Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dining area da two bedrooms,k’ofar side d’in nata yana kusa dana Kausar na Yasira kuma kusa dana Mommy.
Tare ta zo da yarinyar ta Munirat mai kirki sosai da hankali ga nutsuwa
gata kyakkyawa sosai
doguwa dirarriya black beauty, ga gashi tubarkallah.
Ummi taso Munirat ta zauna
a d’ayan d’akin gefen ta
amma sai Mommy tayi insisting
akan itama a ware mata nata d’akin a gefen na su Yasmeen,hakan kuwa aka yi
aka ware mata d’aki anan side d’in nasu su uku
Ita,Yasmeen sai Yadira
kowa da d’akin ta amman suna sharing parlour….
Lamarin Yasir ya ishi Mommy
gashi gidan an dawo kamar komai bai faru ba dan hatta Kausar ta ware sosai ta ci gaba da shiga mutane,
Daddy ma yad’an sak’k’o yana d’an wasa da yaran
Shi da Mommyn ne dai har yanzu daga gaisuwa shikenan
shima sai in a gaban yaran ne
saboda in iyaka su biyu ne ko kallon ta baya yi.
Amman shi Yasir har yanzu shiru Allah kad’ai ya san inda yaje ya zauna.
Dan haka ta yanke shawarar tunkarar Daddy da maganar yau duk da bata san ya za su kaya ba amma ta saka a ran ta zata yi koma menene muddin za a nemo mata Yasir d’in ta.
Dama yau ita ce da girki dan haka ana gama dinner bayan an d’an tab’a hira kowa ya watse itama ta je ta d’an kimtsa ta nufi chan sama hawa na uku inda side d’in sa yake.
A parlourn sa ta same sa yana waya dan haka ta koma gefe ta samu guri ta zauna.






MANNUBIYA
17

Na
Humayrah Bulama

Elegant Online Writers.

Ya fi 1 hour yana wayar kafin finally ya katse kiran ya ci gaba da danna computer dake a gaban sa.Taji zafin yadda ya yi mata dama a wuya take dashi yau ko kunya babu haka ya dinga zolayar Ummi dazu a wajen dinner a gaban kowa ita kuwa ko kallo ba ta ishe sa ba.
Dakyar ta samu ta danne abun da takeji yana taso mata,ahankali tace’’barka da dare,Daddy’’.
Ba tare da ya kalle ta ba
Yace ‘’zaki iya tafiya,na gode.’’
Yana gama fad’in haka ya mik’e ya tartare kayayyakin sa dake zube a gaban sa kan centre table,daga nan ya nufi hanyar d’akin sa.
Da sauri itama ta mik’e tace’’a kan Yasir nazo muyi magana’’.
Kamar ba zai kula ta ba sai kuma yace’’what about him?’’
Ba tare daya kalle ta ba.
Sai da ta sauk’e ajiyar zuciya tukunna tace
‘’Ba ka lura baya gidan nan ba?yafi 4 weeks fa ba ya nan’’.
Sunfi 2 minutes a tsaye dan sam Daddy bai so ya kula ta,ya so ya danne fushin sa ya manna mata kawai ya yi wucewar sa amma sai hakan ya gagara..
Ahankali ya juyo ya ajjiye computer sa da wayoyin
a kan kujerar dake kusa da shi
sannan ya taka ya k’arasa inda take yace
‘’Khadijah,kar ki yadda ki kai ni bango a cikin gidan nan, ba ki san ya nake ji ba in na kalli fuskar ki ina zaune da ke ne kawai saboda y’ay’an dake a tsakanin mu da kuma alk’awarin dana yiwa su Abba kafin su rasu sannan na dawo gidan nan ne dan na lura in dai na zauna a saperate house da y’ay’ana tou tabbas zaki iya raba ni da su.
Banason yawan magana ta da ke saboda na lura misery,da tashin hanakli na kike son gani a koda yaushe kin fi so ki ganni cikin tashin hankali
Dana haka na zab’a yin nesa dake,
Ina samu peace da kwanciyar hankali daga wajen Saddik’a abun da kika gagara ki bani.’’

Bakin Mommy har rawa yake yi ganin tana shirin fara magana yasa yayi saurin d’aga mata hannu alamun ‘stop’yace
‘’Ba na buk’atar komai daga gareki u have done an say enough, kin san bani da lafiya amma a wannan shekarun kika zab’i ki tunamin da case d’in ‘Khadijah’.Ban san mai zan ce miki ba.
Amma kamar yadda nayi miki sutura na bar ki a cikin y’ay’an ki sannan bayan na zab’i raba gida dake na hak’ura na dawo na ci gaba da zama dake a k’ark’ashin inuwa d’aya tou nima inaso kiyimin alfarma d’aya tak ‘ki fita a harka ta’
Iyaka wannan kawai nake da buk’ata daga gare ki.
Case d’in Yasir ke kika san yadda za ki yi ki je ki nemo sa,amma Yasir ba jariri bane ba da zaki fake da case d’in sa ki k’ulla wata alak’a a tsakanin mu,duk inda yaje in ya gaji zai dawo in bai gaji ba kuma
Ubangiji ya sada fuskokinmu
A aljannah abu na k’arshe da zan ce da ke shine ki tabbata wannan ita ce magana ta mai tsayi ta k’arshe dake,in ba haka ba wallahi zan baki mamaki.’’

Wasu zafafan hawaye ne suka zubo wa Mommy a hankali yana shirin wuce wa tace
‘‘Ubangiji ma muna yi masa laifi mu rok’i gafara ya yafe mana,ba ce kayi hak’uri Daddy
ka bani last chance
I love u kar kayimin haka…..’’
Cikin fushi yace
‘’Ba kya so na ba kya k’aunata sam,shiyasa kike turturing d’ina,ko kinsan cewa akan maganar da kika yimin kad’an ya rage in mik’a kaina ga hukuma?kuma nasan kinsan menene hukunci na ko?’’
Cikin xubar hawaye Mommy tace.
‘’Ka yi hak’uri mu bar wannan maganar ta wuce…..’’
‘’Get out!’’
Daddy ya fad’a cikin katse ta.
Za ta yi magana ya sake cewa
‘’Get out,nace.’’
Da d’an k’arfi.
A hankali ta sa hannu ta share hawayen ta kafin cikin tsananin mutuwar jiki tace’’ka yi hak’uri’’
daga nan ta juya ta fita.
Ya dad’e a wajen kafiin da k’yar ya samu ya juya ya wuce d’akin sa.

A d’akin ta ta tarar da Kausar da Yasira,ta so ta b’oye musu damuwar ta amma suna had’a ido ta karaya bata san lokacin da ta fashe da wani irin kuka ba.
Sai da suka yi da gaske tukunna suka samu suka lallashe ta tayi shiru,Yasira ce ta d’au waya ta kira Baaba larai,tana zuwa suka shiga tattaunawa.Ba su suka bar d’akin nata ba sai wajajen k’arfe d’ayan dare bayan sun saka Kausar tayi musu alk’awarin kiran Yasir washegari,
In Allah ya kaimu…..

Washegari da sassafe
Kausar ta tashi ta shirya cikin wata dress mai kyau wadda bata k’arasa rufe mata k’afafun ta ba jan jambaki ja da kwalliya ta rambad’a sosai wanda hakan ya sake fito da ainihin kalar farar fatar ta,hula kawai ta saka a kan ta daga nan ta kama hanya ta fice ta nufi side d’in su Yashjub tana adduar Allah yasa bai fita ba,dan dukda yau ba aiki taji Yasira tana cewa sunada important meeting.

A parlourn ta same sa shirye tsaf cikin suite ga briefcase d’in sa a gefe yana zaune yana sipping tea.A hankali ta saki wani lallausan murmushi kafin ta k’arasa ciki,cikin takun ta mai tsananin d’aukar hankali,sai da taje kusa dashi tukunna tace
‘’Salam alaika’’.
Tun lokacin data turo k’ofar ta shigo ya lura da ita dan haka ya sake tamke fuska ta mau kamar bai tab’a murmushi ba.

Ahankali ta nema waje ta zauna a gefen sa,sannan tace
‘’Ya Yash,Ina kwana’’.
Ci gaba kawai yayi da sipping tea d’in sa yana kallon tv still bai ce mata uffan ba.
Badaban Kausar A ce a wajen tsaurin ido ba
a yadda ya tamke fuska ya Isa yasa ta tsorata ta fita.
Duk da tana d’an fargaba haka ta daure a karo na uku tace’’Ya Yash’’.
Lumshe kyawawan idanuwan sa yayi a hankali ya juyo gare ta sannan ya bud’e yana mai kallon ta ido cikin ido
tukunna yace
‘’Duk abun da kike buk’ata ki turomin Yadira anjima,tashi ki fita.’’
Ganin yadda ta kafe sa da idanuwa ne yasa kawai ya mik’e ya d’au briefcase d’in sa ba tare da ya sake bi takanta ba ya nufi hanyar fita.
Dasauri ta sha gaban sa cikin d’an gudu tace
‘’Ya Yash Mommy ce fa ta aiko ni wajen ka’’
Ta fad’i haka tana k’ok’arin matsawa jikin sa sosai sannan ta saka hannu zata kamo briefcase din sa.
Duk kalar tsaurin idon ta sai da taji tsoron kalar kallon da yayi mata dan haka ta d’an ja baya kad’an ta sunkuyar da kanta k’asa.
Dakyar Yashjub ya samu yad’an lallashi kan sa ya wuce ya fice ya barta anan wajen
amma da so yayi ya d’an wanke ta da mari watakila zata dawo saiti,
In akwai abun da yafi tsana a rayuwar sa bayan cin amana to shine mace mara kamun kai,
tabbas Kausar y’ar uwarsa ce
amman kwata kwata jinin sa bai d’auke ta ba tun filazal gashi yanzu kuma rashin kamun kan ta ya sanya ta kuma fita a kan shi ko ganin yarinyar baya son yi,wallahi.

Da wannan tunanin ya k’arasa motar sa ya shiga ya zauna ya
lumshe idanuwan sa,
A take idanun ta wanda izuwa yanzu ya zame masa jiki suka hau yi masa gizo.
A ran sa yace
‘’Ga inda ake mace nan,gaisuwar ta ma tsada ne da ita,sannan tayi laifi amman tsabar sanin darajar kai
bata yi gigitar da d’ayan namijin yayi yana bada hak’uri ba,ya kuma lura da yanda ta rud’e amma ta dake sam bata yarda ta zubar da class d’in ta ba.
A hankali wani lallausan murmushi ya sub’uce masa
A fili yace
‘’Sai shegen kukan shagwab’a kmr wata y’ar baby’’…
Yana nan zaune ya nata tunani
kira ya shigo wayar sa,
Ba k’aramin fad’uwa gaban sa yayi ba daya d’auko wayar zai amsa idanuwan sa suka sauk’a akan time,zaman sa anan har yayi 30 minutes kenan??
ya yiwa kansa tambayar ba tare da ya samu mai basa amsa ba.
Ganin kiran yana shirin tsinkewa ne yasa yayi sauri ya d’auka ya kara a kunnen sa ahankali yace
‘’Daddy Ina kwana,sorry i got
held up,gani nan zuwa’’ .
Yana gama fad’in haka ya kashe wayar ya kunna motar ya bata wuta ya wuce,
A ran sa yace
‘’I really need to see Najeeb.
Zuwa yanzu ya fahimci in dai ba son yarinyar nan yake yi ba
to tabbas akwai dalilin daya sanya Ubangiji ya turo ta cikin rayuwar sa,ya san ma ba zai you ace yana son ta ba tun da bai san ta ba,ya yi addu’o’i dan haka definitely ba aljana ko mayya bace ba tunda gashi har yanzu bai bar tunanin ta ba.Tun yana k’ok’arin yakice tunanin ta har ta kai ta kawo zuwa yanzu ya daina saboda in yana tunanin nata wani
nutsuwa annashuwa da farin ciki na musamman ne suke dirar masa wanda har ya kan ji
baya k’aunar abun da zai gilma ko ya gifta a tsakanin sa da tunanin ta….
Dan haka kawai ya gama deciding zai ajjiye b’oye b’oye a gefe yayi facing Najeeb akan maganar ta yau yau d’innan inshaaAllah ,tun kafin a samu matsala,he wants to know her!..






MANNUBIYA
18

Na
Humayrah Bulama

Elegant Online Writers.

Da wannan tunannin
Ya k’arasa makeken company d’in Daddyn nasu,sanin da yayi suna da bak’i ne yasa bai wani tsaya ko ya biya ta office d’in sa ba,direct ya wuce in da ake meeting d’in…

Bai samu sun kammala
Komai ba kuwa sai wajajen k’arfe biyu,duk saurin sa bai samu damar k’arasawa office d’in Najeeb ba sai pass 3.

A parking lot suka had’u da Najeeb d’in yana shirin fita,tun da ya hango Yashjub d’in ya taho ya tsaya daga k’okarin bud’e k’ofar motar da ya ke yi ya zuba k’asa ido yana murmushi yana girgiza kai a ransa yace’’Allah mai halittar kowa da yanayin na sa halin
ya san zai zo kuma yasan ba lallai ya same sa ba amma ya d’auka waya yace nasa ya jira sa kawai shine yana ganin aiki, ya gwammaci yazo in bai same sa ba ya juya’’.

‘’Kai lafiyar ka kuwa!’’
Yashjub wan da ya k’araso kusa da shi yanzun yayi masa tambayar cikin tsare gida.

Y’ar guntuwar dariya Najeeb ya saki kafin yace
‘’Mamakin ka nake yi,kasan wani abu ne ya d’an rike ni,ba dan haka ba da na dad’e da fita daga nan’’

‘’Hmmm’’
Ya ce
Kafin ya d’aura da cewa
‘’Ka kyauta kuwa,bani key d’in in shiga in ka gaji da tsayuwa ka same ni a office d’in mama.’’

Murmushi Kawai Najeeb d’in yayi daganan ya mik’a masa key d’in ya wuce shi kuma ya bud’e motar sa ya zuba kayayyakin sa ya rufe tukunna ya bi bayan Yashjub d’in.

Kusan a tare suka shiga
Office d’in daya kenan k’all gwanin ban sha’awa sai faman tashin kamshi yake yi.
Fridge Yashjub ya nufa ya d’auki ruwa da cup tukunna ya nemi guri ya zauna akan sofa kusa da Najeeb d’in,yana zama ya b’alle marfin ruwan ya zuba a cup ya kafa a baki yayi bismillah ya shiga sha.
Ajiyar zuciya Najeeb ya sauk’e kafin yace
‘’Uncle yace in baka hak’uri
inshaaAllah nan da sati biyu za’a gama ginin estate d’in,
k’ofofin ne suka d’an yi wahala
gashi kace dole sai irin na estate d’in Abuja da Kano za a saka shiyasa abun ya d’an yi musu tsauri amma yanzu haka an samu anyo order yace kawai za’a fara fenti da fixing electronics in an kawo ya zama na shine last kawai.’’

Kallon dayaga Yashjub d’in yana ma sa ne yasa yace ‘’Me nene kuma?Yash!..Uncle d’ina ne dai,ido yasan na gida.’’

Murmushi yaga Yashjub d’in yayi kafin yace
‘’Kallon da kaga Ina maka na mamakin yadda kahau zuba ba tare da ka ji dalilin zuwana ne,ce maka aka yi akan maganar estate nazo nan?’’
Yayi ma sa tambayar yana kafe sa da ido.
Ajiyar zuciya Najeeb ya sauk’e kafin yace
‘’To naga ai shine priority d’in ka a yanzu mu kuma muna ta yi maka delay’’.

‘’Yeah, days ago shine priority d’ina amma yanzu kam ba shi bane ba kawai dai tunda ka taso maganar tou ka gayawa waenda ka ce sun ce suna son guda d’aya rent su jira sai nan da one month in xa su iya.’’
Yash ya fad’a hakan yana sake zuba ruwan a cup sannan ya kai baki.

‘’Ok’’
Kawai Najeeb ya iya cewa
yana mai k’ok’arin fahimtar mood d’in Yashjub d’in.

Wani d’an guntun murmushi yaga Yash d’in yayi,ba tare da ya kalle sa ba Yace
‘’Ina Manubiya?’’

Da d’an k’arfi Najeeb yace’’what!’’Kafin ya d’aura da cewa wai dama da gaske kake kenan kuma ka tsaya ka na ta yimin kwana kwana??ba fa a zurfin ciki a harkar nan dan in ka tsaya wasa tsaff sai dai kaji sold out!wallahi.
Kaii amma nnaji dad’i ni zan fara kai wa Mommy good news Alhamdulillah dutse is in love finally’’.
Najeeb ya k’arashe maganar yana mai fashewa da dariya.

Tsayawa kawai Yashjub yayi yana Kallon sa bai ce masa uffan ba

Haka nan Najeeb ya tisa sana gaba yayi ta zolayar sa,sau da ya gaji dan kan sa yayi tukunna Yashjub yace masa
‘’Ka gama?zaka iya saurara na yanzu muyi abun da ya kawo ni, ko in tafi kawai?’’

Cikin dariya k’asa k’asa yace
‘’Sorry,Ina jin ka angon Manubiya’’.

Ahankali y ya lumshe lumsassun dogayen idanuwan sa ya bud’e tukunna yace
‘’Najeeb ba wai son yarinyar nake yi ba…..’’

Cikin tarar numfashin sa Najeeb yace
‘’Yet,buy you like he ko?ai dama abun da zaka ji kenan yanzu tunda kwata kwata sau d’aya ka tab’a ganin ta,haka abun yake ai.Get to know her Man!InshaaAllah nan da en watanni za mu sha biki…’’

‘’Ya Allah,
This is so awkward’’.
Yash ya fad’a yana mai sauk’e wata nannuyar ajiyar zuciya.
Dariya Najeeb ya saka Kafin ‘’Ai yanzu zan baza ka a groups kaff friends d’inmu sai sun san aljannar data aureka ta rabu da kai finally ko kuma ta mutu,wannan abun farin cikin har walima zamu had’a.’’

‘’Pls don’t,haba Najeeb ya kake yi min haka?na zo maka da matsalata a matsayin ka na Aboki na instead of ka tsaya ka saurare ni amma sai faman shirme kake yi min,shikenan kawai bara in tafi…’’
Yashjub ya fad’a yana k’ok’arin mik’ewa da alama ran sa ya d’an sosu.

Dasauri Najeeb
Yace
‘’Yi haku’uri’’yana mai rik’o hannun sa sannan ya yi serious face yace ‘’na daina,
Talk to me ,friend .’’

Sai da Yashjub yad’an k’ura masa ido tukunna ya koma ya zauna.
Ya dafe kan sa da hannun d’aya ya d’an sunkuyar da kan sa ya lumshe ido ahankali yace
‘’Ba wai son yarinyar nan nake yi ba Najeeb,saboda wallahi yanzu inda ace za a kawo mata goma a kulle musu Iyaka idon su a bar fuskar a bud’e to ba lalle in iya nuna ta a cikin su ba,iyakar idon ta kawai na gani that very day amman tun daga lokacin na gaza sukuni
In fa na lumshe ido na har ganin idonta nake yi
sannan haka kurum sai in dinga ji kmr muryarta tana yimin gizo a kunnuwana
sannan inba tunanin ta nake yi ba ko maganar ta as in in nayi forcing kaina in cireta a raina to gaba d’aya sai in ji Ina neman susucewa kaga alal misali yanzu haka maganar ta muke yi dakai ko?to ni kad’ai na san irin peace of mind d’in da nake samu,wani sanyi nake ji har k’asan zuciya ta da annashuwa Sannan with each passing second na rayuwata
all i want to do shine
In san ta
As in kamar akwai abun da yake pushing d’ina akan in je in santa inyi bincike akan ta in zama very close to her like sooooo close..may be a friend.’’
Ya k’arashe maganar tasa a hankali yana mai d’agowa ya kalli Najeeb wanda yaga ya yi shiruu ya k’ura nasa ido kawai saida ya fesar da iska tukunna ya ci gaba da cewa
‘’Na san me kake tunani amma dan Allah karka fad’a,I can’t love her tun da ban riga na san ta kuma na gan ta ganta sosai ba shiyasa ma na riga nayi concluding abun as ba so bane
it’s definitely something else
So just
Ka bani shawara mu tattauna a nemo mafita amma kar ka ce min son yarinyar nan nake yi dan nasan ba son ta nake yi ba.’’

Dakyar Najeeb ya samu ya iya danne dariyar da take ta faman taso masa,duk da tausayin daya ba sa amman kuma ya ba sa dariya at the same time.
Gashi dai Yashjub is in love da ikon Allah saboda gaba d’aya bayanan shi akan Manubiya
amsar d’aya ce tak ‘’KAUNA’’
although bai ganta sosai ba
amma idanuwanta da muryarta da ruhinta sun riga sun hana sa sukuni tun yanzu
Ina kuma ga in sun kasance frnds d’in kamar yadda yake da buk’ata a yanzu
Lokacin da zai amayar da abun da yake ran sa ma ba zai saniba
Tabbas kuma za’ayi soyayyar da ba lalle an tab’ayin kwatankwacin irin ta a tarihi ba dan tabbas ya lura da Manubiyan itama a ranar da suka fara had’uwa da Yash d’in.

‘’Najeeb’’
Yashjub ya kira sunan sa.
Kame kame Najeeb ya fara yana tunanin mai zai ce masa,saboda shi dai ya riga ya gama fahimtar Yashjub d’in tsaff to amma shi kuma gashi yace kar a ce masa yana son yarinyar ne
Which is the absolute truth…
Dan haka a hankali cikin son fahimtar dashi ta ruwan sanyi Najeeb d’in yace
‘’Mai yasa kake tunanin ba son ta kake yi ba?soboda kai ba mutum bane?’’
Ganin yak’i ma ya kula sa ne yasanyaNajeeb d’in cewa
‘’Shikenan bara zansan abun yi
amma gaskiya ni a yanzu ba zan iya nema maka mafita ba.
Frnds d’in dai daka ambata inshaaAllah zan had’aku friendship,although ni ban amma san ta Ina zan fara ba tun da kaga ni Maganin ta ne amma inshaaAllah zuwa gobe zaka ji ni zan nemo idea soon,bari zan jira dan kamar suna da exams d’in Dr Auwal,’’
Shiruu Najeeb d’in yayi daga magana kafin ya sake cewa
bari zan san yadda zan yi kar ka damu na ma nemo idea’’.

‘’Ok’’
Kawai Yashjub yace
Kafin ya sake cewa
‘’Kuma wannan wanda na gan su tare kana tunanin a kwai wani abun a tsakanin su’’?

Dariya najeeb yayi a ran sa yace
‘’Ga wani sign din ‘kishi ‘
A fili kuma sai yace
‘’I don’t think so amma dai zan yi finding out’’
Shiruu Yashjub yayi dan sai kuma ya d’an fara jin haushin kan sa na tambayar da yayi wa Najeeb d’in ta yanzu.
Ganin yayi shiru ne
Yasa Najeeb d’in kawo wata hirar daganan suka hau tattaunawa…

Kiran sallar laasar ne ya tashi zaman nasu
Yashjub ya wuce
Najeeb kuma ya nema wani ya aika shi inda su Manubiya suke exams yau yace masa ya kira mishi Abbbakar.
Daganan ya wuce masjid…..

Tun rabuwar Kausar da Yashjub data shige d’akin ta ta rufe bata bud’e ba
Mommy taje har sau biyu
Jin tayi knocking ba a bud’e ba
yasa tayi tunanin ko ta fita ne maybe
dan haka ta hak’ura tahau zaman jiran ta.
Ganin har yamma tayi bata ganta ba yasa ta sake komawa dan ta sake dubawa dai dai nan ita kuma Kausar d’in tana shirin fitowa daga side d’in nata.
Kana ganin fuskarta kasan taci kuka ba kad’an ba.
Ahankali cikin rashin dad’i Mommy tace
‘’Haba Kausar yanzu ashe tun dazu kike ta faman kuka,mai ya faru haka,mai ya sameki?’’
Tayi mata tambayar tana mai tsare ta da idanuwa.

Fad’awa tayi jikin Mommy ta sake fashewa da wani irin kuka
cikin kukan tace
‘’Mommy ko kallo ban ishi Ya
Yash ba,is like ya ma tsane ni,
tayaya kike tunanin zai kalle ni ma
Talkless of ya bani time da chance d’in da zan kafa kaina a cikin zuciyar sa?.
Keda Baaba Larai kullum sai cewa kuke yi in jira in jira yau an fi wata d’aya kuna cewa in jira,so kuke yi inyi ta jira har sai lokacin daya had’u da wata ya fara son ta tukunnna ni kuma in nuna mishi ra’ayina? nikam a gaskiya Wallahi ba zan sake bin ta maganar ku ba ko zai
ko zai kasheni da duka zan gaya ma sa in yaso keda Baaaba Larai kusan abun yi daganan.’’
Da kyar Mommy ta samu ta zaro ta daga jikin ta cikin son fahimtar da ita tace
‘’Kausar gaggawa aikin shed’an ne ki tsaya ki nutsu
na gaya miki nasan abun yi kinji saurin me kike yi ?
Yash naki….’’

Cikin ture hannun Mommyn daga jikin ta tana kuka sosai tace
‘’Mommy dole inyi sauri baki san ya nake ji game da shi a cikin zuciya ta ba ina tsoron kar ya sub’uce min sannan ga fargabar kar Yasir ya sanya Daddy yayi min dole,
Ko da yaushe fa a cikin fargaba nake.Kar in rasa Ya Yash
In ya sub’uce min mutuwa zan yi,wallahi mommy inban aure sa ba ………

Tsit maganarta ta katse ganin Yash d’in yana hawowa sama cikin main parlour d’in saman

Cikin zuciyar ta kuma sai tace
‘’Ai da ban yi shiru ba gara kawai in fad’a yaji ko zan huta,’’dan haka tayi saurin kau da kai kamar ba ta gan shi ba,ta bud’e baki zata yi magana kenan shi kuma yace’’Mommy’’da d’an k’arfi.
Dasauri mommy tasa hannu ta toshewa Kausar baki dan har ta cigaba da cewa’’wallahi…’’.
Ba tare daya kalli Kausar d’in ba ya k’araso wajen ya na kallon Mommy
Fuskarshi a murtuke kamar bai tab’a dariya ba yace
‘’Barka da gida Mommy’’bai jira jin me zata ce ba ya d’aura da cewa
‘’Mommy dan girman Allah kar ki sake aiko min yarinyar nan side d’inmu,tun da kin san Bata da hankali kuma bata san ciwon kanta ba
da baki turomin ita ba,ko mayafi fa babu a jikin ta dazu haka taje min.’’

Cikin lallashi Mommy tace
‘’Yash wayoyin ta fa da atms har ma da passport duk ka had’a ka kwace yau kusan wata ko in ce fiye da wata d’aya ma,kaga kuwa ai kai ka kira ta side d’in ka ba niba’’.
Cikin fushi yace
‘’Au dama ba ke kika turo ta ba
zuwan kanta ta yi?’’
Ya fad’i hakan yana nufar Kausar d’in a zuciye kamar zai make ta.
Dasauri Mommy ta sake shiga tsakanin su cikin lallashi tace ‘’A’a ni na turota mana
Hausa ce nayi maka
Anyways tunda baka gane ba shikenan
yanzu ka yi hak’uri

Please Login or Register in order to submit comment