Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ka bata wayarta muna son ta kira Yasir ya kamata ace yayi hak’uri haka ya dawo gida naga alama Daddyn ku yana k’ok’arin mantawa dashi a cikin ya’yan sa’’.

Tunda Mommy ta fara magana idon Yashjub yana kan Kausar
wadda ta sunkuyar da kanta k’asa,wata kalar hararar tsana yake jifan ta da shi.
Ahankali Mommy ta d’an kamo hannunshi tace
‘’Kaji Yash,d’an uwanka ne kar
mahaifinku yayi zuciya ta har abada dashi ata dalilin shirmen nan na sa,ka bata wayoyin ta ta kira sa,in ta kira shi zai dawo.’’
Sai yanzu ya d’auke idonshi daga kan Kausar ya maida kan Mommy tukunna yace
‘’Na san inda yake,anjima zan je in taho dashi
Dan naga alama absence d’in sa yana k’ok’arin janyomin bala’i’’.

Shiruu duk su biyun sukayi
Mommy tana adduar Allah yasa ba maganar su ta yanzu itada Kausar yaji ba,
Kausar kuma tana adduar Allah yasa yaji d’in.

Muryarshi ce ta katsewa duk su biyun tunani
Jin yana cewa
‘’Mommy dan Allah dan annabi kar ki sake turomin yarinyar nan zan kawo miki phones d’in nata da komai anjima,
Ina shikenan?’’
Yayi maganar yana mai d’aga hannun shi duka biyu da gira d’aya.
Murmushi Mommy tayi
sannan tasa hannu ta shafa kumatun shi ahankali tana murmushin tace
‘’Shikenan son,shikenan na gode’’.
Kama hannun Mommy Wanda yake a ke fuskar sa yayi kawai yana kallon ta,
Itanma shi take kallo tana nazartar shi
So take ta gano yaji zancen nasu ko a ‘a.
Bai bata dama ba kuwa dan k’asa yayi da kan sa ya furzar da iska ba tare daya ce uffan ba ya cika hannun nata ya juya ya fita ya nufi side d’insu bayan ya tsaya ya d’auki belongings d’insa daga motar sa
Ko shiga side d’in nasu dama bai yi ba ya nufi wajen Mommyn dan ba kad’an ba yaji haushin zuwan da Kausar tayi masa dazu da safe bagatatan…..





MANNUBIYA
19

Na
Humayrah Bulama

Elegant Online Writers.

Kamar kullum yau ma tare Abbakar da Manubiya suka fito
daga jarabawa,suna tafe yana bata labarin Baraka a jiya data je gidan su.
Adashe ta ke yi ashe ta kwashi nata har naira dubu d’ari uku a jiyan,ya na d’akin sa na soro yaji ita da maman shi da maman ta suna hirar ‘wai fili zata cika ta siya ta yi gini’.

Ahankali Manubiya ta sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya a fili tace’’Allah yasa tafi haka
Allah ya bata ikon siyan wasu filaye dayawa nan gaba..’’

‘’Abbakar!’’
Su kaji an kira sa

Cikin yanayin maganar sa ta masu sanyin jiki ya juya ya kalli mai kiran nasa yace
‘’Na’am’’.

Dariya saurayin yayi kafin yace ‘’ka bi ka dage wa k’awance da mace dama kai gaka ga yanayin ka yanzu kam ba marabar muryarka data mace,
ka je Sir Najeeb yana neman ka’’
Ya k’arashe maganar ta sa yana me tapping shoulder d’in Abbakar d’in daga nan yayi gaba ya wuce ya bar su nan tsaye.

Yana wuce wa Manubiya tace
‘’Allah yasa lafiya’’
Murmushi yayi yace ‘’InshaaAllah ma lafiya,muje sai mu ji menene’’
Dasauri tace
‘’Wa?Ni?tab!inaaaa..’’.
wata kalar harara yayi mata
kafin yace
‘’Ban gane ba,ba za ki raka ni ba?’’.
Cikin nemo mafita da sauri tace
Abbakar na fa gaya maka na bar aiki burjik a gidan Ammi,gashi yanzu 4har ya d’an wuce,dan Allah kayi hak’uri kar muje yau ma mu tarar yana da bak’o muyi ta zaman jiran sa in yi letti wajen Ammi,sannan ka ga ga karatun exams d’in jibi ta yau ma ta bani wahala wallahi.’’

Cikin sigar tsokana yace
‘’Ko dai ba kya so yau ma ki sake yin gamo da crush d’in ki ba.’’

Da sauri ta zaro ido sai kuma ta buga ma sa littafin hannun ta tana mai cewa
‘’To k’arya dak’ik’in tunanin ka ya baka,wallahi ba wani crush’’.
Dariya yayi yace
‘’Auch’’.yana sosa inda ta buga masa littafin sannan still yana dariyar yace
‘’Shikenan,ki je sai mun had’u gobe inshaaAllah.’’
Hararar sa tayi daganan ta juya ta wuce.
Ahankali ya sunkuyar da kan sa yana murmushi kafin ya d’aga kai yabi bayan ta da kallo,sai da ta b’ace wa ganin sa tukunna ya juya ya nufi office d’in Sir Najeeb…

Yana zuwa wajen ana shiga sallah sanin halin Sir Najeeb d’in ne yasa sai da yaje office d’in na sa ya tabbatar da baya nan tukunna ya nufi masallacin shima.
Yana shiga ya tarar dashi a sahun gaban sa.
Cikin nutsuwa aka gaba tar da sallar la’asar ana idar wa shi da wasu a cikin masallacin da suka rasa raka’a suka tashi domin ramawa masu addu’a kuma suna yi.

Yana idarwa shima yayi addu’a ya shafa daganan ya zauna zaman jiran Sir Najeeb
yana mai ha’dawa da adduar Allah dai yasa ba wani laifi ya kuma yi ba,dan bayan class rep in dai ka ganka a office d’in Sir Najeeb to ba k’aramin abu bane ba.
Ko wani abun ne ma kake da buk’atar yi ko gaya masa to daman an san ka’idarshi’ka gayawa class rep shi kuma ya fad’a ma sa’….

Ganin fitar sa ne ya sanya
Abbakar d’in mi’kewa da sauri ya bi bayan sa.
A bakin office d’in na sa suka had’u yana k’ok’arin bud’ewa dan haka yana bud’ewa suka shiga tare Abbakar ya shiga da sallama sannan ya shiga gaida shi da ladabi.
Cikin nutsuwa ya amsa masa
yana mai neman guri ya zauna akan d’aya daga cikin
sofa d’in dake a office d’in kafin ya d’ago ya kalle sa
ya ce ‘’d’an zauna.’’

Cikin d’an d’ari d’ari Abbakar ya nemi waje ya d’an d’osana mazaunin sa ya yi shiruu
zuciyar sa tana masa sak’e sak’e kala kala.

Shiruu shima Najeeb yayi yana tunanin ta ina ma zai fara ne,
Wallahi ba daban Yashjub bane Allah da babu abun da zai sa ya yi wannan abun
haba!student d’in sa fa abun is soo wani iri,amma ya ya iya dole ya daure ko ba komai shima yana so yaga Yashjub yayi settling kuma tun da har yaga Yashjub ya zo ya same sa a kan maganarta tou kuwa ya san abun is serious hakanne ya sa shima ba zai yarda yayi taking issue d’in likely ba.
Ahankali ya sauk’e ajiyar zuciya ya d’an yi gyaran murya
Wanda hakan ya sanya Abbakar ya mik’a masa
dukkan nin attention d’in sa.
Cikin nutsuwa Najeeb yace
‘‘About that your friend na kira ka,Manubiya.’’

Shiruuu Abbakar d’in yayi da farko
kafin a hankali yace’’Ok,Sir.’’
Dan zuwa yanzu
Kwakwalwar sa ta gama bashi
amsar dalilin kiran da aka yi masa.

‘’Tana da wata matsala ne?,as in family issue besides rashin lafiyar mahaifiyart?’’
..
Manubiya is his close frnd a ganin sa bai kamata ya kunce mata zani a kasuwa ba.
Dan haka yace
‘’A’a rashin lafiyar maman nata ne kawai issue d’in ta’’.

‘’Shiyasa take kuka kusan kullum a class?’’
Sir Najeeb ya sake jeho masa wata tambayar cikin katse sa.

Shiruu ne ya d’an biyo baya kafin Sir Najeeb d’in yace
‘’Kamar yadda na fad’a muku the other day
Malamai kamar iyaye suke,
a yadda na ke ganin ta so disturbed kullum nayi tunanin tanada financial issue ne.
Am nasan ba hurumin mu bane
but Aboki na daka gan mu tare ne yake da offer na aiki very simple wanda mace ko tsoho za su iya yi …
A Ta’kaice yayi wa Abbakar bayanin aikin dayaga damar had’awa a kan sa a yanzun nan kafin ya d’aura da cewa
‘’Na yi tunanin tana da financial problem shiyasa nace mishi akwai wadda zan nemo tayi mishi aikin but tun da kace ba haka bane shikenan zan ce mishi ya nemi wata kawai’’.

Shiruuu Abbakar yayi..
,tabbas ya san Manubiya zata yi farin ciki da offer d’in nan amma kuma ….

Cikin katse ma sa tunani Sir Najeeb d’in yace’’Shikenan,u can leave dama reason d’in kiran naka kenan’’.

Duk da b’oye b’oye da kwana kwanar da Sir Najeeb d’in yayi tashi d’aya Abbakar ya fahimci inda suka dosa,shiyasa ya shiga tsaka mai wuya dan on the other hand no matter how koma menene yake ji yake tunani bai kamata yayi wa Manubiya bak’in ciki ba
Besides a rayuwa a ko da yaushe yana saka farin cikin ta a saman nashi ne..
Da kyar ya iya danne zuciyar sa ya d’ago manyan fararen idanuwan sa da suka d’an fara surkuwa da kalar ja yace’’za ta yi,baku da matsala she’ll gladly do it,inshaaAllah.’’
Yana gama fad’in haka ya maida kan sa k’asa.
Har cikin zuciyar sa yayi wa Manubiya farin ciki da samun wannan aiki dan daga gani mai tsoka ne,ya san zata rage damuwa kwarai sannan za ta yi maganin matsalolin,duk da kuwa ya riga ya san akwai ulterior motive behind it,amma dama tun ba yau ba ya dad’e da yankewa ‘indai rana mai kama data yau tazo to ba zai bari zuciyar sa ta rinjayi tunanin sa ba’.Ya san ba wai Sir Najeeb d’in ne yake son ta ba but definitely kamar yadda ya lura da itama ta tab’u da ganin wannan Abokin nasa haka zalika shima Abokin,tun da gashi ya fara fakewa da bata aiki.Ahankali ya fesar da iska a ran sa yana sake jaddadawa kan sa cewa ‘’inshaaAllah,ba zai tab’a bari shirme da day dreaming d’in sa su shiga tsakanin Manubiya da auren wannan mutumin ko aikin data samu ba..’’

A b’angaren Najeeb shima shiruu kawai yayi yana nazartar Abbakar d’in kafin daga baya yace’’ok,ga katin friend d’in nawa in ta shirya sai ta kira sa tace masa itace Manubiya Musa da zata yi masa aikin da Najeeb yace zai had’asa da wadda za ta yi’’.
Ya fad’i hakan yana mik’awa Abbakar katin.

Ahankali kamar mara lakka a jiki Abbakar d’in ya mik’e ya k’arasa yaje ya amsa,sannan yace
‘’Mun gode kwarai Sir,Allah ya k’ara d’aukaka da arzik’i Allah ya ji k’an magabata’’.

Ahankali Najeeb yayi murmushi yace
‘‘Ameen Abbakar,ta kira soon’’

‘‘InshaaAllah’’
Abbakar d’in ya ce da murmushi kwance akan fuskar sa.
Daga nan Sir Najeeb ya sallame sa suka yi sallama ya tafi…
Tabbas Najeeb ya gama fahimtar komai game da Abbakar amma ko hauka yake ko da wasa bai isa ya gayawa Yash ba dan ya san zai kunno fad’an da ba lalle ya iya kawo k’arshen sa ba, dan a yadda yaga kishi k’arara a idanun Yashjub dazu ya san tabbas in ya bari ya ji wannan batu to sai ya raba su ko da bala’i ne.Shiyasa ya bari akan ba zai fad’a mishi ba,shi ya san
ta yadda zai bi ya taya Abokin na sa akan Abbakar da komai ma
InshaaAllah komai zai tafi normal..

Abbakar kuwa abubuwa biyu ne suka had’e masa na farko damuwar sa dayake ta k’ok’arin b’intikewa wadda yaji mamakin yadda take shirin cin galaba akan sa na biyu kuma farin cikin taya Manubiya murnar samun riba biyu da tayi na aiki da masoyi InshaaAllah.
A hankali yayi murmushin da yafi kuka ciwo a chan k’asan zuciyar sa yana adduar ‘Allah yasa yadda ya tsara yake kuma tunani ya tafi yadda ya ke zato,Allah yasa yadda yake tunanin zuciyar sa zata huta zata samu nutsuwa in Mannubiya tayi auren ta, hakan ya kasance,sannan Allah kar yasa yayi regretting decision d’in sa.’

Hakanan ya na tafe yana tunani ya nufi gate dan ya san dama ta riga ta tafi gida tun dazu,ya san zai ga farin ciki a kan fuskarta in taji labarin aikin dan haka yake ta sauri dan ba kad’an ba yake kwad’ayin ganin wannan farin cikin nata.Duk da yadda yake fargaba amma hakan bai sanya yaji zai fasa ba dan yafi bid’ar ganin farin cikin ta da walwalar ta sama da komai…..

Adaidaita ya samu ta kai shi har k’ofar gidan su Manu
amma sai jidda tace ma sa
‘’Da ta dawo jakarta kawai ta ajjiye tayi alwallah ta nufi gidan Ammi.’’

A k’ofar makeken gate d’in ya tsaya
ya d’an buga kad’an..
Dakyar,bayan mai gadin yaji buk’atar shi ya yadda zai je ya kira masa ita dan a cewar sa k’a’ida ne sai an fad’a a day before tukunna visitors suke zuwar ma masu aikin gidan.
Ba ‘ayi 5minutes ba
Manubiya ta d’an lek’o da fuskarta ta k’aramar k’ofar gate d’in,suna had’a ido ta sauk’e ajiyar zuciya kafin tace
‘’Ashe da gaske kai d’in ne’’.
Ta fad’i hakan tana mai fitowa daga gidan gaba d’aya..
Ahankali cikin tsananin sanyin jiki ta fito ta tsaya tukunna tace’’Na yi mantuwa ne?ko handout aka bada?’’

Sai da Abbakar ya fesar da iska tukunna ya ce’’yau dai na tabbatar da duk abun da yake sanya ku tunani kike ta faman b’oyemin for the past weeks a gidan Ammi yake,meye ne Manu?akwai abun da take yi miki na cutarwa?’’

Murmushin yak’e Manubiya tayi kafin tace
‘’Kawai na gaji ne,shiyasa kaga haka,meya faru ance kana nema na wai kace it’s important,ko?’’
Tayi mishi tambayar cike da son kaucewa tambayar ta shi dan bata san amsar da zata bashi ba.

‘’Manu yau fa ba zaki kaucemin ba wallahi sai kin fad’amin damuwar ki.’
Ya fad’i hakan yana mai zama akan tebur d’in dake anan ta gefen gate d’in Kad’an
Kafin ya sake cewa
‘’Sam ba haka mood d’in ki yake lokacin da muka rabu da ke d’azu ba,so definitely anan gidan ne kike da damuwa.
Talk
Ki gayamin mu nemo mafita b 4 it’s too late.Infact ba inda zan je ma sai kin fad’a min kin dai sanni da naci ko?’’

Ahankali Manubiya ta lumshe idanuwan ta ta bud’e,ta san halin Abbakar da shegen naci a yadda ya kafe d’inne in bata gaya masa ba to ko ruwa ba zai barta ta sha ba,bayaga haka ma in ba shi ko Jiddah ba
bata san wa zata gayawa ta samu sauk’i ba,although bama ta san inda damuwar tata ta dosa ba bata san yaya za ta yi defining damuwar tata ba saboda ba lalle ta yi making sense to anyone ba,ita kad’ai ta san me take going through so ba lalle a fahimce ta ba..

‘’Manu ke nake sauraro’’
Abbakar ya fad’a yana sake gyara zaman shi.
Cikin tsare gida Manubiya tace
‘’Ok,zan fad’a maka amma sai kayi min alk’awarin ba zaka yimin mummunar fahimta ba’’.
Murmushi yayi kafin yace’’inshaaAllah,ina jinki’’.

Sai da ta had’iye wani abu dakyar daya tokare mak’oshin ta tukunna tace
‘’Wannan mutumin na office d’in Sir Najeeb na ranar nan to shine nake ganin wata mata mai kama dashi anan gidan kuma in dai na ganta to sai in yi ta tunanin sa har mafarki fa,ni kuma bana so ina yawan tunanin sa bana buk’atar abun da zai had’ani dashi sam,shi yasa nake tunanin barin aikin nan..’’
Ta k’arashe maganar cikin tsananin sanyin murya da rashin jin dad’i.

Shiruu Abbakar ya yi yana tunani,har sai da ta sake cewa
‘’Ka fahimce ni?’’

Tukunnan ya d’an yi firgigit
Yace
‘’Yeah,yeah na fahimceki’’.
Daganan ya yi shiruuu ya sake dulmiyawa duniyar tunani.

‘‘Shikenan tou tun da ba ka ma da abun da zaka ce,yanzu gayamin abun da yake tafe da kai’’
Ta fad’i hakan cikin d’an had’e gira alamun taji haushin kanta na fad’a masa ta kuma ji haushin shirun da ya yi dan in ba dakyar ba to tasan tunanin abun da bata so kwakwalwar sa ta bashi yake yi. ……………….





MANNUBIYA
20

Na
Humayrah Bulama

Elegant Online Writers.

Murmushi Abbakar yayi kafin yace
‘’Yi hak’uri, ban san me zan ce ba shiyasa kika ga nayi shiru
abun ne ni kaina ya sakani a tunani da damuwa ballantana kuma ke, shawara d’aya
itace
kawai kiyi ta addu’a..Allah ya sa mu dace.

Ahankali tace’’Ameen’’
Sai da Abbakar ya d’an sake yin nazari tukunna yace
‘’Am..kiran da Sir Najeeb yayi min dazu akan ki ne fa.’’

Da sauri ta zaro ido sai kuma tace
‘’A kan me wai???’’
Tayi ma sa tambayar a d’an tsorace.

Murmushi yayi tukunna yace ‘’Relax,abun alkhairi ne.Aiki kika samu,a wata a yadda ya ce min 30k,kuma sau d’aya kawai zaki dinga zuwa a sati
ragowar kwanakin duk ta waya za ki dinga reporting.’’

Dasauri tace
‘’Da gaske?how a ina kuma?’’
Ta yi masa tambayar cikin zumud’i da d’aurewar kai.

Cikin murmushi yace
‘’Kina cewa sir Najeeb bashi da kirki ko?
To ba haka abun yake ba and also maybe yana da wani attachment da emotional mommy issue,cewa yayi yana yawan ganin ki a damuwa
,dayake kin san ranar ai kin ce
masa Inna bata da lafiya to inaga yana tunanin ko akwai wani problem d’in da ba za ki iya fad’awa kowa ba
shiyasa yaga ya dace ya taimaka miki ke kuma ki taimaki Inna.’’Abbakar ya zaiyyane mata hakan cikin son rufe duk wata k’ofar da zata sa ta fahimci wani abun.

Ahankali ta ce
‘’Allah sarki Sir Najeeb
Allah ya saka ma sa da gidan Aljannah.Amma aikin nasa ne?I mean a Ina ne?company ne?’’

‘’Eh to nima ban sani ba gaskiya amma inaga kamar na Uncle d’in sa ne or something like that,ga dai katin wanda aka ce ki kira nan shi zai yi miki bayanin komai’’.
Abbakar d’in ya bata amsa,yana mai mik’o mata card d’in Yashjub wanda Najeeb ya ba sa.

Ahankali ta sa hannu ta karb’a katin tana mai jin yanayin ta yana chanjawa,haka kurum.
Cikin nutsuwa take kallon had’ad’d’en business card d’in mai d’auke da sunan ‘Yashjub Imam Kura’.
Shiruu tayi tana sake kallon sunan tana sake maimaitawa,
kamar wadda ta tuna wani abun kuma sai ta d’ago da sauri ta kalli Abbakar tace
‘’Abbakar ko dai wannan mutumin ne wanda muka had’u a office d’in sa wanda na gama maka maganar sa yanzu?’’

Cikin katse ta yace
‘’A’a ba shi bane ba, in da ace shine da zai gaya min,
wannan d’in cemun ya yi kamar Uncle d’in sa ne fa,Kinga wanchan kuma ai bashi da shekarun da za’a ce masa uncle ko?’’sannan duba katin da kyau wannan fa landlord ne
Estate gareshi har a su Abuja da nan garin,yaushe aka haifi wanchan mutumin wanda banajin ya kai 30yrs da har zai gina estates haka??’’.

‘’Eh kam.’’
Manubiya tace.Tana mai k’ok’arin son yarda da maganar Abbakar d’in,daga nan ta saka a ranta
maybe kawai taji fad’uwar gaban data saba ji in tayi tunanin shi ko ta had’u da Mama
By mistake ne,
Amman wannan ba wanchan mutumin bane ba.

Ahankali ta shiga karanta sunan tana sake maimaitawa
yayi mata dad’i sosai
A fili tace
‘’Yashjub’’
A hankali,sai kuma ta d’an yi murmushi.
Ba tare data kalli Abbakar ba
Still idanunta na akan katin
Tace
‘’Nagode kwarai Abbakar,
Allah yasa mu dace’’.
Sai kuma ta d’ago kyawawan idanuwanta tana kallon sa tukunna tace
‘’Amman kasan sai nayi shawara dasu Ya Musbah da Baba,mu yi adduar Allah yasa su yarda dan ka san halin su ba sa so su ga ni ko Jidda wani a cikin mu yana contributing wajen ciyar da gidan.
Ya Musbah ya dage yana k’ok’arin d’aurawa kan sa abun da ba zai iya ba,wuni yake yi yana guga da wanki
A shagon mati kullum in ka gan sa a gajiye yake abun tausayi.’’
Ta k’arashe maganar tata idanuwanta suna ciccikowa da kwallah.
Murmushi Abbakar yayi kafin yace
‘’Ai har aiki yake yi a wajen masu ginin chan na bayan layi
ya tura suminti ya tura bulo duk dai wani aikin k’arfi yi yake,
ni fa yana burgeni Manu,Namiji da neman na kanshi aka san shi.’’
Cikin karyewar zuciya tace
‘’Yeah,hakane Abbakar
amma shi abun na sa yayi yawa kuma kar aje ayi biyu babu,ka duba fa ka gani saboda d’aurawa kai aikin wahala Baba ya rasa k’afar sa guda d’ayar kuma taji rauni,
Inna ma saboda yawan tunani kalli halin da take ciki
Kar muje shima Ya Musbah
abu yayi mishi yawa shima aje ya samu wata matsalar,in haka ta faru( Allah ya rufa asiri )
Dani da Jiddan da basa so mu wahala mu zamu zama a wahale ai ga Muhsin shima.
A rayuwa in dai ana so a ga abu yayi perfect sai fa an had’a hannu da hannu k’arfi da k’arfi.’’
Ta k’arashe maganar tata wasu siraran hawaye suna zubo mata

Ahankali Abbakar ya sauk’e ajiyar zuciya kafin yace
‘’Manubiya k’addara kowa da irin tasa ki daina kuka dan Allah ki yi addu’a ki kwantar da hankalin ki wata rana sai labari.’’

Ahankali tace
‘’Astaghfirullah!amman Abbakar k’addara ta mai xafi c…’’
Cikin katse ta yace ‘’shiii‘’Sai kuma ya sauk’e wata nannuyar ajiyar zuciya kafin yace’’Taki kawai kika sani.’’
Kamar zai ce wani abun sai kuma ya mik’e yace
‘’Bara in wuce,duk yadda kukayi kya gaya min gobe’’.

Ahankali tace
‘’To’’.
Daganan suka yi sallama ta koma gidan Ammi shi kuma ya wuce yana tunanin Allah yasa Manubiya kar taji haushin sa Sosai in ta fahimci yasan Yashjub za ta yiwa aiki amma ya b’oye mata..dama bai yi niyyar gaya mata ba,ya fiso taje ta fara aikin tukunna ta fahimci Yashjub d’in ne yasan kafin nan ba lalle ta iya bari ba.To kuma yanzu a yadda yaji tana ik’irarin zata bar gidan Ammi saboda mai kama dashi ya san babu dalilin da zai sanya ta aminta da aikin in ta san shi d’in ne wannan dalilin ya sanya shi ninke ta ta baibai..

Sai dare tukunna ta samu gayawa family d’inta har Inna,duk da sun san ba iya magana zata yi ba amma zata ji su kuma ance in ta amince ta lumshe idanuwanta za su fahimta.

Kamar yadda suka yi zato tashi d’aya Baba da Ya Musbah suka ce A’a,shi Ya Musbah ma cewa yayi ‘’mutumin d’an kidnapping ne ko kuma dai yanada wani mummunan nufi akan ta,in ba haka ba taya za ayi mutumin da kullum shine yake bata tsoro a cikin Malaman ta ace tashi d’aya ya bata aiki kuma aikin ma ba zuwa zata dinga yi kullum ba iyaka sau d’aya a sati kawai sannan a wata ya d’auki dubu talatin zuwait ya bata,cike da bin bayan ya Musbah Baba yace ‘’Tabbas maganar ka hak’uk’un Musbahu ke manubiya inaso ki..’’
Cikin katse su sukaji Jiddah tace
‘’Inna ta amince’’.
Da mamaki duk suka maida duban su gare ta,ai kuwa ta sake lumshe idanuwan ta kamar yadda tayi da farko.
Cikin rashin jin dadi Ya Musbah yace
‘’Inna,Manu mace ce,nauyin
family d’in nan akai na yake
Pls karki…’’

Ahankali yaji Baba ya dafa kafad’ar sa,Kafin da sanyin murya yaji yace
‘Shikenan’’
Sai kuma ya juya ya kalli Manubiya yace
‘’Ki kira mutumin ranar da ya baki yace kije sai ku tafi tare
keda Musbahu’’.
Yana gama fad’in haka ya mik’e ya fice daga d’akin.

Ko bayan fitar Baba sai da Ya
Musbah ya kuma yiwa Inna bud’ad’d’an bayani akan illolin dashi yake hangowa game da aikin Manu da kuma yadda ya kamata ace shi ne yake d’awainiya da family d’in bawai ita mace ba.

Amman yana gamawa da ya sake ce mata
‘’Kin yarda Manubiya taje tayi aikin da aka nemeta tayi?’’

Sai yaga ta lumshe masa idanuwan ta ta bud’e.
Cikin rashin jin dad’i ya kalli Manu yace
‘’Ki kira sa,duk yadda kukayi kya gaya min gobe,sai da safen ku.’’
Ya fad’i haka ya mai mik’ewa shima ya fita.

Haka kurum kuma itama Manu d’in sai taji duk bata son kira, sai da Jidda da Muhsin waenda suke ta murna da zumud’i suka tisa ta a gaba tukunna ta fita taje ta aro wayar Siyama ta dawo d’akin.

Gani suka yi kawai Manubiyan tana ta kallon wayar da katin tana juya wa dan haka Jidda ta sa hannu ta karb’i wayar da katin ta kwafe nambobin farko a cikin jerin nambobin waya guda ukun da ta gani ata chan k’asan katin,ta dannna call ta saka a speaker..
Yadda wayar take ringing tana d’uu d’uu haka zuciyar Manubiya take bugawa kamar zata faso k’irjin ta ta fito.

Jin Hatta tsinke ba a d’aga ba
ya sanya ta sauk’e wani bahagon numfashi dan haka kurum taji tana fargabar jin muryar wanda zai amsa kiran.
Ahankali ta lumshe kyawawan idanuwanta tana mai sauk’e numfashi a hankal a hankali.
Tana shirin bud’e idon ta tayi magana ta ji Jidda ta sake danna kiran a karo na biyu
ta shiga ringing..
Da sauri ta bud’e idanuwan ta ta wafce wayar tace
‘’Ke ya isa haka,ba ki ga dare yayi ba mutum Babba da matar sa kin dame sa da kira haka ki bari gobe ma sake gwadaw……’’ta fad’i haka tana duban wayar dan ta ga ko ta kashe ne saboda taji ta daina ringin d’in
Tsit!haka muryarta ta katse sakamokon ganin timer data yi

Please Login or Register in order to submit comment