Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

rabi toilet rabin kuma ta zo ta shiga gogewa Inna jiki.Cikin sanyin jiki Baba ya mik’e yaje ya gasa k’afar sa data addabe sa kwana biyun nan daganan yayi uzuri,brush da alwalla ya fito yazo ya yi addua ya kwanta yana tunanin mai gobe kuma zata k’unsa,babbar damuwar sa shine ‘abinci’ dan wannan ma a bashi aka basa da kyar,dan haka ya san ba lalle wanda ya
basa bashin ya kuma basa gobe ba.
Yana jin su suka shiga one by one kowa yayi brush yayi alwallah ya fito daga nan Manubiya ta kunna musu mosquito coils Jidda ta yi musu shimfida suka nema waje suka kwanta..
Har bacci ya kwashe su gaba d’aya amma shi ya gagara kawai dai ya lumshe idanuwan sa ne kamar mai bacci ….

Ummi bata cewa munirat komai ba har suka k’arasa d’akin ummin sai da suka shiga ta rufe k’ofar d’akin nata tukunna ta juyo Munirat tana shirin yin magana Ummin ta kwashe ta da wani gigitaccen mari,cikin fushi tace’’na baki minti biyar kiyi min cikekken bayani,Munirat kina haukane ?
Yahansu fa?ba wai ina zargin ki da yi mata snatching ba amman kamar yadda Daddy ya fad’a da mutumin ya fara miki zancen banza da sai ki yi fitar ki ki bar shi, a iya d’azun yana ganin ki kawai yace miki zai aureki ko kuwa ya abun yake?’’
Cikin kuka Munirat tace
‘’Ummi alhaji Bashir ne fa kuma tare mun hanya yayi,amma wallahi Ina ganin sa na so in juya amma sai ya tare min hanya…’’
Shiruuu
Ummin tayi ta kasa cewa komai kafin chan ta cewa Munirat d’in ‘’je ki yi alwallah ki yi sallah ki kwanta,’’
Daga haka ta juya ta fice daga d’akin.
Ko da Ummin ta fita a parlourn ta ta zauna tayi tagumi,ta jima sosai a haka kafin daga baya ta mik’e ta nufi side d’in Daddy..

A d’akin Munirat taci y’an biscuits da apple data tarar a fridge ta sha ruwa bayan ta yi sallah ta kwanta tun tana tsammanin ganin Ummi har bacci ya kwashe ta tana sheshek’a tana ajiyar zuciya.

Kamar yadda Yashjub ya fad’a,sai da ya huta ya tabbatar Daddy ma ya gama duk wasu aiyyuka da uzururrukan sa tukunna ya nufi cikin gidan,bai tarar da kowa ba dan gidan yayi shiruu dare yayi kowa yana d’akin sa, yana tafe ya turawa Mommy massage daganan ya nufi sama side d’in Daddy yana k’arasa wa k’ofar parlourn ya d’an yi knocking tukunna ya shiga da sallama.Yana shiga ya hango sa ya rafka tagumi ya zurfafa a tunani,sai da ya je kusa da shi sosai ya zauna a kan 1 seater d’in da take facing 3 seater da yake zaune akai yace
‘’Daddy’’
Tukunna yayi firgigit ya d’ago yana kallon sa.




MANNUBIYA
24

Na
Humayrah Bulama

Mikiya Writers Association.

Numfashi Daddy ya fesar kafin ya gyara zama ya bawa Yashjub dukkannin attention d’insa tukunna yace’’kana da buk’atar wani abu ne?’’
Ganin Yashjub d’in ya yi shiru ya gagara cewa komai ne ya sanya Daddy d’in sake cewa’’ina jin ka akwai matsala ne?’’

Ahankali Yashjub ya sunkuyar da kanshi yana tunani,sai da Daddyn ya sake basa dukkan nin hankalin sa ya ce’’Talk,mana.’’tukunna Yash d’in ya sauk’e ajiyar zuciya cikin nutsuwa da sanin kan zance ya fara magana
‘’DaddyAllah ya huci zuciyar ka akan abun da zan fad’a maka yanzu,inyayi maka zafi ka yafe min,sai da ya d’an yi shiru tukunna ya ce
‘’Daddy abun da akayiwa Ummi a gidan nan yau bai kamata ba,sannan su Yasira a gaban ka suka din ga yi mata rashin kunya amma aka kasa tsawatar musu bayan ba ma laifin yarinyar nata bane ba tun da ba ita tace tana son mutumin ba,kar so da tausayin Yahanasu ya rufe mana ido mu d’auki alhaki Ummi da y’ar ta bayan kai ne kayi alk’awarin zaka zame mata uba.
Sannan magana ta biyu su Ya’isha ya kamata a taka musu burki tun yanzu kar su saka yarinyar nan a gaba and also tun daga kan Yasir har izuwa kan Yadira gaskiya Daddy ya kamata ayi wani abun saboda kwata kwata basu san ya kamata ba ko ni da na tashi a Uk ba zan yi abubuwan da suke yi ba na san muna iyakar k’ok’arin mu wajen basu tarbiyya amma abun nasu kullum k’ara gaba yake yi
Kalli abun da suka yiwa Munirat da Ummi yau sannan
Yassir yau da na je gidan da yake abun da na gani ba zan ma iya sake fad’a ba k’azantar ta yi yawa da shi da abokan sa guest house guda suka ware suke zaune da y’an mata abun ba kyan gani,ya kamata a tsawatar musu tun wuri Daddy,
B4 it’s too late.

Shiruu Daddy yayi yana nazari’
Tabbas shima sai da ya shigo ya nutsu yanzu tukunna ya fara ganin rashin kyautarwar sa,kawai dai itama Ummin bai kamata k’iri k’iri ta bi bayan y’ar ta ba ya san wannan dalilin ne ya sake fusa ta shi.Sannan bai san daliliba
amma tana yawan bashi haushi haka kurum wani lokaci ki magana tayi sai ya fusata
Saddik’a ba ta da laifi tana da
biyayya ga tsafta shiyasa yake k’ok’arin danne zuciyar sa su zauna lafiya sannan yake danne duk wani takaicin ta da yake ji ya kyautata mata amma duk da haka bata appreciating sam kalli yadda yau ta bad’a masa k’asa a ido a gaban jama’a yana fad’a tana fad’a.’

‘’Assalama alaikom’’
Sallamar Mommy ta katsewa Daddy tunani.
Cikin nutsuwa ta k’araso Yassir yana biye mata a baya,a kan one seater Yassir ya nemi guri ya zauna Mommy kuma ta zauna akan 2 seater,
daganan parlourn yayi shiru.

Da kyar sannan ciki ciki Yassir yace‘’Daddy ina wuni’’.
Ko kallon shi Daddy bai yi ba instead sai ya juya ya kalli Mommy sannan yace’’Kin san d’an ki a guest house yaje ya zauna yana shed’ana?ya ce ki yi masa aure kin k’i bada had’in kai kin tarwatsa abun
to gashi yanzu ya nuna miki kalar b’arnar da zai yi in aka k’i ayi masa auren.Mai yasa ba kya so ya auri Kausar?’’
Daddy ya k’arashe maganar tasa ta tambaya,kan sa tsaye yana mai sake fuskantar ta.
Gaba d’aya diriricewa Mommy tayi tana mai jin takaicin
yadda Daddy yake k’ok’arin
had’a mata bomb tsakanin ta da Yassir har ma da Yashjub.

Cikin katse mata tunani Daddy yace
‘’Anyways shikenan ku kuka sani,na riga na cire hannu na a lamarin kuma wallahi I’m very glad about the fact that
Yassir bai auri Kausar ba
duk da cewa shima naga alamun ya zana d’an duniya
amma duk lalacewar giwa tafi kare…..yanzu dai abu biyu zuwa uku nake so in miki magana kuma in ja miki kunne akai ki saurara ki jini da kyau
Ki san yadda za kiyi ki gyara d’an ki ‘Yassir’ in ba haka ba zan kwace company d’in da na bud’e masa saboda naga sai yayi morethan one month ma bai je ba dan haka a gani na ba bu amfanin a bar masa,akwai yaran Abokai na architecture’s da yawa zan iya bawa d’aya daga cikin su
C’e’o kawai zan chanja cikin k’ank’anin lokaci za a chanja suna da komai.
Sannan in bai shiryu ba ba k’aramin aiki bane dan na kore sa a cikin gida na gaba d’aya
Saboda
ba zai yiu ya dinga yin yadda yaga dama anyhow ba,ban ga dalilin da zai sa yaje yayi iskancin sa ya dawo min sannan in bashi shelter ba,
Ya nuna zai iya rayuwa shi kad’ai tun da gashi ya fi month ba ya tare damu dan haka in na sake jin wani shirme daga garesa wallahi sai na baku mamaki.Amma for now a matsayi na na uban sa zan saka ayi masa sauk’a a raba sadak’a a saka shi a addu’a
Allah ya shirye shi..daganan kuma in bai shiryu ba ya nuna min ya fi k’arfi na to sai dai mu raba gari ni da shi..’’
Daddy ya k’arashe maganar cikin tsananin fad’a da takaici.

Yassir ji yake yi kamar ya tashi ya rufe Yashjub da duka,tabbas ya san shi ne yazo ya had’a masa munafurci a wajen Daddy.
Saboda Allah d’an k’aramin company d’in nasa da aka bud’e masa shine yake so a kwace ko yaya?it’s obvious shi ne favorite d’in Daddy ya san
Daddy ya fi son shi,shi kuma ya san Daddy ya tsane sa.
Already Yashjub is above him ta kud’i da fame da komai tou dan me yasa zai saka masa ido ya sakawa d’an business d’in sa ido sannan ya sake hura wutar k’iyayyar sa a zuciyar Daddy,anya kuwa jinin su d’aya da Yashjub?,ya yiwa kan sa tambayar yana jin yadda zuciyar sa take sake tafarfasa.

Ahankali Mommy tace
‘’InshaaaAllah Daddy za a gyara kuma zamu kiyaye,ba za mu baka kunya ba.’’

Dai dai nan Ummi ta shigo, har zata koma dan tana ganin su ta fahimci meeting suke yi amma sai Daddy yace mata ta so ta zauna ba komai..
Cikin nutsuwa ta gaida Daddy daganan ta juya ta gaida Mommy suka amsa ba yabo ba fallasa Yashjub kuma ya gaida ita,sai da Daddy ya zabgawa Yassir harara tukunnaya ce ‘’Ina wuni’’
Ba tare daya kalle ta ba,da
kulawa ta amsa kafin ta kalli Daddy cikin sunkuyar da kai tace’’
Kayi hak’uri Daddy akan abun da ya faru dazu,
In shaaAllah hakan ba zai sake faruwa ba’’

Ahankali Daddy wanda duk ya ji jikin shi yayi sanyi yace ‘’ba komai’’.

Ajiyar zuciya ta sauk’e kafin
ta fara magana
‘’Alhaji Bashir,ya san Munirat 3 years back,sun had’u a instagram ne tun kafin ya ganta in person suke tare,
tun da yazo suka had’u kuwa sai ya fara maganar aure.
Cikin watanni biyu komai ya k’ullu,aka saka ranar auren su wata uku.A ranar hennah party d’in ta ne muka ji labarin ashe matar sa psyco ce ita ta kashe y’ar su ta farko ma amma da
yake mahaifin ta influential person ne sai aka rufe abun aka ce depression ne yake damun ta shi yasa take hauka,daga baya ma aka ce ba ita ta kashe yarinyar ba.
A ranar d’aurin auren Munirat da Bashir ne matar ta sa ta d’auki karamar y’ar ta su data rage ta tafi da ita Cairo ta turo masa video ta na treatning d’insa akan’ko dai ya fasa auren Munirat,ko kuma ta kashe wannan yarinya data gudu da ita sanann itama ta kashe kanta’.Sai a lokacin ne mu kaji labarin ashe haukar tata tana tashi ne in Bashir d’in ya kula wata ko kuma yayi yunk’urin k’ara aure,shiyasa shi kuma yake b’oye mata.
Ko ba komai a wannan lokacin mun fahimci yadda Bashir yake k’aunar matar sa duk da a lokacin yace saboda y’ar sa yayi abun da yayi amman yadda matar ta hanasa dawowa bayan tafiyar sa despite yadda ya bar Munirat ya ci ace an fahimci yadda yake gudun b’acin ranta.
Bai tashi fad’ama wakilin sa ya fasa auren ba sai da ya isa airport ya tabbatar ya samu jirgi tukunna ya iya nutsuwa ya turawa wakilin sa da na Munirat message

Watan Munira d’aya tana rashin lafiya saboda yadda k’awayenta makwafta da kuma y’an uwa suka dinga gulmace gulmace ga ko ba komai itama nasan tana son
Bashir a wannan lokacin.
Tun wannan lokacin bai tashi dawowa ba sai after five months bayan ya gama theraphy d’in matar sa ya gama lallab’ata ta zauna achan Cairo d’in,sai gashi ya
dawo da niyyar auren Munirat
ba tare da sanin matar ta sa ba ni kuma nace a’a Munirat ma tace a’a ta hak’ura.
Da farko lallab’a mu ya fara yi
da yaga dai mun dage,sai ya
fito mana da asalin fuskar sa,
Duk da mun maidawa gidan su
duk wasu kayan lefe da na Al’ada sannan an janye bashi itan da akayi amma sai ya dage akan cewa shi fa an riga an bashi so anytime ko mu na so ko bama so zai je a d’aura musu aure.
A lokacin Munirat har tayi wani saurayin ana shirin saka rana
amma sai da Bashir ya shiga ya fita ya raba ta da wannan Yaron.
Ganin yana neman takurawa rayuwar mu kuma dama na gama sabon gini na ne
yasanya na d’auke Munirat muka tafi chan garin mu
mu kayi wattanni bakwai kuma da muka tashi dawowa bamu tare a gidan daya sanmu ba.
Yayar ta ma cewa tayi sai da mijinta yayi da gaske tukunna ya d’aga musu k’afa dan da ya neme mu ya rasa kanta ya koma wai sai ta fito masa da fiancé…….’’

Sai da Ummi ta sauk’e ajiyar zuciya tukunna tace ‘’
Munirat bata da niyyar cutar da Yahanasu dan Allah kar abun da aka d’an samu misunderstanding sannan ya riga ya wuce ya zama silar samun matsalar mu’’.

Ahankali Daddy yace
‘‘InshaaAllah Ummi,kema kuma ki yi hak’uri ke da Munirat d’in bamu san da haka ba kuma shima Bashir ko da nayi masa magana bai yi min wannan bayanin ba,zan samu
samu lokaci in saka su Yasmeen d’in su baku hak’uri a fahimci juna komai ya wuce inshaaAllah’’.

Ahankali Mommy ma tace
‘’Allah yasa mu dace’’.
A tare Daddy da Yashjub da Ummi suka ce’’Ameen’’
Daganan Ummi ta mik’e ta ce
musu ‘’sai da safen su’’.
Tana fita,Daddy ma ya mik’e ya ce’’we are done here,Allah ya bamu alheri.’’

Sai da safe su Yashjub suka yi musu suka fice,yayin da Mommy ta mik’e ta bi bayan Daddy amma tana shiga yauma kamar kullum ya sallame ta,haka nan ta fito hankalin ta a tashe.
Tabbas ita kanta ta san tana da kissa amma bata jin wannan karan she can keep on hiding her pain, abubuwan sun yi mata yawa
abun da ta rena yana k’ok’arin fin k’arfin ta.Ga shi yanzu zargin su a kan Yashjub ya tabbata duk da ya ce mata friend d’in shi ce amma ita bata wani yarda ba besides a ina ake wani k’awance tsakanin mace da namiji,tun da ya gaya mata d’azu har yanzu hankalin ta bai kwanta na second d’aya ba,kar dai ace wannan ita ce yarinyar da zata zama obstacle d’in nasu…….

Bayan kwana d’aya,Monday!.

Da asubah Manubiya ta tashi,tana idar da sallah ta yi karatun Qur’ani ta idar daga nan ta d’auki handout d’in ta ta hau karatu bayan ta je ta d’aura ruwa.Sai da garin ya d’an yi haske tukunna ta mik’e ta je ta d’an d’ebi ruwan ta watsa ta barwa su Jidda nasu.
Tun da Baba ya fita sallah bai dawo ba har ta gama shirin ta
ta san kuma dalilin daya hana sa dawowar,tunani ta shiga yi tana lissafin ‘ko dai su hak’ura da zuwa office d’in mutumin nan ko kuma suje a k’afa in za su iya in yaso d’an kud’in motar da suka tana da sai a siyawa inna kunun ta su Muhsin ma su ci abinci dan ta san shima Ya Musbah ba lallai a samu wani abun daga wajen sa ba.
K’arfe 7 dai dai ta fita gidan Ammi tana addu’ar Allah yasa yau d’aya dai ta samu ko da
left over d’in jiya ne.
Kamar yadda tayi expecting
sai da suka fafata da Ammi dan jiya basu had’uba wai ta tafi sunan k’anwar ta tun sassafe so bata samu ta tambaye ta akan fitar da za ta yi yau ba,sai da Mama ta saka baki yauma tukunna ta barta akan nan da k’arfe goma za ta zo.
Abinci n da tayi tunanin samu kuwa san bata samo ba,haka nan ta dawo hankalin ta a mugun tashe dan bata san mai za su ci ba.
Da ikon Allah tana shigowa
ta tarar Ya Musbah ya zo musu da koko Jidda har tana bawa inna nata,ba k’aramin dad’i ta ji ba kuwa dan haka ta yiwa Allah godiya,itama ta karb’a ta sha nata daga nan Baba ya yi musu addu’a su Jidda suka yi musu a dawo lafiya suka fito ita da Ya Musbah kowa a d’akin yana musu fatan alkhairi.
Lokacin karfe 7:36.

A bakin k’ofa suka tarar da ya Yusuf yana tsaye yana daddana waya sanye cikin suite,da murmushi Ya Musbah ya k’arasa ya mik’a masa hannu yana mai cewa
‘’Yusuf ina ta so in lek’a in maka murna,naji Baba yana cewa ya ji Kaka mallan a masallaci yana gayawa Abokin sa ka samu aiki a banki ko?,Allah ya sanya alkhairi’’
Ya k’arasa maganar ta sa da tsananin murmushi kwance akan kyakkyawar fuskar sa.

Ko kallon sa Ya Yusuf bai yi ba ballantana yayi tunanin zai bashi hannu su gaisa,a hankali Ya Musbah ya janye hannun sa kafin cikin rashin kuzari ya sake cewa’’Allah ya sanya alkhairi.’’
Yanzun ma bai ko kalle sa ba sai wayar sa daya ci gaba da dannawa.
Ahankali Ya Musbah ya juya ya kalli Manubiya data k’ule ta zo iya wuya yace mata ‘’Manu,mu je’’daga nan ya sa kai ya fice daga gidan jikin sa a mugun sanyaye.
Manubiya har zata fita itama
sai kuma ta juya ta kalle Yusuf d’in dai dai shima ya d’ago yana kallon ta,a hankali k’asa k’asa tace’’Jidda ce dai,ba za mu bayar ba!dan Allah in kaga dama ka zama sarkin gaba.’’
Tana gama fad’in haka ta fice da sauri tana mai jin takaicin yana d’an raguwa.

Karfe 7:56
Adaidaita sahun su ta yi
parking a bakin ‘Yashjub Limited’Sunayen su kawai masu gadin suka tambaya,Manubiya tana fad’ar sunanta suka shiga yi musu sannu da zuwa suka bud’e musu k’aramar k’ofa suka shiga.
A reception suka zauna bayan sun je sun fad’i sunayen su an ce ‘su d’an jira.’
Ahankali Ya Musbah yake kallon gurin yana adduar Ina ma ace ya samu aiki a gurin ko masinja ne in dai zai samu abun da zai ciyar da Inna da Baba da y’an uwan sa da Baraka da d’an sa to Alhamdulilla,aikin gini da wanki da gugan nan daya ke yi ba k’aramin wahala yake sha ba sannan ogannin na sa basa biyan sa sosai,ga shi kullum a gajiye yake,Baraka har ta fara masa mitar baya sauk’e mata hakkin ta na aure da yake a kan sa saboda kullum yana zuwa gida yake baje wa sai barci,tsabar gajiya.A nan kam ya san ba zai dinga yin gajiyar da yake yi a wankau ba,ga gurin ko Ina AC ….

‘’Ya Musbah dan Allah ka daina kula Ya Yusuf tun da bashi da mutunci.’’
Muryar Manubiya ta katse masa tunani,murmushi kawai ya yi kafin ya kalle ta tukunna yace’’Manu,in na biye masa ai sai zumuncin namu yafi yanzu lalacewa…’’

‘’Miss Manubiya,follow me.’’
Wata baturiya cikin suite da skirt ta ce da su kafin ta
juya ta nufi hanyar sama,

A tare suka mik’e ita da Ya Musbah suka bi bayan matar,
a bakin lift matar ta tsaya
sai da ta juya ta tabbatar suna bayan ta tukunna ta danna lifter ya bud’u sannan ta shige ta kallesu tace’’come in,pls’’

A hankali suka shiga k’irjin Manubiya yana dukan uku uku,dan bata tab’a shiga ba ta dai san menene amma bata tab’a shiga ba.
4th floor dama matar ta danna wanda shine last floor dan haka suna isa lift d’in ya tsaya k’ofar ta bud’u matar ta fice suma suka bi ta a baya.
Sai da numfashi su ya kusan d’auke wa saboda tsananin had’uwa da kyawun wajen,ko ina glass dan kana iya hango har chan waje har titi,ga wasu fitilu da suka haska wajen suka sa yayi wani irin haske tarr.
Hijabin idi n ta na last year ne a jikin ta brown colour
a wanke tass a goge har k’asa sai shek’i yake yi dan tun sallar data saka bata sake saka wa,Ya Musbah kuma yana sanye da jallabiya bak’a da hula fara tashi ka fiye naci,kayan su duk a goge suna shek’i amma duk da haka sai suka raina kansu saboda had’uwar wajen da kyawun shi
sai ya fito da rashin kyau da tsadar kayan nasu.Apart from wannan baturiyar da take yi musu jagora basu ga kowa a wajen ba,a k’asa ma kwata kwata mutum shida suka gani daga receptionists sai wani a cikin suite sai masu gadi da cleaner,da alama dai company d’in bayan kasancewar sa private to mai company d’in ma baya buk’atar mutane da hayaniya tun da gashi itama ce mata aka yi dama’sau d’aya zata dinga zuwa a sati’.

Suna tafe ita da Ya Musbah suna bin bayan wannan baturiyar kowa da abun da yake aiyyanawa a ransa,wani dogon corridor suka bi kafin su k’arasa wani babban guri,ata chan gefen hagu suka hango wani waje kamar d’an k’aramin parlour mai d’auke da wasu d’urma d’urman sofa 3seater guda uku masu tsananin kyau da d’aukar hankali sai center table a tsakiyar su da fridge da dispenser a gefe da gefen su.
Yayin da tsakiyar wajen ke d’auke da wani makeken roundabout wanda aka cika sa da shuke shuken flowers masu tsananin kyau da kamshi,yayin da wuta kamar na pop yake ratsowa ta k’asan flowers d’in yana k’arawa shuke shuken asalin kyau da d’aukar hankali,
Manubiya bata gama tunanin taya ake bawa flowers d’in ruwa ba ta ji baturiyar tace
mata’’ this way miss’’kafin ta kalli Ya Musbah tace masa
‘’U can wait,right there.’’
Ta fad’i haka tana mai nuna masa wannan d’an mini parlour d’in da yake ata chan gefen hagu.
Kwata Kwata k’ofofi uku ne a wajen na glass,biyu suna kallon juna d’aya kuma yana opposite wannan mini parlourn da aka ce ya Musbah ya zauna
duk da roundabout d’in flowers d’in da yake a tsakiyar su tsaf kake iya hango komai dayake a ciikin dukkan wajajen.
Biyun da suke facing juna, a d’ayan kana iya hango tebura
da chairs d’in su da computer a kan ko wanne tebur,yayinda wanda yake kallon sa kuma yake d’auke da k’atoton tebur da kujeru wajen sama da arba’in sai doguwar micro a gaban ko wacce kujera a ajjiye kan tebur d’in sai projector d’insu da suka bari a kunne.
Sai last one d’in wanda yake kallon mini parlourn,a saman shi an rubuta C.E.O,kana iya hango normal tebur sai kujeru biyu a gaban tebur d’in da kuma d’aya tana kallon biyun
sai parlour mai kyau a gefe da kuma wani mutum sanye cikin white suite dogo k’ak’k’arfa giant ya juya baya yana kallon waje da waya a kare a kunnen sa….

Da farko Ya Musbah yaso yayi musu da aka ce kar ya shiga,sai kuma yaga ai yana iya hango komai na cikin inda aka ce Manubiyan ta shiga dan haka ya je ya nemi waje ya zauna, yana kallon su har wannan baturiyar ta shiga Manubiya tabi bayan ta suka mayar da k’ofar suka rufe ….





MANNUBIYA
25

Na
Humayrah Bulama

Mikiya Writers Association.

Tun lokacin da suka shigo cikin company d’in ya gan su ta cctv kuma ya fahimci ita ce dan ba shi da appointment da kowa yau,babban abun da ya d’aga masa hankali shine Ya Musbah,ba ya ganin fuskokin su sosai shiyasa bai fahimci fusgen kamar da suke yi ba dan shi a tunanin sa ma Abbakar ne tun da tare ya gansu the other day,a ran sa ya ce ‘’to ko dai saurayin ta ne da gaske’’a take wata zuciyar tace masa’’to idan ma saurayin nata ne ina ruwan ka,kai naka ba kawai ka san more about her ba..’’
Yadda yake jin zuciyar sa tana tafarfasa ne ya sanya ya kasa jurewa ya rufe computer ya mik’e ya bar gaban tebur d’in nasa ya isa jikin glass ya juya baya yana mai kallon waje.
A haka secretary d’in tasa ta shigo ta same sa tace ma sa’’ Ga Manubiya ta zo’’.
Yana bata izinin taje ta shigo da ita ya zaro waya ya hau kiran Najeeb dan ji yake yi kamar ya sa security su fitar da wanda yake tunanin Abbakar ne,yana so ya san alak’ar ta da shi kafin ma su shigo masa office..

‘’You are suppose to be busy by this time,ko ba da safe ka ce mata ta zo ba?’’muryar Najeeb ta katse masa tunanin da yake yi.

‘’Yeah, gata nan ta zo amma basu shigo ba,amm..Najeeb wanann yaron da na gan su tare ranar a office d’in ka waye ne shi d’in saboda yau ma gasu nan ta taho min da shi.’’

D’an guntun murmushi Najeeb yayi yana mai jiyo kishi k’arara

Please Login or Register in order to submit comment