Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya dubeta kana yace “Wanne kenan...?”

“Ka sani sarai maganar k’anwarka Yesmin nake maka, naga alama yi kake kaman ma bakasan tana gidan nan ba... What’s wrong with you Son...?”

Girgiza kai Khalid yayi had’ida kishingida cikin kujera kana yace “But Ammi I thought we’ve already talked about that... Ammi I’m not interested, I don’t love her for heaven’s sake..”

“Kai kai rufe min baki meye haka...? Wani you don’t love her ka samu banson sakarcin banza, a ina zaka samu mace kaman ita donma ka samu anason baka ita ai dai kasan Yesmin ba class d’inka bace, Khalid ka natsu kaji abinda nake fad’a maka tun wuri ka aje wannan masifar girman kan naka ku daidaita da ‘yar uwarka nasan ba sonta bane bakayi kawai tsaban jidakan tsiyarka ne kake cewa haka, Yesmin tana nan a gidan nan har tsawon sati biyu don haka kafin ta tafi naji batu mai dad’i....”

Kallon Ammi kurum yake ba tareda ya iya furta komai ba, rai b’ace ya mik’e yana fad’in “Da safe zan wuce Kano In sha Allah zan sami Daddy a office na mishi sallama....”

Yana tafe Ammi na fad’in “Ka tabbata kayiwa Yesmin ma sallama...”

Bai tsaya amsa Ammin nasa ba ya fice takaicin Yesmin na d’awainiya dashi...

Jiki a sanyaye Yesmin ta koma sama ba tareda ta iya sauk’owa ba..


Washe gari Khalid ya sauk’a a birnin Kano....

Niko nace Nabilah kinada bak’o...LoL

SameenaAleeyou 📚
*INDA RAI*
_..............DA RABO_




*24*




*©Sameena Aleeyou...✍🏽*



Suna barbaje a parlorn Hajiya suna tattauna batun auren Yayansu Hafiz Sahariyya ta kuma kwashewa da dariya had’ida rangad’a gud’a tace “Hajiya wllhi zanso ace Zulfah na gidan Ya Hafiz za’ai auren nan nasan bak’in ciki sai kusan aikata lahira...”

Hajiya ta murmusa cikeda jin dad’i kana tace “Yanzu ne Hafiz ya nuna min cewa ni na haifsa, kuma banda abinki Sahariyya ai yanzu ma labarin ya risketa sai taji kaman tai hauka don kishi tinda sakinta akai aka auro wata, kuma a d’akin Zulfa’u za’ai jeren Sawwama, duk wata tsiyar Zulfa’u tattare mata zaiyi idan yaga dama ya zuba a shara tinda yak’i aminta a sanar da iyayenta babu aurensa akanta...”

Suka kuma washe baki suna k’ek’eta dariya cikeda farin ciki...

Naja takai dubanta ga Kausar dake wasanta hankali kwance kana tace “Yarinya kin kusa komawa gidan ubanki kiyi tashin hannun kishiyar uwa....”

Sahariyya ta b’allawa yarinyar harara kana tace “Aikuwa kaman kin sani ana gama cin amarci zan kwashi wannan tsiyar na kaita gidan ubanta, badai gani yake muna musgunama gudan jininsa ba, tau kaw yanaji yana gani matarsa zata lallasa mata bugu bai isa cewa komai ba, aini naji dad’i ko banza jinin Zulfah zatai girman hannun kishiya...”

Suka kuma b’allewa da dariya idan ka d’auke Hajiya dake zullumin abubuwan da suke fad’i, ko tak’i ko taso Kausar jininta ne, wannan abu idan ta tuna sai taji kaman idan ana musguna mata na d’anta Hafiz ake musugunawa, a d’an hasale tace dasu “Toh toh ya isa haka... Najah d’auko Kausar ki mata wanka...”

Wani kallo Naja ta aikawa Hajiya kana tace “Tab wllhi ban iya rainon d’anda ban haifa ba Hajiya, Uwarta na biyu Raihana ta mata...” Ta k’arashe tana k’ishingid’a cikin kujera had’ida danna earpiece a kunnuwanta...

K’wafa Hajiya tai kana ta mik’e ta d’auko Kausar da kanta ta shiga kwab’e mata kaya don Raihana na kitchen na aikin abincin rana da babu wanda yayi har saida ta dawo daga makaranta....

***

Fitowarsu kenan daga class suna tattauna lecture d’in da suka fito, sai dariya suke suna jinjina rashin mutuncin malamin nasu da yanda Nabilah bata tsoronsa har saida ya zamto idan bata aji sai ya gane, da yawan malamai sabida tsaurin idanunta da rashin tsoronta suka santa, gashi ba halin ka kayar da ita don babu laifi tana karatun ta daidai gwargwado..

Habib d’aya daga cikin course mates d’in nasu yace “Dr Manzo yau ya had’uda gamonsa... Ni tun last semester da akace zai d’aukemu kuma he’s very strict nace toh akwai aiki randa sukai arangama da Nabila....”

Yusrah k’awarta k’waya d’aya tak saiko Habib da Safwan da suke taimaka masu da tutorials tace “Wllhi ni damuwata ma kardai taje ta janyo mutumin nan ya tsanemu mu shiga uku ga course d’in nasa ita kanta ba wai fahimta ake ba...”

Safwan yace “Kuma kuna magana tayi k’us kaman bata wajen....”

Harara ta watso masu gaba d’aya kana tace “Iyakaci yace na daina shigar masa aji ba shikenan ba tinda kuna nan zaku koyan.... Ke Yussy dan Allah kizo mu tafi wllhi na gaji sallah ma a gida zanyi...” Ta k’arashe tana rataye side bag d’inta....

Gaba d’aya suka shiga darawa suna fad’in tai a hankali Dr Manzo ba kaman sauran lecturers d’in bane yanda course d’insa take a baud’e haka shima yake a baud’e....

Zata kuma magana wayarta dake cikin jaka ta d’auki ruri....

Lalumar wayar ta shigayi tana fad’in “Sai kuyi ai daga ku har shi Dr Manzon banida lokacinku....” Aya ta sakawa kalaman nata ganin bak’uwar lambar da ake kiranta dashi, kaman bazata d’aga ba sai kuma ta d’aga a dak’ile don ba kasafai take d’aga lambar da bata sani ba don idan an fad’i mata abinda bai mata ba ko wanene mai kiran zaiji maras dad’i ne shiyasama wani sa’in bata d’agawa...

Gabanta ne yayi mummunar fad’uwa jin muryar dake mata magana cikin wayar, ta kasa furta koda kalma sai lugude da k’irjinta ke ci gaba dayi, dukda cewa bai wuce a k’irga ba ta tab’a jin muryar tasa amma ko kusa bazata iya mance sautin muryar ba wanda shi kad’aine mai irinta a iyaka saninta....

Murmushi yayi a hankali kana yace “Are you surprise... Kin d’auka na mance koh...?”

K’ok’arin saita kanta tai kana tace “Malam inaga wrong number ka kira please do not call this line again.....”

Bai bari takai aya ba yace “Don’t think of hanging up on me.... Ina kallonki daga yanda nake, ki sallami samarukan naki kizo mu k’arashe deal d’inmu...”

Waige waige ta soma tana neman ta yanda zata hangoshi amma ko k’yallin mai kamanninsa bata gani ba, murmushin yak’e tai lokaci guda ta kuma had’e fuska kaman tasan yana kallontan kana tace “Malam ba wani deal tsakanina dakai idan kuma ka matsa sai na biyaka kud’in gyaran motarka nima sai ka biyani kayana da ka b’ata...”

Murmushi maras sauti ya kumayi kana yace “Ki daina wahalan juye juye just turn to your left....”

Waigowa ta kumayi ta direction d’in da ya fad’i nan ta hangi motarsa pake k’asar bishiya....

Sauk’e ajiyan zuciya tai kana tace “Kaga Malam ka k’yaleni ka daina bibiyata....”

Katseta Khalid yayi da fad’in “You haven’t asked about my wound... Ko kinsan cewa har yanzu bai warke ba, har yanzu ina ganin likita a sabida ciwon da kikajimin... To add it to your expenses zaki biya....” Saurin kasteta tai da fad’in “Malam kodai kai d’an 419 ne... Toh idanma kai d’an damfara ne babu abinda zaka samu daga gareni just stop stalking me...”

Wannan karon sosai ta basa dariya amma ya gimtse yace “But you know I can press charges, ciwon dake fuskata is enough evidence kin yarda.....?”

Fuzar da iska tai kafin ta kashe wayar ta nufi yanda motar tasa ke pake kaman zata tashi sama sabida tsananin huci da take....

Su Yusrah kam saidai hango k’allin mayafinta da sukai ta nufi wani wajen, Yusrah na kiran sunanta inaa ko tsayawa batai ba balle ta tankata...

Gaba d’aya suka murmusa suna fad’in “Nabila case ko ya tab’owa kansa kuma sai Allah....”

Yusra ta girgiza kai had’ida tab’e baki tace “K’awata ta kaina, ku k’yaleta zata dawo idan taje ta saita duk abinda ta taro, kaga Safwan ci gaba da ciremu daga ruwa kafin ta dawo tinda ance mutumin nan unannounced test yakeyi...”

Basu kuma bi takanta ba sukaci gaba da abinda suke....

Koda ta iso babban abinda yafi bata takaici shine ta kusan minti uku masu kyau tsaye a wajen Khalid baisan tama iso ba yana kwance cikin motarsa yana shan AC, sarai tasan salon wulak’ancinsa ne yana kallonta itace dai bata ganin sa tinda glass d’in motar mai duhu ne...

Kaman ta shige tai tafiyarta sai kuma ta shiga bubbuga masa glass d’in motar da iyaka k’arfinta....

A hankali ya shiga zuge glass d’in motar....

Lokaci guda ta d’ago idanu tana dubansa fuskarta kaman zata kurma ihu... Wani ni’imtaccen k’amshi ne had’ida tururin AC suka fara mata sallama kafin ta iya d’ago idanu tana dubansa

Kwanceccen murmushi ta hango saman kyakkyawan fuskarsa, idanunta na duban wajen ciwon nasa da yace bai warke ba, bata hango ciwon ba sai d’an sauran alamun tabo alamun ya gama healing, batasan dalili ba amma sai taji zuciyarta ta nastu da ganin ciwon nasa ya warke, tai saurin d’auke idanu daga duban nasa, fuska a tamke tace “Malam wai mai na maka da tsanani kake bibiyata...?”

D’an kauda kansa gefe kad’an yayi kana ya juyo yana kuma dubanta “First one has to say salam before anything else....”

A kaikaice ta kuma dubansa kana tace “Kaga Malam let’s settle this once and for all, Im pretty tired gida nakeson tafiya... You want money... Is that the only thing that matters....?” Tayi maganar cikin tsananin fad’a

Tinda ta soma magana yake dubanta ba tareda ko k’yafta idanu ba, sosai yakeso yaga mace na masifa irin haka, murmushi yayi da gefen bakinsa ba tareda ya katseta ba har ta ida masifan nata kana yace

“Of course not... I just want you to learn how not to go through life hurting beautiful innocent people....”

Baki sake take dubansa yanda yayi maganar babu ko alamun wasa tattareda shi...

Murmushin yak’e tai kana tace “I think that’s what you’ve to learn.... I came because you scared me... I’ve to see your wound...” Ta k’arashe murya can k’asan mak’oshi....

Da mamaki yake subanta kana ya fito da kanshi sosai yana kuma dubanta, murya a hankali ya furta “Just my wound...?” Yayi tambayar idanunsa a kanne sihirtaccen murmushi kwance saman fuskarsa...

Ganin irin duban da yake mata ya sanyata d’an daburcewa, a hasle ta kuma cewa dashi “Eh.. eh mana sabida na tabbatar ba 419 kazo kamin ba... If you don’t have more to say ni zan tafi friends d’ina na jirana....”

Tasa kai zata wuce tajiyo sautin muryarsa na ambaton sunanta a karo na biyu bayan kiran sunanta da yayi randa suka soma had’uwa....

“Nabeelah.....!”

Cak ta tsaya na wasu ‘yan dak’ik’ai kafin ta juyo a hasale tace “What again...!!!”

“We haven’t finished talking yet, idan da gaske kin gaji kuma gida kike son tafiya toh ki shigo na kaiki...”

Galala take dubansa kafin ta dawo da baya ta point kanta tana mai furta “Ni.. Na shiga wannan motar taka... Allah ya sawwak’e mun... Wait what do you think of me...?” Ta k’arashe tana mai d’aura hannu saman kunkumi...

Khalid ya kauda kai gefe had’ida rausayar da idanu bai tab’a zaton akwai macen da zatai ta gaya masa maganganu baijin zafinsu ba sai wannan yarinya mai d’an uban masifan....

Dawo da dubansa gareta yayi kana yace “Idan kinaso naje na sami Abbah ne fine kinsan har parlornsa na sani...” Ya k’arashe murya babu alamun wasa...

Cuno baki gaba tai tanaji kaman ta rufesa da duka don har yau batasan meye alak’ansa da mahaifinta ba gashi kuma har parlorn Abbah ta ganshi yana cin abinci...

Wannan karon murya k’asa k’asa tai maganar “Kaga an hanani shiga motar strangers idan kanaso mu k’arasa maganar nan kowama ya huta ka fito daga motarka mu k’arasa...

Yanda tai maganar cikin kwantar da murya sai ya masa banbarak’wai, da gefen bakinsa ya kuma murmusawa kana yace “No... Really, I’m scared of people ban saba da irin universities d’inku na nan ba...”

Baki sake take dubansa, lallai wannan babban d’an rainin hankali ne... A fili ta furta “You’re unbelievable....” Tasa kai abinta tayi wucewarta cikin sauri... Tuni shima ya tada motar ya shiga bin bayanta, A hanya suka had’uda Yusra ta gaji da jiranta don harsu Safwan sun wuce hostel...

Yusrah taga hamshak’iyar motar sai bin k’awarta take, kafin Yusrah tai magana Nabilah ta finciko hannunta tana fad’in “Kar kice komai wuce mu tafi...”

Yusrah na waige take fad’in “Ke dilla ki tsaya muga waye, why is he following you... Dan Allah Naby ki tsaya mu....”

Bata kai aya ba Khalid ya kuma shan gabansu da motar, Nabilah tazo wuya sabida tsananin k’uluwa ji take kaman ta d’au dutse ta kuma fasa masa gilashin mota....

Yusrah bata kuma sumewan tsaye ba saida ya shiga zuge gilashin motar ta hango matuk’un motar wanda har yafi motar had’uwa...

Fuska babu alamun wasa yace “Shige muje.....”

Harara kurum take galla masa kana tace “Too bad ban shiga...”

Yusra ta kalli wannan ta kalli wannan, nan ta shiga mintsilin Nabila tana fad’in “Kiyiwa Allah ki cecemu mu shiga motar nan...”

Nabila ta aika mata mugun kallo kana tace “Idan kin matsu kya shiga yakaiki daga nan yayi kud’i da kanki...” Ta kuma sa kai zata shige yace “Idan kinaso mu gama deal d’in once and for all kowa ya kama gabansa kina iya shiga motar, idan kuma yankan kai kike tsoro kaman yanda kikace har cikin gidan naku zan iya shiga...”

Kaman zata kurma ihu haka take dubansa, rai b’ace ta finciki marfin motar tayi shigewarta baya “You better keep your word..” , Yusrah ma sim sim ta shige d’aya side d’in tana mamakin ina Nabilah ta samo wannan had’edd’en guy d’in babu ko labari...

Kashe motar mai gaba d’aya yayi alamun idan ta dawo fronts eat zasu tafi....

A hasale ta kuma fincikar marfin motar ta koma gaba tasan idan bata dawo gaban ba haka zasuci gaba da tsayuwa gashi tuni la’asar ta shige....

Yusrah ta d’an kanne murya tana gaisheshi, tinda ya amsa a tak’ice bai kuma cewa komai ba, saima wayarsa data d’auki ruri, Siyama ce mai kiransa... Kaman bazai d’aga ba sai kuma ya d’aga, hannunsa guda na rik’eda waya guda kuma naga steering wheel...

Kaman baison maganar yace “Yes Siyaam....”

Daga d’aya b’angaren Siyama tace “Khalid we need to talk, is about Yesmin...”

Saida ya d’an fuzar da iska yana jiran traffic ya basu hannu kana yace “I’m busy right now.... We talk later...”

Yusrah kam tana daga baya tana k’arewa wannan miskili kallo da gani za’asha fama dashi, itakaw Nabila tinda taji ya ambaci sunan mace tabada k’eya tana duban window ko ba’a fad’i mata ba ta sani da budurwarsa yake waya, tayi k’wafa cikin zuciyarta tana mamakin duk wanda ta kasance budurwan wannan d’an rainin hankalin, don dagajin yanda yake maganawa budurwar ma ba dad’insa takeji ba, ta kuma tab’e baki ita kad’ai tana ayyanawa cikin zuciyarta ko maza sun k’are bazata tsaya da wannan d’an rainin sense d’in ba....

Tafiya kawai suke a motar babu mai cewa komai sai sassanyar music dake tashi cikin radio d’in motar, Yusrah dai tuni ta shiga shafa wayarta ana zuwa layin gidansu ta sanar dashi ga yanda zata sauk’a, ga mamakinta kaw harda sallama Khalid ya mata ya saci kallon Nabila dake sallama da k’awarta tana sanar da ita ta turo mata assignment question d’in Dr Man....

Bayan Yusrah ta fice Khalid yace “Mai ya hanaki kwafa a class sai ta waya za’a turo miki...?” Yayi maganar idanunsa naga kwalta

Da gefen idanu ta dubesa kafin ta kuma kawda kai tace “Ra’ayina ne...”

“Ba tareda ya dubeta ba shima yace “Ra’ayinki kokuma kina jira ayi solving a turo miki ba...”

A kufule take dubansa kafin ta kauda kai ba tareda ta kuma cewa komai ba don ta lura shi wannan zaman lafiya ne sam baiso a rayuwarsa tanson tambayarsa yanda ya sami lambarta da yanda akai yasan sch d’insu amma tasan bazataji mai dad’i ba kuma bazatai hak’uri bata rama ba kawai ta fasa tambayan nashi, ana isowa layinsu ta hangi ‘yan islamiya nakan faman tafiya bata k’aunan suyi artabo da magulmatan ‘yan gidansu don tasan idan suka ganta motar wani shikenan zance ya karad’a gidan har ya isa ga Abbanta...

Aiko suna tana fitowa daga motar ta hangi su Basma zasu tafi islamiya kuma sarai tasan sun ganta sai juyo suke ta danna masu harara suka wuce sim sim... Kotakan Khalid bata kuma bi ba tasa kai ta shige...

Ya kai dubansa ga kujeran data zauna nan ya hangi note book d’inta ta mance kuma da alama littafi ne mai d’aukeda courses daban daban...

Murmushi ya sake a hankali kafin yaja motarsa ya wuce yasan dole ta nemeshi ko don littafinta data mance....

Daga nan waya yayiwa Sameer yaji ko yana gida su gaisa, Sameer sai mamaki yake mai yake kawo Khalid Kano akai akai, nan dai Sameer d’in ke sanar dashi bai gida yana hospital...

****

Mamy na hankalce da yanayin Nabilar, duk yanda akai wani abun na damunta...

Suna zaune gaba d’aya a parlor da magrib Mamy ke tambayarta meke damunta...

“Mamy ba komai....” Ta fad’i tana mai shan jinin jikinta...

Jinjina kai Mamy tai kana tace “Idan ya dame ki kya fad’i...”

Nabilah da Marliya suka kalli juna Marliya na k’ok’arin had’iye dariyarta....

Misalin k’arfe 10pm ta gama shirin baccinta ta d’auko wayarta da niyyan yin assignment d’inta ta nemi littafinta ta rasa...

Cikin sauri ta shiga neman layin Yusrah tana tambayarta idan littafinta na tareda ita...

“Yusrah tace “Gaskiya baya wajena ban tsammanin na wajensu Safwan ma....”

Nabilah ta dafe kanta tana fad’in “Ya Salam, toh ina na jefar...”

Yusrah tace “Hey wait... Could it be a mortar mutumin nan kika bari ba...?”

Gaban Nabila ya yanke ya fad’i, saurin rintse idanunta tai tana tunanin tabbas ta yiwu a motar tasa ta mance...Ya Salam yanzu ya zatai ta ina zata soma nemansa...

Lambar da ya kirata dashi takai kai ta tsura masa idanu na lokaci... Kaman zatai dialing sai kuma ta fasa tai jifa da wayar saman gado tana mai jin haushin kanta dama ta yarda ta shiga motar tasa...

Cikeda masifa ita kad’ai take fad’in “No wllhi bazan kiraka ba... Oh I hate you..!” Ta k’arashe sakin k’ara...

Marliya dake bacci gadonta daga can gefe bud’e idanu tai a hankali tana tambayar Nabila meke faruwa....

A dak’ile Nabila ta kalleta ba tareda tace komai ba....

Kwanciya kawai tai don bazata iya yin assignment d’inba tinda duk working d’in na cikin littafinta...

Sanin cewa Mr Edward bai bari a zauna masa a aji ba tareda ganin littafinka ba kuma kana rubutu ya sata yanke shawarin kiran d’an rainin hankalin nan...

Yana ganin wayarta murmushi ya kufce masa, shi kad’ai yana kallon screen d’in wayar a zuciyarsa yana furta “I know you’ll call...”

Saida taji kaman ta katse kiran don takaici kafin ya d’aga..

Kishingid’a ya kumayi kana yace “So why is miss Grumpy calling me now..? Did you call to give me a goodnight scold or to ask me about my wound again......?”

Fuzar da iska tai kana tace “Don’t get wrong ideas, I call because I think I left my book in your car....”

Murmushi yayi don d’an rabuwan da sukayi na wasu mintoci har yaji kewar masifarta...

Saida ya d’an d’auki lokaci kaman bazaice komai ba yana iya jiyo hucinta kana yace “Oh really... Sabida tsaban bakiso deal d’inmu ya k’are shine saida kikayi kikasan yanda kika bar book d’inki a mota ta... Alright since you insist on seeing me zan kawo miki littafinki but as you can see is pretty late now, ko babu matsala...”

Murya na rawa kaman mai shirin kuka take fad’in “Think whatever you want to think nidai ka kawo min littafina...”

Mik’ewa sosai yayi ya zauna yana mamakin canzawan muryarta kana yace “Alright fine ki karb’i littafinki gobe a makaranta..”

Ta sauk’e ajiyan zuciya ba tareda tace komai ba,shiru ya gifta tsakaninsu na d’an lokaci kowa da abinda yake tunani kana yace “May I know where to keep the notebook...?” Wannan karon cikin kashe murya yayi maganar...

A sanyaye tace dashi “I’ve class by 8, just come straight to auditorium....” Daga nan bata kuma cewa komai ba sai katse wayar da tai...

Kallo yabi wayar dashi murmushi saman fuskarsa kafin ya shiga tura mata sak’o

_Too bad I’m not used to waking up early..._

Girgiza kai kurum tai had’ida jifa da wayan tasan wannan baza’a tab’a abin arziki dashi ba...

Washe gari sai raba idanu take tana neman ta yanda zata hangosa gashi har Malamin ya shiga aji...

Yusra na hankalce da ita don tasan kwanan zancen....

Mr Edward ya soma going round ya hangi mutum tsaye bakin k’ofa yana taking excuse

Nabila sai raba idanu take don tasan Allah ne ya taimaketa Mr Edward bai k’araso ta wajensu ba don bawai fad’ansa take tsoro ba attendance ne kawai bataso ta rasa...

Mr Edward ya baiwa mutumin izinin shigowa, daga mazan har matan fad’in had’uwarsa suke...

Nabila kam kanta na k’asa batasan wainar da ake toyawa ba saida Yusra ta shiga jjjigata tana fad’in “Ke tashi tashi kiga waye a nan...”

Nabila na d’ago kai sukai idanu hud’uda Khalid yana maganawa Mr Edward a hankali alamun ita yake tambaya...

“Oh there she’s mr...” Ya k’arashe yana pointing d’inta da littafin...

Jinjina kai Mr Edward yayi kana ya kirawo Nabila tazo ta amshi littafinta, gaba d’aya idanu akanta ta mik’e ta nufi gaban hall, kallon kallo sukewa juna har ta amshi littafin kafin ta koma ta zauna...

Suka kuma yin sallama da Mr Edward Khalid ya fice, sai mamaki take don batayi zaton ganinshi da uwar safiyan nan ba...

Tana zama Yusrah ta shiga mintsilinta tana fad’in “I told you if you matters to him zai kawo miki... see gashi yazo, dukda dai nada jin kai amma kun dace...”

Harara kawai Nabila ta aika mata kana ta shiga bud’e littafinta da tuni ya kama k’amshin turaren Khalid...

***

A daren Daddy yayi wayawa Khalid ya sanar dashi maza ya dawo Kaduna something came up at the company ana buk’atarsa...

Wasa wasa sabo na neman shiga tsakanin Nabila da Khalid dukda cewa ko ya kirata fad’a kawai suke, duk randa bai kira ba sai taji wani iri sai taji kaman ta kirashi koda zasuyi fad’an, har yanzu cikinsu babu wanda ya yarda yanajin wani abu gameda d’an uwansa..

Bikin Hafiz ne ya taso gadan gadan don tuni an shiga satin bikin, saidai har wannan lokaci Zulfah batada labari, Aunty B ce ta kirawo Mamy tana bata baki cewa kar ta d’aga hankalinta gameda Zulfah ma zatai mata magana yanda zata fahimta...

Mamy tai mata godiya sannan ta d’an sami sauk’i cikin zuciyarta...

Hakan kuwa akayi Aunty B tai maganawa Zulfa’u cikin natsuwa da kwantar da hankali had’ida nusar da ita duk abinda Allah ya k’addarawa bawa jarabawa ne, hak’uri shine riban rayuwar zaman duniya...

Dukda tawakkali da Zulfah tai labarin auren Hafiz sosai ya d’aga mata hankali, taci kuka har ta gode Allah k’arshe ta fawwala wa Allah lamuranta...

Ranar da ake jira tazo ranar auren Sawwama da Hafiz, tun safe marok’a ke busa algaita a gidan Magajiya, banda kad’e kad’e da raye raye ba’a komai...

A b’angaren Hajiya ma babu sauk’i d’anta zaiyi auren gata auren jin dad’i ba auren wahala ba irin wanda yayi a baya, basu samu sun koma wajen Malam nakan buzu ba sabida hidiman auren Hafiz da yasha kansu...

Da yammaci Magajiya ta rufo d’iyarta ta kawo don ko jiran ‘yan d’aukan amarya bata tsayayi ba kafin ‘yan d’auka suzo munafukan unguwarsu su zayyane masu wacece Sawwama a fasa aure...

Su Hajiya suna tsaka da hidima sai sautin gud’e gud’e suka soma jiyowa Sa’adu Gurmi na gefe yana kad’ada gurmi Magajiya na gaba tana taka rawa d’aurin kallabi a gefe ga mayafi a kafad’a, tana tafe tana rawa har k’asa k’awayenta na biyeda ita rik’eda Sawwama cikin lullub’i..

Kowa ya daina abinda yake yana kallon ikon Allah...




SameenaAleeyou 📚
*INDA RAI*
_...............DA RABO_


*25*


*©Sameena Aleeyou...✍🏽*



Fatan Alheri gareku🤝

Haleematu Maikeke
Sadiya Auwal Z
BabyMahe
Farida S Maina
Maman Najwa
Deejoh Omar
Fatee Beni
Maryam Mu’azu

Alherin Allah yakai maku🥰





Hajiya da kanta zaune dirshan tai tsakar gidan tana kallon ikon Allah, ita ko a fina finai bata tab’a gani ko jin yanda akace uwar amarya ta rufo d’iyarta ta kawo ba tareda anje an amshi amarya ba...

Aunty Lami ta d’an tab’a Hajiya kana tace “Haule yau ina ganin bariki tsirarta, yo ni duk zaman danayi a bariki ai ban tab’a cin karo da irin haka ba, anya kaw Haule ba ruwan dafa kanki kika d’ebo ba...?”

Hajiya ta yatsina fuska kana tace “Haba Lami ya kike magana haka kaman baki sanni ba, yo ni ai walki ce daidai da uban kowa, ke nifah duk wanda sukazo dashi toh billahillazi shi zamuyi, kinga kafin su raina mana tashi mu tayasu tik’ar rawar, don wllhi nafi kowa jin dad’in auren nan...” Ta k’arashe tana mai shan d’amara da mayafinta... Haba nan fah fili ya kuma kacamewa uwar ango da amarya sai tik’ar rawa suke kowacce tanaso ta burge, idan Magajiya tayi k’asa Hajiya tai sama haka zalika idan Hajiya tai k’asa Magajiya tai sama nan fah k’awayen ko wacce ta shiga burge abokiyarta da lik’i... Mai Gurmi kaw mai zaiyi banda yaci gaba da kad’a masu gurmi yana washe su had’ida tattaran

Please Login or Register in order to submit comment