Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta tafi,
dan haka ya k’arasa da sauri ya tare gabanta.
Kasa magana ta yi dan haka kawai sai ta kawar da kanta gefe.

Cikin sanyin murya yace ‘’i don’t mean to…ki yi hak’uri,ba zan sake rik’e miki hannu ba yanzun ma mistake ne..let’s start a fresh
InshaaAllah bazan sake ba.’’
Ya fad’i hakan yana kallonta shi kanshi yana mamakin yanda ya koma,dan sam bayar da hak’uri baya cikin tsarinshi bai ma iya ba amma a iya yau a iya shigowarta office d’insa kawo yanzu ya bata hak’uri yafi ak’irga.


…….’’sam basuyi kama da d’ayar ba dan tama fi kama da y’an china,har gara ma d’ayar ita sun d’an yi kama maybe ko cousin d’in shi ce,to Itakuma d’ayar fa wacece?dan sarai ta lura da yadda idanuwanta suka cicciko da suka had’a ido,wacece ita?su waye su?
sannan wacece Mommy!?
dan ta tabbatar inda ace wadda aka ambata da Mommy mahaifiyar sa ce to da bazai k’i tsayawa ya saurari abunda sukazo takanas fad’a masa akanta ba’’…..
Manubiya ta fad’i hakan a cikin ranta.

Tunanin ta ne ya katse jin yace
‘’Mannubiya’’
ahankali


Ajiyar zuciya ta sauk’e tukunna ta d’ago ta d’an kalleshi.
Kalar tausayi yayi mata kafin yace
‘‘Plsss’’
Ya fad’i hakan yana k’ok’arin durk’usawa a wajen

Batasan lokacin da ita kanta tace’’a’a pls kar ka sunkuya’’

Ba tare da ya damu ba yace’’ai bakice ya wuce ba’’
Ya fad’i hakan yana me durk’usawa a gaban ta

Gaba d’aya kunya da takaicin kanta ne suka lullub’e ta batasan lokacin da tace’’ya wuce!nima sai yanzu na lura baka ma sani ba,dan Allah ka tashi’’

Murmushi yayi kafin ya mik’e a hankali yana kallonta sannan yace’’ashe dai ana so na!’’

Da sauri ta runtse idanunta a ranta tace ‘’Tabbas Ina sonka Yashjub!’’

Dariya yayi kafin yace’’dole ki runtse ido mana’’

Ahankali ta sunkuyar da kanta k’asa ta yi shiruuu,kafin chan tace’’wacece Mommy?’’


Murmushi yayi Ahankali yake kallon fuskarta yana karantarta yana jin wani sanyi yana ratsashi….


Sai da ta sake cewa ‘’um?’’

Tukunna yace
‘’Sisters d’ina ne dukkan su,
Mommy kuma is my mom.’’

Bai bata damar cewa komai ba
Yace’’mu bar wannan maganar,let’s talk about us’’

Ahankali yaji tace
‘’Kuma ita ta haifeka?’’

Lumshe idonshi yayi ya bud’e tukunna yace’’ki bar maganar mana,um??’’


Girgiza kanta kawai tayi
Kafin tace’’kawai naga yadda kayi ne
Kamar baka wani damu ba
which is wrong
Nasan bai kamata in shiga cikin personal issues d’inka ba
amman uwa ta fi k’arfin wasa,
Indai har wadda suka kira da Mommy mahaifiyarka ce to a gaskiya abunda ka yi bai kamata ba.
Ni yanzu haka so nake ace Innata ta turo wani ya bani sak’o ko mu yi magana baki da baki ma da ita
amman ba ni da damar yin hakan.
Shawara ce nake baka
although nasan nayi maka shishshigi amman i can’t help it tunda abun ya shafi uwa
dan babu abunda yake b’atmin rai kamar inga ana d’aukar mahaifiya ba da muhimmanci ba
So
dan Allah if possible ka yi k’ok’ari ka gyara hakan,
Once again ka yi hak’uri in nayi crossing line d’ina.’’


Shiruuu kawai yayi yana sauraron ta tunda ta fara har ta dasa aya.

Jin yayi shiru yasa ta d’an d’ago ta kalleshi…ganin ya yi shiru ya kafeta da idanuwa ne yasa ta d’an kauda idanunta daga garesa a hankali.

A lokaci d’aya ta ji ya sauk’e ajiyar zuciya kafin yace
‘’Thankyou!inshaaAllah na yi
miki alk’awarin zan gyara,
Kawai dama mun d’an samu issue ne amman inshaaAllah
komai ya wuce daga yau
I promise.
And
Kar ki sake cewa kinyi crossing line d’in ki a cikin rayuwata ko personal life d’ina saboda Mannubiya kece rayuwar tawa
duk abunda ya shafe ni ya shafe ki
Inaso kiyi kutse ki shiga ki yi duk yadda kika ga dama dan tabbas in kikayi hakan zai sanyani farin ciki.
A yanzu’Yes’d’inki kawai nake jira daganan in mun zama d’aya komai nawa ya zama naki.
Na dad’e da gama tsarawa matata itace ni
nine ita.
I just hope zaki bani chance d’in da zan nuna miki how much I love you …….’’


Manubiya ji take yi kmr ta ce mishi’’itama tana son shi amman tana buk’atar shawara dasu Jidda kafin tace komai dan ita kanta tasan kuma tana gani kamar Yash yafi k’arfinta amma still tana buk’atar shawara da wani
wanda zai bata go ahead saboda abunda take so d’in kenan.

Abu na biyu kuma ko da ace zata ce masa tana son shi harga Allah baza ta iya kallon cikin idonshi ayanzu dai ta fad’a mishi ba
dan wata tsananin kunya kwarjini da girman sa take ji take kuma gani

Abu na uku kuma abunda yayi mata yanzu ta ji zafi dukda kuwa ya bata hak’uri kuma ita kanta ta lura dagaske bai sani d’in ba amman tanaso ta sake jaddada mishi sannan su fahimci juna sosai
‘Ko bakin hijabinta bata yarda ya sake tab’a wa ba’….’’


Dan haka kawai sai tace masa
‘’Ones again mun gode kwarai
bari in wuce gida’’

Murmushi kawai yayi yayi yace
‘‘Okay your majesty!duk yadda kikac,
In kai ki?ko in saka a maidake?’’
Yayi mata tambayar yana mai tsare ta da idanuwa.

Ahankali ta girgiza kai kafin tace’’na gode’’ daga haka ta juya ta wuce


Numfashi ya fesar kafin yace
‘’Ina jiran yes d’in ki’’

‘’Tsayawa tayi ta kasa gaba ta kuma kasa juyowa’’

Bata san lokacin da ya matso kusa da ita ba saida taji maganar sa a setin kunnenta
ahankali yana cewa‘’pls dear,don’t keep me waiting‘’

Da sauri ta yi gaba ta fice daga office d’in tana mai sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya……


Shima ajiyar zuciyar ya sauk’e sannan ya fesar da iska yana wani sihirtaccen murmushi kafin ya koma ya zauna a fili ya ce ‘’Alhamdulillah’’

Kamar wanda ya tuna wani abun haka ya mik’e ya bi bayanta da sauri…..sai da ya nemi adaidata sahun data kwanta masa ya sakata tukunna hankalin sa ya kwanta…hkanan suka rabu kamar basa so bayan ya ce mata akwai special sister d’insa da zata kirata mai suna Yahanasu.

Saida suka k’ule ya daina ganinsu tukunna ya juya ya koma office d’in shi,shi kad’ai sai faman blushing yakeyi


Ba drivers ba hatta securities d’in company d’in nashi sun sha mamaki yau,dan haka sukayi ta y’an kuskus d’in su a tsakani shikam Yashjub bai ma san sunayi ba.

Sai da suka yi nisa da company d’in tukunna Manubiya ta samu ta shak’a sanann ta fesar da wani bahagon numfashi,dan tun d’azu ji takeyi kmr an shak’e ta,gaba d’aya kunya!k’auna!shauk’i!da asalin mamakin Yash sun hanata sukuni…

Yashjub yana zama a office aikin Yassir wanda ya saka a gaba ya d’an tab’a,kafin daga baya ya fad’a duniyar tunani ya kuwa dad’e yana lissafe lissafein sa kafin ya mik’e ya fice daga company d’in gaba d’aya dan dama saboda Mannubiya ya zo yau…..



A b’angaren su Kausar kuwa suna fita ta sami gaban company d’in chan da d’an nisa ta yi parking.
Kallonta kawai Yassira takeyi
tana mai jin wani tsananin tausayinta ya lullubeta a lokaci guda kuma tana data sanin gaiyyatar ta da tayi dan inda ace ta san za su yi wannan mugun ganin da ta zo abinta ita kad’ai sun tattauna ita da Yash d’in akan Mommy sun magance matsalar iyaka su biyu’ba zai yiu ace ta zuba ido tana gani yana gaba da uwar su ba’.
Ta lura da yadda Kausar d’in ta ci uban kwalliyar da ita kanta ta ma manta rabon data ga tayi kwatan kwacin ta,gashi ta zo ko kallonta Yash d’in ma bai yi ba,gashi kuma sun yi mugun gani…..
Yassira tana cikin wannan tunanin ta ga Kausar d’in ta zaro wayarta.Wani cleaner wanda suke shiri kuma suka shirya akan zai ke fad’a mata shige da ficen Yash!ta kira.

Yana zuwa ya fara sosa k’eya bayan sun gaisa yayi shiru ya sunkuyar da kanshi k’asa dan tun a ranar da yaga Manubiya tazo an kaita har office d’in Yash ya kamata ace ya kira Kausar d’in ya sanar da ita a yadda suka tsara amman kawai shi baya son wannan harkar ne dan ya zama kamar munafurci da cin dunduniyar Yash kenan
Mutumin da wani lokacin in wata ya k’are har k’ari yake musu akan salary d’in su.

‘’Ka san laifin ka kena’’
Muryar Kausar ta katsewa cleaner d’in tunani

Murmushi yayi yad’an sosa k’eya ahankali yace
‘’Afuwan hajiya!na d’an yi
tafiya ne nima yau na fara ganinta da na tambaya shine aka cemin ai ta d’an kwan biyu’’


Sarai Kausar ta fahimci k’arya ya shirga mata,shiyasa tace‘’Ina da recording d’in wayoyin da muka yi ni da kai,
ba zan damu ba dan Yash yasan me nakeyi
dan in baka bi min yarinyar chan ka ganomin gidansu ba
tou zan kwashe komai in tura masa.’’

Da sauri yace ‘’ki yi hak’uri dan Allah,inshaaAllah zan bi ta,yanzu ma kuwa.

‘’Ka d’auko min number gidan adress d’in ta da sunanta da komai’’

Dasauri yace
‘’To to,angama…’’

Kafin ma ya gama amsawa har ta kunna motar,bata sake bi ta kansa ba ta figi motar suka wuce.

Sai a lokacin Yassira wadda tun d’azu ta kumbura sannan al’ajabi ya rufeta ga kuma tausayin Kausar d’in
Tace
‘’Kausar!me za mu yi da adress d’in ta?
Kin dai san duk abunda kikaje kikayi mata zata gaya masa ko??
Besides ba ajin mu bace,sannan bai kamata ace
mun tsaya muna chachar baki da wannan yarinyar wadda banajin ta kai sa’ar Yusra ma.Kuma in ya sani ko ya ji labari ina fatan kin san kashinki ya bushe ko?
Ki duba ki gani dai yadda duk ya burkice ya rikice yake ta faman lallashinta
saboda ya ga tana hawaye….’’


Mahaukacin burkin da Kausar ta ja wanda sai da Yassirar ta buga kanta kad’an ne yasanya ta yi shiru,dama Yasira a zuciye take kuma ranta a mugun b’ace yake ‘na ganin Manubiya da tayi’ dan haka ta d’ago tace’’Girl!re’u crazy!,kallifa ya…’’


Maganar ta ce ta mak’ale sakamokon hawayen da ta gani ya fara zubowa ta idanun Kausar d’in,shiyasa gaba day’a sai tausayinta ya lullub’e Yasirar….tabbas ko da ace itace
take da saurayi yayi budurwa kamar wachchar yarinyar dasuka tarar a office d’in Yashjub
to it’s either ta hak’ura da shi ko kuma ta bi ta ko wacce hanya ta rabasu,dan ita kanta tunda ta ganta tashi d’aya sai da ta raina kanta ga wani kishi da yabi ya lullub’eta tashi d’aya,Ina kuma ga ga Kausar
Allah kad’ai ya san mai take ji
bata riga ta samu attention d’in Yashjub d’in bama gashi har wata ta yi wuff da shi,dan a iyakar abunda ta yi witnessing yau tabbas ta san sunada aiki jaaa!a gaban su.

‘’Yassira har mu je gida kar ki sake cewa komai
Dan Allah’’
Muryar Kausar ta katsewa Yasirar tunanin.
Tana gama fad’in hakan ta ja motar da gudu suka wuce.

Suna zuwa gida ba ta ko kalli Yasira ba ta bud’e motar ta fice ta wuce sama direct side d’inta ta nufa zuciyarta tana wani irin tafarfasa.Tana shiga parlournta ta yi cilla da wayarta da d’an ficicin vail d’inta ta fara kai kawo tana safa da marwa sai kuma
ta fara d’aukar abubuwa tana farfasawa.Wanda hakan ya janyo hankalin Mommy dan
haka da nufi side d’in nata.

Tana shiga ta zaro ido waje sai
kuma ta k’arasa inda Kausar d’in take ta rik’eta cikin tashin hankali tace
‘’Lafiyar ki kuwa?’’
tayi mata tambayar tana mai shafa fuskarta wadda ta yi jajawur idanunta sun sake k’ank’ancewa tsabar tashin hankali tama kasa magana,so take ta yi kuka sosai amma ta kasa hawayen ma ya k’afe…

Suna tsaye a haka Yasira ta iso,tun daga bakin k’ofar ta fara cewa’’Kausar bani takardun nan akwai wanda yake jirana a office kins…’’
Maganartace ta mak’ale sakamokon kutso
kai da ta yi cikin parlourn.Da sauri tace’’Ya subahanallah!’’sai
kuma ta k’arasa inda suke tsaye su duka…tana zuwa ta yi hugging Kausar d’in,ahankali
cikin son kwantar mata da hankali tace ‘’kar ki damu za mu nemo mafita’’

Hakanan Mommy ma ta shiga rarrashin Kausar d’in dukda bata san dalili ba amma dama tunda Yassira tace mata ‘’za su je office d’in Yash itada Kausar tasan za a rina’’.


Suna nan tsaye wayar Kausar ta d’au k’ara

A hankali ta janye jikinta daga na Yassira ta koma gefe ta durk’usa ta d’auki wayar tata
wadda ta farfashe dan tana shigowa dama da ita ta fara yin cilli.Ganin mai kiran nata ne yasa ta d’auka
ahankali tace ‘’ina jin ka’’

Daga chan d’ayan b’angaren yace mata’’gani nan yanzunnan aka ajjiyeta a k’ofar gidan nasu ta shiga’’daganan ya fad’i mata adress da number gidan yace ‘’bai samu
sunan yarinyar ba dai amman
yana kan bincike.’’



‘’Tam’’kawai Kausar ta iya cewa daganan ta zare wayar daga kunnenta ta kashe sannan ta shiga contact d’inta


Zuwa yanzu Yassira ta fahimci da wa ta gama waya dan haka ta matsa ta ce mata’’Kausar me za ki yi ne??’’

Dai dai nan ta kara wayar ta a kunne tace’’Hello!na’am…zan turo maka adress d’in wani gida yanzu!inaso ku je duk wata budurwar da bata kai 25 ba a gidan ku yi resetting d’inta….’’

A zabure Yassira ta wafce wayar ta yi jifa da ita
cikin fushi tace’’Eh!lalle zuciyarki kam ta kama da wuta kuma baki da hankali!

Cikin rashin fahimta sannan a d’an tsorace Mommy ma ta
matso ta d’an rik’e hannun Kausar d’in sannan tace
‘’Kausar!su wa kika bada order a kashe??yaushe kika fara harka da y’an daba ba mu saniba????’’



Ba tare da Yassira ta kalli Mommy ba tace’’matar da Yash yake so zai aura take so a kashe saboda mahaukaciya ce ita’’ta fad’i hakan still idanunta na akan Kausar d’in.

Sai a sannan Kausar ta d’ago ta kalleta itama tukunna tace’’ kina da wata idea d’in apart from ‘ku bani hak’uri ku ce za a san abun yi’bayan wannan ???ki fad’a min in akwai wata mafitar da ta fi wannan
yanzu inaso inji’’


Cikin takaici da tsananin b’acin rai Yassira tace’’ban tab’a tunanin abun naki ya kai har haka ba!ban tab’a tunanin za kiyi going far har izuwa haka ba!Kausar kin san menene rai kuwa??a kan Yashjub wanda idan Ubangiji bai rubuta mijinki bane ko sama da k’asa za ta had’e baki Isa ki auresa ba shine zaki d’auki jinin bama mutum d’aya ba?tunda bamu san y’an mata nawa ne a gidan ba.’’
Runtse ido Yassirar ta yi ta tsaya da magana saboda yadda al’amarin Kausar ya k’ulle mata kai ya bata tsoro gaba d’aya yasa kanta har wani jujjuyawa yakeyi.Sai da ta d’an dawo daidai tukunna ta bud’e idanunta ta kalli Kausar ido cikin ido tace’’ki saurara ki kasa kunne ki jini da kyau!
Ina mai shawartar ki!
had’e da gargadi!
mai tafe da zazzafan warning!da kuma threat!na rantse da Allah in wani abun ya sami Yarinyar nan
da bakina zan fad’awa Yash komai sannan babu ni babu ke har abada!dan ban shirya zama a k’ark’ashin inuwa d’aya da murderer ba.
In ba ki nutsu kin dawo hankalinki ba za ki rasa komai kuma za ki rasa kowa…duk tak’amar ki da kuma isar ki baki kai Yash ba dan haka inaso ki saka a ranki cewa’idan kika kashe ta da shi za ki yi shari’ah!’.Kar ki lalata rayuwarki da hannun ki wannan zafin da kika d’auka babu in da zai kai ki sai garin dana sani,mu d’in da muke ce miki ‘ki yi hkr ki bi komai a hankali za a nemo mafita’ mu ne
masoyanki kuma mun fi ki gaskiya.
Ki nutsu ki yi lissafi ki ga yadda duk iyakar k’ok’ari muna yi
amma sai da yayi budurwa gashi har ana maganar aure bakisan menene a k’asa ba dan haka mu bi komai a hankali a nemo mafita
amman kashe ran d’an Adam sam ba namu baneba.

I’ve been standing by your side throughout amma wallahi Kausar idan kika zarce iyaka na fad’a miki na sake maimaitawa
Ni da ke pam!pam!!pam!!!’’.
Ta fad’i hakan tana mai karkad’e tafukan hannayenta duk biyun.


Jinjina kai Kausar ta yi cikin b’acin rai tace
‘’Tabbas a yau Yassira nasan cewa blood is thick!’’

Cikin tarar numfashinta Yasira tace‘’this isn’t about blood Kausar’’


Cikin fushi Kausar tace
‘’To dan mai yasa kike taking side d’in sa?bamafa ki san wannan yarinyar ba amman it felt like you like her,kuma na tabbatar farin cikin da kika gani a fuskar d’an uwanki ne yasanya kika fara sonta da har kike tunanin kareta.Na san banida kowa Yassir amman ban yi tunanin I’m this alone ba
sai yau’’


Matsowa yassira tayi ta kama kafad’unta tukunna tace
‘’Kausar wallahi yadda kika tsani yarinyar nan nima haka na tsaneta abu d’aya da nake so ki gane shine
No mattaer what bazan tab’a goya miki baya kiyi abunda kike shirin yi ba,kuma in har kika aikata hakan do you know what that means???’’
Bata jira jin amsar Kausar d’in ba tace
‘’It means kin tsorata,kin ji tsoronta kin yi giving up
kin san ta fiki da komai
kin yarda babu ta yadda za’ayi ki iya kwace sa daga hannunta’’


Ahankali Mommy wadda tun d’azu tayi shiruuu kawai tana kallonsu tace’’bari I’m je kiran Daddyn ku shi ne ya kira ni na
na fito,Ina zuwa yanzu zan dawo’’

‘’Tam’’kawai Yasira tace daganan ta ci gaba da cewa Kausar’’ita mace ce kema mace ce
Fight her
Destroy her
That
I’ll stand by you
Kausar through thick and thin
amman wannan tunanin naki
Is morethan horrible’’
Ta k’arashe maganar tata a hankali.


‘’Wanne tunanin nata ne is morethan horrible?and what
exactly happen inhere??’’
Yassir wanda shigowar sa kenan ya fad’i hakan yana bin parlourn da kallo.

Ahankali Kausar tace
‘’Nothing’’
Sai kuma ta juya da sauri ta wuce d’akin ta ta rufe k’ofar.

Ya jima yana kallon k’ofar d’akin nata kafin ya furzar da iska ya k’araso ciki inda Yassira take ya tsaya yana kallon ta.

Ajiyar zuciya ta sauk’e kafin tace’’na yi tunanin ka na office,na ji Daddy yace ka samu contract,me kake yi a gida??’’

‘’Yasira yau fa Sunday tun jiya na gana abubuwan da nasan a important yau kuma
P.A d’ina yana chan,
I need to rest
he can handle everything’’
Yassir ya faiyyace mata hakan kansa tsaye.

Cikin rashin jin dad’i Yasira tace’’Yassir wannan dalilin fa yasanya Daddy ya fi bawa Yashjub jari saboda ya san ko an baka asara ne saboda Allah kalli yanda ka tarwatsa company d’inka in banda ci baya ba abunda yake yi kullum
sannan ka d’an samu contract dakyar amma ji yadda kake miss using d’in sa?
I’m so sorry to say this to your face
But you are very lazy…’’

‘’Am,Yassira!me ya faru da Kausar??me kuke tattunawa kafin na shigo?’’
Yayi mata tambayar yana mai gyara tsayuwar shi.


Fusata Yassira ta yi ganin
Yanda k’iri k’iri ya gwale ta
ya ma k’i sauraron ta
dama ga takaicin Manubiya da Kausar shiyasa cikin fushi
tace’’Y don’t you go and ask her yourself !!!
Daga haka ta bangaje shi ta fice.Ta nufi d’akin Mommy da
niyyar jiranta ta dawo daga d’akin Daddy su yi magana
amman sai ta ganta a d’akin nata a zaune ta zabga uban tagumi.

Ta d’an yi mamaki but sai ta kawar kawai tace
‘’Mommy sai kin bud’ewa Kausar ido fa!kar ta je tayi wani shirmen,ganin
wannan yarinyar da tayi ya haukatata
Ni kaina na tsorata Mommy
dan in dai wannan ce yarinyar da ya ke so zai aura
I don’t think we stand a chance
sannan ga dukkan alamu yana tsananin santa! na manta rabon da in ji Yash yana bada hak’uri but in kinga yadda yake lallashinta
za ki yi mamaki,in dai har ta
shigo gidan nan
To a idanunsa da mu da kashi duk d’aya
dan na san ita kawai zai dinga gani….we have to do something but first ya kamata ki tsawatarwa kausar wannan
shirmen nata is not the best idea …’’




MANNUBIYA
47
Na
Humayrah Bulama

Mikiya Writers Association.

Ahankali Mommy tace
‘’InshaaAllah I’ll talk to her
amman Yassira ban ji dad’in yadda kika yi mata magana ba yau sam,language d’inki is very bad’’.

Ajiyar zuciya Yassira ta sauk’e kafin ta nemi guri ta zauna a gefen Mommy tace
‘’zan bata hak’uri Mommy,but
ya kamata mu fara nuna mata kuskurenta tukunna.I love her shiyasa kika ga na yi mata haka
Kinga na farko abunda take shirin yi bai
kamata ba

Abu na biyu Mommy ni kad’ai na san abunda na gani a kwayar idon Yash game da Yarinyar nan,idan Kausar ta yi gigin raba ta da duniya
wallahi ba ita ba bincike in ya biyo har ta kanmu to mu da shi har abada sannan kashin mu ya bushe har ke kanki

A ganina
gwara ya tsaneta da kansa cikin sauk’i tsana ta har abada instead of ya tsanemu tsana ta har abada saboda ita.’’

Dafe kai Mommy ta yi tukunna tace’’Kausar bazata yi komai ba inshaaAllah,Yash kuma nace muku ku barni da shi
da shi da yarinyar ku bar ni da su.Yanzu ki je abunki ina buk’atar hutu sosai ki koma office kince ana jiranki.

Shiruu Yasira ta yi tanajin wani kalar tausayin mahaifiyar ta su yana lullubeta
ace wai d’anka ba ya kulaka
zai yi aure bama ka saniba sai y’ar kishiyarka ya gayamawa.
Sannan yanzu ga Kausar ta sake d’aga mata hankali….shiyasa dole ta shiga damuwa.
Har Yasira ta mik’e zata fita sai
kuma ta koma ta rungume Mommyn,sun jima a haka tukunna ta cika ta ahankali tace ‘’komai zai gyaru Mommy,inshaaAllah’’
Ahankali Mommyn tace
‘’Nagode Yassira Allah ya miki albarka’’
Murmushi
Yassirar tayi
tukunna ta cikata tace’’ameen,sai na dawo’’daga haka ta fita
A ranta tana adduar Allah ya kawo ranar da Mommy Yash Daddy za su had’a kai su so
juna su k’aunaci juna komai ya s dawo dai dai Family ya gyaru yayi dad’i……




A b’angaren Yassir kuwa
Yassira tana fita ya k’arasa k’ofar d’akin Kausar da niyyar shiga amman sai ya ji ta a rufe
dan haka ya sake tabbatar wa
kansa
‘Tabbas akwai abun da Kausar take b’oyewa’
Amma kuwa in ta yi masa haka ta yi mugun janyowa kanta bala’i da masifa….
Bai bar bakin k’ofar ba sai da
ya gama tsara abunda zai yi
‘Zai jefi tsuntsu biyu da tarko d’aya’
Tsuntsun farko…zai kawo k’arshen matsalarsa.
Tsuntsu na biyu kuma…zai fallasa masa Kausar ya gano abunda take b’oyewa dan ya san indai har da gaske Kausar son Yashjub take yi kamar yadda ya ke zargi
to
tabbas in ta ji labarin mutuwar Yashjub sai ta yi haukan da zai fallasa ta b’aro b’aro.

Ta hakan ne
zai gane gaskiya
a daina playin nashi as a fool
daga nan kuma ya ci ubanta for toying with him
sannan ya aureta
ba yadda ta iya ……



Ko gida Manubiya ba kai ga k’arasawa ba Yahanasu ta kira ta…tashi d’aya kuwa ta ji Yahanasun ta kwanta mata itama Yahanasu nutsuwa da hankalin Manubiya yasa ta ji ta k’ara sonta,sun d’an tab’a hira daganan ta taya d’an uwanta campaign kafin suka yiwa juna sallama.

A k’ofar gidan nasu aka ajjiye ta kamar had’in baki mai adaidaita sahun yana wucewa tana shirin shiga gida ta ji an kira sunan ta dan haka ta juya.Murmushi ne ya wanzu akan kyakkyawar fuskarta sakamokon had’a idanu da suka yi da Mama.
Sai da ta gaida ita ta amsa tukunna Maman tace’’ki yi hak’uri nima kwana biyun nan ban ji dad’i ba shiyasa ban samu na shigo na duba innar ta ku ba.

Murmushi Manubiya ta yi tana mai jin k’aunar matar tana ratsata a lokaci guda kuma tana mamakin tsananin kamar ta da Yashjub kafin cikin kwantar da murya tace
‘’Allah sarki!Allah ya baku lafiya gaba d’aya
Innar ma nasan bata nan dan ba lalle sun dawo ba amman mu shiga dai mu duba’’
Daga haka suka wuce tare bayan Mama tace ‘’ameen’’

Sai da ta yi sallama ta shiga tukunna Maama ta bi bayanta itama ta shiga bakinta d’auke da sallama.
Da ikon Allah kuwa har sun dawo dan’a wata na’ura
kawai aka saka innar aka fitar’
amman Dr Sofia tace ‘’ta mayar da therapy d’in sau biyu a rana and su kwantar da hankalin su ba wata matsala saboda abun nata ma ashe minor ne so anytime zata warke in an bata kulawar da ta kamata.’’

Manubiya ta yi mamakin yadda ta gansu a zaune gaba d’ayan su sunyi jugum har ya Nafi’u,bata gama nazartar su ba aka fara gaisawa da Mama
wadda hankalin ta ya tashi matuk’a daga ganin jikin inna dan sam ba ta yi tunanin jikin nata

Please Login or Register in order to submit comment