Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kinga ai hakan bai yi dai dai ba,ku zauna lafiya dukkan mu a k’ark’ashin mutum d’aya muke,duniyar ma duka duka nawa take?d’an zama ne fa na k’ankanin lokaci bayaga haka ma na tabbata nan da five years ba lalle a tarar da hatta Yadira a cikin gidan nan ba..
Ya’isha ki gayawa Kausar in kin hau sama ki yi mata bayanin da na yi muku ita da Yasira tunda su ne ba….’’
Da k’arfi Ya’isha ta dire kofin juice d’in dake hannun ta wanda hakan ya katsewa Ummi maganar ta,Allah ya so cup d’in unbreakable ne da tuni ya fashe saboda yadda ta buga sa.
Cikin tsananin b’acin rai ta mik’e ta kalli Munirat da ta d’ago itama tana kallon ta,zuciya a wuya tace’’
‘’Dan Allah yadda kika had’a kayan ki kar ki kwance ki kwashe su kiyi gaba yau kar in sake ganin k’afar ki anan.’’
Sannan ta juya ta kalli Ummi
tace’’Ummi do you know wat your problem is?’’bata tsaya jin mai Ummin zata ce ba ta ce’’Son kai!,son kai shine matsalar ki,kalli yadda kika tisa mu a gaba kina mana maganar dole sai mun so y’ar ki dole sai mun yi zaman lafiya da ita,shin wai ana dole?kuma naga ita ta janyo komai in the first place tunda tun da ta zo gidan nan babu wanda ya Kyamace ta
Despite the fact that
She’s not even our class but haka muka ja ta a jiki duk dan a zauna lafiya amma duk bataga wannan ba haka tazo ta tafkawa mutane shirme,it doesn’t matter wai wani saurayin ta ne ko ma mijin ta ne tun farko ai dai yanzu Yahanasu zai aura
amma bata ga wannan ba tsabar cin fuska haka ta biye masa
Although Yahanasu ta ce babu ruwan mu da case d’in ta but yadda ki ke supporting y’ar ki kike k’ok’arin goge laifin ta k’arfi da yaji ni shine matsalata da ke,sannan bari ki ji in gaya miki ni kam har abada i’ll never be friends with her tun na lura ba ki san mutunci,kawaici da arzik’i ba ke kawai naki kika sani you are morethan selfish dan haka babu zaman lafiya a tsakani na da ke da y’ar ki har abada wallahi,ba da irin ku ake zaman lafiya ba dan naga in aka baku fuska next time sai kun yi abun da ya fi wannan
dan haka dole mu taka miki burki mu nuna miki matsayin ki a cikin gidan nan tun yanzu,ke ba kowa bace ba,you are just holding a place here..’’

Cikin tsawa Ummi ta mik’e tsaye tace
‘’Ya’isha!!’’

Itama Ya’isha cikin tsawar da tafi ta Ummi ta ce
‘’Kar ki sake d’aga min murya
gaskiya ce dole in fad’eta,kuma naga da farko baku san mu ba muma bamu san ku ba amman ai mun rayu kuma kun rayu,a kan wanne dalili za ki tilastamana dole sai mun kula y’ar ki?
Sannan last warning kar ki sake cewa za ki tara mu da ni da sisters d’ina kiyi mana fad’a ko kuma ki bamu wani useless labarin ki wanda already mun riga mun san shi dan an fad’a mana tun d’azu da safe,and one more thing..in kina son magana da Yasira ko Kausar kin san in da d’akunan su yake kar ki sake cewa zaki aikeni tun da ni ba y’ar aiken ki bace ba…
Tana gama fad’in haka ta wuce ta bar wajen fuuu kamar zata tashi sama.
Tana wucewa Yusra ma ta mik’e ta bi bayan ta haka ma Yadira.
Ahankali Yasmeen ta mik’e
tace’’Mommy good night,muna da wani surgery d’in gobe da sassafe,Baabaa larai ayi min faten doya irin na jiya pls’’
Ta fad’a hakan tana langab’ar da kai
Murmushi Baaba larai tayi daga nan tace ‘’inshaaAllah y’ar albarka,Allah ya taimaka
sai da safe.’’
‘’Na gode Baaba larai d’in mu’’
Yasmeen ta fad’a hakan da murmushi akan fuskar ta kafin ita ma ta wuce abun ta ba tare da ta kalli inda Ummi take nan a daskare ba.

Ahankali Yahanasu ta lumshe idanuwan ta a ranta tace’’ dama Bashir bai shigo cikin rayuwarta ba,gashi dai yanzu ba auren ta zai yi ba amman kuma ya zamo silar da zai tarwatsa auren Daddy da Ummi wanda take addu’ar a samu ya d’auree har abada.

Da gudu Munirat ta mik’e ta bar wajen ta na hawaye,wannan shine duka biyu ga cin mutunci gashi kuma Ummi ta hanata magana.

Ahankali Mommy tace ‘’Sai da safen ku’’
Daga nan ta mik’e ta bar wajen

Ummi zata bar wajen kenan
Yahanasu ta mik’e ta matso ta kamo hannun ta tace’’ Ummi dan Allah ki yi hak’uri, ko da ace kowa bai fahimce ki ba ni na fahimce ki,tun a jiya Yash yayi min bayanin komai ta waya,nima kuma a jiyan duk na yiwa Yasira bayani kuma naji suna maganar Yassira ta tura a group d’in su dan haka kinga sun san labarin kenan kawai dai gaskiyar ce ba sa so kuma suke k’ok’arin dannewa tunda dama ba shine asalin dalilin su na kyarar ku ba,kawai ki yi hak’uri Ummi ki daina k’ok’arin had’a kan su da Munirat dan ba zai tab’a had’uwa ba,ki zuba musu ido kawai ki kwantar da hankalin ki Munirat is not alone a cikin gidan nan tun da ina nan ba za ta yi zaman kad’aici ba inshaaAllah…’’

Cikin takaici Ummi tace
‘’Na gode Yahanasu,amma ko ba komai ya zama dole in ji takaicin yadda Mommy ta ke yin burus akan lamarin nan ki duba ki ga yadda nake bata girman ta amma ita in yaran nan zasu wanka min mari ba za ta tab’a hanawa ba.’’
Cikin katse ta Baaba larai tace
‘’Ummi,sai dai fa ki yi hak’uri ,duk cikin yaran nan ki gaya min waye kika ga yana jin maganar Mommy a cikin su?tun daga kan Yassira har izuwa kan Yadira.
Yahanasu kada’i keyi mata biyayya amman ragowar duk binsu kawai take yi.
Dalilin da kika ga yasanya bata saka muku baki
Shine
Bata so ta shiga fad’an kuma su disgata a gaban ki,dan itama ba jin maganar ta akeyi a cikin gidan nan,hatta shi kan sa Daddy d’in ba bi takan ta yake yi ba kuma na san kin san me ke faruwa a tsakanin su shi da ita tun da ta ce min rannan a gaban ki ya koreta.Ba wai Ina gaya miki hakan dan ki raina ta ba,A’a ina gaya miki ne dan ki daina jin haushin ta.
Dan haka idan zan baki shawara ki d’auka to ki daina k’ok’arin tilastawa yaran nan akan dole sai sun biki dan hakan da kike yi kamar kina sake rura wutar rikici a tsakanin ki da su ne.Sannan wani abun da na lura kamar baki sani ba
shine
ko dambatuwa kuka yi da ke da yaran nan to fa idan uban su yazo bayan su zai bi dan babu abun da ya tsana a duniya kamar ka tab’a masa ya’ya,dan haka tun da har kika ga uwarsu ma bata tilas ta musu to kema ki koma gefe ki zubawa kowa ido.’’
Tana gama fad’ar haka ta
wuce ta nufi sama wajen Mommy..

A d’akin ta ta sameta tanata faman safa da marwa,tana ganin shigowar ta tayi maza ta k’arasa wajen ta a d’an rikice ta ce’’yauwa Larai,ke nake ta jira ya ake ciki?

Ajiyar zuciya Baaba larai ta sauk’e kafin tace
‘’Na barta a k’asa ita da Yahanasu’’

Cikin katse ta Mommy tace ‘’Ba maganar ta nake yi miki ba ,maganar Yashjub nake yi..na gaya miki tun jiya ai..maganar ki gaskiya ce,da bakin sa ya tabbatar min amman har yanzu ban ji kin ce komai ba.’’
Murmushi Baaba larai ta yi kafin ta nemi waje ta zauna sannan ta ce ‘’Tun da kika ji nayi shiru akwai dalili,yanzu
Yahanasu ce naga bakin ta ya fara bud’e wa,kina ganin ba matsala kuwa?na lura da ita bata shakkar kowa kwana biyun nan yanzu haka a gabana ta gama aibanta su Kausar sannan k’iri k’iri Ina kallon idonta tana kallon nawa amma ta bi bayan Ummi ta bata gaskiya,shiyasa naga gara ayi wani abun tun kafin ta je ta b’allo ruwa.

Ajiyar zuciya Mommy ta sauk’e kafin tace
‘’Larai bar batun Yahanasu tukunna,Ina tunanin shurun nata da rashin fitar da take yi ne ya shafe ta har a ta b’angaren aure fa,ko ke baki yi wannan lissafin ba?ba ki fahimci komai ba?saboda har ga Allah na fara jin tsoron zalintar Yahanasu da nake yi dayawa har haka saboda nawa gain d’in’’
Shiruu Baaba larai tayi kafin tace’’gaskiya ni kam ba zan bi ta taki ba khadija,saboda in bakin Yahanasu ya bud’u ba ke kadaice a wahala ba,bari ki ji in gaya miki yau tun safe da ta bar gidan nan bata dawo ba sai magrib.’’
Cikin rashin jinn dad’i Mommy ta nemi guri ta zauna itama a kusa da ita kafin a hankali tace ‘’shikenan larai ki yi abunda kike gani ya dace.’’

Murmushi Baaba larai tayi
kafin ta gyara zama ta ce
‘’Ita kuma Ummi………..’’




MANNUBIYA
27

Na
Humayrah Bulama

Mikiya Writers Association.

Sai da Ummi ta yi da gaske tukunna Munirat ta fasa zuwa gidan yayar ta,da fad’a da lallashi haka ta samu ta d’an kwantar mata da hankali duk da kuwa ita ma hankalin nata ba a kwance ya ke ba,abun tausayi haka itama Munirat d’in ta shiga kwantar wa da mahaifiyar tata hankali,sun jima suna magana kafin Ummi ta mik’e ta nufi wajen Daddy jiki ba kwari.
A bakin k’ofar shiga parlourn
suka had’u da Yasmin,tana shiga Yasmeen d’in kuma tana fito wa..ko kallon ta bata yi ba
Itama Ummin bata kulata ba.
Da sallama ta shiga,ba ta same shi a parlourn sa ba sai a chan cikin d’akin sa a zaune a kan gado,
Yayi shiruu alamun tunani yake yi.
A kusa dashi taje ta nemi guri ta zauna kafin a hankali tace
‘’Barka da dawowa Daddy,ya
meeting d’in?’’

Ba tare daya kalle ta ba yace
‘’Alhamdulillah’’
Daga nan ya mik’e ya fad’a toilet.

Har ya fito tana nan a zaune
ta yi zurfi a tunani..

Sai da ya gama shirin bacci tukunna tace
‘’Bara in kawo maka abinci’’
Ta fad’a hakan tana shirin mik’ewa,

Cikin katse ta yace ‘’don’t bother,a k’oshe na ke.’’

Cikin kwantar da murya ta ce
‘’Daddy,ka d’an ci ko kad’an ne m….’’

‘’Wai Saddik’a ni k’aramin Yaro ne?d’ura zaki yi min ko me?nace miki a k’oshe nake amma kin bi kin ishe ni,daga meeting na dawo Ina buk’atar hutu shin baki da fahimta ne????
Ahankali tace ‘’ka yi hak’uri
Allah ya huci zuciyar ka’’…

Har zai kwanta sai kuma yace
‘’Ki koma parlour ko kuma ki zab’i wani bedroom d’in ki kwana,ban ce ki fita a side d’ina ba,just ki nemi wani bedroom d’in a parlourn..’’
Sai da ya sake cewa’’bakya ji na ne?’’
Tukunna da kyar Ummi tace ‘’to Daddy,sai da safe.’’

Washegari da sassafe ta tashi tun da tayi sallar asuba ba ta koma ba,dama tun a daren jiya ta fitar da abincin da ya ce ba zai ci ba ta saka a fridge dan alokacin hatta gwaggo ta riga ta tafi side d’in su na masu aiki.
Had’add’en breakfast mai rai da lafiya yau ma Ummi ta shiga had’awa Daddy,tana cikin yi su gwaggo suka shigo dan haka ta shiga akayi har na gaba d’aya gidan tare da ita.

K’arfe bakwai da kwata suka kammala dan haka ta d’auki na Daddy ta nufi sama dashi cike da sassarfa.

A bakin k’ofar d’akin shi ta same sa yana gyara zaman necktie d’in sa,tun kafin ta gaida shi yace’’koma da abincin ki yanzu ma na k’oshi’’

Ahankali ta nufe sa da tray d’in a hannun ta da niyyar in taje ta durk’usa ta bashi hak’uri,amma tana zuwa kusa da shi tun kafin ta durk’usa ya yi wani irin fatali da abincin wanda ta sanadiyyar hakan gaba d’aya parlourn,kayan jikin sa da kayan jikin ta suka b’aci….

Cikin fushi ya juya ya koma d’aki ya bar ta nan a tsaye cikin tsananin tashin hankali da mamaki bata san lokacin da wasu hawaye masu zafi suka shiga tsilalo mata ba.
Da kyar ta samu ta goge wajen tana yi tana kuka haka ta je ta chanja kayan jikin ta tukunna ta dawo ta tattare kwanukan ta nufi k’asa.
A hanyar stairs ta tsaya ta goge hawayen ta tukunna ta k’arasa sauk’a ta nufi kitchen.A kitchen d’in ta tarar da Yasira Kausar Yasmeen da Ya’isha,da alamun kowa fita zata yi kuma masu aikin ba su gama jerawa a kan dining d’in ba shine suka zo suke d’iba anan d’in,a cikin su ba wanda yace mata ci kan ki haka ta wuce ta ajjiye kwanukan ta shiga wanke hannun ta.cikin rashin mutunci ta ji Ya’isha na cewa
‘’Dad’ina da talaka bai iya samun guri ba,a yi employing d’inka amma ka nemi zak’ewa,na rantse da Allah Asabe duk ranar da kuka sake yin letti baku jera mana abinci har kuka ja muka makara to
ko wacce shegiya sai ta koma inda ta fito,sai ku dinga yin abu kamar ku kuka haifi mutum,
Mtswwwww’’
Ta k’arashe maganar tata tana mai jan wani uban tsaki
daganan ta sa kai ta fice

Wata dariya Yasmeen tayi
Irin wadda tayi wa Ummi jiya ciki ciki.
Dariya sosai Kausar ta yi kafin tace
‘’Kin ga Malama,ki saki baki ki yi dariyar ki ba uban wanda ya Isa ya hanaki.’’
Ahankali amma yadda ta tabbatar Ummin za ta ji Yasira tace
‘’Tana jin tsoron a shiga tsakanin ta da Daddy ne’’

Cikin dariya k’asa k’asa ta rainin hankali
Kausar tace ‘’au,haka ne fa’’

Daganan duk suka d’auka abincin da suka zuzzuba suka fita suka nufi dining table banda Yasmeen wadda ta tsaya haada tea a cikin kitchen d’in.Har Ummi ta fita sai kuma ta tuna akwai flask d’in da ferfesun ciki bai gama zubewa ba dan haka ta juya da niyyar cewa gwaggwo su juye mai kyau ne,a k’ofar kitchen d’in suka yi kicibus da Yasmeen wadda ta yi kamar irin ta tare k’ofar nan ita ba ta matsawa Ummin ta wuce ba sannan ita bata fito ba,da mamaki Ummi take kallon yarinyar tana so taga iya gudun ruwanta.
Ahankali Yasmeen wadda ta hango Daddy yana sauk’owa daga bene tace’’na ga kin shigo da kwanuka a hargitse
kuma idonki kamar kin yi kuka,gaya min gaskiya dukan ki Daddy ya yi?’’..
Dama tun dazu da kyar Ummi take danne kan ta dan bata so ta kula yaran Amman duk maganganun da suka yi a kitchen d’in ta san da ita suke ga kuma takaici da tashin hankalin da Daddy ya tsoma ta a ciki tun jiya shiyasa duk yadda ta so hana kan ta ta kasa dan haka ta d’aga hannu ta zabgawa Yasmeen wani irin gigitaccen mari,dai dai nan kuma Daddy ya k’arasa saukk’owa cikin parlourn.

Wani irin kuka Yasmeen ta saka ta durk’ushe a wajen ta dafe kunnnenta tana ihun ‘’Wayyo Allah kunne na’’

Daidai nan Daddy ya k’araso wajen a gigice,da k’arfi yace
‘’Innalillahi wa inna ilaihirrajiun’’sakamokon ganin jini yana zubowa ta kunnen Yasmeen.

Sai a lokacin Ummi ta ji ashe wai Yasmeen tana da abu a cikin kunnenta yana zuk’o mata magana sakamokon rashin aiki da kunnuwan nata basa yi sosai.kuma k’iri k’iri Kausar har da rantsuwa tace wai ai sun gaya wa Ummin jiya da ta yi niyyar marin Yasmeen d’in amma shine yau sai da ta mare ta, shikenan yanzu in ba da kyar ba ta danna mata abun ciki ta lalata mata kunne gaba d’aya.

Cikin tsananin gigita Ummi tace
‘’Kausar kiji tsoron Allah,yaushe….

Wata rikitacciyar tsawa da Daddy ya buga mata ne ya sanya ta kasa ci gaba da magana,cikin tsananin fushi yace’’ki b’ace min a wajen nan tun kafin na illataki .’’

Ahankali sannan k’afafuwan ta suna wani irin karkarwa ta samu da kyar ta juya ta kama hanyar sama zuciyar ta tana wani irin tafarfasa.
Yayinda su kuma suka d’unguma kai Yasmeen asibiti,gaba d’ayan su.



Sai yau Manubiya ta d’auki wayar ta a jikin charji daga gian Ammi,dan sai da ta bar wayar ta yi awannin da aka rubuta ana buk’atar ta yi a jikin charjin.Layin ta na jiya da suka yiwa register ta saka,bayan kamar 30 minutes ta d’auki wayar ta dudduba daganan ta d’auko katin Yashjub cikin nutsuwa ta juye number sa tukunna ta tura masa sak’o kmar haka’’Good morning Sir,yau na kunna wayar tawa daga charji,my mail is empty as for today..in sun turo I’ll report everything to you on Friday
InshaaAllah
Thankyou..Manubiya Musa..’’

Fitowar Yashjub daga wanka kenan dan lokacin 7 daidai,itama Ammi ce tace mata ta tabbata ta je da wuri fiye da yadda take zuwa kullum,wai tana da bak’in da za su zo daga abuja so akwai aiki sosai.
Yana fitowa yaga wayar sa ta yi k’ara dan haka ya k’arasa ya d’auka ya shiga duba message d’in,dama ya saka a ran sa maybe ita d’in ce dan tun jiya yake ta jiran yaga kira ko messge d’in ta.

Murmushi kawai yayi ya sake karanta sak’on ya kuma maimaitawa ya sake maimaitawa kafin ya ajjiye wayar da kyar yana mai sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya,yanzu mene ne abun yi,saboda duk taurin kan sa da kauce kaucen sa ya riga ya sak’k’o,ya fahimci yana mahaukacin son Manubiya..duk yadda ya yi ta denying yana kaucewa,a iya jiya kad’ai ya tabbatar k’aunar ta yake yi k’auna ba ta wasa ba,amma kuma taya zai fad’a mata abun da ko Najeeb yana tunanin anya zai iya fad’awa kuwa,numfashi ya fesar ya nemi guri ya zauna a ran sa yace ‘’Yashjub a yadda kake son Manubiya b’oye b’oye ba na ka bane ba,’’domin
shi kan sa ya san yana da buk’atar wani abun ya faru soon…a fahimci juna a yi aure tun kafin son ta ya zautar da shi sannan ga wannan cousin d’in nata da ya ga take taken kamar shima son ta yake yi,kasancewar sa na gida ne ya sanya Yashjub yake ganin gara ya d’auke Manubiya tun wuri tun kafin iyayen ta su yi abun da zai kai sa lahira ta hanyar aura mata Abbakar.A part from all these a yanda yake jin Manubiya a zuciyar sa da ransa to tabbas
ba ya jin zai iya ci gaba da rayuwa daga nan zuwa watanni hud’u ko uku gaba ba tare daya mallake ta a matsayin matar sa ba…..

Da wannan tunanin ya shirya ya fice office,ko Daddy bai tsaya jira ba dan yana buk’atar ya yi tunani sosai sannan ya san ta inda zai fara Kafin Daddy ya zo su fara aiki,kuma yana da buk’atar lek’awa d’ayan company d’in nasa duk a yau.
……
Manubiya tana ajjiye wayar ta juya kenan suka yi ido biyu da Maamaa,da sauri ta sunkuyar da kanta k’asa kafin tace’’Maamaa Ina kwana.’’sai kuma ta fara k’ok’arin fita daga kitchen d’in.
Murmushi Mama tayi kafin ta ce’’ni kam Manubiya tsoro na kikeyi ne?naga kwata kwata kin k’i ki yarda ki saki jiki da ni ga shi kuma k’addara ta had’a mu zama guri d’aya,ya kenan?’’
Ta k’arashe maganar tata da tambaya tana murmushi.


Murmushi Manubiya tayi
kafin a ranta tace
‘’Tabbas k’addara ta had’a ni zama guri d’aya bama da ke kad’ai ba har da wanda nake
gudun ki domin shi.’’
A fili kuma sai tace
‘’Ba komai Maama ba gudun ki nake yi ba kawai dai abubuwan ne suka d’an yi min yawa,shiyasa.’’

Cikin rashin jin dad’i Maama tace’’Ayya!na ji Ammi tana cewa maman ki ma ba lafiya ko?’’
Ahankali Manubiya ta d’aga kanta alamun’’eh’’

Cikin tsananin jin tausayin ta
Inna tace
‘’Allah ya bata lafiya Allah ya sauwwak’e,ku yi ta addu’a za ta warke inshaaAllah kin ji ko?’’

Ahankali ta jinjina mata kai tukunna tace ‘’nagode Maama’’
ta fad’a hakan tana mai Jin tsananin k’aunar matar tana shiga ranta.

Murmushi Mama ta yi ta matso ta d’an shafa fuskar Manubiya
tukunna tace
‘’Allah ya miki albarka’’daga nan ta wuce ta fita daga kitchen d’in..so gamon jini,ita dai haka kurum Ubangiji ya d’aura mata k’aunar yarinyar
tana jinta ne har cikin ranta…….







MANNUBIYA
28

Na
Humayrah Bulama

Mikiya Writers Association.

Har wajajen 11 shiru babu Daddy ba Yasira a company,bak’in da suka yi
ma Yashjub ne yayi handling d’in su shi kad’ai,gashi yana ta kiran number Daddy baya d’auka ita kuma Yasira nambobinta duk basa shiga.
Dan haka bak’in suna tafiya
shima ya kamo hanyar gida.

Sai k’arfe 10 tukunna likitocin da suka karb’i Yasmeen suka fito,cikin son fahimtar da su
Babban likitan ya kalle su yace
‘It’s nothing serious,bai tab’a komai ba kawai dai d’an kurjewa tayi shiyasa kuka ga jini,abun nata dama ina so in ba ta sabo shine kawai muka tsaya aka d’an yi dressing wajen na bata sabo na bata drugs da 1 week off ta huta a gida,
Allah ya kare gaba.’’

Cikin samun relief dukkan su suka ce ‘’Ameen’’sai a lokacin tukunna Yasira ta d’au waya ta kira Mommy take gaya mata komai.
Office Yasira ta wuce
Yusra da Ya’isha da Yadira kuma school,yayin da Daddy da Kausar suka kama hanya domin maida Yasmeen gida.
Suna shiga Daddy ya ce wa Kausar ta kai Yasmeen d’akin ta shi kuma ya nufi b’angaren Ummi,bai same ta a d’akin nata ba ashe ya baro ta a k’asa a d’akin Yahanasu wadda zazzab’i ya rufe tun jiya da daddare ba wanda ya sani.
Munirat ya tarar tana share d’akin,cike da girmamawa ta durk’usa har k’asa ta gaida shi,ba yabo ba fallasa ya amsa
kafin yace mata’’Ina saddik’a?’’
Ahanakali tace ma sa
‘’Tana d’akin Yahanasu wadda batada lafiya’’
A ranta tana mamakin Allah dai yasa lafiya dan bata tab’a ganin shi by this time a gida ba
kuma a side d’in Ummi.
Cikin fushi ya juya da niyyar fita a bakin k’ofa suka yi kicibis da Ummi wadda taji shigowar su ta biyo domin ta ji ya jikin Yasmeen d’in,tun da suka fita ta ke trying numbers d’in sa,saboda ita shi kuma ya saka wayoyinshi gaba d’aya a silent..

Da kyar Daddy ya iya cewa
‘’Munirat give us a moment’’ya fad’a hakan idanuwan sa a kan Ummi,ba tare da ya kalli munirat d’in ba.

Da sauri ta ajjiye parker da abun sharar ta fice daga d’akin,tana tafe tana waiwaye gaba d’aya hankalin ta a tashe
tana mamakin me ya had’a su haka dan ita Ummi bata ce mata komai ba tun dazu,gashi
taga ran Daddy a mugun b’ace
ba abun da yafi d’aga mata hankali irin yadda taga mood d’in nasa kar taje ya bugi Umminta,tana tafe tana waiwaye haka ta fice a parlourn bata yi auni ba kawai ta ji ta afka kan mutum,da sauri ta ce ‘‘Innalillahi’’
sai kuma ta fara k’ok’arin kwace kanta daga rikon da Yassir yayi mata.
Tunda ta taho tana kallon baya ya ganta dan lokacin dai dai shi kuma ya fito daga corridor na side d’in Mommy kenan,ahankali ya wani lumshe ido ya bud’e saboda yauma riga da wando ke jikin ta na bacci irin me bin jikin nan rigar iya cinya wandon kuma har k’asa,dan haka a ran sa yace ‘’lucky me’’
Ganin bata gan sa ba ne ya sanya shi sake nutsuwa yak’i motsi gudun kar ya ankarar da ita,ai kuwa da ikon Allah ta afka jikin sa,
Without thinking twice shi kuwa ya rungume ta gamgam,tana d’agowa suka yi ido biyu da shi,cikin tsananin firgici tace’’get off me,ka cika ni baka da hankali ne’’
Ta k’arashe maganar cikin tsawa.

Wani irin murmushi yayi kafin yace
‘’Munirat yo ai ko malaikan mutuwa ne yazo d’aukar raina
to
Sai ya d’aga min k’afa na gama appreciating moment d’innan
tukunna ..’’

Wani irin kuka ta saka kafin ta fara k’ok’arin kwace kanta tana magiya tana kai masa duka,ganin ta na neman cika masa kunne ne ya sanya ya fara k’ok’arin kissing d’inta.
A gigice ta kwala wata mahaukaciyar k’ara daidai shima Yashjub yace
‘’Yassir’’
Cikin tsawa
………….
Achan d’aki kuwa Munirat tana fita
Daddy yacewa Ummi ‘’Ki had’a kayan ki, duk wani abu da kika san naki ne ki tartare ki bar min gidana’’

Ahankali Ummi tace
‘‘Daddy har me yayi zafi haka?
Wallahi Kausar k’arya take yi ban san Yasmeen tana da matsala a kunne ba
sannan ya kamata ka tsaya kaji abun da yaran nan suka yi min

Please Login or Register in order to submit comment