Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yafewa Al’ameen d’inki ki yafewa Ammi itama kinji’’?.
Ya karashe maganar kamar zai fashe da kuka

Shiru Jidda tayi ta fad’a duniyar tunani
Ita kanta tasan k’arya takeyi tace batason Al’ameen wanda tun tana ss1 suke soyayyar su a b’oye a layin
dan a lokacin tasan Baba ba zai tab’a barinta kula samari ba.
Haka yayi hak’uri yayi ta jiran ta har ta kammala tukunna ya baiyyana wa Baba da Ya musbah manufar sa,
sun kuwa yi farin ciki bawai dan tsananin arzikin mahaifin sa ba wanda kaff unguwar ba za’a nuna wanda ya kamo k’afar sa a kud’i ba,
sai dan hankali da sanin ya kamatan Al’ameen d’in

Duk arzik’in mahaifin sa shima bai nuna k’in amince wa ko Kyama ba,
Ammin sa ce a lokacin ta kafa ta tsare ta zuba musu tujara Sosai
Sannan tace
‘sam bata yarda d’anta ya auri y’ar talakan miskini ba’.

To yanzu kam in dai Ammin sa ta amince kamar yadda ya fad’a
shikenan ai bata da wani issue sam,Ammi kamar uwa take a wajen ta kamar yadda al’ameen yace ta yafe mata tsaf zata yafe mata dukkan nin abunda tayi mata ita da ahalin ta wannan ba matsala bace ba ..

‘’Jidderty’’
Taji ya kira sunan ta

Ahankali ta d’an kalle sa sai kuma ta sunkuyar da kanta.

Zai yi magana kenan Manubiya ta turo k’ofa ta shigo,
Suna had’a ido ya fara murmushi kafin yace
‘’Yayata wadda bata k’aunar gani na’’.

Cikin tarar numfashin sa tace
‘’Ka fad’a da k’arfi ka buga a jaridar da zata fita gobe dan maganar ka hakan take’’’

Da sauri Jidda tace
‘’Adda ‘’

Wani kallo Manubiya tayi mata dan haka ta ja bakin ta tayi tsit ta sunkuyar da kanta bata sake cewa komai ba.
kusa da Inna kawai ta k’arasa ta nemi waje ta zauna ta had’e rai, taso ta wanke Al’ameen
amma Takaicine sa da na jidda sam sai suka hanata cewa komai.
Sunfi minti talatin a haka
kafin daga baya Al’ameen d’in ya mik’e
Yace
‘’ni zan wuce’’

‘’Mun gode’’ kawai Jidda tace
Manubiya kuma ta mike ta ce
‘’Muje,inason ganin ka’’

Ko da suka fita nicely
Manubiya ta rok’e sa akan ya daina bibiyar su,

Amman sai ya tabbatar mata dacewa
‘’Ai Ammi ta sauk’o ta ce a basu ma hak’uri zata zo dakanta ta duba Inna’’

Ita dai Manubiya still cewa tayi
‘’Ya d’an jira sannan ya daina yawan zuwan
har sai an tabbatar da amincewar Ammi
domin su a yanzu rikici da tashin hankali is the last thing da za su yi involving kansu a ciki ‘’

Ba dan yaso ba sai dan yadda Manubiyan ta dage
haka nan ya ce mata’’ tou ‘’
kawai ya wuce

Ko da ta koma ciki ma
saida ta zubawa Jidda serious warning
Kuma ta ga jiddan ta yarda tukunna ta kyale ta.
Tana kokwanton maganar Al’ameen
‘Wai ammi ta yarda ya auri Jidda ‘


Bayan sati biyu
Successfully akayi aikin Inna,
Manubiya da jidda ne suke mata wanka da komai dan har yanzu b’arin jikin ta sam baya aiki,ko magana ba iyawa take yi ba

Sun so su koma ward amma sai aka ce musu ai Al’ameen kud’in wata d’aya ya bayar so koda ace ba a kai one month d’inba
Yace su za a bawa chanjin.

Tunda Jidda take a rayuwar ta bata tab’a b’oyewa Manubiya wani abu ba sai wannan karon

Dan a washegarin ranar da Manubiyan ta ce karta sake kula Al’ameen sannan shima kar ya sake zuwa ma saida ya dawo kuma ya sake cin sa ar samun Jiddah ita kad’ai
lokacin Manubiya ta tafi allura.

Ganin tsoro k’arara a idanun Jiddahn ne yasa yace mata gobe zai dawo Karfe 4 na yamma yayi mata kwatancen in da zasu had’u

Haka nan sukeyi
In lokacin zuwan sa yayi saita kwashi wanke wanke ko ta karb’a sak’o
In taje Bata dawo wa
sai sun sake had’a Appointment na inda zasu had’u washegari

Shi Al’ameen bayason causing mata problem da su Manubiya
kuma Ammin na sa bata samu daman xuwa ba ta tafi ummara
Shi kuma yana ganin tunda har mahaifiyar sa da mahaifin sa sun amince a gaskiya ba zai iya yin nesa da Jiddah ba
dan yana mutuwar k’aunar ta

Ita ma jiddan tana son abunta
Kuma saura masa sati uku a lokacin yanzu kuma saura sati d’aya ya tafi wani course da zaiyi na 4weeks
Shiyasa kawai ta amince
kuma ta b’oyewa Manubiya dan karta hanata,
A cikin sati biyun nan kuwa
soyayya da shakuwa ta sake kulluwa tsakanin su bata wasa ba ……..




MANNUBIYA
09
Na
Humayrah Bulama

ELEGANT Online ✍️

2weeks ago

Kamar yadda Mommy ta yi tsammani
Washegari da safe ba zancen auren Yassir da Kausar
Sannan ba bu Daddy babu alamar sa.
Ita a tunanin ta fushi yayi ya zauna a d’aki saida dare yayi
taje kai masa dinner tukunna
ta fahimci bama ya gidan gaba d’aya
dan anan inda ta ajjiye masa breakfast da lunch a kan dining table d’in parlourn na sa
anan ta dawo ta same su yadda ta ajjiye babu ko alamar alamar an tab’a ma.
Tabbas ta d’an firgita musamman ma data shiga d’akin sa ta tarar ya kwashe kusan kaff kayan sa,tun anan ta sha jinin jikin ta sannan ta fara data sanin ambato Khadija data yi a jiya bacin k’wak’kwaran warning d’in daya zabga mata ita da su Yahanasu akan kar wanda
ya kuskura ya ambato Khadijah a cikin gidan..

Tana tsaye tana tunanin ta hanyar da zata bi ta shawo kan Daddy domin tasan ba k’aramin yaji yayi mata ba,
Yassir ya shigo.
Ahankali ta sauk’e ajiyar zuciya domin tun safe yake tambayar ta ita Daddy ita kuma ta zabga masa k’aryar ‘Daddyn yace sai gobe za a d’aura musu auren sannan ya tafi shirye shiryen gidan da za su zauna ne shiyasa bai gansa ba.
A b’angaren Yasir kuwa
dama tun dazu da safen da ta fad’a ma sa maganar bai wani gasgata ta ba shiyasa gaba d’aya tun safe hankalin sa a tashe yake
Kausar ta ma k’i ta bari ya ganta ta kashe wayoyin ta
Daddy baya amsa call d’in sa
Mommy kuma ya lura kamar avoiding d’in sa ma takeyi.
Jiya bai yi barci ba sai da ya had’a Dinner ta gani ta fad’a wadda za a gudanar a yau da daddare bayan an kai masa Kausar gidan sa,kusan kaff Abokanayen su babu wanda bai fad’ama yau auren sa da Kausar ba,yanzu haka side d’in su shi da Yashjub a cike yake taff da abokanayen su waenda suke gari maza,matan kuma ya kaisu side d’in Yasira dan kausar tayi wuyar gani.

Ahankali ya tako yazo gaban Mommy ya tsaya,farar fuskar sa har tayi jajawur dan tashi d’aya ya hango rashin gaskiya a tare da Mommy,
Manyan idanuwan sa da sukayi jazir ya zuba mata kafin yace
‘’Mommy stop toying with me,
na rok’e ki da girman Allah ki fad’a min me ke faruwa’’

Sam, Mommy bata yi tsammanin wannan bacin ran daga Yasir lokaci d’aya ba
hatta jijiyoyiin kan sa sun fito sunyi rud’u rud’u kan dogon hancin sa ma yayi jaa sosai

Ahankali cikin in ina tace
‘’Son,mun d’an samu matsala ne da Daddyn naku jiya,so ya yi fushi ya tafi.’’

Ba tare daya daina kallon ta ba
Cikin tarar numfashin ta yace
‘’Ina yaje???’’

A d’an rikice tace
‘’In da ace na sani da zan fad’a maka,’’

da d’an k’arfi yace
‘’Dole kin sani,ai nasan intentionally kika janyo fad’an saboda bakya son auren bakya son farin ciki na dan haka dole ki sani kuma dole ki nemo sa,haba Mommy how could u????
kinfi son farin cikin Kausar akan nawa ne ???
kamar ba ni ne d’anki ba.’’

Da sauri ta matso ta kamo hannu sa kafin tace
‘’Ba haka bane ba Yassir wallahi duk abun da kaga nayi
Gaba nake hange maka,farin cikin ka dauwwamar cikar burin ka shi nake tayaka nema,
Kai farin cikin yanzu kake so ka samu
Ni kuma hangen nesa nakeyi maka.Yassir ka fahimce ni ka yarda dani duk abun da nayi
nayi sa ne saboda kai kad’ai
Wallahi,
Trust me.’’

Cikin fushi ya fincike hannun sa a nata kafin yace
‘’I’m not interested in anything u have to say Mommy,na baki 3 hours ki nemo sa
If not
nima zan bar gidan nan kamar yadda Daddy ya bari har sai kin gyara abun da kika b’ata
an d’aura mana aure da Kausar tukunna zaki ganni.’’
Yana gama fad’in haka ya juya zai fita,
da sauri ta sha gaban sa da niyyar lallashi.
Tun Kafin tayi magana ya d’aga mata yatsun sa guda uku
Cikin tsananin bacin rai wanda ya had’e ma sa da tashin hankali
Yace
‘’3 days Mommy,kwan uku kacal.’’

Ko bi takan frnds d’in su bai yi,dan bai san taya zai yi facing d’in su ba.
Hatta other phone d’in sa bai biya ya d’auka ba
Allah yaso akwai car key a jikin sa dan haka ya nufi mota ya shiga ya kunna yaja ya fice daga mansion d’in.

Tun daga nan ba Daddy ba bu labarin sa
Ba kuma Yassir shima,
Koda abokin Daddy yazo ganin yahanasu yashjub ne ya tsaya ya tarbi bak’on,haka Itakuma ya san dabarar da tayi ta sallami frnds d’insu en biki da Yassir ya tara……..


Yau satin Inna biyu a asibiti tunda ta kwanta a asibitin sau biyu kawai Manubiya ta samu taje makaranta.
Ita kanta ba wai lafiyar gareta ba dan zazzab’i da ciwon kai sun sakota a gaba.

Yau suna zaune da rana gaba d’ayan su sai ga Baraka ita da maman ta da Abbakar da maman sa.
Tun lokacin da Innar ta kwanta jinya yau ne zuwan Baraka na farko kuma shima haka nan ta taho ko ruwa bata ruk’o ba ballantana azo kan maganar yiwa mara lafiya girki,
En gidansu Manubiyan ma siyama kawai Anty umma ta turo bayan ita ba wanda yazo

Abbakar,ya Nafi’u da al’ameen wanda yake zuwa a b’oye ne kullum sai sun zo
Matar ya Nafi’u ma zuwanta har hud’u …..

A nan kan k’atuwar taburmar dasuka shimfid’e a tsakiyar d’akin suma duk suka nemi waje suka zazzauna.
Cikin mutunta juna suka gaisa da Baba tare da tambayar sa ya mai jiki ya amsa musu da ‘’da sauk’i’’daga nan ya mik’e ya fita ya bar musu d’akin
Haka ma ya Musbah shima ya mik’e ya fita bayan sun gama gaisawa da surukan na sa.

Dakin ya rage saura matan kawai da Innar sai Abbakar dan Muhsin ma hannun Baba k’arami ya kama suka fita tare da Ya musbah

Gaisawa suka sake yi daga nan suka shiga tambayar su ya mai jiki da yanayin jikin nata.

Baraka bata wani dad’e a zaune ba ta mik’e ta bi bayan Ya Musbah.
Tana fita Abbakar ya kalli Manubiya yace
‘’Jiya fa sir najeeb yayi test’’

A firgice tace
‘’Wasa kake yi,Amma ko?’’

Cikin dariya yace
‘’A’a wallahi da gaske nake,yayi test jiya’’

Kamar zata fashe da kuka tace
‘’Haba Abbakar shine kuma baka gayamin ba nazo tun a lokacin nayi’’

Da sauri cikin katse ta yace
‘’In kinzo mai zaki iya rubuta wa ?ai nasan sai dai kiyi ta kukan da baya so a ajin’’


Still yanzun ma kamar mai shirin yin kuka tace
‘’Still dai ai da ko attendance ne nayi
Yanxu shikenan bani da test d’in?’’

Cikin son sake firgitata Abbakar yace
‘’Kuma yace shine na continuous assessment’’


‘’Innalillahi wa inna ilaihirrajiun’’
Manubiya tace duk ta rikice

Ganin yadda duk ta gigi ce ne ya sanya ya yi dariya yace
‘’Matsoraciya kawai,nayi miki tou’

Dasauri tana mai sauk’e ajiyar zuciya tace
‘’Da gaske ?
Test din ?’’

‘’Eh mana’’
ya bata amsa yana Murmushi

Ahankali tace
‘’Allah sarki , Abbakar
Na gode Sosai’’

A tare duk sukayi dariya har Jiddah

Mik’e wa yayi yace
‘’bara in wuce kasuwa Allah ya k’ara sauk’i,
Muje in baki handouts d’in daya fitar a jiya ya ce gobe zai kuma yin open test shima part of CA dinmu ne’’.

‘’Okay’’ tace tana mai mik’ewa
Sannan ta k’ara da cewa
‘’Mutumin nan d’an wahala ne Wallahi
Da shi da test 5&6’’.

Dariya yayi daga nan suka saka kai suka fita a tare.

A bakin ward d’in ta hango Ya musbah da Baraka a tsaye,
Kana ganin fuskokin su kasan fad’a sukeyi.
Baraka ce take facing d’in ta dan haka tana ganin tahowar ta tayi shiru har suka zo suka wuce.
A cikin garden ta chan gefe ta hango su Muhsin da Baba a zaune……


Allah sarki Abbakar
Duk wasu handouts d’in da aka fitar na course d’in da suke yi sai da ya siya mata,dan daman exams ta taho,
Duk haka ya had’a ya bata
Sannan ya sake tabbatar mata
Da
ta zo gobe.

Tasan saboda maman sa ne yasa yace iya na sir Najeeb ya siyo dan ta lura da yadda sukayi a lokacin da yace yayi mata test d’in ma

Shiyasa itama data karb’i jakar tayi godiya ta goya a bayanta
ta ci alwashin b’oye wa ……

Har ta karya kwana ta nufi su Ya Musbah suke sam basu hange ta ba,
ran sa a tsananin b’ace yake Itakuma Baraka ta bata baya
Shiyasa duk basu lura da ita tun kafin ta k’arasa kusa dasu
taji Ya Musbah yana cewa
‘’Yanxu Baraka ya kike so inyi ?
ko sata kike so inje inyi?
Na fad’a miki wallahi babu kud’i a hannu na’’

Cikin tsiwa tace
Eh kam babu kud’i a hannun ka ga alama nan ai na gani
rashin kud’in yasanya Innar ka take kwance a aminity
d’aki cike da kaji da lemuka,
ko y’an uwan ku ne suka kawo? ‘’

A zuciye yace
‘’Bana son cin fuska kuma,nace miki ba ni da kud’i
hidima kuma da kika gani ba ni nake yi ba
Ki yarda ko karki yarda wannan ba matsala ta bace ba,akwai kud’i a hannun ki ba wai babu ba dan haka in za kiyi hidimar gida dashi Bismillah
Duk ranar dana samu zan maida miki
In kuma zaki iya barin d’an da kika haifa a cikin ki da yunwa saboda rashin sanin ciwon kai to shima Bismillah,
Sannan in kinga ba zaki iya ci gaba da zaman ba
nan ma kin san mai zaki cemin inyi
ni kuma inshaaAllah zan yi miki yadda kike so’’

Cikin tsananin b’acin rai
Tace
‘’Eh lalle Musbahu kayi arziki ga alama ai dama ku maza haka kuke,wato kud’i sun fara zama maka shine ni Baraka nice a bar wulakanta wa ko?
Ka barmu da yunwa nida d’anka
ka dauko babarka ka kawo aminity kuma nayi magana kace zaka sakeni
Saboda yanzu kasan kana da kud’in da za ka yi wani auren in na tafi …’’


Cikin katse ta yace
‘’Ba wai cewa nayi zan sake ki ba,cewa nayi in kinga baza ki iya zama ba to ki fad’i abun da yake ranki ni kuma in aiwatar.
Magana ta ta karshe ki yarda ko kar ki yarda
Ba nine nake hidimar asibitin nan ba ,saboda bani dashi.’’
Dan haka in zan baki shawara ki d’auka to,
Kije ki siyo kayan abinci kuci da ke da mai sunan Baba
kar ki damu da ciki na
InshaaAllah zan samu abun da zan ci kuma duk lokacin da Allah ya bani kud’i zan mayar miki …’’

Yana gama fad’in haka ya juya ya wuce ciki
Yana adduar Allah yasa Manubiya bataji conversation d’insu ba dan shi sai yanzu ya lura da ita

Takaici kamar ya kar Manubiya,sam batayi niyyar kula Baraka ba dan haka ta zo zata wuceta da sauri tanajin wani takaicin ta na musamman yana rufe ta,
Ita kuma dai dai ta juya dan haka sukayi kicibus

Wani tsaki Baraka ta ja
Kafin tace
‘’Nikam wannan aure,
a cuce ka kuma kayi magana aji haushi
Sannan ga ido ta ko ina…’’

Har Manubiya ta d’anyi gaba
sai kuma ta juyo ta dawo ta sha gaban Baraka ta tsaya

Gyara tsayuwa kawai Baraka tayi
Ta shiga watsa mata kallon wlak’anci

Cikin takaici Manubiya tace
‘’Wallahi kin bada mata,ai ko kishi da rashin hankalin ma yanzu an daina yayin irin wannan.Duk abubuwan da kike yi zuba miki ido kawai mukayi bawai dan bamu san mai kike yi ba ne
sai dan
a kullum adduar mu itace ki shiryu.
Haba Baraka
Mahaifiya fa ?
Itace abar kishi ?
Inda ace ma lafiyar ta k’alau tou da da sauk’i
amman bata fa da lafiya,a kwance take,in baki taimako ba a gani na bai kamata ki d’aga wa kowa hankali ba,
Kaico!!Wallahi Ya Musbah bai yi sa’ar mace ba.’’

Yadda Baraka ta zaro idanuwa zaka d’auka daddana wa iyayen ta zagi Manubiya tayi,
ta san dama Manubiya bata da hak’uri amman bata tab’a tunanin zata iya gaggaya mata magana har haka ba.
Tijara da zuciya da suka ciyota ne ya sanya ta ta figo hannun Manubiya da dukkan nin k’arfin da Allah ya bata sukayi ciki tare.

Tun daga bakin k’ofa ake kallon su ga security ya biyo su ya nata faman yi wa Baraka magana
Yana cewa ta saki ma ta hannu
amman sam Baraka bata da niyyar sauraren sa,
ita kuma Manubiya taso yin tirjiya ko kuma ta fisge hannun ta amman kuma sai tace a ranta bara kawai ta barta kar suyi kokawa ta sake tada wani case d’in a tsakiyar asibiti.
Ta fahimci d’akin da Inna take take shirin kaita shiyasa ta gama rayawa a ranta suna shiga d’akin in ta cika ta zata fice ta barta dan ta lura burin Baraka tabbas bai wuce taga gawar Inna ba …

Da k’arfi ta tura k’ofar suka shiga tare ita da Manubiya
da sauri su Jidda suka mik’e tsaye saboda a yadda Baraka ta shigo kamar wata mahaukaciya zaka d’auka wani gagarumin abu ya faru,
Duk yadda Manubiya taso ta cika mata hannu takiya
ta rik’eta gam,
sai a sannan Manubiya tayi dana sanin k’in kwace hannun ta tun a waje suyita ta k’are dan tana shigowa d’akin da inna ta fara tozali ta bud’e idanuwan ta sab’anin dazu data barta tana bacci.

Dakyar Ya musbah ya samu ya had’iye wani k’ululun takaici daya tokare masa makoshi tukunna ya k’arasa wajen su,
Ba tare daya kalli Baraka ba ya cewa Manubiya
‘’D’auki jakar ki ki wuce gida’’
Dan yasan tabbas akan maganar da Manubiyan taji suna yi ne shi da Baraka
tayiwa Barakan magana
shine ita kuma ta janyo ta nan dan ta d’agawa Innar hankali.

Cikin d’aga murya hargowa da hargagi tace
‘‘Kasan mai tayi min ne
da zakace ta tafi haka kawai
wato ta zagi banza kenan ko?,
Allah na tuba in ban da k’addarar aure data kanainaye ni a gidan ka
Manubiya ta isa ta taka inda na taka ?
ballan tana har ta kalle ni ta fad’a min maganar banza?

Ahankali Ya Musbah ya lumshe idanuwan sa da sukayi jajawur kafin ya bud’e su ya zubawa Baraka yace
‘’Baraka saki hannun Manubiya ta wuce gida
zanyi mata magana.’’

Cikin gurb’atacciyar Hausa security d’in daya biyosu shima ya matso yace
‘’Madam ,cika mishi hannu ,ki bar fad’a ,ba ‘a hayaniya ,kalle patient fa ‘
Yayi maganar yana nuna inna wadda ta kafesu da Idanuwa

Ahankali Ya Musbah wanda ya keji kamar ya nutse a cikin k’asa ya d’an juya ya kalli Innar
kafin ya juya da d’an zafi yace
‘’Baraka ki sake ta ta wuce nace,ko?’’


Cikin tsananin tsiwa rashin kunya sannan da k’arfi tace
‘’Kaga rufe bakin ka,tunda ba za kayi adalci ba,
k’anwat ka ta zage ta zuba min rashin kunya sannan ko bin ba’asi ma baka yiba kace kawai in cika ta ta tafi ?
wato ban isa bama kenan ko ?
To Bari kaji
bayan cin kashin da kake yi min da azabtar dani da kake yi wallahi ban shirya sake d’aukar rashin kunyar k’annen ka ba sai ta bani hak’uri yanzu ba sai anjima ba sannan ka kora mata zazzafan warning in ba haka ba wallahi sai mun kwashi y’an kallo nida ita’’

Da mamaki Manubiya take kallon Baraka
ba abun da yafi bata mamaki irin yadda Barakar ta ke ihu bayan ga Inna a kwance sannan ta bi ta wani dage wai tayi mata rashin kunya
bayan ita Manubiyan ta bata wata biyu a duniya
yanzu haka ita ta cika shekaru ashirin da biyu
ita kuma Baraka sai watan gobe….

Security ya yunk’uro kenan zai yi magana
Maman Abbakar ta mik’e tace ma sa
‘’Yi hak’uri jeka,za suyi shiru bara inyi musu magana’’

Ba dan yaso ba ya juya ya fita dan ya k’ule sosai da Baraka.

Yana fita Baba yana shigowa rik’e da hannun takwaran sa Muhsin na biye a bayan su,
dama tun kafin ya k’arasa ya ke jiyo hayaniya gashi kuma ya tadda su cirko cirko
dan haka ya hau tambayar su ko lafiya

Maman Abbakar ce tace
‘’Tou Baba Musa,kasan dai Manu da baki da rashin kunya
to inaga yau abun nata ya biyo ta kan yayar tata ne
dan gashi har janyo ta tayi ta kawo k’ara shi kuma Musbah ya ma k’i ya bari ayi maganar sai cewa yake yi Manubiya ta wuce ta tafi kawai zai mata magana’’.

Ahankali Baba ya shiga karanto sunayen Allah a cikin zuciyar sa.

Tsit haka d’akin ya d’auka

Sai da Baba yaji ya d’an dedeta tukunna
Yace
‘’Musbahu yace Manubiya ta tafi za suyi magana saboda nan d’in d’akin mai jinya ne wadda take fama da kumburin zuciya hawan jini k’oda da kuma mutuwar b’arin jiki,
Ina fatan kun fahimci dalilin daya sanya baya so a yi wata rigimar a gaban idanun ta kar kuyi masa mummunar fahimta
ba wai son kai yake shirin gwadawa ba ….’’
Ahankali
Ya juya ya kalli Baraka yace
‘’Me kike so Manubiya tayi miki yanzu?’’


Ahankali ta sunkuyar da kanta ta cika hannun Manubiya tukunna tace
‘’Baba ta bani hak’uri, karta sake kuma’’

‘’InshaaAllah ‘’Baban yace
Sannan ya juya ga Manubiya har
Idanuwan sa sunyi jajir suna kyalli tsabar bacin rai
zai yi magana da sauri y tace
‘’Kiyi hak’uri sharrin zuciya ne
ba zan sake ba inshaaAllah’’

Ajiyar zuciya maman Baraka ta sauk’e sannan ta mik’e
Baba kawai ta cewa
‘’Allah ya k’ara sauk’i’’ daganan ta taho kamar zata bangaje Manubiya
ganin haka yasa tayi sauri ta matsa
Itakuma ta bud’e k’ofar ta wuce.
Baraka ma hannun Baba k’arami kawai ta kama suka fita bata cewa kowa uffan ba.
Maman Abbakar ce ta d’an tsaya tayi musu sallama daga nan tasaka kai ta fice
Jidda da Baba suna masu ce mata sun gode.

Ahankali Baba ya ga wasu hawaye suna tsilalalowa Inna ta ido d’aya

da sauri ya k’arasa ya sunkuya dai dai fuskar ta ya shiga share mata hawayen nata yana girgiza mata kai alamun tayi shiru,
Sun jima a haka kafin
ba tare daya juyo ba
Yace
‘’Manubiya ki kwashi duk Kayan ki da suke anan
Ki wuce gida.’’

Fashewa tayi da kuka
Cikin kukan tace
‘’Baba dan Allah kayi hak’uri
wallahi banyi tunanin Baraka zata yi haka ba’’

Still bai d’ago ya kalle ta ba
Yace
‘’Ni kuma banyi tunanin har yanzu bakiyi hankali ba,ban yi tunanin har yanzu ba zaki iya barin abu d’an k’ank’ani ya wuce ba tare da kinyi magana ba’’

Cikin fushi Ya musbah yace
‘’Ko ma mai ki ka ji tsakani na ne nida ita
Dan meyasa zaki shiga har kiyi magana ?

Ahankali Tana kuka tace
‘’kuyi hak’uri’’

Ya d’an jima yana kallon ta kafin yace
‘’Ki kwashe Kayan ki ki wuce gida kije ki fara karatu
Jidda xata ci gaba da xama anan,
Ke kuma kya dinga yin girki daga gida.’’

Zata yi magana
Yace
‘’Manubiya kije a ka ce ko ?’’

Ahankali ta d’aga kanta ta k’arasa taje ta shiga had’a kayan ta,har ta gama bata yadda ta d’ago sun had’a ido da Inna ba
Dan ta san ita take kallo
sai da ta zo tafiya tukunna taje ta rungeme ta tace’’Inna Allah ya baki lafiya’’
Still bata yarda ta kalle ta ba.
Daganan ta yi wa su Jidda sallama Baba ya bata kudi’n mota ta sa kai ta fita,
Ya musbah ji yake kamar ya fashe da kuka tabbas Baraka ta kai sa bango k’iri k’iri duba yadda ta disga sa ta wulak’anta sa a gaban jama’a harda wani cewa k’addarar aure,babban takaicin sa shine in ya d’au mataki yanzu yasan sai ya had’u da fushin Baba saboda cewa zaiyi dan mai yasa zai biye mata a case d’in daya had’a da su Manubiya dan yasan cewa za ayi ya bi bayan k’anwar sa sam baza’a duba rashin d’a ‘a da furucin data yi a gaban iyayen sa ba……….



Chan yamma
Jidda na zaune ita kad’ai gashi

Please Login or Register in order to submit comment