Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

lokacin zuwan Al’ameen yayi
ta rasa yadda zata yi ta fita,
saida innar tayi bacci tukunna ta samu ta fita tana ta sauri.
A cikin mota ta same sa ya na ta jiran ta

Ba tare da b’ata lokaci ba tace ‘’ya zo suje d’akin
Adda Manu bata nan yau,ta bar Inna ita kad’ai’’

Murmushi yayi
Daganan ya fito suka jera suka nufi d’akin gwanin ban sha’awa.

Sun jima kuwa suna hira
tukunna yayi mata sallama ya wuce.

Allah daya taimaki Jidda sam Ya Yusuf bai had’u da Al’ameen ba dan tana dawo wa daga raka Al’ameen d’in ta tarar da shi a d’akin
ko waye yayi ma sa kwatance,sai Allah .

Tunda ta shigo ta gan sa ta tamke fuska,daga gaisuwa bata yarda sunyi wata hirar kirki ba.

Ita sai da ya fad’a mata ma tukunna ta gane
wai ashe fushi yayi tun ranar data gudu
shiyasa yak’i zuwa ya duba Innar sai yanzu ….

Ganin dai duk yadda yayi fad’a fushi da lallashi sam ya gagara samun fuska a wajen Jiddan ne ya sanya kawai ya tashi ya tafi dan ya riga ya gama tsara yadda zaiyi da ita next tunda ya lura bata san a bita ta sauk’i ba,katamau haka ya tamke fuskar nan ya fice bayan ya ajjiye musu dubu d’aya akan gadon, wai su sayi abun da basu da shi…..





MANNUBIYA
10
Na
Humayrah Bulama

ELEGANT Online Writers

Ko da Baba ya koma gida da daddare sai da Manubiya ta sake r’ok’on sa akan ya barta taje asibitin washegari amman furr yak’i amince wa illa yace’’tayi karatu ta dinga zuwa makaranta akai
akai, kawai.

Da asubah ta tashi ta shirya musu breakfast har lunch tace Muhsin ya d’umama miyar in an zo kaiwa daganan ta wuce makaranta saboda tana so suyi karatu da Abbakar yau sosai,gashi lecture d’in sir Najeeb gare su da sassafe shiyasa take ta sauri saboda ta san baya bari a shiga muddin ya riga ya shiga.Duk saurin ta kuwa sai da tayi
rashin sa’a domin ta na karya kwanar inda k’ofar tafkeken hall d’in ya ke ta hango sa yana shiga dan haka ta k’ara sauri sai dai duk saurin ta kafin ma ta k’arasa bakin k’ofar har ya rufe.
Haka nan ita da ragowar d’aliban da su ka yi letti suka ja suka tsaya a bakin k’ofar hall d’in dan waata k’ila in sun ci sa’ar sa
In ya fito ya karb’a sunayen su da Matrc number ya basu ko da maki half half ne.
3 hours ne lecture d’in kuma sir Najeeb d’an ka’ida ne shiyasa sai da ya cike 3 hours d’in sa tsaf tukunna ya fito.Bai yi musu kamar yadda sukayi zato ba dan kamar ma ran sa a b’ace yake daya fito d’in
saboda ya had’e girar sama data k’asa fuskar nan tamau kamar bai tab’a dariya ba,
shiyasa kowa yasha jinin jikin sa.

Koda wani a cikin su yaje yana k’ok’arin gaya masa uzurin sa
ma,a take ya daka ma sa tsawa
Dan haka duk sai suka sake rud’e wa,kowa yaja ya yi tsit suna ganin sa ya wuce ya tunkari parking lot.

Har ya nufi inda yayi parking motar sa sai kuma ya juyo,dan in dai ba gizo tayi ma sa ba tou yarinyar dayake nema ya hango a cikin dandazon y’an letti.
Ya na juyawa kuwa su ka yi ido biyu dan itanma bayan sa ta raka da harara saboda ba kad’an ba taji haushin tsawar daya dakawa wannan wanda yazo zai ba sa uzuri,Sosai .
Da sauri ta sunkuyar da kanta k’asa tana adduar Allah yasa bai fahimci hararar sa take yi ba.

‘’Manubiya musa,follow me’’
Ya fad’a ba tare daya damu taji ko bata ji ba haka ya sa kai ya wuce ya shiga motar sa yaja ya nufi building d’in da office d’in sa yake,a nan cikin buk d’in.
Bata ji d’in ba kuwa ragowar mutanen da suke wajen ne suka ce mata ‘’yace ta bi sa’’.
A take kuwa ta rud’e dan laifi a makaranta wanda zai janyo su Baba su sake yin fushi da ita is the last thing da take tunanin za tayi involving kanta a ciki.’’
Dan haka ta gama yanke shawarar tana zuwa zata durk’usa ta basa hak’uri sannan tace masa
Itafa haka idanuwan ta suke ya yi hak’uri ba hararar sa ta ke yi ba.
Tana shirin barin wajen Abbakar na fito wa da ga hall d’in,kana ganin ta kasan a rikice take a haka ta k’arasa kusa da Abbakar tace
‘’Yauwa Abbakar dan Allah zo muje kayi min shaida,ka cewa Sir Najeeb tun muna yara haka idanu na suke ba harara ce nayi ma sa ba’’.

Kallon ta sosai Abbakar yayi Kafin yace
‘’Cewa yayi ki bi sa?’’

Dasauri tace
‘’Eh,saboda ya kama ni Ina hararar sa’’.

Wata nannuyar ajiyar zuciya Abbakar ya sauk’e kafin yace
‘’Inaa! Ba saboda harara ya ce ki je ba,Manu!yau ni da ke kashin mu ya bushe,ni ma yace min in biyo sa’’.

Za ta yi magana yace
‘’Muje , muje da sauri ke dai kiyi ta addu’a kawai’’.

..Da hanzari suka k’arasa block d’in da office d’in Sir Najeeb yake ba tare da b’ata lokaci ba suka kutsa kai cikin building d’in,Manubiya ba ta san hanyar office d’in ba Abbakar ne ya yi musu jagora.
A corridorn
office d’in sa ne na farko farko dan haka suka k’arasa da hanzari,duk saurin da suke yi sai da suka tsaya suka yi addu’a tukunna Abbakar ya d’aga hannu dakyar ya fara knocking a hankali kamar wanda baya son yi…
Sunfi 5 minutes a bakin k’ofar office d’in idan Abbakar ya d’an buga sai ya tsaya yaji ko za’a basu izinin shiga,
amma shiru.
Badaban sun ga motar sa ba
Kuma yanzu haka ma da suke knocking d’in kamar suna d’an jin murya k’asa k’asa,da sai suce ba ya nan.Sai da suka cire rai knuckles d’in Abbakar har sun fara ciwo,
Tukunna sukaji yace
‘’Come in’’.

Abbakar ne ya d’an murza handle d’in ya fara shiga da sallama,dan Manubiya sai da ta tsaya ta karanto addu’o’in da za su saka zuciyar ta tayi sanyi tukunna ta bi bayan sa ta shiga da sallama itama,
kanta a k’asa.

Ahankali ta lumshe kyawawan idanuwan ta tana me shak’ar kamshin AC, room freshner dana zafafan designer turarurrukan su waenda su ka had’e waje guda suka bada wani zazzafan kamshi,
dama tunda suka shigo ta fahimci kamar ba shi kad’ai bane ba
yanzu kuwa da suka sake bawa iska ajiyar su suka ci gaba da hirar su yasan ya ta tabbatar da
ba shi kad’ai d’in baneba
duk da kuwa har yanzu bata yarda ta kalli direction d’in da table da kujerun da suke zaune a kai yake ba,sam ta rasa dalili
daya sanya ta tsinci kanta da samun faduwar gaba tun farkon shigowar ta cikin office d’in.
Abbakar kuwa ganin computer har uku a kan table d’in nasu
gashi daga gani da shi da Abokin na sa abu mai mahimmanci suke tattaunawa,ne
Ya sanya ya ja bakin sa ya yi shiru gudun kar ya katse su yaje ya yi laifi
Dan tun dazu a rikice yake
Jiya dama tunda maman sa taji ya yiwa Manubiya test taketa faman surutai kuma ta tabbatar ma sa muddin ya janyowa kan sa kora daga makaranta wallahi sai dai ya koma k’auye yayi noma ko yayi aure dan ba zai yiu ace tayi ta kashe kud’i akan karatun sa tun yana k’ank’ani amma ya b’arar a banza sannan a yanxu daya kamata ace taji dad’in karatun nasa yazo ya sake zama mata liability saboda wata Manubiya.
Gaba d’aya ta d’aga masa hankali ta daga wa kanta,dan tun jiya take fad’a Tana sake nanatawa akan muddin aka gano su tou ya tabbata ya shiga case ya gama.
Abbakar yana tsananin son karatu gashi ba k’aramar wahala yasha ba kafin finally ya samu gurbi ya ci gaba da karatun na sa,shiyasa tayi nasara wajen rikita sa da kalaman ta..
Ahanakali manubiya ta shiga bin office d’in da kallo a ran ta tace
‘’Aljannar duniya,ina ma za a bata aron nan ta kawo Inna ko shekara d’aya ne tayi ta huta sosai da abinci mai kyau sannan ba hayaniya,ta san tabbas za ta rage wata damuwar.
Ba abunda yafi burge ta da office d’in irin yadda aka ware wajen Hutu daban wajen aiki daban,
Inda suke zaune shida Abokin sa yayi kamar office sai kuma chan gefe wasu lumtsuma lumtsuman sofa ga fridge dispenser tv da center table kamar wani parlourn amarya ….
‘’You Guys Are Very Stupid,
GET OUT !!!!!’’
Su kaji muryar Sir Najeeb ya daka musu tsawa..




MANNUBIYA
1 1
Na
Humayrah Bulama

ELEGANT Online Writers


Tsananin rikici da tsoro ne suka sanya Abbakar durk’ushe wa a wajen ya shiga ba sa hak’uri.
Manubiya kuwa takaici da bak’in ciki ne suka saka ta fashewa da kuka,
Tun farkon zuwan su dama da ya shanyasu a waje takaici ya isheta,daurewa kawai take yi
yanzu kuwa abun na sa ya kaita bango gaskiya.
….Hakuri sosai Abbakar yake ba sa amma sam yak’i ma ya tsaya ya saurare sa,tijara kawai yake zuba ma sa da ihu kamar wani uban sa,ba abun da yafi b’ata wa Manubiya rai irin yadda ya sako iyayen su a lamarin
Ta inda yace ..
‘’..in da mom d’in su ko Dad d’in su suka zo suka gani a wajen ai da za su gaishe su
amma dayake sun raina sa shine suka zo suka tsaya musu kyam aka ko shirin gaida su ma basu da da yake ga sa’annin su, ko ?
To in basu sani ba yau su sani
Malamin ka shima kamar iyayen ka yake in kuma suna da ja,akan maganar sa to su kama hanya su fita shikuma
Ya basu c.o in fact har spill sai sunyi wallahi
In sun isa suje Iyayen su uwa ko uba wani a cikin su ya basu A a course d’in sa……..’’

Kukan da Manubiya ta sake fashewa da shi sai da ya sanya Hatta Sir Najeeb d’in yin shiru

In wani ya zo wucewa ba abun da zai hana yace dukan ta ake yi a cikin office d’in,duk tsura mata ido suka yi suna kallon ta
Banda Yashjub wanda tun lokacin data fara kukan in fact
tun farkon shigowar su ya daina fahimtar Najeeb,yanzu kuwa kukan nata gaba d’aya ya sake dagula masa lissafi,
bai ganta ba dan bai juyo ba
sai dai kuma wani abun mamaki
Iya muryar ta kad’ai ya ji lokacin data yi sallama da kuma sautin kukan ta wanda a yanzu yake ji har cikin ran sa
hakan ne yasan ya sa jin kamr ya tashi yaje kawai ya rarrashe ta
Tun a lokacin data fara kukan
Abbakar ya fahimci takaici da kuma tuno Inna ne suka saka ta kuka.
Sir Najeeb kuwa takaicin ta ne ya sake lullub’e sa,ya lura da yadda ba ta mayi attempting ta ba sa hak’uri ba tun farko yanzu kuma ta cika masa office da koke koke,abun da yace ta daina yi masa a aji shine yau ta kwaso ta kawo masa har office,dan haka a fusace ya zagaye tebur d’in dake a gaban sa ya wuce Yashjub ya nufi inda take kamar wanda zai dake ta.


Cikin hanzari Yashjub ya tashi tsaye ba tare da ya juyo ba ya ruk’o hannun Najeeb da sauri dan already har ya gota sa
‘’Wait pls!’’
Kawai ya iya cewa .
Dga haka ya cika ma sa hannu tukunna ya juyo ya nufi inda Abbakar yake a durk’ushe yace ma sa
‘’Stand up!.’’
Sai da ya lumshe idanuwan sa ya bud’e tukunna yace ‘’ki yi shiru ko ki fita’’ yayi mata maganar ba tare da ya kalle taba.

Da kyar Manubiya ta samu ta share hawayen ta ta shiga sauk’e ajiyar zuciya a jejjere itama har yanzu bata bari sun yi ido biyu ba.
Dasauri abbakar ya mik’e yace
‘’Wallahi , I don’t want to interrupt you ne dats y muka yi shiru dan Allah kuyi hak’uri’’

Kamar ba zai ce komai ba sai kuma kawai ya juya yace
‘’Sir Najeeb ayi musu afuwa mana’’

Shiruu kawai Najeeb yayi ya k’urawa Yashjub ido yana mamakin sa,tun da ya san shi
bai tab’a gani yayi irin haka ba,
lamari wanda ya shafe sa ma
barin wajen yake yi ballantana wannan da bai shafe sa ba,
Shi harga Allah daya ji ya ce ma sa wait pls yayi tunanin so yake ya mik’e ya fita inyaso daga na sa cigaba da hayaniyar su …..
Sai da Najeeb d’in yaga Yashjub d’in ya d’an yi masa murmushi tukunna ya kawar da nazarin daya soma ya d’aga masa kai kawai ya juya ya koma wajen zaman sa ya zauna,
Ya xubawa Abbakar idanu.

Chan kan sofa Yashjub ya koma ya zauna ya tsurawa tV d’in da ba a jone take ba ido.

Da sauri Abbakar gudun kar su sake yin wani laifin yace
‘’Morning !
Sir,ka ce mu biyo ka shine..’’

Cikin katse sa Najeeb ya kalli Manubiya yace
‘’Discuss on Email and Linguistics’’
Dibi dibi ta hau yi kafin kawai tayi bismillah ta rufe idon ta
ahankali tace
‘’Ban iya ba’’.

Cikin fushi yace
‘’Ko kuma dai kin manta,ko?saboda a takardar ki in da ace ban gano yi miki akayi ba
Da tsaf zan baki A.’’

Ahankali gaban ta yana fad’uwa ga b’acin rai tace
‘’Ka yi hak’uri sir,mahaifiya ta ce bata da lafiya tana kwance a asibiti ma yanzu haka
Shiyasa ya yimin,kayi punishing d’ina amman dan Allah ka kyale Abbakar
tausaya min yayi , bashi da laifi dan Allah.’’

Tabbas ya tausaya mata dan ko ba a fad’a ba yasan da gaske take iyakar yanayin yadda kalar idon ta ya chanza da kuma zafafan hawayen da yaga sun zuba ya isa tabbatar masa da gaskiya take fad’a.

Tun yana k’ank’ani mahaifiyar sa ta rasu bayan doguwar jinya amma sam bai manta zafi da ciwon rashin lafiyar mahifiya da rasuwar ta ba,
Hakan yasa ya d’an sauk’o zuciyar sa ta d’an yi sanyi.

Tsit office d’in yayi baka Jin k’arar komai sai na Ac yayin da manubiya take ta faman sauk’e ajiyar zuciya a jejjere,ahankali.
Yashjub yana nan a yadda ya ke tun dazu ya k’urawa waje d’aya ido,k’arar wayar sa ce ta katse wa kowa tunani,
Ahankali ya zaro wayar daga aljihu ganin sunan Daddy ne ya sanya sa mik’ewa ya amsa wayar ya kara a kunnen sa kafin ya nufi k’ofa da dan hanzari cike da k’asaita.
Tun lokacin da Manubiya ta shigo take tsaye a bakin k’ofar har yanzu,ganin da tayi ya mik’e kuma ya nufo ta ne yasa gaba d’aya ta diririce,d’azu ta ji k’arar waya a zaton ta bai amsa ba ko kuma ma maybe ta sir Najeeb ce ya bari akan in sun fita ya amsa sam
Bata lura da wayar data ke a kare a kunnen sa ba dan ba shi take kallo ba kawai dai tana iya ganin Motsin sa ne.

Ganin data yi dai da gaske itan ya nufo ne yasa tayi sauri da k’ok’arin kaucewa dai dai shima ya kauce da niyyar zagaye ta ya bi ta bayan ta ya fice,a tare suka sauk’e ajiyar zuciya saboda d’an kusancin da suka sake samu ya sake dilmiya su a wani yanayi na daban.Sai da Yashjub ya lumshe idanuwan sa ya bud’e tukunna ya sake k’ok’arin kaucewa ya wuce ta inda take da farko, ba tare da ya kalle ta ba yanzu
amman sai akai rashin sa a dan a dai dai wannan lokacin itama ta kauce ta niyyar ba sa hanya a karo na biyu,d’an
taku d’ayan daya yi da niyyar kaucewa kuma sai ya sanya suka matso daff da juna kamar za su yi gware.
Zuwa yanzu Manubiya ta tabbatar fad’uwar gaban da take samu da yadda bugun zuciyar ta ya sauya tun farkon shigowar ta office d’in
ta dalilin wannan bawan Allah n ne
Saboda
The more yana kusanto ta
The more bugun zuciyar ta yake k’aruwa,haka kurum ta tsinci kanta da son kallon fuskar sa dan haka ta d’ago kyawawan idanuwan ta waenda ruwan hawaye,takaici bak’in ciki damuwa da k’unci
Suka cikasu taff..

Ganin sun kusan yin gware a karo na biyu ne ya sanya Yashjub saita kwayar idanun sa a fuskar ta da niyyar ce mata
Ta tsaya shi zai matsa ya wuce ya fita,
Karaff!idanuwan su suka sark’e a cikin na juna.
Sau da numfashin Manubiya ya d’auke na y’an sakannni
tukunna dakyar ta samu ta nemo sa ta dai dai ta sa ya dawo mata dai dai,
A Chan kasan zuciyar ta tace
‘’MashaaAllah!!!!’’

Duk yadda Yashjub yaso ya d’auke idanuwan sa a kanta kasawa yayi,a lokacin in da za a tambaye sa yanayin bakin ta ko hanci hatta ma kalar fatar ta ba lalle ya iya fad’a ba
tsabar yadda zuciyar sa da ruhin sa suka karkata sannan suka dulmiya a cikin kwayar idanun ta……

Kamar irin in mutum yana bacci ya dinga jiyo muryar mutum daga chan nesa ana tashin sa,haka ya fara jiyo muryar Daddy a chan nesa yana cewa
‘’Hello,Yash!Yash!!Yashh!!!!are u with me, kana jina kuwa?’’

Wani bagwaren numfashi ya fesar sannan yayi saurin lumshe idanun sa,ahankali ya sake runtse idanuwan nasa da bai riga ya bud’e ba har yanxu,
da kyar ya had’iye wani abu daya tokare masa mak’oshi
kafin ya sauk’e ajiyar zuciya tukunna yace
‘’Yes!,Daddy’’
daganan ya zagaye ta tukunna ya bud’e idanun sa ya kama handle d’in da sauri ya murza ya fita..


Sai da Abbakar yace’’Manu!’’
tukunna Manubiya ta dawo office d’in, a take kunya da takaici suka lullub’e ta dan tasan tabbas sun lura da irin kallon da ta yiwa wannan bawan Allah da kuma yanda ta k’ame k’am bayan fitar sa.

‘’Hmm’’
Kawai Sir Najeeb yace kafin ya fara magana
‘’Dole zan yi cancelling test d’in ku both of you,sai ku dage a exams.Bai kamata a ce na d’aga muku k’afa har haka ba bayan gashi na kama ku dumu dumu
Amman uzurin ki ya taima ke ku, ku dage a exams sannan ko da wasa karku k’ara yi min wannan shirmen a test ko assignment,in mom d’in ki bata da lafiya kizo kiyi reporting’’.

Dasauri suka had’a baki suka ce
‘‘InshaaAllah,mun gode Sir
Sosai.’’

Ahankali ya jawo computer sa ya fara latsawa
Kafin yace
‘’U can leave’’
Ba tare daya kalle su ba.
………………………






MANNUBIYA
12

Na
Humayrah Bulama

ELEGANT Oline Writers

Tun lokacin da Yashjub ya baro office d’in Najeeb ya rasa nutsuwar sa,har ya k’arasa gida yayi wanka yayi sallah ya nufi side d’in Mommy domin ya Isar mata da sak’on Daddy gaba d’aya hankalin sa yana kan yarinyar da ya gani dazu a office d’in Najeeb.sai da yayi addu’a sosai tukunna ya samu tunanin ta ya bar sa yayi sallah a nutse.

Bai samu Mommy a parlour d’in ta ba dan haka ya wuce d’aki nan ma bata nan har ga Allah kan sa har ya fara ciwo shiyasa ya bi gadon ta ya kwanta shi kad’ai ya yi shiruu.
So yake ya lumshe idanuwan sa ya d’an huta amma baya son yin haka dan yasan yana lumshe su idanuwan wannan yarinyar zai ke gani

Abun takaicin shine ko sunan ta bai sani ba sannan ya san in za’a jere masa mata blindfolded ace ya nuna ta a cikin su sam ba zai iya gano ta ba yasan
bashi da wata alak’a da ita amman kuma sam muryarta da idanuwan ta sun addabi zaman lafiyar sa ya rasa nutsuwa ya kasa yakiceta sam ya rasa sukuni tun dazu daya ganta har kawo yanzu babu dak’ik’ar data wuce baiyi tunanin ta ba.
Sai da yayi da gaske ya had’a da addu’o’i tukunna dazu ta d’an lafa a ran sa ya samu yayi sallah cikin nutsuwa …..

Wani bahagon tsaki yaja ya mike ya zauna a kan gadon
kafin ya zaro waya ya danna kiran Najeeb sai da ta katse ya sake kira da ta kusan katsewa tukunna ya d’auka da sallama,
Ahankali Yashjub ya amsa,
tun kafin yayi k’orafi Najeeb yace
‘’Sorry ina wanka ne yanzun nan fito wa ta naga wayar tana haske’’
Ya k’arashe maganar yana mai shirin ajjiye wayar dan yasan tunda Yashjub d’in yaji haka zai ce ok
Inya shirya ya kira sa kawai.
Har ya maida wayar kan side drawer sai kuma yaga still ba’a kashe ba,shiru ya d’an yi kafin ya sunkuya ya d’auki wayar ya mayar ya kara a kunnen sa
yana tunani a ran sa me yake damun Yashjub haka ko dai family matter ne tun da dama yaga Daddy ya kira sa d’azu kuma tunda ya fita ko sallama bai dawo yayi masa ba kiran sa kawai yayi yace masa ya wuce
It’s very unlike him….

A hankali yaji yashjub d’in yace
‘’Am..Najeeb yaran d’azu ya sunansu?
I mean ,ya sunan ta?’’

Shiruuuu Najeeb d’in yayi ya zaro wayar daga kunnen sa ya kalli sunan da kyau ya tabbatar Yashjub d’in ne sannan ya mayar yad’an tab’e baki ya d’aga gira yana murmushi kad’an kad’an yana jinjina kai alamun yes tukunna yace
‘’Okay!!…’’
sai kuma ya kwashe da dariya.

Da sauri Yashjub wanda dama
tunda yayi masa tambayar yafara jin inama he can take it back yace
‘’Kaji matsalar ka,ko?ba abun da kake tunani bane ba tou she just looks like some one shiyasa inaso inyi confirming
Ita d’in ce ko ba ita bace ba,that’s all.

Cikin son k’ok’arin danne dariyar sa dan ya lura mutumin na sa har ya dan k’ule yace
‘’Maybe ita ce,a ina kasan wacchar d’in?’’

Cikin rashin gaskiya Yash yace ‘’A uk,neighbor d’in mu ce amma gidan nasu gaba d’aya sun dawo Nigeria har ita
Last year’’

‘’Girlfriend??’’
Najeeb ya sake jeho ma sa tambayar yana mamakin yadda Yash d’in ya k’irk’iro k’arya haka tashi guda ya zabga masa.


Cikin d’an d’aga murya
Yashjub yace
I said neighbor ife ifen d’alibai ya kurmantar da kai ne ban sani ba
She’s just our neighbor ka fad’a min sunan ta kawai mu wuce gurin’’
Ya k’arashe maganar tasa a k’age,dan ji yake yi kamar ya shiga ta waya ya zak’ulo sunan ta daga bakin Najeeb d’in.

Ahankali Najeeb yace
‘’Gaskiya ba ita bace ba
Yarinyar daka gani dazu I don’t think tasan ko hanyar airport ma ko last time dakyar tayi registration fa har aka fara exams tana cike crf da k’in yi mata signing ma mukayi
sai da hod yace muyi mata tana da d’an issue tukunna’’

Zuwa yanzu Yashjub ya fara ji kamar ya shiga ta waya ya shak’o Najeeb
Although tashi d’aya ya ji damuwa daga jin labarin nata
amman kuma jan ran da Najeeb yake masa ya gama k’ular dashi dan haka ya kira sunan sa da dakakkiyar murya yace
‘’Najeeb!’’

‘’Na’am,Yash.’’
Najeeb d’in ya amsa

Ya sunan yarinyar dana gani dazu a office d’inka?’’


Sarai dama Najeeb ya gano sa ya fahimci inda ya nufa
Kwana kwanar daya tsaya yi masa ne ta sanya shima yaso ya ja ma sa rai amma jin yanayi sa yasa kawai ya hak’ura
Yasan zai dawo gareshi soon.
Dan haka kawai yace masa
‘’Manubiya Musa’’

Ajiyar zuciyar daya sauk’e saida Najeeb d’in ya ji
dan haka kawai yayi murmushi
Ya na adduar Allah yasa su daidaita dan yasan
in Yashjub ya samu ya auri wadda yake so zai fita daga wannan k’uncin daya d’aurawa kansa k’arfi da yaji ta dalilin miskilanci
Yo miskilanci mana
Inba haka ba
Mutum successful kamar Yashjub ace ba shi da aiki sai yamutse fuska da fushi da rashin hira da dariya da Walwala kullum …………

Yashjub yana gama jin sunan Manubiya yayi sallama da Najeeb ko komawa bai yi ya kwanta ba
Ya hau instagram ya shiga searching Manubiya Musa
dan ya san in yaga pictures dinta complete maybe sai samu yad’an rage damuwa
ya samu ta daina yi masa yawo a ido da kunne
Saidai kuma sam bai samu ba
Shine twitter
Shine
Facebook
Ko ina ya duba amman Sam bai samu ba
Dan ko da ace bai santa ba idanuwan waenda ya ke gani masu irin sunan ta sam ba irin nata bane

Please Login or Register in order to submit comment