ya balle jama'a mun shiga uku, Nadirah mata saman kanki ga inna nan tafe🤣😁😁😁





Cmmnt, sabon posting 😁
8/13/22, 22:55 - Buhainat: *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍?*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*


🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻
*OUMOUGHLOUK ITIBEL*
_(ZAKIN SARAKAI)_
🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻

_FREE BOOK_

*Na*


*SAJIDA NIGER*




0️⃣8️⃣



Raf Nadirah ta yi da hannunsa a lokacin da ya sake nufar aljihunsa ta tsayar da rawar tana kallonsa ta ce" Kai Aminu kudin nan fa? Ko kijmashin ka fara?"

Sai a lokacin Aminu ya tino a cikin wani kudi ne yake baje kolinsa

Idannuwa ya zarro ya kalli makadi, makadi ya kalle shi
Gabansa sai da ya karra kwonci kwonci ya rufto, sai dai lokaci daya ya ji wani karfi ya zo masa a lokacin da amininsa Adamu ya dafa kafadarsa ya ce" Kai daya kake tal gaya na Indirah ikon Allah, kai ja mata ja mai dogon hanci kaine zaka haifowa dan mai gari mata gaba gaba kauyen LABA tafin hannunka mutumena, dole ka yi jarumin gwarzon kauyen LABA kai daya gaya, ko jaka dari ka zuba a rawar nan ta yi elhajina, idan baka daka da karfi ba watarana a gaban idannuwanka za'a cireta, nake fada maka Indirah ba karamar kadarah bace tanadinta mayar da kudi gida ne"

Daria ya yi yana gyada kansa ya kalleta ya ce" Saki aljihun mana Indin Aminu?"

Nadirah ta girgiza kanta ta ce" Wasa kake Aminu, kudin wa ka samu kake bararwa haka? Kardai na shago ne kake yiwa barin mahaukaciyar nan?"

Kamata Yar dubu ta yi ta jata tana fadin" ke zo mu tafi, mu je mu je ga cen su hansatu sun kaure da fadan karin da Aminu ya yi, wai Hansatu ce take fadin a da fa Aminu ita ya so? Mu za'a kawowa bidi'a? Sun ha Aminu ya yi kudi za'a fara kawo masa hari ko? Aminu na INDIRAHn Yar dubu ne ba wata shegiya walahi!"

Sakinsa ta yi tana kunce dan kwalinta ta ci damara ta ce" Ta samu , mu je, yo a kan Aminu in dan ni a kwana ana tseren rai a garin nan, sai gobe masoyi....."

Daga nan wajen fadan nan suka je aka casu da su, Yar dubu kam ta jigata, ita kuwa ta sha dukewa domin ba zata yarda a lalata mata fuska ba gaskiya, da kyar suka raba kansu da kansu suka raka kuma tare ana tafe ana zaurance da yade yaden magana har kowace ta karasa gidansu ta shige


*Safiya maraicen kura in ji yan magana*


Bankadowar kofar gidansu ya sakata sakin tulun da ta nada gamo ta dora a kanta dan ta je ta dibowa Innarta ruwa a rafi

Butar da HINDU ke kuskurar baki ta ajiye tana tafa hannayenta ta ce" Zan ga annabi idan na yi hali na gari, yanzu Indirar inna ba zaki daina kashe min tulu ba? Kin san tulun nan mu uku muka yi jayaya a kansa dan yanada saurin sanyaya ruwa? Kin fashe shi Indirah saura wancen na babanki shima ki dan dauko ki maka a kasa sai mu huta!"

NADIRAH ta hadiyi yawu tana dake kasa kunne tana jiyo muryar innar Aminu a kofar gidansu

Dam dam ta karaso ta rage murya ta ce" INNATA kamar muryar Inna Aminu fa, bakya ji tana fadin idan bai shigo ba zata muka masa faskare?"

Kaffafuwanta ta janyo da kyau ta yi zaman yan makaranta tana kallon NADIRAH da sin karrin bayani, me kuma zai kawo innar Aminunta a karro na biyu gidan nan? Mema ta aikata to?


"Allah jikanmu!" Innar aminu ta fada a takaice ta daka hannunta ta tankado keyar Aminu ya yi taga taga ya dake dukawa kansa a kasa , kana kallon gefen fuskarsa ka san ya maru bawan Allah

Ido Hindu ta zarro ta zabura ta mike tana fadin" Ke bani hijabi ashe siriki ne da asusuba ko hantsi bai fito ba da Innarsa, Allah ya sa alkhairin da ya saba zuwar mana da sanyin safiya ne ya zo mana yauma"

Rai bace innar Aminu ta ce" Zaki fadi haka, zaki fada haka uwar yan cin amana da cin zali, to bara ki ji Hindu ni nan innar Aminu a kan wannan mai ido ya na mayun sai na tsine masa albarka, ace na bi kasuwani, na sha zafin rana, na yi dakan fura na samo kudina na dashe ya je ya zubawa wannan la'ananiyar? Ni kuwa ai aure da Aminuna da wannan y'a sai dai idan kasa ta birni idona, kai dan Ubanka ka amso min sauran cenjin a wajenta ko sai na jibga maka faskaran nan ka summe kowama ya huta?....." Ta karashe da tartsatsin ihun da ya saka Aminu sake sinne kai

NADIRAH hankalinta ya sake tashi, ta karaso ta duka tana kallon Innarta da ta ja tana kallon ikon Allah, a rikice ta ce" Inna kar ki tsine mana kin ji? Nawa ne kudin sai na saka Abana ya bani na kawo maki idan ya dawo daga birni, sababima zai bamu, ama inna ku daina shiga soyayarmu ni da Aminuna dan Allah, ni bai bani ko taro ba ki tambayeshi, ki daina dukansa kin ga fa ya yi uwa igiyar leko a ruwa"

Ai kuwa innarsa ta sake kifa masa mari tana hankade NADIRAH da gangan domin dama damar nan take nema

A zabure innar NADIRAH ta karaso ta saka hannunta ta hankade Innar Aminu sannan ta shaki kwalarta ta daga hannu zata rufta mata mari ihun NADIRAH da Aminu ya sakata dakatawa

Da ihu NADIRAH tana dira ta ce" Innata aa aa maman Aminu ce"

Shima a haukace ya ce" Inna kar ki yi mari ta hannani aurenta na bi duniya kar ki yi"

Lebenta ta dantse ta daki kwalar innar tasa ta shige uwar dakanta

Cen kasan gadonta na karaga ta lalubo asusun mijinta ta zauna ta fasashi ta shiga irga kudin dake ciki
Biyu ta raba ta fito da shi ta mikawa Innar Aminu tana kallonta ta ce" Asabe, ki ji tsoron Allah, ki ji tsoron Allah asabe, ki sanni Allah ya yi hanni da zurfafa soyaya ko kiyaya, sannan ya ce idan zaka yi soyaya ka yi dominsa, haka idan zaka ki bawansa ka ki shi dominsa, kar ki kasance mutun mai fitina da rashin son zaman lafiya, ki sani nima uwa ce, kuma yarnan da gatanta, ba shegiya bace, ba maya bace, ba barauniya bace, ba yar iska bace, dan rashin son gaskiya danki fa ya yi likin nan ba wuka ta saka masa a wuya ya yi ba, a duniya menene maza basa yiwa mata?, Na karashe maki magana ni nan na hanneta amsar sisin Aminu, ko rake bai taba siya mata ba, bata amsa , bata so , nace ta bari idan ita din matar aminu ce a gidansa ya ciyar da ita, bana neman kai da yarinyar nan, ban kasa rike abina ba, ki sani du abinda kike yi da amsu ziga ki ba masoyanki bane, domin baki tsaya a kan huja kakarfa ba sai wata bankadafiyar hujarki marr ma'ana, kin dage dan yarinyar nan ta cika kyau ko me? Shin ita ta halici kanta, idan zaki iya ki iya da danki ki hannashi shiga sabgarta, ni kuma na rantse da girman Allah daga lokacin da Aminu ya nuna baya ra'ayin indi ta fita a harkarsa kennan dan ki bar ganninta haka na isa da ita!, Sannan ke kin san daraja kike ci, kina min takakiya ki ci min mutunci har gidana ni ta sarkin makada ko?, Ba damuwa, idan har kika kaini bango nice zan tarda ke!, Ke kin san wacece ni, ina daga kafa dan na ga yara sun dage, aure kuwa ba'a yi masa haka, to bari ki ji na gama maki

Please Login or Register in order to submit comment