Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ace sun d’an fi haka
da sai ya bawa Baraka dubunta goma ragowar kuma ayi hidimar asibiti da shi …

Godiya Sosai yayi har sai da ya bawa ‘dan uwan nafi’un kunya ma
Daganan yayi musu sallama ya burga mashin d’in sa ya wuce
ya barsu anan a tsaye
Kafin suma su juya su nufi k’ofofin gidajen su .
Har suka k’arasa k’ofar gidanjen nasu guda biyu
Ya musbah tunani yake yi ,
tausayin sa Nafi’u yake ji sosai dan yasan in ba matsalar Baraka ba tou matsalar rashin lafiyar mahaifiyar su ce ta sanya shi a damuwa haka

Yana shirin yi ma sa magana yaji Ya musbah ya ce
‘Nafi’u kud’in nan fa Baraka zan bawa ‘’.
A d’an fusace nafi’un yace
‘’Saboda ka zama mijin tace ?’’

Ya musbah
Bai boye wa Abokin na sa komai ba haka ya zaiyyane ma sa abunda ya faru
Sannan ya ‘kara da cewa
‘’ Ba wata maganar en sanda ,
Biki ne take da shi
tsabar bala’i wai ankon super za suyi
Me sunan baba kan sa tayi mishi kaya Masu kyau da tsada sama da kala uku
Amman saboda
Allah ace mahaifiya ta Bata da lafiya
amma sam Baraka Bata damuba ….’’
Ya karashe maganar hawaye suna silalo masa

Da kyar Nafi’u ya iya danne fushin sa
gudun kar ya sake tunzura Abokin nasa,
Sai da yad’an daidaita kan sa
daga takaicin Baraka
Tukunna
Ahankali ya dafa shi
Kafin yace
Kayi hkr Musbah
Komai yayi zafi maganin sa Allah ,
Tunda tayi maka haka kuma Baba yace a Bata kawai a Bata din ,
Ita ta sani
Inde duniya ce
Dede take da ita,
Kawai yanzu matsalar shine inda zamu nemo wani kud’in
Saboda Nima Wallahi babu a waje na
da ace ina da shi Wallahi dana baka,
kasan lokacin biyan kud’in gida yayi
Mutumin nan Sam kasan baya tab’a d’aga min k’afa
har gara kai
Yakan ce ai yasan baka aiki
Gashi wannan term din khairat ta shiga makaranta
shiyasa nima duk na zama a matse ,bani da shi .’’
Shiru ya d’an yi kamar me tunani kafin yaci gaba da cewa
‘’kuma kaga yaya na guda daya tak a duniya na tambaya maka shi shima
amma bara muga ko akwai….’’

Dasauri Ya musbah ya katse sa ta hanyar cewa
‘Nafi’u Karka damu
Na gode Wallahi ban san da wanne baki zan maka godiya ba
Banajin akwai Aboki irinka har yanzu
a duniya
In kuma akwai tou tabbas baku da yawa
Nagode nagode
ka kwantar da hankalin ka
bara inje in bata kud’in
dole haka zan hak’ura in lek’a Innar babu ko sisi
In naje sai a san yadda za ayi’’.

‘’Ok’’
Nafi’un yace
Cikin rashin Jin dad’i
Kafin ya sake cewa
‘’Nima bara in duba gida
In komai normal sai mu tafi tare wajen Innar …..







MANNUBIYA
O4
Na
Humayrah Bulama

ELEGANT Online ✍️

Babu kunya ba tsoron Allah haka Baraka tasaka hannu ta amshe kud’in nan,duk da kuwa ragowar kwallar data gani a idanun mai gidan nata wanda hakan ya tabbbatar mata da kuka yayi ,
Sannan ga jijiyoyin kan sa sun fito rad’au ga kuma farar fuskar sa tayi jajawur
wanda haka yake sake nuna tsananin tashin hankalin da yake a ciki.
Tana amshe kud’in ta shige cikin parlourn su mai ‘dauke da d’akuna biyu ,dama fitowarta daga band’aki kenan ta tarar da shi yana jiran ta .

Ya dad’e a tsaye , kafin ya samu ya ja
Kafafuwan sa ya juya ya fice daga gidan, gabadaya .
Sai a Sannan tabar bakin window inda ta lab’e tana kallon sa tana mai tab’e baki
a ranta tace
‘’Haka kurum in bada kud’ina akai uwar wani ba tawa ba asibiti,bayan ga biki a gabana ,
In na biyeka Musbahu naga alamun sai na gagara shiga k’awaye na wallahi,da mutunci na ka auro ni
amma iyakar inda ka ajjiye ni da suturun daka jeremin a lefe ya sanya yanzu ko hamshak’in taro za’ayi k’awaye na basa gaiyyata ta.’’
Hakanan tayita mita a cikin ranta daga karshe ta shiga kasafta mai da me zata siya da kud’in……

Tun lokacin da suka rabu da Ya musbah ,Baba’ yake tunanin ta Ina zai samo kud’i , duk inda ya duba ya zaga ya zagayo babu hanya , shiyasa gaba d’aya hankalin sa ya sake tashi ,
ahaka sukayi alwallah sukayi salla daganan suka fito daga masallacin suka zauna akan d’an dakalin k’ofar gidan
da shi da muhsin.

Yana cikin tunani yaji wasu zafafan hawaye suna zuba akan kyakkyawar tsohuwar fuskar sa ,sai da ya faki idon Muhsin wanda yayi shiruu shima ya sunkuyar da kan sa k’asa tun dazu
Tukunna yasa hannu ya share hawayen nasa Kafin a hankali ya fad’a duniyar wani tunanin na daban
………Yanzu haka , a tsakiyar en uwan sa yake
Babban yayan su
BABA HABU da matan sa biyu
Umma DIJE da umma KULUWA
Umma dije yaranta mata uku
Zainab ,Hauwa sai Maryam ,
gaba d’ayan su sunyi aure.
Sai Umma kuluwa
tanada Yaro d’aya namiji
‘Ya Yusuf ‘ya girmi Ya musbah da shekara d’aya amma shi bai yi aureba .

Sai d’ayan yayan nashi
UTHMAN
Wanda kowa yake kiran sa da
UNCLE
Uncle yanada mata uku
Kasancewar yana aiki a banki yasa duk ya ‘dan fisu rufin asiri
Matarshi ta farko FATIMA
Umma Fati
Yaro daya tak ta Haifa
Ya iliya (yayi aure)daganan ta samu matsala Bata sake haihu wa ba
ta biyun sunan ta khadija
Itakam ko b’atan wata ma Bata tab’a yi ba ,
Sai ta ukun Anty RUMASATU
Anty amarya
tanada yara biyu mata twins
Shamsiyya da Salaha masu shekaru goma a duniya.

Sai yayar sa
Anty umma (Binta),wadda mijin ta ya rasu ta komo gidan da zama
Yaranta biyu mata ta farkon sunan ta Fiddausi tana aure a illorin sai autar ta wadda ta ke tare da ita ‘Siyama’
Siyama ta girmi Jidda Manubiya kuma ta bata shekara d’aya .

Sai shi Baba (MUSA)
Matarshi d’aya Aminatu (Inna)
Da yaran su hudu
Musbahu mai shekaru 27
Sai
Manubiya mai shekaru 22
Sai
Maijiddah mai shekaru sha bakwai
Da auta Muhsin wanda bai k’arasa rufe shekaru sha d’aya ba .

Duk a cikin y’an uwan nan na sa da suke zaune tare a gida d’aya babu wanda zai tambaya kwandala a cikin su yau ace ya d’auka ya ba sa ,
In ana maganar asalin rashin had’in Kai
Tou shine definition d’in rayuwar Baba da y’an uwan sa ,
Ba hassada babu fad’a babu hayaniya amma fa kowa na sa kawai ya sani ,hatta Anty umma , ba mai ciyar da ita a tsakanin yayyun nasu maza biyu Masu rufin asiri , sai dai ta ci da kanta ta ci da y’arta
Da taimakon y’ar sana’ar siye da siyarwar da takeyi , sai kuma sistern siyaman itama tana taimakawa ba laifi.

A takaice dai kowa ta kan sa yake yi a gidan, kowa nasa ya sani sannan babu ruwan kowa da kowa , yanayin zaman sam babu dad’i ,ga baki ga hanci compound d’aya amma in ba su Manubiyan ba babu wanda wani abun zai faru ace wai ya lek’a d’an uwansa yaji halin da ake ciki.
Mai k’ananun maganganu ,rigima da son had’a fad’a a gidan mutum d’aya ne
Kaka Malan ,
Wani d’an uwan mahaifin su da Allah bai ba sa haihuwa ba
Suka d’auko suka bashi d’aki mai bandaki a cikin compound d’in nasu,
Wanda shima sai yayi da gaske tukunna suke kula sa su zuba ma sa abinci,dan Kaka Mallan irin tsoffin nanne masu tijara ,gulmace gulmace,shishshigi da zalama.
Sukam a tsakanin su babu jita jita
Sai dai
Sam basa tausayin juna
basa kuma taimakawa juna
Idan d’an uwan ka zai kwana bai ciba
Babu ruwan ka ba abunda ya shafeka .

Tun suna yara su uku ,mahaifin su ya zaunar da su ya tambaye su abun da kowa yake son yayi a rayuwa,
Yayyun Baba biyu Uncle da Baba Habu suka zab’a karatu
Shi kuma ya zab’a Sana’a

Kamar yanda mahaifinsu yayi alkawari
Karatu har sai da sukace sun gaji
Shi kuma aka damk’a ma sa mak’udan kud’ad’e aka ce yaje ya yi Sana’a.
Abun nashi kamar sa hannu
duk sana ‘ar daya soma bata Al’barka
A haka har jarin na sa ya k’are tass.

Uncle Baba habu da Anty umma mahaifiyar su d’aya
Yayinda shi kuma ya kasance d’an gidan amarya
Mahaifiyarsu Uncle ce ta fara rasuwa kafin tashi mahaifiyar wadda ta rasu wajen haihuwar sa.
Tun suna yara sun taso basu da wani had’in kai ,tun lokacin da iyayen su mata suka rasu mahaifinsu bai k’ara aure ba shima har ya bar duniya.
Hakanan suka tashi a wannan gida da suka gada kowa yayi
auren shi yake rayuwar sa daga shi sai iyalin sa
Duk cikinsu shine mai d’an karamin waje
Sakamokon siyar musu nashi portion d’in daya dinga yi saboda ya samu ya sake jan wani jarin sannan kuma aci abinci a gidan sa .
Ko da ya haifi musbahu,ya kai minzalin hankali
Yaso ya d’aura shi akan layin Sana’a shima,har rantar kud’i ya dunga yi yana bashi jari
amma shima Sam sanar tashi batayi Albarka ba
Ganin sanaar baxata yiu ba yasa suka hak’ura
Da ragowar en kudin hannun su da bai kai ya kawo ba suka fara makanikanci dan a lokacin
shekarun Musbahu sun Kai sha bakwai ba damar komawa makaranta
A wannan lokacin ne kuma
Allah ya ‘daurawa baba Musa tsananin son yaga yaran shi sunyi karatu
Shiyasa ya tsaya tsayin daka akan karatun nasu ,
Dan bai yi k’asa a guiwa ba sai da ya sanya su a makaranta,
A lokacin Manubiya har dariya akeyi mata dan tayi girma a ajin yara
Tare ya saka su a aji daya
Manubiya muhsin da jidda
Duk a aji ‘daya
Hatta jidda a lokacin tayi girma a ajin,amma Sam yaran basu wani damu ba
Dan suma suna tsananin son karatu
Sannan sunada tsananin k’ok’ari da naci akan karatun
Dan cikin ikon Allah hazak’ar su ta sanya aka dinga yi musu double promotion wanda har ta kaisu ga taddo sa’o’insu

Da farko private suka fara
Amman yanayin rayuwa ya sanya dole Baba ya maida su ta gwamnati
Wanda
duk gidan su kad’ai ne
suke zuwa makarantar gwamnati

Jamb ne ya so bawa manubiya matsala
Amman waec d’inta da neco har mamaki ya dunga bawa mutane
Saboda yanda ta fito da flying colours.Rashin cin jamb d’in ne yasa ta shiga poly tayi diploma
Ta shiga BUK da D E ,yanzu haka Tana level 3 suna karantar English tare ita da Abbakar
Tun a poly suke tare ita da Abbakar
Bata da kawa mace
Saboda yanayin rayuwarta
Kullum Kayanta a kode ,
Gashi ko kudin handout wani lokacin sai dai ta ara tayi karatun a iya makarantar
Sannan in anzo tafiya cafeteria sai dai ta gudu
Dan inde Anje sai dai a siya mata tasan rayuwa bazata yiwu a haka ba shiyasa ta shafawa kanta lafiya,
Abubakar ne kawai Abokin ta
anan unguwar tasu yake bayan layin su
Maman shi k’awar Maman Baraka ce
Tare suka bude gidan abincin su
Tun shekaru baya da dad’ewa .

Jidda kuma wannan Shekarar ta zana waec ,taci itama kuma cikin Ikon Allah taci har jamb
yanzu saura mata post utme .

Muhsin kuma yana js2 tun last year ,yanayin rayuwa yasa ya kasa ci gaba da karatun.
…….
‘’Baba Ina wuni,’’
Muryar Abbakar ta katsewa Baba tunanin sa.
Ahankali sannan a d’an boye ya sake goge idanuwan sa
tukunna ya juya yana kallon su shi da Muhsin.
Da kulawa ya amsa shi yana tambayar sa ya Maman sa shi kuma yace Mishi ‘’tana lafiya’’
kafin
Cikin yin k’asa da Kai yace ‘’Baba dazu a aji ana ta bayani amma sai na lura sam hankalin Manubiya baya a ajin
daga baya ma sai na fahimci ashe ma kuka takeyi
naso in taimake ta dan nasan akan rashin lafiyar Inna ne amma sam sai tak’i yarda,
Dan Allah Baba ga kud’i na bawa muhsin a kai Innar asibiti dasu
Kar kace a’a , nima kamar uwa Inna take a waje na ’’
Ahankali ya d’aura da cewa
Allah ya bata lafiya ya kawo
mata sauk’i’’
Yana gama fad’in haka ya musu sallama ya juya ya wuce…






MANNUBIYA
05
Na
Humayrah Bulama

ELEGANT Online ✍️

Sai da Muhsin ya d’an tab’a Baba tukunna yayi firgigit yace ‘’Na’am.’’
Neman Abbakar ya fara yi amma sai yaga babu shi babu alamun sa
Ahankali yace wa Muhsin d’in ‘’kaje gidan su kace ma sa na gode
Sam banga wucewar sa ba ‘’.

‘’To’’
Muhsin yace daganan ya mik’a ma sa kud’in yace ‘’gashi.’’

Sai da kwallah ta zubo wa Baba kafin yasa hannu ya karb’a kafin ya mik’e ya wuce cikin gidan da sauri
Muhsin kuma ya wuce gidan su Abbakar.

Kusan karo sukayi shi da Manubiya wadda ta fito da gudu
Suna had’a ido da Baban nata ta fashe da kuka ta fara waiwaye tana nuna ma sa d’akin tana juyowa tana kuka wiwi tama kasa magana.
Da sauri suka d’unguma zuwa d’akin.
Abunda yayi tunani d’in ne kuwa
Dan haka ya durkusa ya fara k’ok’arin kinkimar Inna wadda ta sank’ame idanuwan ta suka k’ak’k’afe
dai dai nan ya musbah ya shigo …..

Allah ya taimake su Nafi’u ya taho da motar sa 206 dan haka aka saka ta a ciki suka wuce da Baba da Ya musbah da Nafi’u wanda ke driving da innar
rashin gurin zama da kuma jiran Muhsin ne ya sanya su Manuniya suka hak’ura ba don sun so ba ,Amman har waje bak’in k’ofa suka biyo su kowa tana kuka,sai da suka ga wucewar su tukunna suka fara k’ok’arin komawa ciki dakyar.
Anan bakin k’ofar suka had’u da Baba habu shi da Uncle wanda dawowar sa kenan daga parking motar sa a gidan makwafcin su inda yake ajjiyewa.
Gaisuwarsu kawai ya iya amsa wa daganan ya shige ciki ya barsu tsaye su da
Baba habu,shima kamar bazai tambaye su ba
Sai kuma ya ce musu ‘’lafiya kuwa?’’
Jidda ce ta iya bashi amsa
dan ita Manubiya haushin sa takeji, ba sa shiga harkarsu
sannan ba sa taimaka musu
amman ya tashi ya tsaya yana k’ok’arin k’ulla aure tsakanin Jidda da Ya yusuf,bai damu da yadda jiddan bata son Ya yusuf d’in ba
kawai shi dai farin cikin d’an sa yake dubawa….

A tunanin Jidda zai bi bayan su Baba tunda ta lura tunda aka fara maganarta da Ya Yusuf ya na d’an kula su
amma sai taji yace
‘’Allah ya Bata lafiya’’
Daganan shima ya ja k’afafun sa ya shige ciki.

Yana wuce wa dai dai nan Muhsin yana k’arasowa
dan haka suka wuce ciki.
Sai chan dare tukunna ya Nafi’u yazo yace su kwantar da hankalin su jikin innar da sauk’i.
Yanayi sa yasa tashi d’aya suka fahimci ya fad’a musu hakan ne kawai dan su d’an kwantar da hankalin su.
Daman basuyi girki ba
Tashin hankali yasa suka kasa ma jin yunwar,jugum ranar haka suka kwana ita da Jidda sam basu runtsa ba
Muhsin ma barcin d’an kad’an yayi,safiya tana yi zazzab’i mai zafi ya rufe Manubiya dan yau kwanan ta na uku kenan batayi bacci ba ……


Tun lokacin da Yasir ya fita daga d’akin da kausar take ciki
bata sake ganin sa ba

Hada hadar komawa ma Abokin sa ya d’aura akan komai shi kuma yayi wucewar sa.
Banda addua ba abunda takeyi a ranta akan Allah ubangiji yasa Yasir zuciya yayi
Sannan ya hak’ura da ita har abada,shaka ta kwana Tana wannan adduar tare da tunani barkatai a ranta
washegari itama suka had’a komai itada k’awayenta suka nufi airport ……
da safe around 8 flight d’insu yayi landing a gida Nigeria,
Suna fitowa suka tarar da
Sister d’inta ’Yasira’ ta na jiransu ….
Sai da suka fara ajjiye k’awayen nata da suka dawo tare tukunna suka d’auki hanyar gidan su dake a sultan road,shiru motar ta d’auka ba mai cewa komai kafin chan Yasira tayi murmushi tace
‘’tun jiya daya dawo
dama nasan fad’a kukayi,
yanzu kuma mood d’inki ya tabbbatar min da hakan,
Did u tell him?’’
Ta karashe maganar tata da tambaya tana me d’an waiwayowa ta kalle ta kafin ta maida hankalin ta akan tuk’in da takeyi.
Kamar kausar d’in bazata amsa ta ba
sai kuma tace
‘’Na ce ma sa bana son sa, yayan sa nake so???’’

Wata er siririyar dariya Yasirar tayi kafin tace
‘’Noo!ki dai san ta yadda zaku yi breaking up tunda wuri kuma cikin sauk’i domin in kika bari kukayi baram baram,to fa ki tabbatar auren ki da Ya Yashjub ba mai yiuwa bane ba
So find a way out soon,
rikitacciyar zuciyar ki data d’auko mana aiki mai zafi , ta nemo mana mafita,a samu a rabu cikin sauki.’’

Wata nannauyar ajiyar zuciya kausar ta sauk’e kafin tace
‘’Abun da nake ta so inyi kenan
shi kuma Yasir nacin bala’i ne da shi kamar maye haka yake,yak’i ya bani had’in kai, ban….’’
Ganin yadda Yasirar tayi
Shiruuu ta d’an b’ata fuska ne
yasanya Kausar d’in yin shiru kafin ta d’an yi gyaran murya
Ahankali tace
‘’Sorry.’’

Murmushi kawai Yasira tayi kafin tace
‘’Kausar,inda ace zanji haushin ki akan issue d’in Yasir, tou da tuni tun farko da kika gayamin yanda feelings d’inki sukayi bouncing daga kan Yasir zuwa kan Ya yashjub da naji haushinki
But
You are my best friend hakan ne ya sa nayi supporting d’inki,kasancewar Yasir twin brother d’ina ba zai sanya in zuba ido Inaji Ina gani , ki cuce sa ki cuci kanki ba domin nasan tunda har
Kika iya kallon ido na kika cemin bakya son Yasir tou tabbas bakya kaunar sa
Kuma in kukayi aure a haka akwai babbar matsala,
dan haka ,ko da ace baki samu Ya yashjub ba
bazan so ki auri Yasir ba ….’’

A hankali
Kausar d’in tace
‘’InshaaAllah Allah zan samu Ya Yash
da izinin Allah
I just need your support
Yasira.’’
Ta karashe maganar ahankali tana kallon Yasirar abun tausayi.

Murmushi Yasira tayi
Kafin tasa hannu ta kamo na Kausar d’in
tana Murmushin tace
‘’Zan taimake ki har sai inda k’arfi na ya k’are InshaaAllah,
tun yarin ta kin kasance k’awata y’ar uwata da take tsayamin tsayin daka akan komai
In na k’i inyi miki wannan taimakon kwaya d’aya danasan shine farin cikin ki ai na zama butulu.’’

Cike da Jin dadi
Kausar tace ‘’Thankyou’’
tana Murmushi.
Daganan suka shiga tattaunawa akan yadda za suyi da Yasir saboda sun fahimci sai sunyi da wayo da dabara tukunna zasu ci nasara
domin sai yanzu suka fahimci
ashe su sunyi underestimating soyayyar dayake yi wa kausar d’in….
Kamar yadda sukayi zato
A compound d’in dank’areren mansion d’in suka tarar da mommy tana jiran su,murmushi Yasira tayi kafin ta juya ta kalli kausar wadda ta had’e rai
tace
‘’Your guarding angel,
ai na san ta daina fushin dake,gashi har ta zo tarbarki,
Jiya da Daddy yace mata zai dawo yau,bakiga yadda hankalin ta yayi bala’in tashi ba gudun kar ya dawo bai tadda ki ba,
Tun jiyan take tambaya ta
Flight din naku dai 8:00am ne ko ?in tabbatar naje na dauk’o ki da wuri
Kar Ya Yash ma ya fahimci bakya kasar kuma kar Daddy yazo bakya nan.’’

Duk da yadda kausar ta shirya k’in yin murmushi sai da wata y’ar siririyar dariya ta subuce mata
A Chan k’asan ranta tana mamaki da yaba tsantsar k’aunar da momyn nata takeyi mata
But
bazata bari taga lagonta ba
In ba hakaba tasan yau sai ta sha fad’a ,
Dan haka ta sake had’e rai ta turb’une fuska kamar bata tab’a dariya ba
tukunna ta murza handle d’in ta fito.

Duk yadda mommy ta so sauk’e wa kausar ruwan bala’i suna hada ido sai taji fushin nata yana d’an sauk’a,tabbas ita kanta ba zata iya fad’in adadin k’aunar da take yi wa Kausar ba.Ganin yanayin fuskar Kausar d’in kuma sai ya sanya ta tad’an fara d’ar d’ar
amman dukda haka yau kam ba zata bari kausar ta ga lagon ta ba,Ita ce uwa
Ita yakamata subi bawai ita ta dunga binsu ba.
Tana cikin wannan tunanin kawai taga Kausar d’in tazo ta wuce ta ba tare data ko gaida ita ba.
A fusace mommyn ta juya ta shiga kwala mata kira,
d’aga mata hannu kawai Kausar d’in tayi tana wani yatsine fuska kamar irin kin isheni d’in nan daganan ta wuce ta bi takan had’ad’d’iyar Barandar dake kewaye da main door d’in
ta murza handle d’in ta tura ta shige abunta.
Ba mommy ba hatta Yasira sai da ranta yad’an baci
kamar zata bi Kausar d’in tayi mata magana
sai kuma ta tuna yadda suke ita da mommy ba’a shiga fad’an su yanzun sai su shirya su barta tana fushinta ita kad’ai.

A mugun fusace gudu gudu sauri sauri mommy tabi bayan Kausar,a bakin stairs ta hange ta tana shirin fara hawa
Dan haka ta tafi da gudu ta finciko ta ta dawo da ita gaban stairs din ta fara fada baki da kumfa
‘’Kiyi laifi , kuma ki dawo min da wannan attitude d’in?mai kike nufi kenan ?
Tou bari Kiji wallahi zan barki da Daddyn ku wannan karan
dan naga abun naku daga ke har Yasir d’in fitina yake k’ok’arin zamewa mutane,
In auren kuke so ku fad’a ayi muku kowa ya huta
dan Wallahi na gama rufa muku asiri.
Bazai yiu ace kina bin sa kuna yawo k’asa k’asa ba mu kuma muna gida a shantake,
Banda iskanci wanne irin birthday celebration ne da baza a yi miki a Nigeria ba
Sai ya d’auke ki kuntafi wata uwa duniya..’’

A hankali Yasira ta d’an matso ta tab’o ta
Kafin tace
‘’Mommy.’’
Cikin fada ,mommyn
Ta ture hannun Yasirar kafin taci gaba da cewa
‘’Rabu dani Yasira
Kausar ta kaini bango Wallahi,
A gaban ki na ce mata ban amince su tafi ko Ina ba ai
amma dayake ta raina ni shine ta wanke k’afa da bi sa,
to kuwa kamar yadda ta wanke kafa haka nima zan wanke hannaye na daga rufa musu asiri tund…’’

A karo na biyu Yasira ta sake katseta ta hanyar cewa
‘’Mommy!!!’’
Da d’an k’arfi

Juya wa mommyn tayi a fusace zata rufe Yasirar da fad’a amma sai
tagan ta duk a d’imauce tana kallon ta tana waiwayawa tana kallon k’ofar shigowa ..
….Giant,ne sosai mai fad’in k’ashi
Sanye yake da riga da wando ‘pyjamas ‘farare tass masu ratsin silver,skin colour din sa light brown ne
Kamar na half cast
mai tsananin kyau ,shek’i da daukar ido
Normal lowcut da tsadadden gyaran fuska yayi
Amman yanayin yanda sumar tashi yadanyi coiling dukda kankantar sumar da aka bari
ne
zai sanya ka fahimci,lallausar suma gare sa
Fuskarnan tasha gyaran fuska ..
Wanda
Hakan ya taimakawa ba’kak’irin d’in sumar ta sa sake haskaka kyakkyawar fuskar sa
Kasancewar ba sa da sank’o ko kad’an
ne ya taimaka wajen sake fitowa da k’awata matured handsome face d’in sa wadda k’awataccen saje da d’an siririn gashin baki,had’e da d’an mitsisin tudun gemun sa da ko hannun yara bazai iya kamawaba
suka yiwa fuskar ta sa k’awanya.

Dogayen idanuwa gareshi,manya kamar na maijin bacci wanda yayi dai dai da tsararriyar girar sa,
Hancin sa dogo ne sosai,har baka
Wanda yad’an bud’e Kad’an ta k’asan ya bada shape d’in M,
Sai d’an mitstsin light nude lips d’in sa…
…….
Ita kanta Kausar sai yanzu ta lura da YASHJUB,tsaye
a bakin k’ofar,
Wani irin sanyi takeji yana ratsa ta tun daga tsakiyar kanta har izuwa babban d’an yatsar kafarta.Duk da

Please Login or Register in order to submit comment