Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya yi tsanani har haka ba.
Itama ba wani k’arfi ne da ita ba balle ta taimaka musu,dan ta lura lamarin na Inna har da d’an rashi da babu.
Cikin rashin jin dad’in ganin Innar a haka tace’’akwai baba mai gadi na gidan ammi,malamin tsangaya ne kafin ya dawo gadin ya barwa ya’yan sa,za ta ce masa ya dinga yiwa inna rubutu duk jumaah sai Ya Musbah ya dinga karb’a sadak’a saboda Allah’’

Sun ji dad’i kuwa sosai suka yi mata godiya tanata cewa’’kar su damu ba komai,’’daga nan suka d’an tab’a maganganu
kafin daga bisani ta yi musu sallama ta tafi.
Manu ce ta rakata har k’ofar gate daganan ta juyo ta komo
Tana shiga d’akin ta gansu sun koma jigum d’in su kowa kana ganinsa kasan yana cikin damuwa.Dan haka ta shiga tambayar su ‘’me ya faru!’’.
Ya Nafi’u ne ya iya bata amsa ta inda yake cewa’’kiran da Kaka Mallan ya yiwa Baba d’azu akan wai su Baba Habu sun kawo k’arar ku ne akan dukan da kukayi wa Yusuf…so considering that
Uncle zai siye nan d’akin da band’akin da d’an filin baya wanda yake mallakin ku sai ku tashi a gidan’’

Cikin fushi
Manubiya tace’’ashe kuwa da sun tabbata mahaukata,mu bamu yi magana akan abunda shi Yusuf d’in yayi ba
sai shi me uba ??’’

Ciki fushi Baba yace
‘’Manubiya bana son shirme fa,ai kamata yayi ace da kuka zargi yayi wani abun da sai ku tuntub’eni ku ji asalin bayani bawai ku rufe shi da duka sai kace wasu tab’ab’u ba!
Yusuf d’in d’anku ne da za ku d’aga hannu ku dakeshi??
baya ga haka ma ai sai da na gayawa Musbahu k……’’

Cikin fad’a fad’a ya juya ya kalli ya Musbah yace
‘’Lokacin da ka zo ka same su ba ka gaya musu taimakon da Yusuf d’in yayi min ba??
shine ka biye musu kuka dake sa??.Har yau yana asibiti
kuma Baba Habu yace duk mu za mu biya kud’in jinyar sa.’’


Tsabar takaici Manubiya bata san lokacin da ta fashe da kuka ba,cikin kuka tace
‘’Baba yaudarar ka ma fa yayi!
cutar ka yayi! takardun da ya baka ka sa hannu ba abun da ya fad’a maka ne rubuce a jiki ba!.Baka ga black snake ya zo ba?me ya had’o ka da shi tou tunda shi Yusuf d’in cewa yayi banki ne’’


Cikin fushi Baba yace
‘’Ko da ace ban yi karatu ba
nasan abunda yake a rubuce a jikin takardar nan tunda nasan
Yusuf ba zai cutar da ni ya had’ani da wannan mugun mutumin ba.
Shi kansa Yusuf d’in yanzu haka a cikin danger yake.
Shi wannan black snake d’in shi ne ya had’a da ni da shi gaba d’aya ya biyo mana ta k’ark’ashin k’asa’’


‘’To tayaya akayi shi Yusuf d’in ya san mutum irin….’’.
Maficin da Baba ya jeho mata ne yasa ta yin shiru….cikin fad’a sosai yace
‘’Ungo naki’’ya fad’i hakan yana yi mata dak’uwa kafin ya d’aura da cewa’’ina fad’a kina fad’ace miki akayi ban san me nakeyi ba??’’


Ya Musbah ta kalla wanda taga ya na yi mata alamun ta yi shiru kawai ta hanyar
d’aura yatsunsa a kan bakin sa.

Kuka kawai ta fashe da shi tsabar takaici da bak’in ciki hakanan ta yi shiru
Baba ya balbaleta ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba kafin daga k’arshe ya tashi ya fita.
Bai ma san ta ina zai fara ba
gashi Uncle yace
‘’Idan ya k’i yarda ya siyar da d’akin nashi da filin cikin sauk’i zai sako hukuma ya fad’i abunda y’ay’ansa sukayi’’.Saboda Allah ta ya zasu yi masa haka taya za su tsame sa a cikin gidan besides ta Ina ma zai fara neman wani d’akin a wannan d’an kud’in da suka ambata za su siye d’akin.
Yana fita direct masallaci ya nufa ya ci sa’a kuwa babu kowa a ciki….tun tasowar su su Uncle ba su tab’a yi masa abunda ya ji zafinsa kamar na yau ba,wato sun nuna cewa su uwarsu d’aya kenan
shine bare a cikin su
abunda ba su tab’a yi ba kenan.
In ba haka sukeson nunawa ba
ta ya za a yi case da Yusuf d’an gidan Baba Habu wanda yake kamar d’a a tsakanin su su duka ukun
abunda ya kamata ace su yi sulhu a tsakanin su gyara
amman ace wai Uncle ya shigar wa Baba Habu!
Wannan wanne irin nuna banbanci!wulak’anci! da cin fuska ne……!.
Duk yadda Baba ya so daurewa kasawa yayi
bai san lokacin da ya fashe da wani irin kuka ba……



Baba yana fita su ya Nafi’u ma suka mik’e suka fita aka bar Manubiya Inna Jidda da Muhsin
Jidda gaba d’aya ta yi laushi dan gani takeyi kmr duk laifinta ne shiyasa ta ma kasa lallashin Manubiyan dan ita ba ma ta san me zata yi ba kuka ko ihu!,da kyar ta lallab’a ta iya mik’ewa ta je ta kwanta a gefen inna ta yi shiruuu.
Sun jima a haka kafin Manu ta tashi ta fita dan azahar har ta yi.
A kithchen d’in ta zauna tunda ta fara girkin har ta gama sam ba ta damu da hayak’in ba
sai da ta gama tukunna ta juye a kula ta koma d’akin.

Hakanan gidan ya kasance jigum mai sunan baba ne kawai yaketa faman tsalle tallen sa.

Ya Nafi’u da ya Musbah kuwa ba su zauna ba har dare,duk
inda suka je it’s either a lissafo musu uban kud’i ace su nemi lawyer ko kuma tashi d’aya ana ganinsu ma
ace su yi hkr kawai dan ansan ba iya wa za su yi ba.

Manubiya ma sai dare tukunna ta d’auki wayarta ba ta yi mamakin ganin misscalls kusan takwas duk na Yashjub ba dan tunda ta dawo bata bi takan wayar ba kuma tun jiya lokacin da ya ce zai kira ta after thirty minutes ta saka wayar a silent gudun kar ta tashi su Baba.

Bataso ta kira sa dan kunya takeji amman haka ta daure ta danna call tana sauk’e numfashi a hankali a hankali.
Har ta katse bai d’auka ba dama addua takeyi kar ya dauka d’in saboda na flashing ne kawai da ita tasan yana d’auka zai katse.

Tana kashe wa kuwa immediately ya biyo kiran ahankali ta d’auka ta kara a kunnen ta bakinta d’auke da sallama …….……..bayan kamar awa biyu Jidda ta fito ta zauna a gefen ta ta na yi mata nuni da alamun lokaci.

Jinjina kai ta yi kafin ta zaro wayar
ta d’an kalli screen d’in,ba k’aramin mamaki ta yi ba da ta ga har sun wuce awa biyu suna wayar dan haka ta fara yi masa sallama,
Da kyar kuwa ya hak’ura ya kashe bayan tace masa bacci take ji sosai……


Murmushi Jidda ta yi bayan Manubiya ta kashe wayar cikin d’an sigar tsokana ta kalle ta tace’’yau ansha till down,dama gani na yi tun d’azu Baba yana zaune kar ya fara tambayar ki shiyasa.Dan naga kamar kun manta da kowa a duniyar sai faman I love u ilove you ake…’’

Toshe mata baki Manubiya ta yi tana d’an hararar ta kafin ta ce’’ba wani I love you kusan ma duk labarin ku ke da Muhsin nake ta basa’’

Ahankali Jidda tace ‘’amman dai zuwa yanzu ke kan ki na san kin yarda son ki yake yi ko?’’

Ahankali Manubiya ta d’an gyara zama ta kalli Jidda tun d’azu basu samu sun zauna hankalinsu ya dawo jikinsu ba Shiyasa bata gaya mata komai ba, sai yanzu ne da ta d’an ga walwala a fuskar Jidda yasanya itama ta samu kwarin guiwar zaiyyane mata yadda sukayi ita da Yashjub d’azu da safe…..tiryan tiryan haka ta bata labari kafin ta d’aura da cewa‘’yanzu ma muna fara waya yace wai yanaso zai kira ya Musbah a fara magana,ba yadda ban yi da shi ba amman ya dage wai gobe da safe inshaaAllah zai kira sa’’

Dariya Jidda ta yi kafin tace’’to da farko dai ‘Alhamdulillah’wallahi na ji dad’i sosai saboda kun dace,abu na biyu kuma shi wannan bawan Allah haka ake yi?irin wnnan zumud’i haka?ke da baki riga kin ce masa ‘eh’ ba ma
saurin me yake yi?’’

D’an turo baki Manu ta yi kafin tace’’ Nima dai abunda na gani kenan’’

Dariya ce take ciyo Jidda ganin yadda Manubiyan take so ta yi mata basaja k’iri k’iri
Dan haka tace’’to kawai ki fito ki gaya masa gaskiya mana,ki ce masa kawai bakya son shi’’

Da sauri Manu ta d’ago ta kalle ta ganin yadda Jiddan take guntse baki tana dariya k’asa k’asa ne ya sanya ta fahimci jan magana Jiddan take yi dan haka ta kai mata dukan wasa tace’’ja’ira’’

Ahankali Jiddan ta matso ta rungume Manubiya tukunna tace’’Ba sai kin fad’a min ba Adda Manu kema nasan kina son shi tun ba yau ba,Ina miki addu’ar Allah ubangiji ya tabbatar da alkhairi sannan ya dauwwamar da farin ciki a rayuwar ku ya tabbatar da aurenku ya sa kar a samu matsalar komai.’’

Ahankali Manubiya ta sa hannu itama ta rungumo k’anwar tata tana mai jin tsananin tausayin ta yana ratsata…..ba dan Ammi ce mahaifiyar Al’ameen ba da ba abunda zai hanata tsayawa tsayin daka har sai ta ga Jidda ta auri Al’ameen,dan ta san yadda Jidda take son Al’ameen tun kafin ta yi wayo shiyasa take tsananin jin tausayin ta dan soyayyar da ta ke yiwa Yashjub ta sanyata ta sake fahimtar yadda Jidda ta ji a lokacin da aka rabata da Al’amee,dan tabbas in da ace itace wani yayi gigin rabata da Yashjub da batasan ya zata yi ba,da wuya idan bata rasa ranta ba.

A hankali ta zaro Jidda daga jikinta cikin lallashi da bada baki ta shiga kwantar mata da hankali tare da yi mata addu’ar Allah ya bata wnada zata so sama da al’ameen wanda zai so ta shima tsakani da Allah.
Sun jima Sosai a wajen suna kwantarwa da juna hankali tare da bada shawarwari kafin su mik’e suka shiga d’aki.


Sai da kowa yayi bacci tukunna Manubiya ta yi. Tunanin ta ya karkata ga Abbakar wanda tun ranar da suka bar asibiti ya daina d’aukar wayarta baya kiranta
gashi su Baba sun hanata zuwa ta dubosa,su ya Nafi’u dai sun koma duba shi dukda kuwa abunda mahaifiyar sa ta yi hakan bai hanasu zuwa ba
amma ita sun ce ba zata je ba.

Ta d’an ji haushin abunda yayi mata dan bata yi tunanin zai
d’auke mata wuta lokaci d’aya haka ba duk da ta san dama dole mahaifiyar sa za ta kora masa warning a kanta amman bata yi expecting wannan d’aukewar d’iff d’in daga garesa ba amma kuma da ta tuna daraja irinta uwa sai ta goge duk wani takaicinshi a ranta.

Tabbas ta san za ta yi misssing Abbakar he’s her only friend amman tunda haka shi da mahaifiyarshi suka tsara ba komai
za ta jure
Allah yasa hakan ne mafi alkhairi.
tana wannan tunanin itama ta ja abin rufa ta yi luff sai kuma ta fara tunanin Yash kafin ta
fara karatun Al’kurani ahankali ahankali a cikin ranta
daganan bacci yayi awon wgaba da ita….

A b’angaren Abbakar kuwa
dama tun kafin ya farka mahaifiyar sa da maman Baraka suka gama had’a plan d’in su…….yana farkawa kuwa ko likita ba su kira ya duba shi ba suka shirga masa k’aryar’’ai Manubiya ta yi aure Baban ta ya aurar da ita a wani mutum yanzunnan aka gama d’aura auren a cikin asibitin.’’
Tashi d’aya Abbakar ya amince kuma tunanin sa ya bashi ai Yashjub aka aurawa Manubiya watak’il ya zo ya taimakesu Baba kuma ya ji dad’in taimakon da ya zo yayi musu shi ne ya ba sa Manubiya.

Shiyasa gaba d’aya hankalin sa ya tashi tashi d’aya ya birkice musu ita kanta mahaifiyar ta sa sai da ta tsorata……abu d’aya da yayi danasani shine farkawar da yayi!he wish black snake a k’irji ko ciki ko kai ya harbesa
ya san babu kyau amma a ranar ji yayi ina ma ya wuce lahira kawai Ina ma bai tashi ba.
Tun daga ranar kuwa ya daina magana sam maman nashi ta kasa gane kanshi
Iyakar shi ya bud’e ido yaci abinci tayi mishi alwala yayi sallah ba um ba um um
Kuma doctor ya tabbatar mata he’s totally fine.

So yake kawai a sallameshi
ya je ya nemi transfer ya yi
nesa da garin Kano first,daganan sai ya san abun yi dan a yanzu kam ya san
Manubiya ta yi masa nisa shi kuma ba zai iya jurar ganinta da kowa ba.

Amman fa in akwai abu d’aya da ya sani shine zai yi duk yadda zai yi bai damu ba ko ya’ya goma ta haifa
yana nan dawowa dan ba’a haifi mutumin da zai barwa Manubiya ba……..





MANNUBIYA
48
Na
Humayrah Bulama

Mikiya Writers Association.

Kamar kullum yau ma tun da Yashjub yayi sallar asubah bai
koma bacci ba,yana gama azkar da karatun Alk’urani ya hau aikin Yassir wanda yake so ya kammala a yau inshaaAllah
yana cikin aikin Najeeb ya kira sa dama yanata tsammanin sa tun jiya yace masa zasuyi waya da hajiya mama in sun gama zai kira sa amman ya ji shiruu…….
Ba k’aramin dad’i Yashjub ya ji ba da Najeeb d’in yace masa ‘’ai hajiya mama ta amince 💯,tana ta murna kuma tace za ta yi magana da Daddy shima Yash d’in ya je ya same sa su yi magana ana gama bincike sai maganar aure inshaaAllah’’kuma itama ta nuna bata so ma a d’au lokaci me tsayi’’.


Tashi d’aya wani kalar farin ciki ya lullub’e Yash ya ma kasa b’oye murnar sa har sai da Najeeb d’in ya tusa shi a gaba da tsokana tukunna ya d’an sassauta yayi masa godiya sukayi sallama.

Sai da ya shirya shirin office tsaf tukunna ya d’au waya ya kira ya Musbah dan baya so
yayi masa kiran asubah ya saka shi a al’ajabi amma dukda haka sai da ya Musbah yayi mamakin ganin kiran Yash d’in k’arfe 7:48.

Ba maganar b’oye b’oye bayan sun gaisa ya sanar da shi
shifa Manubiya yake so yana so ya samu Baba yayi mishi maganar zai turo magabatansa.

Ba k’aramin shock ya Musbah ya shiga ba amman kawai sai ya bar Yashjub d’in akan in sun tattauna da Baban duk yadda suka yi zai sanar ma sa ….

Yashjub yaji dad’in yadda ya Musbah yayi masa tabbas ya hango silver lining
dan haka ya fara shirya samun Daddy kawai
ta yadda in sun ce ya turo ba sai ya tsaya k’umbiya k’umbiya ba,dukda yasan tsakanin a jiya ko yau dole Daddy zai ji maganar daga wajen hajiya mama but still shima ya kamata ya d’an cire kunya ya same sa.

A b’angaren ya Musbah kuwa
Yasan ya cewa Yashjub zai yi magana da Baba amman fa a asalin gaskiya shi ba zai yi magana da Baba ba har sai ya ji ta bakin Manubiya sannan ya gama bincike tare da deciding abunda ya kamata ayi tukunna. Dan a yadda Baba yake kwana biyun nan tsaf zai iya cewa Yashjub yazo a d’aura masa auren Manubiya ba tare da anyi kwak’kwaran bincike ba.

Sai da yayiwa me sunan Baba wanka ya shirya sa shima ya yi wanka ya shirya suka karya tukunna suka fita suka nufi gida da niyyar in sun gama tattaunawa da Manubiya zai d’auki Jidda ta zo ta gyara masa gidan dan yayi datti a cikin kwana biyu kacal kyankyamin koina yake yi.

Inna da Jidda ya samu kawai a dak’in
Jidda tana ganinsa tace ta gaida shi ya amsa tukunna tace’’dan Allah ga inna nan,bari inje nan baya in aro wani littafi da na tab’a gani a wajen su mami kwanaki gobe post utme,inaso in duba sosai.’’

‘’To’’kawai yace da ita daganan suka zauna shi da me sunan baba a gefen innar suka shiga gaida ita.

Ba su yi minti biyu da zama ba Manubiya ta shigo cikin d’akin da laida a hannunta ta siyo omo da maggi

Kallonta yayi ya kalli laidar kafin yace ‘’meyasa ba ki aiki Muhsin ba??’’
Sai da ta zauna ta gaida shi ya amsa tukunna tace’’ai ya tafi islamiyyar safe’’

‘’oh haka fa,na manta’’
ya Musbah ya fad’i hakan kafin ya d’aura da cewa’’ke kika bawa Yashjub damar ya kirani?’’

Diriricewa ta yi ga wata kunya da ta lullub’e ta ta shi d’aya a ranta tace’’wato har ya kira shi?,
wai zumud’in Yashjub yake yi ne har haka?’’
Ta yiwa kanta tambayar ba tare da ta san wa zai bata amsa ba.
‘’Kin yi shiru!!’’
d’in da ya Musbah yace mata ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ya lula,ahankali ta jin jina kai alamun’’Eh!’’.

‘’Kin san akan maganar me ya kira ni?’’
Ya sake jeho mata tambayar.

Sunkuyar da kanta ta kuma yi kmr wuyanta zai karye kafin tace’’Eh!!’’ahankali.

Shiruu ya Musbah yayi kawai yana kallon ta kafin cikin fad’a sosai yace’’kuma amma shine kika basa go ahead?kin shirya kenan kema ko?so kike a aurar da ke da wuri?ba ki san mutun ba ba ki san daga ina ya fito ba ba ayi bincike ba shine har zaki ce ya kira ni ayi maganar aure? Yaushe har kika san shi yaushe ma kuka fara soyayyar da har kuka fahimci juna wanda yasa kika samu kwarin guiwar ce masa ya kira ni akan maganar aure???daga yace miki ilove you sau d’aya zuwa biyu shikenan har kin aminta dashi ??
Tou bari ki ji abunda baki sani ba!dama Baba so yake ya aurar da ku da wurwuri,tun a asibiti ya riga ya gama yankewa kuma ya fad’a mana,kinga in kika yiwa kanki
kika bari Baba ya ji wannan zancen ba tare da anyi wani cikakken bincike akan Yashjub ba tou ina tabbatar miki ko
sati biyu ba za ‘a rufa ba za ki ganki a gidan Yashjub a matsayin mata Wallahi!

,dan haka Baba ya tsara.’’

Motsin da ya ji ne ya sanya shi d’aga kai ya kalli bak’in k’ofar toilet,ba k’aramin bugawa k’irjin shi yayi ba sakamakon had’a ido da sukayi da Baba wanda ya fito a wanka.In’i’na ya Musbah ya fara yana shirin yin magana Baba ya kalli Manubiya yace ki ‘’ki ba sa number ta ki ce nace ya kirani’’. Yana gama fad’in haka ya wuce yana d’ingishi yana tafiya dakyar ya fice
dan kamar gyambo haka yake jin y’an yatsun sa ba k’aramin zugi suke yi masa ba.

Yana fita ya Musbah yace ‘’innalillahi wa inna ilaihirrajiun’’
Yasan halin Baba ya san waye Baba ya san in ya saka kanshi abu babu wanda ya Isa ya hana shi.
Babban tashin hankalinsa kar aje Yashjub yana da wani mugun hali wanda ba a san da shi ba su je su aura masa Manubiya
Har gara Baraka da ya Yusuf Allah ya rufa asiri
in sukayi abu za a iya hukuntasu aci ubansu,
wannan Yashjub d’in yanda yake da arzik’i Ina su Ina yin rigima da shi……


Ahankali Manubiya tace
‘’Ya Musbah cewa fa yayi kawai….’’

Wani uban tsaki ya ja,ba tare da ya kalli inda take ba ya mik’e ya fice ranshi a mugun b’ace.

Sai da Jidda tayi da gaske bayan dawowar ta,tukunna Manubiya ta yarda ta turawa Yashjub number Baba ta ce ‘’ya kirashi number Baba ne,’’
Already dama yanada number dan haka yace mata’’ai yanada ita dama izini kawai yake jira dan haka ya gode’’haka nan ya yi ta murna kamar wanda aka yi wa albishir da gidan aljannah,kafin daga baya suka yi sallama gaba d’aya jikinta babu kuzari.
Saboda itama sai yanzu ta fara data sanin basa go ahead da ta yi da wuri haka..shikenan
zai raina ta tun yanzu zai ga kamar tana neman kai da kanta,ga kuma abunda ya Musbah ya gaya mata wanda gaba d’aya ya d’aga mata hankali…..

Atake a lokacin ba b’ata lokaci ya kira Baba.
Sai da Baba ya sake yi masa godiya tukunna suka fara tattaunawa
Baba da so yayi suyi magana a waya kawai amman Yashjub d’in yak’i amincewa a ranar suka zo da shi da Najeeb suka had’u a masallaci ya amsa tambayoyin Baba.
Daganan Baba ya nemi da ya tura masa da adress d’in sa,yace‘’inshaaAllah bayan kwana biyu za su neme sa.

Ba abunda yafi b’atawa ya Musbah rai irin yadda Baba ya sake d’aura masa alhakin yin bincike akan Yash kuma ya hura masa wuta ko d’aga kafa babu
ko duba halin da suke a ciki ma bai yi ba.

A b’angren Baba kuwa babu abunda zai iya shiga tsakanin sa da maganar Yash da Manubiya dan har ga Allah yayi farin ciki matuka da ya ji Yash d’in yanason Manu
ba wai kwad’ayi ko wani abun ba kawai dai ya san in Manubiya ta auri Yash hatta Jidda zata zama safe daga sharrin black snake
Tun jiya da suka samu matsala da su Baba Habu hankalinsa yake a tashe dan ya san auren Jiddan da yake gani tana da miji a hannu ba mai yiwuwa baneba
Shiyasa gaba d’aya hankalin sa ya sake tashi sai gashi da ikon Allah Allah ya kawo Yashjub…..in dai aka yi bincike yaji komai daidai akan sa to inshaaAllah a cikin sati biyu kmr yadda ya fad’a zai aura masa ita.


A cikin kwana biyu ya Musbah yayi bincike ya gama,ya so yak’i gayawa Baba
Amman sai ya Nafi’u yayi mishi nasiha yace’’ka kalli komai da kyakykyawar fuska kar ka yi
mummunar zato mu bi komai da addua tunda bamu Isa mu hana Baba yin abunda yayi niyya ba,uwa uba idan Ubangiji ya riga ya rubuta matar sa ce to fa ba mu Isa mu hana ba’’

Kamar ya Musbah zai fashe da kuka yace’’Nafi’u ba fa anan ya girma ba
taya za ayi amfani da shaidar da aka bayar akansa anan Nigeria??’’

Nasiha da fahimtar wa sosai ya Nafi’u yayi masa sannan ya masa nuni da rashin son tsananta bincike kafin ya k’are da cewa’’mu bi komai da addua za a ga alkhairi inshaaAllah’’.

Ya Musbah bai iya gayawa Baba komai ba
Ya Nafi’u ne ya same sa yayi mishi bayani.

Sai washegari tukunna Baba yana shirin kiran Yashjub d’in shi ya kira sa.
Dan shi Yashjub har ga Allah ya k’agu,abu har kwana uku sun ce za su neme sa amma har yanzu shiru…ya san ba shi da wani mummunan hali amman he can’t help but to feel nervous.

Dukda ya san za a ga zumud’in sa amman shi fa akan Manubiya aga komai ma bai damu ba.
………Bayan doguwar gaisuwa da tambayar Baba ya jiki da jikin inna kuma sai kuma ya hau kame kame.
Murmushi Baba yayi yana yaba yanda Yashjub d’in ya ke son Manubiya shifa tun lokacin da aka bata aiki dama ya fara tunanin wani abun
Shi a zaton sa ma sir Najeeb d’in ne sai da yaga Yashjub da yanda yayi lokacin da ya ga black snake rik’e da hannunta tukunna ya tabbatar Yashjub d’in ne.

Cike da kamala Baba yace’’yanzu nake shirin kiranka’’

Sai da Yashjub ya d’an sosa k’eya tukunna yace’’to Bara inzo yanzun Baba’’…kamar wachchar ranar Baba so yayi kawai su gama a waya tunda ba wata magana mai tsaho bace ba amman sai Yash d’in ya dage akan yana so ya zo d’in….bayan kamar mintina goma sai ga shi,a masallaci yau ma suka sauk’e sa Baba ya so ace su Uncle sun d’an shiga maganar amman ko da ya je musu ma ko kallo bai ishe su ba dan gaba suke yi da shi k’iri k’iri dan haka suka tari Yashjub iya su uku,Baba Ya Nafi’u da Ya Musbah.

Cike da fahimtar juna Baban yace ‘’zuwa ko yaushe ya turo!
In ta shi ne yanaso ayi a cikin sati biyu amman ko yaushe suka shirya sai su fad’i lokacin da suka ga ya fi musu’’


Godiya da murnar Yashjub saida ta bawa Baba dariya dan kasa b’oyuwa ta yi,especially da ya ji Baba ya ce a cikin sati biyu!abun yayi masa dad’i matuk’a,shiyasa farin cikin sa ya kasa b’oyewa haka yai ta murmushi bayan yayi godiya
kafin daga baya suka yiwa juna sallama tare da fatan alkhairi,ya wuce.

Washe gari …..

Yau ya shirya samun Daddy
jiya kwana yayi yana sallah yau ma sai addu’o’i yake yi
tare da addua’ar Allah kar ya sa a samu matsala ta ko Ina,ya san tun da har hajiya mama ta amince to a rubuce yake Daddy ma ya amince,dan ko jiya sai da ta kira sa suka yi magana,kawai dama shi addu’ar sa Allah yasa su yarda ayi a cikin 2 weeks d’in sannan Allah ya

Please Login or Register in order to submit comment