Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fesar da iska kafin ya furta kalmar ‘’so gamon jini’’a fili daga haka ya datse ya kira class rep yace ya tura mass number Abbakar yanzunnan
A ransa yana mai cewa’’ k’iri k’iri Yash sai ya janyo min raini a wajen yaran nan dan yanzu kam babu batun kwana kwana dan ana ji na tambayi kwatancen gida za a fahimci inda muka dosa’’……



Gaba d’aya hankalin Abbakar a tashe yake tun lokacin da
Sir Najeeb ya kira sa ya tambayesa kwtancen
gidan su Manu,ji yake dama bai yiwa sir Najeeb kwatancen ba…tsabar halin da yake a ciki tashi d’aya idanuwan sa suka ka’da suka yi jajawur.
Ya tsani abun da zuciyar shi ta gama aiyyana masa da ya yi
amman kuma bashi da yadda zai yi..ya san abun da yake shirin aikatawa bai kamata ba amman fa zuwa yanzu ya fahimci decision d’in daya yanke kwanakin baya ba shi ne mafita ba don tun kafin a je koina ya fahimci in bai d’au mataki ba tou tabbas hakan na iya zama ajalin sa.
Ba ya so sam baya k’aunar abunda zuciyar sa take tunzura sa akan ya aikata dan ya san hakan bai dace ba amma kuma babu yadda ya iya,dan haka ya d’ago wayar tasa ya bi number sir Najeeb wadda ya kira sa yanzu da ita ya danna call….


Najeeb yana zaune a office d’in shi yana duba wasu takardu Yashjub ya shigo tare da sallamar sa,
Murmushi kawai yayi ya mik’e yana kallon sa kafin yace’’na Manubiya bada kan ka a sare’’

Kallon sa kawai Yashjub d’in ya tsaya yana yi dukda yaji dad’in furucin na sa amman kuma yadda ya gansa ba a shirye chap ba ne ya b’ata masa rai,cikin rashin jin dad’i yace ‘’Najeeb ni da nake tunanin zan same ka a parking lot kalla ko socks babu a k’afar ka balle takalmi sannan duba suits d’inka a gefe!Ina wayarka? Itama nasan sai ka nemo ta ko??’’

Dariya Najeeb yayi sannan yayi sauri ya saka socks d’in ya d’auka suit d’in da takalmin sa ya rik’e a hannu tukunna ya d’au wayar sa da makullin office d’in ya na me kashe computer yace ‘’muje Oga’’ya fad’i hakan yana dariya.

Suna fita a office d’in ya samu ya saka takalmin sa sannan ya rufe office d’in yabi bayan Yashjub wanda ya riga yayi gaba da d’an sauri yana tafe yana saka suit d’in tasa.
Suna shiga motar Yashjub yana shirin yiwa motar key kira ya shigo wayar Najeeb bai d’auka ba dan baya buk’atar takura a yanzu yana so Yashjub ya bashi labarin mai ya faru tsakanin sa shi da Manubiya da ya rikici ya gigice yake buk’atar zuwa gidan su da gaggawa haka,
Ganin an kira har sau biyu bai d’auka ba sannan ga na uku ya shigo yasanya ya zaro wayar yna mamakin waye ne haka..ya
d’anyi mamakin ganin sunan Abbakar da yayi saving d’azun dan haka ya d’auka ya kara a kunnen sa ba tare da ya ce komai ba.

Daga d’ayan b’angaren Abbakar yace’’Assalam alaikom,Sir!d’azu na ji ka tambayeni gidan su Manu ban sani ba ko zuwa zaka yi?’’

Saida Najeeb yad’an juya ya kalli Yashjub wanda ya cilla kan motar ga titi tukunna ya d’an jinjina kai kafin yace’’Eh,muna hanya ma’’
Dum!! Haka k’irjin Abbakar ya buga ya ma kasa magana ya kasa cewa komai..kafin da kyar ya samu yace ‘’yanzunnan suka tafi k’auye gaba d’aya y’an gidansu sai jibi
zasu dawo’’

Shiruu Sir Najeeb yayi yana d’an nazari kafin yace ‘’okay shikenan ma zo jibin in sun dawo’’
Daga haka ya kashe kiran ya juya ga Yashjub wnda yake tambayar sa ‘kai da waye ne’

Shiruu Najeeb ya d’anyi yana so ya fahimci wani abun game da Abbakar kafin kawai ya juya ga Yashjub ya ce’’ba fa sa nan yanzunnan suka tafi k’auye’’

K’iiiiii!!!! haka Yashjub ya ja burki kafin ya juyo a d’an fusace ya cewa Najeeb d’in ‘’kuma shine ban ji ka tambayi wanne k’auye ne ba?ko ka san k’auyen?’’

Shiru Najeeb ya kuma yi yna kallon shi kafin chan yace
‘’In na tambaya zuwa za muyi?’’

‘’Ba tare da b’ata lokaci ba ma kuwa’’
Yash d’in ya ba sa amsa ya na me matsar da motar ta sa gefen titi dan ya tare hanya har ya fara tara goslow.Sannan ya sake cewa Najeeb
‘’Wai tunanin mai kake yi ne ?, ka kira da wuri mana mu samu mu kama hanya time is against us’’ ya fad’i haka yana kammala parking d’in sannan ya juyo ya zubawa Najeeb lumsassun idanuwan sa
Sai kuma cikin fushi sosai ganin Najeeb d’in still shi yake kallo sannan yak’i ya sake kiran wayar yace
‘’Bani number in kira su, bani mana da wuri ‘’ya fad’i haka yana mik’awa Najeeb hannun sa.

Ahankali cikin kwantar da murya Najeeb yace ‘’dan Allah ka d’an nutsu ka sarrafa komai ko da ace na mintuna biyar ne a kwakwalwar ka,saboda ita kanta in ka wanke k’afa ka bita har k’auyen su a haka tou akwai matsala,ka tsaya ka fad’amin abun da ya faru sai a san abun yi, dan Allah.’’


Shiruu Yashjub yayi kafin kawai ya d’auke kai dan in ya biyewa jayayya da Najeeb yaga alamar ran sa ne zai sake b’aci,a hankali ya kwantar da kan sa a jikin seat d’in da yake zaune a kai…sun kusa minti talatin ahaka kafin Yashjub ya gyara zaman sa ya kunna motar ya ja suka koma inda suka fito

Har ya sauk’e Najeeb bai sake kallon inda yake ba haka nan ya juya ya wuce ko sallamar Najeeb d’in bai tsaya ya amsa ba,girgiza kai kawai Najeeb d’in yayi daga haka ya nufi ta sa motar ya shiga yayi mata key shima yayi gaba yana mamakin Yashjub da zazzafar soyyayar Manubiya wadda ya lura ta d’an fara tab’a masa Aboki…

Zuwa yanzu Najeeb ya fahimci k’arya Abbakar yayi masa dan sai yanzu ya tuna suna da exams ma yau da safe around 9 yanzu haka ma maybe sun shiga,but baya so Yashjub ya je wa manubiya a haka dukda bai san me ya had’a su ba, zai bari in Allah ya kaimu gobe sai ya je ya lallab’a Abokin nasa ya fad’a masa me ya faru daganan su san abun yi dan a yadda suka rabu da Yashjub ya san ba zai tab’a sauraron sa yau ba.
Lamarain Abbakar kuma akwai sark’ak’iya.. ya lura Manubiyan kanta tana ji da shi,shiyasa yake so ya nemi bakin zaren yasan abunyi dan yasan in Yashjub ya san wani abun tou abun ba zai yi dad’i ba shi kuma bayaso Yash ya samu matsala da Manubiya saboda wani Abbakar…..


In ban da ciwo ba abun da kan Yashjub yake yi tashi d’aya idanuwan sa suka kad’a suka yi ja ,in da ace zai san inda Manubiyan take da sai yaje.
Kawai dai ya tabbatar tunda Najeeb ya masa haka ba zai tab’a fad’a masa ba shiyasa kawai ya hak’ura ya yanke shawarar ya tafi gida yayi sabon shiri……


Yau ma kamar kullum haka Manubiya ta tartara Abbakar ta zuba a kwandon shara tak’i kula sa.Ya riga ta kammala wa dan haka yana gama submitting ya yi sauri ya d’auke jakarta daga in da ake tara jakankuna ya fice ya tsaya jiran fitowar ta.

A wajen ta same sa yana tsaye yana jiran fitowar ta.
‘’Ba ni jaka ta’’ shine kawai abunda ta ce da shi cikin tsare gida.

Murmushi ya yi ya d’an k’arasa in da take tsaye kafin yace
‘‘Ki yi hkr tou,dan Allah’’

‘’Ba komai ya wuce Abbakar
kawai dai naji haushi ne..bai kamata you of all people ace wai ka b’oye min abu irin wannan ba shiyasa na ji zafin
abun yanzu kuma na huce
so ba komai ya wuce.’’

Ahankali cikin sanyin murya da mutuwar jiki sannan idanun sa akanta kyam yace
‘’Sure?ba za ki tambaye ni dalilin na na yin hakan ba??’’

Da sauri tace’’komai ya riga ya wuce in da bai wuce ba da ko kallon ka ba zan yi ba kai ka san halina tunda har kaga na kula ka tou ya wuce kenan,kuma bana so ka sake yin maganar’’

Ajiyar zuciya ya sauk’e,ahankali yace ‘’Thankyou’’

‘’Um’’kawai ta ce daganan tayi gaba ya bita rike da jakartata a hannun sa suna tafe suna d’an tab’a hira.

Gaba d’aya Abbakar haushin kan sa yake ji na k’aryar da ya yiwa sir Najeeb sannan on top of that gata nan a gaban sa amman ya kasa fad’a mata abun da yayi , shi sai yanzu ma ya yi tunanin watak’ila fa sir Najeeb d’in zai iya ganin su a cikin makarantar kuma tare dan haka yayita addua Allah yasa har su fita kar su had’u da shi.


Kafin su k’arasa gida har sun shirya kamar basu tab’a yin fad’a ba
Manubiya ta lura da waensu changes daga Abbakar tun ba ma da ta ba sa labarin ta da Yashjub na yau ba
dan tashi d’aya taga
gaba d’aya hankalinshi ya tashi kuma ran sa ya b’aci dan sam ya kasa danne kan sa wannan karon,
ta so ta tambaye shi sai kuma kawai ta kawar ta basar da zancen ta sako wata hirar..

Da kyar Abbakar ya dinga yak’e har suka isa gida ya yi mata sallama tare da fatan hutu mai albarka daga nan
ya wuce gida shima.

Dakyar ya iya k’arasawa ya tsaya ya gaisa da maman sa wadda take zaune a tsakar gida daganan ya koma d’akin shi da ke a soro,yana shiga ya tura k’ofa ya sak’ala sakata tukunna ya saki zafafan hawayen da yake ta k’ok’arin dannewa tun a makaranta…bai yi tunanin ba zai iya hak’ura da Manubiya ba sai yanzu,tsananin k’aunar da yakeyi mata ne yasa ya hak’ura yayi saurin had’a ta da Yash.

A ganin sa da lissafin sa na farko Manubiya tafi k’arfin sa sannan kusan age mates suke shi da ita dan ko kwak’kwaran watanni biyu bai bata ba,sannan a kalar matsin rayuwa da wahalar da Manubiya ta sha ya kamata ace ta auri mai arzik’i ta yadda zata kula da kanta da ahalinta itama ta samu ta huta ta ji dad’in rayuwa,shiyasa ya hak’ura da ita dan ta ji dad’in rayuwa kuma ya yi saurin had’ata da Yash dan a tunanin sa in ya had’a ta da wani yaga tana farin ciki tou zai hak’ura ya samu zuciyar sa ta samu salama
sai dai kuma a tashi d’aya a iya yau kad’ai ya fahimci abun ba haka yake ba,kuma ya fahimci ya tafka babban kuskuren da in dai bai gyara ba to shine ajalin sa,
Tun yanzu ya fara shiga tashin hankali Ina kuma ga in soyayya tayi nisa tsakanin ta da Yash….

Yayi kuka ranar kamar ran sa zai fita kafin daga baya ya yi shiru ya shiga duniyar tunanin nemawa kan sa mafita
dan tabbas da sake …..




MANNUBIYA
33

Na
Humayrah Bulama

Mikiya Writers Association.

Manubiya Tana shiga gida ta d’auki kud’in da Baba ya bata na Ammi ta nufi gidan dan bata samu ta tsaya sun yi magana ba d’azun,tana shiga ta tarar da aiki birjik Ammi ta hana d’ayar mai aikin na ta tab’awa dan hadda nata tace ta bar wa Manubiya yau duk ita za ta yi ..punishment d’in lettin da ta yi kenan..haka suka zauna ba wanda ya had’a tsinke tsinke ana jiran Manubiya ta zo ta yi dan Ammi ta fusata yau da lettin da Manubiyan ta yi ba na wasa ba shiyasa ko da Maama ta saka baki wannan karon Ammi ba ta saurare ta ba dan haka itama maman sai ta kyaleta dan ta lura yau matar tijara take ji.

Ba k’aramin tashi hankalin Ammi ya yi ba da ta ji wai su Manubiya za su bar aiki,ba damar ta ce bata yarda ba tun da dai ga kud’in ta an riga an bata..dan haka ta shiga gaggaya mata maganganu ta samu ta d’an rage takaici kuma tace sai ta yi aikin yau,Manubiya so take su rabu lafiya dan haka ta yi aikin ta gama tsaf taje ta yi mata sallama,
Bak’in ciki agun Ammi kamar ta d’aura hannu aka tayi ta kurma uban ihu.
Har k’ofa maama ta rakota matar ta ji dad’in aikin da Manubiyan ta bari dan ta lura Ammi so take ta wahalar da yarinyar dan ko Muhsin k’iri k’iri ta hana sa shigar mata cikin gida in ya zo ko Manubiya baya samu ya gani dan iyakar sa tsakar gidan yayi shara ya tafi,a cewarta ba ta so namiji ya shigar mata cikin parlour da kitchen ba…….



Zuwa yanzu Yassir ya warke garau dan har ya koma office ma.
Ba k’aramin tashi hankalin Mommy yayi ba ganin yadda
Yassir ya k’ulla gaba da Yashjub gashi Daddy yak’i ya sa baki,ta rasa wanne irin dak’ik’in Yaro ne Yassir wanda ba a isa a gaya masa yaji ba,sam ya k’i yarda da ita akan ya hak’ura ya kula d’an uwan sa… ta san muddin Yashjub ya tsame Yassir a lamarin shi Wallahi in ba dakyar ba
sun rabu kenan har abada.

Gashi yanxu ita kanta Yashjub d’in fushi ya d’auki yi da ita gadan gdan tunda ta mare sa sannan ta yi waennan furucin garesa duk akan Yassir,
ko sunanta baya kira
Iyakaci yace mata Ina kwana ko Ina wuni ruwanta ta amsa ruwanta karta amsa.

Ita kanta ta fara data sanin marin da ta yi masa da furucin da ta yi dan gashi sun janyo mata ya k’ullace ta ita gani take yi ma kamar gaba d’aya ya tsaneta
kamar ba uwar data tsugunna ta haife shiba
Shiyasa gaba daya duniyar tayi mata zafi.

Tsakanin Ummi da yaran gidan ma abun ba dad’i sam,d’azu
da safe har bangajeta Kausar tayi ..

Yassir ma ya samu gindin zama a wajen Munirat tun bata kula sa har tazo ta fara kula sa sakamokon nacin da yake yi mata sannan duk wani abun da ya san zai janyo ta so shi to shi yake yi tun bama da ya lura tanaso taga yayi repenting akan abunda yayi ba dan haka ya mai da bata hak’uri d’abi’ar sa ba dare ba rana,kullum sai sun had’u a wajen dining kitchen har back yard binta yakeyi in ta fita shan iska,
ta sake da shi kuwa dan
Munirat irin matan nan ne masu raunin zuciya ga tausayi
kuma Yassir yaci sa’a dan tun a ranar farko kyawunshi ya tafi da hankalinta kulawar sa da tausayin sa sun k’ara ingiza ta
towards him


A ranar da Ummi ta ganta ta fito daga d’akin shi ta ja mata kunne sosai ta kuma hanata shiga d’akin shi
Gaisuwa ta mutunci dai tunda ya nuna yanaso ayi suyi
amma kar ta sake shigar mishi d’aki wannan ba dabi’a mai kyau bace ba

Ita kanta Munirat tayi mamakin yadda ta kasa gayawa Ummi dalilin daya sanya Yashjub ya daki Yassir a wannan ranar
maybe kodan bata so Ummin ta tsani Yassir d’in ne ko kuma tace za ta raba su har abada,
Ita kuma Ummi bata tambaya ba kawai a tunanin ta fad’an su ne ya had’o su shi da Yashjub d’in.
Da Allah ya tashi kama Munirat kuwa ranar Yassir ya biyo ta har d’akin ta akan ta zo suje d’akin sa yanada surprise d’in da zai nuna mata..kawai sai ga Ummi ta shigo d’akin daidai Yassir ya janyo hannun ta mistakenly ita kuma ta fad’a jikin sa.Da kyar Ummi ta yi controlling kanta ta cewa Yassir ya basu waje ya na fita Munirat Tana shirin yin magana Ummi ta wanka mata mari ta rufeta da fad’a kuma tace ta bata sati biyu ta fito da miji ayi mata aure..

Ba abun da ya fi b’atawa Munirat rai irin yadda Ummi ta k’i tsayawa ta saurareta da kuma yadda ta yi zargin wani abun suke yi ita da Yassir d’in.

Munirat taci kuka kamar ranta zai fita dan bayan Ummi ta tafi da kamar awa d’aya ta kira yayarta zata labarta mata amman sai taji itama yayar tata ta rufe ta da fad’a ashe har Ummi ta kirata ta kora mata jawabi sai da tayi mata fad’a sosai tukunna ta kashe wayar ko sallama bata tsaya sunyi ba ..

Ranar haka y’an gidan suka gabatar da dinner d’in su ba ummi ba munirat
Kausar kamar ta zuba ruwa a k’asa ta sha.
Tabbas ta fara hango silver lining ba kamar da da komai yayi musu du d’um ba.

Sai k’arfe sha biyu na dare tukunna Munirat ta sauk’o k’asa ta d’ebi abinci ta nufi sama wasu ma har an saka su a fridge haka ta d’auka ta yi warming a micro wave
tana hawa saman ta nufi hanyar side d’in su kenan taji Yassir yace’’Munirat’’

A zuciye ta juyo amma sai yayi sauri ya rufe mata baki da tafin hannun ya karb’e plate d’in nata ya ajjiye akan centre parlourn saman kafin ya jata zuwa d’akin sa,ko da suka shiga sai da ya sa ta yi masa alk’awarin baza ta yi ihu ba tukunna ya cikata ya cika mata baki ya matsa gefe

Duk masifar da Munirat take ji ta shi d’aya ta b’ace sakamin abun da ta gani ya yi decorating d’akin sosai da candles gashi an rubuta I love you Munirat da ballon’s gwanin ban sha’awa …cikin sanyin jiki yace mata ‘’dama surprise d’in daya ke so ya nuna mata kenan he wants to propose to her amma kuma yarasa a ina zai yi dan ya san ba zata yarda ta bishi suje wani waje ba kuma ba zai yiu ya yi mata a cikin gidan ba,

A hankali ya durk’usa a gaban ta ya yi mata sahihin proposal.

Duk yadda Munirat ta so ta d’an ja aji kasa wa tayi tashi d’aya tace masa ‘yes’ sai kuma ta juya da sauri ta fita
dan duk sai taji wata kunyar shi ta lullub’eta.
Ko abinci nata bata tsaya ta d’auka ta ci ba dan tashi d’aya ta ji ta a koshe…

Tana fita Yassir ya saki wani kalar murmushi a ran sa ya ce
‘’Allah sarki!zuciyar mace bata da wuyar samu,very innocent soul’’
‘’Na san kin sa ta fita ko?so zaki iya fitowa,and next time please ki dai na motsi da k’ofa
wajen yin lek’e dan kad’an ya rage ba ki yi drawing attention d’in ta towards inda kike ba.’’
Yassir ya fad’i hakan ba
tare daya juya ya kalli k’ofar bathroom d’in ba kafin a hankali ya durk’usa ya fara d’auke candles d’in yana kashewa.Dai dai nan Kausar wadda ta fito daga toilet d’in ta k’araso kusa da shi ita ma ta sunkuya ta fara tayashi suna kwashewa suna kashewa tare.

Ganin yak’i kulata ne yasa tace
‘‘Haba dear!wai har yanzu fushin ne?’’
Mik’ewa ya yi fuskar sa ba alamun wasa yace
‘’Kausar!it’s either you talk ko kuma inyi abandoning gaba d’aya plan d’in nan wallahi,kin san dai yin hakan ba k’aramin aiki na bane ba ko?’’

Murmushi ta yi kafin tace
‘’Are you sure?na fa san halinka,take taken ka ma akan yarinyar na gani shiyasa na zo maka da wannan tayin domin mu samu mu jefi tsuntsu biyu da dutse d’aya.
Are you sure zaka iya abondoning mission d’in nan ba tare da ka samu abun da kake so ba?’’

Cikin fushi ya mik’ar da ita yace’’and your are not even jealous!tabbas yanzu na sake tabbatar wa
raina min hankali kika son ki yi..kin ga Kausar i’m your pet
sannan ni ba k’aramin Yaro baneba .
Weeks ago you hate me yanzu
kuma a cikin kwana biyu kawai kin dawomin!.
In kinsan playing d’ina za ki yi saboda wani game d’in ki to wallahi tun wuri ki janye
In ba haka ba this time around zan ba ki mamaki bar ganin wai Ina son ki wallahi I can be your worst nightmare…ba wanchan Yassir d’in da kika sani baneba har yanzu
Yanzu na chanja.

Sannan
kin ce akwai reason d’in daya sa kukayi calling off auren mu ke da Mommy,inaso in ji komai inaso ki fad’amin komai inaso in san menene plan d’in ku dan ba zan yi participating a game d’in da ban san inda aka dosa ba,ba zai yiu ki dinga yi min abu ta bai bai ba,akwai abubuwa da dama dana ke so ki fahimtar dani
If not
kawai inaga gara abar……’’

Hugging d’in shi tayi wanda yasa ya kasa ci gaba da magana,sun d’an jima a haka
tukunna ta d’ago tace
‘’Yassir ba zan iya gaya maka dalilin mu ni da Mommy ba
I’m sorry,na fad’a maka mun fasa ne saboda kai da farin cikinka duk abun da mukayi saboda kai ne
In baka yarda dani ba
na san ka san dai Mommy ba za ta tab’a nemo bak’in cikin ka da hannnunta ba ko
You just need to trust us on this one
Saboda ba zan iya fad’a maka ba.Abu na biyu kuma kai nake so Yassir Ina son ka tun farko
fushin da kaga Ina yi da kai kwanaki kawai Ina yi ne saboda ka bani space a fasa auren mu da gaske, ba za ka tab’a samun abun da kake so ba tare da ni ba
Help us
Ko kuma ince help me
In fitar da Ummi a gidan nan
In gyara tsakanin Daddy da Mommy ta yadda za mu samu mu yi maka gatan da muke son yi maka daga nan sai a yi maganar auren mu,
ka fahimceni?’’


Kanshi tsaye ya girgiza mata kai kafin ya matsa daga inda take sannan ya juya mata baya tukunna yace’’ban fahimceki ba Kausar!not untill you tell me
ko da ace d’an single hint ne,
ba zan tab’a fahimtarki ba in ba gaya min kika yi ba kuma in ban fahimceki ba
ba zan taimake ki ba.

Ajiyar zuciya ta sauk’e kafin ta ce’’shikenan Yassir amma kar ka bari Mommy ta san ka sani dan Allah’’

‘’I promise’’ kawai yace
yana mai juyo wa ya kafeta da idanuwa.


Sai da ta sauk’e numfashi tukunna ta fara magana
‘’Ka san tun lokacin da aka haifi su Yahanasu
Daddy ya bawa Yashjub rabin dukiyar shi ko?’’

‘’Continue’’
Yassir yace yana mai gyara tsayuwarshi

Ahankali Kausar ta ci gaba da cewa’’Da wannan rabin dukiyar da kuma hardwork d’in Yashjub ne suka zama silar da a yanzu haka hatta Daddy bai isa ya kamo k’afar sa a kud’i ba
Bayan estates d’in da muka sani yanada hannun jari a companies daban daban da gidanjen man fetur
Ita kanta Mommy bata san da hakaba sai last two years ta fahimci d’umbin arzik’in Yashjub
Daddy ne kawai ya san komai na sa amma abun da zai baka mamaki last year a will d’in Daddy share d’in Yashjub a company d’in Daddy
50%ne
Na Daddy 18%
Su Yasira su 6 kowa tanada 1% masu hannun jari
dama nasu already 5 ne
Mommy bata da komai ita dama
Mama 20%
naka kai kuma 1%


Da k’arfi Yassir yace ‘’watt??’’

‘’Kwarai da gaske’’
Kausar tace
kafin ta d’aura da cewa
‘‘Mommy ta b’oye maka ne saboda ta san in ka sani ba za ka ji dad’i ba,Yassir
In taji na fad’a maka ba za ta min da sauk’i ba ko su Yasmeen basu san da maganar nan ba Yasira ce kawai ta sani
So karka fad’awa kowa dan Allah
sannan promise me ba zaka yi komai ba

Ahankali yace’’I promise
Cigaba Ina jinki .’’

Cikin son fahimtar da shi Kausar ta ci gaba da cewa
‘’Kasan a tsarin Daddy
In mutun yayi graduating ya fara aiki ma to tsame hannun sa yakeyi a kan sa
kuma tun ba yau ba ya riga ya ce’a cikin ku in kuka riga kuka yi aure
tsakanin sa da ku sai dai ku
dinga kawowa gida dan ya gama baku kwandalar sa,’
Already ya riga ya gama gina Yashjub
Wat about you?
In ka kuskura kayi aure a yanzu shikenan ka tashi da 1 percent da company d’in ka wanda banajin a shekara ma yana kawo maka

Please Login or Register in order to submit comment