Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a muryar Yashjub d’in,kafin yace’’inaga kamar d’an uwan ta ne,Maybe cousin dan surname d’in su ba d’aya bane amma wani lokacin ma tare suke shigowa aji ina ga kamar a gida d’aya suke zaune,are u jealous?’’Najeeb ya k’arashe bayanin nasa da tambaya,yana mai dariya k’asa k’asa.

Tsaki Yashjub d’in ya yi,dai dai nan Racheal ta d’an yi knocking tukunna ta yi sliding k’ofar ta shigo Manubiya na biye da ita a baya.
Sama sama ya fara jin Najeeb
saboda lokaci d’aya jikin sa ya yi sanyi sannan bugun zuciyar sa ta k’aru,ahankali ya cewa Najeeb’’I’ll call you back’’bai jira jin mai Najeeb d’in zai ce ba ya katse kiran,yana jin yadda yanayin sa ya sauya ta shi d’aya.

Cikin nutsuwa Racheal tace’’Sir she’s here’’
Ahankali ba tare da ya juyo ba yace’’Thankyou,you can leave’’.

Racheal d’in ce ta nunawa Manubiya in da zata zauna kafin ta juya ta fita bayan Manubiyan ta zauna da kyar, tun da suka shigo company d’in jikin ta yayi sanyi,tun da ta hango sa a tsaye ya juya baya ta nemi kuzarin ta ta rasa gashi yanzu kuma tun da ta shigo office d’in k’irjin ta ya hanata sukuni
Kamshin turaren daya karad’e ilahirin office d’in ya yi mata kamar na mutumin data had’u dashi a office d’in Sir Najeeb
dan tabbas hancin ta ya shak’i kamshin sosai a wachchar ranar a lokacin daya matso kusa da ita zai fita,sannan ba abun da ya fi d’aga mata hankali irin muryar da ta ji a yanzu a lokacin da ya yiwa Racheal magana,kar dai fa ace wannan mutumin ne,dan in dai ba gizo muryar sa tayi mata ba to kuwa tabbas wannan mutumin shine wanda suka had’u da shi a office d’in Sir Najeeb kwanakin baya.

Da kyar Yashjub ya d’an nemo nutsuwa ya sakawa gangar jikin sa tukunna ya juyo cikin takun shi na k’asaita ya nufo tebur d’in ba tare daya kalle ta ba.
Wani mahaukacin bugawa zuciyar Manubiya ta shiga yi
dan yana juyo wa ta shaida shi
‘’amma Abbakar bai kyauta min ba’’ta fad’i hakan a chan k’asan zuciyar ta,kafin a hankali ta sunkuyar da kanta k’asa tana jin kamar ta tashi ta fita da mugun gudu.
Idanuwan ta da zuciyar ta sam
sun gagara daina zuzuta mata
tsananin kyawun da yayi ga wani haiba da kwarjinin da yayi mata wanda suka taimaka wajen sake hautsina mata lissafi,a ranta ta shiga aiyyana cewa’’ashe last time ban gansa sosai ba.’’
Tana wannan tunanin Yashjub ya nemi waje ya zauna a kujerar da take facing d’in ta,yana mai jin k’irjin sa yana bugawa,kafin a hankali ya d’ago lumsassun idanuwan sa ya zuba su a kanta.
Wani irin sanyi yake ji yana ratsa sa tun daga saman kan sa har zuwa kan babban d’an yatsan k’afar sa,a take wata nutsuwa da kasala suka sak’e rufar masa yana mai jin wani irin nishad’in da bai tab’a jin kwatankwacin irin shi ba.
Duk da yadda ta sunkuyar da kanta hakan bai hana sa k’arewa kyakkyawar fuskar ta dake zagaye a cikin hijabi kallo ba a hankali a chan k’asan zuciyar sa yace
‘’Subahanallah,MashaaAllah,
Allahu akbar!..’’

Tun lokacin daya zauna ya fara kallon ta ta diririce,da kyar da mugun kyar ta samu ta iya d’ago fuskar ta da niyyar gaida shi amma sai taga ya kafeta da kyawawan idanuwan sa,da saurin ta kauda kanta gefe saboda girma da nauyin da taga kwayar idanun nasa sunyi mata…a hankali tace
‘’Good morning,Sir,’’da kyar.

Lumshe idanun sa yayi ya bud’e yana kallon yadda take kallon gefe kad’an ita ala dole ba za ta had’a ido da shi ba bayan kwanakin baya da kyar ta iya zare idanunta a nashi..bai san lokacin da wani murmushi ya kufce ma sa ba
wanda har sai da ta d’an jiyo sautin kad’an,kafin cikin kamala da dad’in sauraro ta ji ya ce ’’’Morning,you called me yesterday’’ya fad’i hakan har yanzu idanuwan sa na a kanta yana mata wani irin kallo kamar wanda yake so ya k’irga duk wata b’ular gashin da ke a fuskarta ne.Shi kan sa yana so ya d’an d’auke idanun sa daga kanta amma sam ya gagara,ba bu abun da ya fi d’aure masa kai kamar yadda tashi d’aya ya shiga nutsuwa walwala da farin ciki da annashuwar da bai tab’a shiga ba.
Ahankali yaji tace
Sir Najeeb said you have a job for me,that’s why I called.
Ta k’arashe maganar ahankali
kamar tana jin tsoro.
Shiruu yayi yana kallon ta kafin chan yace’’Yeah,i do,can i see your credentials.
A hankali ta lumshe idanuwan ta dan sai yanzu ta tuna bata d’auko na secondary school ba dayake shi a chan sama yake a cikin akwati dama tana ta zuci zucin zata d’auko ta had’a da ragowar sai dai kuma har ta fito Allah bai bata iko ba,haka nan ta mik’a masa na primary da diplomar ta tace masa’’ ta manta na secondary school d’in’’dan haka yace ‘’next zuwan ta ta zo da shi’’.

Ya d’an jima yana nazari kafin
ya fara yi mata bayanin aikin
nata yadda zata fahimta
‘’Akwai estate a Kano,Lagos da Abuja,bana so in abu ya b’aci a dinga kira na direct almost everyday sannan secretary d’ina is very busy itama,therefore zan tura musu number d’in ki duk wani complain za su gaya miki ki tara ki ajjiye,u can then report to me on Friday,every Friday,yau Monday so nan da 4 days zaki zo nan kenan,but if abun is urgent zaku iya kira ko ki gaya min ta online,k’arshen wata zan dinga baki 30k.Mun fahimci juna?’’

Ahankali ta jinjina kai kafin ta ce ‘’Yes,Sir
Thankyou so much.’’

Jinjina kai kawai yayi yana mai sauk’e wata b’oyayyiyar ajiyar zuciya kafin ya mik’a mata wata takarda mai d’auke da wajen saka;
Full name
Address
Personal sickness
Email
Phone number,da sauran su yace’’ki yi filling wannan’’.

Cikin nutsuwa ta zaro biro a jakar ta ta hau cikewa,wajen phone number ne ta bari blank dan bata san ya zata yi ba,da farko ta yi tunanin ta saka number Siyama tun da ita bata da waya sai kuma taga ai aiki ne bai kamata ta d’aura mata komai a wayarta ta takura mata ba sannan anytime za ‘a iya kiran ta kar aji wata ta d’auka ya zamana kamar bata d’auki aikin ma da mahimman ci ba,shiyasa taga gara a yi
yi k’ok’ari a san yadda za ayi inshaaAllah ko mai torchlight ce su nemo sai ta taho da number tare da certificate d’in nata,dan haka ta bar wajen blank
ta cike ragowar,tana gamawa ta mik’a masa,tana addu’ar Allah ya sa daga wannan ya sallame ta.

D’auka yayi ya kalla yaga ta bar wajen phone number blank
dan haka ya ce ta k’arba ta k’arasa cike wa.
Sai da ta d’an yi shiruu tukunna tace masa ‘’ba ta da waya,amma inshaaAllah zata taho da phone number d’in a next zuwan ta tare da secondary school certificate d’in na ta.’’
Shiruu yayi kawai ya zuba mata ido yana mamakin taya kamar ta ace bata da waya’wanda hakan ya sanya Manubiya taji kmr ta kurma ihu
gaba d’aya ya d’aure ta da idanuwan sa, ta koina jin kwayar idanun sa take yi suna mata yawa a jiki.Ya jima yana k’are mata kallo kafin ya d’an sunkuya ya janyo d’aya a cikin drawer da ke jikin tebur d’in ya zaro wata farar leda,jiya ya sayi A1 d’in zai bawa mai wankin su da ya ce masa wayar sa ta fad’a a ruwa,a hankali ya mik’a mata yace ‘’ga shi,in kinyi charji sai ki turomin messge da number ki meanwhile zan basu email d’in ki in number ya zama ready sai ki turomin in tura musu ta yadda zaki fara aikin asap.’’ya fad’i hakan yana mai mik’a mata wayar.sai da ya sake cewa ‘’ki karb’a mana,consider it as an allowance’’tukunna ahankali kamar mara lakka a jiki ta sa hannu ta karb’a tace’’Nagode,sosai,’’dan dama har ga Allah bata san ta ina zata fara neman waya ba su da suke fama da abinci.Ganin ya yi shiruu ya koma ya jingina kawai yana k’are mata kallo ne ya sa ahankali ta sake cewa’’na gode’’daga nan ta yi masa sallama ta mik’e ta nufi k’ofa tana adduar Allah ya sa kar ya sake tsayar da ita,a haka har ta fice daga office d’in.

Ta na fita ya lumshe kyawawan idanuwan sa ya kwantar da kan sa a jikin kujerar da yake kai a zaune
a hankali a fili yace
‘’It’s official,I’m in love.’’

Sai da ta fita daga office d’in ta tabbatar ta rufe k’ofar tukunna ta bud’e hanci ta iska sosai sannan ta sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya,da kyar ta samu ta ja k’afafuwan ta nufi inda Ya Musbah ya ke wanda ya riga ya mik’e tsaye tun lokacin da ya hango fitowar ta.Kallon sa take yi tana jin k’auna da tausayin d’an uwan nata suna ratsa ta, dole haka zata hak’ura tayi aiki da Yashjub ko dan y’an uwan ta ta samu ta bawa Ya Musbah jari sannan ta kula da ahalinta,duk da bata san ta yaya zata iya rayuwa da wannan mutumin wanda yake k’ok’arin tarwatsa mata zuciya ba amma dole ta dage ta taimaki ahalinta under any circumstances,zata tsaya tsayin daka InshaaAllah ta yak’i tunanin ta sannan ta taimaki kanta ta hanyar tirsasawa zuciyar ta da tunanin ta akan su daina yaba mata kyau,kwarjini,jarumta da nutsuwar Yashjub,inshaaAllah daga yau duk wani abu mai kyau nasa zata yi k’ok’ari wajen ganin ta maidasa mara kyau a idanu da tunanin ta,
Opportunity comes at ones shiyasa ba za ta zubar da wannan ba,inshaaAllah za ta yi k’ok’ari ta daure ta dage ta yak’i zuciyar ta,ta samu ta taimaki ahalinta..
Da wannan tunanin ta k’arasa inda ya Musbah yake tsaye.Jarumta ta aro ta yafawa gangar jikinta ta k’ak’alo murmushi sannan tace’’Na samu aikin ya bani har da allowance na waya ma,nan ta d’an yi briefing masa akan yadda suka yi da Yashjub.’’

Cikin tsananin murna ya Musbah yace mata ‘’congratulations Manu kin ga rabo ko?lecturer d’in da kika tsana ga shi yau yayi miki gata,na miki murna gaskiya,
gashi aikin ba wahala kwata kwata, kuma na yarda da company d’in a yadda yake d’innan nasan an sanshi kuma ya na bin k’a’idoji kin ga kuwa ba za’a cutar da ke anan ba..muje’’
Ya fad’i haka yana wucewa gaba,a hankali Manubiya tace
‘’Tam’’daga haka ta bi sa suka kama hanya suka fita……
Tana jin tsoron kasancewar ta tare da Yashjub amma ya zame mata dole ta taimaki ahalinta,ahankali ta sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya..tabbas gaskiya Abbakar ya fad’a ranar chan daya ce mata Yashjub ne ‘crush d’in ta,’da sauri ta kawar da tunanin,a ranta tace
‘’Manubiya wake up!!,mutumin nan ba sa’an ki bane ba,ki duba ki ga ko shekaru talatin ba lalle ya rufa ba amma ya mallaki estates nashi na kan sa,matsalolin rayuwar ki ma kad’ai sun ishe ki kar ki je ki jefa kan ki ga halaka…





MANNUBIYA
26

Na
Humayrah Bulama

Mikiya Writers Association.

Tun Shekaran jiya Munirat ba ta fito ba,kasancewar ta gama exams bata da abun yi da gurin zuwa ne ya sanya ko lek’owa bata yi,abinci ma bata sauk’a ta ci kuma ko Ummi ta kai mata ba iya cin mai nauyin take yi ba sai dai ta yi y’ar kwalamar ta a fridge d’in Ummi ko kuma in dare yayi sosai ta sakk’o ta dafa indomie ta ci ta koma.

Tun sassafe Yahanasu ta fita dan tana da client kasancewar ta independent lawyer,ko da ta gama abun da zata yi bata komo gida ba direct sai ta wuce gidan k’awarta.
Ya’isha ma tana so ta d’an yi wasu aiyyuka dan haka ta fita tare da Kausar domin ta rakata tayi depending project d’in ta daga nan,yayinda
Yasmin take da surgery itakam tun 6 ma ta fita.
Yusra da Yadira ma duk suna da exams d’in sassafe
Yadira er level 1 itakam biyu ne ma da ita safe da yamma,
Yassira ma tun sassafe ta fita aiki
Dan haka gidan ya rage daga
Mommy sai Ummi Baaba larai Yassir da Munirat

Sai wajajen 2 tukunna da kyar Munirat ta fito ta shiga taya Ummi aiki saboda yau Ummin za ta karb’a girki kuma ta na so ta burge Daddy dan ta samu su sake shirya wa da shi sosai.
Sai kusa da k’arfe 4 tukunna suka samu suka kammala
kasancewar Munirat tana fashin Sallah ne yasa Ummi ta barta a kan ta jujjuye a flask ta kai side d’in Daddy ita kuma Ummin ta tafi yin sallah da wanka.

Cikin nutsuwa take juye abincin a cooler suna hira da gwaggo mai aiki dan su Husaina da Asabe y’an matan sun tafi shirin islamiyya,ji tayi kmr ana kallon ta dan haka ta d’an juya a hankali,
da sauri ta d’auke kanta ta juya ranta a d’an bace sai kuma ta ja kujera zauna
saboda riga da wando sai er k’aramar hula ne a jikin ta wandon pencil kuma ya kama ta,sam bata yi tunanin anan yake ba ta d’auka a side d’in Yashjub yake,ta san kuma Ummi ma ta manta ne da baza ta bar ta ta zauna a haka ba,ba abun da ya fi bata haushi irin yadda ya kafe ta da dara daran idanuwan sa yana k’are mata kallo..

‘’Ina wuni,d’an albarka’’
Muryar Gwaggo ta katse wa Yassir da Munirat tunani,a hankali ya k’araso cikin kitchen d’in yana mai cewa ‘’lafiya’’yayinda idanun sa suke yawo a jikin Munirat wadda ko kallon inda yake bata yi ba,ganin da yayi bata da niyyar gaida shi ne ya sanya shi ya gaida ita ta hanyar cewa’’Anty Munirat,Ina wuni.’’
Da mamaki ta d’ago manyan idanuwan ta ta d’an kalle shi dan bata yi tunanin ya san sunanan ta ba
sai kuma ta sunkuyar da kanta tace’’ina wuni’’a hankali.Murmushi kawai yayi daga haka ya juya ya kalli gwaggwo yace’’gyaran jiya bai fita ba fa,sannan kinsanni bana son white bedsheets,a cire a saka wani sannan a sake gyara d’akin.’’
Yana dire aya,da sauri gwaggo tace
‘’Yanzu kuwa d’an albarka.’’
Ta fad’i hakan tana mai fice wa daga kitchen d’in daga nan ta nufi sama d’akin shi kusa da na Mommy,amma fa a ranta ta gama aiyyana yadda zata zaiyyane wa Munirat halayen Yasir,dan ba za ta bari Yassir ya cuci y’ar marainiyar Alllah ba, sarai ta lura da yanayin kallon da yake yi mata,
bayaga tijarar da y’an uwan shi suka yi mata shekaran jiya shine shima yake so zai d’aura mata da nasa kalar cin zalin.

Gwaggo tana fita Munirat ma ta mik’e zata fita,da sauri Yassir ya ce’’We haven’t met,sunana Yassir,3rd born na wannan family d’in,I’m an architect
C.E.O
Yassir Limited’’
Ya fad’i hakan yana mik’o mata hannunshi alamun su gaisa yana d’an murmushi.

Ba tare da ta kalle sa ba tace’’nice to meet you’’ta fad’a hakan tana k’ok’arin wucewa

Da sauri yasha gaban ta yace
‘’Am..dama Ina so in baki hak’uri a kan abun da su Ya’isha suka yi miki the other day…’’

Cikin katse sa tace
‘’Dan Allah ya Yassir ka bar maganar,za mu yi resolving a tsakanin mu,girls.’’

Murmushi yayi yana yi mata wani irin kallo kafin kansa tsaye yace’’you don’t like me,Y?
kar ki damu ki fad’a min ba zan ji haushi ba’’

Cikin k’aguwa tace.’’ a gajiye nake,sannan Ina da damuwa kai kuma ka zo kana ta magana,bana son yawan magana.’’

Ahankali yace
Sorry dear!na fahimta kuma ban ji haushi ba.’’ya fad’a hakan yana mai matsawa sannan ya nuna mata hanya da hannun sa ya d’an rissinar da kai yana wani kalar murmushi.Da sauri ta wuce ta fita tana waiwayen sa kamar wanda akace zai biyo ta ya kama ta ne.

A Chan corridor ta lab’e sai da taga hawan shi sama da juice da cake da alamun su ya zo d’auka,tukunna ta fito ta koma
kitchen d’in ta k’arasa zuba abincin ta kai d’akin Daddy,ragowar kuma ta jere musu a kan babban dining table d’in tukunna ta zuba nata ta ci a kitchen d’in dan sai yanzu yunwa ta fara kwak’ular ta saboda rabon ta da abinci mai nauyi tun shekaran jiya.
Gwaggo ta riga ta gama wanke wanke shiyasa itama tana gama ci ta shiga d’auraye plate d’in da ta b’ata.
Tana cikin wankewa
Ya’isha da Kausar suka shigo
suna hira,ko kallon ta ba su yi ba haka suka ci gaba da hirar su kamar ba su ga mutum a kitchen d’in ba,suna hira suna shewa Kausar ta d’auko pizza a fridge ta sa a microwave ta d’auko cake da drinks suka nufi d’an mini dining d’in da ke a cikin kitchen d’in suka zauna.

Su ne ya kamata su kula Munirat duba da abun da ya faru a tsakanin su tun da itace bak’uwa,sannan yanzu ma ita suka tarar a cikin kitchen d’in,
but basu ko kalle ta ba..gudun magana ne ya sa har
Munirat ta juya za ta fita sai kuma ta koma inda suke ta tsaya
tace’’Am..Ya’isha sannun ku da zuwa,dama tun jiya ina so mu yi magana,amma sai ban samu ganin ku ba sai yanzu,dama a kan abun da ya faru ne ku yi hak’uri mu fahimci juna komai ya wuce.

Dai dai nan Kausar ta mik’e ta nufi microwave d’in da ta fara k’ara Ya’isha kuma ta d’auko wayarta ta hau daddannawa.

‘’Ya’isha’’
Munirat ta sake kiran sunan ta tana mai k’ok’arin danne zuciyar ta.

Ba tare da Ya’ishan ta d’ago ta kalle ta ba ta ce’’Ni fa,waya zan yi da boyfriend d’ina,so pls leave..dan na tabbata turare ko wankan da kika yi shekaran jiya bai gama barin jikin ki ba,Najeeb is a very handsome and nice guy dan haka ban shirya bar miki shi ba…’’
Ya’isha ta fad’a mata hakan tana mai daddana wayarta
ba tare da ta kalli Munirat d’in ba,kamar ma bada ita take maganar ba.
Dai dai nan Kausar ta dawo da pizza ta ajjiye musu suka shiga ci.
Har Munirat zata ce wani abun
sai kuma ta juya kawai ta fita zuciyar ta tana wani irin tafarfasa.


Tana fita Kausar ta kalli Ya’isha ta ce’’na san ni cousin d’in ku ce amman a yadda muka taso
Ni , kamar sister nake a wajen su Yash da Yassir,sab’anin Munirat dan haka ya kamata mu yi wa Ummi magana ta daina barin katuwar y’ar ta tana yi mana yawo tib’ir tib’ir a gida,dan naga kamar ma tallar y’ar tata take yi.’’
Kausar ta k’arashe maganar cikin tsananin takaici tana addu’ar Allah yasa ba a yi
rashin sa’a Yashjub d’in ta ya shigo by mistake ya ga Munirat a haka ba.
Murmushi Ya’isha ta yi cikin kamo hannun Kausar d’in tace’’
Kausar ki dena cewa ke cousin d’in mu ce saboda you are more than a sister to all of us,muna son ki muna k’aunar ki fiye da zaton ki,’’cikin sake ruk’o hannun ta ce ‘’bara in baki misali,‘’sannan ta d’aura da cewa’’ in da ace wata ce ta yi breaking heart d’in Yassir a tunanin ki ya za mu yi mata?k’iri k’iri kika ce bakya son Yassir on top of that kika ce Yashjub kike so amma mu ka yi supporting d’inki 💯 ba tare da mun ji haushin ki ko mun tuhume ki ba dan haka dan Allah ki daina cewa ke cousin d’in mu ce,ki yarda ki saka a ran ki
You are part of this family and we love you,always &forever,ita kuma wachchar ki bar ni da ita,zan san maganin ta soon,in dai ina numfashi sai ta bar gidan nan da k’afarta walllahi..d’azu ai Yasira ta turo message a group akan labarin da uwar tata ta bayar,kin gani?’’

Tab’e baki kausar tayi sannan tace’’Yeah!na gani,amman hakan ba zai chanja komai ba,dole sai ta bar gidan nan tun da babu gadon uban ta a ciki.’’

‘’Ita da uwar ta’’
Ya’isha ta k’arashe mata maganar tata tana dariya.
Dariya duk suka yi kafin su ci gaba da cin abincin su suna yi suna tattaunawa.


Duk yadda Munirat ta so ta hana kanta kuka sam sai ta kasa,tana fita hawaye suka fara tsiyaya daga idanuwan ta.
Abun yayi mata ciwo sosai
gashi Ummi tace kar ta sake mayar musu da magana instead a ko da yaushe ta nemi zaman lafiya da su..tana tafe tana hawaye a haka har ta k’arasa d’akin Ummi ,ba ta tarar da ita a d’akin ba dama abunda take so kenan
dan haka ta zaro akwati ta je d’akin ta na b’angaren su ta jido kayanta ta had’a komai tana gama had’awa ta kira sister d’in ta tace mata za tazo ta yi mata kwana biyu,yayar tata tanata murna a haka suka yi sallama ta zauna zaman jiran Ummi ta samu ta yi mata sallama daga nan ta kama gaban ta,sai dai kuma Ummin tana zuwa tace bata san zance ba,ba yadda Munirat bata yi da ita ba amma Ummin ta hana ta tafiya k’arshema sai ta rufe ta da fad’a,tana ji tana gani haka ta hak’ura ba dan ranta yaso ba…

Kamar kullum bayan sallar isha,sai da Ummi ta yi da gaske tukunna Munirat ta yarda ta bita suka sauk’a domin yin dinner.
Dama sun san yau su Daddy suna da meeting,dan haka shi da Yassira da Yashjub basu zauna dinner ba.A dining d’in suka tarar da kowa har Yahanasu,a kusa da Mommy Ummi ta ja kujera ta zauna da murmushi a fuskar ta tace ‘’Barka da dare Mommy’’ba yabo ba fallasa da d’an murmushi a kan fuskar Mommyn ta ce’’Lafiya Ummi ya gida ?’’

‘’Alhamdulillah’’ta bata amsa da ga nan Munirat ma ta gaida Mommy da Baaba larai da Yahanasu kafin ta ja kujera ta zauna,sai da ta zauna tukunna ta lura ashe opposite d’in Yassir ta zauna,ta so ta tashi amma kuma in ta tashi duk inda za ta koma to dole sai dai ta shiga tsakiyar su Kausar ne dan a rarrabe suka zazzauna,dan haka kawai ta hak’ura ta zauna.
Cikin girmamawa Yahanasu ta gaida Ummi ita kuma ta amsa mata da kulawa.

Tana shirin zuba abinci suka had’a ido da Yassir,a hankali ya d’an motsa bakin sa alamun ‘Hi’
D’auke kan ta kawai tayi ta ci gaba da zuba musu abinci itada Ummi.
Murmushi yayi kafin ya juya ya kalli Ummi yace’’Ummi ina wuni’’

Da sauri Ya’isha da Baaba larai suka kalle sa,sai kuma suka d’auke kai suna mamaki.

Cikin jin dad’i da murmushi
Ummin tace
‘’Lafiya Alhamdulillah,Yassir.

Wata kalar dariya Yasmeen tayi ciki ciki kamar irin mutun yana k’ok’arin gimtse dariyar sa d’innan amma kuma ta yadda ta tabbatar da Ummin za ta ji.

Ta kuwa ji
amma sai bata kulata ba,daga haka kowa ya shiga cin abincin sa.
Yassir ne ya fara mik’ewa yayi musu sai da safe yana ta satar kallon Munirat,ita bata ma lura da shi ba amma Ya’isha da Yadira sun lura.
Yadira tana shirin mik’ewa
Ummi tace ‘’Yadira d’an zauna ina son magana da ku’’.
Kamar ba za ta zauna ba,sai kuma ta koma ta zauna ba tare da ta kalle ta ba,ta wani had’e rai ta d’auke kai.
Kausar ko rabin abincin ta bata ci ba bata da niyyar tashi da farko amma tana jin Ummi tace ‘tana son magana da su’
Kawai sai ta mik’e ta wuce sama.

Shiruu Ummin tayi kmr tace kowa ya tafi kawai sai kuma ta fesar da numfashi kafin ta ce
‘’Ya’isha in kun hau sama sai ku gaya wa Kausar da Yassira abun da nace…’’tiryan tiryan
haka Ummi ta zaiyyano musu labarin senator da Munirat kamar yadda ta gayawa su Daddy kafin ta d’aura da cewa ‘’Munirat ba za ta tab’a auren shi ba,dan in da ace zan bari ta aure shi da tun lokacin da ya dawo an d’aura musu aure ballantana kuma yanzu da yake a matsayin saurayin Yahanasu.’’cikin lallami Ummi ta ce’’dan Allah komai ya wuce let bygones be bygones’’

‘’Ummi komai ya riga ya wuce,what more do you need from us?’’
Yusra ta yi mata tambayar cikin tsare ta da idanuwa.
Cikin rashin jin dad’i Ummi tace’’Yusra zumunci da zaman lafiya nake so a tsakanina da ku,sannan a lokacin da Daddyn ku ya aure ni ya yi alk’awarin zai rik’e Munirat kamar y’ar cikin sa yace za ta ji dad’i a tsakanin ku,zaman gidan nan ba zai tab’a yi mata dad’i ba in dai kuna yi mata irin haka,dazu fa tarar da ita nayi ta had’a kayan ta zata bar gidan nan

Please Login or Register in order to submit comment