Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bai yi murnar barin su aiki a gidan Ammi ba kamar yadda ya yi murnar saka shi a makaranta da za ‘ayi.Tun daga lokacin da ya ji zancen kuwa..in dai ya san sunan abu da turanci to fa ba zai fad’a da Hausa ba,murna da shak’iyanci kala kala haka ya dinga yi ya yi ta saka su dariya da walwala kuwa
dan wunin ranar haka suka kasance cikin farin ciki wanda hakan ne ya taimakawa Manubiya ta samu fargaba da tunanin had’uwa da Yash gobe ya d’an yi skipping mind d’in ta.



Da ikon Allah yau har aka fara gabatar da dinner su Yasira ba suyi wa Ummi rashin d’a’a ko kallon banza ba wnda hakan ya riga ya zama d’abiar su..dan in dai suka had’u to wajibi ne ta fuskanci rashin mutunci daga gare su.Ba su gaishe ta ba kuma Daddy bai ce su gaishe tan ba kamar kullum,haka ake kan gabatar da dinner d’in,ta ji zafi kuwa amma yadda ta yi alk’awarin fita harkar Daddy da ya’yan sa ne ya sanya ta tartarasu ta zuba a kwandon shara.Sai da aka kusa kammalawa tukunna Yassir ya sak’k’o k’asan,Daddy kawai ya gaisar daga nan ya cewa Yusra tayi serving d’in sa,a hankali Munirat ta d’an d’ago ta kalle sa ai kuwa suka had’a ido,murmushi yayi mata daga nan ya d’auke kai da sauri gudun kar Kausar ta kama sa..

Ahankali duk suka shiga watsewa har dining d’in ya rage daga Yassir sai Daddy, Ya’isha da Yash.

Yassir yana shirin tashi
Yash yace ‘’Days ago na je d’akin ka kana bacci’’

‘’Yeah’’kawai Yassir d’in yace ba tare da ya kalli inda Yash d’in yake ba daga haka ya mik’e da niyyar barin wajen gaba d’aya.

Har ga Allah Yash ya d’an so su fahimci juna a kan abun da ya faru amma attitude d’in da Yassir yayi masa ne yasan ya ya fasa,dan haka cikin b’acin rai yace’’ban gama da kai ba’’

Still ba ta re da Yassir d’in ya kalli Yash ba yace’’good 9te,Daddy’’.

A zuciye Yash ya mik’e amma kafin ya yi wani abun tuni Daddy ya tsaida shi ta hanyar ruk’o hannun sa da sauri ya maida shi ya zaunar da shi.
Hakanan Yassir ya sa kai ya wuce,yana wucewa Ya’isha ma ta yi musu sai da safe ta wuce..

Dakyar Yashjub ya d’an yi
controlling kan sa tukunna ya bawa Daddy labarin abun da yafaru wanda har ta kai sa ga dukan Yassir d’in.
Sannan ya d’aura da cewa’’ ya kamata Yassir ya bar cikin gida haka tun kafin a samu matsala’’.

Cikin son fahimtar dashi Daddy yace’’Yashjub,kai ne ka ce Yassir ya dawo cikin gida,bai yi ja’in’ja da kai ba haka Yaron nan ya yi maka biyayya duk da baya so amma haka ya hak’ura ya dawo ya zauna duk dan a zauna lafiya..kaga kuwa in ka ce sai ya sake komawa wajen ka yanzu a gaskiya ba ka yi adalci ba Yash,besides i don’t think bayan abun da ya faru a tsakanin ku zai yarda ya dawo ku zauna tare.
Yayi min maganar kafin kai kayi,ka kwantar da hankalin ka zai bar cikin gida amman sai nan da three months in an gama masa nashi ginin da za a fara a wanchan filin da yake jikin gidan nan in yaso in an gama sai a fasa a had’e da nan.
Yassir is not a kid dan haka bai
kamata mu ce za mu dinga juya shi muna controlling d’in sa haka ba he deserves to make his own decisions.
Maganar yarinyar nan kuma na fahimci komai da kaina tun kafin ma in ji wannan bayanin naka tsaf na fahimci ita take kai kanta gare sa,so na same sa na ja masa kunne kuma ya yi min alk’awarin zai fita a harkarta har abada..therefore
Yassir is good to live here
har zuwa lokacin da za a gama masa ginin sa shima,ya koma.

Kar ma ka ce ya koma side d’in ka a gaban shi yayi maka musu daganan raini ya shiga tsakanin ku,dan nima ban goyi bayan ya koma d’in ba after abun da ya faru a tsakanin ku naga dacewar ku zauna a separate wajen zama,dan na san ba zaku zauna lafiya ba na san ka da zuciya..za ka ce ya yi abu which na san definitely ba zai yi ba zai yi maka rashin kunya zaka ce zaka dake sa shi kuma zai ce zai rama daganan kuma abun ba zai yi dad’i ba,so tun kafin abun ya kai ga haka..maganin bari kar a soma.Ina yi masa addu’a kai ma ka taya ni..Allah ya shirya sa,bana so in sake jin wata maganar.’’

Dakyar bayan minti biyu Yash ya samu yacewa Daddy’’ to ‘’
dan sai da yayi da gaske tukunna ya iya danne fushin sa.Tukunna ya yi masa sai da safe ya mik’e ya fice,ya bar sa yana tunanin Ummi,
Matar da da har farce take yanke masa biyayya
kala kala amman wai ita ce yanzu banda gaisuwa ba abun da yake shiga tsakanin su,yadda take treating kowa a gidan haka take treating d’in sa ba wani special kulawa da take bashi,abincin sa d’azu data kai masa (breakfast)
kawai direwa tayi ta juya
sannan bata zo ta wanke masa toilet da gyaran d’aki ba kuma yau ta karb’i girki,yana da tabbacin ba lalle yau ta kwana
d’akin sa ba dan ko kallon sa bata yi,Wallahi!ba dan shekaran jiya jiya ya gama yiwa Hajiya Mama alk’awarin zai zauna da Ummi ba da tuni ya
salleme ta,
He apologized tunda har yace mata ta zauna a gidanshi ai kuwa he apologized amma duk da haka kalli attitude d’in da take bashi….
Ya jima a wajen kafin da kyar ya samu ya mik’e ya nufi sama ranshi a mugun b’ace,kamar yadda ya yi zato kuwa har asubah ba Ummi babu alamarta,dan haka ya kuma kumbura ya nad’i takaicin ta shima yaci alwashin zuba mata ido kuma wallahi mistake d’aya in tayi sai ya koya mata hankali a cikin gidan duk kuwa da shekarunta ai itama bata san darajar shekaru ba tunda gashi ta raina shi.


Takaici da mamakin Daddy ne suka hana Yash bacci,babu yadda bai yi ba amma sam ya gagara yin bacci.
He really can’t believe wai Daddy ne ya ja masa layi a kan Yassir,kenan dai yanzu abun da yake nufi a zubawa Yassir
ido yayi duk abun da yaga dama…ta ya ma zai ce laifin Munirat ne bayan ranar
dakyar ya kwaceta daga hannu Yassir d’in,he hates to think about it amma maganar gaskiya Daddy is very selfish when it comes to his children.

Ganin takaici yana shirin saka shi d’an k’aramin hauka ne yasa kawai ya d’auki waya ya shiga kiran Manubiya lokacin 10 har da rabi.
Sai da wayar ta fara ringin tukunna ya fara tunanin anya kuwa ya dace ya kira ta kar ya je ko ta yi bacci besides me ma zai ce mata in ta d’auka.
But he needs her yanada bukatar ya ji ko da muryar ta ne,
He has no other option..
Yana cikin wannan tunanin yaji
sautin muryarta a hankali tace
‘’Assalama alaikom’’

Ahankali ya lumshe idanuwan sa yana sauraron ta tana ta
hello!hello!!’’
Sai da ta jera wajen hud’u
tukunna dakyar yace
‘’Ki zo da wuri gobe,sannan ki zo da SScertificate d’in ki’’

‘’Ok,inshaaAllah’’
Tace,daga nan ta yi shiru..
Sai da ya d’an d’auki lokaci tukunna ya samu ya kashe wayar dakyar yana jin yadda k’irjin sa yake bugawa….

Washegari..
Ya Musbah ya so ya raka ta sai aka yi rashin sa’a me sunan Baba ba shi da lafiya,dan haka ya barta ta tafi ita kad’ai su kuma shi da Baraka da Muhsin suka tafi kai Yaron asibiti.

7:3O ta Isa bakin company d’in na shi,k’irjin ta yana dukan uku uku haka ta nufi gate d’in,sauri take so ta yi ta gama tana da exams kuma bata samu ta lek’a gidan Ammi ba dan sai da suka d’ayi meeting ita da Ya Musbah akan ‘ya karb’i kud’in da Baba ya bata ya biya kud’in hayan su sa ci gaba da aikin ba komai ‘dama ta san ba zai yarda ba ai kuwa ilai yak’i amincewa,shiyasa bata samu ta je gidan ba saboda bata gama deciding da farko ba da kuma ta gama deciding d’in lokaci ya riga ya shige mata, dan haka in dai ta gama da nan da wuri tana so ta biya gidan Ammi su gama da ita tukunna ta wuce exams saboda kar matar ta ga ko dan ta bar aiki shine yau zata yi mata wulak’anci ta bar ta da aiki ya kai rana.

Tana zuwa bakin gate security ya gaisheta ya bud’e mata k’aramar k’ofa ta wuce ciki.

Yau ma Racheal ce tayi mata rakiya har chan sama office d’in na sa amma yau ba ta shiga ba suna zuwa ta ce mata ta shiga ita kuma ta juya ta koma.

Tana hango shi fad’uwar da gaban ta yake yi ya tsananta,yau black suite yake sanye da
amman ya cire babban suite d’in ya sak’ale ya bar k’aramar ta ciki armless da white long sleeve din da suka yi masa asalin kyau,ba ta san ya aka yi ba kawai sai ta shagala da kallon sa tana mamakin tsananin kyawu da kwarjinin da Allah ya ba shi.

Tana tsayawa a wajen jikin sa ya ba shi dan haka ya d’ago da niyyar tabbatar,yana d’agowa kuwa suka had’a ido da ita.Da sauri ta sunkuyar da kanta dan tashi d’aya duk sai ta diririce…..kafin da kyar ta samu ta d’an d’aga hannun ta ta yi knocking a hankali tukunna ta tura k’ofar ta shiga ahankali bakin ta d’auke da sallama…….



MANNUBIYA
31

Na
Humayrah Bulama

Mikiya Writers Association.

Tana tsayawa a wajen jikin sa ya ba sa,dan haka ya d’ago da niyyar tabbatarwa,yana d’agowa kuwa suka had’a ido da ita.Da sauri ta sunkuyar da kanta dan tashi d’aya duk sai ta diririce…..kafin da kyar ta samu ta d’an d’aga hannun ta ta yi knocking a hankali tukunna ta tura k’ofar ta shiga ahankali bakin ta d’auke da sallama…….

A hankali ya amsa..yau ma kamar ranar farko haka ya kafe ta da idanu tun lokacin da ta shigo har ta k’araso ta zo ta zauna a hankali tace
‘’Good morning Sir.’’

Da kyar Yashjub ya samu ya iya motsa d’an mitsitsin bakin sa yace
‘’Morning’’ya fad’i hakan still idanun sa na a kanta….yana son blue a rayuwar sa gashi yau Manubiya ta sako royal blue d’in hijab wanda colour d’in ya fito sosai,har da kwalli da man leb’e yau ta saka
wanda hakan ya sake rikita Yashjub dan lokaci d’aya ya ji komai ya tsaya masa chak!..tashi d’aya ta tafi da imanin sa.

Ganin da Manubiya tayi Yashjub ba shi da niyyar daina kallon ta ne yasa ta d’auko wayarta ta shiga yi masa bayanin k’orafin da aka bata,baiwar Allah har printing ta yi ta taho dashi dan ita har gobe ganin sauk’in aikin ta ke yi over duba da yadda za’a dinga biyan ta har 3Ok a wata,sai da ta karanta masa ta d’ora da bayani tukunna ta hada da certificate d’in nata da takardar ta tura masa gaban shi.

Shi dai Yash ya ga ta ajjiye takardu kuma ya san tanata magana tun d’azu amma
Wallahi shi bai fahimci komai ba..duk bayanin da ta yi sam bai fahimci ‘Alif’daga ciki ba.

kallon ta kawai yake yi yana jin wani sanyi da nutsuwa sannan yana lissafin mallakar ta a matsayin mata..yana mai addu’ar Allah yasa in an fara maganar auren su kar a d’auki lokaci mai tsayi...shi kad’ai ya san me yake ji game da baiwar Allah n nan,a hankali ya fesar da numfashi ya lumshe idanun sa,
lokacin da yake ganin friends d’in sa a skul suna hauka a kan y’an matan su haushi suke ba sa,yanzu kuwa ya daina ganin laifin su dan a halin da yake ciki baya jin akwai abun da ba zai iya aikata akan baiwar Allah n nan ba muddin bai sab’ama addinin musulunci ba,ko ihu Manubiya tace tana so ya yi ta kurmawa tou tabbas a shirye ya ke …ashe haka so yake?.Yahanasu ta yi gaskiya,dan yana bata labarin Manubiya ta ce masa’’in bai yi sauri ya gaya mata yana son ta ba to nan da y’an kwanaki kad’an sai ya ji kamar ya yi hauka.’’

Sir I’m done’’
Muryar Manubiya ta katsewa Yashjub tunani wadda ta fad’i hakan ba tare data kalle sa ba.

‘’You look cute today!’’
Muryar Yashjub ta dira a cikin dodon kunnuwan Manubiya.

Wani irin mahaukacin fad’uwa gaban ta ya yi wanda har sai da ya sanya ta d’an sake sunkuyar da kan ta k’asa.
Kamar ta fashe da kuka haka taji,Tabbas Yashjub so yake yayi breaking d’in ta so yake sai yaga bayan d’an guntun kwarin guiwar ta,bai san a ta ya take iya yin aikin nan da shi bane bai san me take ji ba bai san yadda take kokawa da zuciyar ta bane ba.
Tana buk’atar aikin nan
saboda ta samu ta kula da ahalinta amma muddin zai din ga torturing d’in ta irin haka gaskiya ba zata iya jura ba gara ta nemi wani alternative d’in dan ba za ta yadda ya juyar mata da tunani ba.
Tana sane dashi akan kiran da ya yi mata jiya akan maganar certificate ..bayan already last had’uwar su ya riga ya ce mata ta taho da certificate d’in na ta
photocopy,amma shine ya kama ya wani kira ta jiya cikin dare.
Ba ta san move d’in da yake planning akan ta ba amma tabbas ba za ta ba shi k’ofa ba,tun da tasan ba auren ta zai yi ba dan wannan ba sa’an auren ta bane ba,dan ko da ace ya yi niyya ma ta san yana zuwa in ya ga yanayin gidan su zai fasa,besides ta ma san yana da matar shi already dan wannan at his age ga kud’i ga kyau ya ci a ce yana da mata da Yaro ko Yara….


Sosai Yashjub yayi mamakin yadda Manubiya ta had’e rai ta tamke fuskar ta tamau,ta k’i cewa komai.
Yadda ta chuno d’an mitsitsin bakin ta ne ya ba sa dariya kuma ya burge sa.
Ahankali ya d’an yi murmushi mai sauti wanda har sai da ta ji sa,ba tare da shakku ba ya sake cewa’’u look cute today!
breathtaking,to be precise’’

Saboda yana so ya tabbatar da’maganar ta sa ce tayi upsetting d’in ta haka
kuma yana so ta sake cuno bakin dan ba kad’an ba kara mata kyau yake yi sannan har ga Allah daga cikin zuciyar sa direct maganar take fitowa.’

Shiyasa tashi d’aya Manubiya ta rikice dan har cikin gangar jiki da tsoka maganganun sa suke shigar ta..jin tana shirin breaking ne ya sanya ta ta mike tsaye da sauri,ba ta yadda ta kalle sa ba tafara magana’’Sir!with all due respect our relationship is professional,ka ba ni aiki saboda Sir Najeeb yana jin tausayi na but hakan ba wai yana nufin zan barka ka ci min fuska ta ko wacce siga ba
Yes
I know I’m poor but ba zan tab’a barin ku ku yi taking advantage d’in hakan ba,dan haka ko ma wanne irin tunani ne a ran ka game da ni
Banaso
Sau biyu kawai ka ganni ta ya ka samu guts d’in gaya min how cute I look??we are nothing more than strangers to each other TBH your late night calls da kuma yadda ka ke yi min are making me feel uncomfortable,aiki ne kawai ya had’ani da kai,noting personal!go home to your wife na tabbatar tana chan ta yi maka kwalliya..ita ya kamata ka ce wa she looks cute ba wai ni ba.’’
Tana gama fad’in haka ta juya da sauri ta nufi k’ofa,ji take yi kamar ta kurma ihu a ranta ta ce ‘’ku yi hak’uri Inna na san na yi muku bak’in cikin albashi na duk wata amman ba zan yarda yayi wasa da tunani ba’’.
Dama tun farko yanayin yadda aka bata aikin yad’an so ya d’aure mata kai amma kamar yadda Abbakar yace
‘tausayin ta Sir Najeeb yake ji’ ne yasa kawai ta kawar da duk wani negative thinking,in ba haka ba a ganin ta tsaf secretary d’in sa za ta iya dan aikin sam ita ba ta ga wani dalilin hiring d’in ta da aka yi ba.


Tun lokacin da ta mik’e ta fara zazzaga masa bala’i ya kasa cewa komai kuma ya kasa d’auke idanun sa a kanta..dama tun ranar farko daya fara ganin ta a office d’in Najeeb yadda tak’i magana da kuma yadda ta saka kuka ya sanya ya fahimci tana da temper but she’s very weak
tun da ga shi yanzu ma sam ta gagara tolerating effects d’in da kallon sa da maganar sa ta yau suka yi mata
He just hope she felt something ko da ace d’an kad’an ne
Affection towards him.

Ba abun da ya fi ba sa mamaki
irin yadda sam ko sau d’aya bai ji zafin maganganun ta ba
In ban da burge sa ba abun da tayi kuma ta sake samun mazauni ta zauna daram a cikin zuciyar sa,tabbas Manubiya ta san darajar kanta.

Babu kuma abun da ya fi ba sa dariya irin yadda ta balbale sa da masifa kamar ta samu d’an cikin ta amman kuma sam ta gagara kallon idon sa ko da sau d’aya ne.

Tana kama hanyar k’ofar Yashjub ya danna wani abu a kan tebur d’in shi ya koma ya jingina da jikin kujerar yana kallon yadda take tafe tana sassarfa kamar wadda aka ce mata zai biyo ta ya kama ta ne.


Tana zuwa jikin k’ofar ta fara k’ok’arin jan glass d’in amman sai ta rasa ta ya ma za ta ja
saboda d’azu k’ofar a d’an bud’e take kad’an amma yanzu kamar an yi sealing glass d’in an manne su duka a waje d’aya dan sam babu alamar ta inda zaka ce zaka zuge ko ka tura ka bud’e,’’innalillahi wa inna ilaihirrajiun’’Manubiya ta furta hakan a fili sai kuma wani irin tsoro ya lullub’e ta,tabbas Yashjub ne ya rufe k’ofar nan..yadda ta zuba masa rashin kunya sannan ta tashi za ta yi walking away ta bar shi..in dai babu mummunar nufi a cikin zuciyar sa game da ita tou zai koreta ne bayan ya dake ta ko kuma shima ya rama bak’aken maganganun da ta zuzzuba masa,dan ita kanta sai yanzu take tariyo wasu maganganun da ta faffad’a masa masu zafi wanda bai kamata ace ta gayawa responsible mutum kamar shi ba,a ranta ta ce ‘’shikenan yanzu ta tonawa kanta da kanta asiri dan shi dai ba cewa yayi yana son ta ba amman ita ta bi ta tak’arkare tana faman cewa ‘their relationship is professional nothing personal’..
In dai kuma mummunan nufi ne a zuciyar sa game da ita to kuwa yadda ya rufe k’ofar nan
Yana zuwa raping d’in ta zai yi shikenan tata ta k’are yau.

Juya wa ta yi da niyyar ganin me yake yi taga ya hard’e hannuwan sa biyu a k’asan k’irjin sa ya jingina da jikin kujera ya zuba mata ido sai kuma ta ga ya taso ya nufo inda take,da sauri sannan rikice ta juya ta fara kiciniya tana shashshafa k’ofar tana addu’ar Allah ya sauk’o da miracle d’in da idanuwan ta za su nuna mata wata tsaga ko alama a jikin glass d’in ta samu ta bud’e ta fice.A rikice take dudduba glass d’in tana yi tana waigen sa a gigice,
ganin dai da gaske itan ya nufo yasa ta fara dukan glass d’in tana kwala k’arar
‘‘Help’’

Murmushi kawai Yashjub yayi,dai dai nan ya k’araso inda take.

Tsoro da rikici ne suka saka Manubiya ta juyo ta runtse idanun ta ta d’aga hannuwan ta sama kamar irin mutun yayi laifi en sanda sunzo za su kama sa d’in nan,kafin a rikice ta ce’’Dan Allah ka yi hak’uri’’




MANNUBIYA
32

Na
Humayrah Bulama

Mikiya Writers Association.

Murmushi kawai Yashjub yayi,dai dai nan ya k’araso inda take.

Tsoro da rikici ne suka saka Manubiya ta juyo ta runtse idanun ta ta d’aga hannuwan ta sama kamar irin mutun yayi laifi en sanda sunzo za su kama sa d’in nan,kafin a rikice ta ce’’Dan Allah ka yi hak’uri’’

Yashjub bai san lokacin da dariya ta kufce masa ba,aikuwa ya shiga yi kalar wadda ya dad’e bai yi ba.
Ba k’aramin k’ulewa tayi ba kuwa sannan ga tsoron daya bi ya dabaibaye ta dan haka ta yi k’asa da kanta a take hawaye suka shiga wanke mata fuska.

A rikice yace
‘’Ooo’O!sorry,i’m so sorry’’
dan tashi d’aya hawayen nata suka d’aga masa hankali.
Bata kalle sa ba kuma bata daina kukan ba sai ma yawa da yaga hawayen nata sun k’ara sannan ya lura hatta jikin ta karkarwa yake yi,a hankali ta d’aga hannun ta ta juya ta shiga k’ok’arin bud’e k’ofar a karo na biyu
alamar so
take kawai ya bud’e ta samu ta fice.

Ba zai tab’a iya jurar ganin ta a haka ba, dan yadda hawayen ta yake zuba akan kumatun ta haka yake ji kamar ruwan zafi ake kora masa a cikin k’irjin sa..
So yake ya ya bud’e mata k’ofar amma kuma ya san muddin ya bud’e fice wa zata yi ba tare da sun fahimci juna ba.

Jin kukan nata ya fara fitar da sauti had’i da jan hanci ne yasa kawai ya d’aga hannun sa,a nan jikin glass d’in ya danna abun da ya bawa k’ofar damar bud’uwa wanda ba kowa ne ma zai fahimci za a iya bud’e k’ofar da shi ba.
Tana ganin glass d’in yad’an motsa tasaka hannu taja ta bud’e tayi waje da wani irin sauri…

Zai zama wani iri idan ya bita kuma ya san baza ma ta so hakan ba dan haka kawai sai ya juya a hankali ya koma ya zauna akan kujerar sa
ya dafe kan sa daya fara sara masa.
Sai yanzu ya fara jin haushin kan sa daya kasa fahimtar ya kamu da kaunar ta ne since day one..tun asalin farko soyayyarta tayiwa zuciyar sa sahihin kamu,but ya gagara fahimta bayan ga gaskiya nan k’iri k’iri amma ya dinga wahalar da kan sa da kuma ita kanta Manubiya har da su bata aiki gashi ynzu ta tashi ta dank’ara ma sa matsayin boss d’in ta a kwakwalwa da tunanin ta… baya jin zata yi accepting d’in shi cikin sauk’i..yanda yaga ta
rikice ta kid’ima sannan ranta ya b’aci daga ya ce mata she looks cute ya san in ba yayi da gaske ba to ba k’aramar wahala zai sha ba kuma sai ta d’auki time d’in da baya so kafin ma ya samu matsayinsa na ‘sir’ya goge a idanun ta na ‘masoyi’ ya shiga.

A hankali ya sake fesar da iska,kafin tashi d’aya ya yanke shawarar zuwa gidan su
,ba zai sake d’aukar lokaci ko jira ba tunda ga abunda jiran ya haifar.

Sai da ya jera mata misscall sama da shida amma bata d’auki ko d’aya ba,gaba d’aya hankalin sa sake tashi ya yi dan haka ya yanke shawarar kiran Najeeb..ko gaisawar kirki bai bari sun yi da Najeeb d’in ba yace ‘’ya nema masa adress d’in Manubiya yanzu gashin nan zuwa wajen sa in yazo zaiji komai’’
Yana gama fad’in haka ya katse kiran ya bar Najeeb kare da waya a kunne..yakamata ace a dai dai wannan lokacin ya fara yiwa Yash dariyar mugunta duba da yadda yake zaginsu in yaga suna abu a kan soyayya dan gashi alhakin su ya kama sa tun da gashi yana nema ya susuce tun kafin a je ko’ina..da kuma alhakin y’an matan da suka sha kuka a gaban sa craving for attention d’in Yash,amman kuma gaba d’aya tausayin Abokin nasa sai ya hana sa sakamokon rikici fargaba hatta da tsoron daya jiyo k’arara a cikin muryar Yashjub d’in,a hankali ya

Please Login or Register in order to submit comment