Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sama da million biyu
ta yaya za ka ciyar da iyalinka?
kuma na san in baka kawo wa gida kamar yadda Daddy ya tsara ba
to kuwa ka had’u da tijarar sa kenan.
Abun da Mommy take so shine
ta samu ta san yadda zata yi ta janyo hankalin Daddy a samu ya k’ara maka wani abun ko da a share d’in Mama da na sa dana Yashjub ne ayi maka karo karo kaima kayi sama..an d’an fara samun nasara to kuma tunda wannan matar Saddik’a ta shigo rayuwar Daddy shine komai ya tab’arb’are
We need to get her out
mu gyara tsakanin Mommy da Daddy a k’ara mata share ka tsaya da k’afafunka kaima tukunna ayi maganar aure Yassir.
A yanzu balance d’in ka na duk shekara da Daddy yace yana tara wa kowa na sa
In aka tashi baka na shekara ukun da suka wuce ba a baku ba
dai dai kake kai dasu Yasira
a matsayinka na d’a Namiji,
Daddy ya tartara komai ya damk’awa Yashjub wanda ba shi da wata kyakkyawar alak’a da d’aya daga cikin mu
hatta Mommy ,
Iyaka Daddy ne kawai ya san cikin sa kuma yake d’an shiri da shi
Kaga kuwa duk ranar da aka ce ya yi aure to komai hannun matar sa zai koma
Mu sai dai mu zama y’an kallo a gefe..Daddy can take care of himself daga nan har tsufan sa yanada kud’in da zai temaki kan sa da Mommy
Kai fa ?
kai da su Yasira
Allah ya rufa asiri
In ba ayi wani abun ba sai dai mu zama a gefe y’an kallo,
Gaba d’aya arzik’in gidan nan ya koma hannun shi shi kad’ai daga shi sai matar sa
tun da tun yanzu ba kulamu yake yi ba
Amman in kuka zma equal kai da shi ko ma ace ka fi sa to
tanan ne kad’ai komai zai tafi normal,tun da munsan kai zaka kula da su Yasira da ita kanta
Mommy sannan ni za ka aura ba wata stranger ba so arzik’in mu yana nan a wajen mu.

Ba abun da yafi d’aga wa Mommy hankali irin yadda
ya yi maka duka ranar nan
ka kasa ramawa saboda baka da power shiyasa take so ku zama equal
bata so wani ya taka wani
kuma tanajin tsoron kar ayi ta zalintar ka ka zo ka ce zaka rama ta hanyar da bata kamata ba…

Wannan itace gaskiyar magana
Yassir we want to help you
amma sai ka bamu hadi’in kai
sannan pls kar ka bari Mommy ta san ka sani dan bata so kowa yaji
Saboda ba lalle a fahimceta ba za’a ga kamar tafi sonka ne akan Yashjub’’.


Hugging d’in ta Yassir yayi
a hankali yace
‘’Sorry Kausar na d’auki alhakinki kwanaki na yi tunanin gudu na kike yi ki yi hak’uri na fahimci komai yanzu.’’

Shiruu ya d’an yi kafin yace
‘’Amma tayaya Munirat zata taimaka wajen case d’in Ummi
da har kike ta k’ok’arin had’ani da ita shin bakya kishina??’’

Murmushi tayi sannan tace
Yassir Ina kishin ka,amma bana so in zama kamar Ina
controlling d’in ka,sannan na san no matter what ni d’in dai ni ce a cikin zuciyar ka,na riga na san halin ka bawai ban saniba..na san ko na yi haukar rabaka da ita a yanzu ba zan yi nasara ba
Inaso mu zama d’aya ni da kai
akan ka je ka yi abu a bayan idona gara kayi a gaban idona,
daga haka ni kuma in yi taking
advantage of the situation
Wannan yarinyar itace weakness d’in uwarta
In ka kafa mata k’ahon zuk’a
lokacin da uwarta zata hak’ura ta bar gidan nan da ita ma ba a sani ba
Bakaji a labarin Yahanasu ba
saboda senator ta bar garin nan ita da y’ar sai bayan
watanni suka dawo
Already yanzu itada Daddy sai dai kallo
We make sure of that
fitar ta a gidan ne matsala
All thanks to hajiya Mama wadda ta hana Daddy sakin ta
indai ba ita ta tafi da kanta ba

Ita ma kuma na lura in ba sakin nata aka yiba ba zata tafi ba
Shiyasa
Mukeso mu sakata ta bar gidan da k’afarta da ga nan
Daddy ya rakata da takardarta.’’

Wani zazzafan numfashi Yassir ya fesar kafin a hankali yace’’Na fahimci komai yanzu
daganan sake k’ank’ame
A ranshi yace
“” Thankyou Kausar
ke da Mommy
Ku saka Daddy ya k’ara min share
Ni kuma zan shiga cikin dukiyar Yashjub
In kwashi rabi
In tarwatsa rabi
In abun yazo da tangard’a in dagargaza komai kowa ma ya rasa
After that
zan dawo gareki
sai dai kawai ki ji ana d’aura mana aure
Saboda
duk da bayanin nan da kikayimin
I still don’t trust you
Inda ace da gaske kina sona
da zanga koda d’an guntun kishina ne a cikin idanun ki da actions d’in ki,
Allah dai kawai yasa ba deceiving d’ina kike yi ba
sannan ba ki da shirin shiga hanyata ki taremin abun da nakeson achieving…Of all people ke kad’ai ce banaso ki shiga hanyata
dan a shirye nake in bi takan duk wanda ya yi k’ok’arin tare min hanyar achieving abun da nake so in yi ….’’


Tunda Kausar take a rayuwar ta bata tab’a jin shakkar Yassir irin na yau ba,dan kamar yadda ya fad’a mata’wannan ba shine Yassir d’in data sani ba’
Idanuwanshi sun tabbatar mata da haka,shi yasa ta d’an tsorata da shi dan ta san in ya fahimci gaskiyar lamari to akwai matsala,dan ita har ga Allah baya gaban ta asalin gaskiya ma ita so take ta yi getting rid of him cikin sauk’i shiyasa ta zo suka shirya,akwai plan d’in maganganun data gaya masa ba wai babu ba kuma duk gaskiya ne amma ko su Mommyn kawai biye su take yi but ita a cikin zuciyar ta bata damu Yassir ya ji dad’i ko kar ya ji ba dan ba shine a gabanta ba,ita kwata kwata babu shi a cikin tsarin ta na asalin gaskiya ma,,
Plan d’in su itada su Yassira
su fitar da Ummi.
Plan d’in su ita da Mommy da baba larai kuma
su saka a bawa Yassir share mai yawa sannan
hatta Yash suna so ya janyo shi ya saka shi a cikin company d’in shi.
Ita kuma plan d’in ta shine ta yi wa
Yassir wayo gudun kar ya je ya yi mata wani shirmen, ta samu ya bata time da space
ta samu ta shiga jikin Yash shi kuma ta kwak’uma masa Munirat
daganan sai dai kawai yaga ana d’aura mata aure da Yash.

But yanzu kam dole ta chanja taku
ta san Yassir tun suna yara
In zuciyar sa ta motsa ba abun daba zai iya aikatawa ba
ya zama dole tayi betraying Baba larai da Mommy dan ba za ta tab’a bari
Yash ya ja Yassir a jiki ba
dan a yadda Yassir yake a zuciyen nan tsaf zai iya cutar da Yash ko dukiyar sa.
Kuma dole tayi sauri ta ko wachche hanya ta auri Yash
daga nan ta san yadda za ta yi ta kare kanta ita da Yash
daga sharrin Yassir.

Zuwa yanzu Ummi ba matsalar ta baceba
dama so take yi ta bak’antawa Daddy rai sannan ta hana sa jin dad’i sakamokon abubuwan da yake yi mata
Shiyasa ta had’a guiwa da su Yassira,kuma ta ci riba
tunda gashi baya samun farin ciki da soyayyar Ummin
kuma he’s not happy
Dan haka ta tsame hannunta
su je su yi ta fama dan tana da
abubuwan da sukafi case d’in Ummi barkatai a gabanta
Ita kad’ai ce on this
dan haka dole ta so kanta fiye da komai da kowa.


A hankali taji yanayin ruk’on da Yassir yayi mata yana sauyawa,wani k’ululun bak’in ciki ne ya tokare ta,da kyar
ta iya controlling kanta ta d’ago ta kalleshi tana murmushi tace
‘’I’m not going to spend the night with you
Da sunan wata a sak’ale a saman mu ‘’

Murmushi yayi
kafin yace’’sorry’’
daga haka ya cika ta yaje ya cire ballon d’in da suka had’a sunan Munirat ya jefar a k’asa ya dawo

Yana shirin rik’e ta tace
‘’Yassir a ganina bai kamata mu’’

‘’Shii’’yace a hankali kafin ya d’aura da cewa
‘’Come on!dont be a grandma mana,you know i miss u,ryt?…’’

Ba yadda ta iya dan bata so ya gano ta ko ya dasa question mark a kanta,hakanan tana ji tana gani ta hak’ura ta zuba masa idanu..



A b’angaren Yash kuwa yana chan bai ma san suna yi ba..damuwa da tunani sun saka shi a gaba dan za’a iya cewa yadda yaga rana haka yaga dare,saboda k’iri k’iri ya gagara yin bacci ganin haka ya sa ya tashi ya dinga jero nafila,tukunna ya d’an ji sanyi a ranshi,zuwa yanzu ya huce daga fushi da Najeeb dan haka ya sa a ransa inshaaAllah gobe suna fitowa daga meeting d’in su na sassafe da suke da .. da shi da su Daddy zai kira Najeeb ya san yadda zai yi da shi ya tambaya masa kwatancen k’auyen su Manubiya..yana wannan lissafin ya sake zaro waya bai damu da cikin dare bane haka ya yanke shawarar gwada sa’ar sa sai dai tun kafin ya kai ga kara wayar a kunnen sa yanzun ma ya ji an ce masa a kashe
kamar yadda tun d’azu da safe yake jin layin nata’a kashe.’


….washegari da safe….

A rikice Baba ya shigo cikin d’akin su,bai tadda kowa ba sai Inna dan Manubiya ta fita siyo sugar Muhsin ya je gidan Ya Musbah Jidda
kuma tana wanka

Yana shiga ya nufi wajen kayan sa ya hau dudduba wa,duk wasu ragowar kud’ad’en da yake da su haka ya kwaso ya tara su a gaban sa ya hau lissafi dai dai nan
Jidda ta fito daga wanka tana mai gyara zaman hijabin a fuskarta.

Ganin bai ma lura da ita bane yasa ta k’arasa kusa da shi ahankali tace’’Baba’’
Sai a sannan yayi firgigit ya mik’e sai kuma ya fara dube dube kmr yana neman wani abun,
Sai da ya tabbatar ba kowa tukunna yace
‘’Yauwa Jidda ki kira Manu
zan fita yanzu in kuka ga na kai awa uku ban dawo ba to ku d’auki innarku ku je wani gidan ku b’uya,in na samu na dawo zan yi muku bayanin komai
ku kira Musbahu kice shima su b’uya shi da Baraka….





MANNUBIYA
34

Na
Humayrah Bulama

Mikiya Writers Association.

Yana shiga ya nufi wajen kayan sa ya hau dudduba wa,duk wasu ragowar kud’ad’en da yake da su haka ya kwaso ya tara su a gaban sa ya hau lissafi dai dai nan
Jidda ta fito daga wanka tana mai gyara zaman hijabin a fuskarta

Ganin bai ma lura da ita bane yasa ta k’arasa kusa da shi ahankali tace’’Baba’’
Sai a sannan yayi firgigit ya mik’e sai kuma ya fara dube dube kmr yana neman wani abun,
Sai da ya tabbatar ba kowa tukunna yace
‘’Yauwa Jidda ki kira Manu

Zan fita yanzu in kuka ga na kai awa uku ban dawo ba to ku d’auki innarku ku je wani gidan ku b’uya,in na samu na dawo zan yi muku bayanin komai
ku kira Musbahu kice shima su b’uya shi da Baraka

Ba ni da ishashshen lokaci inshaaAllah in na samu na dawo zan yi muku bayani,ba
wani abun cutarwa ko zalinci na aikata ba..kuskure nayi amma da yarda Allah komai zai yi gyaru.

Yana gama fad’in
haka ya juya ya nufi k’ofa yana zuwa ya d’aga labulen d’akin ya fice,fitt!.

Da kyar Jiddah ta samu ta d’an dawo daidai tukunna ta juya ta bi bayan Baba da sassarfa tana mai cewa’’Baba,Baba,Babaa!’’a mugun firgice gaba d’aya jikin ta yana karkarwa.
Tana bud’e labulen suka yi karo da Ya Yusuf
Murmushi yayi mata kafin yace
‘’Sai mun dawo’’
daga haka ya juya ya bi bayan Baba wanda already ya riga ya yi gaba shi.A gigice ta fito ta bi bayan su,kafin ta kai soron ta fara hangensu a ta chan waje su biyu akan mashin d’in Ya Yusuf d’in amman kafin ta kai ga fita tuni Ya Yusuf ya burga mashin d’in nasa suka wuce.

Kasa tab’uka komai ta yi tsabar rikici kafin kawai ta fashe da kuka ta durk’ushe a wajen abun tausayi,ta dad’e a haka kafin da kyar ta samu ta tsayar da kukan nata,ta na shirin mik’ewa Manubiya ta shigo,a rikice ta k’arasa inda take ta shiga tambayar ta ‘mai ya faru?’
Da kyar Jidda ta iya yiwa Manubiya bayani aikuwa a take ita ma ta gigice ta fita a hankalin ta duk yadda ta so k’in yin kuka kasawa ta yi dan haka ta bar hawayen suka shiga sintiri akan kyakkyawar fuskarta…da kyar suka lallashi junan su suka share hawayen su gudun kar su shiga su je maybe ko Inna ta farka ta gane sun yi kuka, suna shiga kuwa suka tarar da ita ta farka dan haka suka danni kansu suka Bata abinci da maganin ta dakyar, duk da sun lura da yadda take ta kallon su ma’snar ta gane suna cikin matsala kuma tana buk’atar k’arin bayani amma cikinsu ba wanda ya ce mata komai suka nuna kamar basu fahimci me take nufi ba ,haka nan ta hak’ura ta kyale su.Har sama da minti talatin amman sun gagara tab’uka komai dan gaba d’aya a gigice suke ga kuma k’ok’arin b’oyewa Inna damuwar su da suke ta faman yi,da kyar suka d’an fara sauk’k’o da jakankunan suna tunanin inda zasu gan shi ko su san abun da ya faru daganan sai a san abun yi
Ganin bazama su iya had’a kayan bane gashi sun ma kasa yin lissafi mai kyau tsabar rikice wa ya sanya kawai suka yi alwallah suka shiga jero nafil fili suna masu kaiwa ubangiji kukan su,ahaka har aka shafe kusan awa biyu da rabi
sai da suka ji sun d’an dawo dai dai tukunna k’asa k’asa Manubiya ta ce su had’a kayayyakin nasu kamar yadda yace in ya so sai su san inda za su kai inna daga nan su shiga neman Baba da neman mafita,sai da suka gyrawa inna kwanciya suka juyar da ita ta yadda baza ta ga mai suke yi ba tukunna suka shiga had’a kayan a hankali gudun kar ta fahimci mai suke yi,tsaff suka had’a komai suka zauna suka yi jugum!a haka har aka shafe awa biyu ba Baba ba labarin shi sai a lokacin sukayi lissafin su nemi Ya Musbah dan tsabar yadda suka gigice sam ba suyi wannan tunanin da farko ba
Manubiya ce ta ce bari taje ta dubo sa dan wayarta ba kud’i Jiddah kuma ta zauna da inna wadda ta fara bacci yanzunnan….


Ganin har kusan mintuna ashirin ba Manubiya ba alamarta ne yasanya Jidda ta mik’e ta nufi k’ofa da niyyar zuwa kiran Manubiya.

Tana d’aga labulen suka yi ido biyu da Ya Yusuf…bayan sa ta kalla sannan ta d’an lek’a wai ko za ta ga Baba amman sai ta ga wayam,ba tare da ta sake kallon sa ba ta dake sannan ta danne tsoron sa ta fito ta zo za ta wuceshi.
Hijab d’in ta ya janyo ya fisgo ta ya dawo da ita gaban sa ya tsayar
Da sauri Jiddah ta sunkuyar da kan ta dan tashi d’aya hawaye suka shiga silalo mata,
hab’ar ta ya kama ya d’ago da fuskar ta ta da k’arfi wanda hakan ya sanya ta yi saurin runtse idanuwanta hawayen suka shiga sintiri da sauri da sauri akan kyakkyawar fuskarta.
Ya jima yana kallon ta tana kukan kafin yace
‘’Ok,sorry!’’
Ya fad’i hakan yana cika hab’ar tata kafin ya d’aura da cewa ‘’Gani nayi kina neman ki nunamin taurin kai,shiyasa ni kuma na dawo da ke seti..wannan kukan da kika yi ya nuna min ke d’in ce dai Jiddah ta’’,sai da ya fesar da iska tukunna yace’’za mu iya yin magana yanzu’’
ba tare da ya jira jin mai zata ce ba ya fara da cewa
‘’Baba bai dawo ba har yanzu
naji d’azu yace ku gudu ko??
So a gani na a yanzu gaskiya gudawar itace kad’ai option d’in ku amman kuma tsaf za ki iya gyara komai dan komai a hannun ki yake.
Ga Baba mallan chan a d’akin shi Baba na ma yana nan kizo mu je kawai a d’aura mana aure daganan ni kuma nayi alk’awarin zan saki Baba.’’

A rikice ta d’ago tace ‘’Ya Yusuf kai ne ka kama sa?mai ka
yiwa Baba na?ta ya akayi ya yarda ya bika?’’
Ta k’arashe tambayar tata
cikin tsananin rud’ani da tashin hankali.

Murmushi ya yi kafin yace
‘’Ba ni na kama sa ba amma ni na yi silar da aka kama sa,
Jidda abun takaicin shine
akan naira miliyan d’aya tak za’a kulle Baban ki kina ji kina gani saboda tsabar taurin kan ki haka zai yi ta shan wahala bayan kina da ikon da zaki taimake sa…bari in faiyyace miki mai ya faru….Ranar chan a masallaci na gan sa yana kuka sai na nuna masa na ji tausayin sa ne na ce masa ana bada loan a bankin da nake aiki in yana so zai iya k’arba yayi business bayan shekara uku ya biya,na yi masa alk’awarin a k’asan suna na ma zan saka shi
ta yadda ko da ace ta kwab’e ya kasa biya ba za’a kama sa ba tun da sunana ne a wajen
kuma ma inshaaAllah kafin nan za mu biya kud’in.
A take ya ce min akwai business d’in dama da yake da shi a rai
InshaaAllah a cikin shekara biyu ma zai had’a kan kud’in ya cire ribar sa,
A lokacin alhaji Baba har rungume ni yayi
Allah sarki na ji tausayin shi naso in janye k’udirina da na k’ulla akan sa amma kuma da na tuno da kalar cin fuskar da kukayi min
Sannan na riga na fahimci indai ba ta haka na biyo ba
ba zan tab’a samun ki ba
shiyasa ni kuma na kauda tausayin sa a raina na d’auke sa mukaje ya cike form kala kala ba tare da ya san mai yake cike wa ba…..wanda a ranar tabbas rashin zuwa makarantar Baba ya taimaka min ya kuma yi min amfani matuk’a saboda dama Inata adduar Allah ya sa kar ya fahimci wani abun amman sai naga ashe…’’sai da ya d’an guntse dariyar sa yayi k’asa da murya sosai tukunna yace’’ashe Baba ko cikakken sunan sa ma bai iya rubutawa ba’’
Ya fad’i hakan yana mai kwashewa da dariya,
Sannan yaci gaba da cewa
Ni na dinga yi masa spelling
na nuna masa in da zai yi tumbprint ya yi ya mik’a.
Bawan Allah har muka dawo gida yanamin godiya,Ina ga
yasan in ya gaya muku zaku tuhume shi shiyasa ya yi shiru dan har d’azu ma sai da na tambaye shi ya ce min ba ku sani ba ni kuma nace to zan zo in yi muku bayani ta yadda zaki fahimceni dalla dalla,dan har ga Allah dama na ji dad’in shirun da yayi saboda dama banaso kowa ya sani sai a yau d’in.Na san za ki ce min mai naci ko mara zuciya amma inaso ki san cewa duk abun da na yi na yi sa ne saboda farin cikin ki Jiddah!sai kin aure ni tukunna zaki fahimci gatan da nake ta k’ok’arin ganin na tsunduma ki a ciki.
Ki taimake mu ki yi abunda nake so daganan sai muje mu ceto Baba dan muddin suka riga suka tafi da shi to ko an biya kud’in fito dashi aiki ne,inada dubu d’ari tara zan bada cash nasan ba za’a rasa cikon da zai had’a kan kud’in ba har intrest d’in ma all you have to do is say ‘yes’daga nan komai zai tafi cikin tsari.
Ya yarda da ni sosai yanzu haka yana chan yana jirana inje in fitar da shi,dan ce masa na yi zan zo in yi muku bayani in kwantar maku da hankali daganan in tafi neman kud’in da za’a harhad’a a fito da shi.
To ni kuma kin ga sai kin yi min abunda nakeso tukunna zan fitar dashi
Therefore kinga freedom d’in Babanku a hannun ku yake.

Sannan bayan an tafi dashi
za’a zo a kama ku dukkan ku har sai kun fito da kud’in nan
daga nan kuma a fara kiciniyar fito dashi..’’


Wani irin kuka Jidda takeyi abun tausayi,da kyar ta samu ta d’ago kenan za ta yi magana idanuwan ta suka sauka akan Manubiya wadda ta gama yawon neman Ya Musbah a wajen wankin su da Gidan sa amman bata same sa ba.Da gudu Jidda ta tafi ta fad’a jikinta ta fashe da wani Irin kuka….

Tsabar tsananin mamakin Ya Yusuf da takaicin sa da kuma tsananin tashin hankali sam Manubiya ta ma kasa kuka ta kasa magana,haka kawai ta kafe Ya Yusuf da idanu kafin ta samu ta janye Jidda daga jikin ta ahankali idanunta har yanzu akan Yusuf d’in tukunna ta nufesa,yadda Yusuf yaga ta nufosa sai da ta yi masa kwarjini aikuwa tana k’arasawa inda yake bata yi wata wata ba ta d’aga hannu ta zabga masa wani irin gigiceccen marin da ita kanta bata san tana da k’arfin yin shi ba…..

A rikice Ya Musbah wanda suka dinga tafka sab’ani da shi da Manubiya ya iso hanyar d’akin nasu..tun d’azu Baba ya bada number sa aka kira sa har ma sunyi magana da Baban.
Bai ga marin da Manubiya ta yiwa Ya Yusuf d’in ba sakamokon k’ofar d’akin nasu da take a ta d’an lungu amman fa yana karya kwana ya hango Ya Yusuf ya shak’e Manubiya da dukkanin k’arfin da Allah yayi masa,ga Jidda a gefe tanata k’ok’arin kwatar Manubiya amma ta kasa.
Dama Ya Musbah neman Ya Yusuf d’in yake yi dan a iya bayanin da Baba ya yi masa d’azu ya fahimci Baban bai lura tarko ne Yusuf d’in ya d’ana masa ba,amman shi yana fara yi masa bayani ya fahimci hakan…a ganin Ya Musbah duk hauka da iskancin Ya Yusuf bai kamata ya sako Baba a cikin rashin mutuncin sa ba.

Da gudu ya nufesu ya je ya fara k’ok’arin kwatar Manubiya daga hannun Ya Yusuf,ganin yak’i cikata ne yasa ya Musbah ya fara kai masa duka,kamar jira Jidda take yi haka itama ta saka dukkannin k’arfinta ta dinga zuba masa duka a baya …Abun ya yiwa Ya Yusuf yawa shiyasa bai san lokacin da ya cika wuyan Manubiya ba,yana cikata kuwa itama ta sa hannu suka had’u har ita suka rufe Ya Yusuf da duka duka bana wasa ba dan dukkan su su ukun a zuciye suke da shi,sai da suka kaisa har k’asa…


Duk da haushin sa da Ya Musbah yake ji sai kuma ya ga rashin dacewar hakan ga halin y’an gidan kar Baban sa ko wani nashi ya gansu yace sun yi masa taron dangi suje su b’ullo da wani sabon case d’in na daban kuma,dan haka ya tsayar da dukan da ya ke yi masa sannan ya fara k’ok’arin janye su Manubiya.
Amman sai akayi rashin sa a Baba Habu ya k’araso wajen sakamokon hayaniyar su data fara fita harabar gidan kuma yaji kamar muryar Yusuf d’in.

Da kyar Ya Musbah da Baba Habu suka samu suka janye su Manubiya dan rufar wa Ya Yusuf sukayi,suka yi masa
dukan mata ta koina kamar sun kama b’arawo.
Haushi da takaici ne suka sanya Baba Habu yarfawa Ya Yusuf mari bayan ya d’ago sa,a cewarsa ta ya zai tsaya su Manubiya su dake sa.
Dakyar dan ya jigata ko gani bayayi sosai saboda Ya Musbah ya fasa masa gefen ido..ya samu ya iya cewa Baban nasa’’ai harda Musbahu
shine ma ya fara kai masa dukan da ya kai sa k’asa.’’

Cikin fushi Baba Habu ya juya ya kalli Ya Musbah,kamar zai ce wani abun sai kuma kawai ya ja hannun Ya Yusuf suka wuce wanda gaba d’aya jikinsa baki hanci da gefen ido suke fitar da

Please Login or Register in order to submit comment