Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

aura masa mata d’aya in bar masa d’aya kamar yadda ya keso
kowa ya tafi safe
A rabu ba tare da wani fad’a ko grudges ba,kaga sai mun fi keeping relationship d’in dake a tsakani na da kai safe and alive.
One more thing
Inaso kusan cewa ba za ku iya sharia da black snake ba,
So idan ma kuna tunanin court ne
na wuce nan a very long time ago
I have my ways!.’’

Dakyar Abbakar ya iya d’ago wayarshi ya kira sir Najeeb
bai d’auka ba dan haka ya samu ya tura mishi message
da taimakon ya Nafi’u wanda ya tambayeshi ‘’mai zai yi?’’shi kuma yace masa ’’wanda zai taimakesu zai kira’’

Dan haka ya gaya mishi
ya rubuta;
Manubiya tana buk’atar taimakon Yash da gaggawa
Da
Address d’in police station d’in da suke a k’asa.

Daga haka suka tura ba tare da an gansu ba.

Kishi haushi da takaicin abun da ya sake aikatawa wanda ya yiwa kan sa alk’awarin ba zai kuma ba ne…suka taru suka sake zuzutamasa azabar daya ke a ciki…dishi dishi ya fara gani daga haka idanuwansa suka rufe,ya sume a wajen yana mai addu’ar Allah ya sa Yash d’in ya zo , dukda kuwa kishi da takaicin sake had’ashi da Manu da yayi a karo na biyu yana ta addabar zuciya da ruhin sa amman kuma ba zai iya barin Manubiya a cikin wannan bala’in ba,bayan ya san akwai hanyar da zai bi ya cece ta.

A chan gefe kuwa,wani
a cikin guards d’in black snake ne ya tak’ark’are yana yi masa
bayanin yadda ake auren Musulmai dalla dalla,dan bai
gama sani ba kasancewar sa Christian.

A take suka yanke shawarar za a yi na musulmai
kuma za a yi na Christian’s duk a wajen a yau
dan haka ya ce wa d’aya a cikin guards d’in nasa ya tafi ya d’auko pastor dinsu na church ya zo da shi kafin a gama d’aura na musulman.
………
Kuka gaba d’ayan su sukeyi
ga Abbakar a yashe ance za a kaishi asibiti
Black snake yace’babu uban wanda zai yi motsi sai an gama aura masa Manubiya.
Zuwa yanzu su kam sun d’auka ma Abbakar d’in ya rasu ne saboda dogon suma yayi mai nauyi in ka gan shi baza ka yi tunanin akwai rai a jikin sa ba.

Saida aka saitawa ya Musbah da ya Nafi’u bindiga tukunna suka nutsu
Baba kuma ya ce shikenan ya yarda zai d’aura auren ya fad’I haka yana tunanin ta yadda zai nemi mafita su samu su zille.

Wani kalar murmushi black snake yake ta zubawa wanda ya ke nuna tsantsar farin cikin daya ke ciki,bai tab’a had’uwa da macen da ta sace zuciyar sa tashi d’aya kamar Manubiya ba shiyasa har Allah Allah yake ayi ayi a d’aura musu aure ya samu full control over her zata ga soyayya,ya san za ta yarda da shi duk kuwa taurin kanta da yadda ya fahimci tanajin tsoronshi yasan in ta ga ya riga ya zama mijinta to dole ta yarda da shi sannan zai samu full control akanta dan yasan za tayi mishi biyayya….Ga Manubiya matar sa wadda zata haifa mishi y’a y’a ga kuma jidda a gefensa mistress
wannan wacce irin lucky rana ce ta riskeshi haka!
ya zama dole ya yiwa Kabir babban kyauta in komai ya tabbata.

Around 2:OO pm
yana tsakiyar meeting kira ya shigo wayarshi,kamar ba zai kalla ba sai kuma ya d’an zaro wayar,ganin sunan Najeeb yasanya shi saka wayar a silent ya ajjiye ta a gefen sa dukda kuwa ya san koma menene tou it’s very important tunda har Najeeb ya sake kiran shi a yanzu a wannan time d’in…dan ba su dad’e da gama waya da shi ba ya ce masa ‘zai sake shiga wani important meeting d’in da su Daddy bak’in nasu har yanzu basu tafi ba but in ya fito zai kira shi.’
Ba zai yiu ya amsa wayar ba,dan meeting d’in da suke yi is very important,shiyasa ya bari akan in sun gama meeting d’in sai ya kira Najeeb d’in ya ji dalilin kiran,he just hope abun is not too important and urgent sannan he hope by the time d’in da zasu gama meeting d’in abun bai riga ya zama too late ba….




MANNUBIYA
37
Na
Humayrah Bulama

Mikiya Writers Association.

Ba zai yiu ya amsa wayar ba,dan meeting d’in da suke yi is very important,shiyasa ya bari akan in sun gama meeting d’in sai ya kira Najeeb d’in ya ji dalilin kiran,he just hope abun is not too important and urgent sannan he hope by the time d’in da zasu gama meeting d’in abun bai riga ya zama too late ba….

Kiran Yashjub Najeeb yakeyi yana sake maimaitawa..ganin ya jera masa kira ya fi sha biyar amman bai d’aga ba ne ya sanya Najeeb d’in ya yanke shawarar ya tura masa message kawai,dan haka ya rubuta:’Yash,Manubiya needs you,ban san menene ya faru ba amma her friend(Abbakar)yace
It’s very urgent!.’
Daga haka ya tura masa tare da adress d’in police station d’in da su Abbakar d’in suka turo,yana adduar Allah yasa ya gani ya kira.

A b’abgaren Yashjub kuwa dama tun d’azu ya nemi nutsuwar sa ya rasa haka kurum yake jin wani iri,so yake ya amsa kiran ko yayi excusing kan sa ya fita amma kuma yasan in yayi haka zai gamu da b’acin ran Daddy ba na wasaba,yana cikin wannan tunanin ya ji k’arar shigowar message dan haka ya juya ya kalli wayar tasa.
Wani Irin mahaukacin bugawa k’irjin sa yayi,bai san lokacin da ya mik’e tsaye ba
sakamokon message d’in sir Najeeb daya samu damar karantawa ta saman notification bar.

Dasauri Daddy yace
‘’Yash.’’

A d’an rikice ya kalli Daddy
sai kuma ya kalli Yasira da ragowar turawan dake a wajen kafin ya ce’’sorry,i have to
go it’s very important’’
Ya fad’i hakan yana mai kallon wayar ta sa sannan yana kallonsu,kafin ya tura kujerar tasa baya ya d’au wayar ya fita daga hall d’in gaba d’aya
kamar walkiya yana mai cewa’’ pls excuse me’’


Yana fita ya shiga dialing number Najeeb…in banda bugawa ba abun da k’irjinsa yake yi..Manubiya a police station kuma!how?garin yaya!, shi da yake ta fafutukar zuwa k’auye wajen ta,mai ya dawo da ita har ta kaita ga zuwa police station.
Yana wannan tunanin yaji Najeeb ya d’auka a d’an rikice yaji muryar Najeeb d’in sannan kamar ma driving yake yi,dan yana amsa kiran yaji Najeeb d’in ya fara magana’’kaga message d’ina ko?
Abbakar ne ya kirani yanzun ban samu na d’auka ba shine ya turomin message inaga shima yana wajen.
Ina ganin message d’in na kira sa,an d’auka but ba a magana,
Babban abun tashin hankalin kamar muryar black snake naji a wajen,kuma Yash it’s like maganar aure suke yi
da shi da Manubiya!amma
ka kwantar da hankalinka
ganinan nama kusa police station d’in.’’

Kashe wayar kawai yaji Yashjub d’in yayi…..a yadda ya nufi k’asa sai da ya bawa wasu
tsoro da mamaki,dai dai nan Daddy yana fitowa dan akwai
speech d’in da Yashjub d’in zai bada kuma lokaci yayi.
Cikin fushi Daddy ya bi sa a baya amman kafin ma ya gama sauk’a k’asan ya hango tashin motar Yashjub ta glass d’in gefen stairs d’in…Tabbas zai ci uwar Yashjub kam yau!Daddy ya raya hakan a cikin ransa
amma yanzu bari ya koma ya gama da waennan mutanen,first.

Kafin ya koma hall d’in ya turawa Yasira message yace ta shirya ita za ta bada speech d’in a madadin Yash,hakan kuwa aka yi Allah ya taimaka Yasirar ta san kan abun,dan haka ta d’an had’a abubuwan da za ta iya ta bayar taron ya watse.
Daddy kamar ya fashe saboda tsananin takaici dan ko da ya koma kiran Yashjub yaci gaba da yi amman sam bai d’auka ko d’aya ba,k’arshe ma message ya yo masa wai ‘’wani abu important ya taso masa,su k’arashe meeting d’in babu shi kawai!’’.
What could be more important than meeting d’in nan da saving dignity d’in company da dignity d’in shi kan sa Daddyn,wanne
irin abune zai sanya ya tafi ya bar sa stranded cikin bak’in mutane haka ya kunyatashi…..


Tun kafin ya k’arasa police station d’in ya kira babban office na dss yace ‘yana
buk’atar su
Black snake yana Nigeria,kano.Sannan ya fad’a musu sunan police station d’in.’
Ashe da ma neman sa ake yi ruwa a jallo.

Sun tab’a yin case da Yashjub ‘ya so ya cinye masa fili da kyar ya kwato filin sa’
a ta dalilin hakan ne Yashjub ya san wayene black snake da kuma record d’in sa dan ko last week sai da sukayi maganar sa da Najeeb akan ‘ya je ya gina hotel a filin wani yace filin na sa ne ana tsakiyar yin case d’in daya ga za a damk’e sa shine ya gudu’.
Kuma still an banka’do ‘yayi snadiyyar sace y’an mata y’an secondary school guda ashirin’.
Shiyasa da yaga za a masa tunb’ir a tona masa asiri sannan a kamasa shine fa ya gudu zaman Nigeria ya gagare sa,ya bari akan in komai ya lafa sai ya dawo.

Yash yana gama waya da DSS
ya kira AIG yace ‘’a dakatar da duk wani abu da ake gudanarwa a police station d’in da Najeeb ya gaya masa su Manubiyan suke’’,sannan yace’’ kar a bar kowa ya fita,dss suna hanya za su kama black snake’’

Tafiyar minti goma ce ta kaishi police station d’in dan bashi da nisa dasu sannan bai bi k’a’idodin hanya da titi ko guda d’aya ba sakamokon uban gudun da ya tsula kamar ba gobe.

Motar sa tana yin parking ta wani dss shi d’aya ko uniform babu a jikin sa ta yi parking,da sauri ya k’araso ya nuna wa Yashjub id card d’in sa kafin yace ‘’kai ne ka yi waya ko?ina kusa sosai naga assignment d’in shine na k’araso da wuri but mota biyar tana hanya yanzunnan zaka gansu inshaaAllah.

Sam Yashjub bai ji dad’i ba dan yaso tawagar su ce tazo da wuri haka saboda ya san black snake baya yawo shi kad’ai
dan ga police station d’in ma yanzu haka ya cika tapp da motocin daya tabbatar na sa ne da shi da Jama’ar sa.

Kamar yadda jami’in dss d’in ya nunawa Yashjub Id card haka ya k’arasa ya nuna wa ragowar y’an sandan dake harabar wajen id card d’insa dan haka a take suka sara masa suka bi bayan sa sukai ciki gaba d’ayan su……

4 minutes before now.

Ana shirin fara d’aura aure
Dpo ya fita domin amsa waya
kafin minti d’aya sai gashi ya dawo…jikin sa har yana d’an karkarwa.
Da mamaki black snake ya ke kallon sa yana shirin yin magana Dpo d’in ya k’arasa inda yake yace
‘’Muna da problem fa!an san kana nan’’

Dariya black snake d’in yayi kafin yace
‘’Relax babu wanda ya Isa ya yi arresting ko ya yi stoping d’ina’’


Cikin yin k’asa da murya yace
‘’Ban san ya akayi ba amman Dss ne a hanyar zuwa nan fa black snake,sun san kana nan gurin
they are on their way as we speak,sannan oga kwata kwata ya kirani yace
In tsayar da koma me ake yi anan sannan inyi arresting d’in ka,da farko ma suspending d’ina ya yi sai da na rantse masa akan ban san da case d’in ‘ana neman ka’ ba tukunna ya bar ni yace in tabbata na yi arresting d’in ka!’’

Take a alokaci d’aya fuskar black snake ta chanza daga jin batun dpo,cikin fushi ya d’ago yana kallon kowa….sai kuma yayi tunanin ai mutanen nan basu da power d’in da zasu kira someone influential haka.
Maybe wani Abokin hamaiyyarshi ne yaji labarin zuwan sa shine akayi masa chune
Besides ai tun d’azu yana tare dasu Manubiyan kuma babu wanda ya ga yayi waya a cikin su.

Yana wannan tunanin yaji dpo yace
‘’Sir,wannan ba lokacin tunani baneba,u need to leave now!ka san su kamar aljanu yanzun nan zaka ga sun k’araso.’’

Cikin fushi black snake d’in ya juya buguzun buguzun
Yaje shi ya damk’i hannun Manu ya fara janta sannan yacewa yaran nasa su kamo
Jidda
duk wanda yayi yunk’urin hanasu su kaishi lahira.

Ya Nafi’u ne ya danne zuciyar sa da kkyar ya iya rik’e Ya Musbah dan ya san muddin suka shiga to kashe su mutanen nan za suyi kuma in sun mutu ba za su samu su kwato su Jiddan daga hannunsu ba.

Dakyar Baba ya had’a gaba d’aya k’arfin sa da ragowar kuzarin da ya rage masa ya samu ya mik’e tsaye,jikinsa
yana karkarwa ya tsaya a inda black snake yake k’ok’arin bi ya wuce,yace’’ka kashe ni kawai!a kan in bari ka tafi da y’ay’ana har biyu a gaban idona gara kawai ka kashe ni!’’.

Wani wurgi black snake yayi dashi wanda ya sanya shi ya tafi ya je ya daki gini
Cikin fushi black snake yace
‘’Ban tab’a had’uwa da tsoho mai audacity irin ka ba!kar ka damu ba zan kashe ka ba amma tun da na lura kamar ka fi son wanchan Yaron naka mai kama da kai a cikin y’ayan naka maza to shi zan kashe’’.
Ya yi maganar referring to ya Musbah.

Now.

‘’Ba za ka kashe kowa ba black snake’’
Muryar jami’in dss d’in da suka shigo tareeda Yash ta
katsesu sannan ta maida hankalin kowa gare su.

A take Yashjub ya ji ran sa yayi wani irin b’aci,zuciyar sa ta cunkushe tana tafarfasa sakamokon yadda yaga black snake ya k’ank’ame hannun Manu
gashi sai k’ok’arin kwace wa takeyi tana wani irin kuka kuma ko damuwa bai yi ba
gashi daga ita sai doguwar riga da hula wuyanta duk a waje!
Bai san lokacin da ya k’arasa ya fincike hannunta a cikin na black snake d’in ba sannan ya hankad’asa gefe

Wani irin murmushin takaici black snake yayi kafin yace
‘’Yashjub!the hero..we meet again!’’

Banza Yashjub d’in ya yi dashi kawai ya juya inda ya hango hijabin Manu a yashe ya k’arasa yaje ya d’auko ya mik’a mata yana mai k’ok’arin danne fushin sa.
Dai dai nan jami’in dss tare da dandazon y’an sandan da suka biyo bayan su da shi da Yashjub suka yi kan black snake

Without thinking twice
Black snake ya harbi ss d’in a ciki
wanda hakan yasanya gaba d’aya y’an sandan suka rufar masa dama rabi a cikinsu duk bakin su d’aya da dpo ba wai son kama black snake d’in sukeyi ba,ai kuwa hakan ya bashi dama da shi da tawagar sa suka fice da gudu
Bayan ya kalli Baba yace masa,’’zan dawo d’aukar matata soon’’

Da sauri Yashjub yayi kan jami’in da aka harba,ganin
yana motsi yasa yace su danne gurin su kai sa mota a wuce dashi asibiti.
Shi kuma yabi bayan su black snake da gudu
amman ya na zuwa
sai k’urar motocin su kawai ya tarar.
‘’Damn it!!’’
Ya furta da k’arfi,yana jin
takaici kamar ya kurma uban ihu.
Dai dai nan motar Najeeb ta k’araso cikin harabar gurin tare da dandazon motocin jami’an dss.
Najeeb yana k’araso wa yace
‘’Kar ka damu,rabin motocin sun bisu,za’a kama sa inshaaAllah,bai dai tab’a kowa ba ko?’’

Cikin b’acin rai Yashjub yace
‘’Ya harbi mutane uku’’

A rikice Najeeb yace’’subahanaallah,da wa da wa??,ina Manubiyan take?’’

‘’Tana ciki!’’
kawai Yash ya iya cewa
daga haka ya juya ya nufi ciki
bayan ya kira ambulance
dan wani irin takaici yake ji,ya riga ya san definitely ba za a iya kama black snake ba.

Suna shiga polisawan da wasu a cikin ss d’in suna fitowa d’auke da jami’in da aka harba.
Statement ya tarar ragowar ss d’in suna karb’a a wajen ya Musbah da ya Nafi’u yayin da Jidda da Manubiya suke kuka suna dudduba Baba.

Dukda abun da black snake ya aikata sai da Yashjub ya karb’i acc number d’in sa a wajen dpo ya tura masa 1 million d’in sa dayake bin Baba bayan yaji bayanin komai da ga bakin dpo.Zuwa yanzu gaba d’aya ran Yashjub ya sake b’aci daga jin bayanin,tabbas in da ace zai ga black snake yanzu to kuwa in bai kashe sa ba sai ya sumar da shi,musamman ma da ya ji cikakken labarin maganar auren da yaso a d’aura masa shi da Manubiya!
wato da niyyar auren Manubiya yake yi!in ya yi tunani ma akan
‘Black snake d’in fa yayi tunanin auren Manubiya,kenan
ta kwanta masa shima son ta
yake yi’, sai ya ji kamar ya bazama ya nemo sa ya chaka masa wuk’a,how dare he!.




MANNUBIYA
38

Na
Humayrah Bulama

Mikiya Writers Association.


Shi yasa gaba d’aya har aka gama case d’in aka gama karb’ar statements d’in su
suka nufi asibiti sam fuskar sa babu walwala ya had’e girar sama data k’asa ko magana ma ya daina yi.

Private hospital aka nufa da Baba da Abbakar,suna zuwa aka karb’esu emergency.
……
Wayar da Yashjub yayi aka tabbatar masa da ‘black snake ya gudu ba a samu damar kamasa ba’ne ya sake harzuk’a sa!

Duk da halin da take a ciki sai da ta lura da shi dama tun d’azu yanzu kuma ta tabbatar wayar da akayi masa ce ta sake b’ata masa rai,so take atleast taje ta ce musu sun gode dukda ta ga su Ya Musbah sun yi musu godiya sosai har exchanging phone numbers ma taga sun yiyyi but still itama ya kamata suje suyi musu godiya ita da Jidda sai dai kuma tana shakkar kar ta je ya maketa dan in ba lokacin da suke exchanging numbers da su Ya Musbah ba to bataga ya saki fuska dede da na second d’aya ba!sannan kuma
tana jin kunyar sa dan in ta tuna abunda ta yi masa jiya da safe gaba d’aya sai ta ji wani iri babu dad’i! duba da yadda yanzu yake tsaye tsayin daka akan al’amarin daya kusan tarwatsa rayuwarta da ahalinta.
Gashi yanzun kwata kwata bata hango walwala a tare da shi ba
masifa yake yi wa kowa hatta sir Najeeb yanayin yadda taga yana masa magana kamar zai rufe sa da duka take gani,waennan dalilan ya sanya ta d’an dakata tana mai tunanin ta yadda zata yi masa godiyar.


Sallar la’asar aka kira dan haka gaba d’aya mazan suka fita masallaci su kuma suka nufi band’akin da suka tambaya aka nuna musu,Sallah kuma suka nemi waje inda babu mutane sosai suka gabatar da ita cikin nutsuwa,bayan sun idar sukayi addu’oin samun lafiya wa Baba da Abbakar har ma da Inna.

Basu dad’e da dawowa wajen ba su Yashjub ma suka shigo
shida sir Najeeb su Ya musbah a bayansu

Ba k’aramin dad’i Manubiya ta ji ba,dan bata yi tunanin za su dawo su jira har sai an gama treatment d’in su Baba ba,hakan ya sanya har bata san lokacin da murmushi ya sub’uce mata ba tana murmushin tana kallon Yash d’in
dai dai shi kuma ya d’ago kan sa shima da niyyar ya d’an saci kallon ta ai kuwa karaff suka had’a ido da ita tana kallon sa tana murmushi.
Da mugun sauri ta sunkuyar da kanta k’asa ta fara wasa da y’an yatsun hannun ta,murmushi sosai ne ya kufcewa Yash wanda har sai da sautin murmushin ya fito fili
Dasauri sir Najeeb ya d’ago yana kallon sa
ganin inda yake kalla yana murmushin ne yasa Najeeb d’in yin wata y’ar guntuwar dariya kafin yace’’Romeo a asibitin ma ba za’a d’aga k’afa ba?’’

‘’Hmm’’
Kawai Yashjub ya iya cewa Najeeb dan gaba d’aya Manubiya ta sanya shi a wani yanayi shiyasa ko iya juyawa ya kalli Najeeb d’in ma bai yi ba dan gaba d’aya idanuwansa da hankalin sa kacokam yana akan ta ne!so yake yi ta sake d’agowa ya kalleta amman sam tak’i ta ma yi k’asa da kanta sosai.
Ganin tak’i d’agowa shi kuma zullumi yana shirin susuta shi ne ya sanya kawai ya nufi inda take.
Dama kuma yanata so ya d’an yi mata magana ko akwai wani abun bayan wanda dpo ya gaya mishi amma ya lura tanata kuka shiyasa ya d’aga mata k’afa saboda jin kukan nata yake yi har cikin ransa a lokacin da take yi….dan har ga Allah yasan in ya je kusa da ita tana wannan kukan za’a iya samun matsala,kukan ta yana cikin worst things d’in da baya buk’atar gani a duniyar nan.

Tabbas Manubiya ta fahimci inda take yake nufo wa,dan haka tashi d’aya fargabarta ta k’aru,dama ga fargabar jikin su Baba dan ma an tabbatar musu da jikin na Baba
Is not that serious
Abbakar kuma yanada rai

Tana wannan tunanin ta ji sa a tsaye a kanta,ji ta yi kamar ta mik’e tsaye ta ruga a guje.Ba ta ida jan numfashin daya mak’ale take kokawar janyoshi da kyar ba ta ji yace’’in zauna??’’

Dakyar da mugun kyar dan sai da ya sake maimaitawa tukunna yaga tad’an matsa kusa da Jidda sosai sannan tace masa’’eh’’a hankali.
Murmushi yayi kafin ahankali ya nemi gefen ta da d’an tazara kad’an ya zauna cikin nutsuwar sa bayan yayi bismillah.Yanayin zaman da tayi sai da ta bashi dariya,
ya lura da yadda ta wani zabura lokacin da ya zauna d’in sannan ta kuma matsawa jikin Jidda sosai
Murmushi kawai yayi ya amsa gaisuwar Jidda yana mai kallon ta
Ahankali tace’’Mun gode sosai Allah ya saka da alkhairi’’
Murmushi yayi kafin yace’’ba komai Allah ya kare gaba ya ba su lafiya’’

‘’Ameen’’ tace,daganan ta yunk’ura zata tashi dan ta lura kamar yana d’an bukatar space da Manubiyan amma sai ta ji Manubiyan tayi saurin damk’ar hannunta ta rik’eta gam.
Ahankali Jiddan ta gyara ta zauna a wajen ba dan taso ba
itama ta sunkuyar da kanta ta shiga wasa da bakin hijab d’in jikin ta,har ga Allah ta jinjinawa Yashjub da abun da ya yi musu
dan tun d’azu da Manubiya tace mata ai shine wanda take yiwa aiki Jiddan take ta mamaki,a zamanin nan na yanzu wanne employer ne yake damuwa da matsalar employee d’insa haka,wata zuciyar ce tace mata ‘’kodai!kodai!!’’dan haka ta d’an yi murmushi ita kad’ai taci gaba da lissafe lissafen ta.

Ba k’aramin burge Yash su Manubiya sukayi ba…yadda suke da kunya da kamun kai
tabbas yasan iyayen su sunyi k’ok’ari wajen tarbiyyar su
dan ko ba a fad’a mishi ba
ya fahimci jiddda k’anwar Manubiya ce sakamokon tsananin kamanni da yaga sunayi
Banbancin Jidda da Manubiya
yanayin girman jiki kalar fata da ido ne kawai..Manubiya tafi Jidda tsayi da jiki kad’an,kalar
fatar Jidda fara ce ita tass sosai Manubiya kuma ba b’aka bace ba kuma fara bace sosai,
Idanuwan Jidda sunfi na Manubiya girma sosai amma na Manu sunfi na Jidda kyau da d’aukar hankali..a ransa yace’’ idanuwan da suka kusan haukatani ‘’sai kuma ya d’an yi murmushi kad’an.

Shiruu duk suka yi kafin Yash ya katse shirun ta hanyar ce wa Manubiya
‘’Sister d’in ki ce ko?’’

Ahankali ta d’an jinjina kanta sai kuma tace ‘’eh’’daganan shiru ya sake biyo baya

Still shi ne ya sake kawo k’arshen shirun ta hanyar cewa ‘’Baba zai samu sauk’i,inshaaAllah kar ki damu everything will be fine inshaaAllah’’

Ahankali tace
‘’InshaaAllah,’’itama Jidda tace’’inshaaAllah’’a cikin ranta.

Ahankali Manubiya ta lumshe idanuwanta tana mamakin yadda k’iri k’iri ta gagara yi masa godiyar da take ta zumud’in son yi,gaba d’aya duk sai taji ba dad’i ta yadda ko ishashshiyar gaisuwa ta gagagara shiga tsakanin su..Yo ta inama zata iya itafa tunda ya zo ya zauna a kusa da ita shikenan ya sakawa tunani,kuzari da duk wasu lissafin ta full stop.
Ganin rashin kyautuwar abunda ta yi ne yasa ta yi da gaske da kyar ta samu ta d’an d’ago kanta da niyyar ta kalle shi shi tayi mishi godiya, suna had’a ido tayi sauri ta fara kallon gefen kunnen sa sakamokon wani irin kallo da ta ga yana

Please Login or Register in order to submit comment