Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kigani Yash aure zai yi aure yake shirin yi nan da one month for that mattter amman kaff d’inmu nan babu wanda ya gayawa ko kyallin zancen babu wanda ya tab’a ji tsabar yadda kanmu da nashi yake ba’a had’e ba.Wannan shegiyar Yahanasun ita kad’ai ce ta sani,ita kad’ai ya gayamawa,ashe tun farko ta san da yarinyar amman tayi mana shiru..’’

Cikin fushi Yasmeen tace
‘’Ai ita take cin dunduniyar mu dama,ku gayamin dalilin da zai hanani cin uwar matar nan yau a cikin gidan nan!’’
Ta fad’i haka tana shirin fita da niyyar zuwa ta sami Yahanasun.

Dasauri Baba Larai ta sha gabanta ta rik’eta kafin tace
‘’Ba zaki tab’a Yahanasu ba,ba zaki ce mata komai ba’’

Cikin fushi Ya’isha tace
‘’Haba Baaaba!ya zaki ce haka???yanzu inda ace ta gaya mana tun farko ai da munsan abun yi da ba’a kawo ga haka ba,amma yanzu kalli abunda b’oyewar da tayi ya janyo,saboda Allah idan mu bata shiri da mu ai ko ke ko
Mommy ya kamata ace ta gayamawa tunda nasan tasan definitely ba’a san da zancen ba.Har ga Allah Yahanasu ta fara wuce limits d’inta those days,ranar nan fa data gaggaya mana magana
ranar da akayi case d’in senator
da Yassira taje d’akinta in kinga yadda tayi zakisha mamaki,Yasira tana fad’a atake tana mayar mata k’arshema toilet ta shige ta banko mana k’ofa.
Kwata Kwata bata shakkar uban kowa a cikin mu amma dukda haka kuna gani kun yi shiru sannan da ance za a gyara mata zama sai ku hana….yanzu kalli abunda saken da kukayi ya janyo’’


Ahankali Mommy wadda zuwa yanzu tama daina gani sosai tsabar b’acin rai tace’’Ya’isha so kuke ku kasheni?akace ku bari tukunna yanzu a san abun yi in ba hakaba wallahi zan tura ku d’akin ku kamar Yusra da Yadira tunda kuma yaran ne,
Ku tsaye ga matsalar daya kamata ayi magana akai nan amman kun tsaya kuna shirme?’’
Mommy ta k’arashe maganar tata cikin d’an d’aga murya da tsananin b’acin rai.


Komawa Yasmeen tayi ta zauna haka ma Ya’isha ammafa dukda haka a kumbure suke kamar zasu fashe..

Shiruu d’akin ya d’auka kowa ya shiga tunani,’’To kenan Daddy shima ya sani amma ya b’oye mata ko dai ya abun yake ne???Mommy tayiwa kanta tambayar ba tare da ta san wa zai bata amsa ba,a take wata zuciyar tace mata’’da wuya in ya sani kuma ko da ace bai sani d’in ba tasan wuyarta Yashjub yace masa yana son aure ko acikin sati d’aya ne ba abunda ya shafesa tsaf zai d’aurawa Yash aure,muddin hajiya mama ta amince kuma anyi bincike’’,dan haka tasan yanzu Baba ce kad’ai zata iya taimakon su dan haka ta d’ago da niyyar yi mata magana kenan idanuwanta suka sauk’a akan Kausar wadda ta turo k’ofar d’akin yanzunnan.

Lumshe ido Mommy tayi ta bud’e saboda yadda taga hawaye shab’e shab’e a fuskar kausar d’in tasan ta riga ta gama jin komai.

Ahankali ta d’an matsa kusa da ita da niyyar yi mata magana amma sai Kausar d’in ta yi saurin d’aga mata hannu alamun’ stop! ‘Kafin ta juya da
sauri ta ta bar wajen.

Da sauri su Ya’ isha suka bita
da hanzari su Mommy ma suka rufa musu baya duk suka d’unguma side d’in Kausar d’in inda suka ga ta shige.
Suna zuwa suka tarar har ta shige ta turo k’ofar bedroom d’in ta dan haka suka tura cikin ikon Allah bata rufe ba suna shiga suka tarar da ita ta fasa kwalba tana k’ok’arin yanka jijiyan wrist d’in ta.


Dasauri sannan a tsorace suka je suka rirrik’eta Mommy Tana cewa ‘’haba Kausar bafa auren aka ce miki an riga an d’aura ba’’
Inaa!ko jin ta Kausar bata yi ba
in banda kuka da hauka ba abunda take musu
Dan haka Mommy ta juyo da ita ta wanka mata wani gigitaccen mari.

Wani sabon kuka Kausar d’in ta sake fashewa dashi kafin ta fad’a jikin Mommy ta rungume ta tana wani irin kuka kamar zata shid’e tace
‘’Mommy kawai ki barni in mutu,all my life I’ve been unlucky Ammi na ta rasu
Mahaifina bana jin ma ya san da ni, Daddy shima ya tsaneni,
tare muka fara karatu da su Yassira duk sun gama sun kama aiki
amman ni har yanzu Ina project.
Dan Allah ku barni in mutu
In na zauna Yash ya rayu da wata a matsayin mata mutuwa zanyi Mommy,gara kawai in mutu….


Ahankali Mommy ta rungumo ta jikinta sannan tace’’Nayi miki alk’awari,Yashjub ba zai auri kowa ba sai ke,

Cikin katseta tace
‘’Mommy haka kike cewa kullum gashi yanzu har yayi budurwa yana shirin aurenta bama mu sani ba’’

Ahankali Mommy ta d’ago da fuskarta tayi cupping a cikin tafin hannun ta kafin tace mata‘’do you trust me???’’
Mommy tayi mata tambayar tana kallonta

Ahankali kausar wadda duk ta yi giving up ta jin jina mata kai alamun’yes’
Idanuwanta shab’e shab’e da hawaye,har ga Allah ta karaya da yadda taji maganar ta taho gadan gadan dan tasan tunda akace in one month time to hatta su Hajiya mama sun sani kuma sun amince ta riga tasan duk bala’i ba’a isa a chanja wa hajiya mama ra’syi ba ,shiyasa kawai ta zab’i ta mutu amma hope d’in da Mommy ta bata yanzun ya d’an bata kwarin guiwa kuma dama it’s her easiest option dan haka ta zab’i d’aura gaba d’aya trust da hope d’inta akan Mommy.

Sai da Mommy ta sauk’e ajiyar zuciya tukunna taci gaba da cewa’’ki kwantar da hankalinki
babu wadda ta Isa ta shigo cikin gidan nan a matsayin matarsa,ki zuba ido ki ga ikon Allah’’


Ya’isha ce tace
‘’Mommy me za a iya yi a cikin sati uku zuwa wata d’aya?maybe ma an riga an kai komai

Ba dai ni nace muku ku zubamin ido ba?….dan haka bana so in sake jin wata magana concerning maganar auren Yash a cikin gidan nan’’
Sai da ta sake sauk’e ajiyar zuciya tukunna tace’’zanga ta yadda zai yi auren,zanga ta yadda zai aureta.’’

Ahankali ta kamo fuskar Kausar tace’’alfarma d’aya nake so daga gareki…ki kwantar da hankalinki ki cire komai aranki,kar ki damu in dai kinada ‘Ni’ na dad’e da yi miki alk’awarin baza kiyi kuka ba………..




Washegari da sassafe Manubiya ta tashi ta shirya tsaf dan tun a jiyan Ya Musbah yace mata’’ta shirya da wuri zasuje su dawo saboda Ya Nafi’u yana da interview by ten‘’shiyasa take ta sauri ta shirya sai dai bata ko fara karyawa ba sai gashi sun shigo shi da mai sunan baba.

Bayan an gama gaggaisawa ne
Manubiya ta sanar dasu yadda sukayi da Yash d’in da kuma yadda yace yau doctor zatazo ta duba inna.
Shiruu Baba yayi da jin bayanin ta kafin chan ya nisa yace’’Manubiya daga wannan karki sake gaya masa wata damuwar ki d’awainiyar tayi yawa haka’’

Ahankali ta sunkuyar da kanta tace ‘’to Baba,’’ dan dama ta san za’a rina har ga Allah ita ta mayi tunanin zai yi mata fad’a in ya ji.

Shiruu kawai Baba yayi yana wani lissafin na daban kafin ya sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya tukunna ya mik’e da kyar dan ciwo k’afar takeyi masa,inda aka cire farcen ya kumbura ya sake taso masa da ciwon k’afar sa dayake ta fama da shi dama,dauriya kawai yakeyi amma azaba yake sha dan hatta farcen hannun sa da suka cire shima ciwo yake masa.Ahankali ya d’ingisa ya nufi toilet domin ya watsa ruwa dan tun d’azu Manubiya ta kai masa ruwan wanka.


Yana shiga Jidda ta shigo musu da breakfast dan haka suka zauna su uku suna ci har da mai sunan baba wanda ya Musbah yaketa tsokanar sa da acici dan sai da suka ci wainsr gero tukunna suka fito.

Inna ma tun d’azu an bata nata an shirya ta.

Ganin sun kusan kammala wa ne yasa ya Musbah mik’ewa ya fita dan ya duba ko Nafi’u ya zo in bai zo ba ya kira sa


Sai da Muhsin ya mik’e ya fita tukunna Jidda ta kalli Manu tace’’na d’auka Muhsin zai yi fushi ko kuka da aka ce an fasa kaishi makaranta,ashe ya girma yayi hankali yanzu’’

Murmushi Manu tayi kafin tace
‘’Ya ban tausayi,Allah ubangiji ya bamu ikon sanya shi a makarantar’’

‘’Ameen’’ jidda tace daganan ta zare hannun ta a abincin ta d’an matsa kusa da Manubiya sosai sannan tace’’yanzu ya za’ayi?zaki siya mishi ne a hanya tukunna ku wuce office d’in nasa?dan bai kamata ku had’u ba ba tare da kin bashi d’an gift ba’’

‘’Ba gift d’in da zan basa’’
Manu ta fad’a hakan ba tare da ta kalleta ba.

Da sauri Jiddah ta d’an zabura sai kuma tace’’amma wasa kikeyi ko?’’

Sai a sannan Manu ta d’ago kyawawan idanuwanta ta kalleta tukunna tace
‘’Dagaske nakeyi,ya riga ya fara rok’on tukuici da kanshi,kinga kuwa ai yayi wa kansa’’

Dariya Jidda tayi kafin tace ‘’kamar yaya?’’

…… yadda suka yi dashi jiya ta kwashe tsaf ta gaya wa jidda…
Kafin ta d’aura da cewa’’tun d’azu nake ta faman fargaba
bansan me zai ce yana so ba,na riga na yi trusting d’in
shi na san ba zai cutar dani ba
amma kawai I’m so nervous’’
Ta k’arashe maganar tata tana mai mayar da idanunta kan jellof d’in taliyar dake a gaban su.

Shiruuu Jidda tayi ta zuba mata ido,har sai da Manubiyan ta gaji dan kanta ta d’ago ta kalleta
Tukunna Jidda tayi murmushi
tace’’kema kina son shi ko??’’

Wata mahaukaciyar zabura Manu tayi a lokaci d’aya ta yi amfani da d’ayan hannunta na hagu ta toshema Jidda baki ta fara rarraba ido a cikin d’akin.
Dai dai nan Baba ya fito daga toilet d’in sanye da kayan daya chanja a ciki wanda ya cire kuma a hannunshi rik’e da brush da vaseline d’in shi,


Kallonsu yayi kafin yace’’d’azu kaka mallan ya kira yana buk’atar ganin mu ni da su uncle da gaggawa,idan likitar tazo
kuyi komai in kunga ban dawo ba sai ku wuce kawai ba sai kun jira ni ba’’

Daga haka ya ajjiye kayan wankin a wajen da suke tarawa ya ajjiye brush da Vaseline d’in sannan ya wuce yana mai cewa’’idan na dawo na ci nawa abincin’’..


Yana fita Jidda tace’’yanzu ya za’a….’’

Cikin katseta Manubiya tace’’Jidda dan Allah karkiyi min haka,karki sake rikitani’’

Dariya Jidda tayi kafin tace ‘’ki tsaya tou kiji abunda zan fad’a ma mana’’

Kamar Manubiya zata fashe da kuka tace’’Plss Jidda….’’
Daganan ta mik’e ta fad’a toilet ta kuskure bakinta ta d’auro alwallah ta fito

Tana fitowa wayarta ta d’auki k’ara .
Tana dubawa taga Yash ne
batayi mamaki ba dan itama tunanin sa takeyi dan haka ta d’auka a hankali ta kara a kunnenta….
…bayan kashe mata jiki da doguwar gaisuwa yace
mata’’Dr Sofia fa tana waje tazo tun d’azu’’

‘’Ok’’tace suka yi sllama daga haka ta nufi k’ofa da niyyar fita ta shigo da ita amman sai suka yi karo da ya Musbah da ya Nafi’u dan haka ta gaya musu ita kuma ta koma ciki.

Su ne suka je suka shigo da baturiyar likitar mai suna Sofia
matar mai kirki sosai da bagwariyar Hausar ta…sama
da awa d’aya ta d’auka tana examining inna kafin tace’’su wuce asibitin ta’’

A inda ta gaya musu asibitin nata yake ya baud’e sosai da office d’in Yashjub
gashi sun riga sun ce masa zasuzo,kuma shi kansa ya Nafi’u ya kamata ace yana wajen interview by now…shiyasa suka yanke akan
Ya Nafi’u ya tafi interview d’inshi
Manubiya taje tayiwa Yashjub godiya on their behalf sannan ta gaya ma sa dalilin daya sanya basuzo su duka ba,
Ya Musbah kuma ya tafi asibiti tare da inna.



MANNUBIYA
45
Na
Humayrah Bulama

Mikiya Writers Association.

A inda ta gaya musu asibitin nata yake ya baud’e sosai da office d’in Yashjub
gashi sun riga sun ce masa zasuzo,kuma shi kansa ya Nafi’u ya kamata ace yana wajen interview by now…shiyasa suka yanke akan
Ya Nafi’u ya tafi interview d’inshi
Manubiya taje tayiwa Yashjub godiya on their behalf sannan ta gaya ma sa dalilin daya sanya basuzo su duka ba,
Ya Musbah kuma ya tafi asibiti tare da inna.

Babu kalar lallamin da Manubiya batayiwa Jidda akan ‘tazo suje tare’ ba,amma k’iri k’iri Jidda tace ‘’A’a!,idan na bi ki wa zai kula da su mai sunan baba da Muhsin?’’

Da sauri Manubiya tace
‘’To duk ku zo mu tafi tare’’

Cikin tarar numfashinta Jidda tace ‘’kuma in Baba ya dawo sai yaga ba kowa?’’

Haka suka yi ta fama,dan duk ta inda ta b’ullo sai Jidda ta toshe.
Ya Musbah ma bayan Jidda yabi yace’’ko baya ga hakama Taya ancewa Yashjub d’in zasuzo su uku yanzu kuma kawai yaga yara
Kawai taje d’in in yaso tace masa inshaaAllah shima shi da ya Nafi’u suna nan zuwa’’.


Hakanan Manubiya ta fita ko sallama bata yiwa Jidda ba
Jiddan tanata tsokanarta
k’asa k’asa
Da
‘‘Oga wife’’

Ita dai Manubiya bata kulata ba,ta barta kawai akan sai ta dawo sai suyi ta.

Har ta Isa company d’in kuwa tana fargaba!,bata san
tukuicin da zai ce yana so ba
sannan ga abunda Jidda ta riga ta gama concluding
da kuma abunda ita kanta zuciyarta take raya mata
shiyasa gaba d’ayanta tabi ta sake diriricewa.

Yau tana zuwa receptionist d’in yace mata ‘’ an ce in tazo kawai ta wuce office d’in ceo ba sai an rakata ba’’
‘’Okay’’ kawai tace
daga nan ta nufi office d’in nashi dake a chan sama kai tsaye.

A bakin glass door d’in
ta tsaya ta d’an yi knocking glass d’in tukunna ta tura ta shiga da sallama.

A zaune ta sameshi ya k’urawa k’ofar ido…fuskarsa tamau kamar bai tab’a dariya ba dan har sai da ya d’an bata tsoro amman kawai sai ta dake ta k’arasa ta nemi waje ta zauna,a hankali tace’’ ina kwana’’.

Tunda yake a rayuwar sa bai tab’a ganinta da mayafi ba sai yau,mayafin ma kuma mai shara shara….sanye take da doguwar riga d’inkin Ashape,atamfar army green da d’an kwalliyar milk da black,rigar bata wani kamata ba
amma yanayin jikinta da kuma mayafin data rufa (black clour)wanda bata saba sakawa ba ne
ya taimaka wajen fito da surar jikinnata,mayafin nata babba ne sai dai ya d’anyi shara shara.Ta yi normal d’aurin d’ankwalinta ta gaba ta baya kuma ta nannad’e sa akan ribbon d’inta wanda ta tufke uban tulin gashinta dashi ta d’aura mayafin nata akai.
Kwalli powder sai man leb’e ne kawai a fuskarta
amman ba k’aramin kyau ta yi ba
Dan har wani fisfisga Yash yaji numfashinsa yanayi
‘‘Yanzu duk inda ta bi ta wuce tun daga gidansu har nan haka maza suka ganta kuma suma haka suka dinga ji kenan?
bata tab’a saka mayafi ba sai yanzu da ya ke jin masifaffen kishin ta’’Yashjub ya aiyyana hakan a cikin ransa.

A b’angaren Manubiya kuwa ita kanta tun d’azu a takure take dan ba wani sabawa tayi da mayafin ba,ta yi mistake ta bar hijabanta duk sunyi datti kuma bata samu sunyi wanki da wuri wannan satin ita da Jidda ba sannan ga abunda yazo ya faru gaba d’aya ya d’auke musu hankali shiyasa basu nutsu ba ma ballantana ayi maganar yin wanki.

Ahankali ta d’an kalleshi taga still ita yake kallo dan haka ta sake yin k’asa da kanta tace’’ina kwana’’

Ahankali ya lumshe lumsassun idanuwansa ya had’iye wani k’ululun abun daya tokare mak’oshinsa yake shirin hanasa numfashi
tukunna yace
‘’Me ya faru da hijaban ki yau?’’
Yayi mata tambayar yana mai matsar da computer dake a gabanshi gefe wanda hakan
ya bashi damar sakata a gaba ya tsura mata ido sosai.

Gaba d’aya diriricewa Manubiya tayi sam ta kasa
magana
dan haka kawai sai ta sake yin k’asa da kanta…zuwa yanzu ta fahimci maybe mayafin da ta rufo ne ya b’ata masa rai shiyasa duk sai taji ba dad’i dan sam bataso ta zama silar b’acin ransa.Ga kuma tunanin ta na ‘maybe kishina yakeyi’
gaba d’aya sai ya sake kashe mata jiki.


Yanayin yadda tayi ‘k’asa da kai tayi shiru’ ne yasa yayi tunanin maybe ranta ya d’an
b’aci ne ga kuma yadda ya tamke fuska ko welcoming nata bai yiba wanda shi kanshi sai yanzu ya lura da hakan,shiyasa tashi d’aya shima duk sai yaji ba dad’i dan haka ya sauk’e wata y’ar siririyar ajiyar zuciya kafin ahankali ya lumshe idanunsa ya bud’e tukunna yace’’Sorry!’’
kawai.


Duk shiruu sukayi kafin ya sake cewa
‘’Ya jikin Baba ??’’

Ba tare da ta d’ago fuskarta ba sannan ahankali tace’’Alhamdulillah’’

Murmushi yayi kafin yace
‘’Fushi kikayi?’’

Girgiza kai tayi batasan ya akayi ba amman kawai sai ta tsinci kanta da cemasa
‘’’sorry!’’itama.


Murmushi mai sauti yayi kafin yad’an had’e rai yace
‘’Kar ki damu next time in kika sake saka wannan abun ni kad’ai nasan me zanyi miki’’
Ya k’arashe maganar yana dariya ahankali ahankali.

Bata san lokacin da murmushi ya sub’uce mata ba itama kafin ahankali ta fara magana’’Sofia tazo,tun ayau kawai har ta k’ara mana haske akan yanda zamu dinga yiwa inna, naji tace kullum itama zata dinga zuwa ko?’’

‘’Um’’kawai yace
Idanun sa akanta

Ahankali taci gaba da cewa’’ ban samu nayi maka godiya sosai ba
da tare zamu taho da su ya Musbah tou dole sai da shi tukunna za’a kai Inna asibiti shiyasa yace in baka hak’uri ince suma suna nan zuwa kuma mun gode sosai
Baba!Jidda!da Muhsin suma duk sunce ayi maka godiya
Allah ya saka maka da alkhairi’’

Murmushi yayi kafin yace’’Allah ya k’arawa su inna lafiya, bana buk’atar godiya daga gareki ko Ahalinki
Pls kicewa su Musbah suma ba sai sun zo ba…’’

Ahankali tace’’a ganina ya zama dole mu yi maka godiya’’

Jin yayi shiru yanata kallonta ne kawai yasa tace’’once again mun gode,Allah ya biyaka,’’kamar bazata yi magana ba sai kuma tace’’zan tafi’’ta fad’i hakan tana mai sunkuyar da kanta k’asa sosai.So takeyi kawai ta tafi tunda ta gama abun da ya kawota maganar aikin daya ce akwai yau dama tasan kawai jan magana ne.

Ahankali ya sauk’e nannauyar ajiyar zuciya sai kuma ya sunkuyar da kanshi yana murmushi
kafin ya d’ago yace’’nima,a ganina ya zame min dole inyi protecting abun da nake tsananin k’auna.’’


‘’Innalillahi wa inna ilaihirrajiun’’
Haka Manubiya wadda ta runtse idanuwanta tashi d’aya ta shiga nanatawa a cikin zuciyar ta tana mai jin wani kalar fad’uwar gaban da bata tab’a ji ba tunda take a rayuwarta,atake gaba d’aya ilahirin jikinta yayi wani irin sanyi,kamar babu jini ko
rai a k’afafuwanta haka taji
dan tabbas inda ace za a tsikara mata allura tou ba lalle taji ba!infact she can’t even feel her whole body.
Dakyar ta samu ta dawo daidai ta d’an fara jin jinin jikinta yana circulating sai kuma ta d’an fara kyarma
ahankali ahankali.


Ganin yadda ta runtse idanunta ta k’ame a waje d’aya ne
yasanya Yashjub ya furzar da wata nannauyar ajiyar zuciya kafin ya tashi ya koma inda take ya zauna a kujerar dake gefenta.
Yadda ta zabura saida ta kusan bashi dariya…Kamar zata fashe da kuka haka ta juyo ba tare data yarda sun had’a ido ba tace’’Dan Allah ka daina,banaso.’’

‘’Bakya so ince miki Ina sonki?
K’arya kike so inyi miki?
Ko so kikeyi inci gaba da azabtar da zuciyata ta hanyar hanata muradin ta??’’


Mik’ewa Manubiya tayi da wani kalar sauri ta juya zata fita amma kafin ma tayi taku d’aya kawai sai taji ya damk’o hannunta!.


Da sauri ta juyo saidai kafin ma tace wani abun tuni taji hawaye ya b’alle mata.

Ahankali Yashjub ya sauk’e wata nannuyar ajiyar zuciya kafin ya lumshe idanuwansa ya bud’e tukunna ahankali ya mik’e tsayen shima still yana rik’e da hannunnata wanda
yake jinsa kamar kar ya cika kmr ya rik’e har abada kar ya barta taje ko ina ga wani taushi da d’umi wanda atake suka taru suka d’imauta sa.

Dakyar ya iya cewa’’ki yi
hak’uri Mannubiya in abunda na gaya miki ya b’ata miki rai ne kiyi hak’uri
Dan Allah
banason ganin hawayenki bakisan yadda nakeji a cikin raina ba pls ki daina kukan nan….burina in sanya ki farin ciki in kula dake a koda yaushe
ba zan so in zama silar zubar hawayenki ba,kar ki sa in kasa yafewa kaina pls.A ganina ba laifi bane in na gaya miki sirrin zuciyata shiyasa tun jiya nace miki alfarma da kuma tukuici,nasan dama ba lalle kema kina jin abunda nake ji ba amma in har kikayi min wannan alfarmar kika bani wannan damar kika amince da ni kika bani damar kasancewa tare da ke har abada
Mannubiya
kin gama min komai.
Tun ba yau ba a matse nake inaso in faiyyace miki sirrin raina inaso kuma inji naki
Inaso inji abunda yake cikin zuciyarki kema gameda ni amman tabbas a yanzu inajin tsoro saboda hawayen nan naki dana gani is not a good sign!dan haka in dai kinsan amsar ki ‘No’ zata kasance na rok’e ki da girman Allah kar ma ki ce komai,ki je ki sake tunani
dan tabbas nasan zan iya rasa raina in kika ce min
A’A …..’’.


Bata ce dashi komai ba,bata ma da niyyar cewa komai,kukanta kawai takeyi tana d’an k’ok’arin kwace hannunta a cikin nasa.
Ahankali ya lumshe idanunsa yana mai sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya kafin ya bud’e ya d’an sunkuyar da kanshi k’asa..ba abunda ya tsana a ynzu irin kukan nan da takeyi sam ko da wasa baya son ganin hawayenta…shiyasa ya bud’e idanunsa ya d’an runtse hannunta dayake a cikin nashi sannan a hankali ya sake matsowa kusa da ita,ya d’aga d’ayan free hand d’in nasa ya kai dai dai setin fuskarta.

Tabbas ta fahimci so yake ya goge mata hawaye dan haka cikin kuka wanda yake d’auke da b’acin rai tace’’iyakar hannuna da ka rik’e bai ishe ka ba??’’

‘’Oh no’’Yashjub ya fad’i hakan a fili dan shi wallahi sai yanzu ya fahimta ya kuma fara ganewa,shifa Indai yana gabanta to mantawa yake yi da kowa da komai
Har ga Allah bai san lokacin da ya damk’i hannun nata ba da kuma ya rik’e d’in sam sai ya gagara saki.

Damn it! Ya fad’a a chan kasan ranshi yanajin takaicin kanshi
dan tabbas ya san ya kwasa.

Da ikon Allah kuma gashi har yanzu ya gagara sakar mata hannun nata har.


Da k’arfi Yassira ta daki glass d’in k’ofar wanda yake nuni da alamun knocking

a tare gaba d’ayan su suka d’aga kai suna kallon k’ofar shigowar.

Sunyi mamakin ganin Kausar da Yassira a tsaye a cikin office d’in dan basu san lokacin da suka k’araso ba ballantana su san lokacin da suka shigo.

Da sauri Manubiya ta juya ta goge hawayenta daganana bata sake yarda ta juyo ba.

Cika mata hannu Yashjub yayi sannan ya janye d’ayan hannunshi daya d’aga da niyyar goge mata hawaye tukunna ya d’an matsa kusa da su ya kalli Yassira fuskarshi ba yabo ba fallasa
Yace
‘‘Lafiya dai ko?’’

Dakyar Yassira ta samu ta iya cewa ‘’yeah!lafiya,we come to
to you ne,sai kuma naga kamar you are busy!’’

‘’Yep!very busy..’’
Ya bata amsar kansa tsaye,kafin yace
‘’Ki jira in mun had’u a gida sai muyi’’
Ya k’arashe maganar tasa cikin takaici dan sam bai so sukaga Manubiya yanzu ba.
Daga haka ya fara k’ok’arin juyawa yaji tace
‘’Akan Mommy ne fa,ba zai yiu muyi a cikin gidan ba dama shiyasa muka biyo ka nan’’

This time around had’e fuska Yashjub yayi tamau kafin yace’’Yassira i’m busy,ki jrani ko menene in na dawo gida sai in ji ko?!.Thankyou’’


Shiruu Yasirar tayi kafin
daga baya ta d’an k’ak’alo murmushi a hankali tace
‘‘Okay Yash’’


Jinjina kai yayi still fuskarshi a had’e yace
‘’Good bye’’ har ga Allah
Allah Allah kawai yakeyi suyi su fita saboda gaba d’aya Kausar!da shigarta!da kwalliyarta!juya mishi kai takeyi.

Sai da Yassira ta sake kallon Manubiya wadda ta juya baya tun shigowarsu tukunna ta kamo hannun Kausar wadda tunda suka shigo ta yi ido biyu da Manubiya ta sunkuyar da kanta k’asa ta k’i cewa komai.
Ahankali Yasira tace mata
‘’Let’s go!’’
Ganin da tayi kmr ma Kausar d’in batajin abunda take ce mata ne yasanya kawai ta ja
hannun ta suka fice daga office d’in


Suna fita Yash ya zagaya ya d’auki wayarshi ya turawa Yassira massage
…’The next time kika sake zuwamin da ita office
I’m going to humiliate the two of you like hell….’




MANNUBIYA
46
Na
Humayrah Bulama

Mikiya Writers Association.

Yana gama turawa Yassira message yaga
Manubiya ta sak’ala jakarta tana shirin juyawa

Please Login or Register in order to submit comment