Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sunan ta,da sauri ta juya da niyyar fita amma sai ta kasa sakomakon magiya da hak’urin daya shiga bata yana cewa sharrin shaid’an ne ta yi hak’uri ba zai sake ba,kawai he got carried away by her beauty ne ya biyewa feelings d’insa towards her,bai san me ya shiga kansa ya aikata hakan ba amma inshaaAllah ba zai sake ba.’’

Yadda jikin ta yayi sanyi shi kan shi Yassir d’in ya lura da hakan,yana shirin cigaba da magana ta juya da sauri ta fita dan tabbas in ta ci gaba da zama a d’akin tou za’a samu matsala.

Tana fita Yassir yayi wani killer smile,tun day1 dama ya fahimci yarinyar za ya yi saurin shiga hannu kuma ya lura kamar tana d’an son shi,he has to get wat he wants daga gareta ta ko wacce hanya sannan yayi using d’in ta yayi getting back at Ummi,dan ya lura lamarin Mommy da Daddy ya sake tab’arb’arewa kuma yana da tabbacin Ummi ce sila.Sannan yarinyar ta tafi da imanin sa,ya san baya sonta
amma fa tabbas a cikin mata in za a rabasu kashi d’ari tou kashi 1 zuwa biyu ne za a same su da irin zubin Munirat….

Yana wannan lissafin yana murmushi ya juya da niyyar d’aukar bowl d’in dan yunwa yakeji amma sai ya gagara sakamokon tsamin da hannun sa yayi,dole haka ya hak’ura..a hankali ya koma ya sake langab’ewa saboda ko’ina na jikin sa ciwo yake masa..he can’t believe it he really can’t believe this wai Yashjub ne yayi masa haka da girman sa da kud’in shi da class d’in sa,tabbas abun da friends d’in shi suke gaya masa ya tabbata
‘’In yayi wasa sai ya zama d’an kallo a gidan’’.
Shi fa daman tun farko kokawa kawai yakeyi da zuciyar sa saboda ya san Yashjub d’an uwan sa ne kuma Mommy ba za ta so taga basa shiri ba
amma wallahi tun yarinta shi kam ya tsani Yashjub,duk wani abu dayake so ko yake son yi
to sai abun yayi ta zuwar ma Yashjub d’in cikin sauk’i.
Tun yana Yaro yake da burin zama business man babba sosai kamar Daddy,
Daddy yace sai sunyi phd tukunna zai basu jari
amma Yashjub ko da ya gama phd d’inma already yanada estate all thanks to son kan da Daddy ya yi tun ranar da aka haifi Yashjub d’in, shiyasa da Daddy ya basa jarin sai arzik’in sa ya sake nunkuwa,shi kuwa da aka
bashi na sa aka bud’e masa company compared to na Yashjub.. duk sai ya rena dan a lokacin har ma a yanzu bai Isa ya tsaya yace zai goga da Yashjub a harkar business da kud’i ba ya fi sa ya tsere masa ta koina..kuma har gobe Yashjub d’in kamar wani aljani duk abun da ya saka a gaba tou Sai ya cin masa kuma sai ya yi albarka, baya jin tun tasowar su ya tab’a ganin abun da Yashjub ya nema bai samu ba.
Shi yasa tun kafin a zo nan Abokanayen sa suke ba sa shawarar ya tashi ya tsaya dan it’s clear Daddy ya fi son Yashjub ga shi ya fi sa kud’i da fame shekarun Mommy ma suna dad’a yin sama wanda yafi arzik’i a tsakanin su shi zata fi so…yana k’ok’ari yana danne zuciyar sa ne dan baya so ya cutar da Yash amman gaskiya he can’t take ita anymore ya tsane shi tsana bata wasa ba dariya kawai yake yi masa kasancewar shi d’an uwan shi dolen shi sannan ya san ba shi da yadda zai yi da shi amma yanzu kam
lokaci yayi daya kamata ya tashi tsaye ya nema wa kanshi mafita kuma yaga bayan Yash.
ta hakan ne kawai k’ima da martabar sa za su dauwwama a idanun y’an gidan da duniya baki d’aya..
………
Munirat tana fita Ummi ta ce
‘‘Daddy kar ka ja inyi maka musu ka yi hak’uri komai ya wuce amma dole in tafi,yaran ma ba sa k’auna ta ba za mu zauna k’ark’ashin inuwa d’aya da su lafiya ba’’

Cikin katse ta yace
‘’Ummi I’m not going to apologize ke kin sani.
Kawai nace ki zauna kuma
i‘m expecting u to obey me
As my wife
sannan su Yasmeen dolen ki ne
A cikin gidan nan it will be better ki nemo solution akan yadda za ki zauna…’’
Ummi za ta yi magana kenan
Daddy ya toshe mata baki yana kallon k’ofa,ba tare da b’ata lokaci ba yayi sauri yayi wuff ya fice.

Da sauri Mommy ta shiga gyara d’aurin zaninta data kamo bakin za ta kunto a d’an rikice ta ce ‘’wajen ka na zo’’ bata jira jin mai zece ba
sannan bata damu da kallon tuhumar da yake yi mata ba ta d’aura da cewa’’ am..an bugi Yassir akan Munirat but itama ya kamata a ja mata barrier akan zuwa d’akin shi,ita yarin ya ce kar mu je ya Yashjub ya ce zai yi mata shegen dukan da ya yiwa Yassir kaga in haka ta faru maman ta nasan a za ta daliliba ga kuma halin da ake ciki Daddy dan Allah ka d’aga musu k’afa mana ….

Cikin rashin fahimta Daddy yace’’ban gane ba’’dan gaba d’aya zancen nata a hargitse ya ke kamar yadda ita ma ta hargitse ganin an kusan kamata.Dai dai nan Ummi ta fito,da dauri Mommy ta matsa kusa da ita ta rungume ta tace
‘’Dan Allah ki yi hak’uri akan abun da ya faru d’azu na yi masa magana hakan ba za ta sake faruwa ba,ki zo mu je kuma ina son ganin ki akwai maganar da za mu yi in babu damuwa’’kafin ta kalli Daddy ta ce ‘’za mu iya tafiya dan Allah ?’’

Ahankali ya d’aga mata kai
yana tunanin tou lab’e take yi musu ko kuma dai da gaske zuwan ta yi suyi magana,dan har ga Allah bai ganta lokacin daya fara magana ba yana ganin inuwar ta kuma yayi sauri ya fito which means
bata dad’e a wajen ba kenan. ‘’’muje dan Allah?’’ya ji muryar ta cikin sanyi a hankali.

D’aga mata kai kawai yayi
ya bari akan in sun had’u su biyu ya tambayeta,ya san ba lalle ta fad’a mishi gaskiya ba
amma ai tsoratata dan ba zai iya tolerating wani sabon bad habit daga Mommy ba
Apart from waenda takeda su.

Suna fita shima kawai ya wuce ya bi bayan su,suna fitowa daidai ita ma Munirat ta fito daga d’akin Yassir,haka kurum sai ta diririce
Kamar mommy bata ganta ba
hakanan kawai taja hannun Ummi suka nufi side d’in ta,
Daddy ma bece mata uffan ba
Ummi kuma jira tayi skan in su koma d’aki Munirat d’in ta yi mata bayani dan bata fahimci hak’urin da Mommy ta bata ba
sannan ko tana hauka ai d’akin Yassir ba wajen zuwan ta bane ba.

Ko da suka je d’akin Mommyn
hak’uri Mommy ta bawa Ummi
sannan tad’an fad’a mata halayen Daddy tace kuma indai ya nuna baya son abu kar tayi sannan itama musabbabin farkon fad’an ta
da shi akan ta daki Yadira ne.
Kuma da sam ba haka yake ba.
ta yi hak’uri kawai tayi tolerating dinsu Yasmeen mata ne kamar yadda ta fad’a nan da 5 years ba za ta tarar da kowa a gidan ba duk aure xa su yi inshhaaAllah dan haka kar ta bari a ta sanadiyyyar su yasa ta tafi ta bar gidan auren ta.
Sun d’an tab’a hira,har Ummi tana mamakin sakewar da Mommy ta yi da ita ta nata janta a jiki.
Ummi ta na da asthma shiyasa taketa so ta bar d’akin dan suna shiga Mommy ta kunna musu turare wai tun safe data gyara d’akin yau ba ta saka ba,shiyasa har wani d’ad’d’aukewa Ummi ta ji numfashin ta ya soma ga shi kuma Mommy ta k’i barin ta ta tafi sai sake rik’eta ta ke yi da hira,ita kuma kawaici yasanya ta kasa ce mata bata son hayak’in.
Sai da Yadira ta shigo tace musu ‘’Najeeb ya zo yana k’asa yanason gaisawa dasu’’
Tukunna ta samu suka fita a d’akin suka sauk’a k’asa.

Ta gama rayawa a ranta zata zauna ba za ta tafi ba amma wallahi sai Daddy ya san ya tab’o ta,da farko ta yafe mishi
amman yanzu kuwa komai ya chanza besides tun da ya yi mata wannan wulak’ancin kuma ya fifita ‘ya ‘yan shi akan kowa to tabbas ita ma ba zata
sake saka shi a priority ba,ita
bama ta san ya aka yiba
amma wallahi fit ya fice a ranta a cikin mintinan da ba su fi talatin ba,gaba d’aya ta tsaneshi ……


Cikin mutun ta juna da kulawa suka gaisa da Najeeb Mommy ta gaba tar mata da shi a matsayin wnda yake neman Ya’isha da aure kuma Abokin yash sannan family friend d’in su.

Anan parlourn Mommy ta barsu ita kuma ta mik’e taje kitchen dan ta nunawa masu aikin abun da za a d’aura,dan haka Ummi ma ta mik’e ta bi bayanta suka bar Yash da Najeeb a zaune wanda yake ta zaman jiran dawowar Ya’isha

Ummi tana zuwa za ta hau dining ta nufi kitchen Ya’isha ta shigo,ba tare da ta kalle ta ba tace’’Ban yi tsammanin ganin ki ba ai,ko da yake na manta ashe zuciyar kare ya cinye.’’
Tayi maganar kamar ba da ita take ba dan ko kallon Ummin ba ta yi ba kuma bata daina tafiya ba..daga haka ta wuce cikin parlourn.
Suna gaisawa da Yash ya mik’e ya fice daga parlourn ya bar ta ita da Najeeb.
Zama ta yi a kujerar da take facing d’in sa kafin ta ce ‘’Sorry Ya Najeeb Ina y’an wasu abubuwa ne’’
Cikin nutsuwa ya d’an k’ura mata ido kafin ya ce ‘’shine kika kasa yimin ko da message ne?’’
D’an turo baki ta yi tukunna tace’’Ya Najeeb daga shigowata sai fad’a?,to raina ne a b’ace tun safe da kyar na yi abun da na fita yi d’in ma’’
Ya’isha tana yi masa abubuwa da yawa masu zafi yana kau da kai amma na yau yayi mishi ciwo sosai
Wato
ranta ne a b’ace kuma bama shine yayi mata laifin ba laifin wani ne ya shafe sa shine ta gagara d’aukar wayar sa,shi yana nan yana tunanin ko maybe fushin da ta Saba yi da shi ta yi ashe abun ba haka bane ba wani sabon iya shege ne ta fito da shi…

Bai sake cewa komai ba haka kawai ya mik’e ya ce mata ‘’Allah bamu alkhairi’’daga nan ya sa kai ya fice.
Bata damu ba kan ta tsaye ko alamar nadama ko tunanin ta bashi hak’uri babu haka tace ‘’sai anjima’’kawai,
saboda ta riga ta san ba zai m iya kwana biyu bai neme ta ba.


Yana fice wa ta nufi sama a gigice,direct d’akin Kausar ta nufa tana shiga ta tarar da ita tana waya da Yasira,cikin tsananin tashin hankali tace ‘’she’s still here,bata ta fi ba har yanzu,how?’’

Numfashi kausar ta fesar kafin ta ce''baki fimu tashin hankali ba,ki nustu ki zo ki zauna ki ji''

Dakyar ta nemi waje ta zauna daganan Kausar ta saka wayar a hands free suka shiga magana da Yasirar har ita….

……..Thursday……..

Cikin ikon Allah
jikin Inna da sauk’i sosai dan har zama tana iya yi in an zaunar da ita kuma tana iya cewa’eh’ da ‘a’a’,wanka ne dai da ragowar abubuwa har yanzu sai anyi mata.

A b’angaren Baba ma ya siyo musu buhun shinkafa,katon d’in taliya da macaroni mai da maggi da tomato paste katon biyu.Rabon da su Manubiya su shiga farin ciki irin haka har sun manta sai dai kuma suna d’an fargaba dan basu san a inda Baba ya samu kud’in ba,ba yadda ba su yi da shi ba amma yak’i gaya musu ya ce musu ba bashi yaci ba k’arshema da suka dame sa da tambayoyi sai ya rufe su da fad’a..haka nan suka hak’ura suka ja bakin su suka yi shiruu.

Ba yadda basu yi da Ya Musbah ba akan ya d’an d’iba kayan abincin ya kai gidan sa amman sam ya k’i yarda yak’i d’iba,a cewar sa in bai kawo ba bai kamata ya d’auka ba kuma ai yanada aikin yi
Alhamdulillah suna samu suci suma yanzu kam ba laifi.

Ba dan sun so ba haka suka hak’ura suka barshi dan ya dage akan ba zai d’iba d’in ba,gaba d’aya tausayin d’an uwan na su sukeji especially yanzu da matsalar kud’in haya ta sako sa a gaba,k’iri k’iri ya hana su gaya wa Baba da Inna dan su ce musu ya yi ya biya gudun kar ya d’aga musu hankali,su Jidda ne kawai suka san bai biya d’in ba,mai gidan ya d’aga mishi hankali a haka ma Ya Nafi’u ya bashi dubu hamsin ya bayar yanzu sauran sabain,shiyasa su Manubiya suka gama deciding ita dasu jidda akan tana d’aukar albashin ta zata ba sa ya bayar,ta san maybe yanzu haka yanata fafutuka so maybe ya samu ya had’a kan 40 d’in dan tun last year daya biya ya fara shirye shiryen biyan na wannan shekarar..
Allah sarki in ka gan sa duk ya rame farar fatar sa mai shek’i da kyan gani ta d’an yi duhu
fuskar nan hanci ya k’ara tsayi idanuwan sun sake fitowa zurr
shiyasa gaba d’aya suke tsananin jin tausayin shi,dauriya kawai suke yi dan ba sa so su karaya su nuna mishi ne suje su kashe mishi kwarin guiwa.

A b’angaren Ya Musbah kuwa,kud’in haya bai d’aga masa hankali ba kamar yadda Baraka ta d’aga masa hankali
gaba d’aya ta birkice mishi especially kwana biyun nan rigimar yau daban ta gobe daban yanzu ta d’aga masa hankali akan wai k’awayenta y’an unguwar suna mata gani gani,a ganin ta bai kamata ya ci gaba da wanki da guga ba saboda za ‘a raina ta wai anyi bikin k’anwar wata k’awar su ba a gaiyyace ta ba saboda tana a matsayin matar mai wanki da guga,ya nemi wata sana’ar amma gaskiya ba wannan ba ya yi low class da yawa.
Shi kuma Ya Musbah da wanki da gugan yake samu yake ciyar da iyalin na sa yake rufawa kan shi asiri shiyasa ya k’i hak’ura ita kuma ta dage shiyasa kullum cikin fad’a suke ita da shi bai san ya zai yi da ita ba dan in ya bar wanki da gugan ita ce ta farkon fara d’aga masa hankali.Gashi yanzu ta tsiri wani salo wai tana da low bp dan haka miyar ta kullum dole sai an saka mata nama a ciki sannan ya siyo mata maltina,yanzu haka ta koya wa me sunan Baba
In ba nama a abinci to ba zai ci ba sannan shima in be sha maltina ba ya dinga zunduma musu ihu kenan duk makwafta sai an jiyo su.
Ya Musbah yanada guilty conscious muddin ya
siyawa Baraka nama da maltina hankalin sa baya tab’a kwanciya sai ya siya ya kaiwa inna da Baba ko kuma ya bawa Baba kud’i ko ya siya wani abun ya kaiwa su Manu,Shiyasa gaba d’aya ya
sake zugewa wani lokacin ko abinci baya samu yaci dan babu enough,
Kuma kullum in ya fita aiki tun safe sai dare yake samu ya zauna ya d’an huta.
Tun suna yara yake son Baraka
ba dan ragowar birbid’in son da yake yi mata ba da kuma darajar me sunan Baba wallahi da tuni ya sallame ta, ya gaji
har ga Allah Baraka ta kai shi bango a kwanakin nan,wayar
hannunta kad’ai abun kallo ce
amman ta siya maggi guda d’aya a gidan aiki ne a gareta
ta gwammaci ta dame sa a waya in me sunan Baba ya fara kukan yunwa,ba abun da ya fi sake bak’an ta masa rai irin yadda ta rena iyayen sa,
Kwanaki baya
Yayan Nafi’u ne yayi hatsari
dama ba shi da mata
So
yana gida a kwance ba lafiya,irin girkin da Matar Nafi’u Aisha tayi ta tafi dubiya sai da ya bashi mamaki dan ranar shima har zubo masa aka yi,tun daga nan kuma bata sati ba ta je ta dubo sa ba,hatta Inna..Aisha bata
yin sati bata je ta duba ta ba..amma ita Baraka tace su Manubiya sun rai na ta kuma ba a ganin girmanta a gidan,tun da Inna ta fara rashin lafiya sau d’aya taje ta dubata
lokacin tana asibiti kuma shima sai da yayi daya sanin zuwan nata,k’iri k’iri ta hana k’annen sa zuwa gidan kuma itama bata zuwa in da suke……


A b’angaren Jidda ma abun ba sauk’i dan hankalinta a tashe yake kwana biyun nan,ko waje da kyar take iya fita dan sai ta tabbatar kuma ta lura Ya Yusuf
baya gidan ko kuma in in yana wajen aiki,saboda ta tsorata da shi sosai tun ranar da suka had’u yayi treatning dinta
………..
‘Abun da suka yi ma sa ita da su Baba... disga shin da suka yi a gaban kowa k’iri k’iri suka ce basa so ta aure shi,to ta sani ya ji zafin hakan sosai,kuma ya tabbatar mata har yanzu yana sonta sannan bata da wani mijin bayan shi
It’s either ta hak’ura ta aure shi
watak’il ya manta da rashin mutuncin da sukayi mishi a gaban su kaka mallan ya fasa d’aukar revenge d’in da ya yi niyya ko kuma ya kunno wa ahalinta bala’in da ba za su tab’a iya kashe wa ba wallahi.
Taje tayi tunani yana jiran amsar ta ya bata kwana biyu,kacal!.’’
……..
Shiyasa tun lokacin da kwana biyun ya cika take wasan y’ar b’uya da shi dan bata san me zata ce masa ba.
Duk da wata zuciyar tana bata shawarar ta hak’ura ta aure shi akan dai ta bari ya tab’a mata ahalinta amma kuma bawai iya bata son Ya Yusuf baneba
har ga Allah ko kallon shi wani lokacin bata son yi,sannan
treatning d’in ta da yayi yasa ta sake tabbatar wa ba mutumin kirki bane ba,a ganin ta rashin mutuncin Baraka is enough bai kamata ace ta k’arawa su Baba da another bad inlaw ba,matsalar su ma ta ishe su.
Gashi yace karta fad’awa kowa ta san kuma in ta fad’a d’in zai sani dan ta san su Manubiya ba za su yi masa da sauk’i ba, ita kuma har ga Allah
tsoro takeji dan a yadda taga idanun sa a ranar sam bata ga alamun wasa a ciki ba.






MANNUBIYA
30

Na
Humayrah Bulama

Mikiya Writers Association.

Duk da wata zuciyar tana bata shawarar gara ta hak’ura ta auri Ya Yusuf akan dai ta bari ya tab’a mata ahalinta amma kuma ba wai iya son shi ne kawai ba ta yi ba, har ga Allah ko kallon sa ba ta son yi,sannan treatning d’in ta da yayi yasa ta sake tabbatar wa ba mutumin kirki bane ba,a ganin ta rashin mutuncin Baraka is enough bai kamata ace ta k’arawa su Baba da another bad inlaw ba,matsalar su ma kad’ai ta ishe su.
Gashi yace karta fad’awa kowa ta san kuma in ta fad’a d’in zai sani dan ta san su Manubiya ba za su yi masa da sauk’i ba, ita kuma har ga Allah
tsoro takeji dan a yadda taga idanun sa a ranar sam bata ga alamun wasa a ciki ba.

‘’Tunanin me kike yi?’’
Muryar Manubiya wadda ta shigo yanzun ta katse wa Jidda tunani.
Da sauri ta d’an matse kwallar data tarar mata tana shirin zubowa sannan tace
‘’Ba komai,ya aikin?’’
Ajiyar zuciya Manubiya ta sauk’e kafin tace
‘’Huh!Alhamdulillah,Ammi fa ta tafi next level,dan ma Allah ya taimake ni gobe zan gama exams d’ina..wallahi abubuwa duk sun yi min yawa especially a gidan Ammi,dan ma akwai Maama.. mace mai kirki wani lokacin fa ita take taya ni wasu abubuwan,ta ma ce za ta shigo ta duba Inna.’’
Manubiya ta k’arashe maganar tana mai neman waje ta zauna a kusa da Jidda.

‘’Allah sarki,sannu!ki yi hak’uri duk ni na janyo muku’’Jidda ta fad’i hakan cikin rashin jin dad’i.

Murmushi Manubiya tayi
tana kallon ta kafin tace ‘’Ba komai kar ki damu,Allah yasa mu dace’’
Ahankali Jidda tace’’Ameen’’dai dai nan Baba ya shigo bakin sa d’auke da sallama ahankali ya nemi guri ya zauna..cikin girmamawa suka gai da shi ya amsa kafin Jidda ta mik’e ta fita domin ta je ta kawo masa abinci,daga haka d’akin ya yi shiru kowa da tunanin da yake yi a ran sa.


Manubiya Yashjub ne ya b’ata mata rai,jiya aka yi mata reporting abu dan haka tace masa akwai report via watsapp..his reply was distracting’’Okay dear,u can report to me tomorrow
as planned,take care.’’
Tabbas ya kusa tarwatsa mata zuciya da ta gani,dan me yasa zai ce mata wani ‘dear’,bai san yadda zuciyar ta ta buga ba da taga reply d’in har yanzu bata gama dawowa daidai ba.Gaba d’aya ya sakar mata da kasala daga reply d’in,anya kuwa ba za ta tura masa bayanan ta watsapp ba goben tak’i zuwa ta yi k’aryar bata da lafiya,dan tun jiya ta fara fargabar had’uwar su ta gobe,bata so ta fara feeling wani abu na daban game da bawan Allahn nan dan bata shirya shan wahala akan soyayya ba..iyakar ganin sa da muryar sa ma kad’ai kid’ima ta suke yi yanzu kuma ya kama ya wani ce mata ‘dear’tun safe ya rikitata.
Shigowar Jidda ne ya katse musu tunani gaba d’aya su biyun,da ladabi ta k’arasa ta ajjiye abincin a gaban Baba sannan ta koma gefe ta zauna.

Ahankali Baba ya d’ago ya kalli Manubiya kafin ya zaro bandir na kud’i daga aljihun sa ya mik’a mata,cikin nutsuwa ta matsa ta sa hannu ta karb’a,tana shirin yin magana yace’’ gashi gobe in kinje ki bawa Ammi,na ke da Muhsin,kun bar aiki kenan inshaaAllah ,ku samu ku huta Allah ya yi muku albarka.
InshaaAllah wani satin in aka koma makaranta dashi za a shiga in kin huta zuwa ko anjima ne sai ki je ki tambayi kud’in uniform da shiga da duk abubuwan da ya kamata a makarantar mazan chan,zuwa dare inshaaAllah zan bawa Musbahu kud’in ya je ya biya masa in Allah ya kaimu aka koma sai a fara tare da shi.

Ahankali Manubiya tace ‘’An gode Baba Allah ya saka da alkhairi ya k’ara bud’i ya bawa Inna lafiya’’

Cikin tsananin sanyin jiki Jiddah ma tace ‘’an gode Baba’’

Ahankali Baba yace’’Ameen’’.

Daga nan duk su biyun suka yi shiru
A Ina yake samun kud’i ?
Gashi tun last time ya kora musu warning d’in kar wadda ta sake tambayar sa a inda yake samun kud’i in ba hakaba kuma ransu zai yi mummunar b’aci,Wallahi….

Har ya gama cin abincin ba wadda ta iya sake cewa komai,ya na gamawa ya mik’e da shirin sake fita…cikin girmamawa suka yi masa a dawo lafiya,sai da ya je ya shafa fuskar inna wadda take baccin ta cikin kwanciyar hankali tukunna ya sa kai ya fice daga d’akin…

Yana fita Jidda tace
‘’Adda Manu inajin tsoro fa,ta
Ina Baba yake samun kud’i haka lokaci guda??’’

Ajiyar zuciya Manubiya ta sauk’e kafin tace ‘’Jiddah nikam taya za ayi in sani?,let’s just hope for the best,dan nima gaskiya kaina a d’aure yake.kina karatu kuwa sosai?
post utme d’in ku fa ta matso. ‘’
Ahankali jiddda tace ‘’eh,Ina yi ku taya ni da addu’a’’

‘‘InshaaAllah’’
Manubiya tace,kafin ta mik’e ta koma gefe ta d’auki takarda ta shiga karatu,gobe mai tashin kafin asuba ce dan exams d’in 9 gare ta,ga shi a goben ne za ta had’u da Yash,Allah ya taimake ta ita da gidan Ammi sun yi bye bye ba dan haka ba da bata san yaya zata yi goben ba.

Kalar tsalle da murnar da Muhsin yayi lokacin da ya ji labarin tafiyar sa makaranta sai da ya bawa su Manubiya mamaki amma da suka tuna yadda Yaron yake da k’ulafucin makaranta sai suka yi masa uzuri,dan

Please Login or Register in order to submit comment