Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shine ya b’ace haka da babu wanda zai damu..kwanaki da yayi fushi ya tafi Daddy baisan inda yake ba amma bai damu ba haka aka share kwanaki ko neman sa baiyi ba kuma bashi da niyyar yi
Inaa,gaskiya da sake dan bazai yiu a dake sa sannan a hanasa kuka ba..ba zai kuma yiu ace uwa d’aya uba d’aya su haifesu amma ace ya fi sa fada !kud’i!farin jini!jama’a!ilimi
sannan ya d’auke soyayayr iyayen su ba…ya zama dole ya gyara hakan in kuma bazai gyaruba to dole ya bi ta ko wacce hanya possible yayi maganin wannan matsalar tun kafin bak’in ciki ya kashe sa dan shi kad’ai yasan me yake ji a cikin zuciyar sa…a yanzu haka k’ok’ari kawai yake yi yana danne kansa amma ji yake yi kamar ya had’a Daddy da Yashjub d’in ya saka musu bomb especially ma daya tuno da abunda Kausar ta gaya masa ‘’ace wai Yashjub yanada 50% shi kuma wai 1 %’’
wannan rashin adalcin har Ina haka!?
…………
A chan b’angaren su Manubiya kuwa tun tafiyar Baraka tsabar
b’acin rai tsakanin Aisha Jidda da Manubiya babu wanda ya iya cewa komai,ko abincin da Aishar ma ta kawo duk kasa ci suka yi,Inna kuwa ta lumshe idanuwanta kawai dan bata so ta bud’e hawaye su fito ta sake d’aga musu hankali shiyasa kawai ta lumshe idon tayi shiruu iskar fiffitar da suke yi mata su duka ukun tana ratsata

Suna a zaune ya Musbah ya shigo da shi da mai sunan baba wanda yaketa faman zabga ihu da shure shuren shi sai ya bi maman sa,ganin khairat abokiyar wasan sa ne ya d’an rage zafin abun,kafin dare sharr Yaron ya sake ya shiga mutane yanata wasa.

basu dad’e sosai ba ya Nafi’u ya zo dan haka gaba d’ayan su suka nufi gida bayan ya Nafi’u ya sanya su Manubiya sunyi mishi alk’awarin ba zasu gayawa Baba komai game da zancen Baraka ba tukunna.


Aranar Baba yaga gata,har da kwallar farinciki sai da yayi.
Kamar komai bai faru ba
haka suka zauna har ya Nafi’u da Aisha aka sha hira
aka d’an kwantar wa da juna hankali.

Sun jima tukunna ya Nafi’u da Aisha suka fara shirin tafiya dan haka Baba ya cewa ya Musbah shima ya tashi ya bisu kar a bar Baraka ita kad’ai.Da to ya amsa shi daganan yayi musu sallama suka fice shida mai sunan baba.

Su ya Musbah suna fita su Jidda suka ce wa Baba’’ai d’azu ma Siyama ta kira lokacin suna asibiti maman ta ba lafiya shiyasa ma bata je ba.’’

Ba tare da b’ata lokaci ba ya ce musu’’su mik’e suje su dubota,ai da sun fad’a tun d’azu,Allah yasa basu riga sun yi bacci ba.’’

Da to suka amsa daga haka suka fita….bayan fitar tasu ne Baba ya matsa kusa da Inna,duk abinda ya faru yau ba abunda ya b’oye mata,yanaso ta sani saboda ta fahimce sa kuma ta goya masa baya akan aurar da su Jidda dayake shirin yi cikin gaggawa.
Yaga alamar amincewa kuwa a fuskarta dan har lumshe masa idanuwa ta yi ta bud’e,dan haka ya sake jin dad’i ya kuma samu kwarin guiwa….hakanan yayi ta mata magana dukda yasan bazata mayar masa ba amma yasan tana sauraronshi kuma ta fahimcesa.



Jikin anty Umma kam ba sauk’i sam,sannan har gara Baba ma shi an samu an kaishi asibiti
Ita kuwa ko asibitin ba a samu me kaita ba.

Siyaman ce take gayawa su Jidda cewa’’babu wanda bata kira a cikin manyan gidan ba,amman kowa sai dai yace mata ba shi da ko sisi.
Uncle ma rufeta yayi da fad’a wai yanzu ya Musbah ya kira shi,ya tura masa kud’i shine itama zata kuma kira,gaskiya
shifa an saka mishi ido!d’an shige da ficen da aka ga yanayi shine ake ganin kamr wani k’arfi ne da shi. Da ga yau indai ta san maganar kud’i ne tou karta sake kiranshi yana wajen aiki shima bashida shi…’’
Muryarta ce ta katse ta dalilin kukan da ya taho mata.

Ahankali Manubiya ta shiga lallashin ta tana bata baki…..duk da damuwar da suke a ciki basu bar parlourn ba sai da suka d’an kwantar wa da y’ar uwar tasu hankali suka ga ta d’an ware tukunna suka yiwa anty umma Allah ya k’ara sauk’i suka mik’e za su tafi.
Mik’ewa itama Siyaman tayi ta cewa Umman nata’’bari ta d’an raka su’’

‘’To’’kawai anty Umman tace daga haka ta yi musu sai da safe tace su gaida Baba.


Suna fita Siyaman ta ce’’Manu akwai abunda nake so in gaya muku kar kuji a bakin wani gara kuji a bakina’’

Ahankali duk suka tsaya suna kallonta dama sun lura akwai
abunda take son fad’a
Anty Umma kuma sai gargad’i take ta yi mata da ido.

Cikin sanyin jiki take gaya musu’ashe Suraj..wanda zai aureta ne ya fasa wai an zab’a masa y’ar uwarsa shine dalilin dayasa Anty Umma ta d’aga hankalin ta har ta kwanta rashin lafiya.’

Tausayin ta ne ya lullub’e Manu
dan haka sai tama kasa cewa komai.

Jidda ce ta iya cewa ‘’Siyama dan Allah ki kwantar da hankalinki kema karki wani d’aga hankalinki
InshaaAllah hakan shine mafi alkhairi,Allah ya riga ya rubuta dama ba mijinki baneba,inshaaAllah shi zai baki wanda ya fi sa.

Ajiyar zuciya Siyama ta sauk’e kafin tace
‘’Jidda sam ban d’aga hankalina ba wallahi ni kaina ina mamakin yadda abun bai wani dameni sosai ba,amma yadda Umma take yi ne banaso sannan Itafa har yanzu tak’i ta hak’ura shiyasa ma kika ji bata gayawa kowa ba ni kuma na riga na san tunda har suka ce sun fasa to sun fasa d’in saboda matsalar daga b’angaren mahaifin sa ne fa tun da y’ar k’anwar mahaifin nasa aka basa ashe shiyasa suke ta ja mana rai wajen kawo kaya suce yau su ce gobe.
Amman wai duk wannan abunda sukayi wa mutane in kika ga yadda Umma take waya da mahaifiyar sa tana wani lallab’a ta abun sai ya b’ata miki rai sai kace irin ana neman kai da ni….dake itama mahaifiyar tasa ba so take ya auri ita wachchar yarinyar ba.’’

‘’Haka iyaye mata suke Siyama
gani takeyi kamar zaki shiga damuwa
She ‘s just looking out for you’’
cewar Manubiya wadda gaba d’aya jikinta yayi sanyi.

Cikin sanyin murya Siyama tace’’da wannan kam gaskiya
and also na lura kamar tana so ma ta nunawa kaka mallan iyakar sa,a nawa tunanin kenan saboda kin san ai ya yiwa makwaftan mu magana akan karb’ar kaya,tou yanzu duk ya je yanata yayatawa wai an
fasa auren nawa…a bakin yayata fa da take aure a illorin mukaji,wai wata makwafciyar mu anan ta kirata takanas dan ta tabbatar,kinga kuwa ai ya gama yaya tawa kenan,amma dukda haka ni bansan me yasa Umma ta ji haushi ba dukda a yanayin da yaketa sanarwar bai dace ba amman kuma ni a ganina gara ma a sani tun wuri
tunda dole dai za’a fasa d’in kuma kowa zai ji.’’
Ajiyar zuciya ta sauk’e cikin son kawo k’arshen zancen tace
‘’Anyways mai faruwa ta riga ta faru,atleast yanzu da nayi muku maganar na d’an samu relief wallahi’’.

Murmushi Manu tayi kafin tace
‘’Siyama ai iyayen mu ne basu gane hakan ba tun wuri
zaman tare dole akwai sab’ani wasu lokutan ma harda rashin fahimtar juna amma muddin akace akwai had’in kai a tsakani sai kiga an dace’’

Dasauri Siyama tace
‘’Wallahi Manu rashin had’in kan y’an gidan nan namu nima yana damuna har gwara ku ku biyu ne
Ni fa ?
Wani zubin fa idan aka k’unsa mana sai dai mu zauna Umma tana kuka nima ina taya ta ba mai rarrashinmu’’

Murmushi Jidda tayi daga haka ta kamo hannun Siyama tace’’rashin had’in kai wannan zab’in iyaye da yayyen mu ne,amman mu zamu iya gyarawa ko da a tsakanin mu ne,wanchan tsarin su ne dan haka inaga muma zamu iya shimfid’a namu tsarin!watak’il in sukaga ribar had’in kan a tsakanin mu suma su gyara….kasancewarsu manya ba shine zai sanya ace
duk abunda sukayi shine daidai kuma muma sai munbi ba’’

Murmushi Siyama tayi kafin tace’tabbas Jidda maganar ki hakan take.Tun tasowata bani da burin da ya wuce inga mun had’a kai ni da y’an uwana,amma kash!side d’inBaba na they are worst than here dan sukam zan iya cewa da su gara babu ma,tou nan d’in ma dande kawai muna zaune a waje d’aya ne Ina ganin ku Ina jin sauk’i amma ta fannnin had’in kai kam duk sammakal,na cire rai da gyaruwar al’amura a tsakanina da side d’in Baba na amman nan kam dama Inada hope.
Naji dad’in wannan goyon bayan dana samu daga gareku y’an uwana Ina rokon Allah Ubangiji ya dafa mana ya bamu ikon gyara zumuncin mu.’’
Ta k’arashe maganar tata tana mai rungumo su gaba d’aya…..

Siyama tayi waec takardar ta batayi wani kyau ba,taji kwad’ayin inama ace itama itace zata zana post utme jibi
kamar Jidda,dan haka suka k’ara k’arfafa mata guiwa akan ta sake yin waec tayi jamb ta koma makaranta
In Allah ya kawo aure tayi in kuma bai zo ba tayi focusing akan future d’in ta,kar ta bari wani chan Suraj dashi ya saka mata damuwa.

Sun d’an tab’a hira tare da shawarwari a tsakanin su sosai,kafin sukayi sallama suka wuce d’akin su itama ta koma side d’insu.

…………

K’arar zuge gate tare da parking d’in motar Yashjub ce ta katse wa kowa tunani,a kurkusa yayi parking d’in shiyasa har ya samu damar shigowa kafin Daddy wanda ya nufi k’ofa kamar wani zararre ya Ida fita.

A bakin k’ofar sukayi karo da shi da Daddy wanda ya sauk’e wata nannuyar ajiyar zuciya sakamokon ganin Yashjub d’in da yayi well and sound.
Cikin kwantar da murya Yash d’in ya d’anyi kalar tausayi yace
‘’Daddy I’m so sorry,dan Allah kayi hak’uri
Tun 5 lokacin da ka kira Najeeb muka fito,to muna fitowa ne sai motar Najeeb ta lalace shine na tsaya na ara masa battery d’ina a samu a tashi tasa ashe wata waya ce ta lalace shiyasa nima haka nawa battery d’in ya samu matsala
Da waya d’aya na fita dayake tun rana muke yawo ni da shi munata waya kuma akayi rashin sa’a duk ba wasu enough charge garemu ba shiyasa duk wayoyin namu suka d’auke bamu samu mun kira kowa ba.D’azu kuma dana fita daga meeting wani abune very important ya taso
I’ll explain but for now kayi hak’uri dan Allah,ka yi hak’uri pls.’’
Ya k’arashe mganar tasa yana me had’e hannuwan sa guri guda’

Juya wa Daddy yayi ya kalli yanda gaba d’ayan su har ummi da Munirat suka zuba musu ido sannan sukayi musu cirko cirko

Ahankali ya juyo ya kalli Yashjub d’in yace
‘’Kaje kayi freshining up ka ci abinci sai ka same ni a sama.’’

Daga haka ya juya ya wuce
Yana wucewa Yahanasu da Mommy suka taho a tare

Fuskar Mommy kamar zata fashe da kuka har da hawaye yaga ya taru a idonta.
Dasauri ta d’an ture Yahanasu ita ta k’araso ta rungume Yashjub d’in kafin ta cikashi ta shiga tattab’a fuskarshi tana dudduba jikin shi sai da ta tabbatar da lafiyar sa k’alau tukunna tace’’Gaba d’aya hankalin mu a tashe yake Son…’’

Wani guntun murmushi Yashjub yayi wa Mommy da kyar kamar irin an saka shi dole d’innan tukunna ya kamo hannunta wanda yake rik’e da kumatun sa a hankali ya sauk’ar mata da hannun nata tukunna ya matsa kusa da Yahanasu wadda
ta ja ta tsaya tun lokacin da aka ture ta gefe.Murmushi yayi mata kafin yace’’sorry na d’aga muku hankali….
Am anjima inaso zamuyi magana dake,stay up pls’’

Murmushi tayi ta d’an shafa fuskar sa tukunna tace ‘’ok,
I’m just glad you are okay.’’

Ahankali yace’’thankyou’’ kafin ya juya ya kalli Yassira wadda ta turo baki tace’’you owe me an apology…ka saka na bada speech d’in da ban shirya ba.’’

Murmushi yayi kafin yace’’I need to rest,good nyt all’’
Har ya juya zai fita sai kuma ya sake juyowa ya kalli yahanasu yace’’stay up!’’daga haka yasa kai ya fice.

Tun lokacin da Yash ya ture hannun Mommy ta k’ame a wajen ta gagara motsi,gaba d’aya kanta ya d’aure ya d’au zafi dan kwata kwata
ta ma kasa fahimtar yanayin Yash d’in.Tashi d’aya kwakwalwarta ta d’au chargi gumi ya shiga keto mata dan indai abubuwan data ji daga bakin Yasira sannan ta fahimta yanzu ne to kuwa tanada babbar matsala a gabanta!a take k’irjin ta ya shiga duka uku uku ta shiga add’ua a ranta akan ‘’Allah dai yasa bata riga ta makara ba’’
A take kwakwalwarta ta fara lissafa mata yadda abubuwa da shirye shiryen ta na sama da shekaru zasu zagwanye
a gaban idanunta muddin batayi da gaske ba!
A chan k’asan ranta tace
‘’Wacce irin shuumar yarinyace wannan da zata shigo musu ba notice haka ta tarwatsa mata duk wasu taka tsantsan d’in ta’’.
Tsabar rud’ani da rikici Mommy batasan lokacin da a fili a hankali kamar me mumbling ta fara cewa’’ba zai yiu ba,ba zai yiu duk wasu sacrifice’s d’ina su tafi a banza ba….’’

Dasauri Baaba Larai ta matso ta rungume ta a cikin kunnen ta tace’’ana dai kallon ki,ki zo muje sama sai mu yi magana’’

Jinjina kai tayi kamar ta fahimta sai kuma ta d’ago ta kalli Baba Larai tace’’kikace mace ce a rayuwar sa ko?kin tabbatar d….’’


‘’Innalillahi!!!nace kizo muje sama ko?!!’’
Baba Larai d’in ta fad’a mata hakan da d’an zafi.

Sai a sannan tukunna Mommy ta samu ta d’anyi snapping out.
Ba tare da ta kalli kowa ba
ta juya ta wuce sama jiki ba lakka Baaba Larai na bin ta a baya.

Anan suka bar Yahanasu wadda ta bisu da ido kawai a tsaye.’’hmmm’’kawai ta ce,kafin ta juya ta nufi d’akin ta
ba tare da ta kalli su Yassira ba.

Ummi ma bayan Mommy ta bi
dan gaba d’aya duk sai taji tausayinta ya lullub’e ta,a gaskiya Yashjub bai kyauta ba
taya zaka dinga treating uwar data haifeka haka…
Da wannan tunanin ta haye sama ta bi bayan Mommy da Baaba Larai dan tana so ta d’an taya babalarai tausar Mommyn.


Achan parlour k’asa kuwa wata hirar su Yassira suka shiga yi gaba d’ayansu suna raha suna dariya,Yayinda Munirat ke tsaye a gefe tana mamakin yadda basu damu da damuwar mahaifiyar su ba suka hau hira haka,sai da tafiya tai tafiya tukunna ta fahimci ashe don ita da ummi suka kafa hirar dan babu komai a cikin ta sai habaice habaice tun suna habaici har suka fara sako sunayen su suna zagi suna dariyar rashin mutunci dukkansu banda Kausar wadda tun d’’azu ta yi shiruu.

Nazartar ta kawai Yassir yakeyi shiyasa yak’i tashi a wajen.

Munirat ce ta katse masa tunanin ta hanyar nufar sama da wani irin sauri dan ita sai yanzun ma ta yi tunanin to me ma ya tsayar da ita a wajen ne.

Wani irin wawan tsaki Yassir yayi dan bai riga ya gama fahimtar Kausar ba amma kuma dole ya tashi ya bi bayan Munirat.

Cikin had’e fuska ya mik’e ya bi bayan ta a ransa yana cewa ‘’gaskiya shifa yana samun abunda yake nema a wajen ta zai yi withdrawing plan d’in Kausar…baya son damuwa,bayajin zai iya ci gaba da tolerating yarinyar nan muddin ya samu buk’atar sa ta biya.’’yana tafe yana mita a cikin ransa fuskar nan tamau haka ya haye saman

Ahankali Kausar d’in ma ta mik’e ta nufi sama jiki ba lakka.



MANNUBIYA
43
Na
Humayrah Bulama

Mikiya Writers Association.

Sai da su Mommy suka kusan shiga d’akinta tukunna suka lura da Ummi a bayansu,Mommy ji tayi kamar ta zurma uban ihu dan a yanzu bata buk’atar ganin kowa da yin magana da kowa in ba Baaba Larai ba….ayanzu daya kamata ace sun keb’ance daga ita sai Baaba Larai shine wannan matar zata kama ta wani biyo su.Da kyar kuwa ta d’an sake ta bata fuska suka shige d’akin nata gaba d’ayan su.


‘’Babe!Babe!!’’
Muryar Yassir ta katsewa Munirat tunani.
dakyar ya samu ya d’an daidata fuskar shi,dai dai nan ita kuma ta juyo,dama tasan sai ya biyota dan haka tana juyawar tace’’i’m okay,sai da safe.’’
Ruk’o hannunta yayi dan
haka ta juyo ranta a b’ace tace ‘’Yassir nace ka daina tab’ani ko??’’

Cikata yayi yana mai d’aga hannuwan sa sama kafin ya maidasu k’asa ya zura su biyun a cikin aljihu tukunna yace’’kin tabbatr?’’

Murmushi tayi tukunna tace’’Yeah!ina buk’atar hutu sai da safe’’
Bata jira jin me zaice ba ta shige ciki ta banko k’ofar!.

Runtse idonshi yayi da k’arfi ya dunk’ule hannunsa a ransa ya raya’’ Tabbas in burin sa ya cika akan yarinyar nan sai yaci uban ta Wallahi’’

Gyaran muryar da Kausar ta yi ne ya sanya sa bud’e idanuwan nasa kafin ya juya ya zuba mata idanu yana kallon ta har ta k’araso in da yake sai da ta kalli k’ofar da Munirat d’in ta banko tukunna ta kallesa tace’’how rude!’’
Sai da ya furzar da iska tukunna ya matsa kusa da ita sosai yace’’kuma dole in yi tolerating d’in ta ba,tunda kin had’ani yin soyayya dole da ita’’

Murmushi tayi kafin tace
‘’Shiyasa k’aunarka take sake nunkuwa a cikin zuciya ta…but still Yassir bafa ka playing cards d’inka well dan nidai bana ganin wani shak’uwa a tsakaninku’’

Motse bakin sa yayi ya d’an chuno lips d’in shi still idonshi yana akan Kausar d’in yace’’ko d’azu ma kamar zamu cinye juna a waya,kawai dai tanada attitude ne sannan bata iya controlling temper d’in ta ba..na lura in ranta ya b’aci a kaina take huce wa’’

Cikin katseshi tace
‘’Ko kuma haushi taji akan baka tsaya mata agaban su Yasira ba’’

Murmushi ya yi ya d’an sunkuyar da kan sa tukunna ya d’ago yace‘’Tabbas hakan ne ma.
Kinga
ni yanzu mu bar maganar ta haka,ke mene ya ke damu ki?’’
Yayi mata tambayar yana me tsare ta da idanuwa.

Itama idon ta zuba masa na y’an dak’ik’u tashi d’aya ta fahimce sa tsaff dan haka tace
‘’Mommy ce take bani tausayi ko kai baka lura da ita tun d’azu ba?I mean da taji labarin Yashjub ya bar office.’’
Sai da ta d’an sunkuyar da kanta ta fesar da iska tukunna ta d’ago tace’’muna tunanin yana tare da wata ne,and kasan dama na gaya maka how she feels about him getting married before a samu a karb’o dukiyar gidannan daga hannunshi……d’azun baka lura da yadda tayi kuka ba kafin su hawo ?’’

Ajiyar zuciya ya sauk’e kafin yace’’yeah na lura’’
A ranshi kuma yanajin wani relief dan shi kansa baya so zargin da yake yi akan Kausar ya tabbata saboda bai san me zai zama ba kuma.

‘’Ya akayi?’’
Muryarta ta katse masa tunani

Murmushi yayi tukunna yace ‘’nothing’’
Ya fad’i hakan yana d’an ruk’ota.

Dariya tayi kafin ahankali da style ta samu ta zille tana mai cewa’’ka je ka kira budurwarka ku shirya,bari inje naji da Mommy’’ daga haka ta wuce ta barshi a nan tsaye.



Yashjub yana fitowa a wanka ko abinci bai ci ba dan dare ya riga yayi
Ya d’auki waya ya kira Manubiya.

Lokacin basu wani jima da dawowa daga wajen Siyama ba suna zaune itada Jiddah suna shawara
Jiddan tace wa
Manubiya ta siya masa jallabiya da Alkur'ani ta kai masa as gift na godiyar abunda yayi musu….

Suna cikin lissafin ta Ina kud’in zai fito ne wayar Manubiya ta
fara k’ara dan haka ta yi sauri ta mik’a hannu ta d’auka daga inda take tayi saurin saka ta a silent gudun karta tashi su Inna.Dukda ta goge numbersa tun lokacin da tayi fushi ta bar masa office amma tana ganin number tashi d’aya ta gane shi ne dan haka ta zuba wa screen d’in ido tana kallo kawai yayin da k’irjinta yake bugawa a hankali a hankali.Lek’awa Jidda tayi kafin ta d’an d’ago ta kalleta tana murmushi tace’’shine ko?’’sai kuma ta kalle ta tace’’Adda Manu anya kuwa mutuminnan ko dai ko dai,d’azu fa naga irin kallon dayake miki’’

Dasauri Manubiya ta d’ago ta kalleta sai kuma ta shiga girgiza mata kai alamun A’a kamar zata yi kuka

Dariya Jidda tayi tace’’to ki d’auka da wuri kar ta tsinke,in yaso sai kije ko bakin dakalin gefen k’ofa ne karki tashi su Baba.

Kamar wata yarinya haka Manu ta d’an jinjina kai alamun tou sai kuma ta mik’e ta fice da sauri dan itanma tanaso ta d’auka d’in…tun d’azu take tunanin sa,sam bataji dad’in yadda har ya tafi bata samu tayi masa cikakkiyar godiya ba
kar yaga rashin kyautawarta..

Tun kafin ta Ida fita ta d’auka
a hankali ta maida k’ofar ta rufe ta nemi waje gefen dakalin ta zauna tukunna tace
‘’Assalama alaikom’’
Ahankali

Sai da ya lumshe idanuwan sa ya bud’e yanajin wani sanyi yana ratsa shi tukunna ya nemi waje ya zauna a bakin gadon ahankali ya fesarda iska sannan yace
‘‘Ameen
Wa alaiki Assalam’’

Daganan shiru ya d’an biyo baya kafin tace
‘’Ina wuni.’’

‘’Alhamdulillah’’yace
tukunna yace’’ya jikin Baba’’

Itama ‘’Alhamdulillah’’d’in tace
daga nan suka sake yin shiruu

A b’angaren Yashjub tunanin kawai yakeyi yana wishing
Inama ace tana gefen shi a yanzu haka

Manu kuwa ta lumshe idanunta ne kawai
dan zuwa yanzu tabbas zuciyarta tayi galaba akanta,
wani farinciki da nutsuwa kawai ta tsinci kanta a ciki.
Bata san meyesa yake son kiran ta ba amma kuma kiran nata da yakeyi da kulawar sa
gareta da kuma taimakon su dayayi ayau
tabbas sun k’ara bada gudun mawa wajen tsundumata cikin tafkin k’aunar sa.
Ta san ba lalle ta sameshi ba
ta san zata sha wahala ta san ya kamata ta yak’i zuciyarta amman kuma ta san ta makara dan ta san ko tayi yunk’urin hana kanta bazata hanuba,
she can’t help it
saboda ta riga ta kamu sannan abunda takeji a duk lokacin da tayi tunanin shi ko kuma take tare dashi
Is heaven
dan haka bata son ta yi loosing wannan feeling d’in ko na second d’aya
Ita kadai tasan me take ji….shiyasa a take tausayin kanta ya lullubeta.


‘’Nayi tunanin zaki kirani’’
Muryar sa ta katse mata tunani

Ahankali tace ‘’tun d’azu ban zauna ba sai yanzu’’

‘’Yeah nima haka…nasan ai ko da ace kin zauna d’in ma ba kiran nawa zakiyi ba.’’

‘’Saboda me’’
Tayi saurin tambayar sa.

‘’Saboda na lura kamar tsoron kulani kike yi bakya so mu fahimci juna in kuma nayi making move sai a balbaleni da fad’a ayi fushi a barmin office d’ina ‘’

Wata irin kunya ce ta lullub’eta kmar tana gaban sa haka ta rufe fuskar ta da tafin hannunta d’ayan
saboda gaba d’aya kunyar sa da kunyar abunda tayi masa jiya da safen take ji
Sai kuma tayi saurin dafe k’irjinta dan sai yanzu kwakwalwarta ta gama mata calculation
In yayi making move kamar yaya ?
Tayi wa kanta tambayar ba tare da tasan wa zai bata amsa ba

Shiruu ne ya biyo baya kafin
da mugun k’arfi kirjin ta ya buga jin a hankali cikin wata kalar murya yace
‘’Mannubiya’’

Bata san lokacin data kashe wayr da wani irin sauri ba
tana hak’i kamar wadda tayi y’ar tsere
Sai kuma ta lumshe idanuwan ta ta shiga sauk’e ajiyar zuciya a jere ajere.

ta d’an d’auki lokaci a haka kafin taji kira ya sake shigowa wayar ta riga ta san shi ne shiyasa ta yanke shawarar k’in d’auka amman kuma sai zuciyar ta tak’i bata goyon bayan yin hakan
dan haka ta amsa kiran…tana d’auka tace zan duba inna sannan zamu zo da ni da da su ya Musbah mu yi maka godiya
a office ban sani ba ko kana nan gobe sundsy’’ta so daga haka kawai ta kashe amma sam sai ta gagara.

Shiruu ya d’anyi kafin yace
‘’Ba za a abar godiyar nan ba kuwa?zaku sa inyi ta jin kunya fa’’

Ahankali tace ‘’ba komai ai da harda Baba ma zamuzo’’

Da sauri yace ‘’Innalillahi dan Allah ku rufa min asiri
In Baba yazo yimin godiya da kanshi ai sai in b’ace,d’azu ma duk sai da naji wani iri daya kira ni Wallahi.’’

Murmushi tayi kafin tace
‘’Eh muma mun lallab’a shi ya hak’ura amma dai ka bari mu d’in muzo saboda bazai yarda ba

Please Login or Register in order to submit comment