Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ajiyar zuciyar da take sauke wa a jejjere .

Da sauri tasa hannu ta goge fuskarta ,
Kafin ta ‘dago ,
Ko kallon su Bata yi ba tadan matsar da ‘kafar ta gefe domin su samu damar wucewa ,
Tanajin dayar tace
‘’Allah ya kyauta
Kowa de yanada damuwar nan daurewa kawai akeyi ‘’.

Bata da lokacin su
Dan zuwa yanzu abunda yake kanta ma ya ishe ta yayi mata yawa
Tunda gashi yau har da kuka tukuru a aji tayi .

Hakanan ta ‘dan juya ta sunkuya ta dauki ko’da’d’diyar Jakarta
Ta mike Bata yadda ta kalli kowa ba haka tanufi ‘kofa.

Hakanan ragowar students din suka bita da kallo wasu ta na basu tausayi wasu Tana basu mamaki
Dan tashi daya in ka kalli fuskarta xaka san kuka tayi

Gaba daya duk se taji wani iri
Ganin kallon da ake mata ,
Taji saukin ra’da’din zuciyar ta tabbas
Amman kuma duk se taji takaicin kukan da tayi a aji dan haka Tana fita ta wuce
Ko ABBAKAR Bata tsaya jira ba .

Tana fara tafiya ta ji yo shi ya biyo ta yana kiran ta
Manu ! Manu !! Manu!!!.

Se da ta dan gyara fuskarta wai ita ala dole kar ya gane kuka tayi
Tukunna ta ‘dan tsaya ba tare da ta juya ba .
A haka ya ‘karaso ya sameta
yana dan haki
Da alamun ya ‘dan ha’da da gudu ne yace
‘’Hope dai Bakiyi attendance ba
Kar sir najeeb yaga sunanki biyu
Naga kin sunkuyar da kanki
Su kuma na gefen ki dasuka gama basu tashe ki ba
Shiyasa na rubuta miki ‘’

Jinjina kanta tayi alamun yes
Sannan tasa hannu ta ‘dan goge fuskarta Sam taki yarda ta kalleshi ita ala dole kar ya fahimci kuka tayi
Ahankali tace ‘’nagode abbakar ‘’

Murmushi ya yi Kafin yace
‘’oh com on Manu
Nasan fa kuka kika yi ’’

Girgixa Kai tayi kafin tace
‘’Banyi komai ba ‘’

Murmushi yayi me ‘dan hade da dariya Kafin yace
‘’Look at me ‘’

Bata ‘dago ‘dinba
Dan haka ya zagayo ya tsaya a gaban ta ya tsare ta da idanu
Yana kallonta kawai kafin
A hankali ya samu bakin shi ya sake futar da Sentence din
‘Manu look at me ‘

Yanzun ma
Bata ‘dago ba
Har
Wani ‘dan ajin su yazo yace
‘’Yauwa ku nake nema
Sir Najeeb yana kiran ku ‘’,
Har yayi gaba se kuma ya dawo yace
‘’ I mean ,yana Kiran ta dan ita yace in Kira but nasan tare zaku je
Shiyasa nace muku yana Kiran ku ‘’
Ya fadi hakan yana dariya kasa kasa
Sannan ya ‘daura da cewa
‘’Ku yi sauri yana ajin har yanzu’’
Kafin yace musu ‘’se anjima ‘’
Daga haka ya juya ya wuce ..

Addua MANUBIYA tashiga yi
Allah yasa ba wani abu serious bane ba
Dan inde kaji kiran sir Najeeb
Tou ba alkhairi bane ,
Dan haka tashi daya ta ‘dan tsure
Wanda hakan yasan ya har Bata ma Jin Abbakar
har seda ya sake cewa
‘’Manu.
Kar yaji haushi fa ‘’
Tukunna suka jera su biyun suka nufi ajin da suka gama lectures din …

Waya suka sameshi yanayi dan haka suka tsaya jira ,
Yafi minti hudu Kafin yayi sallama da Wanda yake wayar tukunna ya mike ya fara harhada takardun shi ..

Yana hada takardun ba tare daya kallesu ba yace
‘’Next time ,In kinsan kuka da rashin maida hankali xakiyimin a aji
Karki sake shigowa ‘’

Daga haka ya sa kai ya fice ,
Ko hak’urin da suka fara bashi bai tsaya ya saurara ba….







MANNUBIYA
O3
Na
Humayrah Bulama

ELEGANT online ✍️

Yana fita Abbakar ya fesar da iska yace
‘’Allah ya taimake mu,
We got lucky’’.
Dan tabbas shi kan sa ya ‘dan tsorata kuma ya san ba ‘karamar sa ‘a suka ci da ya bar Manubiya a iya warning
bai ce kar ta sake shigar mishi aji ba.”

A hankali itama Manubiya ta fesar da iska,bata gama tunani ba ta ji ya ce
‘’Nima ina son ganinki, Bismillah zauna.”
Ya fad’i hakan yana nuna mata wajen zama Sannan shima ya nemi seat ya zauna dan yanzu ba kowa a ajin.

Shiruu tayi kamar baza ta zauna ‘din ba, sai kuma ta nema seat ‘din kusa da ita row din farko taja ta zauna
Kafin tace
‘’Ina jinka.”

Cikin rashin jin da’di yace
‘’Manu,bana jin da’din b’oye b’oyen da kike yi min kwana biyun nan, In akwai wata matsalar da ban san da ita ba
Talk to me, ki gaya min mu nemo mafita mana, Ko kin dena trusting ‘dina ne?”
ya Kara’she tambayar tashi a hankali yana mai kallon ta .

Sai da ta sauk’e ajiyar zuciya tukunna ta ce
‘’Ba haka bane.’’

Cikin tarar numfashin ta yace
‘’To yaya ne?’’

Girgixa kai kawai ta yi tana jin wani takaici yana sake lullu’beta, kafin tace
“Kaka mallan ne yake so ya b’ullo da sabon issue.”
A hankali ta ‘dan sauk’e ajiyar zuciya kafin tace
‘’Sannan Baraka ta gaishe shi
Sai kuma ta ‘dan yi shiru ,
chan kuma tace
‘’kaka mallam ne yace wai in bar makarantar
In yi aure.”

Da sauri Abbakar yace
‘’what? Saboda me wai?”

Ahankali tace
‘’Nima ban san dalilin sa ba ,
Kawai yaga kwana biyu ciwon Inna ya motsa shine yake son sake d’aga mata hankali ita da Baba,In ba haka ba meye na ‘bullo da wani case d’in? Ai y’a san Baba bayaso ace baza mu yi karatu ba,kuma ya san baya son yawan yin jayayya da su.”

‘’Ya kamata ayi wani abun akan wannan tsohon fa ‘’.
Abbakar din ya fa’da cikin rashin jin da’di,
‘’me Baba yace ?‘’
Ya jeho mata tambayar a jere.

Cike da damuwa tace
‘’Shiru yayi ,kuma ni harga Allah ina jin tsoron shirun na sa ,
Ina Jin tsoro kar ya amince kasan shi bayason hayaniya dasu.”
Da sauri Abbakar yace
‘’ Bana jin Baba zai yarda su hana ki karatu, No matter wat ‘’
Cikin gyara zaman sa da bata dukkan nin attention d’in sa
Ya ce
‘’Ki nutsu ki daina d’aga hankalin ki Pls,ki kwantar da hankalin ki kar ki damu inshaaAllah sai kinyi har PhD ,karki bari tsohon nan ya hanaki walwala ya saka ki a damuwa , kalli yadda kike kuka a aji fa.”
Ya k’arashe maganar cikin rashin jin dad’i.

Jin jina kai kawai tayi
Daga haka ta fara
‘ko’karin mi’kewa .

A hankali yana kallonta yace
‘’ Ita kuma Baraka mai tayi?”

Sai da ta ‘dan kalle shi da kyawawan rinannun idanuwan ta tukunna ta kauda kai gefe ta ce
‘’Ba komai ‘’
Daga haka ta mi’ke tsaye .
Da sauri shima ya mi’ke ya ‘karasa gareta sannan yace
‘’Ya jikin Inna?An ha’da kud’in kaita asibitin ?’’

Da sauri tace
‘’An ha’da ‘’
daga haka ta juya ta nufi ‘kofar fita .

Tun dazu dama ya riga ya gano a inda main problem d’in daya saka ta kukan yake ,
Yanzu kuma yadda tayi ya tabbatar mishi ….
Ya riga
Yasan ko me zai yi bazata yarda ta kar’bi sisi a wajen sa ba ,
Sannan
ya fahimci Baraka ta kuma yin abunda tafi komai ‘kwarewa akai wannan karon ma
Duk yadda akayi ta ‘bullo
da wani abun ta amshe ku’din hannun Ya musbah kakaf ,
Ya rasa gane dalilin daya sanya
Baraka take wannan rashin imanin ,baisan meyene a kanta ba
Bai kuma san dalilin daya sanya Baba da Ya musbah suke biye mata suke ‘daga mata k’afa take tsula duk tsiyar data ga dama ba .

Ganin dayayi Manubiya har ta fice ne yasa shima ya bi bayan ta da ‘dan sauri ,a ranshi kuwa ya riga ya gama yanke shawarar abunda ya kamata yayi wajen taimaka mata a samu a kai Innar Asibiti,Satin ta kusan ‘daya tana fama ciwon ta ya motsa ya kamata ace taga likita .

Yana fita ya hango ta
har ta ‘dau hanyar da zai sada ta da gate ,
Dan haka ya k’arasa suka nufi gate din tare shi da ita .
Ba gida zai yi ba shiyasa basu tafi tare ba
amman sai da ya sanya ta a adaidaita sahu ya biya ku’din kmr kullum tukunna ya juya shima ya tari tashi adaidaita sahun ya shige yayi gaba.

Anguwar su ‘daya da Abbakar shine best frnd d’inta tun daga secondary skul suka fara abota sosai hakan ya sanya tun suna yara suke shiri ,
Abokanayen sa har dariya suke ma sa ,
tun yana ‘dan mitsitsi yake
wanke k’afa ya tafi gidan su Manubiya wasa , tun Inna tana hanawa har ta zo ta daina .
Har kawo yanzu kuwa shi ka’dai ne Abokin ta Tun da ita
Ba kula en unguwar su take yi ba saboda munafurce munafurcen su ,
a makarantar ma
ta’ki yarda tayi k’awaye
ana son ta sosai da ‘kawance
kawai dai itace ta’ki yarda ,
Duba da yadda yaran suke en gayu
a ganin ta
In ta biye su sai ta kasa godewa ubangiji na na’imomin daya yi mata
gashi kullum in aka je cafeteria sai dai suyi ta biya mata ,
bawai suna complain bane kawai dai itace ba ta feeling comfortable kuma ta san
yau da gobe sai Allah
shiyasa ta ke dodging .
Tun suna mata naci tana zille wa har suka ha’kura suka rabu da ita .Su suna ganin girman kai gare ta Ita kuwa a ganinta bai kamata ta ‘daura wa kanta abunda yafi k’arfin ta ba ,
Matsalar ta ma ta isheta .

Tana wannan tunanin mai Adaidaita sahun ya k’araso cikin layin nasu dake a Anguwar ‘Gadon’Kaya’,
Ita ta nuna ma sa ‘kofar gidan yayi parking daga haka ta fito ta nufi ‘kofar gidan bayan tace mishi ta gode .

Kallo ‘daya zaka yiwa gidan ka san cewa ya da’de kuma yanayin ginin zai sanya ka fahimci bai ma san ma menene renovation ba ,
Katangar gidan both side sun tsatstsage
yayin da fentin ya goge gabad’ayan shi
baka ganin komai sai jar k’asar bulo din ginin ta k’asa k’asan
ta sama kuma ragowar farar k’asar fentin da bata gama gogewa ba Sai zanen yara na shirme wanda akayi da bak’in gawayi .
Normal k’aure ne a gidan sai dai shima ya ji jiki matuka ……
Tana k’arasawa jikin k’yauren ta kama ta tura k’ofar ta kutsa kanta cikin gidan ,Dama tun daga waje za ka gane babban gida ne ,sakamokon yanayin tsayin katangar both side ..
Ta wani dogon soro tabi
kafin ta k’arasa ainihin cikin farfajiyar gidan
A ta farko farko gefen dama babban kitchen d’in gidan yake wanda murhu da kurfeti suka cika shi taf Wanda hakan zai nuna maka kowa girkin shi yakeyi a daban.
Farfajiyar asalin cikin gidan kuwa d’auke yake da part part wajen guda takwas ,
Wasu sabbi k’al ginin zamani
wasu tsofaffi tukuf ginin k’asa
Wasu manya ne domin ko baka shiga ba zaka fahimci wajen d’akuna uku ne ma a ciki da parlourSai kuma masu ciki da parlour,Yayinda wasu kuma d’aki daya ne kawai sai band’aki…..

Ginin dayafi ko Wanne tsufa da k’ank’anta
ta nufa ,tana zuwa dai dai bakin k’ofar ‘dakin ta sa hannu ta d’aga labulen ta shiga ciki da sallama.
Babban d’aki ne Sosai
Da manya manyan taga guda biyu suna kallon juna
sai k’ofar bandaki data ke a chan kusurwar d’akin .
K’atuwar katifa ce kawai a yashe a gefen d’akin,
Sai babban wardrobe d’in katako ,Laidar d’akin bata wani yage ba ammanfa taji jiki dan tayi laushi matuk’a, Kana gani kasan takatsantsan da kula ne ya kawo ta war haka
ba tare da ta fatattake ba .

Wata farar budurwa fara k’al
wadda bazata wuce shekaru sha bakwai ba ce zaune a kan katifar gefen wata dattijuwar mata tana yi wa matar datake a kwance fifita, Tashi d’aya yanayin matar zai baka tausayi dan kana ganin ta zaka san tana jin jiki matuka .
Setin su kuma wani dattijon tsoho ne zaune da wani Yaro a gefen shi wanda ba zai wuce shekaru sha d’aya ba .
Kai kana ganin tsohon kasan ba wai shekarun shi ne suka kai ya Kai haka tsufa ba Kawai dai yanayin rayuwa.
Fuskokin su gaba ‘daya babu walwala Kowa ka kalla a cikin su yayi jigum bama su san Manubiyan ta d’aga labulen ba saida sukaji sautin muryarta data shiga da sallama .

Jidda wadda ke a zaune kusa da Inna ce ta d’ago ta kalle ta Ahankali tace
‘’har kin dawo ?
Sannu da zuwa.’’
Jinjina kai kawai Manu ta iya yi kafin ta juya ta kalli Muhsin
wanda yake mata sannu da zuwa shima ta yi ma sa d’an guntun murmushi ,ahankali ta k’arasa ta durk’usa a gaban Baba tace
‘’Baba Ina wuni.’’

Kmr ba zai yi mata magana ba sai kuma yace
‘’Mai yasa baki ‘dauki kud’in motar dana ajjiye miki ba?
Bana ce miki munada ku’din abun karyawa ba?
Mai yasa kike da taurin kai ne?’’
ya jero mata tambayoyin a jere kafin ya ‘daura da cewa
‘’Ce miki akayi nan da b.u.k ‘din tafiyar wasa ce?”
Ya k’arasa tambayar ta sa ta ‘karshe cike da rashin jin da’di da takaici .

Ahankali ta sunkuyar da kanta ‘kasa
Tace
‘’Kayi ha’kuri baba bazan ‘kara ba .’’

Sai da ya’dan fesar da iska tukunna ya kauda kai gefe ya ci gaba da tunanin dayake yi kafin ta shigo .

Su Jidda ta juya ta kalla kafin tace
‘’Ya jikin nata‘’?
Dakyar sai da ta had’iye wani abu daya tokare ma ta a ma’koshi tukunna tace
‘’Da sau’ki ,Alhamdulillah .’’

Ahankali tace
‘’Allah ya ‘kara sauki.’’
Kamr muhsin zai fashe da kuka haka ya ‘dago ya kalli Manubiyan kafin yace
‘’Adda Manu ,sai da fa ta kuma suma da kika tafi makaranta dazu’’.

Shiruu tayi chan kuma sai ta sunkuyar da kanta ‘kasa ,
Wanda hakan ya bawa hawaye damar fara gangaro mata ,
Haka ita ma Jidda ta sunkuyar da kanta ‘kasa
ta fara nata kukan ,
Ganin hakan ne ya sanya shima Muhsin ya fara nashi kukan.
Haka suka tusa Baba a gaba kowa yana hawaye .

Ahankali ya zaro wayar sa daga aljihu ya danna kiran Ya Musbah ,
Kamar dazu ,yanzu ma wayar a kashe
dan haka ya ‘dago ya kalla Jidda bayan ya maida wayar cikin aljihun malun malun din sa ,yace
‘’Maijidda kikace dazu yace miki
Mu jira shi zai zo ko?’’

Sai da ta ‘dan yi shiru tukunna Ahankali ta gyada mishi kai sannan tace
‘’Eh, Baba.’’

Tsaki yayi daga haka ya mi’ke tsaye yace
‘’Muhsin taso muje .’’

Dasauri Jiddan tace
‘’Baba ka bari ni in sake komawa in dubo sa ba sai kaje ba.’’

Kallon ta yayi kamar bazai ce wani abun ba
Sai kuma yace
‘’kar ki damu
yanzu zamuje mu dawo
InshaaAllah
Ina son ganawa da shi .’’
Daga haka ya juya ya fita
Bayan ya nunawa manubiya gurasar ta da suka ajjiye mata a cikin kwano yace ta tabbatar ta ‘dauka taci .
Yanayin yadda ya mi’ke , da kuma tafiyar ta sa ce zai sanya ka fahimci ashe k’afa d’aya gare sa ,
Domin tashi ‘daya zaka gane ‘dayar ta roba ce .

Tare suka fice shida muhsin
wanda ya fita da sauri ,
domin shi kan sa yaron hankalin sa a mugun tashe yake,Allah Allah yake a san yadda za a yi a kai innar tasu asibiti dan jikin nata ya tsorata kowa
Babba da Yaro .

Suna fita Manubiya ta mi’ke ta cire hijabin jikinta ,
Daga haka ta karasa inda su Innar suke itada jidda,
Sai da ta tabbatar innar bacci takeyi tukunna ta kalli Jiddan tace
‘’Mai ya faru dazu da kika je gidan ,
kin gan sa ?’’
Ahankali Jidda ta share hawayen da suka xubo mata

Kafin ta shiga koro mata
yadda sukayi
Da yadda ya Musbah yace kawai tazo gida su jira sa ,
Gashi kuma har yanzun bai zo ba .

Shiruuuuu
Duk su biyun sukayi
Ko wacce zuciyar ta babu dad’i
Suna kuma tunanin a ina zasuje su samo ku’di
Dan sun san tunda ya musbah ya fara wasar er buya dasu
Tou shima bashi da yadda zai yi ne.
A take zuciyar Manubiya ta fara bata shawarar ta cire kunya kawai ta gayawa Abbakar gaskiya,tasan zai taimake su….

A bakin ‘kofar gidan sa su Baba suka hango sa , in ba an gaya maka ba bazaka yi tunanin yara yi auren fari ba,
fari sol kyakkyawan gaske bai cika tsayi ba Amman yanada fad’in k’ashi.
cikin sanyin jiki Baba da muhsin suka k’arasa inda
Ya Musbah yake Alwallar sallar magrib
Dan ta k’arato ,tare
da wani makwafci kuma Abokin sa
Mai suna ‘ Nafi’u’.
Cike da girmamawa
shi da Abokin na sa
suka gaida Baba.
Kafin Abokin yace wa Ya Musbah
‘’Bara in wuce
In fara karatun kafin ku kammala .’’
Jin jina kai kawai Ya Musbah yayi
Dan gaba ‘daya hankalin sa a mugun tashe yake ,
gashi yaga
Baba
sai wani irin kallo yake ma sa
wanda ya kasa gane ma’anar.

Rashin sanin abun yi da kame kame ne
Ya sa shi cewa
‘’Bismillah Baba
Mu shiga daga ciki ko ?’’

Sai da Baban ya sauk’e ajiyar zuciya tukunna yace
‘’Naa shiga kuwa ?’’
Ahankali Ya Musbah yace
‘’to ko soro ne ka shiga dan Allah
Akwai bayanin da nake so Inyi maka ne ‘’.

Ba dan Baba yaso ba
Ya Kama hannun Muhsin suka bi bayan ya Musbah.

Anan soron kuwa ya shimfide musu tabarma
Dan ayanzu bai isa shigar dasu cikin gidan ba
Yanzun nan makwafcin sa kuma Abokin sa
Nafi’u ya gama musu shara’ah da Baraka
Saboda kawai Jidda ta zo dazu.
Tunda Jiddah ta zo ta ta tafi take ta faman bambami
Wai tazo har gida tayi mata rashin kunya

Sarai yasan k’arya takeyi
Kawai tana neman hanyar da zata bi ta datse zuwan en uwan na sa gidan ne
Gaba d’aya
Bayan a yanzu kamata yayi ma ace shi yake rik’e da Jidda ko Manubiya…..

‘’Tunanin mai kake yi???’’
Muryar Baba ta Katse ma sa tunani.
Ahankali ya sauk’e ajiyar zuciya
Yana shirin yin magana Baban ya sake katseshi ta hanyar cewa
‘’Innar ku har yanzu tana kwance
Ba kud’in magani babu na zuwa asibiti
Musbahu!kai ne ka hanani aikin k’arfi
Sannan kace k’annen ka mata baza suyi Aikatau ba ,
Badaban haka ba nasan da yanzu mun san yadda mukayi
aka kai ta asibiti .
Tun shekaran jiya muke tsammanin ka
Ka kashe wayarka kuma
Kak’i ka yarda kazo inda muke
Idan kud’in ba su samu ba
ai yakamata ace ka zo ka duba mahaifiyar ka ko ?’’

Ahankali cikin yin kasa da murya
Ya musbah yace
‘’Baba, kalli fa k’afar ka bazaka iya aikin k’arfi da ita ba
In ka saka mata nauyi dayawa
kar muje Itama Kwaya d’ayar data rage maka ya zamana itama ta samu matsala ,
Su Manubiya kuma
ba wai girman Kai bane ya sanya na ce baza suyi aikatau ba
A ganina bai kamata ace ina raye muna zaune a unguwa ‘daya
Amman ace k’anne na mata wai su zasu na kula da iyaye na,ba.
Dan Allah Baba kayi ha’kuri
ka bar maganar dakon dakake so kayi
da duk ma wani aikin k’arfi ,
Zan yi k’ok’ari in San yadda zanyi
InshaaAllah zan iya kula da kowa .
Kud’in ma na nemo bawai ban nemo ba
Amman sai jikin baba k’arami yadan mot……’’
Shiru yayi Kafin yaci gaba da cewa
‘’Amman karka damu
Nafi’u yayi wa ‘dan uwan da magana kuma d’an uwan yace
za’a san yadda za ayi
Mu jira shi
zai kawo kud’in ,
Shiyasa ma kaga ban zo ba
bana so in zo muku ba tare da kud’in ba ,
Shi nake ta jira nafi so in yazo ya bani sai inzo
a kaita asibitin ‘’.

Sai a Sannan
Baraka data lab’e musu tun dazu ta shigo cikin soron ,
Ahankali ta k’arasa inda suke ta zauna
Cikin Ladabi ta gaida Baba,
Da Kulawa ya Amsa yana tambayar ta ‘ Ina takwaran sa ‘
tace ‘mishi yana ciki yana bacci ‘.
Da ladabi muhsin ma ya gaida ita
ta amsa
Daganan soron ya d’auki shiru
kafin a hankali sautin kukan Baraka ya fara tashi .

Da sauri Baba yace
‘’Subahanallah
Baraka lafiya?
mai ya faru ? .

Cikin kukan dakyar tace
‘’Ba komai Baba
ba komai Kuyi hkr
Subuce min yayi.’’
Tana gama fad’in haka ta fara k’ok’arin mik’ewa .

Cikin d’an tsare gida Baba yace
‘’Koma , koma
Baraka
Koma ki zauna’’.
Ya Bata umarni
ran sa duk babu dadi .
Ahankali ta koma ta zauna tana d’an satar kallon Ya musbah wanda ya hade rai
Yana ji kmr ya rufe ta da shegen duka.

Ahankali Baba ya shiga rarrashin ta,
Har sai data yi shiru tukunna yace ta fad’a masa
Meke faru wa ,m
Cikin yin k’asa da murya tace
‘dama kwanakin baya ne Ya musbah ya karb’i kud’in ta kuma itama kud’in ba nata bane ba
Na k’awar Maman ta ne
So
Maman tata ta biya rabi, amma ta kasa biyan rabi shine k’awar ta ta tace xataje da en sanda ta tafi da ita ‘.
Tun jiya take bin sa ya bata kud’in shikuma yak’i ya bata ,
yanzu gashi en sandan sunje za’a tafi da Maman ta ‘..

Shiruuu Baba yayi
da jin batun Baraka ,
Kafin ya mik’e tsaye ya kama hannun muhsin,
Ahankali ya kalli Ya musbah ya ce
‘’Musbahu , in an kawo kud’in da akayi maka alkawari ka bata.’’

Dasauri Ya musbah yace
‘’Amman fa baba..’’

Cikin katse sa yace
‘’Bana son musu
Sannan banason ja’inja
Ka bata kawai
Karka damu zan san abun yi ‘’.
Ahankali ya kalli Baraka
wadda tayi kalar tausayi yace
‘’Karki damu ba za a tafi da maman ki ba
Inada mara lafiya a gida , shiyasa bazan iya bin ki muje inga komai ya lafa ba ,
yanzu kiyi sauri ki je wajen ta
Musbahu zai biyo ki da kud’in
InshaaAllah,
In basu cika ba ma
In na san yadda nayi na ha’da kan en kud’ad’e na kashe wutar gaba na
Ki yi min magana sai in cika miki ‘’.
Yana gama fad’in haka yaja hannun muhsin suka fice daga soron .

Cikin bacin rai ya Musbah ya kalle ta kamar zai ce wani abun
sai kuma kawai ya juya ya fice
Ya bi bayan Baba ranshi a mugun bace .

Yaso ya fahimtar da Baba
akan
yayi ha’kuri ya karb’a kud’in ya bar batun Baraka
Amman furr Baba ya’ki sauraron sa karshe ma fadd’a ya rufe sa da shi
Sannan yace ya koma kar Wanda zai kawo ma sa kud’in ya zo bai same sa ba
kuma Wallahi in ya sake karb’arwa Baraka kud’in ta kuma ya hana ta ran sa sai yayi mugun b’aci.


Ganin yadda ran Baba ya b’aci Sosai ne yasa kawai ya Musbah ya ha’kura
Sannan ya ba sa ha’kuri
Daganan
Ya
juya ya nufi hanyar gidan sa .
Bai shiga ba
direct masallaci ya wuce
ana idar da sallar ‘dan uwan Nafi’u ya kawo kud’i kamar yadda yayi alk’awari ,

Ya musbah
Ji yake yi kamar yace wa ‘dan uwan Nafi’un kawai ya bar kud’in ya fasa ranta ,
Domin yasan in yasa hannu ya karb’a kud’in
ya baiwa Baraka
To
bai san ranar biya ba ,
gashi yana tsananin jin kunyar Nafi’u
Dan yana bin sa bashin kusan dubu d’ari kuma bai san ranar biya ba
Yanxu kuma gana d’an uwan sa ya fara hawa kan shi,
Dama saboda yaga na asibitin mahaifiyar sa ne Shiyasa kawai zai karb’a .

Kamar Nafi’un ya san me yake tunani
Ahankali ya dafa Abokin na sa da suka taso tare tun k’uruciya yace
‘’Ka kwantar da hankalin ka
Kar ka damu
Ko yaushe ne in ka samu kana iya biya ‘’.

Sai da ya d’an sauke ajiyar zuciya
Tukunna
Ahankali yasa hannu ya kar’ba kud’in
Wanda ko bai k’irga suba yasan basufi naira dubu goma ba
Yaso

Please Login or Register in order to submit comment