Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

amfani da ni wajen baiyyana abun da yake a ran ku game da su Ummi,Alh Bashir da farko yace yana so na yanzu kuma yace ya fasa Munirat yake so.
Ni har ga Allah ban ga wani abun tashin hankali anan ba,
iyaka kawai mu yi musu addu’ar Allah ya basu zaman lafiya shikenan magana ta k’are,dan Allah kar wanda na sake ji yayi amfani da bak’in jini na da bad luck d’ina wajen nuna real face d’in shi ku bar ni in ji da abun da yake damu na’’
Ta fad’i haka wani irin kuka yana sub’uce mata da mugun k’arfi.
A hankali Yashjub wanda ya k’araso yanzun ya sa hannu ya juyar da ita ya rungume ta yana jin wani tsananin b’acin rai da takaicin senator Bashir suna taso masa.
Cikin kuka tace
‘’Yash dan Allah kace su dena maganar nan su bar shi ya auri Munirat d’in su dena maganar bana so suna rubbing salt a wounds d’ina ne sanann dan
Allah kar wanda ya sake ce min inyi aure dan Allah dan Annabi’’
Wani kalar kuka abun tausayi take yi wanda yasa gaba d’aya jikin Daddy wanda ya harzuk’a ya fusata ya yi sanyi haka ma Mommy da Ummi duk sai jikin su yayi sanyi.

Munirat kuwa ji take kamar taje ta chakawa senator wuk’a
Yahanasu is the most nice calm and friendly person da zata ce ta tab’a had’uwa da a rayuwarta gashi jinin su ya had’u matuka …..

Ahankali Yashjub ya jata tana a rungume a jikin sa suka wuce d’akin ta.
Suna wucewa Ummi ta ja hannun Munirat suka wuce sama suma.

Gaba d’aya kuma kallo sai ya koma kan Yassir wanda tun dazu da suka shigo ya gagara janye manyan idanuwan sa daga kan Munirat.
Ganin duk sun tsura mishi ido ne yasa ya d’an sunkuyar da kai ya fara sosa k’eya kafin da kyar yace’’Daddy I’m sorry for..
Kafin ma ya rufe bakin sa tuni
Daddy ya zo ya wuce shi ya fice daga gidan gaba d’aya dan a wuya yake dama Ummi bata san a cike yake da itaba kwana biyun nan haka kurum yake jin takaicin ta
yanzu kuma ji abun da tayi,
ta wani bud’e baki tana cewa ai itama Munirat marainiya ce
sannan har tana da bakin cewa wani an juya mishi tunani akan ta,duk irin yadda yake k’ok’arin bata kulawa amma sam ita bata gani how dare she
tun da yake da Mommy bata tab’a yi masa irin haka a gaban yara ba amma ita ta iya bud’e baki yana fad’a tana fad’a,y’ar shi tana cikin wannan halin kalli yadda Mommy take tausaya mata amma ita tata y’ar kawai ta sani.
Yahanasu batayi deserving haka ba y’ar shi mai hankali nutsuwa da sanin ya kamata,cikin fushi a fili yace
‘’Allah ya tsinewa Alhaji Bashir’’

Daddy yana fita Mommy ta k’arasa inda Yassir yake tsaye tahau duddubashi kamar wani k’aramin Yaro idanuwan ta suna kaiwa kan wuyan sa da har yanzu yake nan jajir ta rikice ta hau tambayar sa abun da ya same shi.
‘’A hankali yace ‘’Mommy I’m fine,favorite son d’in ki da kika tura ne ya je ya jiwa Abokai na ciwo ya sumar da d’aya sannan nima ya shak’eni da kyar aka kwace ni daga hannun sa da yau sai dai ki ga gawa ta.’’Kamar zai kurma ihu ya d’aura da cewa’’da kika san yana da anger issue da sai ku taho tare ke da shi ta yadda ko haukar ta sa ta motsa zaki iya shiga tsakanin mu nasan in kina nan
maybe ya d’an nutsu’’

Cikin rashin jin dad’i Mommy tace
‘Subahanallah,wallahi Yassir ban san zai yi haka ba
I was so worried ne shiyasa
ga shi naga Daddynku yana neman mantawa da kai ma gaba d’aya tun da yayi aure
komai ya lalace bai damu dani ba ma kai kam ko zancen ka baya yi,wannan matar da ka gani auntyn ku ce ….’’


Cikin katse ta yace
‘’Yeah na fahimta daga shigowata da kuma scene d’in da nayi witnessing

Ahankali ya Kama lips d’in shi na k’asa ya d’an ciza kafin ya d’ago idanuwan sa ya sauk’e a kan k’annen na sa da sukayi cirko cirko

Ahankali Baabaa larai ta k’araso tace
‘’Ka ji maganar mahaifiyar ka kaji d’an albarka,duk abun da
Babba ya hango Yaro ko ya hau kan dala ba zai gani ba
kar ka sake yunk’urin barin gidan nan.Yanzu lokaci ne da ya kamata ace kun had’a kai da mahaifin ku kun shiga jikin shi sosai duk wanda yayi gangancin yin nesa dashi to kuwa kanshi yayi wa.’’
Tana gama fad’in haka ta kama hanya ta wuce d’akin Yahanasu

Ahankali su Yadira Yusra da Yasmeen suka matso kusa dasu sukace
‘’Welcome home Ya Yassir’’
Sannan Yasmeen tace ‘’we missed u’’ tana d’an murmushi.

Kallon su kawai yayi daga nan ya maida duban sa ga Kausar da ta d’an tsura masa ido tana
mamakin ramar data ga yayi.
Yana kallo ta yace
‘’Mommy bara in je in watsa ruwa as usual nobody cares about me na tafi kuma na dawo da kaina ba tare da an yi min abun da na buk’ata ba,a tunani na Inada loved one’s da zasu damu da damuwata,I guess i was wrong.’’

Ahankali ya d’auke duban sa daga gareta ya maida kan sa k’asa ya fesar da wani numfashi
Sannan yace
‘’Bara in je in d’an watsa ruwa.’’

Tun Kafin ya juya Yashjub wanda ya fito yanzu daga d’akin Yahanasu yace
‘’Yasir,wait!.’’


Lumshe idanuwan sa ya yi ya d’an bud’e tukunna yace
‘’Wanka zan je in yi’’ya fad’i hakan yana mai kallon cikin idon sa.

Batare da Yashjub d’in ya sake kallon sa ba ya juya ga Mommy ya ce
‘’A gyara masa d’aki a sama kusa da side d’in ki.’’

Gaba d’ayan su a tare suka ce
‘’Whattt!!!!’’

Cikin b’acin rai Yassir yace
‘’Look here,Man!
Enough is enough fa haba mana what more can you do?kaje ka ce in biyo ka na biyo ka bayan b’arnar da kayi min sannan yanzu kuma zaka saka ni a tsakiyar mata gaskiya baka isa b…..’’

Kallon da Yashjub yake masa ne yasa ya d’auke kai ya kalli mommy
Yace
‘‘Mommy kiyi min tsakani da shi fa inba hakaba wallahi zamu kwashi y’an kallo.’’

Ahankali Yashjub ya matsa daff da shi ya kamo kafad’un sa ya juyo da shi sannan yace
‘’Yassir kar ka ga muna a gida kuma a gaban su Mommy ka ce za ka yi min shirme,rai na already a b’ace yake kar ka sake provoking d’ina,ka wuce masu aiki za su gyara maka d’aki a chan sama kusa da side d’in Mommy yanda zata fi saka maka ido saboda ni fita nake yi kuma yanzu zan dinga kai dare sosai sannan ina so in yi tafiya so ba zan iya kula dakai ba,tun da ka nuna har yanzu baka yi hankali ba,dan haka dole zaka zauna a inda za’a saka maka ido a kuma kula da kai.
Anjima kuma zamu zauna
da ni da kai da Mommy da Daddy ayi magana akan abun da na gani a gidan da kake cewa na yi maka b’arna,for the last time ka wuce sama’’.

Iya k’uluwa Yassir ya k’ule, ya san tsaf Yashjub zai iya sake fad’in wata maganar da zata sanya Kausar ta d’an fahimci wani abun tunda gashi ya fara dan haka kawai ya yanke shawarar wucewa sama
amma tabbas zuwa yanzu yayi girman da zai gyara wa Yashjub zama,da sake dan gaskiya ba zai yiu a dinga juyashi da girman sa ba.

Ahankali Mommy wadda ta fara firgita da yanayin Yashjub ta kamo hannun Yassir tace
‘’Son!muje,mu je saman anjima baya ce zamu zauna ba sai mu zauna d’in for now mu je kaji ko’’.
Ta fad’i haka tana k’ok’arin janye Yassir d’in daga ruk’on da Yashjub ya yiwa kafad’un sa..
Ai kuwa dakyar sai da ta d’an tab’a Yashjub d’in tace mishi
‘’Cika shi zamu wuce’’
Tukunna Yashjub ya samu ya janye idanuwan sa da suka yi jajir daga kan Yassir ya cika sa da kyar,daga haka kuma ya juya ya fice kamar zai tashi sama.

Ahankali Kausar ta ja numfashi ta bi bayan sa da kallo har ya wuce tukunna ta lumshe idanuwan ya tana ji a ranta’tabbas bata da hutu Bata da sukuni bata da nutsuwa muddin bata samu Yashjub ba,yanzu ne wasan zai fara dan ko ta halin k’ak’a ne
wallahi sai ta mallake shi bata ga dalilin da zai sanya ta rasa shi.

Su Mommy suna wucewa sama ita ma ta bi bayan su haka ma su, Yadira.
Yasira kuma ta wuce d’akin Yahanasu,bata damu da cewar ‘8th fiance d’in ta yayi dumping nata ba dole ta kora mata warning,Wallahi.
..
Wani irin karkarwa jikin Yashjub yake yi tsabar takaici
It will be awkward yaje ya samu senator Bashir da fad’a ko da lallashi zai ga kamar yana neman kai da y’ar uwarsa ne.
Ya jima rabon da ya shiga b’acin rai irin wannan a rayuwar sa baya so ya dinga feeling anger irin haka amma yau senator Bashir da Yassir sun kai sa bango.
Da wannan tunanin ya k’arasa part d’in nasa yana zuwa ya fad’a bathroom ya sakarwa kan shi ruwa mai sanyi…
Sai da ya ji ya fara atishwa tukunna ya d’auro alwalla ya fito ya ya chanja kaya zuwa jallabiya ya na shiriin yanata faman tsaki
dan yana fitowa yaji ana idar da sallah a masallaci.
A nan d’akin na sa yayi sallar sa ya idar ya zauna zaman addu’a.

Yana zaune sai ga Kausar tayi knocking ta shigo da zumbulelen hijabin ta,ta zo ta zauna kusa da shi wai Mommy tace tun da course d’aya suka karanta ta zo ya k’ara duba mata project d’in ta gobe time zai cika
kar a sake dawo da ita wannan shekarar ma,sannan ya manta bai bata wayoyin nata ba.

A yadda ya ke jin kan sa tabbas inya ce zai kula Kausar tou zai iya ji mata rauni,wacce irin mahaukaciyar Yarinya ce wannan mai shegen tsaurin ido haka.
Mik’ewa kawai yayi ba tare daya kalle ta ba ya koma kan sofa ya nemi guri ya zauna.
Duk da tsoron da take ji hakan bai hana ta matsawa dai dai wajen k’afafun sa ta zauna ba,
sannan cikin wata kalar murya
mai tsananin had’ari tace
‘’Ya Yash dan Allah’’

Gaba d’aya tashi d’aya yaji tsigar jikin sa yayi wani iri
Kallon ta yayi da rinannaun idanun sa cikin b’acin rai yace’’Tashi ki fita,in kuma tsaurin ido zaki gwada Bismillah ki k’ara second goma a nan za ki ga ikon Allah’’ya riga ya san k’arya take yi ba Mommy ce ta turo ta ba.
Ahankali tace’’ka yi hak’uri’’daga haka ta mik’e ta fita tana jin zuciyar ta k’all dan ta san ko dai hijabin ko kuma muryar ta da salon ta tabbas akwai abun da ya ba ta ko da k’ank’anuwar nasara ne akan shi.
‘’Slowly but surely’’
Ta furta hakan tana murmushi a lokacin da ta data fito daga b’angaren nasu.
A ranta tace ‘’kwalliya ta biya kud’in sabulu next level kam zan girgizaka ai da na d’auka kai d’in dutse ne.’’

Tabbas in kausar bata fita a hanyar shi ba tou zai bar gidan nan,baya son tab’a lafiyar ta kwata kwata amma kullum sake pushing nashi bango take yi

Yarinya ba jan aji ba nutsuwa
ba sanin darajar kai kamar ba tarbiyyar hausawa ba.
Kalli yadda yake korarta kullum amma Sam ba ta damu ba shak’iyyiyar yarinya ji irin muryar da ta yi amfani da ita
A fili ya yi tsaki ya ce ‘’Allah wadaran naka ya lalace’’..

Ahankali tunanin Manubiya ya fad’o mishi jingina ya yi da jikin gadon ya lumshe idanuwan sa,
nan muryarta da idanun ta suka fara masa gizo,da kad’an da kad’an ya ke jin b’acin ran na sa yana sauk’a har ya samu ya d’an ji dama dama tukunna ya mik’e ya koma kan gadon ya kwanta ringigine yana mai kallon sama yana mamakin ta yadda tunanin ta yayi maganin anger d’in sa a cikin lokaci k’ank’ani haka..
Kad’an kad’an ya fara jin bacci dan haka ya jawo pillow ya d’aura a kan k’irjin sa ya d’an rungume a fili ya furta ‘’Alhamdulillah’’
saboda ya san in yayi baccin ya farka b’acin ran nasa zai ragu sosai da yardar Allah.
Bai dad’e da lumshe idanuwan nasa ba kuwa bacci yayi awwon gaba dashi….

Mafarki ya fara mai masifar dad’i da annashuwa’ga shi ga Manubiya a zaune a cikin wani lambu mai cike tabb da korayen ciyawa,yana sanye da da farar jallabiya yayin da ita kuma ke sanye cikin ba’kar Abaya da nik’abi,iyaka idanuwan ta kawai yake iya gani.

Suna zaune suna fuskantar juna suna hira amma sam ba ya iya jin me suke cewa,sai da ya d’an nutsu tukunna yaji yana cewa
‘’I just want to see your face get to know u,shikenan na san inshaaAllah zan samu nutsuwa ,pls ki fad’a min komai game da ke da rayuwar ki sannan ki nuna min fuskar ki ina so in san ki’’.

Sai da ya sake nutsuwa tukunna ya ji ta ce’’Ka kwantar da hankalin ka jibi inshaaAllah zaka ganni’’

Cikin katse ta yace
‘’Manubiya baki san ya nakeji a raina game da ke ba,ki nuna min fuskar ki yanzu dan Allah,dazu rai na a b’ace yake amma dana fara tunanin ki naji fushin ya fara raguwa na san ina ganin fuskar ki b’acin ran zai b’ace gaba d’aya’’.
Ya k’arashe maganar tasa yana k’ok’arin sa hannu da niyyar janye nik’abin nata.

Ahankali tace
‘’Nace maka fa jibi zaka ganni..‘’
sai kuma yaga ta d’an yi shiru
kamar mai tunani ko sauraron wani abun kafin ta d’ago ta tsare shi da kyawawan idanuwanta tace
‘’Answer your phone’’.
Da d’an mamaki ya ke kallon ta sai kuma ya yi murmushi yana shirin yi mata magana,ya farka daga baccin.
Wani wawan tsaki yaja dan ya manta rabon sa da yayi bacci da mafarki mai d’an karan dad’i irin wannan,da sauri ya lumshe idanuwan sa ya shiga
addu’ar Allah yasa ya samu ya koma baccin ya cigaba da mafarkin
Ya ji
wayar sa ta fara k’ara…
Shiruu kawai yayi yana sauraron ringin tone d’in harta katse.
He just wish Ina ma ace itace
although mafarkin da yadda tace ya amsa wayar shi kuma ya farka a ka fara kiran sa is a little bit wired
But
Shi fa a halin yanzu a yadda yake ji ko da ace aljana ce to zai iya zama friend d’in ta muddin za ta din ga ba sa wannan nutsuwa da kwanciyar hankalin da yake ji a ko da
da yaushe in yana tunanin ta.

Yana wannan lissafin
Yaji wani kiran ya sake shigowa
Gudun kar ta sake tsinkewa ne yasan ya sa ya d’an juya ya d’auki wayar datake k’ara a cikin wayoyin daya zube a gefen gadon tun farkon shigowar sa d’akin,business phone d’in sa ne shiyasa bai yi
mamakin ganin bak’uwar lamba ba.
Ahankali ya amsa ya kara a kunnen sa ya koma ya gyara kwanciyar sa ba tare da ya ce komai ba

Tashi d’aya gaban sa yayi wani irin mahaukacin bugawa sakamokon jin muryar ta da yayi tana cewa
‘’Ke ya isa haka,ba ki ga dare yayi ba,mutum Babba da matar sa kin dame sa da kira haka ki bari gobe ma sake gwadaw……’’
Tsit kuma sai yaji tayi shiruu..
Ahankali ya d’an runtse idon sa
yana jin k’irjin sa yana bugawa
a ran sa yace’’is she really the one?..ta ya aka yi ta samu number sa?,noo it can’t be tabbas yanzu ma gizo take yi masa har a waya ga kuma mafarkin da yayi
Innalillahi wa inna ilaihirrajiun
Ya Allah na yi gamo da aljana amma wallahi bana son rabuwa da ita,Ya Allah ka sa ba muguwa wadda zata cutar da ni bace ba.’’..

Yana wannan addu’ar yaji ance
‘’Adda Manubiya an d’auka fa ki yi magana mana.’’…

Ahankali ya lumshe idanuwan sa ya rintse pillow d’in daya d’aura akan k’irjin sa yana mai sake tabbatar wa da kanshi
tabbas ita d’in ce …….



MANNUBIYA
23

Na
Humayrah Bulama

Elegant Online Writers.

Da kyar Manubiya ta samu ta tattaro gaba d’aya courage d’in ta tace
‘’Assalama alaikom sir
Good evening,Sir Najeeb ya ce zaka bani aikin da zan dinga reporting maka duk sati he gave me your card and ask me to call you for more information…’’

Kitt!!haka suka ji an katse kiran.
Da sauri ta d’ago tana kallon su Jidda da suka zuba mata ido sukayi mata k’urr,
Ahankali Muhsin ya sauk’e ajiyar zuciya ya koma ya zauna daga tsugunnon da yayi dan lek’a wayar tukunna yace
‘’Adda kema kin kwafsa,ya zaki yi masa mix d’in Hausa da turanci..’’

Da sauri Jidda tace
‘’Eh!nima ina tunanin Hausar da kika yi ce ta b’ata masa rai.’’
Ahankali Manubiya tace
‘’Allah yasa ba matar shi ce ta d’auka ba’’
Daga haka ta koma ta jingina da jikin bango..

A b’angaren Yashjub kuwa tun da Manubiya ta fara magana
ya ji numfashin sa yana shirin d’auke wa,the fact that ‘tana yi masa magana referring to him alone’ne ya sanya nishad’i da annashuwa suka mamaye sa sannan ga zuciyar sa daya ji tana shirin tarwatsewa tsabar uban gudun da take yi.
Ganin yarinya k’arama tana shirin sumar da shi ta waya ne yasa ya yanke shawarar ya kashe wayar ya nutsu yayi calming down tukunna ya fahimci wanne irin aiki take magana akai dan kwata kwata
kwakwalwar sa tak’i ta d’auki charji,kuma ya san in yace zai yi mata magana a haka to tabbas za’a samu matsala.
A hankali ya runtse idanuwan sa ya na maida numfashi kamar wani wanda ya yi y’ar tsere.Ya fi mintina goma a haka
sam ya kasa tab’uka komai yana nan kwance a hakan yaji ana knocking k’ofar d’akin nasa.Sai da aka yi sau wajen uku tukunna yace’’come in’’.
Ya riga ya san wacece shiyasa tana shigowa yace’’Mommy kar ki damu fa,i’m fine’’.

Murmushi tayi kafin ta k’arasa
bakin gadon ta nemi waje ta zauna sannan tace’’in kai kana ganin kayi girman da zaka b’oyemin damuwar ka ni har yanzu ganin ka nake yi kamar yau na haifeka,yanzu tashi in zauna sai ka kwanta in yi maka massage a goshin ka na san ciwon kan zai ragu ko?’’
Bud’e idanun sa yayi ya kalle ta na y’an sakanni kafin ya mik’e ya zauna a kan gadon sanann ya kalle ta yace
‘’Mommy da gaske nake miki fa
I’m okay now.’’
Sai da ta d’an k’ura masa idanu na y’an sakanni Kafin tace
‘’How?ko aljannar dana ji kana maganar ta kwanaki a d’aki na ce ta kwantar maka da hankali?’’
Wani sassanyan murmushi da Yashjub d’in yayi sai da ya sanya Mommy a al’ajabi.
Ba ta san lokacin da tace
‘’Akwai ta kenan da gaske,a ina take?talk to me ka fad’amin kar ka b’oye min komai’’

This time around dariya Yashjub yayi kafin ya juyo ya kalle ta sosai sannan yace
‘’Relax!Mommy in lokacin sanin ta yayi zaki santa amma ba yanzu ba,kuma na san tunani kike yi akan ko budurwa ta ce ko kuma ina son ta wanda sam abun ba haka yake ba,she’s just my friend ko kuma ince zata zama k’awata,soon’’
Ya fad’i haka yana koma wa ya kwanta kamar yadda ta shigo ta same sa.
Ganin da yayi kawai tayi shiruu ta fad’a duniyar tunani ne yasa shi cewa’’okay!bye bara in d’an huta kafin in shigo anjima’’.
Ahankali tace’’Byee’’ ba tare da ta motsa ba.
Kamar ba zai yi magana ba
sai kuma yace
‘’Your mood,mai ya faru?’’
Ya yi mata tambayar yana kallon ta sannan ya sake mik’ewa ya zauna.
D’an murmushi tayi a hankali daganan tace
‘’Bye sai mun had’u anjima’’

Tana gama fad’in haka ta mik’e zata fita da sauri yace
‘’Yauwa’’sai kuma ya mik’e ya k’arasa drawer daya ajjiye wayoyi da atms d’in Kausar ya d’auko envelope d’in da ya saka komai nata a ciki ya kai wa Mommyn ya ce ‘’ga shi’’.
Still bai ga change a mood d’in ta ba,dan kawai karb’a ta yi ba tare da ta kalle sa ba ta juya ta fita.
Ya dad’e yana nazarin Mommy
daga k’arshe ya yanke wa mood d’in nata hukuncin’maybe ta d’an ji zafin yadda yak’i tsayawa tayi masa massage saboda wata friend wadda ya sani jiya jiya already ta kwantar masa da hankali.’
Daga haka ya janyo wayar sa ya turawa Manubiya message
kafin ya danna kiran Najeeb …
Yana d’auka kuwa ya kwashe da dariya.
Shiruu Yashjub yayi yana sauraron shi sai da ya yi mai isar sa tukunna ya ce’’ya aka yi ne?’’ya yi masa tambayar still yana dariya k’asa k’asa.
‘’Iyakar plan d’in naka da idear taka kenan?wanne aiki to zan bata?’’Yashjub yayi masa tambayar kai a d’aure.

Cikin dariya Najeeb yace
‘’Iyaka taimkon da zan iya yi maka kenan wallahi,tun da ka ga ka zomin da sharud’a,my hands are tied ta ko ina shiyasa na barka kayi figuring out komai da kan ka,cikin sauk’i.’’

Ajiyar zuciya Yash ya sauk’e kafin yace
‘’To ai ni aikin da zan bayar a dinga zuwa duk sati sau d’aya ne ban san shi ba’’

Yadda najeeb ya yi wa Abbakar tak’aitaccen bayani akan aikin haka yayi wa Yashjub daganan ya d’aura da cewa’’chatting nake yi da k’anwar ka ka kira ni kar ka ja min in je garin gyara maka ni kuma madam ta yi fushi,sai anjima.’’

Yashjub yana shirin yin magana yaji Najeeb ya katse kiran,shiruu ya yi yana tunani kafin kuma ya fara wani kalar murmushin da ya dad’e bai yi ba….

Su Manubiya har sun cire rai suna shirin maidawa Siyama wayar ta suka ji message ya shigo,kamar ba zasu duba ba dan basu sani ba ko na siyaman ne sai kuma suka ga kamar number da suka kira ce dan haka suka duba.
Suna bud’ewa suka ga an turo Time da Adress d’in inda zata same shi jibi Monday da safe inshaaAllah…
A take suka turawa Ya Musbah message d’in ta wayar Siyaman duk da sun san gobe zasu had’u amma duk cikin su Baba ne kawai mai waya so gara su ajjiye message d’in a wayar sa gobe su shirya komai jibi su tafi tun da yace 8 na safe za ta je.Suna gama tura masa Jidda ta maidawa Siyama wayar ta ta dawo ta zauna ita da Muhsin suka shiga surutu da murnar aikin da Manubiya ta samu,tun Manubiyan bata kula su har ta d’an fara saka musu baki a hirar ta su,wadda duk suna yi ne a kan albashin Manubiyan: za su siya kayan abinci da na farko in an sake biyan ta kuma sai su siyawa inna da Baba kayan sakawa,sannan suka ce za su biya wa Muhsin ya yi jarabawa ya wuce ss1 ya ci gaba da karatun sa shima.
Kusan duk a lissafin su ba su sako kan su ba kawai komai su iyayen su sai Muhsin wanda yake ta murna ya ji ance zai ci gaba da karatu..wannan dalilin ne ya sanya hawaye suka b’alle wa inna wadda ta farka daga bacci ba da dad’ewa ba,da kyar ta samu ta lallashi kanta tayi shiru.A haka Baba ya shigo ya same su hannun sa rik’e da bak’ar leda,sai da suka yi masa sannu da zuwa tukunna Manubiya ta mik’e ta d’auko faranti tana zuwa ya mik’a mata ledar ta karb’a ta yi godiya tukunna ta bud’e,
Kunun tsamiya ne a ciki d’an sachet guda d’aya sai gurasa guda hud’u mai gishira an d’an yayyafa mata mai.
Jidda ce ta karb’a kunun tsamiyar taje ta ta damo wa inna ta dawo Manubiya da Muhsin kuma suka d’auki
gurasar d’aya d’aya sukaci bayan sunyi sunyi da Baba akan shima ya ci amma yak’i, ya ce musu ya ci tasa a waje kafin ya shigo,ba dan sun yarda ba sai dan basuson yin ja in ja da shi ne yasa suka hak’ura suka d’auki tashi guda d’ayar suka sake raba ta gida uku suka barwa Jidda da take bawa inna kunu nata su kuma suka ci nasu suka sha ruwa daganan Manubiya ta d’auki bargon Baba da Muhsin ta yi musu shimfid’a ta ajjiye musu abun rufuwa,dai dai nan ita kuma Jidda ta gama bawa Inna kunu,dan haka ta zauna zaman cin tata gurasar Manubiya kuma ta je ta d’an d’umamo ruwa ta dawo ta kaiwa Baba

Please Login or Register in order to submit comment