Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da hud’u in ba haka ba wallahi kotu ce zata raba ni dasu.’’
Tana gama fad’in haka ta juya ta fita fuuuuu.

Cikin rashin jin dad’i Uncle ya kalli Baba yace
‘’Haba Musa,yanzu ina amfanin haka?wutsiyar rak’umi fa ta riga ta yi nesa da k’asa bayan haka ma Ina ce ita Jiddan Yusuf zata aura mai ya sake had’ota kuma da Al’ameen da aka raba ku da
wannan matar kwanakin baya da kyar ????’’
Cikin tsananin bacin rai Ya Musbah yace
‘’Ta je ta tafi kotun in bata da hankali,waye take tunanin zai kalle ta?,kud’i ai Al’ameen ne ya bayar ba ita ba’’

Cikin katse sa Uncle yace
‘’Kai Yaro ne har yanzu Musbahu,kamar yadda tace
akwai fa bambanci mai k’arfi a tsakanin ta daku Allah na tuba ko police station ta kai ku ta kulle wallahi sai kunji a jikin ku
dan babu d’an sandan da zata zubewa kud’i yak’i sakawa a narkeku,barin ma in tace kud’i take bin ku jibgar ku za’ayi tayi tunda ansan baku dashi har sai kun biya,gashi yanzu kowa takan sa yake yi ban san taya zama a fara biyan ta kud’in ba,instead of ka ji da rashin lafiyar matar ka
kaje kana amshe kud’in yaro.’’
Uncle ya karashe maganar tasa cikin b’acin rai.

Ahankali
Baba ya d’ago gajiyayyun idanuwan sa yana kallon yayan na sa,bai basa amsar tambayoyin sa ba
Instead sai shima ya jefa masa tashi tambayar ta hanyar cewa
‘’Menene yake damun matar tawa?’’
Cikin rashin fahimta Uncle yace
‘’Ban gane ba’’
Cikin son fahimtar dashi
Baba yace
‘’Wanne ciwo ne yake damun matata wanda har ta shafe sama da wata d’aya a kwance a gadon asibiti?,kai d’an uwa na ne dan haka nasan kaje ka duba ta kuma ya kamata ace kasan abubuwan da suke damun ta’’.
Cikin kame kame
Uncle yace
‘’Magana zaka gaya min?
bakasan yanayin tsarin aikin banki ba ko?to bari kaji mata na ma hak’uri sukeyi dani
Ni kaine bani da lokacin kaine
balle kuma..’’

‘’Balle kuma wani ni,ko?’’
Baba ya k’arashe masa maganar tasa cikin sanyin murya.
Cikin d’an fad’a fad’a
Uncle yace
‘’Kaga Musa bata wannan muke ba yanzu kar ka zille ta wannan hanyar ka fad’i ta yadda akayi ka karb’i kud’in yaro da dalili in gayawa su Baba Habu muga abun da zamu iya’’.
Kamar Baba ba zai yi magana ba sai kuma yayi murmushi yace
‘’Ba zillewa zan yi ba,amsar da zaka bani ita zata sa ka fahimci yadda akayi na karbMi kud’in.
Ciwon k’oda ne yake damun Amina wanda saida ta kai ga cirewa sannan ta samu stroke
hawan jini ga kumburin zuciya,iyakar allurai da magungunan ta kad’ai aiki ne.
Ba daban Al’ameen ba to da bansan ya zanyi ba’’
Ya k’arashe maganar wasu zafafan hawaye suna zubo masa ….
Ahankali ya share hawayen Kafin ya kalli Uncle yace
‘’Waennan sune abubuwan da suke damun matata suka sanya na karb’i kud’in Al’ameen
Saboda ya nuna kwad’ayin yanaso ya taimakeni sannan shi kad’ai ne ya zo min ya kuma taimakeni.Inaso ka gayamin
In da ace kaine a matsayina
shin,
bazaka amshi kud’in ba?’’

Uncle ya dad’e yana kallon Baba kafin yace
‘’Anjima zamu had’u a parlourn kaka mallan a nemo mafita
tsakanin kai da Ammi
Sannan a tabbatar da maganar Jiddah da Yusuf ta hakane kawai ja’irar yarinyar nan ba zata sake nemo mana magana ba’’
Ya fad’i hakan yana mai kallon direction d’in da Jiddan take
kafin ya juyo ya kalli Ya Musbah yace
‘’Har ga Allah inajin tsoron matarnan,fad’a da mahaukaci sai sarki,ka fahimtar dasu dan Allah.’’
Ya na gama fad’in haka ya kama hanya ya fice .

Sai a lokacin Manubiya ta samu ta saki kukan da take ta k’ok’arin dannewa.
Ahankali Jidda ma ta cigaba da nata kukan.





MANNUBIYA
15

Na
Humayrah Bulama

Elegant Online Writers.

Cikin rashin jin dad’i Baba yace
‘’Ban yi tunanin zan kafa miki doka ki shallaketa ba Jidda,
yaushe har kikayi wayo da girman da za’a rabaki dashi ki kasa hak’ura?,ashe dama ziryar da yake ta yi wajen ki yake zuwa a b’oye? kenan har yanzu kuma tare amman ke da shi kuka ce min ba komai tsakanin ku kun rabu ko?ni kika yi wa k’arya Jiddah?’’
Cikin fashewa da wani irin kuka tace
‘’Baba dan Allah kayi hak’uri,
Cewa yayi zai samu right time yayi maka bayani ta yadda zaka fahimce mu’’.

Cikin fad’a sosai Baba yace
‘Bayanin me?ni zaku yaudara?yanzu shi Al’ameen ashe ba zai iya taimako na ba sai da wani dalili kenan,yaushe aka haifeku
daga ke har shi da zaku rainamin wayo?’’
Ya k’arashe maganar cikin fushi.
Ahankali Ya Musbah yace
‘’Baba kayi hak’uri dan Allah,bara in fita in ga yadda za’ayi da kud’in matar nan,gara kawai a rabu lafiya.’’
Ahankali Manubiya ta share hawayen ta tace
Zanje muyi lissafi da ita ta lissafa kud’in ta zan biyata ta hanyar yi mata aiki
A gidan ta.

Dasauri Ya Musbah yace ‘’za mu san yadda za mu yi ni da Baba ki maida hankali akan karatun ki ki yi shiru,kawai.’’

Murmushi tayi kafin tace
‘’Ka bari nima in taimaka dan Allah,in kuka kawo naku sai a had’a ragowar da bai cika ba
In yi mata aiki na Iyaka kwanakin,kud’in suna da yawa fa ka barni inaso in taimaka nima.Makaranta kuma ba matsala zan iya had’a aikin da makaranta karka damu.’’

Ahankali Muhsin yace
‘’Zamu dinga zuwa tare sai in dinga tayaki da wani abun’’.
Jinjina kai tayi alamun ‘to’
Tana kallon sa tana murmushin da yafi kuka ciwo.

Kafin ta kalli Ya Musbah
Tace
‘’Bara inje tun da wuri muji ko zata amince’’

Sai a sannan Jidda tace
‘’Adda da kin bari na….’’

Cikin katse ta tace
‘’Ba komai Jidda karki damu zamu gyara komai,inshaaAllah’’.
Ahankali Jidda ta matsa ta yi hugging d’inta ba tare da Baba ya gani ba ta saka mata wayar da Al’ameen d’in ya siya mata Kafin ya tafi,karb’a kawai Manubiya tayi tajinjina kai daganan ta d’auki hijab d’in ta tacewa Muhsin ya ta shi.

A gaban Baba taje ta durk’usa tana addu’ar Allah ubangiji yasa kar yace a’a,cikin kwantar da murya tace’’Baba,dan Allah ka barni inje,kar yazo ta tozarta mutane kaga inna Bata da lafiya kar a kuma d’aga mata hankali gara mu bi ta a sannu a rabu lafiy….’’

Yafi minti biyu bai yi magana ba kafin chan ya had’iye wani k’ululun bak’in bak’in ciki da tashin hankali tukunna
ya jinjina mata kai alamun amincewa.
Chan k’asan ranta tace
‘’Alhamdulillah’’.Sannan suka mik’e da niyyar fita,har sun d’an gota taji yace
‘’Manu’’.
Sai da ta lumshe idon ta tukunna ahankali tace
‘‘Na’am Baba’’
Ahankali yace
‘’Kar ki yi ja’inja da ita sannan kiyi mata magana da tattausan lafazi’’.
‘’InshaaAllah Baba’’ tace
Daganan taja hannun Muhsin suka wuce.

Suna fita Baba ma ya juya ya fita.
Chan bayan gidan inda ba kowa yaje,yana zuwa ya fashe da wani irin kuka,ya manta rabon da yayi feeling
helpless irin yau, ba irin wannan rayuwar yaso ya’yan sa suyi ba,ba irin wannan uban yaso ya zama ba amman ba yadda zai yi ba shi da yadda zai yi,ko wacce hanya ko ina ya juya a toshe yake gani..

Ya jima ya na kuka kamar wani k’aramin yaro kafin daga bisani ya share hawayen sa yayi istighfari sannan ahankali ya ce ‘’Alhamdulillah’’ tukunna ya mik’e ya koma d’akin.

A nan ya tarar da Ya Musbah shi da Jidda suna ta lallab’a Inna wadda take ta faman hawaye.
Dan Baban yana fita sukayi la’akari da ita ashe ta farka tun tuni basu sani ba,saida Baba ya fara umartar Ya Musbah akan
yaje gida ya duba Baraka da mai sunan shi yaga komai kalau tunda tun safe yake asibiti kuma da suka dawo bai je ya lek’a gidan nasa ba.
Ba dan yaso ba ya tafi,
tukunna shi da Jidda suka ci gaba da lallab’a Inna………


Sai da su Manubiya suka kusa awa biyu tukunna suka dawo daga gidan Ammi duk su biyun jikin su a sanyaye.Jidda kawai suka samu a d’akin da Inna wadda suka lallab’a dakyar daga nan ta sha maganin ta bacci ya d’auke ta,Jiddan ce tace musu ’’Baba ya fita yanzu bai dad’e ba’’.
Ahankali Muhsin yace’’Bara inje wajen sa nasan yana masallaci’’daga haka ya fice ya bar musu d’akin.

Yanayin yadda Jiddan ta ganta ne yasa ahankali cikin mutuwar jiki tace ‘’lafiya dai ko?nagan ki wani iri’’.
Ahankali Manubiya tace

Wai har mun fara yau,fa
shiyasa ma kika ga mun dad’e
Aikin ba sauk’i gaskiya kuma a haka kinga yanzu dare ne so nasan na safe zai fi wahala,
wanke wanke shara mukayi yau tace kuma gobe harda girki.
Muhsin kuma da muka je da niyyar ya dinga tayani
ta ce shi zai dinga sharar wannan makeken tsakar gidan mai uban girma,albashin mu dubu goma goma,a wata dubu ashirin mu biyu.
In Allah yasa su Baba sun samu kud’i masu nauyi watak’ila wata d’aya ko biyu kawai za mu yi muna aikin,na bata har wayar daya baki ma’’.
Manubiya ta k’arashe maganar tana mai cire hijabin jikin ta.

Ajiyar zuciya Jidda ta sauk’e Kafin tace
‘’Adda manu ko ni in karb’a ke ki huta kiyi karatun ki cikin kwanciyar hankali’’.

Ahankali Manubiya ta koma kusa da ita ta zauna kafin tace
‘’Jiddah,a yadda matarnan take jin zafin ki in kikaje gidan ta tsaf zata iya cutar da ke,kuma bayaga haka ma bai kamata ke d’in kije ba ki bari karki damu ni da Muhsin d’in za mu yi,za mu iya’’.
Cikin zubar hawaye Jidda tace
‘’Adda Manu,taya za ayi ni nayi laifi amma ace kune zaku biya price d’in
A Ina aka tab’a yin haka?’’.
Cikin d’an jan kumatun ta Manubiya tace ‘’A gidan Baba,gidan da y’an uwa suke matukar k’aunar junan su,gidan da kai yake a had’e
In abu ya shafi d’aya tou ya shafi dukkan mu,gidan da mu ke so mu nunawa Jiddan mu tana da gata’’.
This time around fashewa da kuka Jidda tayi ta fada jikin ta tayi hugging d’in ta ahankali tace
‘’Nikam kar ku yi ku barshi zan yi in kuka yi bazan tab’a yafe wa kaina ba
Kullum zan dinga gani kamar na shiga hakkin kune’’

Ahankali Manubiya tace
‘Jidda ki kwantar da hankalin ki bakomai kinji
Kuma inaso ki saka a ran ki muddin zaki ci gaba da kula Al’ameen tou abun da zai faru damu kenan dan Allah Jidda
For the last time ki fita harkar Al’ameen har abada’’.

Ahankali Jiddan ta cika ta ta d’ago tana kallon ta kafin tace
‘’na riga na gama yiwa kaina wannan alk’awarin
InshaaAllah babu ni ba Al’ameen,kawai dai dan Allah kar ku bari a aura min Ya Yusuf
Wallahi bana son shi’’.

Cike da bata assurance had’e da kwarin guiwa Manubiya tace
Su su uncle d’in wacce rawa suka taka tun daga haihuwar ki har kawo yanzu da kike tunanin zamu bar su suyi miki auren dole?ki kwantar da hankalin ki kinji ko
InshaaAllah Yusuf sai dai ya ganki ya bari.’’
Ahankali ta sake hugging d’in ta tanajin wani kwanciyar hankali a cikin ranta,harga Allah bata son Ya Yusuf
bata san ya za tayi ba
In k’addarar Ubangiji ta sanya ya zamo mijin ta,da sauri a ranta tace ‘’ya Allah kar ka sa in auri ya Yusuf,alfarmar annabi s.a.w’’.
Shiruu tayi tana tunani
kafin ta d’ago ta gyara zaman ta tukunna tace
‘’duk naga kin yi kalar gajiya
kin gaji sosai ko?bari in je in d’eba miki ruwan wanka,in d’aura
na fanfon ya d’auke’’.
Murmushin yak’e tayi kafin tace
‘’Mun riga mun tara ni da Muhsin kafin mu shigo,sai da ma muka d’aura a kitchen tukunna muka shigo,nasan zuwa yanzu dai bai yi ba’’…

…Tun ranar da ta gan sa notunan kanta suka kwance,sanin data yi cewa sam shi d’in ba sa’an ta bane ba ta ko Ina,hakan ya sanya ta yiwa kanta fad’a sannan ta dage da addu’a da sallar dare da nafila,ta samu sauk’i kuwa
sai dai kuma bata san k’addarar data kai ta gidan Ammi ba yau gidan da tun da take a rayuwar ta bata tab’a shiga ba
Wacce irin kama ce tsakanin matar data tarar tana yiwa Ammi kitso da wannan bawan Allahn data gani a office d’in Sir Najeeb sati biyu baya da suka wuce.
Tunda taga matar kuma tashi d’aya sai tunanin mutumin ya dawo mata sabo fil.
Innalillahi wainna ilaihirrajiun
‘’Ya Allah kar ka d’aura min abun da zai zama ajalina ya Hayyu ya k’aiyyum’’.
Ta fad’a a chan k’asan ranta…..

Anya kuwa zata iya ci gaba da aikin gidan Ammi tana karo da wannan fuskar kullum,gashi ta lura matar kamar a gidan take
dan inda ace zuwa tayi tou da data gama yiwa Ammi kitso da zata tafi amma sai taga ta kama wani aikin kuma na daban,babban tashin hankali ta shine
kar taje shima mutumin a gidan yake
dan tabbas maybe in dai ba tsananin kama ba to matar nan yayar sa ce.Ta san cewa Ammi d’a d’aya gare su ‘Al’ameen’to kenan wannan mutumin y’an uwan su ne da shi da yayar ta sa a gidan suke kenan?Inaa ba zata iya ba,
gani d’aya tayi masa lissafin ta ya kunce ina kuma ga in taci gaba da ganin sa kulliyaumin?……

‘’Adda Manu,ya kawo ruwan fa’’
Jidda wadda take ta faman yi mata magana bata kula ta ba tun dazu, ta fad’i hakan da d’an k’arfi.

A d’an firgice Manubiya tayi firgigit ta d’ago tana kallon ta kafin ta samu da kyar ta had’iye wani abu daya tokare mata mak’oshi tukunna a hankali tace’’Ok‘’.kafin ta kalli Muhsin wanda ya dawo daga mik’a ruwan band’akin tace
‘’Nagode auta,bari inyi in rage maka’’.
Tana gama fad’in haka ta mik’e
ta d’auki abubuwan da zata buk’ata ta fad’a band’akin. …





MANNUBIYA
16

Na
Humayrah Bulama

Elegant Online Writers.

Tana fitowa daga wanka,
aka aiko kiran su daga wajen Kaka Mallan,Muhsin kawai suka bari a wajen Inna su duka suka d’unguma.Uncle,Ya Yusuf,Baba Habu Anty Umma sai Kaka Mallan suka tarar,
Ko gaisawa Uncle bai bari anyi ba dan yana lura ba Ya Musbah ya d’au waya ya kira sa yana mita akan’an ce za’ayi meeting,amma an bar sa ya tafi’. Sai da aka jira yazo ya fara bud’e taron da addu’a tukunna Uncle ya bari ma aka gaggaisa.

Ba tare da b’ata lokaci ba
Kaka mallan wanda ya amsa gaisuwar su Baba da kyar ya kalli Baba yace
‘’Musa’’!
Sai da Baba ya lumshe ido ya bud’e tukunna yace’’Na’am,Kaka.’’
Sai ya d’an nisa tukunna yace
‘’Dazu d’an uwan ka yazo ya same ni akan batun matar senator da y’ar wajen ka,an yi part 2 kenan?’’
Shiruu Baba yayi kafin chan yace
‘’InshaaAllah hakan ba zata sake faruwa ba na tsawatar mata’’.
Cikin d’an daka tsawa Kaka yace
‘’Kai dallachan gafara, ka tsawatar kuma na yaushe,kwanakin baya ba’an tsawatar mata ba amman kaga tayi amfani da tsawatar war?kuma tsabar cin fuska da rashin sanin ya kamata
MUSA,Yusuf fa da mahaifin sa suna cikin gidan nan amman kuka barta take kula wani Al’ameen.
Dama na fahimce ka tun ba yau ba,komai naka daban yake,duk wata hanyar da zaka bi ka salwantar da had’in kan zuri’ar nan tou ka san ta,kai kenan ace komai naka a botsare?kuma duk in kaje ka dawo baka ganin dai dai sam ka duba kaga yadda ka kafe akan kasuwanci ba riba amma dukda haka sai da ka d’aura Musbahu akan kasuwancin shima,kana gani y’an uwan ka suna karatu amma kai ka nacewa abu d’aya gashi yanzu a ta dalilin botsarancin ka kai da iyalin naka gaba d’aya kun zama abun tausayi.
Da sauri Manubiya ta mik’e ta juya zata fita.
Cikin karsashi Kaka Mallan yace’’Wallahi zan ci uban ki, ni zaki mik’e ki fitar wa ina tsaka da magana, saboda na fad’i gaskiya?dawo ki zauna tun kafin in saka Yusuf ya ladaftarmin da ke’’.
Ko gezau Manubiya bata yi ba
bata fita ba kuma bata koma ta zauna d’in ba, har sai da Ya musbah ya daka mata tsawa yace’’Wai ba da ke ake magana ba?’’Tukunna ta koma ta zauna mess na tana ji kamar ta fashe tsabar takaici.

Baba ,
Kaka mallan ya kalla kafin yace
‘’Ka gani ko,kalli kaga,wannan y’ar sai ta gagare ka wallahi’’ya fad’i hakan yana nuna Manubiyan Kafin ya d’aura da cewa
‘’Babu yadda ba ayi da kai akan ka aurar da ita ba amma ka nace akan karatun da aka kwad’aita maka tun farko ka k’i yi,za tayi.Ita da take y’a mace wadda yaci ace yanzu tayi yara biyu ko uku ma,amma ka ja mata har tayi kwantai tunda ni dai rabon da inji sallamar zance da sunan ta har na manta,ta d’auki shegen girman kai ta azawa kanta bata kula waenda suke zuwa mata ai gashi duk sun gudu, ba fata nake miki ba Amman da wuya ki auru sai kije ki rungumi littafi.’’
Shiruu kowa yayi baka jin maganar kowa sai ta Kaka mallan ta inda ya d’aura da cewa
‘’Duk da ka nuna ban Isa da kai ba dole zan saka baki dalili na na biyu kuma shine
bazai yiu ka tara yara da kai kanka kuyita kurmutsa a d’aki a takure kuma kak’i d’aukar shawara sannan kayi tunanin za muyi shiru ba.
Ba zan zuba ido yaran ka mata har biyu su tagaiyyara ba,ita Manu yanzu ta riga ta zama sai an had’a da addu’a,shiyasa tun kafin Jidda itama tayi kwantai na riga na gama yanke shawara kowa ya saurara yaji..
Nan da sati biyu dama za’a kawo kayan sa ranar Siyama dan haka a tare a kuma rana d’aya Yusuf shima zai bada na Jidda,in Allah ya kaimu nan da wata uku za ‘a had’a a d’aura auren tare da nasu Siyama a mik’a ta d’akin ta in kuma anan cikin gidan ma zai zauna shima sai a ware ma sa nashi fannin.Sai maganar kud’in matar senator,Ummaa da Uncle sun bada dubu bibbiyu Habu ya bada uku nima zan bada uku a had’a a bata kai kuma sai ka nemi cikon ka cikata mata,Allah ya rufa asiri.Akwai mai magana?’’.

Ahankali Anty Umma tace
‘’A’a Kaka’’.
Tana mai jin takaici a ranta,ita da take mace kuma za’ayi auren y’arta,babu wanda a cikin su ya Bata ko sisin kwabo yayar siyama sai ita ne kawai suketa fafutukar hatta lemukan da za’a tarbi bak’i ita ce zata siya,an sakar mata komai an zuba mata ido kuma tasan ba bayarwar za suyi ba har daga nan har akai siyama d’akin ta,amma yanzu ita an hura mata wuta sai da ta bada dubu biyu…

Ahankali Baba yace
‘’Kaka Mallan,Ina da magana’’
Sai da Kaka Mallan ya d’an k’ura masa ido tukunna yace ‘’Muna jin ka’’.
Sai da ya fara yin godiyar karo karon kud’ad’en da suka yi masa tukunnna.
Cikin rashin jin dad’in maganar da zai fad’a yace
‘’Ka yi hak’uri kaka ba wai awai jayayya zan yi da kai ba amma Ina ganin maganar auren Jidda da Yusuf
gara kawai a barta’’

Ba tare da Baba Habu yace komai ba kawai ya mik’e ya fice daga parlourn gaba d’aya.
Cikin fushi Uncle ya kalli Baba yace
‘’To ai shikenan,gata nan sai ka kwad’ata ka cinye,amma wallahi in ta sake janyo magana kar a kuskura a sake involving d’ina a ciki’’.
Daga haka ya juya ga Ya Yusuf wanda ya sunkuyar da kan sa yayi shiruuu
Yace
‘Yusuf dan Allah dan Annabi ka hak’ura da yarinyar nan,kana da degree d’in ka da sana’arka babu gurin yarinyar da zaka je ta k’i ka’’.

Anty Umma dai bata tanka musu ba hakanan taja bakin ta kawai tayi gum Tana kallon kowa.

Da dakakkiyar murya Kaka mallan yace
‘’Musa,inaso ka gaya min laifin yusuf kwara d’aya tak’’.
Ba tare da shakkah ba Baba yace
‘’Yusuf bashi da laifi kaka kawai dai na ga a halin da Jidda take ciki na damuwa da rashin lafiyar mahaifiyar ta bai kamata ayi mata auren dole ba,kuma ni ban shirya aurar da Jidda ba har sai mahaifiyar su ta samu lafiya,InshaaAllah.’’


Sai yanzu Anty umma tace
‘’Ita Jiddan tace maka bata son Yusuf d’in?’’
Tun kafin Baba yayi magana Jidda tayi k’arfin hali da sauri tace’’Eh,Umma’’a hankali.

‘’Uhm, to ai shikenan’’
Anty Umma tace daganan ta ja bakin ta tayi gum.

Tabbas ran Kaka Mallan ya b’aci dan haka kawai yace’’kowa ya tashi ya tafi’’
Yanayin sa kad’ai ya sanya kowa ya fahimci Tabbas in ba da kyar ba to kuwa sun d’aura gaba kenan da shi da Baba har abada..

Hakanan taro ya watse zuciyar kowa da k’unci,dan shi kan sa Baba saboda yaga ba yadda zai yi ne shiyasa yayi magana bayaso ya sako karatu su yi nasa chaa amma yanaso Jidda ta fara ko da level one ne ta d’an saka k’afarta a jami’a tukunna ayi auren ga kuma damuwar da suke ciki ga rashin lafiyar Inna,abubuwan da yawa yasan dama ba lalle su fahimce sa ba.
Shiyasa washegari ya bi Kaka Mallan anty Umma Baba Habu da Uncle,
dan yana so su sasanta a tsaka nin su su manya sannan ya fahimtar dasu.
Amman sai abun bai yi ma sa dad’i ba sam dan Anty Umma ce kawai ya samu ta d’an saurare sa ya gama bayanin sa,tace
‘Ba komai ‘kawai.
Dama ita er i don’t care ce.
Uncle kuwa tun a masallaci yace yana son ganin su shida Baba Habu in an fito amma suna fito wa ya shiga gidan da yake parking motar sa ya zari mota yayi gaba gashi ranar lahadi ne bare ace aiki yaje.
Baba habu kuma yace masa bacci zai yi,lokacin siesta d’in sa yayi.
Kaka kuwa tun kafin ya k’arasa shiga wajen na shi ma ya kore sa.Tun daga ranar kuwa kan y’an gidan ya sake tarwatsewa,da farko lamarin nasu rashin had’in kai ne kawai yanzu kuwa abun ya had’a har da jin haushin juna da fushi.

Satin Manubiya d’aya da fara zuwa aiki gidan Ammi most atimes lectures d’in su da safe suke fara wa shiyasa take zuwa tun kafin gari ya fara haske saboda tayi ta gama ta tafi on time,ranar lectures d’in Sir Najeeb ne kawai ta rok’i Ammi,Allah ma yaso ta yanzu sau d’aya kawai
Zai dinga shigar musu ajin shiyasa tun ana i washegari tace’Dan Allah tayi mata hak’uri
10 zata taso InshaaAllah zuwa 11 za ta zo tayi aikin nata.’
Allah ya taimake ta a lokacin
Mama tana d’akin Ammi
tana shirya mata wardrobe d’in ta a lokacin da taje suke maganar,ai kuwa tashi d’aya Maman ta saka baki,ba dan Ammin taso ba sai dan girman Maman a idanun ta yasa ta hak’ura ta yardar ta amince.
Itafa so take ta maidawa su Manubiya rayuwar su living hell amma ta lura yarinyar ita da k’aninta Muhsin kamar waenda ake jona musu charji,duk kalar uban aikin data tula musu kafin kace kwabo sun kammala tsaf.
A b’angaren Manubiya kuwa sam aiyyukan da Ammi take tula mata basa damun ta,babban tashin hankalin ta a gidan ita ce’Mama’,kamannin ta da wannan mutumin sun yi yawa sannan in dai ta kalli fuskar Mama tou sai ta tuno sa kuma indai ta koma gida ta kwanta barci tabbas sai tayi mafarkin sa maimakon tayi mafarkin Mama tunda ita ta ke gani,
A’a
Mafarkin mutumin take yi
kuma kullum kamar sake ingiza mata tunanin sa ake yi.
Shiyasa a koda yaushe take k’ok’arin ganin tayi nesa da Mama.
Tabbas Hatta ita kanta Maman ta fahimci Manubiya wasan y’ar b’uya take yi da ita bata san dalilin yarinyar na guje mata ba gashi ita harga Allah yarinyar ta shiga ranta,sosai ………

Amaryar Daddy tana cika sati biyu da tarewa rana tsaka yace’ta had’a kayan ta za su koma main house d’in sa,’Ummi
Mace ce mai sauk’in Kai da fahimta ga hak’uri shiyasa tun Kafin auren ma da yace ta ajjiye aikin ta tashi d’aya ta ajjiye,sam bata yarda tayi jayayya da shi shiyasa yanzun ma tashi d’aya tace’’to’’,kuma ita har ga Allah bata ji komai ba dan by then sun saba da Mommy da yaran ta dan bata yi k’asa a guiwa ba sai da ta amshi numbers d’in su kaf suke gaisawa,sam
Bata damu da yadda a ko da yaushe ita take kiran su ba.
Basu samo dawowa ba sai washegari,dama gado da set d’in kujeru kawai tayi amma hatta kayan kitchen a gidan ta tarar dan haka aka kunto mata iya gadon ta da kujerun
aka zo nan mansion d’in aka kafa mata a side d’in da Daddy ya nuna mai d’auke da parlour mini kitchen

Please Login or Register in order to submit comment