Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

jini,gashi ya kasa mik’ewa ya tsaya sosai yanata faman rik’e ciki alamun sun dake sa a wajen….


MANNUBIYA
35

Na
Humayrah Bulama

*BARKAN MU DA BABBAR SALLAH,UBANGIJI ALLAH YA KARB’I IBDUNMU YA MAIMAITA MANA.*

Mikiya Writers Association.

Suna wucewa Ya Musbah ya dafe kan sa,ya fi second ashirin a haka tukunna ya d’ago yace
‘’bari in kai Inna gidana,sai in zo mu tafi wajen Baba,
Muhsin dama tun d’azu na mik’a sa gidan Nafi’u.’’

Dasauri Jidda tace ‘’Ya Musbah kar ka je su ganka kai ma namiji su kamaka,a ganina gara ka bari mu mata muje…ba lallai su d’aga maka k’afa ba kaima inaga shiyasa Baba bai nemi ka je d’in ba yace‘mu gudu’!.Ka bari za muje nasan in suka ganmu mata za su tausaya mana su d’aga mishi k’afa.’’

Ajiyar zuciya ya Musbah ya sauk’e yana mai kallon ta yace
‘’D’azu Baban ne suka saka ya kira ni da kanshi.Na ji tsoro tare da firgici mai tsananin a muryar sa,wanne irin d’a zan kasance idan na gudu na barshi a wannan halin saboda in ceci kaina?
Jidda babu inda d’aya a cikinmu zai gudu yaje ko da kuwa za su d’auke ni a matsayin fansar kud’in da Baba yaci ne.
Inna ma zan kaita gidana ne saboda kar a barta ita kad’ai anan,Dan gaba d’aya mu ukun nake so mu tafi tare.’’

Cikin katseshi Manubiya tace
‘’Ya Musbah kasan dai Baraka ba za ta kula da ita ba ko’’.

Ahankali yace ‘’Manu na sani.Yanzu haka Muhsin yana wajen matar Nafi’u,in na kai Inna zan tura mata shi kuma zan ce masa in Inna tana buk’atar wani abun da ya san ba zai iya ba ya je ya kira matar Nafi’u
Ina so mu tafi mu dukan mu mu uku saboda Baba yana buk’atar mu dukkan mu,sannan kinga ni ban iya karatu ba dan haka ba zai yiu in je ni kad’ai ba,
Jidda ba zai yiu muje da ita
kad’ai ba kema kuma ba zai yiu in je dake ke kad’ai mu bar Jidda anan hankalin ta ba zai kwantaba,ni kuma ba zan barka ku tafi iya ku biyu ba.

Ba za mu bar Inna anan ba
kar mu tafi Yusuf ya shiga yayi mata wani abun dan izuwa
yanzu na gama tabbatar wa Yusuf babu abunda ba zai iya aikatawa ba….na Kira Nafi’u yace yana hanya,ku zo mu je mu had’a k’arfi da k’arfi mu hud’un tunda ba mu da wanda zai tsaya mana,na san Allah zai taimakemu shi zai tsaya mana
InshaaAllah
In ma sunk’i yarda su hak’ura ni zan bada kaina a matsayin fansar kud’in ba komai.’’

Shiruu duk sukayi kafin
Manubiya tayi sauri ta wuce
tana share hawayenta tana mai cewa,’’zan jira ku a titi’’.


Ya Nafi’u yana zuwa suka saka inna a motarshi suka kaita gidan Ya Musbah,kana ganinsu ka san suna cikin tsananin tashin hankali Jidda kam in banda hawaye ba abunda takeyi ya Musbah ma da kyar yake iya rik’e kwallar sa,dan basu da tabbacin dawowar tasu…

Baraka tana kitchen ya lek’a ya ce mata ‘’za su je wani waje ga inna nan a d’akin bak’i.’’
Bata ko kalle sa ba ballantana
yayi tunanin zata amsa shi.
Hakanan ya juya ya bar mata kitchen d’in ya samu Muhsin yace masa in yana buk’atar
wani abu yaje ya kira anty Aisha daga haka ya kama hanya ya fito ran sa duk ba dad’i.
Yana zama a cikin motar Nafi’u ya lura da yanayin shi dan haka yace’’in ba zata yarda ba Musbahu kawai mu kai Inna wajen Aisha,tun d’azu da ka kirani dama na kira ta na gaya mata dan da ni da ita duk mun d’auka a gida na ma za a ajjiye innar a wajenta…shiyasa ma har ta gyara mata d’ayan d’akin bak’in dake a tsakar gida.’’

Girgiza kai kawai ya Musbah yayi kafin yace’’karka damu Nafi’u,ba zai yiu ace ni da
gidana amma mahaifiyata bazata shiga ba!ba zai yiu ba!.Ka bar batun Baraka kawai dan bata da lissafi da ishashshen hankali,mu yi sauri mu yi abun da yake a gaban mu kar mutanen nan su fara shirme.’’

A bakin titi suka tsaya suka d’auki Manubiya tukunna suka kama hanyar Bankin…cikin d’aurewar kai Ya Nafi’u
Yace
‘’Ni fa duk ban gane komai ba,wanne irin banki ne za su ranta kud’i iya na kwana uku
kuma su ce za su kama mutum tashi d’aya?Sannan naji kace Baban yace maka da kan sa yaje bankin to ya akayi kuma suka kamashi????’’
Ajiyar zuciya ya Musbah ya sauk’e kafin yace’’wallahi nima kaina a d’aure yake da lamarin nan,na dai san sharrin Yusuf ne bani da tantama shi ne ya had’a komai
Shi kuma Baba ya yarda dashi
kuma ka san shi da b’oye b’oye
sannan yak’i yin shawara da kowa har ta chab’e.
Bara dai mu je d’in,sai mu ji komai,Allah ya shige mana gaba.’’

‘’Ameeen’’
gaba d’ayan su suka ce,daga haka motar ta d’au shiruuu kowa yana tunani da fargaba dan haka suka shiga jero addu’o’i a cikin ransu.


Aikuwa da suka je abun da suka yi zato d’in ne,dan ko cikin bankin ma ba su shiga ba a waje ake case d’in,saboda babu bashin banki tsakanin Baba da banki.
Bashi!
a tsakanin Baba da wani mai kud’i ne wai shi ‘Black Snake’
wanda k’asa take zargin sa dan a file d’in na shi ma har da case da nnpc suna kan yi

A jikin takardar
….Baba ya tambayi mutumin aron miliyan d’aya,akan yana buk’ata urgent kud’in sa sun d’an mak’ale amma suna fitowa nan da 2 days zai maida masa har da interest!
In bai maida ba kuma to ya yarda mutumin ya yi masa
duk abunda yaga dama…

Su ya Yusuf su suka yi shaida suka tsaya a tsakani da shi da
wasu Abokan shi guda biyu.

Babban abun takaicin
shine yadda mutumin yak’i baiyyana su gan sa balle su samu suyi mishi magana
an ma ce musu baya ma k’asar gaba d’aya
Wasu mutane ya aiko su biyu
bak’ak’e murd’ad’d’u,kai kana
kana ganin su ka san babu d’igon Imani a tare da su.

Ana cikin haka aka ce ‘’ai case ya tashi anan awa uku ta cika dan haka yanzu sai dai a tafi da shi
Police station.
Kamar wani shahararren b’arawo haka aka datsa masa ankwa aka saka shi a mota.
Gaba dayansu yaran suna kuka haka aka tafi dashi.
Ba tare da b’aata lokaci ba suka bishi a motar ya Nafi’u.
Suna zuwa suka tarar da wani sabon tashin hankali
Wai an bada order a yi masa horo mai tsanani gashi an k’i a basu bail d’in shi.
D’ayan police d’in ma ce musu yayi su gudu wai black snake d’in tun d’azu ya bada order a kama har family d’in Baban a had’asu waje d’aya..suna tsaye daga reception suka fara jiyo ihu, babu yadda basu yi ba amma aka hana su shiga,d’ayan police d’in ne ya d’an kwantar musu da hankali ta hanyar ce musu ai ba ihun Baba baneba sannan ya basu shawarar su je da su nemo kud’in tun kafin abun ya fi haka lalacewa,dakyar dai aka samu suka hak’ura suka yi waje a gigice masu hawaye suna yi
masu kuka sunayi,suna fita
Ya musbah da ya Nafi’u
kowa ya d’au waya suka shiga neman mafita a rikice.

Sun shafe sama da awa d’aya
suna tambayar jam’ar da suka sani bashi amma daga Ya Musbah har Ya Nafi’un kwata kwata dubu goma suka had’a,
Uncle kanshi dubu uku ya turo ta acc d’in ya Nafi’u yace
su jira sa in ya tashi a aiki zai zo ya duba Baban.

Gefe Jidda ta koma ta fashe da wani sabon kuka,ji take kamar ta gudu
Saboda ita Manubiya ta yi aikatau a gidan Ammi
sannan yanzu ma gashi saboda ita aka kama Baba
in ba dakyar ba kuma ta san Ya Yusuf ne yace ayi ma sa horo mai tsanani so yake ya rama dukan da suka yi mishi.

Kuka gaba d’ayan su suke yi daga ita har Manubiya
Su ya Musbah kuma in ban da waya ba abun da suke yi dan kaff
d’an kud’in hannunsu ma duk ya k’are a siyen kati,
suna tsaye a harabar police station d’in suka ga wasu polisawa sun fito da tray da almakashi da wasu k’arafuna akai duk jini,sun nufi fanfo suna wankewa.
Tun kafin kwakwalwar Manubiya ta gama d’aukar charjin watakil jinin Baba ne wannan…ta kwasa a guje tayi cikin police station d’in,da kyar ta iya tsayawa ta tambayi police d’in da ya biyota da niyyar tare ta.
Tana kuka ta ce ya barta ta ga Baba,saboda Allah da Annabi.
Tausayi ta bashi dan haka ya nuna mata k’ofar in da Baba yake ciki ya juya kawai,a ransa yana mamakin mai ya had’a waennan kamilallun mutanen da Black snake.

Sai da ta juya zata koma dan ta baro d’akin a bayan ta tukunna ta lura da su Ya Musbah a bayan ta suma duk a gigice,sai da suka je bakin k’ofar d’akin kuma duk sai suka kasa shiga,kowa yanajin tsoron abunda zai shiga ya tarar.
Dakyar ya Musbah yayi ta maza ya tura k’ofar ya shige
daga haka suma suka samu kwarin guiwar mara masa baya.

Turuss! ya Musbah da ya Nafi’u suka ja suka suka tsaya
Su manubiya kuma suka saki wani irin kuka

A kwance suka sameshi daga shi sai vest da dogon wando
banda karkarwa ba abun da jikin sa yake yi,da alamun bai ma san waye a kan sa ba ga jini a zuzzube a k’asa
Sai da suka matsa kusa dashi dakyar tukunna suka lura ashe harda farcen sa na k’afa d’aya guda d’aya da na hannu yatsu biyu suka fara zarewa.
Da sauri suka zauna a gabanshi Jidda ta d’aura k’afafun shi akan cinyar ta Manubiya ta shiga goge masa gumi tana yi masa fifita,suna yi suna kuka a rikice a gigice.
A zuciye ya Nafi’u ya mik’e cikin fushi yace
‘’Wanne irin rashin imanine da dak’ik’anci wannan a haka zai fito musu da kud’in nasu?’’
Sai kuma ya nufi hanyar waje.
Dasauri ya Musbah ya sha gaban sa ya tare sa.
Cikin fushi ya Nafi’u yace ‘’matsa,matsamin inje in samesu

Cikin son fahimtar da shi ya Musbah yace’’Nafi’u in rai ya b’aci hankali baya gushewa,ka je ka samesu kace musu me?kud’i fa aka basu aka basu order kaga kuwa dole su yi abun da aka ce,kuma baka karanta takardar bane?mutum bai saka hannu bama ya aka k’are ballantana an saka hannu?
Dole suyi abunda aka ce
Kuma ko Ina za muje ba wanda zai tsaya mana,in ka yi fad’a ko kuma ka ce zaka tada rikici yanzu sai a had’a da kai saboda baka da kud’i nima bani da kud’i shima Baba bashi da kud’i.
Ka tsaya yanzu mu nutsu mu San abunyi mu ceto Baba dan hayaniya da rikici ba namu bane ba.’’
Dakyar dai ya Musbah ya samu ya d’an kwantar wa da ya Nafi’u hankali aka samu ya d’an nutsu .

Yana huci yace’’na ji ka fini gaskiya,ba zan je in same su ba amma wallahi tallahi
duk wanda ya shigo da niyyar sake yin wani hauka anan wajen sai na illatashi
Ina nan ba inda zanje’’

Lumshe ido kawai ya Musbah yayi ya bud’e yace’’baza su sake ba in ma bamu samu mun had’a kan kud’ad’en ba ba komai ni sai in fanshe sa’’,
daidai nan Abbakar ya shigo wajen shima a rikice.Yana ganin Manubiya da yanayin kukan da take yi hankalinshi ya sake tashi,hankalinshi bai gama tashi ba sai da idanuwan sa suka kai ga Baba.
Da sauri ya k’arasa ya na salati
sai kuma ya kalli Manubiya,kamar jira take yi kuwa a take ta fashe da wani sabon kukan.Ji yayi kamar shima ya sa kuka,da kyar ya samu ya tsugunna inda take ya ahankali
ya d’aga hannu kamar zai shafa fuskarta sai kuma
ya sauk’e hannun jiki a sanyaye kafin ya runtse idonshi da k’arfi ya bud’e tukunna a hankali yace
‘’Ki yi hak’uri Manu,za mu san yadda za’ayi inshaaAllah,d’azu
ya Musbah ya kirani yake gayamin
3k ne kawai a acc d’ina na tura mishi yanzu kuma ga 20 na sake nemowa…ki kwantar da hankalinki za ‘a samo kin ji dan Allah ki daina kuka’’

Dakyar ta samu tace
‘‘Abbakar kafin nan mukasan mai za su sake yi masa?kall …..


K’arar bundugun da suka ji ba k’ak’k’autawa tare da hayaniya da k’arar motoci ne yasanya duk sukayi tsit

Basu gama tunanin mai ya faru ba suka ji an banko k’ofar da mahaukacin k’arfi an shigo da gudu…



MANNUBIYA
36

Na
Humayrah Bulama

Mikiya Writers Association.

K’arar bundugun da suka ji ba k’ak’k’autawa tare da hayaniya da k’arar motoci ne yasanya duk sukayi tsit.

Basu gama tunanin mai ya faru ba suka ji an banko k’ofar da mahaukacin k’arfi an shigo da gudu…

Body guards ne bak’ak’e k’irin da su sanye da bak’ak’en kaya da bak’in glass,biyu na farkon suna rik’e da manya manyan bindigu ragowar na bayan su kuma k’anana ne a sak’ale a gefen k’ugunsu.


Yanayin wajen suka kalla dan haka d’aya a cikin su ya juya ya fita da gudu yaje ya kawo kujera ya ajjiye kafin ya koma ya shiga cikin layi biyun da suka yi a jere tunda ga bakin k’ofar har izuwa inda suka ajjiye kujerar a gaban Baba.

Tsayawa kawai su Manubiya sukayi gaba d’ayan su suna kallonsu
Basu gama tunani ba..

.. suka fara jiyo wata irin dariya
da wata murya mara dad’in sauraro,yadda ake dariyar ne zai sanya tashi d’aya ka
fahimci rashin kamala da rashin sanin ciwon kan mamallakin mai muryar…yana magana da turanci yana dariya sosai kamar wani tab’abb’e!.
Yadda suke jiyo muryar tana matsosu ne yasanya suka fahimci mutumin nan d’akin zai shigo..
Ta tsakiyar body guards d’in nashi da suka hau layi ya bi ya shigo…k’ato ne sosai,dogo lukuti fari sosai farin nasa irin jaaa d’innan,babu gashi ko
ko guda d’aya tun daga scarf d’in sa har gemun sa da gashin baki duk babu gashi
Iya kar girar sa da eyelashes d’in sa ne kawai masu gashi a kaf ilahirin kan sa zuwa fuskarshi wanda hakan ne ya basu damar ganin asalin yanayin fuskartashi
wadda take d’auke da
k’ananan idanu jajaye da d’an
guntun hanci yayinda bakin sa ya kasance madaidaici.
Yadda dpo yake bin sa yana russuna masa yana yi masa magana kamar zai kwanta
abun dole ya k’ular da jama’a…dariyar sa kawai yake yi yana bawa dpo amsa har ya iso inda Baba yake,shiruu ya yi ya tsayar da dariyar ta sa kafin ya kalli dpo yace’’ku kace yanakan karb’an punishment
But
nagani he’s still conscious,Y?’’
Yayi tambayar yana mai zubawa dpo jajaye idanuwan sa.
A take dpo d’in ya rikice ya fara kame kame ya shiga
karanto addu’o’i daban daban a k’asan ransa yana mai neman tsari daga sharrin ‘Black Snake’
dan kasancewar yanzunnan ya gama raha da dariya da shi
ba zai hana shi sauya masa kamanni a take a yanzunan ba,
kamar kuwa ya sani dan tashi d’aya black snake ya gama rayawa a ran sa zai sanya body guards d’in shi su yiwa dpo asalin horo a yanzu a gaban kowa,ta ydda next time zai fahimci mai ake nufi da horo,dan haka ya d’an d’ago kan sa da niyyar juya wa ya kira biyu a cikin body guards d’in shi amma sai
Idanuwanshi suka sauk’a akan Manubiya
wadda gaba d’aya tashi d’aya ta rikice sannan tsoro ya lullube ta daga ganinsa
Ba abun da ya fi d’aga mata hankali irin zanen bak’in macijin daya fito tarr!!
wanda yake nan a kwance a hannun sa na dama…tun daga kwanjinshi har kan bayan tafin hannunshi
kamar na gaske
ga wasu uban sark’ok’i a jikin sa wuya da hannu da wani burgujejen wando shima mai sark’ok’i a jiki amma kuma rigar jikin sa armless.

Wata mahaukaciyar dariya taga ya kwashe da, ga mamakinta kawai sai ta ga ya nufota aikuwa kafin ya k’araso tuni ta shige bayan ya Musbah ta b’uya,da mamaki ya kalleta ya kalli Jidda sai kuma ya juya ya kalli d’aya daga cikin bodyguards d’in nasa yace
‘’John!dama ita biyu ce?’’

‘’A’a ai dama Kabir d’in yace tanada sister,remember?’’

Dariya yayi kafin ya juya ya shiga yiwa Manubiya wadda ta b’uya a bayan ya Musbah
wani irin kallo harda lek’a wa yakeyi yana sakewa saboda a yadda Abokin Ya Yusuf yayi masa bayani tabbas yarinyar tafi haka kyau a fili..
Ya musbah ya kalla ya kalleta
kafin yayi wani kalar murmushi
basu gama fahimtar ma’anar murmushin nashi ba suka ga yayi fito!.
Da sauri d’aya a cikin body guards d’in shi yazo ya hankad’e ya Musbah ya fisgo hannun Manubiya ya dawo da ita gaban black snake ya tsayar tukunna ya juya ya koma yaje ya tsaya.


Cikin d’an d’aga murya ya Nafi’u yace
‘’Me ye haka wai?’’

Ba wanda ya ko kalle sa balle su bashi amsa,ahankali black snake d’in ya sa hannu ya d’an kamo hab’ar Manubiya ya d’ago yana mai k’are mata kallo.
Dasauri ta kawar da kanta gefe tana wani irin kuka
dan gaba d’aya a tsorace take
ga tashin hankalin da take a ciki tun farko dama ga kuma zuwan wannan abun tsoron
shiyasa duk ta bi ta sake duburcewa,in banda karkarwa babu abun da jikinta yake yi.

‘’Mallan kana haukane!’’ya Musbah wanda ya taso yanzu ya fad’a a zuciye yana shirin yin kan black snake d’in,a take wani a cikin bodyguards d’in nashi ya saita ma sa bindiga.
Da sauri Baba yace’’dan Allah karkuyi musu komai dan Allah
sai kuma ya fashe da Kuka’’.

Shi kam black snake gaba d’aya hankalinshi ya tashi
da ganin Manubiya,babu
k’asar da bai jeba a rayuwarshi sai dai in da ba’a rasaba amman ba zai yi k’arya ba duk yawonsa da gane ganensa bai tab’a ganin mace mai kyawu sannan macen data d’auke hankalinshi lokaci guda kamar Manu ba.
Kallonta yake yana sakewa
kamar ya samu television,
sai da ya lashe bakinshi tukunna ya kamo hijabinta ta k’asa batayi auni ba kawai taji ya d’ago shi ya zare ya yar a gefe…

Tabbas ba k’aramin zafin tozarcin da ya aikata mata ta ji ba dukda kuwa doguwar riga ta Abaya ce a jikinta amma ji tayi kamar ta kurma ihu,tashi
d’aya taji wani irin bak’in ciki
ya lullub’eta bata san lokacin data d’aga hannu zata kifa mishi mari ba.
Ya Musbah da ya Nafi’u ma duk nufar sa sukayi dukda bindigar da ke saite a kan ya Musbah bai ma san lokacin daya motsa ba.
Abbakar ma yana ganin haka yayi kansu cikin fushi.

A lokaci guda black snake ya ya zaro pistol daga aljihun shi
ya saita k’afar Abbakar ya sakar mishi bullet sannan ya rik’e tattausan hannun Manubiya da d’ayan hannun nashi.

‘’Innalillahi wa inna ilaihirrajiun’’gaba d’ayan su sukace sai kuma suka yi kan Abbakar wanda ya fad’i a wajen ya yi suman wucen gadi tsabar azaba ya ma kasa kuka ya kasa magana
Yanajin azabar da tunda uwar shi ta kawoshi duniya bai tab’a ji tana ratsashi ba.

Black snake bai huce ba sai da
ya kuma harbin d’aya a cikin bodyguards d’in sa a kafad’a,wanda d’azu ya saitawa ya Musbah bindiga.
Cikin dakakkiyar murya yace’’da ka saita masa bindiga kaga ya motsa harbesa ya kamata ka yi,next time you should take note!’’.
Ba tare daya cika hannun Manu wadda taketa k’ok’arin kwace wa tana kuka tana kallon Abbakar ba
Ya kalli kowa a wajen tukunna
Yace‘’yanzu na samu attention d’in kowa ko?
Perfect!bari ayi magana’’
‘’My name is black snake
wanda ya kamata ace kuna jin tsoro but naga ku da Baban ku kun raina ni,hakan ne ya nunamin cewa bakusan wayene ni ba ba kuma kusan what i’m capable of ba,Baba na nan kwance’’yayi maganar yana nuna Baba,Kafin ya d’aura da cewa’’ya ci kud’ina!ban san ta ya aka yi this old man ya samu guts da audacity d’in cin kud’ina ba but we all know ya ci min kud’ina,sannan a statement d’in shi ya rubuta in yi mishi duk abun da naga dama in bai biyani ba.’’
Dariya yayi kafin ya d’aura da cewa ‘’sai da na saka aka dubamin aka tabbatar min da mutumin nan ba mahaukaci baneba
Tukunna
Saboda nayi mamakin mutum mai hankali da zai yi wannan rubutun a statement na tsakanina da shi
I’m the black snake’’
Ya fad’i hakan yana d’aga hannuwanshi biyun sama
still yana rik’e da hannun Manubiya,kafin ya ci gaba da cewa’’mutum bai ce in azabtar da shi ba ma na azabtar ballantana kuma ya fad’a?!.
Anyways I was overseas
ba na k’asar aka fara case d’innan ni da Kabir a friend
of your nephew ( Yusuf )
muka tafi and ya ji ni a waya ina magana akan case d’in
shine ya bani labarin da na ji dad’i kuma da idanuwana suka gani na sake jin dad’i.
Da farko ya cemin
wannan Baban ko kashe shi zan yi ba zai biya ni kud’ina ba saboda bashi da kud’i
But akwai option
Baba yanada kyakkyawar yarinya fara k’al! akwai wata rana da ya je a gidan su Yusuf d’in ya ganta ya cewa Yusuf yanason ta to ashe
wai budurwa Yusuf d’in ce’’.
Cikin yin k’asa da murya yace
ban gayawa Yusuf komai ba bai ma san na dawo Nigeria ba as we speak,dan
Kawai
Inajin maganar budurwa na hayo private jet na taho
nazo inyi betraying d’in shi’’
Ya k’arashe maganar yana mai kwashewa da dariya
haka ma guards d’in shi duk suka kwashe da dariya.

‘Da kyar Abbakar ya iya zaro wayarshi ya fara k’okarin kiran sir Najeeb.

Sai da suka gama dariyar su tukunna Black snake yaci gaba da cewa’’da farko ina d’an tantama but yadda na ga Kabir ya rikice yana zuzutamin kyawun yarinyar ne ya sa na amince na bi shawarar daya bani na zo
Akan
‘Baba ya auramin ita ni kuma in bar mishi
1 million
na yafe har intrest d’in’!‘’.

Manubiya bata san tanada k’arfi ba sai da ta samu damar fincike hannunta daga cikin na black snake
dan ba k’aramin girgiza ta maganar sa ta k’arshe tayi ba.

Dariya ya kwashe da ita
kafin yace
‘’Ai ba kiji best part d’in ba ma,’’
Bai jira jin magana ba ya d’aura da cewa ‘’i tot ke d’aya ne to kuma da nazo sai na tarar ku biyu ne kyawawan matan,shiyasa na zo da better
plan
‘Zan auri daya in ajjiye d’aya mistress’.
What a smart boy am i, ko???’’
Ya k’arashe maganar tasa da tambaya yana d’an rawa kad’an kad’an sai kuma gaba d’ayan su suka sake kwashewa da dariya.

Kasa ma motsi Manubiya tayi dan gaba d’aya kanta ya d’au zafi,in banda ambaliyar hawaye ba abun da take yi kamar an kunna famfo.


Su Blake snake sun jima suna dariyar da su Manubiya suka kasa fahimtar abun da yake sakasu dariyar kafin black snake ya d’aga bindigar sa ya harbi window duk suka yi shiru suka nutsu,su Manubiya kuwa in banda karkarwa ba abun da jikinsu yake yi
Addu’o’i kawai suke karantowa
dan tabbas black snake masifa ne.


A kan Baba ya k’arasa ya tsaya tukunna yace
‘’Okay Baba,komai yana hannunka yanzu,kaga dai na
harbi mutane har biyu
But bafa wai nayi releasing gaba d’aya temper d’ina bane ba,na yi iyakar k’ok’arina danne temper d’ina shiyasa kaga na harbesu a wajen dana tabbatar baza su mutu ba
saboda banaso inyi terrible abu a gabanka a matsayinka na father inlaw d’ina
But I promise you
In kayimin gardama musu ko taurin kai,to zan kashe maza guda ukun nan
kuma in tafi da mata na
with or without your consent
kuma ba zaka sake ganinsuba
sai maybe after 15 years in sun tsufa sai su dawo maka
So if I were you
zan yiwa black snake biyayya in

Please Login or Register in order to submit comment