Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wuri da yanzu ina da aiki na.Ina jin tausayin ku a ko da yaushe sai dai yanzu ban san da wanne ido xan iya cigaba da kallon ku ba.
Tun wanchan watan daya wuce mutumin da ya ara min kud’i lokacin da za ayimin aikin k’afa a yanke yazo da takardar sammaci,bana so ya d’aga maganar kowa ya ji,
domin a lokacin ma Innar ku tana asibiti,shiyasa daya buk’aci zai fanshi kud’in sa da gareji na na yarda na amince akayi komai cikin lumana.’’
Sai da Baba ya runtse idanun sa ya bud’e su tukunna ya d’aura da cewa
‘’Jiya kuma na siyar da fili na wanda ake rini a ciki ake biyana duk shekara,
sannan a halin da ake ciki yanzu,mai gareji yace yana buk’atar kangon zai fara gini a ciki
d’an sa zai yi aure,dama ba wani abun kirki ne a ciki ba
sai en kayan gyaran mota da benchi.
Ba komai yasa nake fad’a muku a yanzu ba sai dan kusan a yanzu bani da komai
dama filin nake shirin siyarwa in fanshi gareji na
nasan koda rabin kud’in ne in na ba sa zai iya jira daga baya in cika ma sa ragowar,to kuma sai maganar aikin Innar kun daya taso jiya gadan gadan yasanya dole in siyar da filin a fara shirye shirye tunda lafiya itace a kan gaba.
Kuyi hak’uri ku yafe wa mahaifin ku na gaza maku
tun farko ban baku kyakkyawar rayuwa ba yanzu
kuma bansan wacce irin rayuwa zamu yi a gaba ba,ba fili ba gareji’’.
Ya karashe maganar tashi yana me fashewa da kuka.

Da sauri
Ya musbah ya matsa kusa da shi ya durk’usa a gaban sa ya kamo hannayen sa cikin karyewar zuciya ya fara magana
‘’Baba karkace haka dan Allah,ai ba dole bane sai ka bamu rayuwar daula ba,abun da yake akan ka shine
ka bamu tarbiyya sannan kayi iyakar k’ok’arin ka wajen tufatar damu da ciyar damu
sai kuma muhalli
wanda baka tab’a gaza wa ba,
bamu da abun da zamu ce maka sai godiya ,fatan alkhairi da kuma adduar Allah ya saka muku da gidan aljannah kai da Inna Allah kuma yasa ku gama da duniya lafiya.
Baba kana cikin uban da ko wanne d’a zai yi alfahari da,
dama yanzu ai lokacin hutun ka ne
nema yana a kaina yanzu
Dan haka ka daina d’aga hankalin ka dan Allah’’

Ahankali itama Manubiya ta matso tace
‘’Baba gaskiya Ya Musbah ya fad’a,nasan bamu tashi a had’ad’d’en gida cikin daula ba
Amman Allah ya azurta mu mahaifi mai tsananin son mu da k’aunar mu,dan Allah ka kwantar da hankalin ka,
dan nikam ko da ace za a dawo da duniya sabuwa a bani damar in zab’i mahaifi wallahi kai zan zab’a Baba.’’

Cikin sharar kwallah Jidda tace
‘’Iyaka soyayyar ka da kulawar ka a garemu ta wadatar Baba
InshaaAllah zamu taimaki juna daga yanzu,kar ka damu da salwantar da garejin ka ya yi
nasan ubangijin daya halicce mu bazai hanamu abin da za muci ba
Kuma inshaaAllah ubangiji zai kawo mana mafita cikin sauk’i’’.

Garejin na sa ba wani kud’i yake kawo masa ba tunda babu ciniki sakamokon kayan aiki da suka yi musu k’aranci kuma babu kud’in saye,
sai filin sa da masu rini suke biyan sa dubu talatin duk shekara,
dasu ya dogara da su yake ciyar da iyalin sa gashi yanzu ya rasa su a lokaci guda,
bai san ya zaiyi ba baisan ya zasuci abinci ba amma kamar yadda yaran suka fad’a yanzu,
Allah zai san yadda zai yi da su.

Yarda da k’addara da kuma kalaman su masu dad’i da kwantar da hankali ne suka dan kwantar wa da mahaifin nasu hankali. …


Jidda ce ta zuba masa abinci suka tilasta masa har saida suka ga ya d’an ci da dama tukunna suka kyale sa.

Hamdala da tasbihi
Baba musa ya ke ta jerowa a chan k’asan zuciyar sa
dan shi kam ubangiji ya gama azurta sa,da yaran da ko wanne uba zai yi alfahari da,
hankali, nutsuwa da tsantsar sanin abun da ya dace
duk sun had’a.
Gashi dai yanzu k’iri k’iri sun dage su nata k’ok’arin ganin sun kwantar masa da hankali
sun kuma nuna ma sa ba komai
amma
su kuma gashi k’iri k’iri yake
hango tsantsar tashin hankali a idanun gaba d’ayan su,har Muhsin. ……………





MANNUBIYA
08
Na
Humayrah Bulama

ELEGANT Online ✍️


Kausar Tana fitowa suka sauk’a k’asa tare,ita da Yasira.

A dining table suka hango gaba d’aya ahalin gidan a zaune,in da Daddy yake suka nufa domin su gaida sa Sannan suyi masa sannu da zuwa, suna isa suka durkusa cikin girmamawa suka gaida shi a tare tare da yi masa sannu da zuwa,
da kulawa ya kalli Yasira ya dafa kanta ya amsa kafin ya kalli Kausar kamar zai amsa sai kuma ya dauk’e kai ya dauk’i ruwa yana shirin sha yaji ta sake cewa ‘’barka da dawowa Daddy’’
Ba tare daya kalle ta ba yace
‘’Yauwa’’ daga nan ya kora ruwan daya kai bakin sa ta mak’oshin sa.
Ba iya kausar d’in ba hatta Yasira dakyar ta iya mik’ewa suka wuce suka nema waje suma suka zauna.

Babban dining table ne sosai
mai d’auke da kujeru wajen goma sha biyar
Daddy ne zaune a
Seat d’in tsakiya ata farko wanda yake facing na karshe inda Mommy take zaune,
Yashjub da Yasir sun saka Daddy a tsakiya a ta gefe da gefen sa,a kusa da Mommy kuma
Yasmin da ya’isha ne
Yasmin ita ke bin su Yasir da Yasira
Shekarunta 25 a duniya,likita ce, sai Ya’isha mai shekaru 24 a duniya wadda ta fara masters recently a Dangote Business School.
A kusa dasu kuma
Yusra da Yadira ne
Yusra shekarunta ashirin a duniya ita take bin Ya’isha tana karatu a B u k level 3
Sai auta Yadira wadda take itama a buk level one shekarunta sha bakwai a duniya.

Cikin nutsuwa Daddy yayi serving kan shi daganan kowa ya shiga zuba abunda ran da yake so,
Ganin Daddy bai kai ko loma d’aya ba har yanzu yasanya suma duk suka tsaya,
Shiru dining d’in ya d’auka gaba d’aya
Kafin chan Mommy tace
‘’Na lek’a ta dazu tun kafin ka sak’k’o,amma sai ta cemin a k’oshe take.’’


Shiru yayi bai tanka mata ba
ganin hakan ya sanya ta mik’e ta nufi k’ofar wani d’aki anan cikin main parlourn tana ta faman guna guni.

Batayi mintina hud’u da shiga ba suka fito tare ita da wata farar budurwa wadda ak’alla zata kai kimanin shekaru 29 a duniya,bata da jiki sai dai doguwa ce sosai,kallo d’aya tak zaka yi mata ka gano tsantsar kamannin ta da Daddy wanda tun fitowar su ya kafe ‘yar ta sa da idanuwa yana mamakin tsantsar ramar da yaga ta sake yi.

A kusa da Yashjub Mommy ta zaunar da ita

Daganan ta koma mazaunin ta itama ta zauna.
A hankali suka shiga passing mata kulolin abincin zuwa gaban ta,bata zuba ba sai da ta fara sunkuyar da kanta ta gaida Daddy cikin girmamawa tare da yi masa sannu da xuwa dan itama ya dawo ba,
da kulawa ya amsa ta daganan ta shiga zuba abunda ranta yake so,
tana gama wa Daddy yayi bismillah ya fara,
Bismillah suma duk sukayi
daga nan aka gabatar da dinner d’in cikin nutsuwa.

sai da kowa ya kammala,
tukunna Daddy ya juya ya kalli
Yahanasu
Yace
‘’Lafiyar ki kuwa ?
duk naga kin sake ramewa’’.

Murmushi tayi ahankali
kafin tace
‘’Lafiya ta k’alau Daddy,
Alhamdulillah’’.

Ya jima yana nazartar ta kafin daga baya ya d’auke kai ya maida hankalin sa kan Mommy ya fara magana
‘’Akwai Aboki na senator Bashir
bawai ya kaini shekaru bane ba kawai dai tamu tazo d’aya ne shiyasa muka zama abokanai
Matar sa d’aya,yayi min maganar yanason ya k’ara aure ne
Shine na ba sa izinin yazo yaga Yahanasu
In sun daidaita
Alhamdulillah.
Nasan sa tun ba yau ba shima haka ya sanni so banajin za’a samu matsala wannan karon InshaaAllah,na bar komai a hannun ki ku shirya tarbar sa da kyau ranar juma’ar nan zai zo.’’

Ahankali mommy tace
‘’InshaaAllah Daddy,sannan da yardar Allah baza’a samu matsala ba.’’
Tayi maganar tana mai yiwa Yahanasu addu’ar dacewa a wannan karan ko ba komai hankalin kowa zai kwanta.

Ahankali yahanasu da gaba d’aya hankalin ta ya tashi lokaci guda tace
‘’Daddy, Dan Allah…’’

Cikin rashin son ya saurare ta yace
‘’Sai magana ta ta biyu.’’

Atake duk suka tattara hankulan su suka maida akan sa
Ganin yadda lokaci guda ya sake tamke fuskar sa ne
yasanya
duk suka sha jinin jikin su.

‘’Yashjub ya sanar dani
Irin tabargazar da yaran nan suke shukawa’’
Daddy yayi maganar yana nuna Yasir da Kausar.
Kafin cikin b’acin rai ya kalli Mommy ya ce
‘’I’m really disappointed in you,
da ke da su bansan wa ya fi wani ba.
Anyways,na riga na gama yanke shawarar d’aura musu Aure gobe da safe in sha Allah
dan ban shirya d’aukar shege a karo na biyu a cikin gida na ba’’…

Tun kafin ya kai k’arshen aya Kausar ta fashe da wani irin kuka,cikin sheshshek’ar kuka tace
‘’Allah ba zan aur……’’

Ai kuwa a take Daddy ya mik’e da shirin isa in da take,
ganin haka ya sanya ta kwasa a guje tayi sama.
Yaso ya bita yaci k’aniyar ta dan dama a mugun k’ule yake da ita,bayajin haushin Yasir kamar yadda yake jin haushin ta,sannan a ganin sa ita ta b’ata Yasir tun asalin farko shi kuma bai farga da wuri ba shikenan garin tausayi gashi yarinya tana neman tarwatsa masa tarbiyyar Yaro ko ma ace ta tarwatsa d’in…
Muryar Mommy ce ta katse sa
jin tana cewa
‘’Daddy u need to reconsider,
wannan abun da kake shirin yi ba dai dai bane ba
kuma lokacin daka d’auka a gaskiya yayi kad’an,
dan Allah ka sake tunani.’’

Cikin tsananin bacin rai yace
‘’Bar ganin a gaban ya’yan ki kike,wallahi yanzun zan kifar da ke,kin bar yara suna shashanci sannan yanzu ana k’ok’arin gyara abu amma kina k’ok’arin kawo tangard’a akai ??
karfa ki bari rai na ya k’arasa b’aci dake
wallahi ba za ki ji dad’i na ba’’.

Yana gama fad’in haka ya juya fuuu ya wuce saman shima ya nufi side d’in sa.

A zuciye Mommy itama ta mik’e ta k’arasa inda Yashjub yake tsabar fushi bata san lokacin da ta rufe sa da fad’a ba
baki da kumfa ta shiga cewa
‘’Mai yasa kake da muguwar zuciya ne?yanzu kukan da take yi dad’i yayi maka ko mai?
ka fini sanin ciwon kaina ne?
ko kuwa ka fini sanin abun da yafi dacewa ayi ?tunda har kaga nayi shiru ai kasan akwai dalili dai ko ?’’

Ahankali ya d’ago lumsassun idanuwan sa ya zuba mata ba tare da yace uffan ba,
Ganin yanayin kallon da ya ke yi mata ne ya sanya ta yin shiru a take ta kauda kanta daga gareshi ta had’iye ragowar maganganun ta.

Ya jima yana kallon ta kafin ya d’auke idanuwan sa daga gareta ya fesar da iska ya mik’e tsaye daganan ya fara k’ok’arin barin wajen.

Cikin tsananin sanyin jiki tace
‘’Yash’’
Juyowa kawai yayi ya tsaya yana kallon ta.
Gaba d’aya kuma sai ta diririce ta gagara cewa komai
Ta hau kame kame
‘’am dama a ganina bai kamata ka gayawa Daddy …..

Ahankali yace ‘’Mommy ..’’
ya d’an girgiza mata kai yana mai lumshe idanun sa ya bud’e
daga haka ya juya ga Yahanasu yace
‘’Allah ya tabbatar da alkhairi.’’
Yana gama fad’in haka ya sa kai ya fice daga parlourn ko sai da safen su Yadira bai tsaya amsawa ba.


Mommy ji tayi kamar ta d’aura hannu a ka ta yi ta kurma ihu,
Tabbas in akwai yaron da bai San darajar mahaifiyar sa ba tou Yashjub ne,
tana tsananin k’aunar Yasir amman ya zama dole ya hak’ura da Kausar Yashjub ya aura dan bata hango shak’uwar da take kwad’ayin samu daga gare sa ba muddin yayi aure ya tare chan da wata ba Kausar d’in ta ba
Especially ma inya samu wadda yake so
Shikenan ta zama er kallo a gefe ..

Tana wannan tunanin ta dake ta cire tsoro ta nufi sashen Daddy
da niyyar tana gamawa dashi kuma zata lek’a d’akin baba larai saboda tabbas a yau take so ayita ta k’are!!

Ahankali kowa ya fara watsewa daga dining table d’in
Ya rage saura Yasir kawai

Ya yi mamaki had’e da jin zafin yadda k’iri k’iri ya hango rashin amincewar auren nasu a kwayar idanun Mommy
shiyasa tun lokacin ya fad’a duniyar tunani ya gagara cewa komai har izuwa yanzu da kowa ya watse ya bar sa a wajen.

Ahankali ya mik’e ya nufi sama sashen Kausar
amman ko da yaje sai ya tarar da k’ofar ta a rufe ruff,
Ba kalar bugu da kiran wayar da bai yi mata ba amma sam tak’i yarda ta bud’e
haka nan ya gaji ya kama hanya ya sauk’a ya fita daga sashen gaba d’aya ya nufi nasu
wanda yake a jikin mansion d’in amma k’ofar su ta baya take da wani makeken compound a wajen wanda yafi ma na gaban gidan dan saf za a iya gina irin mansion d’in guda a wajen
Da harda gate d’in su daban
a wajen saboda yawan yawon dare da Yasir ya tsira yakeyi ne
ya sanya aka rufe gate d’in Daddy ya hana fita ta nan gabad’aya.

…. Parlour ne babba sosai
sai kitchen,dining area da 2 bedrooms a k’asan
sama kuma 2 bedrooms ne ko wanne da parlourn sa sai saperate d’aki guda d’aya,
Side d’in nasu ta b’angaren mansion d’in mai hawa biyu ne
sab’anin nasu Daddy da ya had’a hawa uku ….

A nan main parlourn ya tarar da Yash yana zaune yana sipping tea yana waya a hankali,
So yake ya tambaye sa abu dan haka ya nema waje ya zauna shima akan d’aya daga cikin kujerun parlourn,
sai da ya zauna tukunna ya fahimci ashe da Abokin sa ‘Najeeb’ yake waya

Wani dan guntun Murmushi Yasir yayi a ran sa yace
‘’Haba, dama ni dai nasan ba da mace yake wayar nan ba
mutum sai kace waliyyi …..’’

Ya fi 1 hour yana waya kafin finally ya ajjiye wayar ya d’ago ya na kallon Yasir yace
‘’Lafiya?’’
Sai da yad’an sosa kan sa tukunna yace
‘’Um dama ina d’an son…’’

Tun Kafin ya k’arasa Yash din yace
‘’Kud’i,ko?’’

Murmushi yayi Kafin yace ‘’yess,a lot.’’

Ahankali Yash ya mik’e
sannan yace
‘’Yadda Daddy ya zuciya daku
In kayi dinner ko wani shirme a auren nan kasan ranka zai yi mummunan b’aci,therefore ba zaka samu kud’i daga gareni ba gaskiya’’.
Yana gama fad’in haka ya wuce sama.

Yasir ji yayi kamar ya bi sa ya make sa ,a ran sa ya ce
‘’Munafuki ai kaine ka janyo Daddyn ya ke fushin damu duk da dai munafurcin naka yau yayi min rana tunda gashi gobe za a aura min farin ciki na .’’

Mutsutstsuka idanun sa yayi ya fesar da iska kafin ya mik’e shima ya wuce saman yana tunanin ta yadda zai yi raising kud’i
dan ba zai yiu ace bikin su shi da Kausar amma wai ba dinner ba shagali ba ……

…….
A bakin gado Mommy ta samu Daddy a tsaye yana shirin shiga wanka,
Yaji shigowar ta, dan haka ba tare daya kalle ta ba yace
‘’Don’t try anything stupid Khadijah
daga nan har gobe,ban san game d’in ki wannan karon ba amma ina shawartar ki da
kar ma ki fara
In ba haka ba zan baki mamaki.’’

Ba tare da fargaba ko tantama ba tace
‘’Ba wai shirin hana auren zan yi ba,dan na riga na gama shiri na,kawai dama naga kamatar in sanar maka ne
So
Inaso in ce kajanye maganar auren Yasir da Kausar dan
ba mai yiu wa bane ba.’’

Sai yanzu Daddy daya gama d’aura bathrub ya juyo gareta ya d’an taka inda take ya tsaya
tukunna yace
‘’Dole, a gobe Kausar zata fitar min daga gida Khadijah,
It’s either ta wuce gidan Yasir ko kuma tasan inda zata je,
nayi iya yina.’’

Wani kalar murmushin takaici Mommy tayi
kafin tace
‘’Ai dama nasani na san ka gaji da rik’e ta ne shiyasa zaka yi mata auren dole.’’


Cikin fushi Daddy yace
‘’A kul d’inki Khadijah,
In ke dak’ik’iya ce baki san ciwon kan ki ba baki san kishin d’an da kika haifa a cikin ki ba tou ni nasani,
Ki godewa Allah ma da har na yarda Yasir zai auri Kausar d’in,
Allah na tuba Maraici ai ba hauka bane ba
Yarinyar nan fa har haihuwa tayi sannan bata da uba
amma duk da haka na amince na yarda zan aura wa Yasir ita
Shine amma har kike da bakin cewa za ayi mata auren dole?’’
Daddy bai tsaya jin amsarta ba ya d’aura da cewa ‘’Bari kiji,ba don na san Yasir yana da ikon
k’ara aure ba to da ba zan bar shi ya auri shegiya ya rayu da ita ba.’’

Kamar an kunna fanfo haka fuskar Mommy ta jik’e sharkaf da hawaye
Cikin kuka tace
‘’Na gode ‘Imam’ na gode sosai
alk’awarin kenan ko?
Allah ya ji kan Abba da Daddy,
A gaban su ka amince zaka rik’e Kausar ruk’o na amana
amma yau da kanka kake cewa ta fitar maka daga gida
da kanka kake kiran ta da sunan shegiya,
D’an Adam butulu walllahi Allah sai yayi mana hisabi.’’


Cikin tsananin b’acin rai yace
‘’Dole in ce Kausar ta fitar min daga gida,Khadija
‘Ya’yana takwas a duniya amma ba wadda a kullum take d’agamin hankali take janyo min abun kunya da magana sai y’ar ruk’o,ko su mazan basa yin fitinar da take yi,
Kalli yanzu yadda ta lalata Yassir,
shikenan ni
Kullum gidana cikin case saboda ita?
Ki duba fa kiga yau tafiya nayi na dawo amma ko ishashshen sannu da zuwa da hutawa wa ban yi ba na fara da case din y’ar ruk’o.’’

Cikin d’aga hannu (alamun stop )
Mommy tace
‘’Dakata daganan Daddy
Maganganun ka ga Kausar sun ishe ni,sannan in baza ka kirata da Kausar ba to
Kayi shiru
dan shegiya ko y’ar ruk’o ba sunan ta bane ba,gorin ka a cin fuskar ka yayi yawa,
kuma ta Ina kausar ta lalata Yasir?fyad’e tayi masa?
da aka ce maka sun tafi aucland d’in tare shi munafukin naka camera ya mak’ala musu yaga sunyi wani abun
In fact Ina ba su kadai suka tafi ba ??
harda fa frnds d’in su.
Kawai kai dai ka tsani Kausar
na riga na sani tun ba yauba ka tsane ta shiyasa kullum burin ka kaga ka k’untata mata,
tayaya ma za kace wai kausar ta lalata maka ‘da haba Daddy
ka dinga adalci mana
ko kara babu?’’

Cikin takaici Daddy yace
karar dana yi tun farko ita ta cutar dani gashi inaji Ina gani
Yasir zai auri matar da sai addua kawai kuma a matsayin uwar gida
in jikokina suka tashi a gagara nuna musu dangijn uban mahaifiyar su’’.

Cikin jin jina kai Mommy tace
‘’shike nan tunda kai ba mahaifin ta bane ba
ka fad’a ka nuna ka furta
Tou daga yau
Inaso ka tsame hannunka a rayuwar yarinya ta

Aure kuma da Yasir tunda har kana ganin kamar za a cuce sa ne to wallahi baza a d’aura ba
In kuma ka d’aura to za a sha mamaki na.
Tunda baka son had’in
yafi nono fari
muma bama so,
Kuma inshaaAllah daga yau
Ni zan dinga kula da ‘ya ta
babu ruwan ka da duk abun da ya shafe ta
zan nemo cook inn siyo kayan abinci a dinga mata girkin ta a daban
k’arshen wata kuma zamu dinga biyan ka kud’in haya
ruwa dana wuta,all I want from you shine ka daina takura mata kuma ka daina yunk’urin yi mata dole,
Iyakar ku gaisuwa
Tunda a iya sani na ba inda Kausar zataje muddin Ina cikin gidan nan har sai ranar da Allah ya kawo mata wanda take so ta aura tukunna.’’
Tana gama fad’in haka ta juya zata fita sai kuma ta juyo ta dawo inda yake nan tsaye ranshi a mugun b’ace tace
‘’Allah dai yaso ba y’ar uwata kad’ai bace ta fara haifar shege
kafin tayi kafin Kausar tayi sai da aka yi,
Ko inje in kawo maka Yahanasu?
Maybe in ka kalli fuskar ta zaka iya tuno da wadda nake nufi da kuma abubuwa da dama,
saboda kalaman ka da k’iyayyar ka ga shege ta sanya na fara tunanin maybe kayi loosing memory ne.
A yadda ka tsani Kausar kake kyamar ta na tabbatar da cewa tafi dubu saboda na tabbatar in dai Kausar ta auri wanda take so kuma yake son ta
baza ta tab’a cutar sa ba baxa’a kamata da wani ba
saboda ‘yata tanada ruk’on amana kuma nasan tasan darajar soyayya………..


Cikin tsananin fushi Daddy ya yunk’ura da dukkan nin k’arfin sa ya d’auke ta da wani gigitaccen mari.

Dagowa tayi da niyyar ci gaba da tsiwa taga yanayin sa da idanuwan sa dan haka ta had’iye maganganun ta da tsiwar ta
domin a yadda taga yana kallon ta da jajayen idanuwan sa tsaf zai iya illatata.

Dakyar ya iya cewa
‘’Fita kar in sake ganin fuskar ki in ba ni na neme ki ba.’’

Ba musu
Haka ta juya ta fice daga d’akin dan ta tsorata da yanayin sa
tana fita kuma sai taji wani sanyi ya lullub’e ta a haka ta fita daga side d’in nasa gaba d’aya ta sauk’a tanajin zuciyar ta fess,
Tabbas tasan dama in ba da gaske tayi ba ba lalle ta iya hana auren nan ba
Amman a yadda ta tsokalo Daddy ta tuna ma sa da baya
ba lalle ya iya shan ruwa ba ma daga nan har Jibi,Yayin da a chan k’asan zuciyar ta kuma sai taji kishi yana taso mata
Sakamokon k’unci,damuwa da tsananin kishin data gani a idanuwan Daddy kamar
jiya jiya abun ya faru …………


Kamar yadda Al’ameen ya fad’a
Da yamma kusan magrib sai ga sa ya dawo da laidoji nik’i nik’i,yaci sa‘a kuwa Jiddah ce a wajen
Manubiya an tafi yi mata test
saboda tunda Baba ya lura ba ta da lafiya ya damu
Dakyar ya wuce gida shi da Muhsin ya barsu tare da Ya Musbah akan in komai yayi settling shi sai ya dawo ya bar Jidda da Manu su kwana
washegari kuma ya koma su dawo suyi girki,in Allah ya kaimu.

Tunda ya shigo ta diririce
gashi Inna ma bata jima da koma wa bacci ba.
Dariya taso ta ba sa dan kamar irin zai sace ta d’in nan haka yaga tanayi,
Cikin sanyin murya da sanyin jiki ta gaida sa
shikuma
Ya amsata da kulawa yana tambayar ta ya jikin Inna

Ahankali tace ‘’da sauk’i’’

Har zai zauna sai kuma ya k’arasa gaban gadon ya ajjiye ledojin yace mata ‘’gashi’’
tukunna ya dawo ya zauna.
Dakyar tace ‘’mun gode’’
Sai kuma ta d’anyi shiru kafin tace
‘’Ya Al’ameen ka daina dan Allah’’

Wani d’an guntun Murmushi yayi Kafin yace ‘’in daina me?’’
Ya fad’i hakan yana mai kafeta da idanuwa

Sai da ta d’an d’auki lokaci tukunna dakyar tace ‘’ka daina kallo na sannan dan Allah ka daina zuwa mun gode sosai amman Ina tsoron Ammi
kar tazo ta gane kana zuwa nan kaga Inna bata da lafiya in aka fara wani case na daban kuma abun bazaiyi dad’i ba’’.

Ahankali ya sauk’e ajiyar zuciya kafin yace
‘’Ko yanxu kafin in taho saida na gayawa Ammin inda zanje’’

Da sauri Jidda ta dago manyan idanuwan ta tana kallon sa,
Shima itan yake kallo dan haka tayi saurin yin k’asa da kanta.

Murmushi kawai yayi kafin yace
‘’Jidda I love you,
nasan Ammi na
tana son duk abun da nake so,
wanchan karon ma mishkila aka samu kuma bana nan amma yanzu komai ya daidaita
ki kwantar da hankalin ki dan Allah,
Tace ma zata zo har nan ta duba Inna
sannan tace in cewa su Baba suyi hak’uri komai ya wuce.
Kuma ko yau kafin in fito ma sai da mukayi magana da ita akan
Ina dawowa daga tafiyar nan dazanyi inshaaAllah xa a fara maganar auren mu kuma ta amince d’ari bisa d’ari tace baza ma a d’auka lokaci mai tsayi ba,Abba kam dama shi ba shi da problem tun farko.
So please had’in kan ki kawai nake nema a yanzu,
Nasan kwanakin baya dole kunji babu dad’i kuma kunji haushi amma pls darling kiyi hak’uri ki

Please Login or Register in order to submit comment