Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kafin ka yanke wannan d’anyen hukunci hak….’’

Cikin katseta Daddy yace
‘’Na san k’arya Kausar ta yi miki basu gaya miki Yasmeen tana da matsala a kunne ba.
Kinsan abu na farko daya fara had’ani dake?’’.
Cikin zubar kwallah Ummi ta girgixa kanta alamun’’a’a’’
Cikin fushi Daddy yace
‘’Ranar da kika zo d’aki na kika bamu asalin labarin Munirat da Bashir,me na ce miki ??’’

Cikin inda inda saboda duk ta rikice tace
‘’Ce wa kayi komai ya wuce
amman Daddy su Kausar basu..’’

Cikin tsawa yace ‘’ba wannan ba!d’ayar maganar tawa ta k’arshe,me nace miki Saddik’a?’’

A gigice tace
‘’Cewa kayi zaka saka su su bani hak’uri’’

‘’Good’’ Daddy ya furta yana mai sake matsowa kusa da ita
wanda hakan yasa Ummi ta d’an ja baya dan ba kad’an ba ta tsorata da Daddy bata tab’a ganin shi a haka ba tunda suke.

Cikin zafin zuciyar da ya ke ji tana taso masa yace ‘’na fad’a miki bara in sake maimita miki
dan naga kamar kin manta,
Abu uku na fi tsana a yimin
waenda sune suke janyowa mutum yaga other side d’ina;
Ayi crossing d’ina
Aci Amata
na uku,A nuna min ban Isa ba,
Duk yadda na kai ga son mutum da ganin girman sa
muddin yayi min haka to babu
dalilin da zai hana ni yin kacha kacha dashi..da nace miki ki jira zan sanya su su baki hak’uri dan me ya sa kika yi gaban kanki?saboda kin raina ni?saboda ban isa ba?..na ji sarai na kuma san me kika yi
Yasmeen ta gaya min yadda kika tara su a dining table
Kinacewa su zauna lafiya da Munirat kina gindaya musu sharud’a kina jera musu warning alhalin su already komai ya riga ya wuce a wajen su.
Me kike so kiyi proving by doing that??bari kiji nan gidan uban su Yasmeen ne,Munirat kara kawai na yi mata nake bata shelter saboda ke,and if zaki nemi ki takurawa y’ay’ana saboda ita har ta kai ga kina k’in jin magana ta kina k’etare umarni na to kuwa ban ga dalilin da zai sanya in ci gaba da zama da ita a gida d’aya da ke kan ki ba.
Sannan yau har kina da guts d’in da za ki d’aga hannu ki mari Yasmeen?,kin tab’a gani na yiwa Munirat kallon banza???Ko ma me Yasmeen tayi miki ko ma menene
ban ga dalilin da zai sa ki mare ta ba’’

Cikin share hawaye Ummi tace
‘’ko menene?’’

Ciikin fushi Daddy yace
‘’Ko uwar ki ta zaga ban baki ikon ki tab’a d’aya daga cikin ya’yana ba.
Kin tab’a ganin uwar data haife su ta d’ora hannu akan su??’’

Wani Irin kuka Ummi ta fashe dashi ta durk’ushe a wajen,dan ba wanda ya fad’o mata arai sai
Marigayin Mijinta..

Sam bata bawa Daddy tausayi ba,dan shi wani irin haushi ma taci gaba da bashi,ji yake yi kamar ya yi ball da ita.

Kwanakin baya Mommy ta tuno masa da Khadija yanzu kuwa Saddik’a ce ta tuno mishi da ita..ta yadda ta nuna masa bai Isa ba bashi da girma da daraja ta yadda ta nuna son kan ta ta fifita y’ar ta k’iri k’iri sama da shi.


Cikin fushi ya sake cewa’’ki tashi ki had’a kayan ku…’’

Maganar sa ce ta mak’ale
sakamokon ihun Munirat da suka jiyo..da gudu Ummi ta nufi waje..kafin ta k’arasa ta fara jiyo na Yassir ma.
Ummi na fita Daddy ya bi bayan ta da kallo cikin takaici kafin ya nufi wardrobe d’in ta da kan sa ya fara firfito mata da kayanta yana sauk’e akwatunan ta kafin ya ja akwatunan ya fitar parlourn ta
daga nan ya wuce ya fitar dasu daga side d’in ta gaba d’aya ya nufi chan babban parlourn dake a saman,ko damuwa da ife ifen Yassir bai yi ba kawai shi a yanzu burinshi Ummi ta fitar masa daga gida,kawai shi dai ta fita,ya san in ta fita shine zai samu nutsuwa …..


A chan parlourn kuwa,Yashjub yana hango su bayan ya daka masa tsawa sai kuma ya nufe su cikin tsananin tashin hankali,yana zuwa bai yi wata wata ba ya janyo Yassir ya kifa masa wani gigitaccen mari wanda har sai da Yassir d’in ya kai k’asa yana shirin tashi ya zaro belt d’in wandon shi ya rufe sa da duka yana ball da shi.
Yanayin dukan da Yashjub yake masa ba irin dukan da normal mutum zai yi bane ba saboda k’arfin Yashjub d’in na daban ne
shiyasa duk yadda Yassir yaso daurewa sai ya kasa ga shi ya kasa tashi dan yana yunk’urawa zai tashi Yash d’in yake kuma kai masa duka da k’afa ya kwantar dashi.

Kusan a tare Mommy Kausar da Ummi suka k’araso wajen,
Kausar ce ta fara k’arasawa kusa da su da niyyar rabawa ai kuwa itama ya zula mata belt dan dama haushin ta yake ji.
Da sauri Mommy ta matsa taja hannunta ta mayar da ita gefe,tukunna ta yi kan Yashjub d’in,da kyar ita da Ummi suka samu suka rik’e hannun Yashjub wanda idanuwan sa suka kad’a suka yi jazir.

Cikin tsananin b’acin rai Mommy ta fashe da kuka tace ‘’haba Yash,wanne irin abu ne wannan?ko yaro d’an shekaru sha takwas ai baka saka a gaba da duka irin wannan ba’’.

Cikin rashin jin dad’i da dauriya ya Ummi ma tace’’Yash baka kyautaba ko me yayi maka bai kamata ka dake shi haka ba.’’

Sai kuma suka juya ga Munirat dake durk’ushe a wajen
Mommy tace ‘’me ya faru’’

Gaba d’aya ta tsorata ta gigita daga abun da Yassir ya yi mata ga kuma dukan da taga Yash yayi masa shiyasa da gudu ta tafi jikin ummi ta fad’a ta fashe da kuka tukunna tace’’Ummi dan Allah dan Annabi kizo mu bar gidan nan,in ke ba zaki tafi ba ni gaskiya zan tafi’’

Dai dai nan Daddy wanda ya gama janyo akwati ya cillo waje
yace
‘’Kar ki damu yanzun nan zaku tafi’’

Da sauri Yashjub wanda tun d’azu yake karanto sunayen Allah yana k’ok’arin daidai ta kan shi,ya runtse idanuwan sa da k’arfi.
Dai dai nan su Yahanasu da Baba larai suka hawo saman
sakamokon hayaniyar da suka ji.
Yahanasu ce ma ta lura da yadda gefen kan Yassir yake zubar da jini sai kuma taga kamar ma baya motsi da sauri ta k’arasa kan sa ta shiga tattab’asa tana kiran sunan shi’’yasssir! yassir!!’’sai
Kuma ta juya ta kalli
Baaba larai a rikice tace’’baya motsi fa’’.
Cikin tsananin tashin hankali Mommy ta kalli Yassir itama ta tabbatar baya motsin bata san lokacin da ta juyo ta kifawa Yash wani irin gigitaccen mari ba sai kuma ta sake fashewa da kuka ta durk’ushe a kan Yassir,cikin tashin hankali tace
‘’Shikenan ya kashe min yaro na ya kashe min d’ana mafi soyuwa a gare ni shikenan ya kashe min gudan jinina….’’

Da sauri Baba larai tace
‘’Haba Khadijah,ki yi shiru mana,bai mutu ba inshaaAllah’’
Sai kuma ta durk’usa ta mikar da ita,tana tittirjewa tana kuka haka suka jata ita da Kausar suka nufi b’angaren ta da ita,tana kuka kamar ranta zai fita.
Ahankali Daddy ya k’arasa ya dudduba sa,ba tare da ya kalli Yash ba yace’’kama min shi mu kai sa d’akin sa.’’
Yana gama fad’in haka ya d’auko waya ya kira family Dr.d’insu, da ga nan suka fara k’ok’arin kinkimar Yassir.

Har sun kama hanyar k’ofar d’akin Yassir d’in Daddy ya d’an tsaya ya juyo ya kalli Ummi yace ‘’kar ki k’ara minti biyar a cikin gidan nan’’.
Daga haka suka yi gaba suka wuce shi da Yashjub.

Ahankali Munirat ta k’arasa kusa da ita ta rungume ta
cikin zubar hawaye tace’’ sorry Ummi, it’s for the best
InshaaAllah’’Munirat ta fad’a hakan dan ita duk a tunanin ta ita ta sake tunzura Daddy dan taga Daddy ya ji lokacin da ta ce su bar gidan ……

A kan gado suka kwantar da Yassir,Daddy ya sake zaro waya ya shiga kiran Dr dan yace masa ya zo da sauri yayin da Yashjub ya faki idon shi ya juya ya fice,ya nufi wajen su Ummi.
Bai same su a main parlourn saman ba dan haka kanshi tsaye ya wuce side d’in Ummin.
A bakin k’ofar d’akin ta ya tsaya yana knocking,lokacin suna tsaye suna mamakin yadda Daddy ya watsar da gaba d’aya kayan wardrobe d’in Ummin,ahankali Ummi ta fakaici idon Munirat
ta goge hawayen ta ta nufi k’ofar da ta ji ana bugawa tana addu’ar Allah yasa kar Daddy ya sake creating wani scene d’in a gaban Munirat dan ita a tunanin ta shine ya sake dawo wa,amma tana fita sai ta ga ashe Yashjub ne.
Duk da halin da take ciki haka ta daure ta b’oye tata damuwar tace
‘’Yash dan Allah dan Annabi kar ka sake yiwa d’an uwanka irin wannan dukan,
Dan Allah’’

Ahankali Yash ya had’iye wani k’ululun daya mak’ale masa a mak’oshi yana mai mamakin kyakkyawar zuciya irin tata
tukunna yace
‘’Na ji Ummi,ba zan k’ara ba amma kema kar ki je koina
I’ll speak with daddy
In ya huce’’

Murmushi tayi kafin ta ce masa
‘’shigo’’
Ta fad’i hakan tana matsawa ta bashi hanya ya shigo
cikin d’akin nata da sallama a bakin sa,da mamaki ya kalli d’akin sai kuma ya kalle ta.Cikin karyewar zuciya tace
‘’Ni kaina Yash bana son barin gidan nan banaso aurena ya mutu,amma kuma kalli abun da Daddy yayi shiyasa naga tunda har abun ya kai ga haka gara in fita tun da lafiya ta da mutunci na tun kafin ya zo yayi fata fata da ni kamar yadda yayi da kayana,amma Ina so ka fad’a nasa ko bayan na bar gidan nan cewa ina son Y’ay’an sa kuma ba zan tab’a cutar da d’aya daga cikin ku ba.’’

Yadda Ummi take hawaye
da kuma abun da Daddy ya aikata tabbas ya san Ummi ba za ta yarda ta k’ara minti uku ba ma a cikin gidan,shiyasa a hankali ya jinjina mata kai kawai alamun fahimta yayi hakan yana mai kallon windunan d’akin da kuma hanyar closet d’in ta har zuwa toilet ya tabbatar babu ta inda za su fita,ya ji dad’i da balcony d’in ta ya kasance a parlour ne
dan wallahi ko shi ne Daddy yayi mishi wannan tijarar sannan ya ce ya fice mishi a gida
sai ya fita ko ta window ne,daga baya ya dawo a sasanta.

A hankali yace
‘’Na fahimci ki,Ummi.’’

Murmushin da yafi kuka ciwo tayi tace’’ka kula da y’an uwanka Allah yayi maka albarka’’

‘’Ameen’’yace,daga nan ya juya yana zuwa k’ofar yayi sauri yasa hannu ya zare makullin kafin ta k’araso tace wani abun har ya fice ya sak’ala key d’in ta waje tana k’arasowa jikin k’ofar taji ya rufe su ya zare makullin ….


Koda Dr yazo ce musu yayi ba wani abun tashin hanlkali bane ya samu Yassir d’in,kawai azaba ce ta saka shi ya suma sannan kurjewa ne kawai kan sa ya yi bawai dukan ne ya fasa masa kai har yasa yayi jini ba ,
So su kwantar da hankalin su ya basa allurai da duk abun da ya kamata inshaaAllah he’ll be fine..

Yashjub ne ya raka sa har mota yana dawo wa ya tarar da Daddy har yanzu a tsaye a kan Yassir wanda dazu ya farka Dr ya yi masa allurar bacci kafin ya tafi.

K'arasawa yayi ya tsaya shima yana kallon Yassir d'in,tabbas
yana son d'an uwan sa amma kuma halayen Yassir kullum sake tab'arb'arewa suke yi sannan shi kuma ga yanayin zuciyar sa wadda yake sake tunzura sa ga aikata wasu abubuwan,a hankali ya sunkuyar da kan sa a ran sa yace
''bai kamata ace na dake sa ba ,inda ace Yassir yayi aure da wuri da yanzu maybe yana da y'ay'a biyu ma..''

Cikin dakakkiyar murya yaji Daddy yace''abun da ka yi yau was incredibly stupid,ko da wasa kar ka sake yin wannan shirmen,ranar da case d'in Yahansu da Munirat ya faru cewa ka yi saboda ka ga muna wajen ne shiyasa baka hukunta su Yassira ba,
It would be nice of u in ka cigaba da bar min komai a hannuna,ban hai fi ya’ya na
dan wani yaci kashi a kanku ba
na san kafi kowa sanin wannan,
Next time in Yassir yayi laifi
U
report
To me!''
Yana gama fad'in haka ya juya ya fita.Sai da ya biya d'akin Ummi yaje ya murza yaji a rufe kuma bai tarar da akwatunan ta ba,dan haka ya yi tunanin ta tafi ne,a take ya ji wani irin sanyi yana ratsa shi,a chan wani b'angare na zuciyar sa kuma yana takaici da jin haushin tafiyar tata da kuma abun da ya yi mata….

Gaba d’aya Yashjub a hargitse yake,mari da maganganun Mommy sun yi mugun b’ata mishi rai
Ga kuma abun da Daddy yayi masa,sannan ga yadda yaga Yassir and yana kyautata zaton su Yasmeen ne suka shiga tsakanin Daddy da Ummi,ba zai zuba ido ya tsaya
tarbiyyan k’annen sa ya zama haka ba fa amma matsalar shine ta Ina zai fara tun da gashi k’iri k’iri Daddy ya ja masa barrier..
ganin da yayi gaba d’aya yana neman sake b’atawa kan sa rai ne yasanya kawai ya fice ya nufi side d’in sa ran sa a mugun b’ace.

Yana shiga parlourn shi ya tarar da Najeeb a zaune,ajiyar zuciya ya sauk’e Kafin yace ‘’zuwa babu sanarwa?’’

Murmushi Najeeb yayi sanann yace’’inata kiran wayar ka baka d’auka,driver d’in ka na kira ya ce min kana nan,shine na zo,’’

‘’anything important?’’
Kawai Yashjub ya iya cewa.

Murmushi Najeeb ya yi kafin yace’’ko in tafi ne ?’’
Dai dai nan Yashjub ya k’araso ya zauna kusa da shi,sai a lokacin Najeeb ya lura da yadda idanuwan sa suke
wanda hakan ya basa tabbbacin ran sa ne a b’ace.

‘’Me kuma ya faru ??’’Najeeb ya yi masa tambayar.

Numfashi Yashjub ya fesar kafin yace ‘’ba komai’’.

Tunda yace haka Najeeb ya fahimci maybe family issue ne
ko kuma ba shi da niyyar gaya masa ne,dan haka ya kawar da zancen ta hanyar cewa’’tun jiya Ya’isha ta k’i d’aukar wayata,ban san me ya faru ba,Yash sai ka saka baki a lamarin nan fa dan yarinyar nan tana wahalar da ni da yawa.’’

Tsaki Yashjub yayi tukunna yace’’k’aton banza kawai.’’

Dariya Najeeb yayi Kafin ya ce’’ai gara ni,I’m not living in denial sannan bana fakewa da
employing mutum..k’arara nake fitowa,speaking of which..how is she ??’’

Kmr Yashjub ba zai yi magana ba sai kuma yace’’she’s ok’’ya fad’i hakan yana mai jin wani sanyi yana maye gurbin b’acin ransa.
‘’Gaya min yadda kuka yi da ita,lokacin da tazo.’’Najeeb ya fad’i hakan ya na mai gyara zaman sa ya fuskanci Yash d’in sosai .

Tiryan tiryan haka Yashjub ya bashi labarin komai,wanda kafin ya gama gaba d’aya b’acin ran da yake a ciki ya b’ace b’at!.

Shi kan sa Najeeb sai da yayi mamakin yadda Yashjub ya zage yayi doguwar magana haka.

Dan haka yana dasa aya Najeeb yace
‘’Yashjub yarinyar nan I don’t think iyayen ta za su barta ta k’ara shekara d’aya ma basu yi mata aure ba,kar ka tsaya b’ata wa kanka lokaci kaje garin haka miskilanci ya cuce ka,ka san dai kana son ta ko?’’

Shiruu Yashjub yayi a ranshi yace’’ko dai ya cire kunya da taurin kai ya gayawa Najeeb ne dan yana buk’atar shawara,har ga Allah bai san ta Ina zai fara ba,kuma kamar yadda Najeeb ya fad’a tabbas tsaf iyayen ta za su iya aurar da ita anytime..ya zama dole ya ajjiye komai a gefe dan Manubiya ce peace of mind d’in sa
Strength
Happiness
da komai na shi’’

‘’Yash….’’
Muryar Najeeb ta katse masa tunani ta hanyar kiran sunan sa cikin k’ura masa idanu.

Ahankali Yash ya gyara zama yana kallon Najeeb d’in tukunna yace‘’menene abun yi yanzu?’’

D’an fiki fiki Najeeb yayi da idanuwanshi tukunna yace ‘’kana son nata kenan?’’

Murmushi Yashjub yayi tukunna ya d’an d’aga masa kai alamun’’yes’’kafin a hankali yace ‘’a lot’’sai kuma da sauri ya nuna Najeeb d’in da yatsa alamun warning sannan yace‘’don’t laugh,kuma wallahi kar in ji maganar nan a bakin kowa.’’

Duk yadda Najeeb ya so hana kan sa dariya sai da ya yi,kafin daga baya yayi shiru sannan yace’’sorry man,naji dad’in abun ne sosai shiyasa,congratulations Allah ya baka Manubiya.’’

Ahankali Yash yace ‘’Ameen’’yana wani irin blushing.

Kafin Najeeb d’in ya yi serious face sannan ya maida gaba d’aya hankalin sa a kan yashjub d’in tukunna yace’’yanzu abunda ya kamata ka yi shine……’’




MANNUBIYA
29

Na
Humayrah Bulama

Mikiya Writers Association.

Ahankali Yash yace ‘’Ameen’’yana wani irin blushing.

Kafin Najeeb d’in ya yi serious face sannan ya maida gaba d’aya hankalin sa a kan Yashjub d’in tukunna yace’’yanzu abunda ya kamata ka yi shine,ka yi k’ok’arin zama so close to her in Allah ya kaimu kamr nan da one week kana iya tunkarar ta da maganar in ya so mu kuma sai muje mu samu uncle,brother ko mahaifin ta a san da zaman ka’’

Wani irin kallo Yash d’in ya yi masa wnda ya sa Najeeb d’in yin y’ar siririyar dariya kafin yace’’a tunanin ka yanzu in kace mata kana son ta direct sa ta amince ne?ai ya yi too soon,ka fara neman friendship d’in ta first ai ba nan da wata d’aya ko biyu na ce ba iya ka sati d’aya na ce maka,sarkin zalama.

Numfashi Yashjub ya fesar kafin yace’’Najeeb,Manubiya fa ba zata saki jiki da ni har ta yarda mu zama friends ba that too in one week that’s impossible,tanada kamun kai da nutsuwa over..she is not the type da zata zama friends da any stranger tunda that’s what i am to her!,but tabbas maganar ka ma gaskiya ce tunda ko da ace ban tab’a soyayya ba nasan b4 mutum ya samu guri a cikin zuciyar mace ana buk’atar shak’uwa da trust da sauran su amma ni yanzu a hanlin da nake ciki yanzu Najeeb Ina so ka fahimceni ka fahimci yadda nake jin ta a cikin zuciya ta..dan haka Ina ganin gara kawai in nemi su trust d’in daga baya but for now ta san Ina son ta,kar ka manta bayan na gaya mata ta amin ce da ni
akwai fa su tambaya sa rana da buki wnda nasan Daddy da Mommy sai sun d’an d’auki lokaci dole shima kafin ayi auren nikuma gaskiya a matse nake ta zama matata ba wai lust ko wani abun ba a’a abun da na fi buk’ata a yanzu shine ta yarda da ni ta amin ta da ni in mallake ta ta zama tawa ni kad’ai,ka fahimceni??’’

Numfashi Najeeb ya fesar kafin yace’’Yash na fahimce ka amman kuma kaima ka fahimce ni,gaggawa aikin shed’an ne mubi komai a hankali.’’
Najeeb d’in ya fad’i hakan saboda shi yana so su d’an fara shakuwa dan ba zaiyiu ace ya bata aiki Monday kuma Friday tashi d’aya yace yana son ta ba ba lalle ta fahimce sa ba zata ga kamar yaudarar ta ya zo yi…

Ahankali bayan zurfin tunani Yash d’in yace ‘’ok,bara in jira one week d’in’’…

Tunda Daddy ya koma d’akin shi yake ta faman kai kawo,gaba d’aya ran shi a dagule yake hankalin sa a tashe yake sam ya rasa gane me yake damun sa dan shi kansa zuwa yanzu ya fahimci a mugun birkice yake.Tun kafin aje ko’ina har ya fara tunanin bai kamata ya kori Ummi ba ta chanchanci hukunci tabbas dan bai kamata ta tab’a masa y’a ba amma kuma shima bai kamata ya ce ta bar gidan ba,ko ba komai ya san tana son shi tun ba yau ba so na tsakani da Allah dan itama ba matsiyaciya bace balle yace kud’i ta bi tana business tana aiki kuma ya san mijin ta ya bar musu mak’udan kud’ad’e,saboda shi ta yi resigning aiki sam bata damu ba tace itama tafi so dama ta kula da shi da y’ay’an su…
Ahankali ya dafe kan sa yana ji yana wani irin sarawa ….
Da sallama Mommy ta turo k’ofar d’akin ta shigo ahankali ta k’arasa kusa da shi tana d’ar d’ar tace
‘’Daddy Yassir fa har yanzu bai farka ba,lafiya kuwa?’’
Ba tare da ya cika kan nasa ko ya d’ago ya kalle ta ba yace’’lafiya,allurar tana da nauyi ne.’’

Ahankali ta matso tad’an rike hannun shi tace’’am..i’m sorry about umm..’’
Hannun sa rik’e da kai har yanzu ya d’ago ya kalle ta tukunna yace’’Get,out!’’
Ta bud’e baki za ta yi magana ya mik’e ya kamo kafad’un ta da hannu biyu yace’’in kin san kina da hannu a koma meye ne to tun wuri tun kafin mu dena sheda juna ki janye ki fita a idanuwa na Khadijah!’’
Wasu hawaye ne suka zuba mata wanda hakan ya sa Daddy ya ji ina ma bai yi maganar ba.
Ahankali tace ‘’daddy I…’’
Wuce ta kawai shi yayi ya fita da sauri yana daya sanin yi mata hakan dan bai kamata ya d’aurawa kowa laifin abun da ya aika ta ba.Yana fita aka fara kirana sallar azahar dan haka ya wuce masallaci.

A masallaci suka had’u dasu Yashjub,bayan an fito
cikin girmamawa Najeeb ya gaida shi ya amsa da kulawa daganan Najeeb d’in ya wuce side d’in Yash ya barsu a wajen dan yaga kamar suna buk’atar space.
Najeeb na wucewa Yashjub ya bawa Daddy hak’uri kKafin ya fad’ama sa abun da ya yiwa su Ummi.
Bai yi murna ba kuma bai yi bak’in ciki ba,makullin kawai ya karb’a a hannun Yash ya wuce sama.
A zaune ya same su su biyu a kan gado kowa tayi tagumi amma fa sun had’a kayayyakin su tsaf gaba d’aya sun juye a cikin akwatunan da jakan kuna
sun jere su a gaban su.

Tun kafin ya ce wani abu suka mik’e ba tare da ta kalle sa ba tace ‘’Yashjub ne ya kulle mu
ka yi hak’uri yanzu zamu tafi’’
Ta fad’i hakan tana k’ok’arin jan akwatuna biyu da suke cikin jerin akwatunan gaban su,a hankali Munirat ma ta mik’e ta fara k’ok’arin jan wasu akwatunan,cikin sanyin jiki Daddy ya matso kusa da ita yace
‘’Ki tsaya mu fahimci juna …..’m

Munirat ji tayi kamar ta kwala k’ara dan takaici,ya gama ci musu mutunci sannan yanzu taga da alama so yake ya hana su tafiya,har ta bud’e baki za ta yi magana sai kuma ta ajjiye akwatin hannun ta ta fita dan already Daddy har ya kamo hannun Ummi ya hanata fara jan akwatin.

A parlourn ta nemi waje ta zauna tana addu’ar Allah kar yasa Ummi ta yadda su ci gaba da zama a cikin gidan nan.Shigowar Mommy ne ya katse mata tunani..Ahankali Mommy ta sauk’e nannauyar ajiyar zuciya kafin tace’’Munirat na godewa Allah da baku tafi ba na kira wayar mamanki bai shiga ba,kar ku d’au zafi kamar yadda shima ya d’auka kin ji,bara in shiga
inyi mata magana itama’’
Ahankali Munirat tace ‘’ita da Daddy ne.’’

Da sauri Mommy tace
‘’Yauwa perfect,bari in same su duk su biyun.’’
Har ta nufi k’ofar sai kuma tace
‘’Am..Munirat dan Allah d’an jeki kitchen akwai soup d’in dana d’aurawa Yassir kar ya k’one kafin mu gama ki juye a bowl ki kai masa d’akin sa’’.
Kamar za ta yi mata musu
sai kuma kawai ta mik’e ta wuce.

Tun ranar data fara ganin Yassir ya d’an burge ta
Kyakkyawa ne ajin farko
halayyar sa ce data fahimci ba ta da kyau da kuma yadda gwaggwo ta ja mata kunne ya sanya ta cire rai da shi,dan a tashi d’aya ma tun daga ranar ta ji ta tsane shi,amma duk kalar tsanar da tayi masa she can’t help but to feel sorry for him dan ta tabbatar inda ita aka yiwa wannan mahaukacin dukan to da tuni ta mutu.
Tana wannan tunanin ta je kitchen d’in ta juyo soup d’in a bowl,d’akin da taga su Daddy sun shiga da shi dazu ta nufa tana zuwa ta d’an yi knocking, jin shiru yasanya ta tura k’ofar ta shiga bakin ta d’auke da sallama.
Tana shiga ta ganshi a kwance a kan makeken gadon shi,a hankali ta k’arasa ta d’an tsaya akan sa tana kallon yadda fuskar sa ta kumbura,a take kuma sai ta fara data sanin zuwa dan sai da ta gan shi ta ga yanayin jikin nasa tukunna ta fara jin haushin kanta na kasa hak’ura da tayi har sai da ta zo dan haka ta ajjiye bowl d’in da niyyar juyawa ta ji ya kira

Please Login or Register in order to submit comment