Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ko nace masa kace ba sai mun zo ba bazai bari ba
kuma nima inason inyi maka godiyar dan ban samu nayi maka a asibiti ba’’

Shiruuu ya d’anyi har saida ta zare wayar daga kunnenta ta kalla taga still yana kan layin
kafin taji yace’’Nikam ba godiya nake buk’ata daga wajen ki ba
Akwai abunda nake da buk’ata amman sai face to face tukunna zan fad’a miki.
Allah ya kaimu goben inanan’’
‘’akwai aiki dama kinga gobe sai ki nunamin,daganan in mun kammala sai in gaya miki tukuicin danake so a bani,’’

Shiruu tayi har sai da yace ‘’Mannubiya’’
Tukunna tace ‘’to,amma fa ba aiki mutum d’aya ne kawai sannan ya akayi ka sani?’’

Murmushi yayi yace ‘’aikin nasa is important’’

Shiruu ta kuma yi kafin tace
‘’Ai be kamata ka tamabayi tukuici da kanka ba,nice zan ga dama in bayar kuma bai ma gama zama ready ba’’

Dariya yayi yana jiyo wauta a maganar ta ta kafin yace’’banaso ki siyamin komai
In ma wani abun kike shirin siya although naji dadi kuma na gode
amman I’m serious bana son ki siyamin komai
Ni a d’abiata in nayi abu ni zan fad’i tukuicin da nakeso’’


Shiruu tayi kafin tace
Iyakar maidamin zuwan nawa sau biyu da kayi a wannan satin a ganina ai ya ishi tukuici

‘’Um um bai Isa ba,sannan ai ba iya wannan satin nace ba,zuwan ki ya dawo sau biyu kenan Friday and Sunday’’yace hakan yana murmushi

Turo baki tayi kamr tana gaban sa sai kuma tayi shiruu tana tunani kafin ta samu tayi kokawa da zuciyar ta datake ta faman d’aurata akan tunanin abunda zai fad’a mata goben
ahankali tace ‘’bara in duba inna sai da safe’’

Sai da ya d’an d’auki lokaci tukunna yace ‘’dare bai yi sosai ba ko?in ba damuwa inaso mu gaisa’’

Ahankali
Ta sauk’e ajiyar zuciya kafin tace’’ai bata da lafiya’’

‘’Eh Najeeb ya fad’a min kuwa…Allah ya bata lafiya,bata wayar inyi mata ya jikki’’
Ya sake insisting a karo na biyu.

Saida Manubiya ta d’an lumshe idanuwanta ta bud’e tukunna tace ‘’ai bata magana bata iya yin komai’’

Dasauri yace ‘’subahanallah
Stroke?’’
Yayi mata tambayar a d’an rikice

Ahankali tace masa’’eh’’

Shiruu yayi yana nazari kafin yace ‘’wanne physiotherapist d’in take gani?’’

Ahankali ba dan ta so ba tace mishi ‘’in mun kaita tana ganin normal doctor’’

Zuwa yanzu ya fara fahimtar wasu abun dan haka ahankali yace ‘’wanne asibiti take zuwa da magungunan da take sha?’’

Sai da ta sauk’e y’ar siririyar ajiyar zuciya tukunna tace ‘’asibitin murtala’’

Ahankali ya lumshe idanuwan shi yana jin tsananin tausayin ta yana ratsa shi ji yake yi kamar yayi mata kuka

Sai da tace bara inje sai da safe tukunna dakyar yace
‘’Ok’’sai kuma yace ‘’zan iya kiran ki nan da 3O minutes dare bai yi ba?’’

Ahankali tace ‘’tam ba damuwa’’daganan sukayi sallama
Tana mamakin tsantsar tausayin ta itada ahalinta tare da kulawa data jiyo a muryar sa.

Ba ‘a cika mintuna ashirin ba ya kirata yace ‘’gobe su shirya around 8 akwai babbar likitar da yayi booking zatazo ta duba innar zata tafi da ita asibitin ta a goben in kuma ta dawo gida zata dinga zuwa kullum ita ko wakilliyarta tana duba innar ‘’
Daganan yace ‘’ta tura masa adress d’in gidan nasu zai turawa likitar’’

Shiruu Manu tayi dan ita har ga Allah batayi tunanin likita zai kira a daren ba besides batamayi tunanin abun zai damesa har haka ba…ta ji dad’i matuk’a daya damu da damuwarta kuma taji dad’i da innar tasu zata samu special treatment tasan InshaaAllah da taimakon ubangiji zata warke wanda hakan shine babban burinta itada y’an uwanta a halin yanzu(inna ta warke),to amma kuma sai take gani kamar d’awainiyar da Yashjub d’in yake yi dasu ta yi yawa,ba wai ko dan tana tunanin zata d’aura masa nauyi ko kuma aljihun sa zaiyi k’asa ba dan tasan hakan ba zai tab’a aljihun sa ta koina ba tunda ya riga ya tara,kawai dau tanaganin kamar in hakan ta faru su d’in za’a ga kamar sun zira jiki sun sakankance dashi dayawa,kar kuma aga kamar ko kwad’…..’’

Muryar sa ce ta katseta jin yana cewa’’she’s very good doctor d’in karki damu inshaaAllah innarmu ta kusa wrkewa’’
Ajiyar zuciya ta sauk’e kafin ahankali tace ‘’bansan ta Ina zan fara yi maka godiya ba’’

Cikin katseta yace’’Mannubiya tsakani na dake babu godiya’’
Sai kuma ya d’anyi murmushi yace’’kawai dai tukuicin danake da shirin tambayar ki gobe ne nake addu’ar Allah yasa karki ce A’a’’
Ahankali taji ya sauk’e ajiyar zuciya kafin yace
‘’good 9te sweet dreams’’Ahankali kamar itama bataso yaji tace ‘’good nyt’’
Murmushi kawai taji yayi daganan suka yanke kiran a tare kowannen su yana yi kamar bayaso.


Yana katse wayar ya ya kwanta rigingine akan gadon
yana wani kalar murmushi….k’arar wayar sa ce ta katse sa,yana d’auka da ya kalla kawai sai ya maida kanshi ya kwanta ba tare daya amsa ba
yana mai jin mood d’in shi yana chanjawa….tun d’azu Mommy take kiran sa tun yana wayar da Manubiya har yayi da doctor ya koma ya sake yi da Manubiya.
Shi da farko ma bai san ita bace dan bai duba mai kiran ba sai da ya gama fixing appointment da doctor tukunna yaga ashe ita ce.
Yasan ba wani abun bane kawai wayar dataji yana yi ne ya kuma d’aga mata hankali tunda tun daga d’azun har zuwa yanzu bata d’aga k’afa na minti uku ba,kiran sa kawai take ta yi akai akai….ya san yana d’auka zata fara tambayar sa dawa yake waya kamar wani k’aramin Yaro,ba zai iya yi mata dogon bayani ba gaskiya gashi kuma dama a fusace yake da ita.
Zai san abun da zai fad’a mata dan har ga Allah sai komai ya kammala tukunna zataji saboda he don’t trust Mommy when it comes to Kausar sarai ya ji abunda Kausar d’in take fad’a mata aranar dayaje sama wajen Mommyn zai yi mata magana akan ‘karta sake turo masa Kausar side d’in sa’,Shiyasa ya yanke akan ba zasu ji yanzu ba sai Daddy ya amince komai ya kammala tukunna,sannan bayaga wannan dalilin ma yanada reasons dayawa.
Kiran wayar ne ya sake shigowa dan haka ya kalla ya sake d’auke kai,har ga Allah baisan me zai ce mata ba in ya d’auka,shiyasa ya bari akan in ya gama deciding zai saurareta but ba yanzu ba dan baya so ta chanja mishi mood d’in shi na yanzu
Yasan abunda yakeyi baya kyauta wa amman itama Mommy bata kyauta mishi ba
Ba zai iya yi mata dariya ko ya sake mata ba,yana jin zafin ta still har yanzu.….she slapped him a gaban k’annen sa sannan ta fifita Yassir sama da shi har gobe in ya tuno maganganun ta ji yake kamar yayi kuka,abun yayi masa ciwo sosai ya tsaya a ransa ya kasa mantawa.

Cikin son kawar da tunanin ya maida hankalin shi ga Manubiya,tausayinta gaba d’aya ya hana shi sukuni Ahankali yace’’Allah ya sa a dace da treatment din doctor sofia a samu mshaifiyarta ta warke ta fara magana’’yana wannan tunanin text na adress d’inta ya shigo wayar sa dan haka ya turawa Dr sofia d’aga haka ya mik’e ya fice.

Wajen Daddy ya fara biyawa ya bashi hak’uri sosai tukunna yayi masa sai da safe ya wuce .

Yasan cewa uwa daban take kuma tanada daraja shiyasa shiyasa duk yadda yaso sai ya gagara wuce side d’inta ba tare da ya shiga ba yasan hakan bai kamata ba duba da yadda tayi ta kiranshi ma yak’i d’auka

Ba dan ran sa yana so ba
haka ya k’arasa bak’in k’ofar side d’in nata ya shige cikin parlourn ya wuce bedroom d’inta
murd’a k’ofar yayi amman ga mamakin sa sai yaji ta a rufe

Yana shirin fara knocking yaji magana k’asa k’asa kamar zai tsaya kuma sai ya juya kawai ya fita dan ya san ita da Baaba larai ne kuma magana mai mahimmanci sukeyi tunda har ya mud’a handle amman suka gagara lura

Da wannan tunanin ya fice ya nufi d’akin Yahanasu yana mamakin yadda sam bayajin Mommy a jikin shi dan har ga Allah shi kansa abun yana damun sa,kwata kwata baya jin ta kamar yadda yakejin Daddy da su Yasira abunda kamata yayi ma ace yafi jinta a zuciyar sa fiye da kowa tunda ita soyayyar uwa daban take
Har a bakin ka’aba yayi addua Allah ya saka masa soyayyar mahaifiyar sa a zuciyar sa
saboda kar yaje shi bai sani ba rashin shak’uwar su ta ja yayi wani abun da za ta ji haushi taga kamar baya kula da ita yadda ya kamata yaje ya fad’a halaka

Shiyasa ko da yaushe yake iyakar bakin k’ok’arin sa ya samu ya jata a jiki ita kuma gashi yanzu tazo ta kuma bak’anta masa rai akan Yasir
da sauri ya kawar da tunanin a saboda in ya tuna ma ransa sake dagulewa yakeyi
maganganun data farfad’a a ranar sun tsaya masa a rai matuk’a…..

Cikin takunsa ya k’arasa dak’in Yahansu bayan ya gama yankewa sai Daddy ya gama hucewa tukunna maybe gobe ya same sa da maganar Manubiya.

Yasan bashida matsala tunda Daddy da bakin sa ya sha gaya musu cewa’’ ko wanene ko wacece suka kawo zai aura musu a duk lokacin da suke so in dai tarbiyyan su yayi masa’’but still yana adduar Allah yasa ya dace kar Daddy yayi disappointing d’in sa.

Sai da ya shiga da sallama tukunna yad’an sake yi mata knocking dan yaga kamar ma bata san ya shigo ba,akan tebur ya hangeta ta barbaza takardu da alamun aiki takeyi.

Glasses d’in idonta ta zare ta mik’e ta nufesa tana murmushi,a gefen gado ta zauna tukunna tace masa’’Bismillah’’tayi maganar tana nuna masa gefenta,
ganin yadda ya tsura mata ido

Sai a sannan ya d’an sauk’e ajiyar zuciya yana me zama a gefen nata yace’’baki gama warkewa ba amma kika zauna aiki har twelve?ya jikin naki?’’
Yayi mata tambayar yana kallon ta

Murmushi kawai tayi kafin tace
‘’Alhamdulillah’’

Zata yi magana ya katseta ta hanyar cewa
‘’Tunani kike yi ko?har yanzu kin k’i ki kwantar da hankalinki’’

Murmushi tayi kafin tace
‘’Bafa na tunanin komai Yash,mu bar maganar nan yanzu fad’amin meye kake so ka gayamin’’
Ta fad’i hakan da murmushi kwance akan fuskarta.

D’an k’ura mata ido yayi kafin yace’’Mun fara b’oye b’oye a tsakanin mu kenan!
You know you can talk to me right?,ki kwantar da hankalinki dan Allah Yahanasu,ni wallahi har ga Allah banga wani tsufan da kikayi ba meye marabar ki ke da su Kausar d’in??
Kausar is getting up to 28 fa haka ma Yassira ita tama yi 28 d’in
meye marabar ku da zaki bi ki d’aga hankalinki ??’’


Ahankali tace
‘’Yash ba zaka gane ba na tare musu hanya in ban wuce ba taya za su yi feeling comfortable su wuce ???’’

K’ura mata ido yayi wanda har saida ya sanyata d’an sunkuyar da kanta kafin yace
‘’Mommy ko Baaba Larai wani ya gaya miki haka ko?ko kuma su Kaisar d’in?’’

‘’Yash dan Allah mu bar maganar nan kasan dai yadda nakeji in ana irin wannan maganar ka bar maganar kawai’’

Ajiyar zuciya ya sauk’e tukunna yace’’ok naji zan bar maganar
amman sai kinyi min alk’awarin kin daina tunani kuma kin daina keeping things from me
In kinada damuwa share it with me zakiji sanyi a ranki!zama a d’aki ke kad’ai kina dealing da problems d’in ki ba abunda zai ja miki sai depression
ki kwantar da hankalinki
Aure nufi ne na Ubangiji
yanzu fa zaki ma fara 30s d’in ki Yahanasu yanzu ne ma fa kika zama lady,kar ki biyewa al’adar Bahaushe ki kashe kanki kalli yadda kika rame fa.’’

Hawayen daya zubo mata ta ido d’aya ta sa hannu ta share kafin tace’’Yash,dole abun ya dameni….tun Ina 15 years nake so inga nayi aure so nayi Ina gama secondary school ace na yi aurena
ba wai dan komai ba
kawai ni inaso inga nayi aure na haihu na kula da family d’ina amma kalle ni har yanzu

Ajiyar zuciya ya sauk’e ya matso kusa da ita ya kama kafad’unta tukunna
yace’’look at me Yaha’’
Sai da ta d’ago ta kalleshi tukunna yace
‘’Bawa kowa da akwai tashi kalar k’addarar ki d’auka ke wannan ce taki
Ubangiji dama yakan jarabcemu da abunda muke matukar so,zamu samu delay but da ikon shi in mukayi hak’uri sai kiga mun samu har ma da k’ari.
Ki godewa Allah daya jarabceki a yanzu ba sai kin tsufa ba saboda a kullum Ina yi miki addua InshaaAllah wannan ita kad’ai ce mummunar k’addarar ki kuma itama inshaaAllah kwanan nan zaki yi auren ki komai ya daidaita.
InshaaAllah zaki samu mutum mai hankali mai tsananin k’aunar ki kiyi aure ki hayayyafa hankalin ki ya ya kwanta ki samu kwanciyar hankalin da inkika tuna kin tab’a shiga wannan damuwar ma sai ki nemi b’acin ran da kika shiga a yanzu ki rasa kiji kamar bai tab’a faruwa ba.
InshaaAllah zaki samu enough farin ciki a gaba wanda zai goge duk wannan bak’in cikin da kike a ciki,for now ki rungumi k’addararki ki cinye jarabawarki ki kwantar da hankalinki kinji?’’


Ahankali ta jinjina kai ta goge hawayenta tace’’Thankyou Yash Thankyou so much’’

‘’You are welcome’’yace yana murmushi kafin ya cikata
Yace’’good news but promise me ba zaki fad’awa kowa ba for now saboda inaso sai komai ya kankama kafin kowa yaji’’


Tana wani fad’add’en murmushi ta d’aga mishi kai tace ‘’I Promise’’

Wani kalar blushing taga yana yi kafin yace’’kin kusa kiyi k’anwa
InshaaAllah inaga next month ko maybe kafin month ma zanyi aure in Daddy da ita kanta yarinyar ta bani dama’’

Yahanasu batasan lokacin data ce ‘’what!!’’ba
Tana mai zaro idanun ta
Kafin ta d’aura da cewa’’eh lalle Manubiya ta ciri tuta,’’

Ahankali ya yi murmushi yace’’eh ki tayani da addu’a da k’ok’ari a yi auren nan kamar yadda na tsara da sauri saboda Manubiya ta riga ta sace zuciya ta’’

Dariya sosai Yahanasu tayi kafin ta mik’e tace ina zuwa tukunna ta Isa jikin k’ofa ta bud’e ta d’an duba tare da sak’ala key saboda yadda jikinta ya bata akwai mutum a wajen.

Tana dawowa ta zauna kafin tace
‘’Yanzu tou ya ake ciki ?
Itama ta amince ne,sannan Yash kana ganin k’in gayawa su Mommy bazai jawo wata matsalar ba ?
kar suga ka b’oye musu ka gaya musu a k’urarren lokaci kasan ba zasuji dad’i ba,zasuce bama su san kana da budurwar ba nasan in suka ji aure kwatsam zasuga kamar ka b’oye musu ne ko wani abu makamancin haka’’

Iska ya fesar kafin yace ‘’Yaha kinsan abunda na gaya miki kwanaki akan Kausar
In ta ji labarin Inada budurwa aiki ne kuma kinsan Mommy bayanta zata bi
So
Pls ki bar maganar nan dan ni banaso ma Ina tuna abunda naji ranar Kausar d’in ta fad’a a kaina wallahi raina b’aci yake yi
Maganar Manubiya kuma gobe zan gaya mata
dai
inshaaAllah Ina fatan Allah yasa ta amince da ni
dan ba zan ma iya tunanin wai bata amince d’in ba, Ina adduar Allah yasa zargina ya zamo gaskiya dan naga kamar itama tana so na.
In komai ya kammala za ai auren ciki gaggawa dan bazan tsaya Mommy ko Kausar wata ta kawomin cikas ba

Murmushi yahanasu tayi kafin tace’’na fahimceka kuma inshaaAllah baza a samu matsalar komai ba
sannan nasan dole ma Manubiya tace maka yes goben nan dan
banajin a kaf fad’in duniyar nan akwai macen da zatak’i amincewa da lil bro d’ina’’

Dariya yayi kafin ya d’an harare ta sannan yace’’lil bro? ko cikakkaiyar awa d’aya fa baki bani ba’’

‘’Amma dai na girme ka ko second d’aya ne na dai girme ka’’

Dariya duk sukayi kafin Yahanasu tace ‘’amma ta ya kake tunanin iyayen ita Manubiyan zasu amince su aura maka y’ar su a cikin wata d’aya kmr yadda ka fad’a ?ko zaka d’an d’aga k’afa ko wata uku hak….’’

Girgiza kai kawai yayi kafin yace ‘’gaskiya bazan iya ba
dukda bansan ta ya za’ayi su yarda da auren a haka ba amma zan yi ta addu’a kema ki tayani,’’
Yayi mata maganar cikin yin kalar tausayi har da wani karyar da wuya

Tausayi da dariya ya bata dan
haka tace ‘’inshaaAllah komai zai tafi yadda kake so’’

Ahankali yace ‘‘Allah yasa daga nan suka shiga tattaunawa….’’

Yahansu tasan menene so duba da yadda itama ta so first love d’inta kamar ranta saurayin daya fara dumping d’inta
Shiyasa yanzu sam bata ganin laifin Yashjub da ya haukace akan Manubiya
Adduar ta d’aya Allah yasa a bashi ita ayi auren kmr yanda suketa tsarawa yanzun Allah yasa kar su Mommy su kawo cikas d’in komai.

Yash yana k’aunar y’ar uwar tasa sosai..ya lura da yanda su Yasira basa janta a jiki..dukda baisan wasu daga ciki hanatarar da suke yi mata ba
amman yana yawan tsawatar musu da nuna musu gaskiya
kawai dai yasan tunda suka riga suka nuna basa sonta ba lalle ya iya fixing d’in su su dawo su k’aunace yadda ya kamata ba. Yanaso tayi feeling special itama ta ji tanada dan uwa me kaunar a ko da yaushe
kuma har ga Allah ita kad’aice zai yi shawara da ita ya ji dad’i dan sun saba sosai shiaysa yanzun ma yake ta neman shawarwarin ta,ta kuwa ji dad’i
tun ba ma daya ce itace zata had’a masa lefe…bata san lokacin data fashe da kuka ba.

Takan yi kukan rashin jituwa tsakaninta da y’an uwanta mata amma in ta tuna tanada Yash sai ta ji duk damuwar ta ta Kau

Batajin a duniya akwai d’an uwan da yake tsananin k’aunar y’ar uwarshi kamar yanda Yash yakeji da ita ko shawara ce da ita yakeyi
Ko mene ne sai ya gaya mata,shiyasa har yau har gobe ta kasa yafewa kanta duba da yadda ita ta kasa gaya masa the most important abu a rayuwar sa bayan ta sani kuma tanada ikon ta taimaka mishi wajen samun abunda ta san zai sanya shi farinciki fiye da komai…..
Ta jima tana kuka har sai da ta
d’an fara bawa Yash tsoro

Tukunna ya lallasheta dakyar
ya d’an jata da wasa da hira
daga nan suka shiga wata maganar,Kafin daga baya yayi mata sallama ya tafi bayan ya samu ta hak’ura ta karb’i number Manubiya kawai
dan da cewa tayi sai ya kira mata ita sunyi video call
da kyar ya lallab’ata ta hanyar ce mata’’Manu tayi bacci by now.’’daga haka suka yi sallama ya tafi.



……..2 hours before now………

Ummi bata wani dad’e a wajen su Mommy ba ta fita ta wuce d’akin ta,bata dad’e da fita ba su Yassira suka shigo suka taru a d’akin har Yasmeen kamar wasu masu meeting,Mommy ce ta cewa Yasira ita da Kausar suje su saka mata ido a k’ofar Yahanasu,dan tasan tun da ya ce yanaso yayi magana da Yahanasu yau to komin dare sai yaje sun yi kuma ta maganar ta su ne kawai zasu samu haske akan zargin nasu.

Ba k’aramin tashin hankali ta sake shiga ba lokacin da ta kira sa taji yana waya,kawai ita ta yadda ta gama amincewa ta bada amanna akan maganar Baba larai,shiyasa kwata kwata kwakwalwarta bata bata cewa ai waya yake akan business ko wani abun ba
tashi d’aya ta amince da wannan yarinyar yake waya kawai.

Yassira ce ta samu ta ga Yash d’in dan Kausar ta saman balcony ta tsaya tana jiranshi ta yadda yana fito wa daga side d’in shi itakuma zata jira ya shige d’akin Yahanasu sai taje ta lab’e saboda tafi kowa k’aguwa taji menene asalin maganar amma sai Allah bai bata ikon ganin shi ba dan lokacin daidai yazo zai wuce sai aka yi mata text dan haka bata ga shigar sa ba.

A kitchen Yasira ta jira har ya gama da wajen Daddy ya sauk’o ya shiga d’akin Yahansu ,tana ganin ya shige ya turo k’ofar ta fito ta Isa bakin k’ofar da sauri ta lab’e.


Shiruu Yassirar tayi tana sauraron su…wato dai zargin su ya tabbata on top of that kuma aure cikin wata d’aya ma yake son yi taya zasu iya
cin nasara akan wannan abu da ya taho gadan gadan haka?.
Babu tausayin wadda ya lullub’eta sai Kausar!saboda zuwa yanzu in Kausar d’in in tayi wani abun har mamaki take bata,kamar
wata wadda ta fara samun tab’un hankali haka so da k’aunar Yash suka maida ita sam Bata ji bata gani when it comes to him…
Tana cikin wannan tunanin taji Yahanasu zata bud’e k’ofar
dan haka ta yi sauri ta wuce ta
tayi sauri ta wuce ta fad’a kitchen.

……Now……
Sai da Yassira taji fitar Yash tukunna ta fito tana ji kamar zuciyar ta zata tarwatse
ta nufi sama.




MANNUBIYA
44
Na
Humayrah Bulama

Mikiya Writers Association.

Kausar na saman balcony ta hango fitar Yash,ta yi mamakin rashin ganin shigar sa da batayi ba dan haka ta fito da sauri tana adduar Allah yasa Yassira ta samu ikon saurarar su.Dai dai tana fitowa ta hangi Yassirar ta nufi side d’in Mommy a rikice dan ko lura da fitowar Kausar d’in ma bata yi ba.

Da k’arfi k’irjin Kausar ya buga yayinda k’afafuwanta suka fara karkarwa,da kyar ta samu ta tattaro gaba d’aya kuzarinta
ta bi bayan Yassira tanajin kamar zata fad’i a k’asa dan tabbas wannan rikicewar data ga Yassira tayi tou akwai matsala kenan.



Yassira tana shiga d’akin Mommy,duk suka mik’e tsaye!dama gaba d’ayan su sun taru
Yusra da Yadira ne kawai babu

Yasmeen ce ta matso kusa da ita tace
‘’Lafiyan ki kuwa?me ya faru?’’

Wani k’ululu da ya tokare mata mak’oshi ta hadiye tukunna dakyar tace’’Ya‘isha ku d’an fita Ina son magana da Mommy ita kad’ai’’

Cikin d’an b’acin rai Baaba Larai tace’’zancen banza kenan,waye kika gani bare a ciki mu?’’

Ahankali Yasira ta lumshe idanunta ta bud’e tanajin tsananin tausayin Kausar har ma da Mommy suna lullub’eta,kafin tace’’Ba haka bane Baaba,banason maganar ta yayatu da yawa ne gudun kar wata a cikin ku tayi spilling beans ma Kausar.’’


Dai dai nan Kausar wadda ta k’araso bakin k’ofar d’akin Mommy taja ta tsaya,tabbas a yadda ta ga Yasira d’azu da kuma yanda taji muryarta a yanzu da abunda ta ji ta fad’a,ta san in ta ganta bazata fad’a mata komai ba no matterwhat,shiyasa ta yanke shawarar lab’ewa a wajen

Ahanakali Mommy wadda gabanta ya fara fad’uwa ta k’arasa inda Yassira take tace
‘’Yi magana Yassira,ko menene fad’i,we can deal with it!me ya faru?wacce maganar kikaji Yash suna yi da Yahanasu?’’

Dafe kai Yassira tayi ta matsa gefe ta d’an runtse idanunta tayi shiru kafin ta bud’e tace
‘’It’s just so sad!ace lokaci d’aya gaba d’aya hard work d’inku na shekaru dayawa ya tarwatse ba tare da mun ci riba ko d’aya ba’’

Dasauri Mommy ta ruk’o ta ta juyo da ita sannan tace
‘’Yassira inason next maganar da zata fito daga bakinki ta tafi direct to the point!ki fad’amin abunda ya faru tun wuri saboda rai na ya fara b’aci.’’

Kallon ta Yasirar tayi kafin tace’’Bakiji b’acin rai ba
Mommy sai na ce miki Yash zai yi aure!kuma nan da one month naji yace kinga kuwa an gama komai kenan…ba maganar budurwa ake yi ba yanzu maganar aure akeyi’’

Cikata tayi da sauri sai kuma ta k’ame sam ta kasa motsi


Cikin takaici Yassira tace
‘’Yes Mommy,Yash zai yi aure
ba tare da kun fahinci juna ke da shi ba,ba tare da mun samu damar amso uban dukiyar da Daddy ya mallaka masa ba,ba tare da ya damu ko ya had’a kai da d’aya daga cikin mu ba
Sannan above all zai auri wadda bamu sani ba kuma
ga dukkan alamu yana matuk’ar sonta da k’aunarta kinga kuwa zuwa nan da y’an shekaru komai ya zama nata daga ita sai ya’yan su
mu kuma sai dai kallo!’’

Cikin fushi Mommy tace
‘’Yi shiru Yassira ya Isa haka!’’

‘’Y?saboda meyasa zan yi shiru?bakya son ji ne?ai gaskiya na fad’a in ba haka ba Mommy ki dubafa

Please Login or Register in order to submit comment