Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da wani shirin daban, domin da gaske Umma ta dage sai matar da aka daura masa ta zo ta gaishe shi, hakan ya sa ta ki zuwa kawota danma kar su dawo su tardo ya shige barci, sai kawai ta tura Baiwa cewar maza a rakota , idan ta fito jakadiya ta yi jagora a rakota


Sosai HUZNAH ta karra kimtsa zamanta, Auta kuwa ta bude litafinta tana nuna masa cewa zata bashi hardar wata Adu'a da ya koya mata a kauye


Baiwar ta samu shiga falon domin sakon UMUGHLUK ITIBEL ne


Tana shiga NADIRAH ta fito daga kicin, hannayenta sanye da safar hannu, kugunta daure da abin girki, girki suke yi ita da innarta, fuskarta da kwaliyar da akai mata, ama ta cire tufafin ta mayar ta ninke , gashinta a baje yake a bayanta, girki suke gwadawa ire iren WA'INDA masu gyaran nan suka koya mata

Har kasa Baiwar ta duka, kanta a kasa, domun ta tabata matar nan ko wacece ta jikin sarauniyarsu ce

Kanta a kasa ta gaisheta

NADIRAH ta amsa tana sake gyara daurin abin girkinta a kugunta

Baiwar ta sake sada kanta ta ce" Allah ya taimakeki, sako ne wajen sarauniyarmu, daga Umma uwar bayi, aka ce ta fito mu mata jagora baban Falo, a irin wannan lokacin UMUGHLUK ITIBEL na nan zai amshi gaisuwarta"


NADIRAH ta yi tsai tana ta kallonta, a hankali ta fahimci me sakon yake nufi, watau ana nufin ta je ta gaishe da shi babansun?

Baki ta yatsine tana dan waigawa dan bata so Innarta ta ji, domin a wannan lokacin da take jin zumudin su fitar da gashin cen ta dangwali romonsa ta zira a bakinta babu abinda zai sakata wanka ko cenza kaya da zuwa shirmen gaisuwa, wai inama ruwansu da sai ta gaishe shi ne? Su shafa mata lafiya, ko haka ake yiwa matan safakan ne? Dole sai an san ka je wajen miji? Shi yasa a sarauta bata ga komai ba sai tsabar wauta da rashin sakewa

Hankali kwonce NADIRAH ta ce" Idan kin je ki ce, na ce yanzu ina kicin, sai dai wani jikon"


A zabure baiwar ta dago, ba da gangan ba ta yiwa Nadirah kallon tsaf, a rashin gane me NADIRAH ke nufi ta ce" Sakon na sarauniyarmu ne ranki ya dade, sannan sakon daga UMUGHLUK ITIBEL ya fito, domin idan UMMA tace, shi yace"


NADIRAH ta saki lalausan murmushi tana gyara tsayuwarta ta ce" To dada, inaga a nan dai kice kawai matarsa a sanina, sai innata, idan kuwa ita zan kira maki toh sai naje aikar"

Da sauri ta sada kanta, wata zufa na neman karyo mata, ta sake sada kan nata a hankali ta furta" Allah ya huci zuciyarki, Allah ya karra girma, Allah ya karra daraja Sarauniyarmu, In sha Allah zan isar da sakon, A gama lafiya"


NADIRAH na tsaye tana kallon ikon Allah har matar ta fice kamar zata kifa

Ido ta kikifta kasa kasa ta ce" Allah mai alkhairi"
Daga nan ta koma tana yiwa Innarta hira wace ta yi bake bake a wajen Four tana jira abinda suka saka ya gasu su ciro

Tunda ta shigo har falo dan Umma ta bata damar shigowar a tunaninta tare suke da NADIRAH ta zube kasa, kanta a kasa ta kasa fadar sakon da ta gumtso a bakinta, domun har jikinta rawa yake yi a lokacin da ta fahimci kwarai da gaske ZAKIN SARAKAI na zaune

Umma da dan takaici ta ce" Ki fadi sakon mana kin tsugunna a waje kin mana shiru bayan kin ga ke ake jira?"


Kai ta sake dukarwa kamar zata kifu, muryarya a raunane kamar zata fashe da kuka ta ce" Allah ya taimakeki, sako daga sarauniyarmu, tace ace girki take yi, sai dai wani jikon"


Ba Umma ba, harta UMUGHLUK dake dan kallon Huznah sai da ya yi dan tsai , uwa Uba UMMA da ta kallota a zabure, hakama HUZNAH da sai da ta kusan mikewa dan tsorata, a gangaro kan Auta da ta dago tana zarro idannuwa kamar zasu fado tana kallon Baiwar, wace tuni take share hawaye, hawaye na tsoro, domun an hore su da fadin gaskiya, bale irin wannan dole zasu sanar da abinda suka gumtso, sai gashi, sai gashi ta gumtso mai karfi, kuma Umma ta saka ta fada a gabam Uban gidansu baki daya


Umma har hade harshenta take yi wajen fadin" Rufe min baki, wannan wace irin magana kike yi haka?, Na tabata wannan sako ba daga ita ya zo ba, waye zai shige kasam rigarta ya bata mata sunna run kafin ta ga mijinta? Na tabata wannan sako an yi shi ne dan a hadata da UMUGHLUK ITIBEL, maza ki tashi ki rakani wajen wace ta baki wannan sako, ko wacece na ganta, domin na tabata ba dai Sarauniyarmu ba!, Kuma ko waye a bayan haka zai bayana ne!"


Shi ihun da Umma ya fi damunsa, haka kuma kafin ya yi wani abu har Ummar ta fice kamar zata kifa

Juyowa ya yi zai yi magana dan HUZNAH a tsaye take itama , da niyar umartarta ta zauna sia ya ga wani murmushi ya kubuce daga fuskar Auta

Dan kallonta ya yi, sai ya samu kansa da yin murmushin shima

Muryar HUZNAH ce ta dakatar da shi a lokacin da ta duka kanta a kasa ta ce" Allah ya huci zuciyarka, na tabata da wani abin daban, ta yiwu bata gane sakon daga nan ya fito ba, bayan wannan me hadinta da kicin? Sam sakon ba naka bane"

Ido ya dan sake kura mata , haka kawai ya samu kansa da tunanin toh daga ina sako ya same shi haka? A masarautar nan? Ko daga wata masarauta, komai rashin da'ar Yar sarki ko matarsa, ba zasu turo da sako haka ba gaskiya, ta yiwu bata gane din bane, ko kuma ba ita aka ba sakon ba, shi abinda yake dan bashi mamakima shine, bata gane waye aka aura mata bane? Ko an mata nasihar zumudi ne? Dan kwarai ya yi tunanin a kofa zai tardota tana binsa da kallon nan kamar na mahaukata, sai gashi shiru

Murmushi ya sakarwa matarsa, hakan ya sakata suake ajiyar zuciya, domin damuwa ta sameta kar ransa ya bace abin ya shafe su baki daya, domin ba zata iya tuna bacin ransa ba, bata so, bata son tunawa, bata ga da kyau ba ko kadan, a ranar da ya yi bacin rai mai sunna bacin rai? Bata ga da kyau ba ita da kanta, bale wa'inda le zagaye da su


___________________________________


A haukace Umma ta shigo, bayan ta dakatar da Baiwar da ta tabatar mata nan ta shigi ta kuma kwatanta mata wace ta gani

Hankali tashe, rai bace ta dubi Inna dake rauda kai tana kallon TV ta zabura jin budewar da shigowar ta ce" Ashe bata da hankali? Ta san da wace irin wuta take son yin wasa? A tarihin rayuwata ko a zamanin iyayensa ban taba gannin an bashi amsa kai tsaye irin haka ba, hala bata da hankali da zata ce a cewa UMUGHLUK ITIBEL tana kicin ba zata samu zuwa gaishe shi ba sai wani jikon?"


Daga saman kujera sai da HINDU ta fado kasa warwas sannan ta dabi kai kamar mai shirin tayar da aljannu ta ce" Lah ha ila ha ilalahu muhamadu Rasulullah salalahu alaihi Wasallam, wani shegen rikaken dan iskan makaryacin ne ya gilawa Indi karyar nan? Allah na tuba yar da ko fitowa bata yi ba muna ciki muna dahuwa? Ka ga shari irin na masharanta, in itace a yau a yanzu yanzu in zama wancen TVn a ringa jona ni dan Annab............."

"Innata" Indi ta fada da dan karfi tana zarro ido dan gaskiya ba zata iya yin shiru innarta ta yi rantsuwar alkaba'i a kan gaskiya ba,


Ido ta ribga kikiftawa, hakan ya saka HINDU yin wuki wuki murya a raunane ta ce" ki bari na karasa rantsuwar nan kin ji yar indi? Ai ba kina nufin na yi shiru bane ko?, Ba zaki aikata haka wa babanmu ba ai ko?"


Indi ta yi shiru tana murza hannunta, sai kuma ta ce" Gani na yi muna girki a lokacin ne innata"


"Karbi nan, na ce dambulaninki Indi zo nan dan ubanki na gagaura make mari, so kike a shake mu muna ihu har mu daina? Zo nan" HINDU ta fada tana rarumar abu ta mike dan ta shako Yar...........


Mun shiga uku☹️☹️☹️☹️
8/13/22, 22:59 - Buhainat: *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍?*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*


🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻
*OUMOUGHLOUK ITIBEL*
_(ZAKIN SARAKAI)_
🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻

_FREE BOOK_

*Na*


*SAJIDA NIGER*





2️⃣7️⃣



Ba edditing



NADIRAH ta yi tsuru tana kallon Innarta, da Umma dake salalami ta kasa tsayuwa a waje daya

Innarta ta sake kallon Umma, sannan ta kallo NADIRAH ta ce" Yar gidan Habu makadi ki zo ko na zo?"

NADIRAH ta sake shagwagwabe fuskarta ta ce" Innata, gani na yi magariba ta shigo, kafin mu karasa ai ta yiwu kuma ya shiga barci dan ai baba baya jira barci na iya daukansa koda yaushe ko Innata?"

Hindu ta karra tafa hannu tana sumurtu, lokaci daya ta dage zanninta ta haura shi saman ciki sannan ta nemi tsalaka kujerar dake tsakaninta da Nadirah

Ido NADIRAH ta zarro, ta sake kallon innarta

Da gudu NADIRAH ta fala cikin dakinta ta rufo harda saka Ky sannan ta karasa wajen kujera ta zauna tana sauke numfashin gudun da ta sha sannan ta dan tsurawa waje daya ido tana dan balancing din kafafuwanta

Samun kanta ta yi da mikewa ta karasa gaban madubi ta dan rankwafa kadan tana daure gashin kanta a baya

Dan murmushi ta yi tana girgiza kanta kasa kasa ta ce" Amarya , Amarya ce, koda ta auren dole ce, koda ta karkara ce, in ba abinka ba baban su Inna ai mu mutanen karkara mun fi kowa riko da al'adu, a gida ba mace ke fara zuwa wajen miji ba, koda sarki ne, kasancewarka bako koda wanene kai ba shi zai saka a kwasheni a kaini gaisheka ba....., Duda ba maganar fahimtar junna ko tare yawun tsufa zan yi ba, ama a ji labarin nan a labba ai na fadi ba nauyi, Idan har da rabon mu gaisa zamu gaisa in la zo nan da kanka Babansu" ( kuturu🫢🫢🫢 abinda kike shiryawa kennan? Lalle kin traro match)


A falo kuwa zaman dabar Innarta ta yi tana salati tana sanar da ubangiji tana kallon Umma ta rasa me zata ce mata

Umma ta dafe kai itama da takaici ta ce" Ta kula, ta ajiye shirme da yarinta da wasan dake dawainiya da ita, ta ringa bambance baba da kuma dan gidan baba, ki fahintar da ita shi din baba ne, ba maganar wargi tsakaninsa da matarsa, ko waye ba zai rainashi ba, koda matarsa ce shi din sarkinta ne!"

Hindu sai ta samu kanta da jin maganar wata iri, ko matarsa ce shi din sarkinta ne? Toh mutane, yo ai itama da ta tsorata dan Indi bata riga ta zama matarsa a aikace bane, da hakan ta faru ai tana gannin abu ne daka iya faruwa tsakanin mata da miji ko? Ama yaya Umma ke dan so ta nuna kamar Indi ta yi sabo?


Umma ta dora da fadin" Bale a gaban kishiya take, matar da ta ci hakuri ta kora da ruwan zurra ido,matar nan ni na tabata hakurinta zai kasheta wata rana, kin kuma san maza na masifar son macen da sai yadda suka yi da ita ko?"

Hindu ta karra yin tsuru, ita Umma na magana ne ira tana aunawa a kankin kanta, Allah ta tuba ita din nan karan kanta maganar ba wata ji take yi ba, tsakaninta da Habu wani lokacin sai ta zo barci take lalabawa ta tashe shi a yi zaman tsakiyar dare a yi magana a yafewa junna, bama idan wata ya raba tsaka ya zama tulelen nan, takan ji komai a fili yake Alkur'an, takan bashi hakuri shi kuma yakan ce in bai yafe mata ba ai shi zai shiga uku dan idan ta tire daga yadda take yanzu ta yiwu a mata sarauniyar makada......., Gaskiya a nan tana iya cewa Umma kamar ta yi daya, wasu mazan ai a lokacin da kika zama sai yadda suka yi da ke din nema suke cin kaniyarki, Allah mun tuba a rayu da tunnanin za'a mutu kawai, in ba shi ba ai har a dambatu da makocin raba gado

Umma ta ci gaba da fadin" Mema ya hada fatarta da girki?, Ina ita ina aikin da aka zuba mata bayi dan su yi mata? Wanka kansa bai dace ta yi da kanta ba, ya dace ta dauki girman dake kanta fa, bana son abinda zai zamo tsegumi da tsuguri tsoma a cikin bayi, bana so kuma wancen ta yi tunanin ta samu hanyar da zata iya shiga tsakaninta da UMUGHLUK, uwa uba shi din da kansa idan ya fuskanci akoy maganar raini sai ya tsireta walahi!"


A zabure HINDU ta zarro ido , lokaci daya ta ce" In sha Allahu Bama za'a kai cen ba, yanzun ma sharin shedan ne, yar da bata cewa komai? Yar mai tsantsar biyaya? Na tabata rashin fahimta ne, yau zan kwana ina fada mata kuma zata dauka, a yafe mana ba zamu kuma ba"


Umma ta tabe baki tana sauke ajiyar zuciya, tabas yarinyar nan kamar ta mata ila ita din da kanta, a tunaninta yau da wata ce daban ta aikata haka ba wace take ji har kasan zuciyarta ba, da bata san abinda zai iya faruwa ba walahi!

Juyawa ta yi tana fadin" Zan koma bangarena kafin ya gama sallah na koma na bashi hakuri"

Inna ta gyada kai tana kallonta har ta bacewa ganninta

Tagumi ta rafka tana sake kiran sunnan yarta da fadin gwara ta bude kofar nan su fuskanci junna , ita kuma ta yi shiru ta ki fitowar, domin a muryar Innarta tana gane bata sauko ba, idan ta sauko sa yi maganar
Bayan sallar isha'i da kyar Umma ta samu komawaa domin baki ya yi a irin lokacin, sai dai tama zuwa ta sha mamakin gannin Auta har yanzu bata tashi ba

Zama ta yi ta shiga gabatar masa da lamarin ta fuskar rarashi da ban baki, ta karashe da fadin sakon sam na daga wajen sarauniya ya fito ba, wata kula kula ce, in sha Allah tana kan bincike dan ba zata yarda a fara kawo wargi a gaban danta ba

Murmushi ya yi yana basar da maganar, sannan yana karra gannin girman Umma a zuciyarsa, domin irin yadda take tsaye a kan lamarinsu ko iyayensa sai hakan, shi fa tausayinta yake ji baiwar Allah, ya tabata yakinta na ta kawo yarinyar cen gabaansa ba komai bame sai dan ta samu yan jikoki abinta, baban mafarkin Ummansu ta ga yan magadan sa, bata san shi bama zai kwatanta wani abu da yarinyar ba bale har ya dauki wani nauyim zuciyar, kai shi koda ya warke gaskiya da wahala ya tara zuri'a da yarinyar, dan sam bai ga tarbiya a tare da ita ba, irin yadda ta nuna din nan a saudiya ta bashi mamaki, bai taba tunanin akoy irin haka a hausa ba, abu kamar rainon arne? Sai da intacen bawansa ya daka mata tsawa fa a lokacin da ta ga dakinsa ido rufe ta nemi kutsawa da neman fado masa a jiki, bata san ba gidan ta samu ba, yanzu da wani lalatacen ne shikenan ta fado gidan sauki zai murjeta son ransa a bagas, ita a tunaninta soyaya ce sai ya bace mata batttt, kai shi yauma zai kunna wayarsa da ya bata layin, dama bai kunna bane saboda so yake ya huta sosai saboda abokan kasuwanci, layinsa ne sanane wa yan kasuwa kadai,

Umma ta yi murmushi tana kallon Auta ta ce" Babyna kin yi sallah kuwa?"

Auta ta dago a dan tsorace, dama tunda ta ga Ummar hankalinta ya kasa kwonciya ta tabata sai ta mata fadan ba ta hannata jimawa wajen Aba ba

Da sauri ta gyada kanta, sai kuma ta bude bakinta dake dan rawa ta ce" Dama harda ce zan yiwa Abah, shine, shine na jima"

Umma ta yi gagawar tareta dan karma ya saka wani abu a ransa ta ce" Aa ai karatu ba komai Auta, dama bana so kina jimawar ana ta hira kuma ki je baki samu isasshen barci ba , hakan na taba lafiyarki, idan kin gama yanzun tashi mu tafi na gyara maki komai ki sha maganinki ki kwonta"

Auta ta budi baki har tana dan hardewa ta ce" Ummah, ban gama ba, dama so nake na yin, kuma na sha maganin a gaban Aba yanzu ko Aba?"

Daga rubuce rubucen da yake ya dan dago ya gyada kansa, sai kuma a takaice ya ce" Zan rakata idan ta yi Umma"

Dan zuba masa ido ta yi ta ga hankalinsa ya dauku a abinda yake rubutawa
Wani irin harara ta watsawa Auta sannan ta yi kwafa ta mike ta yi masu sai da safe harda jadada a yiwa Auta addu'a fa idan zata kwonta

Bayan tafiyar Umma Auta ta jima tana kallon waje daya fuskarta na nuna alamun she is sad

Sai kuma ta sake tino maganar dazu

Ita abin ne ya sakata dariya ba dan komai ba sai tino maganar mahaifinsu da in dai yan tsokanarsa suka motsa ya kama adabar mhaifiyarsu da maganar kennan, a kan rikicin da suka sha tsakaninsa da ita dan aurwn hadi ne su a lokacin, kuma ita mahaifiyar tasu itace Auta, ya zamto tsaf take cewa ba zata je gaishe shi ba gaskiya ta gaji, shi kuma a lokacin eh lalle an bashi mata ne, ama farat daya ya ji du duniya ta masa iya yi, haka yake sabo babar rigarsa shi ya je ya gaishetan, ko ba komai ai halal ne, to mahaifin nasu ke anfani da haka ya yi ta tsokanar mahaifiyarsu ita kuma tana sinne kai tana dariya, summa sunna shaan dariya da mamakin wai du girman sarauta irin ta mahaifinsu dama zai iya aikata haka? Zai iya tashi da kansa ya tarda iyalinsa? Kwarai so wani abin ne mai girma

Kara sakin murmushi mai sauti ta yi, wanda ya saka yayanta dagowa da dan sauri ya tsura mata ido yana dan kallonta da byron dake hannunsa

Dariya ta yi har sai da jerarun hakoranta suka bayana sannan ta mike ta koma dan kusa da shi kadan da hannunta ta shiga nunawa ta ce" Abah, kana tune da labarin Papah da Anna?, Papah yace a gaban dogarai da fadawa nake saba babar riga na kai gaisuwa dan idan ta kiya tsaf zata ce ai itama mutun ce kulun kulun sai dai ita ta wani zo ta gaisheni?"


Rawanin da bai sauke ba ya samu kansa da yi masa kasa sosai har habarsa ta bayana, Dariyar da kanwarsa ke yi da tsohon tarihin da ta tuno ya daka shi jin kamar numfashi ya masa kadan dan farin ciki

A hankali ya saki lalausan murmushi, domun ya gane da me take hada zancen, sai kuma ya dan karra kure fuskarta da ido kasa kasa ya ce" Auta, ita fa ai ba irin na su Aba bane ba fa"

Auta ta dafe habarta ta ce " Abah, sakon naan daga wifey dinka ne, Allah ma ko"

Ido ya zarro da mamaki ya ce" Noh,kar ki rantse Auta"


Auta ta sake sakin yar dariyar da ta saka Yayanta lumshe idannuwansa yana mai godiya ga Allah, uwa uba ya shiga tunnanin kennan akoy sauran dariya irin haka a tare da ita?, Ya Allah kennan tana da sauran tarihi a zuciyarta da kwakwaluwarta? Kennan kanwarsa bata shige cikin duhu gaba dayanta ba da sauranta?

Auta ta kara dubansa ta ce" Abah, ka bada dama a kawota gobe sai mu gani ka ji? Please Abahna ni ina soma na ganta plz"


Idannuwansa ya kankance, sai kuma ya gyada kai yana murmushi ya ce" Me yasa kika damu haka Auta bayan baki santa bama?" Ya yi tambayar ne dan ya gane idan har ba kanwarsa na neman shakuwa da abar da yake da takaitacen zama da ita a zuciyarsa


Auta ta yi murmushi ta ce" Abah, ina son mutun mai karfin zuciya, mai courage, in dai daga ita sakon nan ya fito nima ina saka ran wata rana na yi karfin zuciyarta, Abah Kaine UMUGHLUK ITIBEL sunnan da talaka ya baka , kuma sarakai suka amsa, ba kai ka sakawa kanka dan isa da fin karfi ba, du wanda ya aiko maka da sakon nan, ko ita, ko ba ita ba i swear ina son ganninsa Abahna"


Murmushi ya yi shima, sosai mamakinta na neman hanna shi yin abinda yake yi,

Idan har zai tuna rabonsa da gannin haka daga Auta gaskiya an jima, irin mugun jimawar nan, murmushinta kansa sai a jima bata yi ba, bale dariya? Kai ko hira ake yi sai ka ga kamar bata san me ake cewa ba, ashe tana iya doguwar magana har haka hankali Kwonce?, Shima sai ya samu kansa da son yi mata abinda take so din, dan haka cikin nutsuwa ya ce" Ohk ohk, zaki gani yarinya da ba ita ta bada sakon nan ba, zaki gani, ama ba gobe ba, gobe da jibi inada zama a fadamai tsanani, inada Shari'a masu tsaurin gaske da rikici a ciki, in sha Allah ranar asabar alhamis sai mi zauna one 12 mu ci abinci tare?"


Da farin ciki Auta ta amsa har ta karra bashi wani mamakin ta ce" zaka cire Rawaninka?"


Da mamaki ya dubeta ya ce "
8/13/22, 22:59 - Buhainat: *NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍?*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.```
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

*https://www.facebook.com/106494781436168/*


🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻
*OUMOUGHLOUK ITIBEL*
_(ZAKIN SARAKAI)_
🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻🤴🏻

_FREE BOOK_

*Na*


*SAJIDA NIGER*





2️⃣8️⃣



Da mamaki ya dubeta ya ce" Me ya kawo maganar cire rawani kuma?"

Auta ta shagwabe fuska ta ce" Please Abah, idan ka yi haka zan ji dadi sosai fa?"


Murmushi ya yi ya mike yana fadin" Oya maza miko ki yi hardar na raka ki dare na yi fa"


Ajiyar zuciya ta sauke ta dauko ta mika masa sannan ta gabatar masa da hardar shi kuwa yana sauraronta har ta gama

Yana murmushi ya nuna mata hanyar da zasu bi ya rakatan sannan suka dauki hanya

Har suka karasa kowane na tunani a zuciyarsa

Shi yana mai karra godewa Allah da tunanin ai idan hakaa ta ci gaba da samuwa tsaf zai mayar da ita wajen mijinta, sauki ya samu Masha Allah, dama a gaban Umma ta yi hirar nan a sake, da Umma ta ji dadi aa ranta

Auta kuwa sunna tafe tana tunani kamar haka' shikenan kai ba zaka bude fuska ba sai kaa yarda da mutun? Na ga ai itama matarka ce, maganar yarda kuma ai ya kare ko?, Abah ban santa ba, hasalima ian tsoron iyayenta domin nice kat cewa summa da wani saka hannunsu a lamarinka, amaa haka kawai tunda akaa ce an daura aurenku nske zumudin son ganninta, ko dan zamu karru ne a cikin duniyarka? Ko dan zan kara samun wata yar uwar ne bayan HUZNAH, sam ba wai ina sonta dan na kuntatawa Huznah bane, ko daya, hasalima HUZNAH ni babu abinda ta min, yannayin mu'amalarmu ne haka, wani lokacin har hira muke yi fa, ama da wata zata karu cikinmu sai nake jin farin ciki sosai, sai maganar da aka fada , na tabata bayin masarautarmu ba dai maganar su ringa kawo karya ba, wannan Umma bata samu galaba a kansu ta wannan fannin ba, du inda maganar nan ta fitoz da tushenta, tushsen nake son gani ni kuma'



Har kofar dakinta ya rakata sannan ya koma ta hanyar da suka biyo bangarensa ya ci gaba da aikinsa yana sake rubuta hukunce hukunce ne na sata, da zina, uwa uba Luwadi .......................shara'ar dake gabansa mai zafi ce, kuma mai cakulewa ce, a dole Sheikh ya kawo masa su dan shi kadai ya isa ya tsaya ido cikin ido ya zartar kuma a bi koda ba'a sallah!


A ranar HINDU bata zauna da yarta ba sai washe gari, tana tsakar yi mata nasiha Kira ya shigo a wayarsu

Tana gannin yayarta

Please Login or Register in order to submit comment