Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yadda taga ya sake tamke fuska fiye da yadda take a kullum amma sai shauk’in data shiga na ganin sa ya lullub’e fargabar ta ta.

Ahankali ya lumshe dogayen idanuwan sa
kafin ya bud’e su ya zuba akan Kausar
Wanda hakan ya bawa Yasira damar silalewa ta gudu kitchen, dan ta lura zuwa yanzu hankalin sa ya koma kan Kausar.
Wani d’an mitsitsin tsaki yaja
Ganin yadda take kallon sa tana wani lumlumshe ido,sai da ya sake had’e rai tukunna ya tunkaro ta cikin takun sa mai cike da k’asaita da kamala.
Har ya k’arasa bata cire idanun ta a na sa ba,shima kuma haka dan yana so yaga k’arshen tsaurin idon ta,
sai da ya matso daff da ita
tukunna dakyar ta cire kwayar idanun ta a nashi ta hanyar lumshe idanuwan ta wanda hakan ya bawa wata y’ar siririyar kwalla damar zubo mata daga ido d’aya,
In akwai abunda yake mishi wahalar yi
tou shine magana
Shiyasa kawai ya tsaya yayi shiru
Har ta gama sauk’e ajiyar zuciyar ta a jejjere sannan ta sake bud’e idanuwan ta tana kallon sa.

He can’t stand her ,ko kallon ta baya son yi,Wallahi inda ace yarinyar ba Marainiya bace ba
da sai ta koma gidan su dan shi da kansa zai maida ita.Ba abunda ya tsana a rayuwar sa
Irin ‘ya mace mara kamun kai.
Bai yi cikakken 3 months da dawo wa gidan ba amma ya fahimci sam yarinyar bata da hankali,dama tun suna yara
tun kafin ya koma Uk da zama ya fahimci hakan dabi’ar ta ce
amma sam bai yi tunanin har yanzu Bata nutsu ba .

Cikin kakkausar dakakkiyar murya yace
‘’ATM’s , phones ,car keys &passport.’’

A rikice ta d’ago tace
‘’Ya Yash pls I ….’’

Wata mahaukaciyar tsawar daya daka mata
Sai da ta kaita ga tsugunnawa a k’asa

‘’Bani nan!!!’’
Sannan ya d’aura da cewa
‘’Karki bari raina ya k’arasa b’aci’’

Taso ta d’an b’oye waya ko atm
amma tana d’ago handbag d’inta ya wafce

Batare daya sake kallon ta ba ya juya
Yace ‘’Mommy ki turomin Yasir.’’
Yana gama fad’in haka ya juya
kamar walkiya fitt ya fice daga parlourn ya bar musu mayataccen kamshin turaren sa.





MANNUBIYA
06
Na
Humayrah Bulama

ELEGANT Online ✍️

Har ya fice idanuwan ta basu daina kallon inda yabi ya fita ba.
Cikin fushi Mommy ta kamo ta ta juyo da ita Sannan tace
‘’Ai ga irinta nan,yanzu kinga magana kam ta riga taje kunnen Daddyn ku ta gama,
Kin janyo wa kanki da kanki.’’

Ahankali kausar ta matso kusa da ita
Tace
‘’Ko kuma dai kin janyo min ba,
In da bakizo kina hargagi da shouting ba ai da bai ji ba,na san dama ai abun da kike so kenan ai,so kike yi yaji kuma yaji d’in
So sai ki zuba ruwa a k’asa ki sha tunda burin ki ya cika!!!’’.
Tana gama fad’in haka ta wuce sama da gudu tana kuka
Ko akwatin ta bata jira d’auka ba.

Mommy ta dad’e a wajen kafin dakyar taja k’afafuwan ta ta wuce,,
hawayen Kausar suna d’aya daga cikin abubuwan da bata k’aunar gani a duniyar nan…


Tunda garin Allah ya waye su Manubiya
Suke zuba idon ganin su baba , amma shiru.Ganin har k’arfe 10 tayi ga jikin Manubiya itama sai k’ara tsanani yakeyi,yasa suka yanke shawarar Jidda taje ta dubo su Baba tun da sun san asibitin da aka kai Innar.
Dakyar suka had’a naira hamsin kud’in mota,ta bata tace ta hau bus,in ba ta gaban asibitin murtala man za subi ba sai su ajjiye ta a hanya ta k’arasa

Ahankali badan tana so ba ta mik’e ta shiga toilet tayi brush ta wanke fuskar ta, ta d’an kimtsa ta fito ta musu sallama ta fita.
Unguwar shiru ba kowa,y’an kasuwa sun tafi harkokin gaban su masu zuwa aiki sun wuce haka ma y’an makaranta,
a takaice dai kowa ya tafi neman abunda zai fishshe sa.

…..Tun lokacin data fito ya hango ta amma yadda ta taho yasan sam bata lura da shi ba.
K’are mata kallo yake yi yana sakewa yana mai sauk’e wata nannuyar ajiyar zuciya,
shifa tunda yake bai tab’a ganin farar mace tass kuma farin mai asalin kyau kamar na Jidda ba
In ka ganta baza ka tab’a cewa Baban ta talaka bane
Fatarta har wani shek’i takeyi
Ga idanuwa dara dara manya Sosai oval shape tubarkallah,
hancin ta pointed nose ne ba dogo chan bane wanda xa a ce masa har baka amma pointed ne mai asalin kyau da d’aukar hankali,bakin ta ma ba slim lips gareta ba suna da d’an tudu kad’an amman kuma bakin d’an mitsitsi ne,
Lips din k’asan tsakiyar sa a d’an rabe kamar an tsaga,
sai dimples d’inta a wajen hab’arta k’asan lips d’inta gefe guda
Ga shape , asalin figure 8 kamar ita ta zana kanta.

Yadda Jidda take , haka sak Manubiya take
Suna tsananin kama da juna
Sai dai Manubiya ta d’an fi Jidda tsayi da jiki, kuma idanuwan ta basu kai na Jidda girma ba , Amman sunfi na Jidda kyau da kyalli da d’aukar hankali , Sannan tafi Jidda tsayin gashi dan nata har gadon baya yake , sab’anin na Jidda da bai ida kaiwa har gadon bayan ta ba instead ya tsaya a iya kafad’un ta,yanayin
dimples d’insu ma ya banbanta jidda guda d’aya ne a k’asan hab’arta na Manubiya kuma a kumatun ta suke both side Masu kyau da d’aukar hankali.
Yanayin tolerance d’in su ma ba d’aya bane
Manubiya tanada d’an fad’a , Jidda kuma in zaka saka mata hannu a baki , ba lalle ta ciza ba ……

Jikin ta ne ya bata kamar ana kallon ta dan haka ta d’an d’ago da kanta,
Suna had’a ido tayi saurin mayar da kanta k’asa ta k’ara sauri dan ta samu ta wuce sa
amma sai ya yi saurin k’arasa wa inda take yana wani kalar murmushin dayake sanya ta take k’ara tsanar sa.

‘’Ina wuni’’
tace dashi,daga nan ta fara k’ok’arin zagaye sa zata wuce,
hannu kawai taga yasaka zai kamo ta
dan haka tayi saurin kaucewa
dakyar
Ya iya ruk’o bakin hijabin ta fuskar sa har yanzu d’auke da murmushi,
Sai da ya dawo da ita gaban sa ta hanyar janyo ta tukunna yace
‘’Matas, bazaki saka wa zuciyar ki da rayuwar ki salama ba ko?kin riga kin san ni ne mijinki har gaban abada
to mai ya sa baza ki tursasawa zuciyar ki k’auna ta ba?’’
Yayi mata tambayar yana mai matsowa kusa da ita.

Da sauri taja baya
Idanuwan ta har sun kawo ruwa
Muryarta na rawa tace
Ya Yusuf ka sakar min hijabi na
Ina sauri ne’’.

Kwaikwayar y’ar siririyar muryar ta mai cike da rauni yayi ta hanyar cewa
‘’A’a ni ba zan saki hijabin matata ba’’.

Duk yadda taso hana kanta kuka kasawa tayi dan haka kawai ta saki kukan datake ta k’ok’arin rikewa,
da sauri ya cika mata hijabin
kafin yace
‘’to to sorry
Wasa fa nake miki mai ya faru har haka ?
Are u okay?’’.

bata san lokacin data ce
‘’Inna ce fa bata da lafiya
tun jiya su Baba suka tafi kaita asibiti har yanzu basu dawo ba , shine zan je kai kuma ka tare min hanya.’’

Cikin rashin jin dadi yace
‘’yi hak’uri ban sani ba ne shiyasa,
Jira ni anan , inje in d’auko mashin d’ina sai muje ko?’’

Kafin ma ta ba sa amsa har ya wuce da d’an sauri da alama yanayin ta da maganar rashin lafiyar Innar ya kid’ima sa.

Kamar wata yarinya Tana ganin shige war sa gida ta d’iba a guje ta shige wani lunga ta b’uya,
tasan babu kyau kace ka tsani mutum amma wallahi ta tsani Ya Yusuf.

Tabbas dama sai da ya shiga gida yayi wannan tunanin
aikuwa ilai gashi ta gudu.
Babu inda bai duba ba amma ya rasata,
dan da taga ya fara neman ta
nan gidan da yake cikin lungun ta afka
Allah yaso sun tab’a yin Islamiyya da y’ar gidan dan haka ta gaida Maman ta tace dan Allah zatayi fitsari matar yace tou daga nan ta afka toilet.
Ta jima tukunna ta fito tayi wa matar sallama da godiya
dan ita kadai ce a gidan
yaran duk sun tafi makaranta

Tana fito wa ta dan tsaya jikin dank’areran gidan da lungun ya ke a jikin da
Ta shiga kalle kalle kamar mara gaskiya,sai da ta tabbatar bata ga Ya Yusuf ba tukunna ta fara shirin nufar titi,
ko taku biyu bata yi ba suka yi ido biyu da Ya Musbah.
Dan haka bata samu taje asibitin ba dan cewa yayi ta komo su je ayi wa Innar girki
an kwantar da ita wai aiki za ayi mata kuma daga yau baza su sake bari taci komai ba har sai bayan anyi aikin da kwana uku .

Sai da suka shiga gida tukunna Ya Musbah yasan Manubiya ma bata da lafiya dan Jidda bata samu damar gaya masa ba,tunda taji wai aiki za’ayi wa Innar gaba d’aya ta d’imauce ta rikice.
ba karamin tashi hankalin Ya musbah ya kuma yi ba
sai da yaga Manubiyan ta tashi ta zauna tanata maimaita masa cewa
‘ jikin nata da sauki ‘
tukunna yad’an ji relief
daganan yake gaya musu
Kidney d’in Innar guda d’aya ya samu matsala
sannan ciwon zuciyar ta ma ya motsa ga hawan jini
kuma basu san garin yaya ba
amma jiya cikin dare ta samu stroke
Maybe ko mak’udan kud’ad’en da taji Likita ya lisaafo ne suka d’aga mata hankali,
Allah kad’ai ya sani.
But yanzu dai ance ana buk’atar a cire kidney d’in d’aya da wuri gudun kar mai kyau d’in itama ta kamu.

Kuka suka saka gaba d’aya su ukun tun kafin ma ya dasa aya,ya so ya daure ya lallashe su amma sai ya gagara
shima kawai ya b’ige da hawaye.
Da kyar Manubiya ta tsaida kukan ta ta shiga lallashinsu
tukunna sukayi shiru,sun jima d’akin shiru kafin manubiya tace
‘’Ya Musbah,yanzu ya za’ayi muyi raising kud’in aikin Dana gado Dana magani?,zai kai kimanin naira nawa ??

Ahankali yace
‘’Baba ya saida gonar sa da tun a jiya da tamu sannan Al’ameen ya cika mana wasu kud’ad’en,’’
Shiru yayi kamar mai tunani
kafin ya kalli Muhsin yace
‘’Zo,muje mu siyo abun kari muyo cefane’’.

Suna fita
Manubiya ta juya ta zubawa Jidda kyawawan idanuwan ta
ba tare da ta ce ko tayi niyyar cewa komai ba.
Sarai Jidda ta gane tuhumar ta Manubiyan take yi
Don haka tace
‘’Ban san maganar ba
bama ma had’u ba rabo na da shi tun wanchan satin.’’

Ajiyar zuciya kawai manubiya ta sauk’e
kafin tace
‘’Jidda kina fita bada jimawa ba
na tsinci naira hamsin a cikin littafi na na makaranta dan haka na aika Muhsin nace yayi gudu yaje titi ya k’ara miki kud’in mota tunda nasan ba lalle kin kai ga zuwa titin ba ma
amma sai ya dawo ya ce bai ganki ba
Kuma ya Musbah yanzu cewa yayi a k’ofar gidan su ya ganki, shi kan sa nasan kawai maganar ce baya so shiyasa yayi miki shiru.’’

Ahankali Jidda tace
‘’Wallahi rabo na da Al’ameen tun wanchan satin,ki yarda dani,
Dan Allah.’’
Ta k’arashe maganar kamar zata fashe da kuka.
A take kuma sai tsananin tausayin ta ya rufe Manubiya,ko babu komai
tasan ba k’aramin Namijin k’ok’ari Jidda take yi wajen ganin ta rabu da Al’ameen ba. …….





MANNUBIYA
07
Na
Humayrah Bulama

ELEGANT Online ✍️

Sai bayan sallar isha
tukunna,Mommy ta tattara gaba d’aya ragowar courage d’inta ta nufi side d’in Kausar,a parlour d’inta ta same ta kwance cikin luntsumemiyar resting chair d’inta dake a bakin balcony d’in parlourn wanda glass ne kawai ya raba da parlourn,Ahankali Mommy ta k’arasa kusa da ita ta zauna a dai dai wajen k’afafun ta,tana tunanin ta ina zata fara lallashin ta.

Tun lokacin data turo k’ofar ta shigo Kausar ta lura da ita
amma sai tayi kamar ma ba ta san mutum ya shigo ba,tana kwance idanun ta suna kallon sama har zuwa lokacin da Mommyn ta zauna a kusa da k’afafunta idon ta yana kallon sama kamar farko alamun tayi zurfi a tunani kenan.

Ahankali Mommy tace
‘’Kausar’’
Jin shiru ya sanya ta d’an sake k’ura mata ido kafin ta sake cewa ‘’Kausar’’
Nan ma shiru taga Kausar d’in tayi,babu ko gezau,dan haka ta kama k’afafun ta ta d’an jijjiga kafin da d’an k’arfi ta sake cewa ‘’Kausar’’
tana me kallon fuskar ta.

A firgice ta d’an kalli Mommy sai kuma wasu hawaye suka tsinke mata a lokaci guda.

Aikuwa nan take Mommyn ta rikice,
Ta shiga tambayar ta a lokaci d’aya ta na mai k’ok’arin zaunar da ita.
Sun jima kafin dakyar Mommy ta samu kausar d’in ta d’an yi shiru tukunna a hankali Mommy ta kamo hannayen ta tace
‘’Indai akan fad’an da nayi miki ne dazu to kiyi hak’uri,bazan sake ba inshaaAllah,ki daina kuka komai ya wuce.’’

Wani kalar murmushi Kausar tayi wanda ake cewa yafi kuka ciwo,kafin ta shiga girgiza kanta sannan ahankali tace
‘’Ba shine ya saka ni kuka ba kawai dai ina tunanin ina ma ace Ammi na tana da rai,ne’’.

Cika hannuwan nata Mommy tayi kafin tace
‘’Kar kiyi min haka Kausar’’.

Dasauri kausar d’in ta ruk’o hannayen ta kafin tace
‘’Kar kiyi misunderstanding d’ina,ko da ace ammi tana nan nasan iyakar soyayyar da kike yimin ita ma zata min
Maybe ma ba lalle ya kai naki ba.I was just wishing wai inda ace tana nan nasan ba lalle in zauna a gidan nan ba,babu ruwa na da takurar Yasir da kuma tsangwamar Yashjub
Har ga Allah mommy bani da matsala dake ko su Yasira
amman Yassir is my worst problem sannan saboda Yash yasa naji inason barin gidan nan gaba d’aya,dan
akwai wani abun da yake damu na wanda indai ba Ammi na ba wallahi ko ke kanki baza ki tab’a iya fahimta ta ba.’’
Ta karashe maganar tata tana mai fashewa da kuka.

Ahankali Mommy ta share hawayen ta kafin tace
‘’Na fahimce ki,na fahimci dalilin furucin ki na daxu.
Abunda nakeso dake shine
Ki fad’a min abu uku
Na farko
mecece matsalar ki da Yasir
Da Yash,sannan wanne irin abu ne yake damun ki wanda har kike tunanin Ammin ki ce kad’ai zata iya fahimta?’’

Ba tare da tantama ba
Kausar tace
‘’Mommy bana son Yasir,shi kuma naga alamun kwana biyun nan kamar wanda aka yiwa wahayi aka ce dole ya aure ni.’’

Duk da Mommyn taji ba dad’i
Yadda direct Kausar d’in tace bata son Yasir,amma sai tayi k’ok’ari ta danne ta sake rik’e hannun Kausar d’in duka biyu Kafin tace
‘’Fad’a kukayi?
wani abun ne ya faru ?’’
Ganin kausar d’in tak’i ta bata amsa ne ya sanya tace
‘’To,koma dai menene ya faru ina mai baki shawarar kiyi hak’uri ki auri Yasir domin shine rufin asirin ki,ko kina tunanin akwai namijin da zai aure ki ba tare daya san wace ce ke ba?’’
Sai da Mommyn ta runtse idanuwan ta ta bud’e tukunna ta kalli Kausar d’in tace
‘’Kausar kiyi hak’uri ki rufa mana asiri kar ki bata mana sunan family’’.

Dasauri tace
‘’Mommy nifa ba wani wajen nace zan je inyi aure ba a cikin gidan nan zanyi,therefore wanda zan aura already shima ya riga da yasan maganar haihuwar dana tab’a yi da maganar mahaifina da komai nawa.’’

Cikin tsananin bacin rai Mommy ta yi wurgi da hannun ta kafin ta mik’e tsaye tace
‘’Kar ki kuskura,
Wallahi kar ki soma Kausar,bana son iskanci da sabon rikici a cikin gidan nan
bazai yiu ba.Dan haka tun wuri ma ki farka,dama naga take taken ki tun last month ashe kuwa hassashen dana keyi gaskiya ne.
To bari kiji,ki bud’e kunnuwan ki da kyau
Wallahi ba zan yarda ki raba min kan ya’yana ba,Ina raye.’’

Ahankali hawaye yana zuba Kausar d’in tace
‘’Saboda ni d’in ba y’ar ki bace ba?’’

Rikici da dimaucewa ne suka sanya Mommy d’auke ta da wani gigitaccen mari

Cikin fushi ta fara magana
‘’Karki kuskura kiyi manipulating d’ina wawuyar yarinya kawai,doluwa,in banda rashin tunani
tayaya ma
zaki bar Yasir dayake tsananin k’aunar ki da tausayin ki
Saboda
Gawurtaccen miskilin mutum irin Yashjub,
wanda nasan ba zai tab’a k’aunar ki ba ko da ace baki kasance budurwar k’anin sa tun asalin farko ba’’.

This time around mikewa tsaye kausar tayi
Cikin fada fada itama tace
‘’Mommy kinga ta inda ake cuta ta ko ?ko kuma ince ta inda ni da kaina na lalata komai sannan na d’aure kaina da jijiyoyin jiki na ta hanyar kasa cewa kowa ba son Yasir nake yi ba,kuma kina so kisan dalilin daya hanani yin magana ?’’
Bata jira jin amsar Mommy wadda ta kafe ta da idanuwa ba ta d’aura da cewa
‘’Saboda kawaici da kunyar in kalli idanun y’an gidan nan in ce musu banason Yasir,
banda haka
Wallahi tallahi kinji dai na rantse ban taba son Yasir ba tunda nayi wayo na san kaina,
friendship dai tun yarinta nasan akwai shi,Ina son sa a matsayin Aboki apart from that nothing else.Yashjub shine wanda nasan inaso tun taso wata har kawo yanzu da soyayyar sa take neman kashe ni Mommy,wallahi inda ace ba Yash nake so ba tou da zan
iya hak’ura in auri Yasir amman matsalar shine baxan iya auran k’anin wanda zuciya ta take k’auna ba.
Ta karashe maganar tana mai durkusawa ta kamo kafafuwan Mommy cikin kuka tace
‘’Mommy dan Allah ki fahimce ni nayi kara nayi kawaici amma zuwa yanzu in na ce zan ci gaba da yin kawaicin tabbas cutuwar zata yi min yawa wallahi mutuwa zanyi
Ki fahimce ni Mommy dan Allah.’’

Suna a haka
Yasira ta shigo ta same su
da sauri ta k’arasa ta d’ago Kausar d’in ta shiga lallashin ta
kafin ta kalli Mommy tace
‘’Daddy ya dawo,ya nata neman ki’’.

Dakyar Mommy ta iya jan k’afafuwan ta ta fice daga parlourn ba tare da ta kalle su ko ta sake ce musu uffan ba.

Tana fita Yasira ta kalli Kausar wadda har yanzu take ta faman gunjin kuka tace
‘’Sannu,dan naga k’ok’arin ki,amma kuma mood d’in Mommy kad’ai yasa jiki na yayi sanyi,i really wanted to help u amman inga gara kawai ki hak’ura haka dan gashi Mommy kanta bata baki goyon baya ba,dama nasan tunda case d’in ya shafi favorites d’in ta ba lalle kiyi nasara ba
no matter yadda kuke ke da ita’’.
Shiru Yasirar tayi kafin taci gaba da cewa
‘’Kiyi hak’uri sis,ki hak’ura kawai.’’

Ahankali cikin goge hawaye Kausar tace
‘’Yasira
Yasir da Yash and me
ne favorites d’in Mommy ko kin manta?zaki ce na gaya miki
Mommy Tana side d’ina.’’

Da mammaki yasira ta ke kallon ta.

With full confidence Kausar d’in ta sake cewa ‘’yeah,
za kuma kice na fad’a miki.’’
Ta na gama fad’in haka ta juya ta fad’a toilet dan ta wanke fuskarta,
duk da tana fargabar yadda zata kaya tsakanin ta da Daddy,Yash da Yassir amma tasan tunda yanxu Mommy m tana bayan ta to komai zaizo da sauk’i,although Mommyn bata fad’a mata direct she’s on her side ba
but ta gani a yanayin ta da idanun ta so tasan definitely tana bayan ta.
Tun kafin yash ya dawo
ta lura da yadda Mommy ta d’aga hankalin ta akan tarin dukiyar sa,
tabbas Yash bai saba da Mommy sosai ba kuma bama a gabanta ya girma ba shiyasa duk ta bi ta d’aga hankalin ta,
babu abunda ta lura Mommyn bata so irin Daddy yayi maganar auren Yash da wata
kuma tasan ba dan komai yasanya Mommy bataso Yash ya yi auren ba sai dan saboda kar wata tazo ta k’arasa janye Yash d’in da dukiyar sa gaba d’aya ba tare da ita Mommyn ta samu sun shaku da Yash d’in ba.
Tasan Mommy kamar yunwar cikin ta
No matter how take ji da Yasir
bazata tab’a bari ga kausar data nuna tanaso ace
Kuma wai Yash yaje ya auri wata ba,dan tasan in dai Yash ya auri Kausar tou da shi da dukiyar sa kamar sun dawo hannun ta ne sun gama ………


Shinkafa mai kyau da kayan miya harda nama Ya Musbah ya kawo,ba yadda Jidda bata yiba amma sam Manubiya tak’i hak’ura sai da ta saka mata hannu a aikin.Dama tun suna girkin suka dunga shiga one by one suna yin wanka
Dan haka
Girki yana kammaluwa dai dai nan suma sun shirya abunsu tsaf.
Babu d’akin da basu shiga a gidan sun sanar musu da rashin lafiyar Inna ba,
Amman ba wanda ya basu ko sisi
Anty umma ce ma tace inshaaAllah zuwa anjima zata je ta asibitin ta duba ta in siyama ta dawo.

Baba Habu kuwa naira d’ari biyu ya basu yace su siya mata lemon zak’ii su gaishe ta suce yana mata ya jiki, Allah ya bata lafiya,
Muhsin ne ya karba sukayi godiya shi da Jidda daganan suka fito suka kama hanyar asibitin ….

A ward ya musbah ya san ya bar su
amma suna zuwa
Nurse d’in tace masa ai an maida ita aminity 2.
Yana mamaki yana komai yayi gaba shi da su Manubiya suka nufi aminity inda aka nuna musu,suna shiga suka tarar da Al’ameen a zaune,In banda kamshin kaji da youghurt ba abunda d’akin yake yi,hatta ruwan sha ya siyo wajen katan goma da lemuka sai kace waenda zasu bud’e shago ne.

Tunda suka fara shigowa ya kafesu da ido,kasancewar jiddan ce a karshe ya sanya bai ganta ba har sai da dukkan su suka ida shigowa tukunna, ahankali ya sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya kafin ya sunkuyar da kan sa k’asa ya lumshe ido.
Itama jiddan tunda ta shigo suka had’a ido gaba daya duk sai ta diririce.

Cike da damuwa da rashin jin dad’i suka matsa kusa dasu baba,da kulawa suka gaida mahaifin nasu su duka hud’un
tare da tambayar sa ya jikin Inna wadda suka tarar tana bacci,
Ahankali shi da Al’ameen sukace ‘’Alhamdulillah’’.
daganan Al’ameen da Ya musbah sukayi musabaha cikin mutanta juna,da girmamawa Muhsin ya gaida sa,haka ma jiddan ta shiga gaida sa dakyar ba tare data kalle sa ba,
sai da ya kalle ta yad’an yi murmushi tukunna ya amsa da kulawa.
Cikin rashin kuzari Ya Musbah wanda ya gama k’arewa d’akin kallo ya kalli Al’ameen d’in yace
‘’Al’ameen, wannan duk aikin ka ne ko ? wahalar batayi yawa ba kuwa ?’’

Sai da yayi murmushi tukunna ya mik’e tsaye yace
‘’ko d’aya Ya musbah fatan mu Allah ya bawa Innarmu lafiya,
ni bari in wuce,zuwa anjima inshaaAllah zan dawo.

Har Manubiya zata yi magana
sai kuma suka had’a ido da baba wanda tun dazu taga ya kafeta da ido.

Cikin d’an sigar zolaya Al’ameen d’in ya k’arasa kusa da ita yace
‘’Adda manubiya ina wuni’’
yana d’an murmushi.
Taso ta amsa sai dai kuma takaicin daya taso mata ya turnuke ta lokaci guda yasanya bata ma san lokacin data wuce sa ta isa kan kujerar daya tashi akai ta zauna ba.
Ahankali ya kalli Jidda datake kallon su tun dazu
Ya ce
‘’Sai anjima,Allah ya k’ara sauk’i’’.

Sai da ta sunkuyar da kanta k’asa tukunna tace
‘’Ameen,mun gode’’.

Murmushi kawai yayi daganan yayi musu sai anjima, yasa kai ya fita.

Yana fita Manubiya tace
‘’Haba Baba,ya zaka yarda Al’ameen yayi mana wannan hidimar haka,salon mahaifiyar sa tazo ta d’agawa kowa hankali??’’

Da sauri ya d’aga mata hannu
Kafin yace
‘’Fad’a kike yi min?’’

Cikin yin k’asa dakai tace
‘’Kayi hak’uri’’
A hankali.

Sai da ya duba Inna ya tabbatar da baccin nata yayi nisa tukunna ya kalli yaran nashi gaba d’ayan su
Kafin a hankali ya fara magana

‘’Kuyi hak’uri,nasan na gaza muku a matsayi na na mahaifin ku,
A koda yaushe ina jin takaicin halin da muka tsinci kanmu a cikin sa duk ta dalilin taurin kaina,dan nasan inda ace tun farko da sana’a tak’i karba ta na koma karatu da

Please Login or Register in order to submit comment