Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tana tafiya akan fuskar wayar alamun wanda aka kira ya riga da ya d’auka.
Ganin yadda manubiyn tayi tsit ta zubawa fuskar wayar ido ne
yasa Jidda da Muhsin suka lek’a fuskar wayar suma,cikin zumud’i k’asa k’asa Muhsin yace
‘’Adda Manubiya an d’auka fa ki yi magana mana.’’…..

Ahankali Yashjub ya lumshe idanuwan sa ya rintse pillow d’in daya d’aura akan k’irjin sa yana mai sake tabbatar wa da kanshi
Tabbas ita d’in ce …….





MANNUBIYA
2 1

Na
Humayrah Bulama

Elegant Online Writers.

Earlier..

Zuwan Abokin Daddy,senator Bashir biyu wajen Yahanasu,yau zai yi na uku.
Suna waya sosai da Yahansun sannan suna chatting ta fahimci yana k’aunar ta sosai dan yana nuna mata kuma yana yawan gaya mata.
Itama kuwa ta kamu ba kad’an ba dan hatta Daddy da Mommy da su Yashjub sun fahimci hakan dan har walwala yanzu suka ga tana yi shiyasa
Daddy Mommy da Yash suka duk’ufa da addu’ar’ Allah ubangiji ya tabbatar da auren ta yasa kar a samu matsala a wannan karon’.

Yau tun safe take shirye shirye, k’arfe biyu tana yi ta shiga kitchen ta fara girke girke
dan yace mata yau yana son cin girkin matar sa,saboda already a jiya suka tsayar ita da shi Akan
Next week zai turo a saka rana kamar wata uku haka ayi aure
so yau suka tsayar za su sanar da Daddy.
Tana cikin aikin Munira ta shigo,tana son Yahanasu dan haka ta dage akan sai ta taya ta.Duk y’an gidan they are nice to her duk da basa zama suyi hira especially da Ya’isha wadda take ganin itace sa’ar ta amma kuma babu kyara ba kallon banza tsakanin su iya gaisuwa ne da murmushi daganan kowa ta shige d’akin ta,duk ranar da bata da makaranta takan je d’akin su Yasmeen don su yi hira amma tana zuwa daga gaisuwa suke shareta ko kuma su fara waya tun da ta ga haka itama sai ta ke zama kawai a d’akin ta wani lokacin kuma ta tafi wajen Maman ta ko Yahanasu su yi hira.
Ba laifi suna shiri da Baaba larai da Mommy ma ba wai za’a zauna a yi hira ayi wasa da dariya ba amman dai ana gaisawa cikin mutunta juna da kulawa.
Mutum d’aya ce ta fahimci ta tsane ta a gidan ‘Kausar’ sai ko Yashjub’wanda shima in ta gaida shi dakyar yake amsawa ciki ciki.Kausar d’in kuwa ko ta gaishe ta bata amsawa bata san mai tayi mata ba
amman tabbas ta fahimci ta tsane ta gashi kuma ta lura kamar kaff gidan su Yasira da su Mommy sun fi son ta da k’aunar ta.

Ba yadda Yahanasu bata yi da Munira ba amma ta dage akan sai ta tayata,a cewar ta dama zaman shiru ya isheta kuma ta riga ta gama exams(finals d’in ta)tun last week so bata da abun yi…
4 tana yi taje tayi Sallah ta dawo daga nan ita ma Yahanasu ta tafi domin ta yi Sallah sannan ta shirya bayan ta cewa Munirat d’in in yayi kafin ta dawo ta juye a cooler dan already komai ya kusan kammaluwa.

Sai da Munira ta had’a komai tukunna ta saka masu aikin suka taya ta ta kai parlourn bak’i
Ta kunna burner ta saka turare ta gyaggyara komai sannan ta wuce d’akin yahanasu.
Agaban madubi ta sameta
sanye cikin wata Turkish gown mai tsananin kyau da tsada
kwalli kawai ta sanya wa idanuwan ta sai powder da lipgloss amma ta yi tsananin kyau asalin kyawun siririya kuma kyakkyawar fuskarta ya fito sosai.
Murmushi Munira tayi kafin tace
‘’Adda Yaha,yau in senator ya gan ki sai ya hantsila’’ta fad’i hakan ta na mai k’arasawa cikin d’akin.
Dariya duk sukayi kafin
Yahanasu tana dariya tace ‘’Ba ki da dama wallahi’’.
Suna tsaye Munira tana taya ta rolling wayar Yahanasu ta fara k’ara.
Tun kafin ta d’auki wayar dama ta fahimci shine dan ringing tone d’in sa daban ne.
Tana d’auka kuwa yace mata ya k’araso yana ma parlourn bak’i Kausar ta shigo da shi.

Da sauri suka kammala
Yahanasu ta nufi parlourn bak’i
Munira kuma tayi sama dan itama zafi take ji tana buk’atar ta d’an watsa ruwa..

Ya yaba kwalliyarta da girkin kuwa,sosai haka yayi ta zuba santi.Sai da ya kammala tukunna ya zaro kud’i ya bata yace ga tukuicin girkin ta sannan ya sake zaro wani yace
wannan kuma na masu aikin da suka d’an taya ta da y’an yanke yanke ne .

Tashi d’aya ta ce masa’’Masu aiki wanke wanke kawai suka yi girkin kuma tare suka yi da sister d’in ta Munira y’ar amaryar Daddy.’’

Ya san lokacin da Daddy ya k’ara aure amman basu tab’a had’uwa da amaryar ba,balle y’ar ta sannan haka kurum tun da tace munirat yanayin sa ya chanja.
Haka de suka d’an tab’a hira,
Sai da tazo fita domin taje ta kira masa Daddy dan yana so suyi maganar akan zai turo
tukunna yace ta’’turo mishi Munirat d’in ya bata tukuicin ta sannan su gaisa’’
Da ‘’to’’ta amsa tukunna ta sa kai ta fice.
Har yahanasu ta k’arasa d’akin Munira d’in tana d’an jin ba dad’i musamman da ta tarar da Munirat d’in tayi wanka ta shirya,fuskar ta ba kwalliya amma yarintar ta da kyawun ta sun fito matuk’a dan haka atake sai taji d’an guntun kishi yana taso mata,amma kawai sai ta saka kyakkyawan zato a kyakkyawar zuciyar ta ta tura masa Munirat d’in ita kuma ta wuce wajen Daddy domin ta sanar masa da sak’on Senator Bashir d’in.
Tana fita itama Munira ta d’auki hijabin ta ta zura ta nufi k’asa d’akin bak’in ba dan ran ta yana so ba.

Ahankali ta k’arasa bakin glass door d’in ta yi knocking tukunna ta shiga kan ta a k’asa da sallama
‘’Ashe rai kanga rai’’
Muryar sa ta daki dodon kunnuwan ta.

Dasauri ta d’ago ai kuwa suna yin ido biyu ta juya da sauri zata fita.
Amman sai aka yi rashin sa a ya riga ta zagayawa ya tare hanyar dama tun da yaga ta shigo ya mik’e daga wajen zaman shi ya Isa kusa da ita.

Dasauri yace
‘’Haba Munira after long time no see shine zaki yi min haka kmr kinga wani Aljani ?kin sa yadda na dinga neman ki kuwa ‘’
Already Munira har ta fara kuka dan haka ta d’ago a gigice tace’’Dan girman Allah ka rufa mun asiri,mamana zata iya ganin ka a gidan nan take aure mijin ta kuma shine baban Yahanasu wadda zaka aure’’

Cikin katseta yace ‘’Munirat ai yanzu maganar aure kuma ta tashi tsakanina da Yahanasu sai dai ayi maganar auren mu dake,dan ni ke zan aura yanzu kam.’’

‘’Cin fuskar da zaka yi min kenan ??’’su kaji muryar Daddy a kansu

Wani irin kuka Munirat ta fashe da shi daman abun da take jin tsoro kenan..
Yahanasu ta riga Daddy k’arasawa bakin parlourn yadda yaga tana hawaye
ya san ba k’aramin abu ta ji ba tunda gashi shima iyakar maganganun senator na karshe yaji amma gaba d’aya hankalin sa ya tashi.
Idonshi a kan senator ya k’arasa cikin parlourn
ba tare daya kalli Munirat ba
cikin fushi yace ‘’bamu guri’’

Dasauri ta juya ta fita har da tuntub’e.
A bakin k’ofar suka yi karo da Yahansu tana hawaye tana ganin ta ta juya da sauri ta nufi main parlour ya yin da Munirat d’in ta bi ta da gudu,sai da suka kusa shiga parlourn tukunna ta samu nasarar cafko hannun Yahanasun tana kuka ta shiga bata hak’uri sannan tace ‘’wallahi bata da niyyar cin amanarta ko maza sun k’are bata ga dalilin da zai sanya ra saurari senator Bashir ba’’

Wani kalar murmushin takaici
Yahanasu tayi kafin tace’’karki damu sam ba laifin ki bane ba Munirat in baki sani ba wannan shine aure na 8 da aka so a kulla min yana warware wa sam ban ji haushin ki dan ya ce ke yake so ba kawai dai ina kuka ne sabo da…..
Salatin da Kausar ta rafka ne ya katse su tashi d’aya ta figo hannun Munirat sai da ta kai ta tsakiyar parlourn tukunna
tace
‘’oya oya!
20 minutes kawai zan iya baki
Ki tartare garbage d’in tsummokaran ki ki bar gidan nan tun kafin in yi miki abun da za ki yi regretting haihuwar ki da aka yi’’

Cikin tsananin b’acin rai takaici da kuma tausayin Yahanasu
Da suka had’e waje d’aya
suka tunzura Munirat ta kalli Kausar da idanuwan ta da suka jik’e da hawaye tace
‘’Ai ba ke kika kawo ni gidan ba
ballan tana ki ce zaki koreni’’

Kamar jira Kausar d’in take yi tashi d’aya ta d’aga hannu ta
d’auke Munirat da mari,
dai dai nan Mommy Ummi
da su Yasira suka faara firfitowa sakamokon hayaniyar da suke ji sama sama tana d’an k’ara yawa.

Kallon kaskanci da tsana Kausar tayi mata kafin ta matso daff da ita
Tace
‘’Ko Yasira kin tab’a jin ta gayamin magana anyhow a cikin gidan nan?’’
Da sauri Ummi ta k’araso tace
‘’Kausar mai ya had’aki da k’anwar taki haka?’’

Cikin rashin kunya da tantiranci
ta kalli Ummi sama da k’asa ta watsar sannan ta juya ga mommy data k’araso yanzun tace,
‘’Mommy senator ya ce ya fasa auren Yahanasu munirat zai aura all thanks to abun da ta zuba masa acikin abinci yau’’

Kusan duk a tare Ya‘isha
Yasira Yusra da Yasmeen sukace ‘’watt!’’
Suna zaro ido

‘’Dama tun da naga tanata faman kai kawo a kitchen da sunan taya ta girki na san za a rina in ba haka ba tayaya tashi d’aya zai ce wani ita yake so?kaff y’an matan gidan nan bai ce yana son kowa ba sai ita’’

‘’Ya Isa haka Kausar’’
Ummi ta fad’a cikin d’an tsare gida

‘’Ke saddik’a bai Isa ba,
ko kowa ba zai yi magana ba ni zan yi magana kuma sai in da k’arfi na ya k’are wallahi sai kun warware abun da kuka yi kafin ta bar gidan nan,dan bazamu iya ci gaba da ganin Yahanasu a wannan situation d’in ba’’
Da sauri Yasira ta matso tace ‘’Tabbas nima xan yi magana kuma bayaga haka ma yau in tayi mata aka yi shiru gobe d’aya a cikin mu zata sake yi wa dan haka dole a d’auki mataki’’

Kamar yadda Kausar da Yasira suka ce ta sai Munira ta bar gidan
After ta warware asirin da ta yiwa senator yau ba sai gobe ba haka ma su Ya’isha da Yasmeen da su Yusra suka yi wa Ummi da Munirat chaa chin kashi Kala kala babu kalar wanda ba suyi musu ba …

Ganin rashin kunyar tasu ta yi yawa ne yasa Ummi ta kalli Mommy da Baabaa larai tace
‘’Yanzu sai na ce ku hana su tukunna za ku yi magana??’’

Dai dai nan Daddy ya shigo cikin parlourn ran sa a b’ace da alamun ya sallami Senator ya fita ta k’ofar baya sannan daga gani basu k’ark’e k’alau ba..

Ahankali Mommy tace
‘’Saddik’a situation d’in nan is out of my hand yaran nan sun fi ku gaskiya,
Yahanasu has sufferd a lot a kan irin wannan issue d’in a ko da yaushe in irin haka ta faru mu kanji inama ace munada ikon gyarawa yanzu kuwa muna da iko kinga kuwa ai bamuda abun yi wanda ya wuce mu gyara d’in,
In ba ki duba komai ba ki duba maraici Yahanasu dan Allah kiyi wa Munirat magana a samu a daidai ta komai wallahi
Yarinyar nan tausayi take bani i cann’t bear to see her in pain anymore’’.
Wani sanyi Daddy ya ji a zuciyar sa,in akwai abun da zai iya rantsuwa akai to shine
pure and sincere love d’in da Mommy take yiwa Yahanasu,duk da ta kasance y’ar kishiyar ta kishiyar daya fifita nesa ba kusa ba a sama da ita amma sam Mommy bata kishi ko jin takaicin Yahanasu.

Cikin kai wa iya wuya
Ummi tace
‘’Haba Mommy
Ita kuma munirat d’in ba marainiyar bace? kamar yadda Yahanasu take marainiya haka Munirat ma
Infact maraicin Munirat yafi na Yahanasu tun da ita uba ta rasa’’

Cikin tsananin fushi Daddy yace
Saddik’a……….



Sai da Yashjub ya yi sallah ya yi wanka ya d’an huta tukunna ya d’au makulli ya nufi gidan da Yasir yake.Shi Yasir a tunanin sa ya b’oyewa kowa ne bai san tun lokacin daya saka k’afa ya bar gidan idon Yashjub yake a kan sa,da farko Abuja ya wuce sai last week tukunna ya dawo shi da tawagar y’an matan sa da Abokan sa suka
tare a guest house d’in su d’aya daga cikin Abokanayen na sa suke cin karen su babu babbaka.
Wallahi,ba daban yana jin tausayin Mommy da halin da take ciki kwana biyu ba
sannan shi kan shi yana jin Yasir d’in a ran sa tun da no mattter what d’an uwan sa ne ciki d’aya suka fito,ba dan waennan dalilan ba da tuni ya turawa su Yasir y’an Hisbah
Kuma ya cikawa y’an Hisbahn aljihu ya had’asu da manyan sojoji sun nad’e kaff d’in su tayadda ba uban wanda ya Isa ya amsosu….
Yana zuwa bakin gate d’in tun kafin ya gama mik’a hancin motar sa ga gate d’in wani mutum k’ak’k’arfa sanye da gajeran wando da vest ya taho daga majalisar chan gefe da gudu yana cewa ‘’kai! Kaii!! Kaii!!’’
Sai da yazo
Jikin glass d’in motar ta dai dai inda yake ya d’an buga tukunna Yashjub d’in ya ma lura da shi.
Glass d’in motar ta sa bullet proof ne sannan hankalin sa ya tafi ga lissafin ta yadda zai shiga gidan saboda ya san Yasir da shegen wayo da taka tsantsan ba zai tab’a zama babu security ba..
Sai da ya gama k’arewa
mutumin kallo tukunna ya zuge glass d’in motar ta sa,ya zuba masa dogayen idanuwan sa kawai ba tare da ya ce komai ba.
Cikin girmamawa mutumin yace
‘’Oga ai masu gidan basa nan
sun yi tafiya,sannan ni ban ma sheda ka ba …’’
Dai dai nan wasu samari guda biyu suka k’araso suka saka mutumin a tsakiya fuskar su babu alamar wasa.

Sai da Yashjub ya d’an lumshe idanuwan sa ya bud’e tukunna
ya d’an matso mutumin
yana kallon cikin idon sa yace
‘’Ni yayan Yassir ne na san ka san shi Yasir dake a cikin wannan gidan yanzu haka’’ya yi maganar yana nuni da gidan kafin ya d’aura da cewa ‘’Ban zo ba sai da aka tabbatar min da yana nan yanzu haka.Ka bud’e min ko in kira maka sojoji da y’an Hisbah,
dan in baka barni na shiga ba hankali na ba zai kwanta ba sai na tabbatar nayi maka d’aurin goro.
Amman in ka barni na shiga
zan baka kud’i yanzu ka kama gaban ka dan kar ma su hukuntaka kuma zan hana Yasir nemo ka ya hukuntaka shi kuma Yasir na san zai yi maka tsakani da Abokan sa.

Shiruu mutumin yayi yana
kallon Yashjub
Suturar jikin sa motar sa da kuma yana yin sa kad’ai ya isa ya sanya ka fahimci tabbas kud’i sun zauna sannan ya jik’u a naira,yana lura da yadda Abokan Yasir d’in suke yi masa fadanci saboda duk ya fi su kud’i Ina kuma ga yayan sa,kar yaje garin gadin y’an tsaki ya janyowa kan sa fad’a da giwa..

‘’Ina da abun yi ka tsaida ni’’.
Yashjub ya fad’a yana d’an kallon tsadadden agogon
hannun sa.
Sai da mutumin ya kalli mazan dake a gefe da gefen sa suka yi masa sign da ido tukunna ya kalli Yashjub ya d’an jinjina kan sa alamun amincewa.
‘’Hmmm’’kawai Yashjub yace
yana mai d’an girgiza kan sa daga nan ya d’auko bandir biyu na kud’i ya mik’a masa.
Wani kalar murmushi mutumin yayi shi da samarin biyu daga nan ya sa hannu ya amshe yayi godiya..

A tare su duka ukun suka shiga gidan ta k’aramar k’ofa suka wangale ma sa gate ya shige su kuma suka d’auki ghana most go d’insu dake a d’akin mai gadi suka yi gaba abun su..
Gida ne mai kyau flat babba sosai dan compound d’in zai d’auki motoci kamar 15 haka,sai pool da pool house d’in shi a ta baya.

Flat din kuma daga gani d’akunan ba zasu wuce 5 ba da maybe 2 two parlours da kitchen haka.
Yana yin parking ba tare da b’ata lokaci ba ya bud’e motar ya d’au wayar sa ya fito ya nufi main door d’in gidan.

Tsaki yayi ganin ta a rufe dan haka ya d’an danna bell ya koma gefe ya tsaya.

Budurwar da take parlourn zaune tana kallo ce ta mik’e a ranta tana cewa’’i wonder who that could be’’

Tana zuwa bakin k’ofar ta d’an tsaya ta lek’a,duk da ta y’ar b’ular k’ofar ta gan shi hakan bai hanata ganinin tsananin kyawaun sa ba,jikin ta da hannun ta har rawa suke yi haka ta sa hannu ta bud’e k’ofar cike da zumud’i.Tana bud’ewa ta d’an saita kanta kana ta d’an karkace tana wani irin shu’umin murmushi.

Innnalillahi wa inna ilaihirrajiun
Ya ambata a ran sa a zahiri kuma ya sake tamke fuska yana mai jin kan sa yana tsananin sarawa sanann yana daya sanin zuwa gidan.
Dakyar ya samu ya bangaje ta
ya wuce ciki dan har ta nufo shi tana shirin yin magana.
Ran sa a mugun b’ace haka ya nufi cikin parlourn ya nemi guri ya zauna yana mamakin yadda take yawo a cikin gidan daga ita sai wannan guntuwa sannan shara sharar bathrobe d’in da ko pant d’in ta bata gama rufewa ba sannan in dai idanuwan sa ba gizo suka yi masa ba to tabbas ko bra babu a jikin ta.

Sam ba ta damu da yadda yayi mata da farko ba dan ta riga ta gama rikicewa da ganin sa.
Haka nan ta wuce kitchen ta had’o ma sa juice da cake
ta fito tana rangwad’a ta zo gaban sa ta ajjiye sanann ta koma gefen sa ta zauna daff da shi.

Ba tare daya kalle ta ba yace
‘’Ina Yasir??’’

Cikin sake matso wa kusa da shi tace
‘’Ooh,he’s a little busy at the moment sai dai ka d’an jira shi kad’an but don’t worry I’ll keep
you company’’.
Ta fad’i haka tana mai d’aura hannun ta akan cinyar sa ta fara shafawa tana masa tafiyar tsutsa tana yin sama da kad’an da kad’an.

Tsabar yadda ran sa ya b’aci bai ma san taya akayi ya mik’e tsaye ya zare belt d’in jikin sa ba dan tsintar kan sa kawai
yayi yana kimarta da belt tana ihun ceton rai…Kafin su Yasir su fito har ya farfasa mata jiki,sai da suka yi da gaske
tukunna Yasir,Abokin sa da d’ayar yarinyar da suka fito tare suka iya kwatar budurwar nan a hannun Yashjub wadda zuwa lokacin har ta suma.

Cikin tsananin tashin hankali Yashjub yake yi wa Yassir wani irin kallo daga shi sai boxers haka ma Abokin na sa sai d’ayar yarinyar ita kuma da towel.Wata mahaukaciyar shak’a ya kai wa wuyan Yassir cikin hargagi da hargowa yace
‘’Dan uban ka gay ka zama’’

Sukam wannan budurwa da saurayi sun ga tashin hankali dan yanzu ma dakyar suka iya kwatar wuyan Yassir daga hannun Yashjub.
Dakyar Yasir ya iya cewa ‘’A’a Wallahi ba abun da kake tunani bane ba ka tsaya zan yi maka bayani.’’
Dakyar Yashjub ya iya danne zuciyar da take tunzura sa,da yatsar sa manuniya ya nunawa Yasir k’ofa.Duk hauka,iskanci da rashin kunyar Yassir yana tsananin jin tsoron Yashjub a irin wannan yanayin dan yadda ya tunzura d’in nan abun ba sauk’i ko last month da yayi irin haka a gida hatta Daddy sai da yayi shakkar sa da kyar da mugun kyar aka ci sa a Yahanasu ta samu ta iya lallab’a sa,amma duk da haka yafi wata d’aya a kumbure.

Dakyar yana jin maganar tana harhad’e masa yana ganin dishi dishi ya sake cewa Yasir
‘’Za ka wuce ko sai na baka mamaki?’’

Ahankali Yassir yana d’an d’ari d’ari yace
‘’Na san motar ka babu tint,ka yi hak’uri in shiga in d’auki kaya na pls’’

‘’In tsaya in jira ka kenan??’’
Yayi masa tanbayar yana sake tunkaro shi da idanuwan sa da suka yi jajawur abun tsoro.
Da gudu wannan budurwa da gaba d’aya ta gama tsorata
ta wuce d’akin ta janyo akwatin Yasir ta fito dashi.
Tana fitowa Yashjub kuma ya juya ya fita dan ya fahimci in dai ya sake dam’kar Yassir tou tabbas zai iya kai shi lahira,cikin fushi ya nufi gate d’in gidan ya na jin kamar ya fincike zuciyar sa ya jefar tsabar tafarfasa da azabar da ta keyi..

Da Sauri Yassir ya bud’e akwatin nasa ya zaro jallabiya ya bi bayan Yashjub da mugun gudu yana zuwa ya bud’e motar dan Yashjub har ya kunna yana shirin bata wuta
dan ma ya tsaya wangale gate ne shiyasa yaci sa’ar samun shi amma da tuni ya tafi.
Ko rufe motar Yassir bai yi ba
Yashjub ya figee ta suka fice da guduu da kyar ya iya rufe motar ya zura jallabiyar shi dan mutane har sun d’an fara kallon su duk inda suka bi ………

Hakanan suka k’arasa gidan da ikon Allah saboda tsananin gudun da Yashjub ya tsula Allah ne kawai ya kaisu gidan lafiya.
Tun kafin su k’arasa main door suke jiyo hayaniya daidai suna shiga suka ga Daddy ya daka wa Ummi wata mahaukaciyar tsawa ya nufe ta gadon gadan kamar zai rufeta da duka ……


Cikin fushi yace
‘’Wacce irin mace ce ke ?
Eh ?
Ashe son kan naki har ya kai haka?’’
‘’Yarinya tayi laifi k’iri k’iri kina k’ok’arin b’oyewa?’’
Sai da ya kalle su tukunna ya juya ga Ummi yace
‘’To laifi mana,in ba haka ba da ta je ta ji ya fara mata maganar banza ai kamata yayi ta bar gurin ko ?
A matsayin shi na wanda yayarta za ta aura’’

Yadda yake mata ihu da hargagi da kuma tuhumar Munirat akan abun da bata tab’a tunanin zai yadda ta aikata bane
ya sanya wasu zafafan hawaye zubo mata cikin d’acin zuciya tace’’Daddy tuhumar ta kai ma kakeyi ?wanne kalar asiri ne zai juyar da lissafin mutum mai
kimanin shekarunka a cikin lokaci k’ank’ani haka?’’Cikin b’acin rai da d’acin zuciya ta share hawayen ta kafin ta d’aura da cewa
‘’Maybe sai dai ko irin wanda akayi maka aka juyar da kanka daga gare ni kwana biyu’’.




MANNUBIYA
22

Na
Humayrah Bulama

Elegant Online Writers.

‘’Babu irin wannan a tsarin mu,
ke kan ki kin san inda ace muna irin haka Wallahi da baki Isa shigowa ki taho har da agola cikin gidan nan ba,sannan duk abun da za ki yi ya tsaya a iyaka kanmu amma kar ki kuskura ki sako Mommy’’Cewar Ya’isha.

Cikin jaddada mata Kausar tace
‘’Tabbas dan in dai kika tab’o Mommy to kuwa muna bazamu ji shakkar rama mata ta ko wacce hanya ba,yanzu dai back to business naga alamar so kike yi a rufe case d’in Munira.

Da mamaki Ummi take kallon Daddy wanda sam ya kasa tsawatarwa ya’yan na sa.
Su kansu su Yashjub sun d’an ji
mamakin sa.

Yusra ce ta k’arasa ta juyo da Munirat da take ta faman kuka tace
‘’Munirat tun muna shaidar juna mu da ke….’’
Cikin fushi Munirat d’in ta fincike hannun ta sanann ta katse ta ta hanyar cewa
‘’Kar mu shedi juna daga yau dan Allah ki yi duk abun da kika ga dama ki illatani ta yadda ba ke kad’ai ba kowa ma ba zai sheda ni ba’’

Munirat wai ya ana k’ok’arin gyara abu kina turjewa ne?kin fi kowa baki da zuciya ne?we are all the same anan so kar ki yi tunanin wai ko ana k’ok’arin nuna miki bambanci ne ko waye a cikin sisters d’ina yayi irin abun da kikayi dole irin haka za ‘ayi mata
We all love Yahanasu dan haka ya kamata mu tsaya mu fahimci juna a samu a gyara abun da kike son ki b’ata’’
Yasira tace tana mai k’arasowa inda
Munirat d’in suke tsaye ita da Yusra.

Ta bud’e baki za ta yi magana kenan cikin d’an d’aga murya suka ji Yahanasu tace’’Ya isa haka’’sanann ta k’arasa inda Yasirar take ta sa hannu ta juyo da ita tukunna ta fara magana’’Da ni da ke da kowa duk an san daga ke har Kausar d’in ba ku wani damu da ni ba
Infact har su Ya’isha suma duk ba damuwa suka yi dani ba
Dan haka
na rok’e ku da girman Allah kar kuyi

Please Login or Register in order to submit comment