Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

naji lokacin da ta fad’a’’

Dasauri yace
‘’au haba!bara mu kira su……

Cikin katseshi tace’’yi maza kaje shagon
Audi ka karb’o mata madara
In tace’Manu’to madara take buk’ata.Bari inje in kawo maka
kud’in’’ ta fad’i hakan tana mai juyawa da niyyar fita

Shiruu Muhsin yayi tana shirin fita yace’’A’a fa,bata ma tab’a
cewa Manu ba sai yau!
Adda Manubiya take nufi
kuma ai yanzun nan muka bata madara nida anty Aisha.

Cikin d’an fushi tace
‘’Muhsin zakayi abun da nace ko kuwa ??’’

‘’Tam’’yace
sai kuma ya sake cewa
‘’Akwai madarar da ya Musbah ya siya mata me yawa a gida,bara inje in d’auko’’

Shiruu tayi kafin ta nufo sa ta kama kafad’unsa tace
‘’Muhsin su ya Musbah sun rufe d’akin naku kafin su tafi ka wuce kaje ka siyo mata a shagon Audi yanzu yanzu bara in kawo maka kud’in
Kana sakani yawan magana kaina ciwo yakeyi.

Ahankali yace ‘’tou Anty’’a ransa yana tunanin nisa da tafiyar shagon audin.
Kamar ya ce mata ‘ba zai iya siyo wa a shagon kusa ba?’
sai kuma kawai yayi shiru dan yasan halin ta
yanzun in ya cika ja’inja da ita tsaf sai ta makesa
Dan haka ya ja bakin sa yayi shiru ya tsaya ya jirata har ta je ta kawo masa naira d’ari tace’’gashi ka yi sauri’’.
Da ‘’to’’ya amsata tukunna ya sa hannu ya karb’i kud’in ya fita,har ya kusan kai k’ofa kamar wanda ya tuna wani abun sai kuma ya koma d’akin yace’’Anty in je in kira Anty Aisha?tace in zan fita in je in kirata kar in bar inna ita kad’ai.

Wannan karon cikin fushi sosai Baraka tayi masa dak’uwa tace’’ ungo naka Muhsin
Innar ita kad’ai ka gani anan? ni ba mutum baceba?
Zaka wuce kaje min aike ko sai jikinka ya gaya maka?

Ahankali ya kamo hannun me sunan Baba yace ‘’zo ka rakani’’
Daganan ya juya kawai ya fita
ba tare da ya sake cewa komai ba.

Yana fita ta kalli inna tana raya abunda zatayi kafin ta kalli k’ofar da Muhsin d’in ya bi ya fita a ranta tace’’ sai dai kawai ka dawo ka gani,nasan in kana nan tsaf zaka kawo min cikas
Ba k’aramin aikin ka bane ka tara min jama’a shegen Yaro mai shegen surutu…
Tana gama fad’in haka ta nufi inda innar take,tana zuwa without thinking twice ta yaye zanin da aka lullub’ewa innar k’afafu da shi ta d’auki pillown dake ajjiye a gefenta ta fita waje
A nan tsakar gidan da sumintin duk ya farfashe ta yi shimfid’a tukunna ta koma d’akin,
da kyar da mugun kyar ta samu ta kinkimi inna k’arshema janta ta yi ta shimfid’eta anan tsakar gidan
Inda ta shimfid’a zani ta saka pillow.
Tana ganin lokacin da hawaye suka shiga sintiri a kan kumatun inna amman ko d’ar Baraka bata ji ba idanun ta sun riga sun rufe
Ita babban tashin hankalinta
Manubiya tayi aure kuma da alamun wani wajen za’a tafi da Baba tunda an riga an kama sa maybe forever shikenan ya tafi kenan ko me yayi oho musu
So definitely gidanta Muhsin Jidda da Inna za su dawo kenan
Dan haka
Wallahi ita kuma ba za ta yi k’asa a guiwa ba wajen nuna musu ba su Isa ba…tun wuri ma su nemi gurin zama!yau za su yi ta ta k’are!garama in suka dawo su gani sannan su tabbatar da cewa uwar tasa ma bata da wajen zama a cikin gidan ballantana kuma k’annensa.

Dama tun d’azu a k’ule take….da ya tashi kawo innar ma ko shawartarta bai yi ba
haka nan kawai sai ganin su tayi
Ai kuwa yanzu zai gani kuma zai san itama ta Isa wallahi taga alama in ba nuna masa tayi ba tou ba lalle ya tuno ‘waccece baraka ba’

Hakanan ta yi ta zancen zuci tana huci ita kad’ai.
Ko bi ta kan inna bata kuma yi ba ta fad’a band’akin dake nan a tsakar gidan tana jin nauyi da zafin da zuciyar ta tayi yana raguwa kad’an kad’an.
A ganinta rainin wayon su yayi yawa a bar ta taji da hak’urin zaman auren ma da takeyi da shi ba sai an k’ara mata da wani takaicin ba,yau za’a yi ta ta k’are
Wallahi
dan bata tsoron uban kowa a cikin su.
…….
Su ya Musbah suna tsaye a d’akin da Abbakar yake su Jidda suka shigo,a take wani irin tausayn su ya lullub’e ya Musbah,dan haka ya kalli ya Nafi’u yace’’bara ya duba Reception ya ji ragowar bill d’in su dan su samu su biya…sun san su Yash sun biya d’azu amma basu san duka suka biya har da na Abbakar ba.
Yana fita ya Nafi’u ya d’auki wayar Abbakar
Manubiya ta bud’e musu password d’in ya kira maman Abbakar.
Ko minti ashirin ba ayi ba kuwa suka k’araso asibitin a hargitse itada maman Baraka,a reception suka had’u da ya Musbah wanda yake ta faman sak’a da warwara sam ya kasa komawa cikin d’akin bayan ya je an ce masa’’ai su Yash sun riga sun gama biyan komai’’.

Hangosu yayi a hargitse suna tambayar wani cleaner dan haka ya k’arasa yayi musu iso har cikin d’akin.
Dama shima d’in da kyar suka amsa gaisuwar sa yanzu kuma ko kallon baba da yake kwance basuyi ba haka suka wuce sa suka d’aga labulen daya ke tsakaninsu da Abbakar
Inda ya Musbah yace musu yana ciki suka afka.
Shi kuma ya tsaya a wajen Baba da ya Nafi’u wanda bai dad’e da fitowa daga wajen abbakar ba,yake sanar musu
‘’ su Yashjub sun riga sun biya komai’’
Baba yana shirin yin magana suka jiyo maman Abbakar ta kurma wani irin ihu

Da sauri su ya Musbah suka nufi inda suke suna addu’ar Allah dai yasa ba wani abun ne ya samu Abbakar d’in bayan fitowar su ba.

A durk’ushe a bakin gadon suka hangeta tana wani irin masifaffen kuka

Kafin daga baya maman Abbakar ta mik’e ta nufi Manubiya gadan gadan tana zuwa ta shak’o ta ta mik’ar da ita tsaye cikin fushi da kuka tace‘’ai duk ke ce kika janyo komai!munafuka muguwa kawai,kin maidamin Yaro kamar wani boyi boyin ki…’’

‘’Haba mama,baki yarda da
k’addara bane?’’
Ya Nafi’u yayi mata tambayar cikin rashin jin dad’i.

Cikin fushi tace’’ai dama nasan baza ku ga laifinta ba,to wallahi ku jirani a kotu dan bazan yarda ba sai munyi shari’a da ku.Amman kafin nan inaso in ja miki kunne!indai kin haifu cikin Musa da Amina tou kar in sake ganin ki a kusa da d’a na.
Kalli cikin azabar da kika jefa sa da ke da y’an uwanki da iyayenki…masifa ce ku!shiyasa duk wanda ya rab’e ku sai ya shafa,na yi k’ok’arin nunawa Abbakar ba so d’aya ba ba sau biyu ba amman dayake kin riga kin shanyemin Yaro kalli sai da kika kusan kai shi lahira…’’
Kukan daya kufce mata ne yasa ta d’an dakata kafin ta sake d’agowa a zuciye tace’’na gaya miki yanzu zan sake maimaitawa ‘in dai kin haifu cikin tsinannun iyayen k…’’

Nufar mata ya Musbah yayi da niyyar rufe ta da duka amman sai maman Baraka ta shiga tsakiya ta rik’e sa,zafin zuciyar da ta ciwo sa ne ya sanya cikin rashin sani ya yi cilli da ita,ya sake yin kan maman Abbakar

Ganin yana shirin yin b’arna ne yasa ya Nafi’u ya taresa yace
‘’Musbahu ka yi hkr ka kyaleta ba dan itaba,ka duba fa Abbakar shi ne ya kira su Yashjub ka rabu da ita ta ci albarcin d’anta.’’
Daga haka ya juya yace mata
‘’mu zamu wuce yanzu,
Ga Abbakar nan zan dawo in duba sa inshaaAllah zuwa anjima…muna buk’atar muyi mishi godiya.
An biya duk wasu charges
abinci kawai zaki dinga basa,
Allah ya basa lafiya.’’

Daga haka ya cewa su Manubiya’’su wuce su tafi’’.
Sai da kuwa yayi da gske tukunna shi da Jidda suka samu suka janye Manu dan ta tsaya kawai tana kallon maman Abbakar ne,so take yi ta maida mata martani amman kuma darajar d’anta yasanya ta kasa magana.

Aikuwa har suka fice maman Abbakar bata yi shiru ba…babu kalar zagin da batayi musu ba
Maman Baraka ma tana tsomo baki
A cewarta ‘’sirikin ta ya hankad’eta ta fad’i kuma ko
kallon inda take bai yi ba
kamar ba y’a ta d’auka ta basa ba’saboda shi d’an marasa tarbiyya ne…baisan darajar ta ba.’’

Hakanan Baba ya tsawatar musu yace ‘’kar wanda yace uffan su rabu dasu’’dan haka suka tartara yanasu yanasu suka fice bayan ya Musbah yaje ya karb’i magungunan Baba.
K’arfe shida dai dai suka bar harabar asibitin suka nufi gida.

A gida suka fara tsayawa
suka ajjiye Baba,tukunna Baban yace musu’’su duka suje su d’auko inna,kar su damu ba komai zai iya zama shi kad’ai’’

Da ‘’to’’suka amsa shi daga haka suka nufi gidan ya Musbah gaba d’ayansu domin suje su d’auko Innar.




MANNUBIYA
4 1
Na
Humayrah Bulama

Mikiya Writers Association.

Suna fita Baba ya saki hawayen da yake ta k’ok’arin dannewa,dama baya so yayi kukan a gaban su gudun karya karya musu guiwa ya d’aga musu hankali..shiyasa yace su tafi gaba d’ayansu.Da ace yana da yadda zai yi da ba zai tab’a aurar da su Jidda ba,ya so yaran sa suyi karatu,yaso ace Jidda ta gama ko da level one ne tukunna,amma yanzu kam sai dai ya bita da addu’a da fatan alkhairi tare da rok’on Allah ubangiji ‘ya had’a Manubiya har ma da Jiddan da surukai na gari ya sa su so
su,kasancewar yasan mahaifin Yusuf ba shi zai sa ya k’i yiwa y’ar sa wannan addu’ar ba yana rok’on Allah yasa su jata a jiki bayan auren,Manubiya kuma Allah ya bata na gari kowa ya zauna lafiya a gidan sa’dan tabbas abunda su maman Baraka sukayi musu yau a asibiti ya tab’a sa sosai ya ji zafin abun.



A k’ofar gidajen nasu biyu motar ya Nafi’u ta yi parking dan haka suka fara firfitowa,Ya Musbah ne ya fara shiga cikin gidan nasa su kuma suna biye da shi a baya,a k’arshen soro kafin ya k’arasa shigewa cikin gidan sukaga ya ja ya tsaya chak!yak’i yayi gaba yak’i yayi baya.
K’arasawa kusa da shi ya Nafi’u yayi yana mai cewa
‘’Ya dai?kar ka…’’
A take maganar sa ta tsaya chak sakamakon hango Inna da shima yayi a yashe a tsakar gidan.

Da farko tunanin su basu yayi’watak’ila ko tayi k’ok’arin tashi ne sai Allah ya bata iko
shine da ta fito kuma sai ta fad’i a wajen’,amman kuma yadda suka ga an shimfid’a mata zani sannan aka d’aura kanta akan pillow ne ya basu tabbacin wannan aikin Baraka ne.

Cikin d’aga muryar ya Nafi’u ya hau kwala kiran ‘’Aisha!Aisha!!’’
Sai kuma ya juya zai fita dai dai sukayi kicib’is da Aishar
dan tana jin tsayuwar motar ta sa a k’ofar gidan ta d’auko kular data gama juye abinci ta janyo hannun y’ar ta suka yo gidan.
Cikin fushi yace’’ya akayi kika barta kika fita?ina Muhsin??’’

Inda inda ta fara,tana shirin yin magana ta ga su Manubiya sun yi cikin gidan da gudu,yadda ya Nafi’u ya d’an gota suka wuce ne ya bata damar hango innar itama dan haka tayi ciki da sauri tana salati.

A take
Jidda da Manubiya suka fashe da kuka saboda yadda suka ji jikin Innar ya d’au zafi hatta kayan jikinta ya d’au zafi ga ranar la’asar da ta kusan fad’uwa ta haske mata fuska gashi ba damar motsawa…….

Dishi dishi ya Musbah ya fara gani tsabar tsananin b’acin rai da tashin hankali…da kyar ya samu ya iya cewa
‘’Baraka!!’’
Da d’an k’arfi,dan jikinsa wani irin karkarwa yake yi hatta muryar tasa rawa takeyi.


Tun lokacin da suka shigo ta jiyo su…..dan ta gama watsa ruwa a jikinta kenan sakamokon zafin da akeyi
ta ji tsayuwar motar ya Nafi’u.

Dan haka ta d’auro zaninta ta yafo mayafinta ta rik’o kayanta a hannu ta fito fuskarta a had’e tamau
…..

Tana fitowa Ya Musbah ya k’arasa inda take ya tsaya..so
yake yayi magana amman sam sai ya gagara,in banda karkarwa babu abunda jikin sa yake yi,dan haka kawai sai ya kafeta da idanu,ya shiga karanto addu’o’i a chan k’asan ransa yana mai neman tsari daga shaid’an saboda a yadda yake jin zuciyarsa a yanzu muddin yayi reacting yasan wallahi kashe Baraka zai yi!sai ya kaita har lahira.

Tunda Baraka take a rayuwarta bata tab’a ganin Ya Musbah a irin wannan yanayin ba,babu abunda ya fi tsoratata irin yadda taga idanuwan sa sunyi jajawur hatta farar fuskarsa ta yi jaa!gashi jikin sa sai wani irin karkarwa yakeyi.
Shiyasa gaba d’aya duk sai ta ji tsoro ya lullub’eta,abunda bata tab’a tunanin zata ji ba kenan dan ko a mafarki bata tab’a kawowa akwai ranar da zata zo ace wai’ta ji tsoro ko shakkar Ya Musbah a rayuwar ta ba’.
A lokacin da suke soyayya
soyayyarshi kawai ta sani,da suka yi aure kuma..hak’uri juriya da lallashin sa kawai ta sani.Shiyasa yanzu da ta ga asalin fushin sa abun ya bata tsoro matuk’a.


Sai da ta d’anyi k’asa da kanta tukunna tace
‘’Flitting nayi a d’akin shine na fito da ita waje…..’’

Ba suga k’arasowar Ya Nafi’u ba sai sauk’ar gigitaccen marin da ya d’auke Baraka da shi.

Da sauri ta d’ago ta kallesa sai kuma ta kasa cewa komai kafin hawaye sharr ya wanke mata fuska,tama kasa maganar.

Dakyar da mugun kyar Ya Nafi’u ya yi k’ok’ari ya danne zuciyar da take tunzura sa akan ya rufe Baraka da duka,yana wani irin huci ya
juya ya kalli Ya Musbah
Yace
‘’Yi hak’uri Musbahu’’
Daga haka ya wuce ya fice daga cikin gidan da sauri,dan yasan in ya cigaba da tsayuwa to tabbas sai an samu matsala.

Yana fita Baraka ta juya tana kallon Ya Musbah wanda yake nan tsaye ya kafeta da idanuwa
A ranta tana mamakin yadda yana gani Nafi’u ya d’aga hannu ya zabga mata mari amman bai tab’uka uwar komai ba,sannan ba shi da alamar yin komai a kan hakan har yanzun,dan haka ta bud’e Baki zatayi magana kenan shi kuma ya riga ta ta hanyar cewa’’ki tafi na sake ki!saki biyu’’

Dede nan Manubiya da suka gama kai inna d’aki ta fito tana zuwa ta yi kan Baraka zata rufeta da duka
Dasauri Aisha wadda dama ta lura da abun da Manubiyan take shirin yi ta taho da gudu ta rik’e ta.
Sai yanzu Baraka ta samu ta goge hawayen da suke zubo mata babu k’ak’k’autawa tukunna dakyar tace
‘’Cika ta,cikata ta dakeni tunda ita mahaukaciya ce,nace muku
flitting nayi amman bai ishe ku ba,uwar taku gwal ce?’’

Cikin fushi Aisha tace
‘’Mahaukaciya!Jahila!Dak’ik’iya!in baki saniba to yau ki sani’uwa ta fi gwal’.Da bata haife sa ba da baki same sa ba,dak’ik’iya kawai.

Ya Musbah yace ya sakeki so zaki iya tafiya,ki tartara kayan ki ki koma gida a sake yi miki tarbiyya watakil in kin gyaru ya dawo dake,dan tabbas ko ni ba zan bada goyon bayan
aci gaba da zama dake da wannan halin da wannan zuciyar ba.’’
Tana gama fad’in haka ta juya ita da Jidda suka ja Manubiya dakyar suka shige d’aki dukkan su Manubiya tana wani irin kuka dan ji takeyi idan bata daki Baraka ba yau tou sai ta mutu!.Ita kanta Aisha ta san
tabbas in ta tsaya tsaf za su kwashi y’an kallo ita da Baraka kuma a ganinta in bata kwantar da husuma ba to bai kamata ta iza wutar ba,dan haka ta duk’ufa tausar Manubiya.

Duk bakin Baraka yau kasa cewa ko yin komai tayi
daga k’arshe kawai sai ta juya
Fuuuuuu ta wuce d’akin ta….

Ya Musbah ma baici gaba da zama a gidan ba
Baraka
tana wucewa d’aki ya lek’a ya cewa su Manu’’kar wanda ya kulata a cikin su,su barta da duniya’’daga haka ya juya ya fita.


Baraka Tana shiga d’aki ta fashe da kuka mara sauti mai
tsananin cin rai,bata tab’a
tunani ba bata tab’a kawowa a ranta Ya Musbah zai iya sakinta ba,to me ya faru,ya akayi har ya iya sakinta!yanzu ya zata yi kenan???
Ta yiwa kanta tambayar ba tare da ta san wa zai bata amsar ba.Ta jima tana kuka tana tunani kafin ta share hawayenta a ranta ta shiga aiyyana’’Tabbas sai ta nunawa Musbahu kuskurensa wallahi
sai ta jaa shi a k’asa.Kallifa kalar cin mutuncin da suka taru sukayi mata,inaa!bazaiyiu ba wallahi da sake dole ta sake shiri zai ga ikon Allah,infact gaba d’ayan su sai ta nuna musu wacece Baraka’’.

Da farko da ta yanke ne akan babu inda zataje,sai kuma ta bawa kanta shawarar ta je ta samu su mamanta itama,a yadda su Ya Musbah suka hayayyak’o sukayi mata wannan aika aikar
tabbas bai kamata ta yanke shawara ita kad’ai ba.
Tana wannan tunanin ta had’a kayanta kaf,ko d’an kunne bata bari ba a ganinta in tayi haka Ya Musbah zai ji tsoro yazo biko da wuri.


Su Manubiya suna d’aki sun zagaye inna suna yi mata fiffita sukaji fitowarta tana ta jidar kaya.
Babu wanda yace mata ci kanki a cikinsu,haka suna
jinta ta dinga kwasar kayanta
tana fitarwa one by one
har ta gama……


Ya Musbah yana fita direct wajen Baba ya nufa,dan ya gama rayawa a ransa’idan ma za su maida Inna gida tou sai dare,dan so yake yi ya nunawa Baraka iyakar ta yadda tana ji tana gani sai dai ita ta fita ta barwa Inna gidan Wallahi’.


A hanya ya had’u da Muhsin da mai sunan baba sun dawo daga siyo madara,dan haka suka wuce wajen Baban dasu
Dama bayaso Baraka ta tafi akan idon me sunan Baba gudun kar yayi ta kuka yace sai ya bita.

Sun d’an jima a wajen Baba bayan yace mishi
‘’Sunje sun tarar Aisha tana bawa innar abinci ne shine aka tsaya ta gama tukunna a kawo ta’’

Sai da suka kuma d’aukar lokaci tukunna ya bar Muhsin anan,shi kuma ya kama hannun me sunan Baba suka nufi gidan nasa,baiyi tunanin tarar da Baraka har yanzu ba amma yana karya kwana ya tarar da ita da adaidaita sahun ta har uku tanata loda kayayyakinta ita da masu nape p d’in a ciki.

Ko iskar da ta d’ebo ta bai yarda ya kalla ba,ya sake rik’e hannun Yaron ya zo zai shige cikin gidan…suna zuwa da
Yaron ya gane ashe uwar sa ce tare da masu adaidaita sahun ai kuwa nan ya hau ihun sai ya bi ta.

Tanagani ya fara tsalle ana jan shi yana tirjewa ta dawo ta kama kunne sa ta ja tace’’in na sake jin sunana a bakin ka sai naci uban ubanka!shegen Yaro kawai sai kace dashi nazo’’
daga haka ta juya zata wuce
taji Musbah yace’’Babana yi
hak’uri mu wuce mu shiga gida
yawo a titi bai kamace ka ba’’

Ai kuwa cikin fushi Baraka ta juyo
‘’Ai sai ka bari in gidan naka ne sai kayi tink’aho dashi,talaka mara matsugunni kawai,gara ni in na tafi yawo a titin ba’a gidan haya zan k’are ba,kai kuwa nan da y’an kwanaki za a zo ayi waje dakai dama darajata yasa mai gidan yake d’aga maka k’afa yanzu kuwa nasan ba zai barka ka cigaba da zama daga kai sai uwarka b……

Da sauri ya d’auke me sunan baba ya wuce ciki ya banko k’ofar dan bai shirya biyewa Baraka a k’ofar gida ba,ta jima kuwa tana ta tijara ita kad’ai sai da masu mashin d’in suka ce mata’’in bata shirya tafiya ba zasu sauk’e mata kayanta suyi gaba’’tukunna ta shiga ta zauna a take kuma sai ta fashe da kuka.

To dai Baraka tun kan aje koina sai da ta ji dama bata fito daga gidan mijin nata ba saboda d’ayan mai mashin d’in bai rik’e mata amana ba…dukda kuwa tafiyar da sukayi bata wuce mintuna biyar a tsakani ba
amma
da yayi wura wura yaga babu ido a kansa
chan ya chanza hanya.
Sai da ta Isa k’ofar gidansu tukunna ta lura babu napep d’aya.
…………
Tun lokacin da Yashjub ya bar office Daddy ya k’ule ganin la’asar har ta gota bai kira kuma bai zo ba ne ya sanya shi ya kira Najeeb a fusace ya bashi sa’ko amman gashi har bayan Magrib Yashjub d’in bai iso ba.

Yassira ce ta guntsa wa su Mommy abun da Yashjub d’in yayi yau a office,gashi har yanzu bai dawo ba..hakan kuwa ba k’aramin sake d’aga musu hankali yayi ba dan tashi
d’aya suka yanke cewa
‘’ wannan yarinyar da suke zargi ce ta kirasa’’
Saboda Yasirar tace musu ko bayan da aka tashi daga office sai da suka biya d’ayan company d’in Yash d’in ita da Daddy amma akace musu yau throughout bai je chan ba.
Racheal kuma tace mata ‘’batun estates d’insa komai stable’’dan haka matslar ba anan take ba kenan.Shiyasa suke da tabbacin wannan yarinyar ce kenan…tabbas kuwa zama bai kamasuba dan Indai har matsalarta zata sanya ya mik’e tsulum ya fice ana tsakiyar meeting sannan yak’i d’aga wayar kowa har yanzu saboda tsabar yadda ya bata mahimmanci,to hakan ya nuna da akwai babban bound a tsakanin sa da ita wanda ya zame musu dole su tarwatsa tun wuri su yakiceta daga cikin rayuwarsa tun kafin ya k’ak’abo musu k’adangaren bakin tulu!.

Hakanan gidan ya kasance shiruu kowa da abun da yake tunani har aka yi dinner aka watse babu Yashjub babu alamar sa.


Zuwa yanzu Daddy ya sauk’o daga duk wani fushin da yayi da Yashjub
dan duk hankalin sa ya tashi
shiyasa ya yanke shawarar in k’arfe goma tayi Yash bai dawoba tou zai kira y’an sanda da sojoji su saka hannu a nemo masa d’anshi.

Tun da sukayi dinner kowa ya bar dining ya koma cikin parlourn ya zauna,
In banda safa da marwa ba abunda Ddaddy yakeyi,tashi d’aya zaka hango tsantsar damuwa da tashin hankali kwance akan fuskarsa,ya kasa tsaye ya kasa zaune…tabbas yau ya a sake tabbatarwa Yashjub shine rayuwar sa.




MANNUBIYA
42
Na
Humayrah Bulama

Mikiya Writers Association.

Tun asalin farko baya k’aunar ganin fushi ko b’acin ransa wannan dalili ya sanya hajiya mama ta d’auke shi ta maida shi gabanta dan ta ce muddin ta barmasa shi a yadda yake tsananin son nan nasa to bazai iya yi masa tarbiyya mai kyau ba.

Daddy ya kasance mutum mai tsananin k’aunar ya’yan shi amma son da yake yiwa Yashjub wani irin so ne na daban wanda bai tab’a jin kwatankwacin son akan kowa ba bayan uwar data haifesa sai ga Khadijah mahaifiyar Yahanasu.

Bayaso ya yarda da cewa yafison Yash dan bayason ya samu banbanci a tsakanin yaran nasa amma yau kam ya yarda ya tabbatar,dan gashi kwata kwata ko awanni 12 ba ayi ba amma rashin sanin whereabout d’in Yashjub yana neman haukatasa ji yake yi kamar ya d’aga hannu ya tsunduma ihu.
Gashi dai laifi yayi masa amma
zuwa yanzu har laifin ya gogu a idanun Daddy…..kawai shi matsalar yanzu itace yaji inda Yashjub d’in yake da lafiyar sa

Gashi ya kira gidansu Najeeb ma ance bai Isa gida ba kuma duk wayoyinsu a kashe,shiyasa tashin hankalin nasa ya sake hauhawa.


Mommy kuwa za’a a iya cewa tashin hankalin nata yakusan k’etare na Daddy dan dai kawai ita tana iya danne nata ne.Babban tashin hankalinta shine wannan yarinyar da ko sunan ta basu saniba ballantana su samu su fara bi takanta dan indai har ita ta kira sa ta sanya shi yayi wannnan dogon zango haka to kuwa sunada babbar matsala.


Kausar ma daurewa kawai takeyi amma had’iyar zuciya ne kawai ya rage batayi ba,basu riga sun gama tabbatarwa ba amma tabbas in dai maganar baba larai ya zama gaskiya ne to wallahi sai ta nemo yarinyar nan ta halaka ta!bata da wani option d’in daya wuce ta kaita lahira dan ba a halicci macen da ta Isa ta shiga zuciyar Yashjub ba Wallahi
Ko ta shiga sai ta fito.


A b’angaren Yassir kuwa
ba k’aramin sake hawa yayi ba,yadda hankalin Daddy ya tashi ne yafi komai d’aga masa hankali…laifi fa Yashjub d’in yayi fushi ya kamata ace Daddyn yayi dashi
amman kalli yadda ya b’ige da damuwa akan rashin sanin inda yake sai kace wani jinjiri.Zuwa yanzu baya buk’atar more proof dan ya yarda ya gama tabbatarwa’Yashjub is special a cikin gidan nan’
Ya tabbatar inda ace

Please Login or Register in order to submit comment