Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba
Dan haka tashi d’aya yake fahimtar ba ita d’in bace ba.
Tunani yayi ko ya kra Najeeb ya tambaye sa ko tana da wani nick name sai kuma yaga zak’ewar sa
Kuma yasan yana tambayar sa
zai fara judging d’in sa Shiyasa ya hak’ura ya koma ya shiga searching Manubiya eyes
A tunanin sa maybe friends d’in ta da haka suke kiran ta
tunda idanuwan ta are one in a million.
Ya jima yana Abu d’aya Kafin chan kuma yayi shiruu
Ya fara tunanin wawtar sa.
Shiruu yayi shi kadai
Yana mamakin yadda ya haukace tashi d’aya dan tabbas wannan d’an k’aramin haukane yake yi,A hankali ya ajjiye wayar ya dafe goshin sa
sai da ya d’an nutsu tukunna ya ja ya kwanta ya shiga sauk’e ajiyar zuciya a jejjere.
Yana kwanciya tashi d’aya
tunanin ta ya dawo masa
Me yake damun ta?
Me ya ke saka ta saurin kuka?
Me yake saurin breaking d’inta
Ya akayi bata samun kud’in registration da wuri??.
Runtse idon sa yayi da k’arfi
cikin b’acin rai yayi tsaki
kafin yace
‘’Yau nikam na had’u da aljana’’
A fili

‘’Wacece aljanar??’’
Muryar Mommy data shigo yanzu ta daki dodon kunnuwan sa.
Sarai ya jita
Sai dai bai bud’e idanun sa ba ma
ballan tana tayi expecting amsa daga gare sa.

Wani k’ululun tashin hankali ta had’iye da kyar kafin ta k’araso ta tsaya a kan sa tukunna ta sake cewa
‘‘Wacece aljanah??’’

Sai da ya d’an d’auki lokaci
tukunna ya bud’e idanuwan sa ya kalle ta yace
‘’Daddy yace gobe zai zo,da daddare yana buk’atar ganin kowa,sannan kin gaya wa Yasir da bakin ki yadda kukayi da shi ?’’

Cikin inda inda tace
‘’Shi Daddyn ya yace maka munyi da shi??
Me yace maka nace?’’

Sai da ya d’an yi murmushi Kafin yace
‘’Nothing,yace dai kawai kisan yadda za kiyi da Yasir kafin yazo dan in yazo baya son jin wata magana game da komai
akwai important abun da zai kawo shi
So kar azo ku bashi kunyata’’
Yana gama fad’in haka ya mik’e ya ‘’sai anjima’’daga haka ya nufi k’ofa

Dasauri ta mik’e tace
‘’Yash
Wacece aljanah?’’


Juyo wa kawai yayi ya kalleta
kamar zai ce wani abun
sai kuma kawai ya sauk’e wata nannuyar ajiyar zuciya
daganan yasa kai ya fice ya barta nan a tsaye ……


Gaba d’aya kan Mommy ya d’aure ta rasa mafita lamarin Daddy da Yashjub da maganganu su
sun d’aure mata kai kwarai

Kamar yanda Daddy ya fad’a washegari da daddare
bayan sallar isha’a,yazo.tare suka shigo da Yashjub Wanda dawowar sa daga masallaci kenan ya had’u dasu suna parking dan haka ya jira suka shigo tare.
Suma zama ya haura sama domin yana son magana da Mommy Kafin ta sauk’o karta ga bambarakwai.




MANNUBIYA
13

Na
Humayrah Bulama

Elegant Online Writers

Waya ya same ta tana yi da alama da Uncle d’in ta ne
yayan Abban ta
Maybe ko k’ara takai,Ahankali ya zauna yana mai lumshe idanuwan sa a ran sa yace
‘’In ban da abun Mommy tabar Abb’oi ya huta mana mutum ko gani bayayi sosai shekaru sun ja amman tana d’aga masa hankali,tabbas shiyasa bata shiri da ya’yan sa da jikokin sa
dan sun lura kashe musu shi take k’ok’arin yi da tension d’in matsalolin ta ……

‘’Yash!’’
Muryar ta ta katse masa tunani,
Ahankali ya bud’e idanuwan sa
kafin ya mik’e ya k’arasa bakin gadon ya zauna ya ruk’o hannayen ta.
Tunda taga yayi mata haka
ta fahimci abu mai matuk’ar mahimmanci zai fad’a mata
dan haka ta tarkata ilahirin hankalin ta gare sa
kirjin ta yana mai dukan uku uku.
Gaba d’aya tashi d’aya sai tausayin ta ya lullub’e sa dan haka ya sake runtse hannuwan ta a na sa tukunna ya fara magana
‘’Mommy dan Allah kiyi hak’uri
duk abun da zan fad’a miki yanzu inaso ki danne zuciyarki
kiyi hak’uri,ki fahimce ni’’.
Gaba d’aya zuwa yanzu hanakalin Mommy ya gama tashi,dakyar ta samu tace masa
‘’InshaaAllah Yash’’.
Ahankali yace ‘’Su Daddy sun zo suna k’asa shi da bak’uwa
mun samu k’arin member a family d’in nan jiya,
Inaso ki fahimci ba wai saboda kun samu matsala yayi miki kishiya ba,dama chan akwai plan d’in b’oye wa yayi,
Nima ban sani ba sai last week
But I think an d’an matso da d’aurin auren saboda a yadda nasani kamata yayi ace yanzu saura two weeks.
Mommy dan Allah kiyi hak’uri
nasan dole zaki ji babu dad’i ni kaina ina jiye miki kinga dai bani da ko budurwa
amman ko tunani nayi
For instance
Inada budurwa taje tana kula wani bansan ya zanyi ba
ballantana kuma ku ma’aurata.
Kiyi hak’uri nasan babu dad’i
amman a yadda Daddy yake a yanzu
In kika b’ata masa rai tabbas bansan kuma mai zai yi ba,
Kiyi hak’uri nasan kina hak’uri da Daddy amma dan Allah ki sake hak’uri
For us ….’’
Tunda ya fara magana ta kafe sa da idanuwa ta kasa motsi sai da ya sake runtse hannunta dake cikin na sa
tukunna tayi firgigit,
tabbas she saw it coming amman basuyi tunanin kwana kusa ba
Innalillahiwainnailaihirrajiun
Ta shiga ambato wa a k’asan ranta ..
Ta manta rabon da ta shiga tashin hankali Irin wannan a rayuwar ta sam ta manta
ta ma kasa kuka ji takeyi kamar an tsunduma zuciyarta a cikin talge tsabar azabar da tsananin tashin hanakalin
ya tsunduma zuciyar ta ta.
‘’Mommy!’’
Yashjub ya sake kiran sunan ta.
Ahankali sannan dakyar ta k’ak’alo wani murmushi wanda ya fi kuka da ife ife ciwo,
Tabbas wannan babban tashin hankali ne da aiki ya same ta,
On the other hand kuma
opportunity ne ta samu dan yadda ta hango tsantsar tausayi ta da kulawarta
A idanuwan Yashjub
wataki’ila wannan auren da Daddy yayi ya janyo mata Kulawa da shakuwa daga d’an nata,ta lura kamar yadda kishi yake weakness d’in Daddy haka Yashjub ma …

Ahankali tace
‘’Zan sak’k’o Yashjub kaje k’asa kawai zan taho
I need some time alone’’.
Har zai mik’e sai kuma ya janyota jikin sa yayi hugging nata ya shiga bubbuga mata baya alamun rarrashi
kafin ahankali yace
‘’Kiyi hak’uri Mommy,Allah zai baki lada’’
Daganan ya cikata ya mik’e ya fita.
A bakin k’ofar d’akin sukayi karo da Baaba larai alamun shiga take shirin yi shi kuma ya fito,murmushi kawai tayi masa daganan ya nufi k’asa inda su Daddy suka jiran su,Baaba larai cousin d’in Mommy ce,kamar yadda mahaifiyar Mommy ta haifesu ita da maman kausar kawai
Haka ma kakarta ta haifi maman ta da maman Baaba larai saidai ita Baaba larai ita kad’ai aka haifa sannan har gobe Allah bai bata mijin aure ba,tun tana budurwa dama bata da samari
In k’awayenta sukayi aure
sai ta koma wajen k’annen su da k’awance, har da niece d’in k’awarta ta tab’a yin k’awance.
A lokacin da takai shekaru talatin a duniya sai y’an k’auyan su suka fara d’aura mata sharrin maita ko dan sun ganta fara sol ga gashi sannan kyakkyawa amman babu miji ne,oho.
A lokacin mahaifiyar ta ta jima da rasuwa
shiyasa mahaifiyar Mommy ta d’aukota daga gaban mahaifinta da matar sa ta rik’e ta,dan sharrin fama ya samo asali ne daga bakin matar uban.A yanzu kuwa iyayen nasu duk sun rasu shiyasa suka rungumi juna su uku
Ita da baba larai da kuma y’ar su Kausar.Badaban shi kan sa yasan Yahanasu y’ar kishiyar Mommy bace ba to da sai ya ce
Maybe a wajen Baba larai ta gado rashin auren amma dukda haka a kullum adduar sa itace’’Allah yasa kar y’ar uwar sa ta k’are kamar Baaba larai’’duk da cewa
ita Yahanasu tanada samari
kawai dai sai anzo maganar aure ganga ganga sai wani abun yazo ya tarwatsa’’

‘’Tana Ina?’’
Muryar Daddy ta katsewa Yashjub tunani.
‘’Tana sauk’owa’’ ya basa amsa yana me k’arasawa cikin parlourn kafin ya nemi waje ya zauna suka sake gaisawa da Anty Amarya dama shi ya Riga ya santa dan employee d’in su ce kawai dai baisan akwai abu tsakanin ta da mahaifin nasa ba sai yau daya ganta a matsayin matar uban sa.

Kafin su Mommy su sauk’o Daddy ya Kira Yadira yace ta kirawo kowa hatta drivers da Masu gadi da Kausar Yassir ne kawai bai hallara a wajen ba saboda har yanzu yau sati biyu kenan amman bai dawo gidan ba ya kashe wayar daya tafi da ita ma gaba d’aya.
Mommy bata wani b’ata lokaci ba suka sauk’o itama tare da Baaba larai
She looks calm amman fa kana ganin fuskar ta kasan tayi kuka.
Tana zama Daddy ya umarci
Yashjub ya bud’e musu taron da addua,ana shafawa ba tare da b’ata lokaci ba
Ya gabatar musu da Hajiya Saddik’a a matsayin Amaryar sa kafin ya d’aura da cewa
‘’Na san ta wajen aikin mu daya
Shekaru sha biyar kenan muna tare da ita
Mijinta ya rasu shekaru ashirin da suka wuce tanada yara mata guda biyu.’’
Daga haka ya ce
‘Ya na so tundaga kan yahanasu har izuwa kan Yadira
Kowa ya bata girma da respect
har masu aiki yana so duk kalar respect d’in da za a ba sa itama a bata baya so yaji wani case ko rashin d’a’a ya taso in kuwa haka ta faru to zai sab’awa ko ma waye’.
Masu aiki,Yahanasu sai Yashjub ne kawai sukace
‘’InshaaAllah Daddy’’.
Daganan masu aikin sukayi introducing kansu sannan suka sake gaisheta.
Sab’anin suYasmeen da suka d’auke kai ba tare da sun ce mishi uffan ba.
Baya son creating scene Shiyasa kawai ya rabu dasu
Da niyyar cin k’aniyar su in ya samu lokacin su.
Cikin kulawa ya juya ga Hajiya saddiqa
Itama yace ‘’ta d’auki yaran shi kamar nata
InshaaAllah bazata samu matsala da suba ‘’.
Ahankali cikin murmushi tace. ‘’InshaaAllah’’.
Sai a sannan Yasira ta daure dakyar ta ce
‘’Daddy tou me zamu dinga ce mata’’
Cikin jin dadi yace
‘‘Ummi, yaranta suke kiranta’’
Murmushi Yasmeen tayi
Tace
‘’sannu da zuwa ummi
We are glad to have u ‘’.
Cikin tsananin jin dad’i Hajiya saddik’a tace
‘’Nagode y’ar albarka’’.
Dan da da farko gabanta har ya d’an fara fad’uwa dan tayi tunanin Yasira zata amsheta fiyeda haka duba da yadda suka riga suka san juna tun a office shiyasa tayi mamakin yadda suka yi mata ita da y’an uwanta
Gasu duk mata.

Bayan an sallami masu aikin
hira ce sosai ta biyo baya
tsakanin Yasira,Yasmeen da ummi
Mommy ma tana d’an sako musu baki sama sama
Kafin daga bisani Daddy yace zasu wuce.
Sun yi mamaki sosai da sukaji Daddy yace ba anan zatazauna ba
Already an kaita sabon gidanshi dake a nndc quarters.
Tsit parlourn yayi dan hatta Yashjub sai da yaji ba dad’i,
Har d’aurin auren sai da yaje jiya amman Daddy bai ce masa ba tare dasu zata zauna ba
Kuma shi ya ce ma sa kar ya gaya wa kowa yayi shiru amman gashi shi ya b’oye ma sa abu bayan haka sabon gidan ai Mommy ya kamata ya kai tun da shima mansion ne kamar girman nan
‘’Okay ba damuwa,zamu
zo inshaaAllah,’’
Muryar Mommy ta dawo da gaba d’ayan su daga duniyar tunanin da suka dulmiya.

Ba yadda Ummi bata yi da
Ya’isha akan ta biyota su tafi tare ba
Saboda y’ar ta Munira age mate d’in Ya’ishan ce kuma jibi zata baro gidan Yayar ta koma wajenta a chan nndc d’in da zama
Amman Ya’ishan tak’i yarda
Tace tanada shirye shirye na masters d’in data fara recently
so tana buk’atar time ta nutsu ita kad’ai ta shirya abubuwa.
Badan taso ba ta tafi bayan sunyi mata alk’awarin zasuje inshaaAllah.
Har mota suka rakasu saids ukaga fitarsu tukunna suka koma ciki

Yadira ce tace
‘’Yanzu dan Allah Daddy ya ..’’
Dasauri Mommy ta kalle ta
dan haka ta ja bakin ta tayi tsit.Har sukayi dinner aka tashi
ba wanda yayi zancen
Ummi ko Daddy
Yashjub yayi musu saida safe
Ya wuce
Kowa ta nufi side d’in ta.
Ba abun da yafi yiwa Kausar dad’i irin yadda ta ga babu Yassir babu dalilin sa.
Dan ita Sam case d’in sabuwar kishiyar Mommy bai wani d’aga mata hankali ba,
saboda ta riga tasan k’aramar alhaki ce…….


Tunda Yashjub ya koma d’aki sam sai ya kasa
tab’uka komai zuwa yanzu tabbas ya fahimci yana buk’atar sanin more about Manubiya.Ya riga ya tsaya akan cewa ba son ta yake yi ba saboda taya ma za ayi ya sota in fact idanuwan ta kawai ya gani so there is anything ma dayake drawing na sa towards her maybe it’s the eyes dan ya tabbatar bai tab’a ganin kwatan kwacin masu kyawun su ba,ko kuma maybe akwai wata k’addarar da take jan sa gare ta watakila shi ya taimake ta a wani abun ko kuma ita ta taimaka masa.
A mazaunin haka ya bar lamarin,daga nan ya d’auki wayar sa ya kira Najeeb,yasan zai sha tsokana
amman gwara tsokanar Najeeb akan wannan rashin kwanciyar hankalin da yake fuskanta daga zuciyar sa dan in banda azalzalar sa ba abun da takeyi,
‘’I just need to hear more about her
daganan nasan shikenan
nothing else’’
Ya fad’a haka a fili cike da son gasgatawa kan sa iyakar
abunda yake buk’ata kenan .

Sai da Najeeb ya yi murmushi yana mamakin taurin kai irin na Yash,dan yasan yauma in ba da kyar ba akan Manubiya ne ya sake kiran sa.
saida ya girgiza kai yace ‘’hmm’’
tukunna ya d’au wayar ya kara a kunnen sa yace’’Hello Yash,how far’’

‘’Kar kace komai kuma karka tambaye ni meyasa,kawai Ina da buk’atar sanin more about wannan yarinyar’’
Yashjub d’in ya fad’a yana mai runtse idanu sannan ya yamutse fuskar sa kamar irin:
Meyasa ma na tambaye sa, d’innan.
Tabbas sai da Najeeb yayi da gaske
tukunna ya samu ya danne dariyar sa sannan yace
‘’To a gaskiya Yash bana keeping record akan students d’ina
Iyakar abun da na gaya maka jiya shi kad’ai nasani a game da ita amma y not in karb’a maka number ta in ya so sai kayi finding out yourself ???’’

Tun kafin ya rufe bakin sa Yashjub yace
‘’Kana hauka ne?kaga bafa
wani abun bane,i just saw her jiya jiya, so kar kayi min tunanin shirme’’.
Yana gama fad’in haka
yayi sauri ya kashe wayar dan tabbas in ya cigaba da magana ba iyakar Najeeb ba shi kan sa zai iya gano abun da yake ta k’ok’arin k’aryatawa tun jiya.

Innalillahi wa innailaihirrajiun
Ya shiga maimaitawa a ran sa
dan yana ajjiye wayar sai kuma ya fara jin haushin kansa na
Kashe wayar dayayi ba tare daya nace wa Najeeb d’in
Ya
nemo masa information about her ba……..





MANNUBIYA
14

Na
Humayrah Bulama

Elegant Online Writers.

Lokacin tafiyar da Al’ameen ya ce zai yi,ya cika,dan haka yaje ya samu Dr da nurses d’in,duk wasu abun buk’ata saida ya biya kuma ya bada number sa ta k’asar da zaije yace a kira sa in wani abun ya taso.Da kyar ya samu jidda ta yadda ta k’arba waya daga hannun sa.
A ranar da zai tafi kuwa kamar kar su rabu haka suka dunga yiwa juna rakiyar kura kafin ya samu ya rakata bakin k’ofar d’akin da Inna take jinyar ya bud’e mata yace ta shiga
tana shiga yaja ya rufe ya juya ya wuce da sauri yana murmushi….

Sai da Innah ta k’ara sati biyu a asibitin tukunna aka sallame ta,ba laifi jikin nata da d’an sauk’i.A cikin sati biyun nan
kuwa Manubiya bata jeba dan k’iri k’iri Baba ya hana ta zuwa dan haka ta hak’ura ta ci gaba da karatun ta dan exams zasu fara nanda kwana d’aya.

Y’an gidan su ma tun zuwan da Siyama tayi har yau ba wanda ya koma sai ya Yusuf dayaje sau uku.Baraka ma bata sake koma wa ba dan cewa tayi
‘’Ba zata je inda za a dinga wulak’an ta ta ba,zata dinga yi wa Innar fatan samun sauk’i
tana daga gida.
Matar Nafi’u kuwa kusan kullum sai taje dama ita tun fil’azal basa shiri da Baraka
amma dukda haka data lura bata zuwa saida taje har gida ta bata shawara,ai kuwa basu k’ark’e k’alau ba dan k’arshe ma baraka k’ofar fita ta nuna mata tace
‘’Ta fice mata a gida’’

Rufe rufen files ne da wasu en gwaje gwaje suka d’an tsaida su Baba daga dawowa da wuri.

Tun safe da Jidda tace wa Manubiya an sallame su ta gyara d’akin tass ta share tayi girki ta kunna turaren wuta ta wanke band’aki,sai zumud’i sukeyi itada Muhsin dan shima ba kasafai aka cika zuwa da shi ba,basu samu sun k’araso ba kuwa sai wajajen k’arfe uku.
Suna zaune a d’aki suka ji Baba yana gaisawa da Anty Umma.

Da zumud’i suka mik’e sukayi waje,anan tsakar gidan suka tadda rabin y’an gidan kowa ya fito yana duba jikin Innar tab’e baki Manubiya tayi a ranta tace
‘’daga baya kenan’’
daganan suka nufe su ita da Muhsin,a tare suka rungume Innar da take zaune akan wheelchair Manubiya harda hawayen ta kafin daga bisani
su wuce ciki y’an gidan ma kowa ya wuce d’akin sa.

Suna shiga Manubiya ta shiga gaba tar musu da abinci,ita da Jidda ne suka bawa Inna,ta ci kuwa ba laifi duk da rabi duk ya zube saboda har yanzu gefen bakin nata ba aiki yake yi sosai ba.Haka suka zauna suna y’ar hira ana cin abinci gwanin ban sha’awa ba wanda zai kalle su yace sunada wata matsalar,dan hankalin Baba a mugun tashe saboda bai san yadda zaiyi ya biya en basusssukan dayaci waenda sauk’a zama dole ba sannan bai san yadda zaiyi ya ci gaba da kula da iyalin nasa ba, amma sam bai bari sun gano ba halin da yake ciki ba haka ya biye su akayi ta raha.
To haka a b’angaren Ya Musbah yayi k’ok’ari ya danne ta sa matsalar aka ci gaba da hirar suna ta yak’e daga shi har Baba


Kiran sallar la’asar ne ya tashi zaman nasu maza suka tafi masallaci matan kuma suka yi a gida.
Sai a lokacin Jidda ta samu damar zama da Manubiya
dan Inna har ta samu bacci

Ahankali suna ida addu’a
Jidda ta kamo hannu ta tace
‘’Adda Manu ina ta so muyi magana amma ban samu right time ba sai yanzu’’. Da kulawa
Manubiya ta juyo tana kallonta
tare da bata dukkannin attention d’in ta.
Tun daga ranar data hana Al’ameen zuwa ta kuma hanata kula sa ita kuma ta cigaba
Ba abunda ta b’oyewa Manubiya sannan ta mik’e taje jakarta ta kawo wayar daya bata ta nuna mata


Cikin son fahimtar da ita manubiya tace
‘’Jidda ban hanaki kula Al’ameen ba saida na duba
na ga abun da hakan kan iya janyowa,Jidda mahaifiyar sa bata k’aunar ki ki duba kiga halin da muke ciki kar ki je ki sake janyo mana wata matsalar,tunda yace miki Ammin na sa zata zo kinji ko waya tayi??’’

Ahankali Jidda tace
‘’Yace min tayi tafiya ne Adda Manu ki fahimce ni dan Allah
Ina son Al’ameen nima,kawai ki tayani da addu’a dan shine farin ciki na banajin zan iya rabuwa da shi,a matsayin ki na y’ar uwata ina tunanin ke zaki fara fahimtata..

Cikin katse ta Manubiya tace
‘‘Jidda,ba wai inaso inyi going against farin cikin ki na yanzu bane ba,Inaso ki samu dauwamammen farin ciki na har abada shiyasa kika ga Ina haka,in yace mahaifiyar sa tayi tafiya ai ya kamata ace ko waya ne kunyi keda ita’’

Sallamar Siyama ce ta katse su dan haka duk suka d’ago atare suna mata murmushi.
Itama murmushin ta mayar musu
Kafin tace
‘’Tare nake da bak’uwa ta shigo?’’

Ba tare da sunsan Wacece ba
Sukace mata ‘’eh.’’
Tana shigowa gaban Manubiya ya yanke ya fad’i amma sai ta dake tace mata ‘’Ina wuni’’
daganan ta mike taje ta d’auko darduma ta shimfid’a mata.

Cikin sunkuyar da kai Jidda ma ta gaida mahaifiyar Al’ameen (Ammi).
Duk jimla tayi musu ta amsa gaisuwar tasu kafin ta juya ga Siyama tace ‘’taje ta kira mata Uncle taga shigowar sa yanzu’’ .
Kana ganin yanayin fuskar ta kasan ba dubiya tazo yiba.
Dan haka duk suka zauna shiruu kowa da abun da yake tunani.
A tare Uncle,Ya Musbah,Baba da Muhsin suka shigo d’akin,da sallama.

Tunda Baba ya ganta a gidan dama yasan ba lafiya ba
amman sanin dayayi ya riga ya raba y’ar sa da d’anta
yasa ya d’an ji sauk’i,duk da yasan ba lalle Al’ameen d’in ya gaya mata ya basu kud’i ba
amma dama a shirye yake
yana ta k’ok’arin neman bashi ya samu ya had’a kan kud’ad’en da Al’ameen d’in ya basu saboda dama ya san fitinar mahaifiyar ta sa
kuma a lokacin da Al’ameen d’in yace zai taimake su
Inda ya k’i amince wa yasan yaron ba zai ji dad’i ba bayaga haka ma basu da yadda za suyi a wannan lokacin.

Da Uncle suka fara gaisawa
sai Ya Musbah da Muhsin
kafin Baba Musa ya kalle ta yace
Barka da yamma,Ammi.

‘’Barka dai,Musa’’
Kawai Ammin tace ba tare da ta kalli inda yake ba.Daganan kowa yayi shiru d’akin kafin
Uncle ya kalli Manubiya yace
‘’Manu ke da su Muhsin ku d’an bamu guri ko?’’

Da sauri Ammi tace
‘’A’a,ai zuwan nasu ne,ma’’.
Bata jira jin mai za’a ce ba ta juya ta kalli Baba ta fara magana
‘’Kwanakin baya,mun samu matsala daku akan wannan yarinyar Maijidda data mak’ale wa Yarona ta shiga tsakani na dashi har sai da takai ta kawo yadena yi min biyayya,an samu an gyara matsalar kwanaki dakyar yanzu kuma an koma ruwa

Dasauri Uncle yace
‘’A’a fa Misunderstanding dai aka samu Ammi dan rabon Jidda da Al’ameen ai tun kwanaki da muka yi musu tsakani ko ba haka ba?Jidda’’
Yayi maganar yana mai kallon side d’in da Jiddah take nan kai a durk’ushe.
Kafin ya juyo ya kalli Ammi yace
‘’Kuma ina Al’ameen d’in baya nan ma?jiya naji yaran nan maza suna cewa ya tafi England ko’’

‘’Eh ya tafi akwai course d’in da zaiyi shiyasa ma na samu nazo nan dan cewa yayi muddin nayi wani yunk’urin sake raba sa da Jidda to babu ni babu shi’’
Cewar ammi
Sannan ta d’aura da cewa
‘’Already Al’ameen yana da matar da zai aura an riga an gama magana,shi kad’ai Allah ya bamu
Dani da mahaifinsa
Muna da burin muga ya samu rayuwa da abokiyar rayuwa wadda ta dace dashi
Baxan b’oye muku ba Jidda is the last person a duniyar nan da zan so yarona ya aura,a kwanakin baya ban fuskanci Jidda da lamarin nan ba na fuskance ku mahaifinta ne saboda naga kune magabatanta kuma a tunani na yarinya ce amma yanzu ta nuna min cewa ta girma kuma tafi k’arfin ku dan haka
Ki saurara kiji’’
Tayi maganar referring to Jidda da ta fara kuka k’asa k’asa.
‘’Duk zuwan da yake yi da irin kud’ad’en daya ke kashewa
nasan komai
Dan haka …..’’
Dasauri Manubiya tace
Ammi Mahaifiyar mu bata da lafiya at least in baki yi considering d’in ta ba..’’

Cikin d’aga murya Ammin tace
‘’Na tabbatar in na bar Al’ameen tare da Jidda nima condition d’ina sai ya dawo irin na mahaifiyar taku tsabar bakin cikin da zata dinga d’ura min.’’
Ciki d’acin zuciya ta juya ta kalli Uncle tace
‘’tun da na haifi Al’ameen
bai tab’a min musu ba
sai da ya had’u da yarinyar nan Wallahi’’.

Cikin katse ta Manubiya tace
‘’Kar ki d’aura alhakin taurin kan d’an ki akan mu,tun da ba ke kad’ai yake yi wa ba,ki tambaye sa kiji yadda muka dinga cewa kar yazo inda muke amma sai da yazo,baya ga haka a gani na ai ke kika haifi Al’ameen in yayi taurin kai
ko yak’i yi miki biyayya it means ke kika kasa sannan ke kika sangarta abunki …..’’

‘’Manu!!’’
Ya Musbah ya kira sunanta da kakkaurar murya yana kallonta
da idanuwan sa da suka kad’a suka yi jazir.
Sai a sannan Ammi ta d’auke idanuwan ta daga kan Manubiya ba tare da tace komai ba ta mik’e ta kalli uncle tace
‘’Shigowa dana yi d’akin nan ya ishi k’ask’an ci ba sai na tsaya wannan y’ar ta gaya min magana ba
Inka lura ko uban su bai isheni kallo ba shiyasa na kira ka akan kayi mana alk’ali nida Jidda,amma tun da basu san sulhu ba sannan basu san
banbancin dake tsakani na dasu ba inaso ka gaya musu nace duk abun da Al’ameen ya kashe musu su dawo min dashi
kafin nan da awanni ashirin

Please Login or Register in order to submit comment