Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yi mata gashi sai wani tsadden murmushi yake zuba mata.Babu yadda ba tayi ba amma da ikon Allah sai ta gagara cewa komai ga wani mahaukacin bugu da zuciyarta ta shiga yi,ganin bazata iya bane ya sanya ta yi sauri ta sunkuyar da kanta tana tunanin ta yadda zata aro jarumta ta yi masa magana ko da ace bata kallesan ba dan zuwa yanzu ta fahimci abun kamar da wuya,a ranta tace’’wannan wanne irin abu ne haka wanne irin feelings ne wannan?’’ta yiwa kanta tambayar ba tare da ta san waye zai bata amsar ba.

A b’angaren Yashjub kuwa kad’an ne ya rage bai fashe da dariya ba a ransa yace’’.to wai menene nata na k’in kallon cikin idonshi ne?’’yadda take yi
tana kallon gefen fuskarshi abun ba k’aramin burge shi da bashi dariya yakeyi ba.’’

Murmushi kawai yayi yana kallon yadda ta sunkuyar da kanta yana jin wani sanyi yana ratsatsi,baisan wanne Hali zai shiga ba in da anyi rashin sa’a black snake ya tafi da ita ko yayi mata wani abun,ganin ransa yana shirin b’aci ne ya sanya ya yi saurin kawar da tunannin cinkin taushin murya ta ji yace’’Allah ya ci gaba da karemin ke tare da family d’inki a duk inda kike’’.

Wani irin bugawa kirjinta yayi,a take ta runtse idonta tana jin yadda kalaman nasa na yanzun suke ratsa zuciya da dukkkannin sassan dake a jikin ta tare da sauk’ar mata da wata sabuwar kasala mai tafe da fad’uwar gaba,cikin mutuwar jiki a chan k’asan ranta tace’’Not again Yash,plsss!’’

Tunani Yashjub ya fara yi akan ko dai ya sako maganar incidence d’in jiya da safe,dan haka
ya bud’e baki zai yi magana kenan aka bud’e k’ofar d’akin da aka shigar da Baba da Abbakar aka fito,da sauri su Manu da ya Musbah da sir Najeeb suka rufar wa Doctor d’in da ya fito.

Yayinda Yashjub yake nan a inda yake ko motsi ya gagara yi ,bayan Manubiya wadda ta mik’e da sauri ta nufi doctor kawai yabi da kallo yana murmushi yanajin wani nishad’i yana ratsashi…ashe haka so yake?shi fa ko wani irin takaici yake ciki to wuyarta ya yi magana da ita ko ya ganta kai ko tunanin ta yayi
to fa da yardar Allah tashi d’aya sai yaji b’acin ran nasa ya kau.

Cikin nustuwa sir Najeeb wanda ya gama jin bayanin likita ya juya ya nufi inda Yash d’in yake a zaune,har ya k’arasa ya tsaya a kan sa sam Yashjub bai lura ba sai da Najeeb d’in ya yi flashing fingers d’in shi a setin fuskar Yashjub tukunna ya d’an d’ago
yana kallon sa.
Murmushi Najeeb yayi ya zauna a gefen sa tukunna yace’’ya dai?’’

Bai da niyyar b’oyewa wa dan haka tashi d’aya ya ce
‘’Najeeb! Manubiya ce rayuwata,adadin yadda nake
numfashi kullum haka k’aunar ta take k’aruwa a cikin zuciya ta,ku yi sauri ku nema min aurenta tun kafin in haukace muku.’’

K’amewa Najeeb yayi kawai yana kallonshi yana mamaki,a ransa yace’’Ubangiji mai’kun fayakun’!’’
Kafin ya yi murmushi ya d’anyi
tapping shoulder Yash d’in cikin sigar zolaya yace’’Man!ai ka riga ka fara hauka,kalli yadda ka maidani slave d’in students d’ina..mun gama duk wasu abunda suka kamata amma ka hanamu tafiya sannan ka ji yadda kake magana kuwa?gaskiya kam ya kamata muyi wani abun da sauri’’ya k’arashe maganar yana dariya k’asa k’asa.
Kafin ya sake cewa’’yanzu dai zo muje ka ga sirikin naka mu samu wuce Inada aiyyuka da yawa wallahi,Doctor yace
Abbakar d’in an cire bullet anyi komai amma bai farfad’o ba yet,Sirikin ka kuma he’s well and conscious so let’s go say hi
daganan mu wuce ko?’’
Ya k’arashe maganar tasa da tambaya yana mai mik’ewa tsaye.

Har ya d’an yi gaba sai kuma yaga Yashjub bai ma taso ba dan haka ya koma ya ce’’ya akayi kuma?’’
Tunda yake bai tab’a ganin Yashjub yayi kalar tausayi ba sai yau,har da wani karkata wuya
Dan haka kawai sai Najeeb d’in ya saki baki yana kallon ikon Allah
Muryar Yashjub d’in ce ta katse masa tunani jin yana cewa’’I’m serious Najeeb,ka fara yiwa hajiya Mama magana ita kuma ta yiwa Daddy kasan halinta yanzun sai ta birkice a kasa gane kanta shiyasa bana so in yi mata magana dan nasan in taga na damu kuma na rikice akan maganar bazata taimakamin ba cewa zata yi tun yanzu Ina haka ina kuma ga in anyi auren,ni kuma na san a yadda nake ji d’innan ba zan iya yin komai calm ba.
Kayi mata magana a samu a fara maganata da yarinyar nan
Najeeb tun kafin a samu matsala

Shiruu Najeeb ya yi kafin ya bud’e baki yana shirin yin magana k’arar wayar sa ta katse sa,dan haka ya cewa Yash d’in’’ a minute pls’’kafin ya sanya hannu a aljihun sa ya ya zaro wayar.

Yashjub ya kalla kafin ya sake maida hankalinsa ga wayar sakamokon ganin sunan Daddy da yayi a matsayin wanda yake kiran nasa,sai kuma ya kalli Yash d’in tukunna yace ‘’Ina wayarka??’’

‘’Tana mota’’Yash d’in ya basa amsa a tak’aice yana mai ci gaba da tunane tunanen sa…’ya riga ya k’arbi har number Baba zai jira ya d’an warke daganan sai ya bawa Daddy number d’in tasa suyi magana a tsakanin su yasan inshaaAllah kafin nan Najeeb kuma ya tsara masa hajiya Mama ita kuma ta yiwa Daddyn magana,daga nan yasan inshaaAllah komai zai zo masa da sauk’i,ta b’angaren Manubiya kuwa yana addu’a tare da yak’inin inshaaAllah zata aminta dashi da yardar ba zai sha wahalar samun soyayyarta ba,shiyasa ma yake so ya je mata ta koinahar ta sama ta yadda zata fi d’aukar sa serious.’….

Cikin nutsuwa da girmama Najeeb ya gaida Daddy ya amsa masa kafin cikin fushi ya ji Daddyn yace‘’kana tare da Yashjub ne??’’

Saida Najeeb ya kalli Yash yaga sam hankalin sa bama ya gurin ya tafi ga tunanin da yake yi tukunna yace’’eh Daddy,‘’kafin ya d’aura da cewa’’gashinan bari in basa’’

Da sauri cikin katseshi Daddy yace’’A’a barshi,kace masa nace dan ubansa ko me yake yi ya bari yazo yanzunnan’’
Daga haka ya kashe wayar kit.

A d’an duburce Najeeb ya kalli Yash dan bai tab’a jin Daddy da irin wannan fushi haka ba,kafin yace’’Yash!Daddy fa a zuciye yake,mai ka aikata?’’

Ahankali Yashjub ya maida kallon sa da tunanin sa ga Najeeb kafin yayi shiruu kamar mai tunani sai kuma chan yace’’kash!wallahi mantawa nayi’’

Cikin tarar numfashin sa Najeeb d’in yace’’me ka manta?yace kaje right away fa,tashi mu wuce na ji b’acin rai sosai a muryar sa’’
Najeeb d’in ya fad’i hakan yana mai juyawa.

Numfashi Yashjub ya fesar kafin ya kalli inda Manubiya ta bi ta shige,wallahi ba daban Daddy ne ya kirasa ba to da bai ga dalilin da zai sanya ya fita a asibitin nan ba tare da sun yi sallama da Manu ba besides shi fa bai ma gaji da ganin ta ba.
A gaggauce suka tsaya suka biya duk wasu bill daga nan suka fice suka nufi motocin su Najeeb yanata sauri yana cewa ‘’ka yi sauri fa Yashjub,kar ka dad’e ransa ya kuma b’aci..’’





MANNUBIYA
39

Na
Humayrah Bulama

Mikiya Writers Association.

A zaune su Manu suka tarar da Baba ana gwada masa sugar dan complete checkup Yash ya biya ayi musu,suna had’a ido da shi gaba d’ayan su sai suka sake zama emotional,tashi d’aya Jidda da manubiya suka fara hawaye ya Musbah ma sai da ya yi da gaske tukunna ya iya hana kansa kuka…ji yake yi kamar ya d’aura hannu aka ya yi ta kurma uban ihu!akan naira miliyan d’aya tak!kalli abunda aka yiwa mahaifin sa sannan akayi shirin tafiya da k’annen sa mata har biyu amma babu abun da ya iya tab’ukawa.

Nurse d’in tana fita suka rufarwa Baba har suna y’ar rige rige wajen k’arasawa tare da tambayar sa ya jikin sa,murmushi ya yi dan dukda hali na tashin hankalin da yake a ciki sai da yaji wani sanyi da fariin ciki suna ratsasa na ganin yanda y’ay’an nasa suka
damu sannan suke d’awainiya dashi,dan haka ya shiga kwantar musu da hankali kafin ya kalli ya Musbah yace‘’Ina yaran suke?ai bai kamata ku barsu a waje ba ko?ku je ku shigo dasu da wuri kar su tafi ban yi musu godiya ba.’’

Jinjina kai ya Nafi’u yayi suka fita da shi da ya Musbah smma ko da suka fita basu tarar da kowa ba wnda hakan yake nuni da cewar su Yash d’in sun tafi kenan dan haka suka koma ciki
Suka sanar wa baba…sai da suka ce masa ai
Suna da numbers d’in su tukunna ya d’an ji sanyi,sannan yace koda sun Kira su a waya ya zama dole
Suje har office d’in sa ayi
Mishi godiya,mutumin dayayi musu alkhairi irin wanda Yashjub yayi musu tabbas ya chanchanci special treatment daga garesu suma.
Ta wayar ya Nafi’u aka kira Yash da wanda gaba d’aya kunya ta lullub’esa sannan duk sai yaji wani iri na daga godiyar da baban yakeya yi masa,Hakanan dai a kunyance suka yi wayar daganan Yash yayi masa sallama tare da fatan Allah ya basa lafiya ya kuma kare gaba
Har Najeeb sai da Baba yasa aka kira shima yayi masa godiya tukunna hankalin sa ya kwanta…dukda kuwa baba k’arfin hali ne kawai yake yi amman gaba d’aya abun wani iri yake jin sa ace wai
Kaci kud’i har za a tafi da y’a y’an ka amma ka gagara tab’uka komai,a hankali ya lumshe idanun sa a ransa yace’Innalillahi a inna ilaihirrajiun,’’

Daidai nan kiran wayar Aisha ya shigo wayar Manubiya dan haka ta d’an fita waje domin ta amsa…bataso tayi wayar a gaban Baba dan bata sani ba ko wani abun ne ya taso daga b’angaren inna tasan yana ji zai ce zai tafi gida to kuma shima ga yanayin jikin nasa sai a hankali….dan haka ta fita tana mai addu’ar Allah yasa lafiya.Jidda ma tana ganin fitar Manubiyan itama ta mik’e ta mara mata baya.

Baba yanajin fitar su ya bud’e idanun sa ya zubawa inda suka bi suka fita idanu yana Jin tsananin tausayin su yana ratsashi dan tabbas shi kansa yasan baza suji dad’in hukuncin daya gama yankewa a kansu ba.

Yaji dad’in fitar da suka yi dan haka ya gyara zama ya kalli ya Nafi’u da ya Musbah ya ce’’ inshaaAllahu nan da sati biyu nake so in aurar da Jidda da Manubiya…’’
Kwarewar da ya Musbah yayi ya fari tari a wahale ne ya katse Baba…da kyar saida ya sha ruwa sosai ya d’an zauna tukunna ya d’an ji dama dama still yana tarin kad’an kad’an bai iya jira tarin ya tsaya gaba d’aya ba yace ‘’Baba aure a cikin sati biyu kuma sab….’’
Cikin tarar numfashin sa Baba yace ‘inshaaAllahu rabbi,yanzu Manubiya nake so ku nemawa tsayayye wanda yake a shirye tsaf nan da sati biyu sai a had’a ayi,Jidda ita dama Yusuf a shirye yake,inshaaAllah Ina fita daga nan zan samu baba habu mu…’’

Duk yadda ya Musbah yaso ya danne fushin sa kasawa yayi,bai san lokacin da ya kats’e Baba ba.. dan cikin tarar numfashin sa a hassale yace’’Baba amma ba dai Yusuf d’an gidan baba habu kake maganar zaka aurawa jidda ba ko?ba dai Yusuf d’an iska wanda ya jefa mu a cikin wannan bala’in zaka d’auki Jidda ka aurawa ba ko? dan indai shi kake nufi to a gaskiya Baba ba zan tab’a barin Jidda ta aure sa ba…’’

Cikin fushi da fad’a Baba yace‘’a kul,d’in ka Musbahu,wannan iftila’in da ya fad’o min babu ruwan Yusuf dan haka kar ka d’aura masa laifin da ba nasa ba,eh’nasan muna yawon samun sab’ani
dasu amma na san ko
Hauka Yusuf yakeyi ba zai tab’a yi min abunda zai jefani cikin wannan halin ba,’’

Cikin fushi ya Musbah yace’’baba habu fa shi y…’’
Cikin tarar numfashin sa Baba yace ‘mMusbahu banason rashin kan gado fa?so nawa nake ce maka ko da wasa karka yarda ka k’ullaci y’an uwana da y’ay’ansu akan abubuwan da suke yi?idan ka k’ullacesu kaima ai ka zama su kenan kaga sai ka bada gudummawar tarwatsewar zumuncin namu cikin sauk’i kenan,in ba rashin kirki ba Musbahu har kai ne wai zaka kalleni kana cewa wani bazaka Bari Jidda ta auri Yusuf ba Kaine ka haifamin ita???

Sai yanzu ya Nafi’u ya fesar da iska ya k’arasa gaban Baba ya zauna akan kujerar dake a bakin gadon tukunna yace’’baba ka yi hak’uri,kar kayi misunderstanding d’in sa,maganar gaskiya Baba Yusuf bai cancanci a bashi Jidda ba duba da yadda….

Cikin katseshi Baba yace‘’Bari ka ji Nafi’u dama nasan zakuyi
Tunanin wai ko ata sanadiyyar Yusuf ne na fad’a wannan halin wanda sam abun ba haka yake ba,Yusuf taimakona yayi sai kuma abun ya zo da tangard’a yayi min bayani kuma na fahimci komai dan haka banason Jin komai daga bakin kowa illah kuce min ‘to’ kawai.Yusuf zai auri
Jidda nan da sati biyu Manubiya kuma ku nema mata miji ,wannan shine kawai abunda nake so ku fahimta kuyimin biyayya akai.’’

Shiruu ya Nafi’u yayi kamar ba zai ce komai ba sai
Kuma yace ‘’amma baba auren gaggawa da’’
Cikin katse shi Baban yace
‘’Nafi’u baka ji abunda mutumin chan black snake ya fad’i mun kafin ya tafi ba?
Idan ba ka jiba bari in maimaita maka
Cemin yayi ‘sai ya dawo d’aukar matarsa’!’’,
Shiruu Baba yayi kafin zafafan hawayen da yake ta k’ok’arin rik’ewa suka samu nasarar zubo masa,cike da rauni yace‘’Nafi’u tun da na haifi yaran nan ban jiyar da su dad’i farin ciki da walwala ba,Allah ya rufa asiri amma in black snake ya dawo kamar yadda ya fad’a ya d’auki yaran nan ban san taya zan fuskanci ni karan kaina ba ballantan su kansu yaran uwa uba ubangijina ban san da wannne bakin zan yi masa bayanin yadda na kula da amanar da ya bani ba’’Baba ya k’arashe maganar tasa yana mai fashewa da wani irin kuka.

Da kyar ya Nafi’u ya samu ya lallashi baba ya yi shiru,shi kansa ya Musbah ya ji ba dad’in kukan da mahaifin nasa yake yi shiyasa gan d’aya jikin sa yayi sanyi,yayin da zuciyarsa take wani irin tafarfasa tabbas Hausawa sunyi gaskiya da sukace’’munafuki in ya rigaka shiga d’akin uwarka ko ruwa baka isa ka sha ba.’’Allah kad’ai yasan me Yusuf ya gayawa Baba shi kuma ya hau
kai d’aram ya zauna.Gashi ya san halin Baba da wata iriyar rikitattiyar kafiya ya riga ya san ko ta ya yayi masa bayani ba zai tab’a yarda ba,gashi yanxu ya say a gaba yana kuka shiyasa tashi d’aya gaba d’aya jikin ya Musbah yayi sanyi dan jin kukan Baba yake yi har cikin ransa,ji yake yi kamar ya je ya samu Yusuf ya d’aga sa sama kawai ya goce…zai bar maganar yanzu ya samu ya lallab’a Baba amma inshaaAllah ba zai bari Jidda ta auri Yusuf ba’’.

Ahankali ya matsa ya shiga lallashin sa shima yana mai basa hak’urin abunda yayi masa yanzun,

Cikin sanyin jiki Baba yace’’mutumin nan ya gudu basu kama sa ba,ku bar ni in aurar da su Jidda tun kafin wani abun ya sake faruwa,nasan inshaaAllah in sunada aurensu darajar aure da kariyar ub…..
Shiruu ysyi sakamokon shigowar da su Manu sukayi,cikin nutsuwar su suka k’arasa suna zuwa wajen ya Musbah ya juya da sauri yace ‘’bara in duba jikin Abbakar!
Ya fad’i hakan yana nufar labulen da aka saka a tsakanin baba da abbakar d’in.
Doga jin haka ya Nafi’u ma ya biye masa baya.
Ya Musbah na gaba ya Nafi’u na biye dashi a baya yana tafe yana dialing number Aisha dan sai yanzu yaga misscalls dinta birjik haka suka shiga inda Abbakar d’in yake a kwance.
Suna shiga ya Musbah ya naushi iska da k’arfi jikin sa har wani irin karkarwa yake yi tsabar takaici.
Dasauri ya Nafi’u ya rik’e shi yace’’haba Musbahu!kayi hak’uri abi komai a hankali with time komai zai yi normal inshaaAllah.’’
Kamar zai fashe da kuka yace
‘’Astaghfirullah Nafi’u wacce irin rayuwa ce wannan kalli family d’ina kalli halin da suke a ciki amma wai ace banida yadda zanyi in taimakesu?ka duba kaga yadda ake shirin aurar da su Manubiya kamar wasu kaji?kuma a yadda Baba yayi bayanin yana da gaskiya ta wani fannin tunda daga ni har shi ba zamu iya karesu ba,amma bai kamata Jidda ta auri Yusuf ba kuma ya kamata ace nayi wani abun amma banida……’’
Kukan da ya kufce masa ne ya sanya shi kasa ci gaba da magana.

Ya Nafi’u ji yayi kamar shima ya fashe da kuka, dan haka cikin sanyin jiki ya matsa kusa da ya Musbah ya rungumesa
cikin sigar lallashi yace’’kuka da k’unci ba shine mafita ba
Musbahu kar ka dasa aya a kan k’addarar ka kaje garin hakan ka kauce hanya,sannan kar ka karaya kace wai dan bakada k’arfi bazaka
Iya yin komai ba,inshaaAllah zamu fahimtar da baba kuma zai fahimcemu dan ko da ace za’a aurar da su Jiddan to ni
kaina ba zan goyi bayan a aurar da su da wuri haka ba kuma ba zan bari Jidda ta auri Yusuf ba inshaaAllah,kawai dai yanzu abunda nake so ka fahimta shine Baba ya d’au zafi Sannan hankalin sa a tashe yake dan haka ka bari nan da kwana biyu inshaaAllah in ya d’an sak’k’o muka lallab’a sa zai fahimce mu.
Ubangiji yana tare damu komai zai yi daidai inshaaAllah’’

Cikashi ya Musbah yayi yaje jikin window ya dawo ya sake komawa…yana yi yana share hawayen sa kafin da kyar ya samu ya tsayar da kukan nasa
tukunna yace‘’Allah ya dafa mana Allah ya tsaya mana,Nafi’u na san zafin rashin dace da Abokin rayuwa in akayi rashin sa’a Baba ya k’i amincewa damu yaje garin neman mafita ya burma su Jidda a hannun mugaye ya kake tunani kenan??kar mu je duk mu ukun mu k’are da…..’’

Da sauri ya Nafi’u yace‘Musbahu ka kyautata zoto dan Allah think positive!inshaaAllah hakan ba zata faru ba’’

Shiruu ya Musbah y d’anyi da farko
yana me sauk’e ajiyar zuciya a
jere a jere kafin ya jinjina kai kawai daga haka ya k’arasa bakin gadon da Abbakar yake nan a kwance ya zuba wa guri d’aya ido yayi shiruuu.

Numfashi ya Nafi’u ya fesar kafin ya d’ago wayarsa da sauri dan shi sai yanzu ma ya tuna yayi dialing number Aisha tun d’azu,yana d’ago wayar yaga timer tanata tafiya alamun ta d’auka kenan tun d’azun.
Ajiyar zuciya ya sauk’e kafin ya kara wayar a kunnen sa yace’’lab’e kika fara kenan!’’

Murmushi tayi sannan tace’’na d’auka sai su khairat suka fara fad’a ita da mai sunan baba shine na ajjiye wayar na je raba su a tunani na na kashe ,amma kuma dukda haka dana d’auka d’in da farko kafin in ajjiye naji maganar data d’an kid’ima ni shiyasa ma na manta ban kashe d’in ba tsabar kid’imar da na yi’’….shiruu ta d’an yi kafin tace’’ da gaske Manubiya aure ta yi???


Dafe kai ya Nafi’u yayi kafin yace’’kinga irin ta ko,baki tsaya kin ji kan zance da k’arshen sa ba kawai daga kin ji ance aure shikenan ke har kin yi concluding.’’

Fahimtar da Aisha ta yi kamar ran maigidan nata a d’an b’ace yake ne yasanya cikin kwantar da murya tace ‘’Allah ya huci zuciyar ka ba zan k’ara ba,dama naga kamar inna tana jin yunwa ne shine na kira inaso in tambaya a bata madara ne ko abinci to sai baka d’auka ba,a lokacin kuma wayar Manu bata shiga amma na same ta ma har ta yimin bayani tun d’azu mun gama magaana.

‘’Okay,sannu Aisha Allah yayi albarka’’ya Nafi’u ya fad’i hakan cikin sanyin jiki.

Ahankali tace ‘’ameen’’ daganan suka yi sallama bayan yace mata ‘ai sun ma kusan dawowa’dan haka ta bari akan idan sun dawo sai ta ji koma mene ya kaisu suka dad’e haka.



Tun lokacin da Ya Musbah ya kai Inna gidan sa ya fita
Baraka ta kumbura ta rasa Ina za ta saka ranta,tashi d’aya ta ji gaba d’aya
duniyar ta yi mata zafi…ita fa dama tun farko abunda take tsoro kenan dan ita babban tashin hankalinta kar rikon inna ya dawo hannun ya Musbah dan wallahi bazata tab’a iya jurar ganin ta a cikin gidan ba,dad’in dad’awa kuma gata liability saboda Allah in banda rashin adalci taya ma za’a had’ata da jinya ai ba dan haka aka aurota ba!.

Takaici da bak’in ciki ne ma suka saka ta kasa tab’uka komai a cikin gidan dan haka ta fito tsakar gidan ta zauna akan y’ar kujerar tsugunno tanata faman cika tana batsewa ko d’akin innar bata lek’a ba tun da su ya Musbah suka kawo ta suka fita,
Muhsin ne da me sunan Baba wanda tunda ya gansu yaketa murna ya shige d’akin shima
suke ta yiwa innar hira.

Baraka kuwa ana tsakar gida ta d’aurawa kanta bala’i in banda tafarfasa babu abunda zuciyar ta takeyi…a haka Aisha ta shigo ta same ta.
Sama sama suka gaisa da Aishar daga haka ta tambayeta d’akin da innar take ta nuna mata
Aishar ta shige.

Tana shigewa Baraka ta mik’e tsaye dan ta ma kasa zama kwata kwata kamar wadda aka aikowa da rikitaccen sak’o haka ta shiga safa da marwa a cikin gidan ta kasa tsaye ta kasa zaune….itafa bazaiyiu a maida mata gida asibiti ba wallahi!gashi y’an dubiya har sun fara zuwa,wannanya shigo wannan ya fita shikenan ita ba ta da sirri a cikin gidan ta kenan,gashi har yanzu su ya Musbah shiru,ta kirasa kuma ya k’i d’agawa
Itafa wallahi inna bazata kwana gidan ta ba yau.!

Sama sama ta fara jiyo muryar
Aisha kamar tana waya da ya Nafi’u dan haka taje ta lab’e…..
wani irin gumi ne ya shiga keto mata sakamokon kunnuwanta da suka jiyo mata lokacin da Aisha take cewa’’da gaske Manubiya aure ta yi???’’

Tashi d’aya Baraka ta shiga tashin hankali a ranta tace
‘Manubiya tayi aure! abunda sukaje yi kenan?to ina batun
Baba kuma dan d’azu maman Abbakar ta kira ta take gaya mata cewar’’ kamasa akayi!
Shiyasa suka kawo innar suka tafi gaba d’ayansu,taso ta
tsaida Abbakar amma yana gaya mata an kama Baban ya fice a gigice har yanzu shiru babu shi babu labarin shi tanata kiran wayar sa kuma baya d’auka’’

Wato Shiyasa aka kawo mata inna da Muhsin tun yanzu kenan
Manubiya tana tare wa a gidan ta ta san jidda ma nan zata dawo
Kut!ai wallahi bazaiyiu ba wannan abu ba zai tab’a sab’uwa ba ba zata zauna a gida d’aya dasu ba wallahi!
Sannan
yanzu haka ma ya aka k’are,
tayaya ya Musbah yake iya ciyar da su biyu kawai
Ina kuma ga in nauyi ya sake yi masa yawa.’
Waennan sak’e sak’en da take ta yi ne ya sanya ta fara jin jiri har wani dishi dishi ta fara gani dan haka ta koma ta zauna a kan y’ar kujerar ta tana ji kamar zuciyar ta zata kama da wuta.

Bata dad’e da zama ba, Aisha ta fito ita da khairat tace mata ‘’ta d’aura girki bara taje ta duba’’

‘’To’’
Kawai Baraka ta iya ce mata dakyar dan wani irin tafarfasa zuciyar ta takeyi

Tana fita Baraka ta mik’e,ta ma rasa me yakeyi mata dad’i ta rasa Ina zata saka ranta taji sanyi.
Tabbas in fa tayi sake tou wallahi ruk’on inna ya dawo hannunta kenan tunda ko
da ace da akwai Jiddah ai
Jidda indai taci post utme d’in ta to makaranta zata fara zuwa
Muhsin yarone ya Musbah kuma aiki zaice ze dinga fita,shikenan ita a barta da inna kenan….a barta da talaucin da ya Musbah ya tsundumata a ciki ma mana
ba sai an k’ara mata da zama gida da dangin miji ba!.

Tsulum!
Haka Muhsin yaga Baraka ta afka d’akin da suke a ciki shi da inna,da sauri ya mik’e yana ce wa’’anty,kin ji yanzunnan
naji inna tace ‘Manu’wallahi!ki matso ki tambayeta kiji’’
Ya fad’i hakan cikin tsananin farin ciki yana Jan hannun Baraka yana dariya

Wafce hannunta tayi ta k’arfi
Tace’’dalla ni cikan….’’




MANNUBIYA
40
Na
Humayrah Bulama

Mikiya Writers Association.


Wafce hannunta tayi ta k’arfi
Tace’’dalla ni cikani’’

Ahankali Muhsin wanda duk jikinshi yay sanyi yace
‘’Da gaske nake fa’’

Dakyar Baraka ta d’an k’ak’alo murmushi tace
‘’Na yarda mana,nima ai tun daga waje

Please Login or Register in order to submit comment