Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

toshe duk wata matsala da take shirin tasowa.

Suna gama waya da Manubiya wadda rikicin ta na kwana biyun nan yake basa dariya sosai,ya mik’e ya nufi parlourn Daddy dan ya san by now ya gama duk wasu aikace aikacen sa……a zaune ya same su shi da Ummi kamar wasu mak’iyan juna!ita ta juya fuska tana kallon makeken aquarium d’in da yake a parlour ta had’e rai,shima Daddyn ya kauda kai yana daddanna wayar sa fuskar nan tamau!.

Ko ishashshiyar gaisuwa Ummi bata tsaya sunyi da Yashjub ba
ta mik’e ta ce ‘’sai da safen ku’’daga haka ta yi wuff ya fice kamar wadda take zaune akan k’aya.

Bin ta kawai Daddy yayi da kallo har ta fice ta rufo musu k’ofar….sam ya kasa gane kanta gaba d’aya,abun nata kamar wata mai aljanu,tun abun bai dame sa ba har ya zo ya fara damunshi…yanzu haka shi ne ya kirata akan su samu su d’an yi magana su d’an dedeta amma tana shigowa daga gaisuwa ta d’auke kai ta had’e rai! Shi kuwa wallahi ta yi kad’an ya bita ya lallasheta
Idan ma abunda take jira kenan……


Ahankali cikin kwantar da murya Yashjub yace mishi
‘’Daddy,wani lokacin fa muma sai mun d’an sak’k’o tukunna zaman yake yin dad’i,kuma na tabbatar inda ace issue na iyakar kai da ita ne da tuni komai ya wuce na san da bazata d’auka da zafi har haka ba amman abun ya had’a da yara shiyasa ta ji ciwo sosai.’’

K’ura masa ido Daddyn yayi kamar ba zai ce komai ba sai kuma ya sauk’e ajiyar zuciya yace’’Yash!!,ko a gidan giya akwai babba.Ban auri matar da zan dinga bin ta tana raina ni tana raina min wayo ba,sorry to say this to your face ba wai cin fuska ba amma ko macen da na so fiye da kowa batayi min wannan abun ba.
Sannan nan gidan su Yasmeen ne abu d’aya dana sani kuma ba zan tab’a koma wa baya akan maganata ba shine
‘Dole a lallab’amin yara a gidan uban su kuma babu wanda ya Isa ya zo nan ya juya min su!’
In ta yarda da haka a zauna lafiya in kuma ba ta yarda ba
ta je tayita fushi
Itace alone……’’.


Ahankali Yashjub yace
‘’Amman Daddy…’’

Cikin d’an fushi Daddyn ya katseshi ta hanyar cewa
‘’Yashjub bar maganar matar nan,banaso!’’



Shiruu Yashjub d’in yayi
kafin ya sauk’e ajiyar zuciya sai kuma ya mik’e daga inda yake ya koma 3seater da Daddyn yake zaune akai ya zauna,ahankali yace’’am Daddy’’

Murmushi Daddyn yayi
kafin yace’’za a yimin wayo kenan’’

Dariya duk sukayi kafin Yashjub d’in ya fara magana ahankali’’am..Daddy dama
alfarmar ka da rufin asirin ka nake nema.’’
Bai jira komai ba ya ci gaba da cewa’’na san it might seem impossible amman in ka yi min wannan ban san wanne irin farin ciki ni kaina zan shiga ba
A baya ka sha gaya mana cewa’ko wacece/wanene muke so a matsayin abokiyar/abokin zama in dai tarbiyyar su ya kwanta maka to ba za ka yi k’asa a guiwa ba wajen ganin mun mallaki juna.To Daddy ni a yanzu mahaifin yarinyar da neke so yana buk’atar d’aurin auren nan da sati biyu ne
shiyasa nake neman alfarmar ka
In ba damuwa a d’aura a cikin sati biyun mai zuwa kamar yadda ya buk’ata.’’

Shiruu Daddy ya yi har sai da Yashjub d’in ya d’ago dan kalar shirun da Daddyn ya yi yayi yawa,had’a ido suka yi kamar an fisgi maganar daga bakin Daddy yace’’yaushe ka yi budurwa ??’’fuskarsa tana baiyyana mamaki

Sunkuyar da kai Yashjub yayi dasauri dan tashi d’aya ya ji wata kunya ta lullub’esa.

Tashi d’aya yaji daddy ya fara dariya cikin dariyar ya sake cewa’’Dan Allah dagaske Yashjub ya akayi kayi budurwa,abun ya bani mamaki hajiya mama ta yi min magana tun lokacin dama nake so ka yi min maganr a tunanin na ita ta had’a ka da yarinyar ashe da gaske kai ka kyallo abarka.’’
Ya fad’i hakan yana dariya….

Kamar Yashjub zai fashe da kuka cikin yin kalar tausayi yace
‘’Daddy dan Allah ka daina’’

Ai kuwa ya sha tsokana a wajen Daddy dan har ga Allah Daddyn ya ji tsananin mamaki
kafin daga bisani ya yi
gyaran murya ya gyara zama tukunna yace’’Yash ka tabbatar kana sonta itace zabin ka’’

Ahankali yace ‘’Yes Daddy!with all my heart.’’

‘’Alhamdulillah’’
Daddyn yace
kafin yaci gaba da cewa
‘’Yash,tabbas alk’awarin da nayi muku yana nan babu abunda ya chanza amma ka san ba zan bari ka cutu ta ko wacce irin hanya ba.
Abu d’aya da nayi mamaki shine ta inda mahaifinta ya dage akan a yi a cikin sati biyu
wannan shine abunda zan fi sakawa microscope
Which i’m hoping ba wata matsala baceba dan nima farin cikin naka nake son gani,in an duba an ga ba matsala sannan aka yi bincike shima akaga ba wata matsala to da yardar Allah sai a d’aura auren a sati biyun kamar yadda suka buk’ata.Allah ya yi maka albarka.

Ahankali Yashjub ya sauk’e ajiyar zuciya yana mai jin wani farin ciki mara misaltuwa kafin a hankali a fili yace ’’Alhamdulillah’’

Muryar Daddy ce ta katse sa jin yana ce wa’’Ka bani adress d’in da wuri saboda ina gama bincike nake so zan aikawa su mama dan su taho da wuri.’’

D’an b’ata fuska Yash yayi ya d’ago yace’’Daddy yanzu wannan tsohuwar itama sai ta zo?’’


Dak’uwa Daddyn yayi masa kafin yace’’Dole ta zo,kuma in ka yi mata abunda bata ji dad’i ba tsaf sai ta ce a fasa
kasan kuma daga ni
har uncle d’in naka dole abunda tace za mu yi
daganan sai in ga k’arshen soyayya’’

Dasauri Yashjub ya ce ‘’Na gode sosai Daddy zan yi maka forwardn adress d’in yanzu inshaaAllah’’daga haka ya mik’e da sauri yace’’sai da safe’’tukunna ya fice
tun kafin Daddy ya sa shi ya nutse cikin k’asa dan ya lura sarai yau Daddy tsokana yakeji
shikuwa ba zai iya ba.hakanan ya wuce zuciyar sa cike taff da farin cikin da bai tab’a tsintar kanshi a cikin kwatan kwacin sa ba….

Bayan fitar Yashjub,a hankali
Daddy ya lumshe idanuwanshi
He s very happy da Yashjub ya samu wadda yakeso kuma gashi da izinin Allah zai aureta.
Yana tuna lokacin da ya auri Mommy……shiyasa a ko da yaushe yake addu’ar Allah kar ya sa d’aya a cikin ya’yan shi yayi experiencing wannan feeling d’in,shi kad’ai yasan mai ya ji shi kad’ai ya san zafin aurar wanda ba ka so!.

Har i yau kuma yana tuna lokacin da ya auri amaryar sa Khadijah…farin cikin da ya rayu a ciki shi yake yiwa gaba d’aya ya’yan sa kwad’ayin
su samu shiyasa ya dad’e da yi musu alk’awarin ko waye sukeso
under any circumstances
InshaaAllah zai shige musu gaba ba zai yi k’asa a guiwa ba sai yaga sun mallaki juna
wannan dalilin ne yasa bai takurawa kowa a cikinsu akan yayi aure ba saboda yana so
kowa ya nemi wanda yake k’auna cikin nutsuwa
Yahanasu ma gani yayi kamar tana cutuwa shiyasa yake saka baki a cikin lamuranta if not da ba zai tab’a cewa komai ba
dan bashida wani burin da ya wuce yaga gaba d’aya y’ay’an sa sun samu pure true
and genuine love and happiness
kamar yadda shima ya samu
A
lokacin da Khadijansa take da rai!!
Ahankali wasu zafafan hawaye suka shiga bin k’uncin sa
wannan wanne irin feeling ne???
He hate her
sannan kuma har yanzu yana mahaukacin sonta da k’aunar ta
and again
he just wants to kill himself for abunda yayi mata.
Zuwa yanzu ya gama deciding
In Allah ya ba shi ikon ganin auren Yadira ya kuma tabbatar da yaran sa are all matured
to inshaaAllah zai mik’a kanshi ga hukuma!!
He can’t bear this pain anymore,shi kad’ai ya san me yake going through babu wanda ya lura ba kuma wanda ya sani amman a ko wacce rana ta duniyar nan he’s going through hell.
……..
Tun ranar da Yassir ya je d’akin Kausar ya tarar da ita suna magana da Yassira…..tunda ga wannan ranar bai sake saka ta a idanu ba dan wasan y’ar b’uya ta hau yi da shi gadan gadan,sai
yau tukunna ta daure da kyar ta ce bari dai ta lek’a sa,sai chan dare around 12 tukunna ta samu ta lek’a d’akin Yassir d’in ita ala dole zata mai basaja gudun kar ya fahimci komai…ba yabo ba fallasa ya karb’eta dan haka ta samu kwarin guiwar zama a kusa da shi suka gaisa tukunna tace’’kwana biyu ka ji ni shiru,sorry mun d’an sake samun case ne ni da Daddy shiyasa ka ga Ina kuka ranar da ka zo to kuma tun daga ranar bani da lafiya sai yau ne na d’an ji dama dama,’’
Ta fad’i hakan tana mamakin yadda tun ranar da ya zo ta rufe k’ofa bai nemeta ba sannan bai sake lek’a d’akin taba ko awaya bai ce mata hi ba yau kwana hud’u kenan.

Murmushi kawai ya yi mata yace kar ta damu ba komai,daganan ya d’an ja ta da hira, faram faram dai haka ya yi mata kamar ba komai

Abu d’aya ne ya bata mamaki ta inda ta nuna za ta kwana a d’akin amman yace mata ‘’its fine ta tashi ta tafi kawai,ita da bata da lafiya ma’’


Itanma daman hakan take so
dan haka ta yi masa sallama
daganan ta fice,tanata mamakin sa.

Sai kamar after 10 minutes da fitar ta tukunna ya d’auki wayar sa ya shiga ya kira wata number tana fara ringin ya mik’e ya fice ya tsaya a balcony d’insa wanda yake opposite inda ake parking motocin gidan
Har ga Allah bai shirya yin haka tun yanzu ba
ya so ace ya basa wahala ya kassara sa tukunna sai yayi deciding abunda zai yi
masa next
But Kausar ta janyo komai
ya lura barin sa a doran k’asa had’ari ne a garesa ta ko wanne fanni!!..
Dakyar yanajin yanda tunanin ya sake tunzura zuciyar sa ta fara tafarfasa yace’’ba kowa
ta nan cameras d’in ma na tsaida su
kayi sauri kafin su yi zagaye.’’

Yana tsaye a wajen d’aya
daga cikin masu yiwa gidan hidima wanda suka gama wayar dashi kenan
Ya lallab’o ya je shi jikin motar da Yashjub yake fita aiki da ita kullum ya kunce tayoyi biyu ba duka ba,ya kunce su ta yadda ba za ayi tafiyar minti biyu da motar ba tayar gaba da ta baya waenda ya kunce d’in za su fita .


Sai da Yassir ya ga mutumin ya kammala komai ya koma inda ya fito tukunna
shima ya koma d’akin shi ya rufe k’ofar balcony d’in
yanajin wani nauyi yana sauk’a daga kan k’irjinsa.Addu’arsa d’aya ‘Allah yasa kar Yashjub ya yi suprising d’in sa ta hanyar chanza motar hawa gobe,yayinda a d’ayan b’angaren zuciyar sa yake mamakin Kausar da kuma tunani da lissafin abun da zai yi mata in zarginsa a kanta ya tabbata,hatta Yassira itama sai ta karb’i rabon ta wallahi
dan ya lura tabbas itama ta san wani abun daman tun ba yauba!za su san sun yi wasa da hankalin sa.
…….
A gidan dai ranar Yashjub ne kawai yayi baccin kirki,Mommy da Baba Larai za ‘a iya cewa sun fi kowa tashin hankali saboda zuwa yanzu su kansu sun san da tahowar auren gadan gadan!ga shi sun nemi ko wacce mafita sun rasa aiki akeyi tuk’ura amma kamar ma rura wutar ake yi wanda hakan ne ya sake hautsina su saboda ba su tab’a zaton abun zai gagare su har haka ba.

Yahanasu kuwa tanachan shoppping online dan Yashjub ya sanar mata yadda sukayi da Daddy shiyasa ta fara dudduba kayayyaki tun ayau saboda taga babu lokaci.

Daddy kuma takaicin abunda Ummi take yi masa ne ya hanasa bacci.

Kausar da Yassira ma kowa a rikice.

Ummi takaici da tsanar Daddy ne ya hanata bacci.

Munirat kuma d’abiun Yassir ne suka taru suka d’aure mata kai
shiyasa ta b’ata lokaci tana
decidin ta ci gaba da kula shi ko ta rabu da shi kawai,ita dama bata da wani abokin shawara dan she’s not good with frnds
Sister d’in ta kuma da Ummi
fushi sukeyi da ita har yau sun k’i su sake mata infact ko
ko ma sun sake mata d’in ita kanta ta san
bata isa ta tunkare su da maganar soyayyar ta da Yassir ba wanda ta san hakan ne ummulaba’isin fushin na su da ita.

Yasmeen da Ya’isha ma duk hankalin su a tashe yake ga kuma k’unci da tashin hankalin da suka gani tartare a fuskar Mommy da kuma abunda Yashjub da Yahanasu sukayi ne ya taru ya b’ata musu rai,shiyasa suma suka gagara runtsawa.

Yassir kuwa abubuwa biyu ne suka had’ar masa
Na farko yanaso ya yi getting rid of Yashjub
saboda komai ya dawo hannunshi kuma he has to do it fast ko dan ya samu ya gano gabas d’in Kausar

amma fa duk da taurin zuciya irin tashi tun d’azu yake fargaba…ba wai fargabar kashe d’an uwanshi da ya shirya yiba,yana fargaba ne kar zarginsa akan Kausar ya tabbata dan in ya tabbata
bai san me zai ji ba
bai kuma san mai zai zama ba in ya tabbatar da cewa Kausar tana son wanin shi
wanin ma yayan shi
sannan har su Yassira sun sani amman suke yi masa rufa rufa
suka munafurcesa,tabbas ya san in zarginsa ya tabbata
ya zama all alone kenan
dan haka kansa kawai zai ke dubawa ko Yassira da yake ji da ita as his twin ba zai sake bi takanta ba tun da suma basu damu da damuwar sa ba.!

Waennan tunane tunanen
da kuma zullumin son ganin gobe ne suka hana shi bacci.

Sai da aka fara kiraye kirayen assalatu tukunna da taimakon shed’an ya samu wani bacci mai d’an karen dad’i ya kwashesa……..


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment